PHPWord

 

نُبذَةٌ فِي العَقِيدَةِ الإِسْلَامِيَّة

(شَرْحُ أُصُولِ الإِيمَانِ)

 

TAKAITACCEN BAYANI AKAN AKIDAR MUSULUNCI

(SHARHIN TUSHEN IMANI)

بِقَلَم فَضِيلَة الشَّيخ العَلَّامَة

مُحَمَّدِ بْنِ صَالِحٍ العُثَيمِين

غَفَرَ اللَّهُ لَهُ وَلِوَالِدَيْهِ وَلِلْمُسْلِمِين

Na

Babban malami mai yawan sani

Muhammad bn Saleh al-Usaimeen

Allah Ya yi masa gafara shi da mahaifan sa da musulmai

 

 

 

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيم

TAKAITACCEN BAYANI AKAN AKIDAR MUSULUNCI

Wallafar babban malami mai yawan sani

Muhammad bn Saleh al-Usaimeen

Allah Ya yi masa gafara shi da mahaifan sa da musulmai.

Da sunan Allah Mai rahama Mai jin ƙai

GABATARWA

Haƙiƙa godiya ta tabbata ga Allah, muna gode maSa, muna neman taimakonSa, muna neman gafararSa, muna tuba zuwa gareShi, muna neman tsarin Allah daga sharrukan kawunanmu, da kuma munanan ayyukanmu, Duk wanda Allah Ya shiryar da shi, babu mai ɓatar da shi, kuma wanda Ya ɓatar babu mai shiryar da shi, ina shaida cewa babu wani abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kaɗai yake, baShi da abokin tarayya, Kuma ina shaida cewa (Annabi) Muhammad bawanSa ne kuma ManzanSa ne, Allah Yayi tsira a gare shi da alayensa da sahabbansa, da waɗanda suka biyo su da kyautatawa, Yayi aminci amincewa.

Bayan haka: Haƙiƙa (Ilimin kaɗaita Allah) (shi ne) Mafi ɗaukakar ilimai, kuma mafi girmansu a daraja, mafi wajabcinsu a nema, domin shi ilimin sanin Allah - Maɗaukakin sarki - ne, da sunayenSa, da siffofinSa, da haƙƙoƙinsa akan bayinSa, kuma domin shi mabuɗin hanya ne zuwa ga Allah - Maɗaukakin sarki -, kuma ginshiƙin shari'oinSa ne.

Saboda haka: Manzanni sun haɗu akan kira zuwa gare shi, Allah - Maɗaukakin sarki - Yace:

﴿وَمَآ أَرۡسَلۡنَا مِن قَبۡلِكَ مِن رَّسُولٍ إِلَّا نُوحِيٓ إِلَيۡهِ أَنَّهُۥ لَآ إِلَٰهَ إِلَّآ أَنَا۠ فَٱعۡبُدُونِ25﴾

{Kuma ba Mu aiki wani Manzo ba a gabãninka fãce Munã yin wahayi zuwa gare shi, cẽwa "Lalle ne Shi, bãbu abin bautãwa da gaskiya fãce , sai ku bauta Mini} [al-Anbiyaa: 25].

Kuma Allh Maɗaukakin sarki Ya shaidarwa kanSa da kaɗaitaka, kuma mala'kunSa sun shaidar maSa da ita, da ma'abota sani, Allah - Maɗaukakin sarki - Yace:

﴿شَهِدَ ٱللَّهُ أَنَّهُۥ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ وَٱلۡمَلَٰٓئِكَةُ وَأُوْلُواْ ٱلۡعِلۡمِ قَآئِمَۢا بِٱلۡقِسۡطِۚ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡحَكِيمُ 18﴾

{Allah Ya shaida cewa, Shi babu abin bautawa da gaskiya sai Shi kuma mala'iku da ma'abota sani (suma sun shaida) Yana mai tsayuwa da adalci, babu abin bautawa da gaskiya sai Shi Mabuwayi Gwani) [Aal Imran: 18].

Yayin da ya kasance wannan shi ne sha'anin tauhidi (kaɗaita Allah) to ya zama wajibi akan kowanne musulmi ya kula da shi a koyo da koyarwa, da bibbiya, da ƙudircewa, dan ya gina addininsa akan kuɓutaccen ginshiƙi, da nutsuwa da miƙa wuya, har ya azurtu da fa'dodinsa, da sakamakonsa.

Allah Shi ne majiɓincin datarwa.

Mawallafi

***

ADDININ MUSULUNCI

Addinin musulunci: Shi ne Addinin da Allah wanda Ya aiko (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da shi, kuma Allah Ya cika Addinai da shi, Ya cika shi ga bayinSa, Ya kuma cika ni'ima a gare su da shi, Ya yarda da shi a garesu a matsayin Addini, ba ya karɓar wani Addini daga wani in ba shi ba, Allah - Maɗaukakin sarki - Yace:

﴿مَّا كَانَ مُحَمَّدٌ أَبَآ أَحَدٖ مِّن رِّجَالِكُمۡ وَلَٰكِن رَّسُولَ ٱللَّهِ وَخَاتَمَ ٱلنَّبِيِّـۧنَۗ وَكَانَ ٱللَّهُ بِكُلِّ شَيۡءٍ عَلِيمٗا40﴾

{Muhammadu bai kasance uba ga wani daga mazajenku ba, sai dai Manzon Allah ne kuma cikamakin Annabawa, Allah Ya kasance Masani ne ga dukkan komai} [al-Ahzab: 40].

Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce:

﴿...ٱلۡيَوۡمَ أَكۡمَلۡتُ لَكُمۡ دِينَكُمۡ وَأَتۡمَمۡتُ عَلَيۡكُمۡ نِعۡمَتِي وَرَضِيتُ لَكُمُ ٱلۡإِسۡلَٰمَ دِينٗاۚ...﴾

{Kuma yau ne Na cika muku Addininku, kuma Na cika muku ni'amarku, kuma Na yarje muku Musulunci a matsayin Addini} [al-Ma'ida: 3].

Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce:

﴿إِنَّ ٱلدِّينَ عِندَ ٱللَّهِ ٱلۡإِسۡلَٰمُ...﴾

{Lallai kaɗai Addini a wajen Allah shi ne Musulunci} [Aal-Imran: 19].

Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce:

﴿وَمَن يَبۡتَغِ غَيۡرَ ٱلۡإِسۡلَٰمِ دِينٗا فَلَن يُقۡبَلَ مِنۡهُ وَهُوَ فِي ٱلۡأٓخِرَةِ مِنَ ٱلۡخَٰسِرِينَ85﴾

{Kuma wanda ya nẽmi wanin Musulunci ya zama addini, to, a karɓa daga gare shi ba. Kuma shi a Lãhira yana daga cikin mãsu hasãra} [Aal-Imran: 85].

Kuma haƙiƙa Allah - Maɗaukakin sarki - Ya farlanta akan dukkanin mutane, da su bautawa Allah - Maɗaukakin sarki - da shi, sai Ya ce Yana yi wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi magana:

﴿قُلۡ يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ إِنِّي رَسُولُ ٱللَّهِ إِلَيۡكُمۡ جَمِيعًا ٱلَّذِي لَهُۥ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۖ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ يُحۡيِۦ وَيُمِيتُۖ فَـَٔامِنُواْ بِٱللَّهِ وَرَسُولِهِ ٱلنَّبِيِّ ٱلۡأُمِّيِّ ٱلَّذِي يُؤۡمِنُ بِٱللَّهِ وَكَلِمَٰتِهِۦ وَٱتَّبِعُوهُ لَعَلَّكُمۡ تَهۡتَدُونَ 158﴾

{Ka ce: Ya ku mutane lalle Ni manzon Allah ne zuwa gare ku baki ɗaya, wanda mulkin sammai da ƙassai suka tabbata a gare Shi, babu abin bautawa da gaskiya sai Shi, Yana rayawa kuma Yana kashewa, ku yi imani da Allah da ManzonSa Annabi ummiyyi wanda Ya yi imani da Allah da kalmominsa ku bi Shi domin ku shiriya} [Al-A'araf: 158].

Kuma ya zo a ckin Sahihu Muslm; daga Abi Huraira- Allah Ya yarda dashi- daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa shi ya ce: " Na rantse da wanda ran Muhammad yake a hannunSa, babu wani da zai ji (bayanin abinda na zo da shi) daga wannan al'umma, Bayahude ne ko Banasare, sannan ya mutu bai yi imani da abinda aka aikoni da shi ba, face sai ya kasance daga ma'aboata wuta".

Kuma imani da shi: (shi ne) gasgata abinda ya zo da shi tare da karɓa da miƙa wuya, ba kawai gasgatawa ba, saboda wannan ne Abu Ɗalib bai kasance mai bada gaskiya da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a garea shi - ba, tare da gasgatawarsa ga abinda ya zo da shi, da kuma shaidawarsa da cewa shi (Musulunci) yana daga mafificin Addinai.

Addinin Musulunci: Mai ƙunsar dukkanin maslahohine, waɗanda Addinan da suka gabata suka ƙunsa, mai keɓentuwa ne a kansu da kasancewarsa, shi wanda ya dace ne da dukkan zamani da al'umma, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce Yana mai magana da ManzonSa:

﴿وَأَنزَلۡنَآ إِلَيۡكَ ٱلۡكِتَٰبَ بِٱلۡحَقِّ مُصَدِّقٗا لِّمَا بَيۡنَ يَدَيۡهِ مِنَ ٱلۡكِتَٰبِ وَمُهَيۡمِنًا عَلَيۡهِ...﴾

{Mun saukar da Littafi zuwa gareka da gaskiya, mai gasgatawa ga abinda ya gabace shi na daga Littafi, kuma mai shaida akansa} [al-Ma'ida: 48].

Ma'anar kasancewarsa wanda ya yi daidaine da kowanne zamani da guri da al'umma: cewa riƙo da shi, ba ya kore maslahar al'umma a kowanne zamani, ko gari, a'a shi ne ingantuwarsu, ma'anar haka, bai zamo cewa shi mai bi ne ga kowanne zamani da guri da al'umma ba, kamar yadda sashin wasu mutane suke nufin shi. (Wato shi ake bi a kowanne Lokaci da wuri).

Addinin musulunci: shi ne Addinin gaskiya, wanda Allah - Maɗaukakin sarki - Ya lamincewa wanda ya yi rIƙo da shi, riƙo na gaskiya, cewa zai taimake shi Ya kuma ba shi rinjaye akan waninsa, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce:

﴿هُوَ ٱلَّذِيٓ أَرۡسَلَ رَسُولَهُۥ بِٱلۡهُدَىٰ وَدِينِ ٱلۡحَقِّ لِيُظۡهِرَهُۥ عَلَى ٱلدِّينِ كُلِّهِۦ وَلَوۡ كَرِهَ ٱلۡمُشۡرِكُونَ 9﴾

{Shi ne wanda Ya aiko manzonSa da shiriya da addinin gaskiya, dõmin ya bayyana shi a kan addini dukansa, kuma mushirikai sun ƙi.} {al-Ssaf:9}.

Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce:

﴿وَعَدَ ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ مِنكُمۡ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ لَيَسۡتَخۡلِفَنَّهُمۡ فِي ٱلۡأَرۡضِ كَمَا ٱسۡتَخۡلَفَ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡ وَلَيُمَكِّنَنَّ لَهُمۡ دِينَهُمُ ٱلَّذِي ٱرۡتَضَىٰ لَهُمۡ وَلَيُبَدِّلَنَّهُم مِّنۢ بَعۡدِ خَوۡفِهِمۡ أَمۡنٗاۚ يَعۡبُدُونَنِي لَا يُشۡرِكُونَ بِي شَيۡـٔٗاۚ وَمَن كَفَرَ بَعۡدَ ذَٰلِكَ فَأُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡفَٰسِقُونَ 55﴾

{Allah Ya yi wa'adi ga waɗanda suka yi ĩmãni daga gare. Ku, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, lalle zai shugabantar da su a cikin ƙasa kamar yadda Ya shugabantar da waɗanda suke daga gabãninsu, kuma lalle ne zai tabbatar musu da addininsu wanda Ya yardar musu, kuma lalle ne Yanã musanya musu daga bãyan tsõronsu da aminci, sunã bauta Mini su haɗa kõme da . Kuma wanda ya kãfirta a bãyan wannan, to, waɗancan, su ne fãsiƙai}. {al-Nur: 55}

Addinin Musulunci: Aƙidane da shari'a, shi cikakke ne a aƙidarsa da kuma shari'arsa:

1- Yana umarni da kaɗaita Allah- Maɗaukakin sarki- yana kuma hani ga shirka.

2- Yana umarni da gaskiya kuma yana hana ƙarya.

3- Yana umarni da adalci kuma yana hani daga zalunci, adalci shi ne dai-daitawa tsakanin masu kamanceceniya da kuma rabewa tsakanin masu sassaɓawa. Adalci bai zamo tsan-tsar dai-daitawa ba, kamar yadda wasu sashin mutane suke furici da shi, yayin da yake cewa: Addinin Musulunci Addinin dai-daitawa ne, kuma ya saki (maganar), domin lalle dai-daitawa tsakanin abubuwan da suka sassaɓa zalunci ne, Musulunci ba ya zuwa da shi, kuma ba ya yabon mai aikata shi.

4- Yana umarni da amana kuma yana hani daga ha'inci.

5- Yana umarni da cika alƙawari kuma yana hani daga yaudara.

6- Yana umarni da biyayya ga mahaifa kuma yana hani ga saɓa (musu).

7- Yana umarni da sada zumunci, su ne makusanta kuma yana hani daga yanke (zumunci).

8- Yana umarni da kyautata maƙwabtaka, kuma yana hani ga munanata.

Gamammiyar magana ita ce: Haƙiƙa (Musulunci) yana umarni da dukkan ɗabi'a mai falala; yana kuma hani ga dukkan ɗabi'a maƙasƙanciya, yana umarni da dukkan aiki na gari, kuma yana hani akan dukkan mummunan aiki.

Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce:

﴿إِنَّ ٱللَّهَ يَأۡمُرُ بِٱلۡعَدۡلِ وَٱلۡإِحۡسَٰنِ وَإِيتَآيِٕ ذِي ٱلۡقُرۡبَىٰ وَيَنۡهَىٰ عَنِ ٱلۡفَحۡشَآءِ وَٱلۡمُنكَرِ وَٱلۡبَغۡيِۚ يَعِظُكُمۡ لَعَلَّكُمۡ تَذَكَّرُونَ 90﴾

{Lalle Allah yin umurni da ãdalci da kyautatãwa, da bai wa ma'abũcin zumunta, kuma yanã hani ga alfãsha da abin da aka ƙi da zalinci. Yanã yi muku gargaɗi, ɗammãnin ku, kunã tunãwa} [al-Nahl: 90].

***

RUKUNAN MUSULUNCI

Rukunanan musulunci: Ginshiƙansa waɗanda yake ginuwa a kansu, su biyar ne: Waɗanda aka ambata a cikin abinda Ibn Umar- Allah Ya yarda da su - ya ruwaito su daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa shi ya ce: "An gina Musulunci abisa abubuwa biyar: Abisa ya kaɗaita Allah- a cikin wata ruwaya kuma abisa abubuwa biyar -: Shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma haƙiƙa (Annabi) Muhammad bawanSa ne kuma ManzanSa ne, da tsaida sallah, da ba da zakka, da azumin watan Ramadan da Hajji". Sai wani mutum ya ce: Hajji da azumin Ramadan? ya ce: "A'a, Azumin Ramadana da Hajji" haka ya ji shi daga Manzan Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

1-Amma shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma (Annabi) Muhammad bawanSa ne kuma ManzanSa ne shi ne:

Kudircewa a yanke wacce za'a bayyanar da wannan shahadar da harshe, kamar cewa shi da yankewarsa a hakan mai shaidawa ne agare shi, kaɗai an sanya wannan shaidawar rukuni guda ɗaya tare da abin shaidawar da shi fiye da ɗaya.

Ko dai: Cewa Manzo - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - mai isarwa ne daga Allah - Maɗaukakin sarki -, shaidawa a gare shi da bauta da kuma manzanci yana daga cikar shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah.

Ko kuma dai: Saboda waɗannan shaidawa guda biyu su ne ginshiƙin ingancin ayyuka da kuma karɓarsu, domin babu inganci ga wani aiki ko karɓa sai da ikhlasi ga Allah - Maɗaukakin sarki -, da kuma biyayya ga ManzanSa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.

Da ikhlasi ne ga Allah shaidawa take tabbatuwa: Cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma da biyayya ga Manzan Allah ne shaidawa take tabbata: Cewa (Annabi) Muhammad bawanSa ne kuma ManzanSa ne.

Yana daga fa'idodin wannan shaidawar mai girma: 'Yantar da zuciya da rai daga bauta ga ababan halitta, kuma daga bin wanin Manzanni.

2- Amma tsaida sallah: To shi ne bauta ga Allah- Maɗaukakin sarki- da zai aikata ta a bisa fuskar daidaituwa da cika a lokutanta, da kuma yadda take.

Yana daga fa'idodnsa: Yalwatuwar ƙirji, da sanyin ido, da hana alfasha da abin ƙi.

3- Amma bada zakka: Shi ne bauta ga Allah - Maɗaukakin sarki - da bada gwargwadan wajibi a dukiyoyi na zakka waɗanda suka cancanta.

Yana daga fa'idodinsa: Tsarkake rai daga ƙasƙantacciyar ɗabi'a (rowa) da biyan buƙatar Musulunci da musulmai.

4- Amma kuma Azumin watan Ramadan: shi ne bauta ga Allah -Maɗaukakin sarki - da kamewa daga abubuwa masu karya (azumi) da rana a Ramadana.

Yana daga fa'idodinsa: Horar da rai a bisa barin abubuwan so, dan neman yardar Allah - Mai girma da ɗaukaka -.

5- Amma ziyartar Ɗakin Allah: Shi ne bauta ga Allah- Maɗaukakin sarki - da nufin Ɗaki mai alfarma dan aikata alamomin (ayyukan) Hajji.

Yana daga fa'idodinsa: Horar da rai a kan bada dukiya da aka tara da karfin jiki a wajen biyayyar Allah - Maɗaukakin sarki - da wannan ne Hajji ya kasance wani nau'i na jihadi akan tafarkin Allah - Maɗaukakin sarki -.

Waɗannan fa'idodin waɗanda muka ambace su, na waɗannan ginshiƙan, dama waɗanda ba mu ambace su ba, suna sa al'umma (su zamo) al'umma ta Musulunci tsarkakkiya mai tsarkaka, tana yin Addini ga Allah Addini na gaskiya, tana kuma mu'amalantar halitta da adalci da kuma gaskiya. Domin abinda ba su ba daga shari'oin Musulinci, yana ingantuwa ne da ingantuwar waɗannan ginshiƙan, kuma halayen al'umma suna ingantuwa da ingantuwar Addininta, kuma ingantuwar halayensu yana tsere mata ne, da gwargwadan abinda ya tsere mata na daga ingantuwar al'amuran Addininta.

Wanda yake son ƙarin bayanin haka, to ya karanta faɗinSa - Allah Maɗaukakin sarki -:

﴿وَلَوۡ أَنَّ أَهۡلَ ٱلۡقُرَىٰٓ ءَامَنُواْ وَٱتَّقَوۡاْ لَفَتَحۡنَا عَلَيۡهِم بَرَكَٰتٖ مِّنَ ٱلسَّمَآءِ وَٱلۡأَرۡضِ وَلَٰكِن كَذَّبُواْ فَأَخَذۡنَٰهُم بِمَا كَانُواْ يَكۡسِبُونَ 96 أَفَأَمِنَ أَهۡلُ ٱلۡقُرَىٰٓ أَن يَأۡتِيَهُم بَأۡسُنَا بَيَٰتٗا وَهُمۡ نَآئِمُونَ 97 أَوَأَمِنَ أَهۡلُ ٱلۡقُرَىٰٓ أَن يَأۡتِيَهُم بَأۡسُنَا ضُحٗى وَهُمۡ يَلۡعَبُونَ98 أَفَأَمِنُواْ مَكۡرَ ٱللَّهِۚ فَلَا يَأۡمَنُ مَكۡرَ ٱللَّهِ إِلَّا ٱلۡقَوۡمُ ٱلۡخَٰسِرُونَ99﴾

{Da a ce ma'abota alƙaryu sun yi imani kuma sun ji tsoran Allah, lalle da mun buɗe musu albarkatu daga sama da ƙasa, sai dai sun ƙaryata, sai muka kamasu da abinda suka kasance suke tsururuta, shin ma'abota alƙaryu sun amintu azabarmu ta zo musu da daddare alhalin suna barci, shin ma'abota alƙaryu sun amintu azabarmu ta zo musu da hantsi alhalin suna wasa, shin sun amintu da makircin Allah, babu wanda yake amintuwa da makircin Allah sai mutane masu hasara} {al'Aaraf: 96-99}.

Ya yi duba a tarihin waɗanda suka gabata, haƙiƙa tarihi izina ne ga ma'abota hankula, kuma abin la'akari ne ga wanda shamaki bai tsare zuciyarsa ba, Allah Shi ne abin neman taimako.

***

GINSHIKAN AKIDAR MUSULUNCI

Addinin Musulunci:-Kamar yadda muka bayyana a baya- aƙida ne da shari'a, haƙiƙa mun yi nuni zuwa wani abu daga shari'o'nsa, kuma mun ambaci rukunansa waɗanda ake la’akari da su ginshiƙai ga shari'o'insa.

Amma aƙidar Musulunci, ginshiƙanta: Imani da Allah, da mala'ikunSa, da littatafanSa da manzanninSa da ranar lahira, da ƙaddara alkhairinsa, da sharrinsa.

Haƙiƙa littafin Allah da sunnar ManzanSa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sun yi nuni a bisa waɗannan ginshiƙan.

Acikin littafin Allah - Allah Maɗaukakin sarki - Yana cewa:

﴿لَّيۡسَ ٱلۡبِرَّ أَن تُوَلُّواْ وُجُوهَكُمۡ قِبَلَ ٱلۡمَشۡرِقِ وَٱلۡمَغۡرِبِ وَلَٰكِنَّ ٱلۡبِرَّ مَنۡ ءَامَنَ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِ وَٱلۡمَلَٰٓئِكَةِ وَٱلۡكِتَٰبِ وَٱلنَّبِيِّـۧنَ...﴾

{Ku fuskantar da fuskokinku ɓangaren gabas da yamma bai zamo kawai biyayya ba, sai dai biyayya wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira da mala'iku da littafi da Annabawa} [al-Baƙara: 177], Yana cewa akan ƙaddara:

﴿إِنَّا كُلَّ شَيۡءٍ خَلَقۡنَٰهُ بِقَدَرٖ 49 وَمَآ أَمۡرُنَآ إِلَّا وَٰحِدَةٞ كَلَمۡحِۭ بِٱلۡبَصَرِ 50﴾

{Haƙiƙa mu kowanne abu mun halicce shi da gwargwado (da muka ƙaddara shi) lamarun mu bai zamo ba, sai (kalma) ɗaya kamar ƙiftawa da ido} {Kamar: 49-50}.

A cikin sunnar Manzan Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- Yana amsawa Jibrila lokacin da ya tambaye shi game da imani: "Imani: (shi ne) ka yi imani da Allah, da mala'ikunSa da littattafanSa, da manzanninSa, da ranar lahira, kuma ka yi imani da ƙaddara: alkhairinta da sharrinta".

***

Imani da Allah - Maɗaukakin sarki -:

Amma imani da Allah, yana ƙunsar abubuwa ne guda huɗu:

Abu na farko: Imani da samuwar Allah - Maɗaukakin sarki -:

Haƙiƙa kyakyyawar Ɗabi’a, da hankali da shari'a, da riska ta sarari, sun yi nuni a bisa samuwarSa - Allah Maɗaukakin sarki -

1- Amma nunin halitta ta asali a bisa samuwarSa- tsarki da ɗaukaka sun tabbata a gare Shi -: Haƙiƙa dukkan abin halitta an halicce shi ne akan imani da mahaliccinsa, ba tare da rigayar tunani ba, ko koyarwa, babu wanda zai juya ya bar abinda wannan halitta ta asali ta hukuntar, sai wanda abinda zai juyar da shi daga gare ta ya ɗarsu akan zuciyarsa; Saboda faɗar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: "Babu wani abin haihuwa face ana haihuwarsa akan ɗabi'a ta musulinci, sai dai iyayensa su mai da shi Bayahude, ko su maida shi Banasare, ko su maida shi mai bautar wuta (mushiriki)".

2- Amma nunin hankali a bisa samuwar Allah - Maɗaukakin sarki - domin cewa waɗannan abubuwan halitta: waɗanda suka gabata da waɗanda za su zo, babu makawa suna da wani mahalici da Ya samar da su, domin ba zai yuwu ba, su samar da kansu da kansu, kuma ba zai yuwu ba su samu haka kwatsam.

Ba zai yuwu ba, su samar da kansu da kansu: domin wani abu ba ya halittar kansa, domin kafin samuwarsa rasasshe ne, to ta yaya zai kasance mahalicci?!

Ba kuma zai yuwu ba, su samu katsahan, domin dukkan fararre lalle ba makawa akwai wanda ya farar da shi, kuma domin cewa samuwarta a bisa wannan tsari mai ƙayatarwa, da jerantuwa mai ɗanfaruwa, da haɗuwa mai cuɗanyuwa tsakanin dalilai da abubuwan da suke haifar da su, da kuma tsakanin kasantattuwa sashinsu tare da sashi, (hakan) zai hana hani yankakke samuwarsu ta kasance katsahan, domin abin samarwa ta hanyar katsahan ba ya zamowa akan tsari a asalin samuwarsa, to ta yaya zai kasance tsararre a halin wanzuwarsa da ci gabansa?!

Idan ba zai yuwu ba cewa waɗannan ababan halitta su samar da kansu da kansu, ko kuma su samu katsahan, to ya tabbata cewa akwai wanda ya samar da su, shi ne Allah Ubangijin talikai.

Haƙiƙa Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ambaci wannan dalili na hankali, da hujja yankakkiya a cikin surar al-Ɗur; a inda Ya ce:

﴿أَمۡ خُلِقُواْ مِنۡ غَيۡرِ شَيۡءٍ أَمۡ هُمُ ٱلۡخَٰلِقُونَ 35﴾

{Ko an haliccesu ne ba daga wani abu (da Ya halitta ba) ko su ne masu halitta} [al-Ɗur: 35]. Yana nufin: Cewa su ba'a haliccesu ba ba tare da Mahalicci ba, ba kuma su ne suka halicci kawunansu ba; to ya tabbata cewa Mahaliccinsu Ya kasance shi ne Allah - Mai girma da ɗaukaka -. Saboda wannan ne, ya yin da Jubairu bn Muɗ'im - Allah Ya yarda da shi - ya ji Manzan Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana karanta Surat al-Ɗur sai ya kai ga waɗannan ayoyin:

﴿أَمۡ خُلِقُواْ مِنۡ غَيۡرِ شَيۡءٍ أَمۡ هُمُ ٱلۡخَٰلِقُونَ 35 أَمۡ خَلَقُواْ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَۚ بَل لَّا يُوقِنُونَ 36 أَمۡ عِندَهُمۡ خَزَآئِنُ رَبِّكَ أَمۡ هُمُ ٱلۡمُصَۜيۡطِرُونَ 37﴾

{Ko an haliccesu ba daga wani abu (da Ya haliccesu ba) ko su ne masu halitta, ko sun halicci sammai da ƙassai, ba hakaba, ba sa sakan-kancewa, ko akwai taskokin Ubangijinka a gurinsu, ko sune masu rinjaye} [al- Ɗur: 35-37].

Jubairu ya kasance a wannan lokacin mushiriki ne ya ce: "Zuciyata ta kusa ta fashe, hakan shi ne farkon abinda ya tabbatar da imani a cikin zuciyata".

Mu buga misali da zai bayyanar da haka: Cewa da ace wani mutum zai ba ka labarin wani katafaren gida mai tsawo, da lambuna suka kewaye shi, kuma ƙoramu suke gudana a tsakaninsu, kuma an cika shi da shimfiɗu da gadaje, an kuma ƙawata shi da nau'oin ado daga masu tabbatar da shi da kuma cika shi, ya kuma ce da kai: Haƙiƙa wannan katafaren gida da abinda yake cikinsa na daga cika, haƙiƙa ya samar da kansa ne, ko ya samu hakanan kwatsam, ba tare da mai samawarwa ba, da ka yi gaggawan musun hakan, da kuma ƙaryata shi, kuma ka ɗauki zancensa wauta ta magana, shin zai yi wu bayan haka, wannan kasantacce mai faɗi ya kasance: da ƙasarsa da samansa da taurarinsa, da halayensa, da tsarinsa mai ƙayatarwa mai rinjaye, ya samar da kansa, ko ya samu kwatsam ba tare da mai samarwa ba?!

3- Amma dalilai na Shari'a a bisa samuwar Allah - Maɗaukakin sarki -; domin cewa dukkanin littattafan sama, suna furici da haka: da abinda suka zo da shi na daga hukunce-hukunce na adalci waɗanda suka ƙunshi maslahohin halitta, dalili ne a bisa cewa, su daga Ubangiji Gwani Masani da maslahohin halittarSa suke, da abinda suka zo da shi na daga labarai na kasantacce waɗanda waƙi'i ya shaida da gaskiyarsu, dalili ne a bisa cewa su daga Ubangiji Mai iko a bisa samar da abinda Ya bada labari da shi suke.

4- Amma dalilan riska ta sarari a bisa samuwar Allah - Maɗaukakin sarki -: To tana daga fuskoki biyu:

Ɗaya daga cikinsu: Cewa mu muna ji kuma muna gani na amsawa masu roƙo da agazawa masu neman dauki, abinda yake nuni nuni yankakke a bisa samuarSa - Maɗaukakin sarki -, Allah - Maɗaukakin Ya ce:

﴿وَنُوحًا إِذۡ نَادَىٰ مِن قَبۡلُ فَٱسۡتَجَبۡنَا لَهُۥ...﴾

[Ka ambaci Nuhu ya yin da Ya kira kafin (Annabawan da aka ambata) sai Muka amsa masa} [al-Anbiya: 76] Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {A ya yin da kuke neman agajin Ubangijinku sai Ya amsa muku} [al-Anfal: 9].

Kuma a cikin Sahihul Bukhari daga Anas bn Malik- Allah Ya yarda da shi - ya ce: Haƙiƙa wani balaraban ƙauye ya shigo ranar Juma'a - alhalin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana huɗuba- sai ya ce: Ya Manzan Allah dukiya ta halaka iyalai sun yunwata, ka roƙar mana Allah; sai ya ɗaga hannayensa ya yi addu'a, sai girgije ya ta so ya yaɗu, kamar duwatsu, bai gushe ba akan mimbarinsa, har naga ruwan sama yana ɗiga daga gemunsa.

A cikin kuma Juma'a ta biyu, sai wannan balaraben ƙauyen ya tashi, ko waninsa ya ce: Ya Manzan Allah, gini ya rushe, kuma dukiya ta dulmiye, ka roƙar mana Allah, sai ya ɗaga hannayensa, kuma tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Ya Allah a gefunanmu ba akanmu ba". Ba ya nuna wata nahiya face sai ta yaye.

Kuma amsawar masu Addu’a bai gushe wani lamari abin shaidawa ba (gani) zuwa wannan zamaninmu, ga wanda ya gasgata fakewa da miƙa lamarinsa ga Allah- Maɗaukakin sarki - ya kuma zo da sharuɗɗan amsawa.

Fuska ta biyu: Haƙiƙa ayoyin Annabawa waɗanda ake kiransu da mu'ujizozi, kuma mutane suke ganinsu, ko suke jin su hujja ce yankakkiya a bisa samuwar Mai aiko su, Shi ne Allah - Maɗaukakin sarki -; domin su wasu al'amura ne da suka fita (wuce) ikon ɗan Adam, Allah - Maɗaukakin sarki - Yana gudanar da su, dan ƙarfafawa ga ManzanninSa da kuma taimako a gare su.

Misalin haka: Mu'ujizar (Annabi) Musa- amincin Allah ya tabbata a gare shi - Allah - Maɗaukakin sarki - Ya umarce shi da ya buga sandarsa akan kogi, sai ya buga ta, sai ya tsage goma sha biyu hanya bushasshiya, ruwa kuma a tsakaninsu kamar duwatsu, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce:

﴿فَأَوۡحَيۡنَآ إِلَىٰ مُوسَىٰٓ أَنِ ٱضۡرِب بِّعَصَاكَ ٱلۡبَحۡرَۖ فَٱنفَلَقَ فَكَانَ كُلُّ فِرۡقٖ كَٱلطَّوۡدِ ٱلۡعَظِيمِ 63﴾

{Sai Muka yi wahayi zuwa ga Mũsã cẽwa "Ka dõki tẽku da sandarka." Sai tẽku ta tsãge, kõwane tsãgi ya kasance kamar falalen dũtse mai girma.} [al- Shu'araa: 63].

Misali na biyu kuma: Mu'ujizar (Annabi) Isa - amincin Allah ya tabbata a gare shi - ta yadda yake rayar da matattu, kuma ya fito da su daga ƙabaruurukansu da izinin Allah, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya faɗa game da shi:

﴿...وَأُحۡيِ ٱلۡمَوۡتَىٰ بِإِذۡنِ ٱللَّهِ...﴾

{Kuma ina rayar da matattu da izinin Allah} [al- Imran: 49] Kuma Ya ce:

﴿...وَإِذۡ تُخۡرِجُ ٱلۡمَوۡتَىٰ بِإِذۡنِي...﴾

{A ya yin da kake fitar da matattu da iziniNa} [al- Ma'ida: 110].

Misali na uku kuma: Na (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- lokacin da ƙuraishawa suka nemi mu'ujiza daga gare shi, sai ya yi nuni zuwa ga wata, sai ya tsage tsagi biyu, mutane suka gan shi, akan haka ne faɗarSa - Maɗaukakin sarki -:

﴿ٱقۡتَرَبَتِ ٱلسَّاعَةُ وَٱنشَقَّ ٱلۡقَمَرُ 1 وَإِن يَرَوۡاْ ءَايَةٗ يُعۡرِضُواْ وَيَقُولُواْ سِحۡرٞ مُّسۡتَمِرّٞ2﴾

{Alƙiyama ta kusanto, wata ya tsage idan suka ga wata mu'ujiza, suna kauda kai kuma suna cewa tsafi ne mai wucewa} [al-Kamar: 1-2].

Waɗannan mu'ujizozin da aka gani, waɗanda Allah - Maɗaukakin sarki - Yake gudanar da su, dan ƙarfafawa ga ManzaninSa, da kuma taimako a gare su, suna nuni nuni yankakke a bisa samuwarsa - Maɗaukakin sarki -.

Al'amari na biyu daga abinda imani da Allah ya ke ƙunshe da shi: Imani da RububiyyarSa ai cewa Shi kaɗai ne Ubangiji ba Shi da abokin tarayya ko mai taimako.

Ubangiji: Shi ne wanda halitta, da mulki, da umarni, suka tabbata a gare Shi, babu wani mahalicci ko mamallaki sai Shi, babu wani umarni sai gare Shi, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce:

﴿...أَلَا لَهُ ٱلۡخَلۡقُ وَٱلۡأَمۡرُ...﴾

{Ku saurara, halittta da umarni sun tabbata a gare Shi} [Aaraf: 54] Kuma Ya ce:

﴿...ذَٰلِكُمُ ٱللَّهُ رَبُّكُمۡ لَهُ ٱلۡمُلۡكُۚ وَٱلَّذِينَ تَدۡعُونَ مِن دُونِهِۦ مَا يَمۡلِكُونَ مِن قِطۡمِيرٍ

{Wancananku Allah Ubangijinku, mulki ya tabbata a gare Shi, waɗanda kuke bautawa wanda ba shi ba, ba sa mallakar wani abu, na daga ɓawan ƙwallan dabino} [Faɗir: 13].

Ba a san cewa wani daga halitta ya yi musun Ubangijintakar Allah - Maɗaukakin sarki ba - sai dai idan ya kasance mai girman kai mara kuɗirce abinda yake faɗa ba, kamar yadda ya faru ga Fir'auna, ya yin da ya ce da mutanansa: {Sai ya ce nine ubangijinku mafi ɗaukaka} [al- Nazi'at: 24] kuma ya ce: {Ya ku manya-manyan (mutane ne na) ban san wani ubangiji a gare ku da ba ni ba} [al- Kasas: 38], sai dai hakan bai zamo daga aƙida ba, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Suka yi musunsu (ayoyi) kawunansu kuma suka tabbatar da su, dan zalinci da girman kai} [al-Naml: 14]. Kuma (Annabi) Musa ya ce da Fir'auna cikin abinda Allah Ya hakaito daga gare shi: {Haƙiƙa ka san ba wanda ya saukar da waɗannan sai Ubangijin sammai da ƙassai, hujjoji (masu nuna girman Allah) kuma haƙiƙa ni ina zatanka ya Fir'auna halakakke} [al- Isra'i: 102], Saboda wannan ne mushirikai suka kasance suke tabbatar da Ubangijintakar Allah - Maɗaukakin sarki -, tare kuma da yadda suke masa tarayya a Allantaka, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce:

﴿قُل لِّمَنِ ٱلۡأَرۡضُ وَمَن فِيهَآ إِن كُنتُمۡ تَعۡلَمُونَ 84 سَيَقُولُونَ لِلَّهِۚ قُلۡ أَفَلَا تَذَكَّرُونَ85 قُلۡ مَن رَّبُّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ ٱلسَّبۡعِ وَرَبُّ ٱلۡعَرۡشِ ٱلۡعَظِيمِ 86 سَيَقُولُونَ لِلَّهِۚ قُلۡ أَفَلَا تَتَّقُونَ 87 قُلۡ مَنۢ بِيَدِهِۦمَلَكُوتُ كُلِّ شَيۡءٖ وَهُوَ يُجِيرُ وَلَا يُجَارُ عَلَيۡهِ إِن كُنتُمۡ تَعۡلَمُونَ 88 سَيَقُولُونَ لِلَّهِۚ قُلۡ فَأَنَّىٰ تُسۡحَرُونَ 89﴾

{Ka ce ƙassai da abin da ke cikinsu na waye in kuna da sani za su ce na Allah ne, Ka ce: shin ba kwa yi tunani ba87 Ka ce wanene Ubangijin sammai bakwai kuma Ubangijin Al’arshi Mai girma Za su ce na Allah ne. Ka ce ashe ba kwa ji tsoron Allah ba88 Ka ce wanene taskokin komai suke a hannunSa wanda ke bayar da mafaka shi ba’a ba shi mafaka in har kun kasance kuna da sani. Za su ce na Allah ne, to tayaya ake sihirce ku89} [al- Mu'uminun: 84-89].

Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce:

﴿وَلَئِن سَأَلۡتَهُم مَّنۡ خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ لَيَقُولُنَّ خَلَقَهُنَّ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡعَلِيمُ 9﴾

{Kuma lalle ne, idan ka tambaye su, "Wãne ne ya halitta sammai da ƙasa?" Lalle su ce, "Mabuwãyi Mai ilmi ne Ya halitta su} [al-Zukhruf: 9].

Kuma tsarki ya tabbatar maSa Ya ce:

﴿وَلَئِن سَأَلۡتَهُم مَّنۡ خَلَقَهُمۡ لَيَقُولُنَّ ٱللَّهُۖ فَأَنَّىٰ يُؤۡفَكُونَ87﴾

{Kuma lalle idan ka tambaye su: "Wãne ne ya halitta su?" Lalle ne su ce Allah ne. To, yãya ake jũyar da su?} [al-Zukhruf: 87].

Lamarin Allah - tsarkakken sarki - mai gamewa ne ga lamari na kasantacce da na shari'a, kamar yadda Shi ne Mai tsara kasantacce mai hukunci a cikinsa, da abinda Yake nufi, gwargwadan abinda hikimarSa take hukuntarwa, to, kuma Shi ne hakanan Mai hukunci a cikinsa da shar'anta ibadu, da hukunce-hukuncen ma'amaloli gwargwadan yadda hikimarSa take hukuntarwa. Wanda ya riƙi wani mai shar'antawa tare da Allah - Maɗaukakin sarki -, ko (ya riƙi) wani mai hukuntawa a ma'amaloli, to haƙiƙa ya yi shirka da Shi, kuma bai tabbatar da imani ba.

Lamari na uku daga abinda imani da Allah yake ƙunsarsa: Imani da Allantakaswa, wato: Cewa shi kaɗai ne abin bautawa da gaskiya, ba Shi da abokin tarayya, (Ilahu) da ma'anar (ma'aluuh) wato (abin bautawa) dan so da girmamawa.

Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Abin bautarku abin bauta ne ɗaya, babu abin bautawa da gaskiya sai Shi Mai rahama Mai jin ƙai} [al- Baƙara: 163]

﴿شَهِدَ ٱللَّهُ أَنَّهُۥ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ وَٱلۡمَلَٰٓئِكَةُ وَأُوْلُواْ ٱلۡعِلۡمِ قَآئِمَۢا بِٱلۡقِسۡطِۚ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡحَكِيمُ 18﴾

Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Allah Ya shaida cewa, Shi babu abin bautawa da gaskiya sai Shi kuma mala'iku da ma'abota sani (suma sun shaida) Yana Mai tsayuwa da adalci, babu abin bautawa da gaskiya sai Shi Mabuwayi Gwani) {al- Imraan: 18], Duk wanda ya riƙi wani abin bautawa tare da Allah, yake bautawa waninSa, to, Ulhiyyarsa ɓatacciya ce, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce:

﴿ذَٰلِكَ بِأَنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلۡحَقُّ وَأَنَّ مَا يَدۡعُونَ مِن دُونِهِۦ هُوَ ٱلۡبَٰطِلُ وَأَنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلۡعَلِيُّ ٱلۡكَبِيرُ 62﴾

{Wancan! sabõda lalle ne Allah, shĩ ne Gaskiya, kuma lalle ne, abin da suke kira waninSa shi ne ƙarya. Kuma lalle ne Allah, Shĩ ne Maɗaukaki, Mai girma} [al- Hajj: 62]. Kuma ambatansu Alloli ba ya ba su can-cantar Allantaka, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: dangane da {Laata, da Uzza, da Manaata}:

﴿إِنۡ هِيَ إِلَّآ أَسۡمَآءٞ سَمَّيۡتُمُوهَآ أَنتُمۡ وَءَابَآؤُكُم مَّآ أَنزَلَ ٱللَّهُ بِهَا مِن سُلۡطَٰنٍ...﴾

{Su ba su zamo ba face sunaye ne da kuka ambacesu, ku da iyayenku, Allah bai saukar da wata hujja a gare su ba} [al-Najm: 23].

Kuma Ya ce dan gane da (Annabi) Hudu - amincin Allah ya tabbata a gare shi - cewa shi ya ce da mutanensa:

﴿...أَتُجَٰدِلُونَنِي فِيٓ أَسۡمَآءٖ سَمَّيۡتُمُوهَآ أَنتُمۡ وَءَابَآؤُكُم مَّا نَزَّلَ ٱللَّهُ بِهَا مِن سُلۡطَٰنٖۚ...﴾

{Shin kwadinga jayayya da ni akan wasu sunayen da ku ka ambace su, ku da iyayenku, Allah bai saukar da wata hujja ba a gare su} [al-A'araf: 71].

Kuma Ya ce dan gane da (Annabi) Yusuf - amincin Allah ya tabbata a gare shi- cewa shi ya ce wa abokansa na kurukuku su biyu:

﴿يَٰصَٰحِبَيِ ٱلسِّجۡنِ ءَأَرۡبَابٞ مُّتَفَرِّقُونَ خَيۡرٌ أَمِ ٱللَّهُ ٱلۡوَٰحِدُ ٱلۡقَهَّارُ 39 مَا تَعۡبُدُونَ مِن دُونِهِۦٓ إِلَّآ أَسۡمَآءٗ سَمَّيۡتُمُوهَآ أَنتُمۡ وَءَابَآؤُكُم مَّآ أَنزَلَ ٱللَّهُ بِهَا مِن سُلۡطَٰنٍۚ...﴾

{Ya ma'abota kurukuku biyu shin (bautar) iyayangiji mabanbanta shi ya fi alkhairi ko (bautar) Allah ɗaya Mai rinjaye? ba wani abu kuke bautawa ba koma bayanSa face wasu sunaye da kuka ambace su, ku da iyayenku, Allah bai saukar da wata hujja a gare su ba} [Yusuf: 39-40].

Saboda wannan ne manzanni- tsira da amincin Allah su tabbata a gare su- suka kasance, suna cewa mutanansu:

﴿...ٱعۡبُدُواْ ٱللَّهَ مَا لَكُم مِّنۡ إِلَٰهٍ غَيۡرُهُ...﴾

{Ku bautawa Allah ba ku da wani abin bauta da gaskiya wanda ba Shi ba} [al-A'araf: 59] Sai dai mushirikai sun ƙi hakan, suka riƙi alloli komabayan Allah, suna bauta musu tare da Allah- tsarkakakken sarki kuma Maɗaukaki- suna neman nasara da taimako da su.

Kuma haƙiƙa- Allah - Maɗaukakin sarki- Ya ɓata riƙar waɗannan iyayengjin da hujjoji biyu na hankali:

Na farko: Cewa shi babu wani abu na abinda ya keɓenci Uluhiyya (Allantaka) ga waɗannan iyayen gijin waɗanda suka riƙe su, su ababan halitta ne, basa halitta, basa janyo wani amfani ga masu bauta musu, ko ingije wata cuta da gare su, kuma basu mallaki rayuwa ko mutuwa a gare su ba, ba sa mallakar wani abu daga sammai, ba sa kuma tarayya a cikinsa.

Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Kuma suka riƙi abũbuwan bautawa, baicin Shi, su yin halittar kõme alhãli ne ake halittãwa kuma su mallakar wa kansu wata cũta ko wani amfãni, kuma su mallakar mutuwa kuma su mallakar rãyarwa, kuma su mallakar tãyarwa} [al-Furƙan:3].

Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Ka ce: Ku kirayi waɗanda kuka riya (cewa abubuwan bauta ne) baicin Allah, ba su mallakar ma'aunin zarra a cikin sammai, kuma ba su mallakarsa a cikin ƙassai kuma ba su da wani abu na tarayya a cikinsu, kuma ba shi da wani mataimaki daga gare su. kuma wani ceto ba ya amafani gare Shi sai ga wanda ya yiwa izini} [al-Saba: 22-23]

﴿أَيُشۡرِكُونَ مَا لَا يَخۡلُقُ شَيۡـٔٗا وَهُمۡ يُخۡلَقُونَ 191 وَلَا يَسۡتَطِيعُونَ لَهُمۡ نَصۡرٗا وَلَآ أَنفُسَهُمۡ يَنصُرُونَ 192﴾

Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: Sa dinga haɗa Allah da abin da ba ya iya halittar komai, alhali kuma su halittar su aka yi (191) ba sa iya yi musu wani taimako, kuma ko kansu ma ba sa iya taimakawa(192)} [al- Aaraf:191-192].

Idan wannan ya kasance shi ne halin waɗancan iyayen giji (ababan bauta), to haƙiƙa riƙarsu a matsayin ababan bauta, yana daga mafi wautar wauta, kuma ɓarna mafi ɓaci.

Na biyu: Haƙiƙa waɗannan mushirikan, sun kasnce suna tabbatar da cewa, Allah - Maɗaukakin sarki - Shi kaɗai ne Ubangiji Mahalicci, wanda mulkin kowanne abu ke hannunSa, Shi Yana amintar da wanda Ya so, kuma ba'a amintar da wanda Ya yi nufin azabtarwa, wannan yana tabbatar da su kaɗaita Shi da bauta, kamar yadda suka kaɗaita Shi da halitta,

﴿يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ ٱعۡبُدُواْ رَبَّكُمُ ٱلَّذِي خَلَقَكُمۡ وَٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِكُمۡ لَعَلَّكُمۡ تَتَّقُونَ 21 ٱلَّذِي جَعَلَ لَكُمُ ٱلۡأَرۡضَ فِرَٰشٗا وَٱلسَّمَآءَ بِنَآءٗ وَأَنزَلَ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءٗ فَأَخۡرَجَ بِهِۦ مِنَ ٱلثَّمَرَٰتِ رِزۡقٗا لَّكُمۡۖ فَلَا تَجۡعَلُواْ لِلَّهِ أَندَادٗا وَأَنتُمۡ تَعۡلَمُونَ 22﴾

Kamar yadda- Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Yaku mutane ku bautawa Ubangijinku, wanda Ya halicce ku da waɗanda suke gabanin ku, domin kwaji tsoran Allah(21) (Shine) wanda Ya sanya ƙasa agare ku shinfiɗa, sama kuma gini (rufi), Ya kuma saukar da ruwa daga sama, sai Ya fitar daga 'ya'yan itatutuwa da shi (ruwan) dan arziƙi agare ku, kada ku sanya kishiyoyi ga Allah alhalin kuna sani} [al-Baƙara: 21-22].

Kuma - Maɗaukakin sarki Ya ce: {Lalle da za ka tambaye su waye ya haliccesu, lalle za su ce Allah ne, ta yaya ake juyar dasu} [al-Zukhruf: 87].

Kuma Maɗaukakin sarki Ya ce: {Kace: Wa yake azurta ku daga sama da ƙasa, ko wanene yake mallakar ji da magannai, waye yake fitar da rayayye daga matacce, kuma yake fitar da matacce daga rayayye, wanene yake tsara lamari, da sannu za su ce Allah ne, bakwa ji tsoran Allah ba, wancananku (shine) Allah Ubangijinku na gaskiyya, ba bu abinda ke bayan gaskiya sai ɓata, ta yaya ake juyar da ku} [Yunus: 31-32].

Lamari na huɗu daga abinda imani da Allah yake ƙunshe da shi: Imani da sunayenSa da kuma siffofinSa:

Yana nufin: Tabbatar da abinda Allah Ya tabbatarwa kanSa a cikin littafinSa, ko sunnar ManzanSa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - na daga sunaye da siffofi, a bisa fuska da ta dace da Shi, ba tare da canja ko kore ko kamanta (siffofi da sunayenSa) ba, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Allah Yana da sunaye kyawawa, ku kiraShi da su, ku bar waɗanda suke shisshigi a cikn sunayenSa da sannu za a saka musu da abinda suka kasance suna aikatawa} [al- Aaraf: 180]

﴿...وَلَهُ ٱلۡمَثَلُ ٱلۡأَعۡلَىٰ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ وَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡحَكِيمُ

وقال تعالى: ﴿...لَيۡسَ كَمِثۡلِهِۦ شَيۡءٞۖ وَهُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡبَصِيرُ

Maɗaukakin sarki Ya ce: {Kuma yana da misali wanda ya fi ɗaukaka a cikin sammai da ƙasa, kuma shi ne Mabuwayi Gwani} [al-Ruum: 27]

Maɗaukakin sarki Ya ce: {Ba bu wani abu da ya yi kama da Shi kuma Shi Mai ji ne kuma Mai gani ne} [al-Shuura: 11].

Haƙiƙa jama'a biyu sun ɓata a wannan lamari:

Na farkonsu: (Masu korewa) waɗanda suka yi musun sunayen da siffofin, ko sashinsu, suna masu riya cewa, tabbatar da su ga Allah zai lazimtar da kamanceceniya, wato: Kamanta Allah - Maɗaukakin sarki - da halittunSa, wannan riyawa ɓatacciya ce, saboda wasu fuskoki, daga cikin fuskokin:

Na farko: Cewa shi yana lazimtar da lazimai ɓatacciya, kamar warwara a cikin zancen Allah tsarkakken sarki, hakan kuwa cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Ya tabbatarwa kanSa sunaye da siffofi, kuma Ya kore wani abu ya kasance tamkarSa, Da a ce tabbatar da su yana lazimtar da kamanceceniya, da tufka da warwara sun tabbata a cikin zancen Allah, da kuma ƙaryata sashinsa da sashi, (tsarki ya tabbata ga Allah).

Na biyu: Cawa haɗuwar abubuwa biyu a suna ko siffa ba ya lazimtar da su kasance masu kamanceceniya, kai kana ganin mutane biyu suna haɗuwa a cewa kowannensu mutum ne mai ji, mai gani mai magana. Ba ya lazimtuwa daga haka su yi kamanceceniya a ma'anoni na mutuntaka, ji, da gani, da magana,

Za ka ga dabbobi suna da hannaye, da ƙafafu, da idanuwa, haɗuwarsu a wannan ba ya lazimtar da hannayensu da ƙafafuwansu da idanuwansu su kasance masu kamanceceniya.

Idan nisan banbanci ya bayyana tsakanin ababan halitta, cikin abinda suka haɗu a cikinsa, na daga sunaye da siffofi, to nisan banbanci tsakanin Mahalicci da ababan halitta, shi ya fi bayyana kuma ya fi girma.

Jama'a ta biyu: (Masu kamantawa) waɗanda suka tabbatar da sunayen da siffofin, tare da kamanta Allah - Maɗaukakin sarki - da halittarSa, suna masu riya cewa wannan shi ne hukuncin abinda nassoshi suka yi nuni da shi, domin Allah Yana magana da bayi da abinda za su fahimta, wannan riyawar ɓatacciya ce, saboda wasu fuskoki, daga cikin fuskokin:

Na farko: Cewa kamantuwar Allah - Maɗaukakin sarki - da halittunSa lamari ne da hankali da sharia'a za su ɓata su, kuma ba zai yi wu ba, abinda nassosin littafi da sunna suka hukuntar ya kasance lamari ɓatacce.

Na biyu: Haƙiƙa Allah - Maɗaukakin sarki - Ya yi magana da bayi da abinda za su fahimta daga asalin ma'ana, amma haƙiƙar abinda waccan ma'anar take kansa, to shi yana daga abinda Allah - Maɗaukakin sarki - Ya keɓanta da saninsa cikin abinda yake da alaƙa da zatinSa da kuma siffofinSa.

Idan Allah Ya tabbatarwa kanSa cewa Shi Mai ji ne: To haƙiƙa ji sananne ne ta ɓangaran ma'ana (shi ne riskar sautuka) sai dai haƙiƙar haka dangane da jin Allah - Maɗaukakin sarki - ba abin sani ba ne, domin haƙiƙar ji tana nisantar juna har ga ababan halitta, to nisantarta tsakanin Mahalicci da ababan halitta shi ya fi bayyana kuma yafi girma.

Idan Allah - Maɗaukakin sarki - Ya bada labari game da kanSa cewa Shi Ya daidaitu akan Al'arshinSa, to haƙiƙar daidaituwa ta ɓangaren asalin ma'ana sananniya ce, sai dai haƙiƙar daidaituwa wacce Shi Yake a kanta ba sananniya ba ce a gare mu, dangane da daidaituwar Allah akan Al'arshinSa, domin haƙiƙar daidaituwa tana banbantar juna a haƙƙin abin halitta. Daidaituwa akan kujera tabbacciya ba ta zamo ba kamar daidaituwa akan siddin raƙumi mai wahalarwa mai tirjiya ba, idan ta banbanta a haƙƙin abin halitta, to banbantata tsakanin Mahalicci da abin halitta shi ya fi bayyana kuma ya fi girma.

Imani da Allah - Maɗaukakin sarki - a bisa abinda muka siffanta yana samarwa mumini fa'idoji masu girma, yana daga cikin su:

Ta farko: Tabbatar da kaɗaitakar Allah - Maɗaukakin sarki -, ta yadda ƙauna ko tsoro ba za su ratayu da waninSa ba, kuma ba zai bautawa wninSa ba.

Ta biyu: Cikar son Allah - Maɗaukakin sarki - da girmamaShi gwargwadon abinda sunayenSa kyawawa da siffofinSa maɗaukaka suka hukunta.

Ta uku: Tabbatar da bauta maSa da aikata abinda Ya yi umarni da shi, da kuma nisantar abinda Ya yi hani agare shi.

***

IMANI DA MALA'IKU

Mala'iku: Wata duiniya ce ta gaibu, ababar halitta, masu bautar Allah - Maɗaukakikn sarki -, ba su da wani abu daga abubuwan da suka keɓanci Ubangijintaka ko Allantaka, Allah - Maɗaukakikn sarki - Ya halicce su daga haske, Ya kuma ba su cikakken miƙa wuya ga umarninSa da ƙarfi a bisa zartar da shi, Allah - Maɗaukakikn sarki - Ya ce: {Waɗanda suke gurinSa ba sa girman kai ga bauta maSa, ba sa ƙosawa, suna tsarkake (Allah) dare da rana ba sa yin rauni} [al- Anbiya: 19-20].

Kuma su adadi ne mai yawa, babu mai ƙididdigesu sai Allah - Maɗaukakikn sarki -, haƙiƙa ya tabbata a cikin Bukhari da Muslim daga hadisin Anas- Allah Ya yarda da shi- a ƙissar Mi'iraji cewa, Annabi-tsira da amincin Amincin Allah su tabbata a gare shi- an ɗago masa Baitul Ma'amur a sama, kowacce rana Mala'iku dubu saba'in ne suke yin sallah a cikinsa, idan suka fita ba sa dawowa zuwa gare shi, ƙarshen abinda ke a kansu.

Imani da Mala'iku yana ƙunsar al'amura huɗu:

Na farko: Imani da samuwarsu.

Na biyu: Imani da wanda muka san sunansa daga cikinsu da sunansa, (kamar Jibril) waɗanda ba mu san sunansu ba, mu yi imani da su a dunƙule.

Na uku: Imani da abinda muka sani daga siffofinsu, kamar siffar (Jibril) haƙiƙa Annabi- tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya bada labarin cewa shi ya gan shi a siffarsa wacce aka halicce shi a kanta, yana da fuka-fukai ɗari shida, haƙiƙa ya rufe sasannin sama.

Kuma haƙiƙa Mala'ika ya kan iya canzawa da umarnin Allah - Maɗaukakikn sarki - zuwa kamannin wani mutum, Kamar yadda ya faru ga (Jibriil) a yayin da Allah - Maɗaukakikn sarki - Ya aika shi zuwa ga Nana Maryam, sai ya kamantu da mutum daidaitacce agareta, kuma lokacin da ya zo zuwa ga Annabi- tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- alhalin shi yana zaune a cikin sahabbansa, ya zo masa da siffar wani mutum mai tsananin farin tufafi mai tsananin baƙin gashi, ba a ganin alamar tafiya agare shi, kuma babu ɗaya daga sahabbai wanda ya san shi, sai ya jingina gwiyoyinsa zuwa gwiyoyinsa, ya kuma ɗora tafukakan hannayensa akan cinyoyinsa, ya tambayi Annabi-tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- dangane da Musulunci da mani, da kyautayi, da tashin alkiyama, da alamominta, sai Annabi-tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya amsa masa, sai ya tafi, sai Annabin Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wannan Jibril ne ya zo muku ne ya sanar da ku Addininku".

Hakanan Mala'iku waɗanda Allah - Maɗaukakin sarki - Ya aika su zuwa (Annabi) Ibrahim da (Annabi) Luɗu sun kasnce ne a bisa surar mutane (mazaje).

Na huɗu daga abinda imani da mala'iku yake ƙunsarsa: Imani da abinda muka sani na daga ayyukansu waɗanda suke tsayawa da su da umarnin Allah - Maɗaukakikn sarki - kamar tsarkake Shi, da bauta maSa dare da rana, ba tare da ƙosawa ko rauni ba.

Kuma wasunsu yakan kasance suna da wasu ayyuka na musamman,

Misalin: Jibril amintacce a bisa wahayin Allah - Maɗaukakin sarki, Allah Yana aika shi da shi (wahayi) zuwa Annabawa da Manzanni.

Kuma misalin: Mika'ilu: Wanda aka wakilta shi ga ruwan sama da tsirrai.

Hakanan misalin Israfil: Wanda aka wakilta ga busa a cikin ƙaho a lokacin tashin alƙiyama da tasowar halitta.

Kuma kamar Mala'ikan mutuwa: Wanda aka wakilta ga karɓar rayuka a lokacin mutuwa.

Da misalin Malik: Wanda aka wakilta ga wuta, shi ne mai tsaran wuta.

Kuma kamar misalin: Mala'iku waɗanda aka wakilta ga 'yan tayi a cikin mahaifa, idan mutum ya cika wata huɗu a cikin mahaifiyarsa, sai Allah Ya aiko mala'ika zuwa gare shi, ya umarce shi da rubuta arziƙinsa, da ajalinsa, da aikinsa, shakiyyi ne ko mai arziƙi.

Da misalin: Mala'iku waɗanda aka wakilta su da kiyaye ayyukan 'yan Adam da rubuta su, kowanne mutum yana da mala'iku biyu, ɗayansu a dama, ɗayan kuma a hagu.

Kuma misalin: Mala'iku waɗanda aka wakilta su da tambayar mamaci idan aka sashi a ckin ƙabari, mala'iku biyu suna zuwar masa, suna tambayarsa dangane da Ubangijinsa, da Addninsa, da Annabinsa.

Imani da Mala'iku yana haifar da fa'idoji masu girma, yana daga cikin su:

Ta farko: Sanin girman Allah - Maɗaukakin sarki -, da ƙarfinSa, da sarautarSa; domin cewa girman ababan halitta yana nuni a bisa girman Mai halitta.

Ta biyu: Godewa Allah- Maɗaukakin sarki- a bisa kulawarSa da 'yan Adam, ta yadda ya wakilta daga waɗannan Mala'iku, waɗanda suke tsayawa da kiyaye su, da rubuta ayyukansu, da wanin hakan daga maslahohinsu.

Ta uku: Son mala'iku a bisa abinda suka tsaya da shi na bautar Allah - Maɗaukakin sarki -.

Kuma haƙiƙa wasu mutane daga karkatattu sun yi musun kasancewar mala'iku suna da jiki, suka ce: Haƙiƙa su bayani ne akan ƙarfin alkhairi wanda ya tabbatu a cikin ababan halitta, wannan ƙaryatawa ne ga littafin Allah- Maɗaukakin sarki- da sunnar ManzanSa -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- da haɗuwar musulmai.

Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Godiya ta tabbata ga Allah, Mahaliccin sammai da ƙasa, Mai sanya Mala'iku 'yan aike, ma'abota fuka-fukai biyu-biyu da uku-uku da huɗu-huɗu} [Faɗir: 1].

Kuma Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Da za ka ga yayin da Mala'iku suke ɗaukar ran waɗanda suka kafirce, suna dukan fuskokinsu da bayayyakinsu} [al-Anfal: 50].

Kuma Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Da za ka ga ya yin da azzalimai suke cikin magagin mutuwa, mala'iku suna shimfiɗa hannayensu (suna cewa) ku fitar da rayukanku) [al- An'am: 93].

Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Har yayin da aka gusar da (tsoro) daga zuciyarsu, suka ce mai Ubangijinku ya ce? suka ce gaskiya shi ne Maɗaukaki Mai girma} [Sabaa: 23].

Kuma Ya ce dangane da 'yan aljanna: {Mala'iku suna shiga a gare su daga kowacce ƙofa (suna cewa) amincin Allah ya tabbata a gare ku da haƙurin da kuka yi madalla da sakamakon wannan gida} [al-Ra'ad:23-24].

Kuma a cikin Sahihul Bukhari, daga Abu Huraira-Allah Ya yarda da shi- daga Annabi-tsra da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya ce: "Idan Allah Ya so bawa sai Ya kira Jibril: Allah Yana son wane ka so shi, sai Jibril ya so shi, sai Jibril yai kira ga ahalin sama; Haƙiƙa Allah Yana son wane ku so shi, sai ahalin sama su so shi, sannan sai a sa masa karɓuwa a ƙasa".

Ya zo kuma a cikinsa daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi- Ya ce: Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a garea shi- ya ce: Idan ranar Juma'a ta kasnce, Mala'iku suna kasancewa a kowacce ƙofa daga ƙofofin masallaci, suna rubuta na farko sannan mai binsa, idan liman ya zauna (akan minbari) sai su naɗe takardun, su zo su dinga sauraran ambato (huɗuba)".

Waɗannan nassosi bayyanannu ne akan cawa Mala'ku jukkuna ne, ba ƙarfi ba ne na ma'ana, kamar yadda karkatattu suka faɗa, kuma akan abinda waɗannan nassosi suka hukuntar musulmai suka haɗu.

***

IMANI DA LITTATTAFAI

Littattafai: Jam'i ne na (littafi) da ma'anar (abin rubutawa).

Abin nufi da su a nan: Littattafai waɗanda Allah - Maɗaukakin sarki - Ya saukar da ga manzanninSa, dan rahama ga halitta da shiryarwa a gare su, dan su sadu da su zuwa arziƙi a dunya da lahira.

Imani da littattafai yana ƙunsar al'amura huɗu:

Na farko: Imani da cewa saukarsu daga Allah gaskiya ne.

Na biyu: Imani da abinda muka san sunansa daga gare su da sunansa: kamar Al'Kur'an wanda Allah Ya saukar ga (Annabi) Muhammad-tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- da Attaura wacce aka saukar ga (Annabi) Musa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da Injiila wacce aka saukar ga (Annabi) Isa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da Zabuura wacce aka saukar ga (Annabi) Dauda - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - amma abinda ba mu san sunansa ba sai mu yi mani da shi a dunƙule.

Na uku: Gasgata abinda ya inganta da labaransu, kamar labaran AlKur'ani, da labaran abinda ba a canza ko jirkita ba daga littattafan da suka gabata.

Na huɗu: Aiki da hukunce-hukunce a abinda ba a shafe ba daga gare su, da kuma yarda da miƙa wuya da shi, daidai ne shin mun fahimci hikimarsa, ko ba mu fahimce ta ba, dukkan littattafan da suka gabata waɗanda aka shafe ne da Alƙur’ani mai girma,

﴿وَأَنزَلۡنَآ إِلَيۡكَ ٱلۡكِتَٰبَ بِٱلۡحَقِّ مُصَدِّقٗا لِّمَا بَيۡنَ يَدَيۡهِ مِنَ ٱلۡكِتَٰبِ وَمُهَيۡمِنًا عَلَيۡهِ...﴾

Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Kuma mun saukar da littafi zuwa gare ka da gaskiya, mai gasgatawa ga abinda ke gabaninsa na daga littafi, kuma mai hukunci a gare shi} [al-Ma'ida: 48], wato (mai hukunci a gare shi).

Saboda wannan ne: Yin aiki da kowanne irin hukunci daga hukunce-hukuncen da suka gabata ba ya halatta, sai abinda ya inganta daga gare su, kuma Alƙu’ani ya tabbatar da su.

Imani da lttattafai yana samar da fa'idoji masu girma, yana daga cikin su:

Ta farko: Sanin kulawar Allah - Maɗaukakin sarki - da bayinSa, ta yadda Ya saukarwa kowacce al'umma littafin da yake shiryar da su da shi.

Ta biyu: Sanin hikimar Allah - Maɗaukakin sarki - a shar'antawarsa ta yadda Ya shar'antawa kowacce al'umma abinda yake dacewa da halayansu,

﴿...لِكُلّٖ جَعَلۡنَا مِنكُمۡ شِرۡعَةٗ وَمِنۡهَاجٗا...﴾

kamar yadda Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Kowacce (al'umma) da gare ku mun sanya (mata) shari'a da da hanya (bayyananiya)} [al'Ma'ida: 48].

Ta uku: Godewa ni'imar Allah a bisa haka.

***

IMANI DA MANZANNI

Manzanni jam'i ne na (Manzo) da ma'anar (abin aikowa) wato abin aikowa da isar da wani abu.

Abin nufi anan: Wanda aka yi wahayi zuwa gare shi daga 'yan Adam, da wata shari'a kuma aka yi umarni da ya isar da ita.

Farkon manzanni (Annabi) Nuhu - amincin Allah ya tabbata a gare shi -, na ƙarshensu kuma (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -.

Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Haƙiƙa mun yi wahayi zuwa gareka kamar yadda muka yi wahayi zuwa Nuhu da annabawa daga bayansa}.

[al-Nisaa:163].

Ackin Sahihul Bukhari daga Anas bn Malk- Allah Ya yarda da shi - a ckin Hadisin ceto cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabba a gare shi -: " Ya ambaci cewa mutane za su zo zuwa (Annabi) Adam, dan ya nema musu ceto, sai yai hanzari a gare su, yace: Kuje (wurin) (Annabi) Nuhu farkon manzo da Allah Ya aiko shi". Sai ya ambaci cikar hadisin.

Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce a sha'anin (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -:

﴿مَّا كَانَ مُحَمَّدٌ أَبَآ أَحَدٖ مِّن رِّجَالِكُمۡ وَلَٰكِن رَّسُولَ ٱللَّهِ وَخَاتَمَ ٱلنَّبِيِّـۧنَ...﴾

{Muhammad bai kasance uba ga ɗaya daga mazajenku ba, sai dai manzan Allah ne kuma cikamakin annabawa}.

[al-Ahzab: 40].

Kuma babu wata al'umma da ta zamo bata da wani manzo, da Allah - Maɗaukakin sarki - zai aiko shi da wata shari'a keɓantacciyya zuwa mutanensa, ko wani Annabi da zai yi wahayi zuwa gare shi da wata shari'ar waɗanda suka gabace shi dan ya sabuntata, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce:

﴿وَلَقَدۡ بَعَثۡنَا فِي كُلِّ أُمَّةٖ رَّسُولًا أَنِ ٱعۡبُدُواْ ٱللَّهَ وَٱجۡتَنِبُواْ ٱلطَّٰغُوتَ...﴾

{Haƙiƙa mun aika manzo ga kowacce al'umma, cewa ku bautawa Allah kuma ku nisanci (bautar) wanin Allah}.

[al-Nahal: 36].

Kuma Allah Maɗaukakin sarki Ya ce: {Ba bu wata al'umma da ta shuɗe face a cikinta akwai mai gargaɗi}. [Faɗir: 24].

Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Haƙiƙa Mun saukar da Attaura a cikinta a kwai shiriya da haske, Annabawa waɗanda suke sun sallama, suna yin hukunci da ita ga waɗanda suka tuba (Yahudu)}.

[al-Ma'ida: 44].

Manzanni 'yan Adam ne ababan halitta, ba su da wani abu da ya keɓanci Ubangijintaka ko allantaka, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya faɗa dan gane da AnnabinSa Muhammad kuma shi ne shugaban manzanni, mafi girmansu da ɗaukaka a gurin Allah:

﴿قُل لَّآ أَمۡلِكُ لِنَفۡسِي نَفۡعٗا وَلَا ضَرًّا إِلَّا مَا شَآءَ ٱللَّهُۚ وَلَوۡ كُنتُ أَعۡلَمُ ٱلۡغَيۡبَ لَٱسۡتَكۡثَرۡتُ مِنَ ٱلۡخَيۡرِ وَمَا مَسَّنِيَ ٱلسُّوٓءُۚ إِنۡ أَنَا۠ إِلَّا نَذِيرٞ وَبَشِيرٞ لِّقَوۡمٖ يُؤۡمِنُونَ 188﴾

{Kace ban mallaki amfanarwa ko cutarwa ga kaina ba sai abinda Allah Ya so, da na kasance na san gaibu (fake) da na nemi yawan alkhari kuma wani mummunan (abu) bai shafe ni ba, ni ban zamo ba fa ce mai gargaɗi mai bushara ga mutane da za su yi imani}.

[al- A'araf: 188].

Kuma Allah Maɗaukakin sarki Ya ce: {Kace lalle ni ba na mallakar cuta ko shiriya a gare ku, kace babu wani ɗaya da zai tserar da ni (amintar da ni) daga Allah, kuma ba zan sami wata mafaka da ba tasa ba}.

[al-Jinn: 21-22].

Kuma abubuwan da suka keɓanci 'yan Adam suna riskarsu: Na daga rashin lafiya, da mutuwa, da buƙatuwa zuwa abinci da abin sha, da wanin haka, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce dan gane da (Annabi) Ibrahim - amincin Allah ya tabbata a agare shi a siffantawarsa ga Ubangijinsa - Allah Maɗaukakin sarki:

﴿وَٱلَّذِي هُوَ يُطۡعِمُنِي وَيَسۡقِينِ 79 وَإِذَا مَرِضۡتُ فَهُوَ يَشۡفِينِ 80 وَٱلَّذِي يُمِيتُنِي ثُمَّ يُحۡيِينِ 81﴾

{Wanda Shi ne Yake ciyar dani kuma Yake shayar da ni (79) Kuma idan na yi jiyya, to Shi ne Yake warkar da ni (80) Kuma wanda Yake matar da ni, sannan Ya rayar da ni(81)}.

[al-Shu'ara: 79-81].

Kuma Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- Ya ce: "Kaɗai ni mutum ne kamar ku, ina yin mantuwa kamar yadda ku ke mantuwa, idan na manta ku tunartar da ni".

Haƙaƙa Allah - Maɗaukakin sarki- Ya siffanta su da yi masa bauta a mafi ɗaukakar matsayinsu, a kuma korowar yabo a gare su, sai Allah Maɗaukakin sarki Ya ce dan gane da (Annabi) Nuhu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi: {Haƙiƙa shi ya kasance bawa mai yawan godiya}.[al-Israa: 3].

Ya ce dangane da (Annabi) Muhammad: {Ya girmama wanda Ya saukar da mai rarrarabewa (Alƙur'an} a bisa bawanSa dan ya kasance mai gargaɗi ga talikai}.

[al- Furƙan:1].

Kuma Ya faɗa dan gane da (Annabi) Ibrahm, da (Annabi) Ishaƙ, da (Annabi) Ya'aƙub - tsira da amincin Allah su tabbata a gare su -: {Ka ambaci bayinmu Ibrahm, da Ishaƙ, da Ya'aƙub, ma'abota ƙarfi da basira, haƙiƙa mun keɓance su da keɓantaccen ambatan gida, kuma haƙiƙa su a gurinmu suna daga cikin zaɓaɓɓu.}.[Saad: 45-47].

Kuma Ya faɗa dangane da (Annabi) Isa ɗan Nana Maryam: {Shi bai zamo ba face bawa ne da Muka yi ni'ima a gare shi, kuma muka sanya shi misali ga 'ya'yan Isra'Il} [al-Zukhruf: 59].

Imani da Manzanni yana ƙunsar al'amura huɗu:

Na farko: Imani da cewa saƙonsu gaskiya ne daga Allah - Maɗaukakin sarki - yake, wanda ya kafirce da saƙon ɗaya daga cikinsu, to haƙiƙa ya kafirce da dukkaninsu, Kamar yadda Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Mutanan Nuhu sun ƙaryata manzanni).[al-Shu'ara'i: 105].

Sai Allah Ya sanya su masu ƙaryatawa ga dukkan manzanni, tare da cewa wani manzo bai kasance ba banda shi (annabi Nuhu), a lokacin da suka ƙarya ta shi, akan wannan ne Nasara waɗanda suka ƙaryata (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - kuma ba su bi shi ba, su masu ƙaryatawa ne ga (Annabi) Isa ɗan Nana Maryam, kuma su ba mabiyane a gare shi ba, musammam ma cewa shi lallai ya yi musu bushara da (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, kuma babu ma'ana da yi musu bushara da shi, sai dan cewa haƙiƙa shi Manzo ne zuwa gare su, da Allah zai tsamar da su da shi daga ɓata, Ya kuma shiryar da su zuwa tafarki madaidaici.

Na biyu: Imani da wanda muka san sunansa daga cikinsu, misalin: (Annabi) Muhammad, da (Annabi) Ibrahim, da (Annabi) Musa, Isa, da (Annabi) Nuhu- tsira da amincin Allah su tabbata a gare su - Waɗannan biyar ɗin sune ma'abota haƙuri da himma maɗaukakiya daga manzanni, haƙiƙa Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ambacesu a guri biyu cikin AlKur'an a cikin faɗarSa:

﴿وَإِذۡ أَخَذۡنَا مِنَ ٱلنَّبِيِّـۧنَ مِيثَٰقَهُمۡ وَمِنكَ وَمِن نُّوحٖ وَإِبۡرَٰهِيمَ وَمُوسَىٰ وَعِيسَى ٱبۡنِ مَرۡيَمَۖ وَأَخَذۡنَا مِنۡهُم مِّيثَٰقًا غَلِيظٗا 7﴾

وقوله: ﴿شَرَعَ لَكُم مِّنَ ٱلدِّينِ مَا وَصَّىٰ بِهِۦ نُوحٗا وَٱلَّذِيٓ أَوۡحَيۡنَآ إِلَيۡكَ وَمَا وَصَّيۡنَا بِهِۦٓ إِبۡرَٰهِيمَ وَمُوسَىٰ وَعِيسَىٰٓۖ أَنۡ أَقِيمُواْ ٱلدِّينَ وَلَا تَتَفَرَّقُواْ فِيهِۚ كَبُرَ عَلَى ٱلۡمُشۡرِكِينَ مَا تَدۡعُوهُمۡ إِلَيۡهِۚ ٱللَّهُ يَجۡتَبِيٓ إِلَيۡهِ مَن يَشَآءُ وَيَهۡدِيٓ إِلَيۡهِ مَن يُنِيبُ 13﴾

{Kuma a lõkacin da Muka riƙi alkawarin Annabawa daga gare su, kuma daga gare ka, kuma daga Nũhu da Ibrãhĩm da Mũsa da kuma Ĩsã ɗan Maryama, kuma Muka riƙi wani alkawari mai kauri daga gare su} [al- Ahzaab:7].

kuma da faɗarSa: {Ya shar'anta muku, game da Addini, abin da Ya yi wasiyya da shi ga Nũhu da abin da Muka yi wahayi da shi zuwa gare ka, da abin da Muka yi wasiyya da shi ga Ibrãhĩm da Mũsã da Ĩsã, cẽwa ku tsayar da addini sõsai kuma kada ku rarrabu a cikinsa. Abin da kuke kira zuwa gare shi, ya yi nauyi a kan mãsu shirki. Allah na zãɓen wanda Yake so zuwa gare Shi, kuma Yanã shiryar da wanda ke tawakkali gare Shi, ga hanyarSa}.[al-Shura: 13].

Amma wanda ba mu san sunansa ba daga cikinsu; to muna imani da shi a dunƙule, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce:

﴿وَلَقَدۡ أَرۡسَلۡنَا رُسُلٗا مِّن قَبۡلِكَ مِنۡهُم مَّن قَصَصۡنَا عَلَيۡكَ وَمِنۡهُم مَّن لَّمۡ نَقۡصُصۡ عَلَيۡكَ...﴾

{Haƙiƙa Mu ne muka aiko da Manzanni gabaninka, a cikin su akwai waɗanda muka baka labarin su akwai kuma wanda bamu baka labarin su ba}.[Gaafir:78].

Na uku: Gasgata abinda ya inganta daga gare su na labarukansu.

Na huɗu: Aiki da shari'ar wanda aka aiko zuwa gare mu daga cikinsu, shi ne cikamakinsu (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - wanda aka aiko zuwa dukkanin mutane, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce:

﴿فَلَا وَرَبِّكَ لَا يُؤۡمِنُونَ حَتَّىٰ يُحَكِّمُوكَ فِيمَا شَجَرَ بَيۡنَهُمۡ ثُمَّ لَا يَجِدُواْ فِيٓ أَنفُسِهِمۡ حَرَجٗا مِّمَّا قَضَيۡتَ وَيُسَلِّمُواْ تَسۡلِيمٗا 65﴾

{To, a'aha! Ina rantsuwa da Ubangijinka, ba za su yi ĩmãni ba, sai sun yarda da hukuncinka ga abin da ya sãɓa a tsakãninsu, sa'an nan kuma ba su sãmi wani ƙunci a cikin zukãtansu ba, daga abin da ka hukunta, kuma su sallama sallamãwa} [al-Nisa'i: 65].

Imani da manzanni yana da fa'idoji masu girma, yana daga cikinsu:

Ta farko: Sanin rahamar Allah - Maɗaukakin sarki -, da kulawarSa ga bayinSa, ta yadda Ya aiko manzanni zuwa gare su; dan Ya shiryar da su zuwa tafarkin Allah - Maɗaukakin sarki -kuma su bayyana musu yaya za su bautawa Allah, domin hankalin ɗan Adam ba zai keɓantu da sanin haka ba.

Ta biyu: Gode maSa - Allah Maɗaukakn sarki - a bisa wannan ni'imar mai girma.

Ta uku: Son manzanni - tsira da amincin Allah su tabbata a gare su - da girmamasu da yabo a garesu da abinda ya da ce da su, domin su manzannin Allah - Maɗaukakin sarki - ne, kuma domin cewa su sun tsaya da bauta maSa, da isar da saƙonSa da kuma nasiha ga bayinSa.

Haƙiƙa masu tsaurin kai sun ƙaryata manzanninsu, suna masu riya cewa manzannin Allah - Maɗaukakin sarki - ba za su kasance daga mutane ba! kuma haƙiƙa Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ambaci wannan riyawar, kuma Ya ɓatata da faɗarSa - tsarkakken sarki -:

﴿وَمَا مَنَعَ ٱلنَّاسَ أَن يُؤۡمِنُوٓاْ إِذۡ جَآءَهُمُ ٱلۡهُدَىٰٓ إِلَّآ أَن قَالُوٓاْ أَبَعَثَ ٱللَّهُ بَشَرٗا رَّسُولٗا 94 قُل لَّوۡ كَانَ فِي ٱلۡأَرۡضِ مَلَٰٓئِكَةٞ يَمۡشُونَ مُطۡمَئِنِّينَ لَنَزَّلۡنَا عَلَيۡهِم مِّنَ ٱلسَّمَآءِ مَلَكٗا رَّسُولٗا 95﴾

{Babu abinda ya hana mutane su yi imani lokacin da shiriya ta zo musu sai dan sunce shin Allah Ya aiko mutum a matsayin manzo?(94) Ka ce: Da a ce akan ƙasa akwai Mala'iku da suke tafiya ababan nutsuwa, lalle da Mun saukar da mala'ika daga sama agaresu a matsayin manzo(95)} [al- Israa: 94-95].

Sai Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ɓata wannan riyawar da cewa lallai ba makawa Manzo ya kasnce mutum; domin shi abin aikowa ne zuwa ahalin ƙasa, su kuma mutane ne, da ace mutanan ƙasa mala'iku ne, da Allah Ya saukar da Mala'ika daga sama a gare su, a matsayin Manzo dan ya zama irinsu, kamar haka Allah - Maɗaukakin sarki - Ya hakaito daga masu ƙaryatawa ga manzanni cewa su sun ce:

﴿...إِنۡ أَنتُمۡ إِلَّا بَشَرٞ مِّثۡلُنَا تُرِيدُونَ أَن تَصُدُّونَا عَمَّا كَانَ يَعۡبُدُ ءَابَآؤُنَا فَأۡتُونَا بِسُلۡطَٰنٖ مُّبِينٖ 10 قَالَتۡ لَهُمۡ رُسُلُهُمۡ إِن نَّحۡنُ إِلَّا بَشَرٞ مِّثۡلُكُمۡ وَلَٰكِنَّ ٱللَّهَ يَمُنُّ عَلَىٰ مَن يَشَآءُ مِنۡ عِبَادِهِۦۖ وَمَا كَانَ لَنَآ أَن نَّأۡتِيَكُم بِسُلۡطَٰنٍ إِلَّا بِإِذۡنِ ٱللَّهِ...﴾

{Ku ba ku zama ba face mutane kamarmu, kuna nufin ku tsare mu daga abinda iyayenmu suke bautawa, to ku zo da wata hujja mabayyaniya, manzanninsu suka ce da su, mu ba mu zama ba face mutane kamarku, sai dai Allah Yana yin baiwarsa ga wanda Yake so daga bayinSa, ba ya kasancewa a garemu mu zo muku da wata hujja sai da izinin Allah}.

[Ibrahm:10-11].

***

IMANI DA RANAR LAHIRA

Ranar lahira: Ranar Alƙiyama wacce za a tashi mutane a cikinta, dan hisabi da sakamako.

An ambace ta da hakan: domin babu wata rana a bayanta, ta yadda 'yan Aljanna zasu tabbata a gidajensu, 'yan wuta kuma (zasu tabbata) a cikin gidajensu.

Imani da ranar lahira yana ƙunsar al'amura uku:

Na ɗaya: Imani da tashi: Shi ne rayar da matattu lokacin da za a yi busa a cikin ƙaho, busa ta biyu, sai mutane su tashi ga Allah Ubangijin talikai, marasa takalma, ba masu takalma ba, matsiraita, ba masu tufafi ba, masu loɓa ba masu kaciya ba, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce:

﴿...كَمَا بَدَأۡنَآ أَوَّلَ خَلۡقٖ نُّعِيدُهُۥۚ وَعۡدًا عَلَيۡنَآۚ إِنَّا كُنَّا فَٰعِلِينَ﴾

{Zamu dawo da shi kamar yadda Muka fare shi a farkon halitta alƙawarin Mune lallai ne Mu Masu aikatawa ne}.

[al-Anbyaa: 104].

Tashi: Gaskiiya ne tabbatacce, da Alƙur’ani da Sunna sun yi nuni a kan hakan, da haɗuwar musulmai.

Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Sannan lalle ku bayan haka lalle masu mutuwa ne, sannan haƙiƙa za'a ta so ku ranar alƙiyama}.

[al-Mu'uminuna: 15-16].

Kuma Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Za a tattara mutane ranar alƙiyama, marasa takalma, matsiraiita, masu loɓa". An haɗu a kansa.

Kuma musulmai sun haɗu a bisa tabbatarsa, kuma shi ne manufar hikima; inda take hukunta cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Yana sanya wa wannan halittar makoma, da Zai yi musu sakayya a cikinta akan abinda Ya shara'anta musu a cikin abinda Ya aiko ManzanninSa da su, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce:

﴿أَفَحَسِبۡتُمۡ أَنَّمَا خَلَقۡنَٰكُمۡ عَبَثٗا وَأَنَّكُمۡ إِلَيۡنَا لَا تُرۡجَعُونَ 115﴾

{Shin, to, kun yi zaton cẽwa Mun halitta ku ne da wãsa kuma lalle ku, zuwa gare Mu, ku kõmo ba} [al- Mu'uminuun: 115]. Kuma Ya ce da AnnabinSa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -:

﴿إِنَّ ٱلَّذِي فَرَضَ عَلَيۡكَ ٱلۡقُرۡءَانَ لَرَآدُّكَ إِلَىٰ مَعَادٖ...﴾

{Haƙiƙa wanda Ya faralanta Alƙur'ani a gareka mai mayar da kaine zuwa makoma} [al-Kasas: 85].

Na biyu: Imani da hisabi da sakamako: za a yi wa bawa hisabi a kan aikinsa, kuma a saka masa a kansa, haƙiƙa Littafi (Alkur’ani), da sunna, da haɗuwar musulmai sun yi nuni a kan haka.

Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Haƙiƙa makomarsu tana zuwa gare Mu sannan hisabunsu Yana gare Mu}.

[al-Gashiya:25-26].

وقال تعالى: ﴿مَن جَآءَ بِٱلۡحَسَنَةِ فَلَهُۥ عَشۡرُ أَمۡثَالِهَاۖ وَمَن جَآءَ بِٱلسَّيِّئَةِ فَلَا يُجۡزَىٰٓ إِلَّا مِثۡلَهَا وَهُمۡ لَا يُظۡلَمُونَ 160﴾

وقال تعالى: ﴿وَنَضَعُ ٱلۡمَوَٰزِينَ ٱلۡقِسۡطَ لِيَوۡمِ ٱلۡقِيَٰمَةِ فَلَا تُظۡلَمُ نَفۡسٞ شَيۡـٔٗاۖ وَإِن كَانَ مِثۡقَالَ حَبَّةٖ مِّنۡ خَرۡدَلٍ أَتَيۡنَا بِهَاۗ وَكَفَىٰ بِنَا حَٰسِبِينَ47﴾

Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Wanda ya zo da kyakkyãwan aiki guda, to, yanã da gõma ɗin misãlansa. Kuma wanda ya zo da mũgun aiki gũda, to, a sãka masa ba fãce da misãlinsa. Kuma a zãluntar su} [al- An'aam: 160].

Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Kuma Munã aza ma'aunan ãdalci ga Rãnar kiyãma, sabõda haka ba a zãluntar rai da kõme. Kuma ya kasance nauyin ƙwãya daga kõmayya ne Mun zo da ita. Kuma Mun isa zama Mãsu hisãbi} [al- Anbiyaa: 47].

Kuma daga Ibnu Umar - Allah Ya yarda da su - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Haƙiƙa Allah Yana kusanto da mumini, sai Ya sanya sitirarSa a kansa, - wato Ya suturce shi -: Sai Ya ce: Shin kana sanin zunubi kaza? shin kana sanin zunubi kaza? sai ya ce: Eh, ya Ubangiji, har ya yin da Ya tabbatar masa da zunubansa, ya tabbatar a kan kansa cewa shi ya halaka, sai (Allah) Ya ce: Na suturta su a gare ka a duniya, a yau Ni kuma zan gafarta su a gare ka, sai a ba shi littafin kyawawan ayyukansa.

Amma kafirai da munafikai, sai a yi kira a gaban halittu: (a ce) waɗannan sune waɗanda suka karyata Ubangijnsu, ku saurara, tsinuwar Allah ta tabbata akan azzalimai". An haɗu a kansa.

Kuma ya inganta daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: "Cewa wanda ya yi nufin (aikata) kyakkyawan aiki guda ɗaya, sai ya aikata ta, Allah zai rubuta shi kyawawa goma a gurinsa, har zuwa ninki ɗari bakwai, zuwa ninke-ninke masu yawa, kuma wanda ya yi nufin (aikata) mummunan aiki, kuma ya aikata shi, Allah zai rubuta shi mummuna guda ɗaya".

Haƙiƙa musulmai sun haɗu akan tabbatar da hisabi da sakamako akan ayyuka, kuma shi ne abinda hikima take hukuntarwa (nema), haƙiƙa Allah - Maɗaukakin sarki - Ya saukar da littattafai, kuma Ya aiko Manzanni, Ya farlanta wa bayi karɓar abinda suka zo da shi, da kuma aiki da abinda aiki yake wajaba da shi daga gare shi, kuma Ya wajabta yaƙar masu bijire masa, Ya halatta jinanansu, da zurriyarsu, da matayensu, da dukiyoyinsu, Kuma da a ce hisabi da sakamako ba za su kasance ba, da hakan ya kasance yana daga wasa, wanda ake tsarkake Ubangiji gwani daga gare shi, haƙiƙa Allah - Maɗaukakin sarki - Ya yi nuni zuwa ga haka a faɗarSa:

﴿فَلَنَسۡـَٔلَنَّ ٱلَّذِينَ أُرۡسِلَ إِلَيۡهِمۡ وَلَنَسۡـَٔلَنَّ ٱلۡمُرۡسَلِينَ 6 فَلَنَقُصَّنَّ عَلَيۡهِم بِعِلۡمٖۖ وَمَا كُنَّا غَآئِبِينَ 7﴾

{Lalle za mu tambayi waɗanda aka aika (Annabawa) zuwa gare su, kuma lalle za mu tambayi Manzanni(6) kuma lalle zamu labarta musu (abinda suka aikata) da sani (da gare Mu) kuma ba Mu kasance a fake (ga barin abinda suke aikatawa) ba(7)}.[al- Aaraf: 6-7].

Na uku: Imani da aljanna da wuta kuma cewa su makoma ce ta har abada ga halitta.

Aljanna gida ne na ni'ima wacce Allah Ya tanade ta ga muminai, masu tsoran Allah, waɗanda suka yi imani da abinda Allah Ya wajabta a kansu da su yi imani da shi, kuma suka tsaya da biyayyar Allah da ManzanSa, suna masu tsarkake (ayyukansu ga Allah, masu bin manzanSa, a cikinta (Aljanna) akwai daga nau'oin ni'ima "Abinda ido bai taɓa gani ba, kunne bai taɓa ji ba, kuma bai taɓa ɗarsuwa a zuciyar wani ɗan Adam ba", Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce:

﴿إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ أُوْلَٰٓئِكَ هُمۡ خَيۡرُ ٱلۡبَرِيَّةِ 7 جَزَآؤُهُمۡ عِندَ رَبِّهِمۡ جَنَّٰتُ عَدۡنٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَآ أَبَدٗاۖ رَّضِيَ ٱللَّهُ عَنۡهُمۡ وَرَضُواْ عَنۡهُۚ ذَٰلِكَ لِمَنۡ خَشِيَ رَبَّهُۥ 8﴾

وقال تعالى: ﴿فَلَا تَعۡلَمُ نَفۡسٞ مَّآ أُخۡفِيَ لَهُم مِّن قُرَّةِ أَعۡيُنٖ جَزَآءَۢ بِمَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ 17﴾

[Lalle waɗanda suka yi imani, kuma suka yi ayyuka managarta waɗannan sune mafi alkhairin halitta(7) sakamakonsu (na lada a lahira) yana gurin Ubangijinsu, Aljannatan dawwama, da ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashin katangunsu, suna masu dawwama a cikinsu har abada, Allah Ya yarda da su, suma sun yarda da (abinda Ya basu na ni'ima) wannan (sakamako kyakkyawa) yana ga wanda ya ji tsoran Ubangijinsa(8)}.

[al- Bayyina: 7-8].

{Sabõda haka wani rai bai san abin da aka ɓõye musu ba, na sanyin idãnu, dõmin sakamako ga abin da suka kasance sunã aikatãwa(17)} [al-ssajada: 17].

Amma wuta: Ita gidan azaba ne wacce Allah - Maɗaukakin sarki - Ya tanade ta dan kafirai azzalumai, waɗanda suka kafirce da shi, kuma suka saɓawa manzanninSa, a cikinta akwai nau'ikan azaba da uƙuba waɗanda ba sa ɗarsuwa a cikin zuciya,

قال تعالى: ﴿وَٱتَّقُواْ ٱلنَّارَ ٱلَّتِيٓ أُعِدَّتۡ لِلۡكَٰفِرِينَ 131﴾

وقال تعالى: ﴿وَقُلِ ٱلۡحَقُّ مِن رَّبِّكُمۡۖ فَمَن شَآءَ فَلۡيُؤۡمِن وَمَن شَآءَ فَلۡيَكۡفُرۡۚ إِنَّآ أَعۡتَدۡنَا لِلظَّٰلِمِينَ نَارًا أَحَاطَ بِهِمۡ سُرَادِقُهَاۚ وَإِن يَسۡتَغِيثُواْ يُغَاثُواْ بِمَآءٖ كَٱلۡمُهۡلِ يَشۡوِي ٱلۡوُجُوهَۚ بِئۡسَ ٱلشَّرَابُ وَسَآءَتۡ مُرۡتَفَقًا 29﴾

وقال تعالى: ﴿إِنَّ ٱللَّهَ لَعَنَ ٱلۡكَٰفِرِينَ وَأَعَدَّ لَهُمۡ سَعِيرًا 64 خَٰلِدِينَ فِيهَآ أَبَدٗاۖ لَّا يَجِدُونَ وَلِيّٗا وَلَا نَصِيرٗا 65 يَوۡمَ تُقَلَّبُ وُجُوهُهُمۡ فِي ٱلنَّارِ يَقُولُونَ يَٰلَيۡتَنَآ أَطَعۡنَا ٱللَّهَ وَأَطَعۡنَا ٱلرَّسُولَا۠ 66﴾

Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Ku tsoraci wuta wacce aka tanade ta dan kafira(131)}.

[al- Imraana: 131]

{Kuma ka ce: "Gaskiya daga Ubangijinku take." Sabõda haka wanda ya so, to, ya yi ĩmãni, kuma wanda ya so, to, ya kãfirta. Lalle ne , Mun yi tattali dõmin azzãlumai wata wuta wadda shãmakunta, sun ƙẽwaye da su. Kuma idan sun nẽmi taimako sai a taimake su da wani ruwa kamar dabzar mai, yanã sõye fuskõki. Tir da abin shansu, kuma wutar ta yi mũnin zama mahũtarsu(29)}.

[al- Kahaf: 29]

Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Haƙiƙa Allah Ya tsinewa kafirai kuma Ya tanadar musu wuta mai ƙonewa(65) Suna masu dawwama a cikinta basu da majibinci ko maitaimako, ranar da za a juya fuskokinsu a cikin wuta, suna cewa inama mun bi Allah kuma mun bi Manzo(66)}.

[al-Ahzab: 64-66].

Imani da ranar lahira yana da fa'idoji masu girma, daga cikin su:

Ta farko: kwaɗayin aikata biyayya, da kwaɗayi a kanta, dan ƙauna ga ladan waccen ranar.

Ta biyu: tsoran aikata saɓo, da yarda da shi; dan tsoro daga uƙubar waccen ranar.

Ta uku: Rarrashin mumini, daga abinda yake rasawa na duniya da abinda yake ƙaunarsa na daga ni'imar lahira, da ladanta.

Haƙiƙa kafirai sun yi musun tashi bayan mutuwa, suna masu riya cewa hakan ba mai yuwuwa ba ne.

Wannan riyawar ɓatacciya, shari'a da riska da sarari, da hankali sun yi nuni a bisa ɓacinsa.

Amma a shari'a haƙiƙa Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Waɗanda suka kafirce sun riya cewa, ba za a tashe su ba, ka ce: Na rantse da Ubangijina lalle za'a tashe ku, sannan lalle za'a ba ku labari da abinda kuka aikata, hakan mai sauki ne ga Allah}.[al- Tagabun: 7]. Kuma haƙiƙa dukkanin littattafan sama sun haɗu akan sa.

Amma riska ta sarari: Haƙiƙa Allah Ya nunawa bayinSa rayar da matattu a wannan duniyar, akwai misalai biyar a cikin surar Baƙara akan haka, su ne:

Misali na farko: Mutanan (Annabi) Musa lokacin da suka ce da shi: {Ba za muyi imani da kai ba, har sai mun ga Allah a bayya ne}.

[al- Baƙara: 55].

 

Sai Allah - Maɗaukakin sarki - Ya kashe su, sannan Ya raya su, Akan haka ne Allah - Maɗaukakin sarki - Yake cewa, Yana Mai magana da 'ya'yan Isra'ila:

﴿وَإِذۡ قُلۡتُمۡ يَٰمُوسَىٰ لَن نُّؤۡمِنَ لَكَ حَتَّىٰ نَرَى ٱللَّهَ جَهۡرَةٗ فَأَخَذَتۡكُمُ ٱلصَّٰعِقَةُ وَأَنتُمۡ تَنظُرُونَ 55 ثُمَّ بَعَثۡنَٰكُم مِّنۢ بَعۡدِ مَوۡتِكُمۡ لَعَلَّكُمۡ تَشۡكُرُونَ 56﴾

{Ya yin da kuka ce ya Musa ba za mu yi imani da kai ba, har sai mun ga Allah a bayya ne, sai tsawa ta kama ku, alhali kuna kallo, sannan Ya tashe ku bayan mutuwarku dan ku godewa (Allah)}.

[al-Baƙara: 55-56].

Misali na biyu: A ƙissar wanda aka kashe, wanda 'ya'yan Isra'il suka yi husuma a sha'aninsa, sai Allah - Maɗaukakin sarki - Ya umarce su da su yanka saniya, su doke shi da shashin ta, dan Ya ba su labarin wanda ya kashe shi, akan haka ne Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ke cewa:

﴿وَإِذۡ قَتَلۡتُمۡ نَفۡسٗا فَٱدَّٰرَٰءۡتُمۡ فِيهَاۖ وَٱللَّهُ مُخۡرِجٞ مَّا كُنتُمۡ تَكۡتُمُونَ 72 فَقُلۡنَا ٱضۡرِبُوهُ بِبَعۡضِهَاۚ كَذَٰلِكَ يُحۡيِ ٱللَّهُ ٱلۡمَوۡتَىٰ وَيُرِيكُمۡ ءَايَٰتِهِۦ لَعَلَّكُمۡ تَعۡقِلُونَ 73﴾

{Yayin da kuka kashe wata rai sai ku ka yi ingijejeniya (saɓani da jayayya) akanta Allah Mai fitar da abinda kuka kasance kuna ɓoyewa ne(72) sai Muka ce ku daketa da sashinta, kamar haka ne Allah Yake raya matattu kuma Yake nuna muku ayoyinSa wataƙila ku zaku hankalta(73)} .

al-Baƙara: 72-73].

Misali na uku: A ƙissar mutanen da suka fita daga gidajensu dan gujewa mutuwa su dubunne ne' sai Allah - Maɗaukakin sarki - Ya kashe su sannan Ya raya su, akan haka ne Allah - Maɗaukakin sarki - Yake cewa:

﴿أَلَمۡ تَرَ إِلَى ٱلَّذِينَ خَرَجُواْ مِن دِيَٰرِهِمۡ وَهُمۡ أُلُوفٌ حَذَرَ ٱلۡمَوۡتِ فَقَالَ لَهُمُ ٱللَّهُ مُوتُواْ ثُمَّ أَحۡيَٰهُمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَذُو فَضۡلٍ عَلَى ٱلنَّاسِ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يَشۡكُرُونَ243﴾

{Shin, ba ka gani ba, zuwa ga waɗanda suka fita daga gidãjensu, alhãli kuwa dubbai ne, dõmin tsõron mutuwa? Sai Allah Ya ce musu: "Ku mutu." Sa'an nan kuma Ya rãyar da su, lalle ne Allah, haƙĩƙa Ma'abũcin falala a kan mutãne ne, kuma amma mafi yawan mutãne su gõdẽwa(243)} [al- Bakara:2243}.

Misali na huɗu: Kissar wanda ya wuce wata alƙarya matacciya, sai ya nisantar da cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Zai (sake) raya ta, sai Allah - Maɗaukakin sarki - Ya kashe shi shekara ɗari, sannan Ya raya shi, akan haka ne Allah - Maɗaukakin sarki - Yake cewa:

﴿أَوۡ كَٱلَّذِي مَرَّ عَلَىٰ قَرۡيَةٖ وَهِيَ خَاوِيَةٌ عَلَىٰ عُرُوشِهَا قَالَ أَنَّىٰ يُحۡيِۦ هَٰذِهِ ٱللَّهُ بَعۡدَ مَوۡتِهَاۖ فَأَمَاتَهُ ٱللَّهُ مِاْئَةَ عَامٖ ثُمَّ بَعَثَهُۥۖ قَالَ كَمۡ لَبِثۡتَۖ قَالَ لَبِثۡتُ يَوۡمًا أَوۡ بَعۡضَ يَوۡمٖۖ قَالَ بَل لَّبِثۡتَ مِاْئَةَ عَامٖ فَٱنظُرۡ إِلَىٰ طَعَامِكَ وَشَرَابِكَ لَمۡ يَتَسَنَّهۡۖ وَٱنظُرۡ إِلَىٰ حِمَارِكَ وَلِنَجۡعَلَكَ ءَايَةٗ لِّلنَّاسِۖ وَٱنظُرۡ إِلَى ٱلۡعِظَامِ كَيۡفَ نُنشِزُهَا ثُمَّ نَكۡسُوهَا لَحۡمٗاۚ فَلَمَّا تَبَيَّنَ لَهُۥ قَالَ أَعۡلَمُ أَنَّ ٱللَّهَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ 259﴾

{ kuwa wanda ya shũɗe a kan wata alƙarya, alhãli kuwa tana wõfintacciya a kan gadãjen rẽsunanta. Ya ce: "Yaya Allah zai rãyar da wannan a bãyan mutuwarta." Sai Allah Ya matar da shi, shẽkara ɗari; sa'an nankuma ya tãyar da shi. Ya ce: "Nawa ka zauna?" Ya ce: "Na zauna yini ɗaya ko kuwa rabin yini." Ya ce: "A'a kã zauna shẽkara ɗari." To, ka dũba zuwa ga abincinka, da abin shanka, (kõwanensu) bai sãke ba, kuma ka dũba zuwa ga jãkinka, kuma dõmin Mu sanya ka wata ãyã ga mutãne. Kuma ka duba zuwa ga ƙasũsuwa yadda Muke mõtsarda su sa'an nan kuma Mu tufãtar da su, da nãma", To, a lõkacin da (abin) ya bayyana a gare shi, ya ce: "Ina sanin cẽwa lalle Allah a kan dukan kõme Mai ĩkõn yi ne." .

[al-Baƙara: 259].

Misali na biyar: A ƙissar (Annabi) Ibrahim badaɗin Allah, lokacin da ya roƙi Allah - Maɗaukakin sarki - da Ya nuna masa yadda Yake raya matattu, sai Allah - Maɗaukakin sarki - Ya umarce shi da ya yanka tsuntsaye huɗu, kuma ya rarrabasu a gutaittsire akan duwatsun da suke kewaye da shi, sannan ya kira su a gutsittsiran za su haɗu shashinsu zuwa shashi, kuma za su zo wurin (annabi) Ibrahim da sauri, akan haka ne Allah - Maɗaukakin sarki - Yake cewa:

﴿وَإِذۡ قَالَ إِبۡرَٰهِـۧمُ رَبِّ أَرِنِي كَيۡفَ تُحۡيِ ٱلۡمَوۡتَىٰۖ قَالَ أَوَلَمۡ تُؤۡمِنۖ قَالَ بَلَىٰ وَلَٰكِن لِّيَطۡمَئِنَّ قَلۡبِيۖ قَالَ فَخُذۡ أَرۡبَعَةٗ مِّنَ ٱلطَّيۡرِ فَصُرۡهُنَّ إِلَيۡكَ ثُمَّ ٱجۡعَلۡ عَلَىٰ كُلِّ جَبَلٖ مِّنۡهُنَّ جُزۡءٗا ثُمَّ ٱدۡعُهُنَّ يَأۡتِينَكَ سَعۡيٗاۚ وَٱعۡلَمۡ أَنَّ ٱللَّهَ عَزِيزٌ حَكِيمٞ 260﴾

{Kuma a lõkacin da Ibrãhĩm ya ce: "Ya Ubangijina! Ka nũna mini yadda Kake rãyar da matattu." Ya ce: "Shin, kuma ba ka yi ĩmãni ba?" Ya ce: "Na'am! Kuma amma dõmin zũciyãta, ta natsu." Ya ce: "To ka riƙi huɗu daga tsuntsãye, ka karkatar da su zuwa gare ka, ka yanka su, sa'an nan kuma ka sanya juzu'i daga gare su a kan kõwane dũtse, sa'an nan kuma ka kira su su zo maka gudãne. Kuma ka sani cẽwa lalle Allah Mabuwãyi ne, Masani(260)} [al- Baƙara: 260].

Waɗannan misalai na sarari waɗanda suka faru, suna nuni a bisa yuwuwar rayar da matattu, haƙiƙa nuni ya gabata zuwa abinda Allah - Maɗaukakin sarki - Ya sanya shi daga mu'ujizozin (Annabi) Isa dan Nana Maryam, na rayar da matattu, da kuma futo da su daga ƙabarurrukansu da izinin Allah - Maɗaukakin sarki -:

Amma nunin hankali: Daga fuskoki biyu ne:

Ɗaya daga cikinsu: Cewa Allah - Maɗaukakin sarki - (Shi ne) Mahaliccin sammai da ƙasa, da abinda yake cikinsu, Mahaliccinsu tun farko, kuma Mai iko akan farar halitta ba ya gajiyawa daga dawo da ita, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce:

﴿وَهُوَ ٱلَّذِي يَبۡدَؤُاْ ٱلۡخَلۡقَ ثُمَّ يُعِيدُهُۥ وَهُوَ أَهۡوَنُ عَلَيۡهِ...﴾

وقال تعالى: ﴿...كَمَا بَدَأۡنَآ أَوَّلَ خَلۡقٖ نُّعِيدُهُۥۚ وَعۡدًا عَلَيۡنَآۚ إِنَّا كُنَّا فَٰعِلِينَ﴾

{Kuma Shi ne ke fara yin halitta, sannan Ya dawo da ita, kuma dawowar tafi sauƙi a gare shi} [al- Ruum: 27].

Kuma maɗaukakin sarki - Ya ce: {Kamar yadda Muka farar da farkon halitta, za Mu dawo da ita, alƙawari ne a gareMu, haƙiƙa Mun kasance masu aikatawa} [al- Anbiyaa: 104]. Kuma Ya ce Yana Mai umarni da maida martani ga wanda ya yi musun rayar da ƙasussuwa, alhaln suna rididdigaggu:

﴿قُلۡ يُحۡيِيهَا ٱلَّذِيٓ أَنشَأَهَآ أَوَّلَ مَرَّةٖۖ وَهُوَ بِكُلِّ خَلۡقٍ عَلِيمٌ 79﴾

{Ka ce: "Wanda ya ƙãga halittarsu a farkon lõkaci Shĩ ke rãyar da su, kuma Shi, game da kõwace halitta, Mai ilmi ne(79)} [Yasin: 79].

Na biyu: Haƙiƙa ƙasa tana kasancewa matacciya rusasshiya, babu koriyar bishiya a kanta, sai ruwan sama ya sauka a kanta, sai ta yi motsi tana koriya rayayyiya, a kanta akwai daga dukkan nau'i biyu masu ƙayatarwa, Mai iko a bisa rayar da ita, bayan mutuwarta, Mai iko ne a bisa raya matattu, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce:

﴿وَمِنۡ ءَايَٰتِهِۦٓ أَنَّكَ تَرَى ٱلۡأَرۡضَ خَٰشِعَةٗ فَإِذَآ أَنزَلۡنَا عَلَيۡهَا ٱلۡمَآءَ ٱهۡتَزَّتۡ وَرَبَتۡۚ إِنَّ ٱلَّذِيٓ أَحۡيَاهَا لَمُحۡيِ ٱلۡمَوۡتَىٰٓۚ إِنَّهُۥ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٌ 39﴾

وقال تعالى: ﴿وَنَزَّلۡنَا مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءٗ مُّبَٰرَكٗا فَأَنۢبَتۡنَا بِهِۦ جَنَّٰتٖ وَحَبَّ ٱلۡحَصِيدِ9 وَٱلنَّخۡلَ بَاسِقَٰتٖ لَّهَا طَلۡعٞ نَّضِيدٞ 10 رِّزۡقٗا لِّلۡعِبَادِۖ وَأَحۡيَيۡنَا بِهِۦ بَلۡدَةٗ مَّيۡتٗاۚ كَذَٰلِكَ ٱلۡخُرُوجُ 11﴾

{Kuma akwai daga ãyõyinSa cẽwa lalle kai kanã ganin ƙasã ƙẽƙasasshiya, to, idan Mun saukar da ruwa a kanta, sai ta girgiza kuma ta kumbura. Lalle wannan da Ya rãya ta, haƙĩƙa, Mai rãyar da matattu ne. Lalle Shĩ Mai ĩkon yi ne a kan kõwane abu} [Fussilaat: 39].

Kuma Maɗaukakin sarki Ya ce: {Kuma Mun saukar da ruwa mai albarka daga sama, sai Muka tsirar da gonakai da ƙwaya (shuka) abar girbewa(9) Da dabinai masu tsawo suna da huda mai hauhawa(10) Dan arziƙi ga bayi, kuma rayar da mataccen gari da shi, (to) kamar haka ne futowa (bayan mutuwa a raye)(11)}.[Kaaf: 9-11].

Kuma yana shiga cikin Imani da ranar lahira yin imani da duk abinda zai kasance bayan mutuwa, misali:

(a) Fitinar ƙabari: Ita ce tambayar mamaci bayan binne shi, dangane da Ubangijinsa, da Addininsa, da Annabinsa, sai Allah Ya tabbatar da waɗanda suka yi imani da magana tabbatacciya, sai ya ce Ubangijina (shi ne) Allah, Addinina Musulinci, Annabina Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -

Allah Yana ɓatar da azzalumai, sai kafiri ya ce: Haa, haa, ban sani ba, munafiki ko mai kokanto sai ya ce: Ban sani ba, na ji mutane suna faɗar wani abu sai na faɗe shi.

(b) Azabar ƙabari da ni'imarsa: Tana kasancewa ga azzalimai daga munafukai da kafirai, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce:

﴿...وَلَوۡ تَرَىٰٓ إِذِ ٱلظَّٰلِمُونَ فِي غَمَرَٰتِ ٱلۡمَوۡتِ وَٱلۡمَلَٰٓئِكَةُ بَاسِطُوٓاْ أَيۡدِيهِمۡ أَخۡرِجُوٓاْ أَنفُسَكُمُۖ ٱلۡيَوۡمَ تُجۡزَوۡنَ عَذَابَ ٱلۡهُونِ بِمَا كُنتُمۡ تَقُولُونَ عَلَى ٱللَّهِ غَيۡرَ ٱلۡحَقِّ وَكُنتُمۡ عَنۡ ءَايَٰتِهِۦ تَسۡتَكۡبِرُونَ

{Kuma da zaka ga lokacin da azzalumai a cikin magagin mutuwa kuma mala'iku suna shimfiɗe da hannayensu ku futo da kawunanku (rayukanku), yau ne za'a saka muku da azabar wulaƙanci saboda abinda kuka kasance kuna faɗawa Allah wanda ba na gaskiya ba, da kuma abinda kuka kasance kuna girman kai da ayoyinSa}.

[al-An'am: 93].

Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce akan Fir'auna: {Wutar (ƙabari) za'a dinga ƙona su da ita, safe da yammaci, ranar da Alƙiyama za ta ta shi (za'a ce da mala'iku) ku shigar da Fir'auna da mutanansa mafi tsananin azba}.[Gaafir:46].

Acikin Sahihu Muslim kuma, daga Hadisin Zaid bn Sabit-Allah Ya yarda da shi- daga Annabi-tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya ce: "Da ba dan kada kubar binne mamatanku ba (dan tsoro) da na roƙi Allah da Ya jiyar da ku daga azabar ƙabari wanda nake ji daga gare shi".

Sannan sai ya fuskanto da fuskarsa ya ce: "Ku nemi tsarin Allah daga azabar wuta" suka ce: Muna neman tsarin Allah daga azabar wuta, ya ce: "Ku nemi tsarin Allah daga azabar ƙabari", suka ce: Muna neman tsarin Allah daga azabar ƙabari, ya ce: "Ku nemi tsarin Allah daga fitintunu abinda ya bayyana daga gare su, da abinda ya ɓoyu", suka ce: Muna neman tsarin Allah daga fitintunu abinda ya bayyana daga gare su, da abinda ya ɓoyu, ya ce: "Ku nemi tsarin Allah daga fitinar Jujal" suka ce: Muna neman tsarin Allah daga fitinar Jujal.

Amma ni'imar ƙabari: Tana ga muminai masu gaskiya, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Haƙiƙa waɗanda suka ce Ubangjinmu shi ne Allah sannan suka tsayu, Mala'iku za su dinga saukowa a gare su (suna cewa) kada ku ji tsoro kada ku yi baƙin ciki, ku yi bushara da Aljanna wacce kuka kasance ana yi muku alƙawari} [Fussilat: 30].

Kuma Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Idan (rai) ya kai maƙogaro, ku a wannan lokaci kuna kallo, (zuwa mai mutuwa) Mune mafi kusanci da shi fiye da ku, ina ma har in kun kasance ku ba ababan yi wa hisabi ba ne, ku dawo da ita (ran mamacin), in har kun kasnce masu gaskiya ne.

Amma idan ya kasance (mamacin) daga makusanta(88) Hutu da arziƙi kyakkyawa sun tabbata a gare shi, da Aljannar ni'ima(89)}.{al- Waƙi'a: 88-89].

An karɓo daga Barraa'u bn Azib-Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce a sha'anin mumini idan ya amsawa mala'iku biyu a cikin ƙabarinsa: "Mai kira zai yi kira daga sama: Cewa bawaNa ya yi gaskiya, ku yi masa shimfiɗa daga Ajanna, ku sanya masa (tufafi) daga Aljanna, ku buɗe masa ƙofa zuwa Aljanna, ya ce sai ya zo masa daga ƙanshinta da daɗinta, kuma a yalwata masa ƙabarinsa iyaka ganinsa".

Ahmad da Abu Dauda ne suka ruwato shi a ckin hadisi mai tsawo.

Haƙiƙa wasu mutanan daga ma'abota karkata

sun ɓata, da suka yi musun azabar ƙabari, da ni'imarsa, suna masu riya cewa hakan ba mai yi wuwa ba ne, saboda saɓawarsa abinda yake faruwa, domin da za’a yaye mamaci a ƙabarinsa, da an same shi kamar yadda ya kasance akansa, ƙabarin kuma bai canza ba da yalwa ko da ƙunci.

Wannan riyawar ɓatacciya ce, a shari'a da riskar sarari da hankali:

Amma a shari'a: Haƙiƙa nassosi sun gabata masu nuni a bisa tabbatar azabar ƙabari da ni'marsa.

A cikin Sahihul Bukhari daga hadisin dan Abbas-Allah Ya yarda da su- ya ce: Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya fita a shingen Madina, sai ya ji sautin mutane biyu anayi musu azaba a cikin ƙabarinsu", sai ya ambaci hadisin, kuma a cikinsa: "Cewa ɗayansu ba ya suturta daga fitsari" a cikin wata ruwaya kuma: "Daga fitsarinsa", ɗayan kuma ya kasance yana tafiya da annamimanci".

A wata ruwaya kuma ta Muslim: "Baya tsarkaka daga bawali".

Amma riskar sarari: Haƙiƙa mai barci yana gani a cikin barcinsa, cewa shi ya kasance a wani guri mai faɗi mai kwarjini, yana ni'imtuwa a cikinsa, ko kuma cewa shi ya kasance a wani guri ƙuntatacce mai kewa, yana jin raɗaɗi daga gare shi, wani lokaci ya kan farka daga abinda ya gani, Kuma duk da haka shi yana kan shinfiɗarsa a cikin ɗakinsa a kan abinda yake a kansa, bacci ɗan uwan mutuwa ne, saboda wannan ne ma Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ambace shi: (mutuwa) Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce:

﴿ٱللَّهُ يَتَوَفَّى ٱلۡأَنفُسَ حِينَ مَوۡتِهَا وَٱلَّتِي لَمۡ تَمُتۡ فِي مَنَامِهَاۖ فَيُمۡسِكُ ٱلَّتِي قَضَىٰ عَلَيۡهَا ٱلۡمَوۡتَ وَيُرۡسِلُ ٱلۡأُخۡرَىٰٓ إِلَىٰٓ أَجَلٖ مُّسَمًّى...﴾

{Allah ne ke karɓar rãyuka a lõkacin mutuwarsu, da waɗannan da ba su mutu ba, a cikin barcinsu. Sannan Ya riƙe wanda Ya hukunta mutuwa a kansa kuma Ya saki gudar, har zuwa ga ajali ambatacce. Lalle a cikin wancan, haƙĩƙa, akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda ke yin tunãni} [al-Zumar: 42].

Amma hankali: Haƙiƙa mai barci yana ganin mafarkin gaskiya ne mai da cewa ne da abinda yake faruwa a barcinsa, yakan iya ganin Annabi- tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- abisa siffarsa, wanda kuma ya gan shi a bisa siffarsa to haƙiƙa ya gan shi da gaske, amma duk da haka, mai barci yana cikin ɗakinsa a kan shimfiɗarsa nesa da abinda ya gani. Idan har wannan ya zama mai yi wuwa ne a abubuwan duniya, to, shin ba zai yi wu ba a abubuwan lahira?!

Amma kuma dogaransu cikin abinda suka riya shi cawa, da za a tone mamaci a cikin ƙabarinsa, da an same shi kamar yadda aka binne shi, kuma ƙabarin bai canza ba, da yalwatuwa ko ƙuntata, to amsarsa akan haka ta wasu fuskoki ne, ga wasu:

Na farko: Cewa bijirewa abinda shari'a ta zo da shi ba ya halatta, da misalin waɗannan shubhohi ɓatattu rusassu, waɗanda da mai bijre musu zai lura da abinda shari'ar gaskiya ta zo da shi, da ya san ɓacin waɗannan shubhohi, haƙiƙa an ce:

Da yawa daga mai aibata magana ingattacciya

Aibukansa na daga mummunar fahimta ne

Na biyu: Cewa halayen barzahu na daga al'amuran gaibu, waɗanda riska ta zahiri ba ta riskarsu, da a ce ana riskarsu da riska ta sarari, da fa'idar imani da gaibu an rasa ta, da kuma masu imani da gaibu da masu musun gasgata shi sun daidaita.

Na uku: Cewa azaba, da ni'ma, da yalwar ƙabari, da ƙuncinsa, kaɗai mamaci ne ya ke riskarsu banda waninsa, wannan kuwa kamar yadda mai barci yake gani a cikin barcinsa, cewa shi yana wani guri ƙuntatacce mai kewa, ko kuma a wani guri mai yalwa mai ƙayatarwa, alhalin wanda ke kewaye da shi ba y ganin hakan ba ya kuma jinsa, Kuma haƙiƙa Annabi- tsira da amincin Allah su tabbata a agare shi- ya kasance ana wahayi zuwa gare shi, alhalin yana tsakanin sahabbansa, sai ya ji wahayi, sahabbai kuma ba sa jinsa, kuma da yawa mala'ika yakan kamantu da mutum sai ya yi masa magana, sahabbai kuma ba sa ganin mala'ikan, ba kuma sa jinsa.

Na huɗu: Cewa riskar halitta abar iyakancewa ce da abinda Allah - Maɗaukakin sarki - Ya tabbatar musu riskarsa, riskar kowanne abu ba zai yi wu ba, sammai bakwai, da ƙasa, da abinda ke cikinsu, kowanne abu suna tsarkake da godewa Allah, tsarkakewa ta haƙiƙa, wani lokaci Allah - Maɗaukakin sarki - Yana jiyar da tsarkakewar ga wanda Ya so daga halittarSa, tare da haka shi abin tsarewa ne a gare mu, akan haka ne, Allah - Maɗaukakin sarki - Yake cewa:

﴿تُسَبِّحُ لَهُ ٱلسَّمَٰوَٰتُ ٱلسَّبۡعُ وَٱلۡأَرۡضُ وَمَن فِيهِنَّۚ وَإِن مِّن شَيۡءٍ إِلَّا يُسَبِّحُ بِحَمۡدِهِۦ وَلَٰكِن لَّا تَفۡقَهُونَ تَسۡبِيحَهُمۡۚ...﴾

{Sammai bakwai, da ƙasa da abinda ya ke cikinsu suna tsarkakewa a gare Shi, babu wani abu face yana tsarkakewa da gode maSa, sai dai ba kwa fahimtar tsarkakewarsu}.[al-isra'i: 44].

Kuma haka nan shaiɗanu da aljanu suna tafiya a bayan ƙasa, tafiya da dawowa, kuma haƙiƙa aljanu sun halarci Manzan Allah suka ji karatunsa, kuma suka saurara, suka juya zuwa mutanansu suna ma su gargaɗi, tare da wannan su ababan shamakancewa ne a gare mu, akan haka ne Allah - Maɗaukakin sarki - Yake cewa:

﴿يَٰبَنِيٓ ءَادَمَ لَا يَفۡتِنَنَّكُمُ ٱلشَّيۡطَٰنُ كَمَآ أَخۡرَجَ أَبَوَيۡكُم مِّنَ ٱلۡجَنَّةِ يَنزِعُ عَنۡهُمَا لِبَاسَهُمَا لِيُرِيَهُمَا سَوۡءَٰتِهِمَآۚ إِنَّهُۥ يَرَىٰكُمۡ هُوَ وَقَبِيلُهُۥ مِنۡ حَيۡثُ لَا تَرَوۡنَهُمۡۗ إِنَّا جَعَلۡنَا ٱلشَّيَٰطِينَ أَوۡلِيَآءَ لِلَّذِينَ لَا يُؤۡمِنُونَ 27﴾

{ ɗiyan Ãdam! Kada Shaiɗan, lalle, ya fitine ku, kamar yadda ya fitar da iyãyenku, biyu daga Aljanna, yanã fizge tufarsu daga gare su, dõmin ya nũna musu al'aurarsu. Lalle ne shĩ, yanã ganin ku, shi da rundunarsa, daga inda ku ganin su. Lalle ne , Mun sanyaShaiɗan majiɓinci ga waɗanda su yin ĩmãni} [al-Aaraf: 27]. Idan ya kasance halitta ba sa riskar kowanne abu, to lalle ba ya halatta su yi musun abinda ya tabbata na daga al'amuran gaibu (fake) da ba su riske shi ba.

***

IMANI DA KADDARA

Kaddara (da yi wa Dal fataha, a ce: KADAR): Kaddarawar Allah - Maɗaukakin sarki - ga kasantattu, gwargwadan abinda saninSa ya gabata da shi, kuma hikimarSa ta hukuntar da shi.

Imani da ƙaddara yana ƙunsar al'amura huɗu:

Na ɗaya: Imani da cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Masani ne da dukkan komai a dunƙule da rarrabe, tun fil'azal kuma har abada, daidai ne hakan ya kasance daga abinda ya ke da alaƙa da ayyukansa, ko da aikin bayinSa.

Na biyu: Imani da cewa haƙiƙa Allah - Maɗaukakin sarki - Ya rubuta haka a Allo abin kiyayewa, (Allon ƙudira), a cikin waɗannan al'amura biyun Allah - Maɗaukakin sarki - Yake cewa:

﴿أَلَمۡ تَعۡلَمۡ أَنَّ ٱللَّهَ يَعۡلَمُ مَا فِي ٱلسَّمَآءِ وَٱلۡأَرۡضِۚ إِنَّ ذَٰلِكَ فِي كِتَٰبٍۚ إِنَّ ذَٰلِكَ عَلَى ٱللَّهِ يَسِيرٞ 70﴾

{Shin baka san cewa ba Allah Yana sanin abinda ke cikin sama da ƙasa, haƙiƙa hakan yana cikin Littafi, lalle hakan mai sauƙi ne ga Allah(70)}.

[al-Hajj: 70].

A cikin Sahihu Muslm daga Abdullahi ɗan Amru ɗan Aas -Allah Ya yarda da su - ya ce: Na ji Manzan Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Allah Ya rubuta ƙaddarorin halitta kafin Ya halicci sammai da ƙasa da shekaru dubu hamsin".

Na uku: Imani da cewa dukkan kasantattu ba sa kasancewa sai da son Allah - Maɗaukakin sarki -, daidai ne shin sun kasance daga abinda yake da alaƙa da ayyukansa, ko abinda yake da alaƙa da ababan halitta, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce cikin abinda yake da alaƙa da aikinSa:

﴿وَرَبُّكَ يَخۡلُقُ مَا يَشَآءُ وَيَخۡتَارُۗ...﴾

وقال: ﴿...وَيَفۡعَلُ ٱللَّهُ مَا يَشَآءُ

وقال: ﴿هُوَ ٱلَّذِي يُصَوِّرُكُمۡ فِي ٱلۡأَرۡحَامِ كَيۡفَ يَشَآءُۚ...﴾

وقال تعالى فيما يتعلّق بفعل المخلوقين: ﴿...وَلَوۡ شَآءَ ٱللَّهُ لَسَلَّطَهُمۡ عَلَيۡكُمۡ فَلَقَٰتَلُوكُمۡ...﴾

وقال: ﴿...وَلَوۡ شَآءَ رَبُّكَ مَا فَعَلُوهُۖ فَذَرۡهُمۡ وَمَا يَفۡتَرُون

{Ubangijinka Yana halittar abinda Yake so kuma Yana zaɓa.

[al-Kasas: 68]

Kuma Ya ce: {Kuma Allah Yana aikata abinda Yake so}.

[Ibrahim: 27]

Kuma Ya ce: {Shi ne wanda Yake suranta ku a cikin mahaifa yadda Yake so}.

[al-Imraan: 6]. kuma Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce a cikin a binda yake da alaƙa da aikin ababan halitta:

{Da Allah Ya so da Ya ba su rinjaye akanku sai su yaƙe ku}.

[al- Nisaa: 90]

{Da Ubangijinka Ya so da basu aikata shi ba, ka barsu da abinda suke ƙirƙira}

[al-An'am:112].

Na huɗu: Imani da cewa dukkanin kasantattu ababan halittar Allah - Maɗaukakin sarki ne -, da zatinsu, da siffofinsu, da motsunsu, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce:

﴿ٱللَّهُ خَٰلِقُ كُلِّ شَيۡءٖۖ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ وَكِيلٞ 62﴾

وقال سبحانه: ﴿...وَخَلَقَ كُلَّ شَيۡءٖ فَقَدَّرَهُۥ تَقۡدِيرٗا

{Allah ne Mai halitta dukan kõme, kuma Shĩ ne Wakĩli a kan kõme} [al-Ruum: 62]

Kuma tsarkakken sarki Ya ce: {Ya halicci kowanne abu Ya ƙaddara shi ƙaddarawa}.[al-Furƙan: 2] Kuma Ya ce dan gane da AnnabinSa Ibrahim - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - cewa shi ya cewa mutanansa:

﴿وَٱللَّهُ خَلَقَكُمۡ وَمَا تَعۡمَلُونَ 96﴾

{Alhãli, Allah ne Ya halicce ku da abin da kuke aikatãwa(96)}.

[al-Saafaat: 96].

Imani da ƙaddara - a bisa abinda muka siiffanta - ba ya kore cewa bawa ya kasance yana da abinda yake so a ayyukansa na zaɓi, da kuma iko a kansu, domin shari'a da abinda yake faruwa, masu nuni ne a bisa tabbatar da haka a gare shi.

Amma shari'a haƙiƙa Allah - Maɗaukakin sarki - Yace a kan Mashi'a (abin so}:

﴿...فَمَن شَآءَ ٱتَّخَذَ إِلَىٰ رَبِّهِۦ مَـَٔابًا

وقال: ﴿...فَأۡتُواْ حَرۡثَكُمۡ أَنَّىٰ شِئۡتُمۡ...﴾

وقال في القدرة: ﴿فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ مَا ٱسۡتَطَعۡتُمۡ وَٱسۡمَعُواْ وَأَطِيعُواْ...﴾

وقال: ﴿لَا يُكَلِّفُ ٱللَّهُ نَفۡسًا إِلَّا وُسۡعَهَاۚ لَهَا مَا كَسَبَتۡ وَعَلَيۡهَا مَا ٱكۡتَسَبَتۡ...﴾

{Wanda ya so ya riƙi makoma zuwa Ubangjnsa}.

[al-Naba'a: 39]

Kuma Ya ce: {Ku jewa gonarku (matayenku) ta yadda kuke so} [al- Baƙara: 223]

Kuma Ya ce game da Iko: {Ku ji tsoran Allah gwargwadan ikonku, ku ji kuma ku bi}.

[al-Tagabun:16]

Kuma Ya ce: {Allah ba Ya ɗorawa rai (wani nauyi) face abinda take da ikonsa, abinda ta tsururuta na alkhari na gare ta, abinda kuma ta tsururuta na sharri yana kanta}

[al Baƙara: 286].

Amma abinda yake faruwa: Haƙiƙa kowanne mutum yana sanin cewa yana da abinda yake so da kuma iko, da sune yake aiki, da sune kuma yake bari, yake kuma rarrabewa tsakanin abinda yake faruwa da nufinsa, kamar tafiya, da abinda yake faruwa ba tare da nufnsa ba, kamar makyarkyata, sai dai nufin bawa da ikonsa suna faruwa ne da abinda Allah - Maɗaukakin sarki - Ya so da kuma ikonSa, saboda faɗar Allah - Maɗaukakin sarki -:

﴿لِمَن شَآءَ مِنكُمۡ أَن يَسۡتَقِيمَ 28 وَمَا تَشَآءُونَ إِلَّآ أَن يَشَآءَ ٱللَّهُ رَبُّ ٱلۡعَٰلَمِينَ29﴾

{Duk wanda ya so daga cikinku to ya tsaya kan tafarki madaidaici, kuma ba komai kuke nufin aikatawa ba sai in Allah Ya so ku aikata ɗin Shi ne Ubangijin talikai}.

[al-Takweer: 28-29] Domin cewa wannan kasantacce dukkaninsa mallaki ne na Allah - Maɗaukakin sarki -, babu wani abu da zai kasance a cikin mulkinSa, ba tare da saninSa da ganin damarSa ba.

Imani da ƙaddara- a bisa abinda muka siffanta- ba ya baiwa bawa wata hujja a bisa barin (wani abu) daga wajibai, ko aikata (wani abu) daga saɓo, akan wannan ne, kafa hujja da shi ɓatacce ne, ta wasu fuskoki:

Na farko: {Waɗanda suka yi shirki su ce: " Allah so ba mu yi shirki ba, kuma ubanninmu ba su yi ba, kuma ba mu haramta wani abu ba." Kamar wannan ne mutãnen da suke a gabãninsu suka ƙaryata, har suka ɗanɗani azãbarMu. Ka ce: "Shin, kunã da wani ilmi a wurinku dõmin ku fito mana da shi? Bã ku bin kõme fãce zato kuma ba ku zama ba fãce ƙiri-faɗi kawai kuke yi}

[al-An'aam: 148] Da ace wata hujja ta kasance a gare su da ƙaddara to da Allah bai ɗanɗana musu azabarSa ba.

Na biyu: FaɗarSa - Allah Maɗaukakin sarki -: {Manzanni mãsu bãyar da bushãra kuma mãsu gargaɗi dõmin kada wata hujja ta kasance ga mutãne a kan Allah bãyan Manzannin.

Kuma Allah kasance Mabuwãyi, Mai hikima} [al-Nisaa:165] Da a ce ƙaddara ta kasance wata hujja ce ga masu saɓawa, da ba a koreta da aiko manzanni ba, domin saɓawa bayan aiko su mai afkuwa ce, da ƙudirar Allah - Maɗaukakin sarki-.

Na uku: Abinda Bukhari da Muslim suka ruwaito shi- lafazin na Bukhari ne- daga Aliyu ɗan Abu Ɗalib- Allah Ya yarda da shi- cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: " Babu ɗaya daga gare ku face an rubuta gurin zamansa a wuta ko a Aljanna". Sai wani mutum daga mutanan ya ce: Bama dogara (da abinda aka rubuta mana ba, mu bar aiki) ya Manzan Allah? ya ce: "Ku yi aiki kowannan ku abin yassarewa ne", sannan ya karanta: {Amma wanda ya bada (dukiyarsa akan tafarkin Allah) kuma ya ji tsoran Allah} [al - Lail:5] A cikin wani lafazin na Muslim: "Kowanne (ɗaya) abin yassarewa ne ga abinda aka halicce shi dan shi" sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi umarni da yin aiki, ya kuma yi hani a bisa dogaro akan ƙaddara,

Na huɗu: Haƙiƙa Allah - Maɗaukakin sarki - Ya umarci bawa kuma Ya hane shi, kuma bai ɗora masa nauyin (wani abu ba) sai abinda yake da iko, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce:

﴿فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ مَا ٱسۡتَطَعۡتُمۡ وَٱسۡمَعُواْ وَأَطِيعُواْ...﴾

وقال: ﴿لَا يُكَلِّفُ ٱللَّهُ نَفۡسًا إِلَّا وُسۡعَهَا...﴾

{Ku ji tsoran Allah gwargwadan ikonku ku ji, kuma ku yi biyayya}.

[al-Tagaabun:16]

{Allah ba Ya ɗorawa wata rai sai abin da zata iya} {al-Baƙara: 286] Da a ce bawa ya kasance abin tiilastawa abisa aiki, da ya zamo abin ɗorawa abinda ba shi da ikon kuɓuta daga gare shi, wannan kuwa ɓatacce ne, saboda haka ne ma idan ya aikata saɓo, da rashin sani, ko mantuwa, ko tilastawa, babu laifi a kansa, domin cewa shi abin yiwa hanzari ne.

Na biyar: Cewa ƙaddarar Allah - Maɗaukakin sarki - sirri ne ɓoyayye, ba a sanin shi sai bayan faruwar abin ƙaddarawar, kuma nufin bawa ga abinda yake aikatawa, mai rigaya ne a bisa aikinsa, saboda haka sai nufinsa aiki ya kasance bai ginu ba a bisa wani sani daga gare shi da ƙaddarar Allah, a wannan lokaci ne hujjarsa da ƙaddara take koruwa, domin babu wata hujja ga mutum cikin abinda ba shi da saninsa.

Na shida: Haƙiƙa cewa mu muna ganin mutum, yana kwaɗayi a bisa abinda yake dacewa da shi na daga al'amuran duniyarsa, har sai ya riske shi, ba ya bauɗewa ga barinsa zuwa abinda ba ya dacewa da shi, sannan ya kafa hujja a bauɗewarsa da ƙaddara, to, idan hakane, dan me yake bauɗewa daga abinda zai amfane shi a al'amuran Addininsa, zuwa abinda zai cutar da shi, sannan ya kafa hujja da ƙaddara? shin sha’anin al'amuran biyu bai zama ɗaya ba?

Ga wani misali nan a gareka da zai bayyanar da hakan;

Da hanyoyi biyu zasu kasance a gaban mutum: Ɗaya daga cikinsu za ta tiƙe da shi zuwa wani gari dukanninsa hayaniya ce da rashin tsari; kisa, da wawaso, da keta mutunci, da tsoro, da yunwa, (hanya). Ta biyu: Zai tiƙe da shi zuwa wani gari dukkaninsa tsari ne, da aminci tabbatacce, da rayuwa mai yalwa, da girmamawa ga rayuka da mutunci da dukiyoyi, to a hanyoyi biyunnan wacce zai bi ?

Haƙiƙa shi zai bi hanya ta biyu ne, wacce zata kai shi zuwa gari mai tsari da aminci, ba zai yi wu ba ga dukkan wani mai hankali har abada ya bi hanyar garin hayaniya da rashin tsari, da tsoro, ya kuma kafa hujja da ƙaddara, To, me ya sa yake bin hanyar wuta a al'amarin Lahira, ba hanyar aljanna ba, kuma ya kafa hujja da ƙaddara?

Wani misalin kuma: Zaka ga mara lafiya, ana umartarsa da magani, sai ya sha shi, alhalin ransa ba ya sha'awarsa, kuma a hana shi (cin) abinci wanda zai cutar da shi, sai ya bar shi, alhalin ransa yana sh'awarsa, dukkanin haka, dan neman waraka da aminci, ba zai yi wu ba ya hanu daga shan magani, ko ya ci abin ci wanda zai cutar da shi, kuma ya kafa hujja da ƙaddara, to, saboda me mutum yake barin abinda Allah da ManzanSa suka umarce shi da shi, ko ya aikata abinda Allah da ManzanSa suka hana shi, sannan kuma ya kafa hujja da ƙaddara?

Na bakwai: Cewa mai kafa hujja da ƙaddara a bisa abinda ya bar shi na daga wajibabbu, ko ya aikata shi na daga saɓo, da wani zai yi shisshigi a gare shi ya ɗauki dukiyarsa, ko ya keta alfarmarsa, sannan ya kafa hujja da ƙaddara, ya ce: Kada ka zarge ni haƙiƙa shisshigina ya kasance ne da ƙaddarar Allah- ba zai karɓi hujjarsa ba. To tayaya ba zai karɓi kafa hujja da ƙddara a shisshigin wani a kansa ba, kuma ya kafa hujja da ita ga kansa a shisshiginsa ga haƙƙin Allah - Maɗaukakin sarki -?!

Ana ambatan cewa sarkin muminai Umar bn Khaɗɗab an kawo wani ɓarawo zuwa gare shi, da ya cancanci yanke (hannu), sai ya yi umarni da a yanke hannunsa, sai ya ce: Ka saurara ya sarkin muminai, kaɗai na yi sata ne da ƙaddarawar Allah, sai Umar ya ce: Muma kuma kaɗai zamu yanke (hannunka) da ƙaddarawar Allah.

Imani da ƙaddara yana da fa'idoji masu girma, daga cikin su:

Ta farko: Dogaro ga Allah - Maɗaukakin sarki - yayin aikata sabubba, ta yadda ba zai dogara akan shikansa sababin ba, domin kowanne abu (yana kasancewa) da ƙudirar Allah - Maɗaukakin sarki -.

Ta biyu: Domin kada mutum ya yi jiji da kansa, lokacin da ya sami abin da yake so; domin saminsa wata ni'ima daga Allah - Maɗaukakin sarki - ne, da abinda Allah Ya ƙaddara shi daga sababin alkhairi da nasara, jiji da kansa kuwa zai mantar da shi godewa wannan ni'imar.

Ta biyu: Nutsuwa, da hutun rai da abinda yake gudana agare shi, daga ƙaddarorin Allah - Maɗaukakin sarki -, ba zai damu ba da rasa wani abin so, ko faruwar wani abin ƙi, domin hakan da ƙaddarawar Allah ne, wanda mulkin sammai da ƙasa ya tabbata a gare Shi, shi kasantacce ne babu makawa.

﴿مَآ أَصَابَ مِن مُّصِيبَةٖ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَلَا فِيٓ أَنفُسِكُمۡ إِلَّا فِي كِتَٰبٖ مِّن قَبۡلِ أَن نَّبۡرَأَهَآۚ إِنَّ ذَٰلِكَ عَلَى ٱللَّهِ يَسِيرٞ 22 لِّكَيۡلَا تَأۡسَوۡاْ عَلَىٰ مَا فَاتَكُمۡ وَلَا تَفۡرَحُواْ بِمَآ ءَاتَىٰكُمۡۗ وَٱللَّهُ لَا يُحِبُّ كُلَّ مُخۡتَالٖ فَخُورٍ 23﴾

{Wata musiba ba za ta faru ba a ƙasa ne ko a sama, face tana cikin Littafi (Allan ƙudira) kafin Mu halicce ta (samar da ita), haƙiƙa hakan mai sauƙi ne ga Allah(22) Domin kada ku yi baƙin ciki a bisa abinda ya tsere muku (kuɓuce muku) kada kuma ku yi farin ciki (na takama) da abinda ya baku, Allah ba Ya san dukkan mai taƙama mai yawan alfari(23)} [al- Hadid:22-23], kuma Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Lamarin mumini da ban mamaki yake, dukkannin al’amuransa alheri ne, kuma hakan ba ya kasancewa ga kowa sai ga mumini. Idan abin farin ciki ya same shi sai ya godewa Allah, sai ya zamar masa alheri, idan kuma na sharri ne ya same shi sai ya yi haƙuri, shi ma sai ya zamar masa alheri’’.

Haƙiƙa jama'a biyu sun ɓata (a sha'anin) ƙaddara:

Na farkonsu: Jabariyya waɗanda suka ce: Haƙiƙa bawa abin tilastawa ne akan aikinsa, ba shi da nufi ko iko.

Ta biyu: Alƙadariyya waɗanda suka ce: Haƙiƙa bawa mai cin gashin kansa ne da aikinsa, a nufi, da ƙudira (iko), babu wani gurbi ga abinda Allah - Maɗaukakin sarki - Yake so da kuma ikonSa a cikinsa (aikinsa).

Maida martani ga Jama'a ta farko (Aljabariyya) a shari'a da abinda ke faruwa:

Amma a shari'ah: Haƙiƙa Allah - Maɗaukakin sarki - Ya tabbatarwa bawa nufi da ganin dama, Ya kuma raɓa aiki zuwa gare shi, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce:

﴿...مِنكُم مَّن يُرِيدُ ٱلدُّنۡيَا وَمِنكُم مَّن يُرِيدُ ٱلۡأٓخِرَةَ...﴾وقال تعالى: ﴿وَقُلِ ٱلۡحَقُّ مِن رَّبِّكُمۡۖ فَمَن شَآءَ فَلۡيُؤۡمِن وَمَن شَآءَ فَلۡيَكۡفُرۡۚ إِنَّآ أَعۡتَدۡنَا لِلظَّٰلِمِينَ نَارًا أَحَاطَ بِهِمۡ سُرَادِقُهَا...﴾

وقال تعالى: ﴿مَّنۡ عَمِلَ صَٰلِحٗا فَلِنَفۡسِهِۦۖ وَمَنۡ أَسَآءَ فَعَلَيۡهَاۗ وَمَا رَبُّكَ بِظَلَّٰمٖ لِّلۡعَبِيدِ 46﴾

{Daga cikinku akwai wanda yake nufin duniya, kuma daga cikinku akwai wanda yake nufin lahira} [al- Imraana: 152],

kuma Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Kuma ka ce: Gaskiya daga Ubangijinku (take), wanda ya so ya yi imani wanda kuma ya so ya kafirce, haƙiƙa Mu mun tanadi wuta ga azzalimai, (wacce) shamakunta sun kewaye su} [al- Kahaf:29],

kuma Maɗaukakin sarki Ya ce: {Wanda ya aikata aiki na ƙwarai to sabõda kansa ne, kuma wanda ya mũnanã, to, yanã akansa. Kuma Ubangiwinka, Mai zãlunci ga bãyinSa ne ba(46)} [Fussilaat: 46].

Amma abinda ke faruwa: Haƙiƙa kowanne mutum ya san banbanci tsakanin ayyukansa na zaɓi waɗanda yake aikatasu da nufinsa: Kamar ci da sha, da siyarwa da siye, da kuma tsakanin abinda ke afkuwa agare shi, ba tare da nufinsa ba, kamar makyarkyata sanadiyyar zazzaɓi, da faɗowa daga rufi, shi ana farko mai aikatawa ne mai zaɓi da nufinsa, ba tare da tilasci ba, a na biyun kuma ba mai zaɓi ba ne, ko nufi ba, ga abinda ya afku a gare shi.

Maida martani akan Jama'a ta biyu (Alƙadariyya) a shari'a da hankali:

Amma a shari'a: Haƙiƙa Allah - Maɗaukakin sarki - Shi ne Mahaliccin komai, kowane abu mai kasancewa ne da abinda Yake so, kuma haƙiƙa Allah - Maɗaukakin sarki - Ya bayyana a littafinSa cewa: Ayyukan bayi suna faruwa ne da ganin damarSa, sai Allah Maɗaukakin sarki Ya ce:

﴿...وَلَوۡ شَآءَ ٱللَّهُ مَا ٱقۡتَتَلَ ٱلَّذِينَ مِنۢ بَعۡدِهِم مِّنۢ بَعۡدِ مَا جَآءَتۡهُمُ ٱلۡبَيِّنَٰتُ وَلَٰكِنِ ٱخۡتَلَفُواْ فَمِنۡهُم مَّنۡ ءَامَنَ وَمِنۡهُم مَّن كَفَرَۚ وَلَوۡ شَآءَ ٱللَّهُ مَا ٱقۡتَتَلُواْ وَلَٰكِنَّ ٱللَّهَ يَفۡعَلُ مَا يُرِيدُ﴾

وقال تعالى: ﴿وَلَوۡ شِئۡنَا لَأٓتَيۡنَا كُلَّ نَفۡسٍ هُدَىٰهَا وَلَٰكِنۡ حَقَّ ٱلۡقَوۡلُ مِنِّي لَأَمۡلَأَنَّ جَهَنَّمَ مِنَ ٱلۡجِنَّةِ وَٱلنَّاسِ أَجۡمَعِينَ 13﴾

{Da Allah Ya so da waɗanda suke daga bayansu, ba za su yi yaƙi ba, daga bayan hujjoji baiyanannu sun je musu. Kuma amma sun saɓawa juna, saboda haka daga cikinsu akwai wanda ya yi imani, kuma daga cikinsu akwai wanda ya kafirta. Kuma da Allah Ya ga dama da ba za su yaƙi juna ba, kuma Allah Yana aikata abinda Yake nufi} [al- Baƙara: 253],

Kuma Maɗaukakin sarki Ya ce:{Kuma Mun so Mun bai wa kõwane rai shiriyarsa to, amma magana ta tabbata daga gare Ni! Lalle ne Inã cika Jahannama daga aljannu da mutãne gabã ɗaya} [al-Sajada:13].

Amma a hankali: Haƙiƙa wannan kasantacce dukkaninsa mallakar Allah - Maɗaukakin sarki - ne, mutum kuma yana daga wannan kasantacce, shi mallakar Allah - Maɗaukakin sarki - ne, ba zai yi wu ba ga wanda aka mallaka ya yi tasarrafi a mulkin mamallaki, sai da izininsa da sonsa.

***

MANUFOFIN AKIDAR MUSULINCI

Alhadaf (a harshen larabci) ana faɗinsnsa da ma'anoni masu yawa, daga cikin su: (karan bara da ake kafawa dan koyon jifa zuwa gare shi, da kuma dukkan wani abu da ake son cimmasa).

Manufofin aƙidar Musulunci: Abubuwan nufinta da tuƙewar fa'idojinsu kyawawa, ababan tabbatarwa a bisa riƙo da su, su kuma masu yawa ne nau'i-nau'i, yana daga cikin su:

Na farko: Tsarkake niyya da ibada ga Allah - Maɗaukakin sarki - Shi kaɗai; domin cewa Shi ne Mahalicci, ba Shi da abokin tarayya, sai ya wajaba cewa niyyar ibada ta kasance a gare Shi, Shi kaɗai.

Na biyu: Tace hankali da tunani daga ruɗani mai faruwa daga wofantar zuciya daga wannan aƙidar, domin duk wanda zuciyar sa ta wofanta daga gare ta (aƙida} to, ko dai (ya zamo) zuciyar sa babu wata a ƙida (ingantacciya) a cikinta, kuma mai bautar ra’ayi na zahiri ne kawai, ko kuma mai faɗawa ne a cikin nau’ukan bata na aƙidu, da tatsuniyoyi.

Na uku: Hutu na rai, dana tunani, babu wata damuwa a rai, ba rarrawa a tunani, domin wannan aƙidar tana sadar da mumini da Ubangijinsa, sai ya yarda da shi a matsayin Ubangiji Mai tsarawa, Mai hukunci Mai shar'antawa, sai zuciyarsa ta natsu da ƙaddararsa, kuma ƙirjnsa ya yalwatu ga musulnci, ba ya neman wani abin da ba shi ba.

Na huɗu: Kuɓutar nufi (niyya) da aiki daga bauɗewa a bautar Allah - Maɗaukakin sarki -, ko ma'amalantar ababan halitta; domim yana daga ginshiƙanta, imani da manzanni, wanda ya ƙunshi bin hanyarsu ma'abociyar tsira a niyya da aiki.

Na biyar: Yankewa da ƙoƙari a cikin al'amura, ta yadda ba zai bar wata dama ba ta aiki nagari ba face sai ya yi amfani da ita a cikinsa, dan ƙaunar lada, kuma ba zai ga gurin saɓo ba, fa ce sai ya nisance shi, dan tsoran uƙuba, domin yana daga ginshiƙanta, imani da ta shi, da sakamako akan ayyuka.

Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Kuma kowanne yana da darajoji daga abinda suka aikata, Ubangijinka bai zamo Mai rafkana ba ga barin abinda suke aikatawa} [al-An'am:132]. Kuma haƙiƙa Annabi- tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya kwaɗaitar a kan wannan manufar a cikin faɗarsa: "Mumini ƙaƙƙarfa ya fi alkairi da soyuwa a wajen Allah sama da mumini rarrauna, akwai alkairi a kowanne, ka yi kwaɗayin yin abinda zai amfane ka, kuma ka nemi taimakon Allah, kada ka gaza, idan wani abu ya sameka kada ka ce: Dana aikata kaza da kaza da kaza ya kasance, saidai ka ce : Kaddarar Allah abinda Ya so zai aikata, domin cewa (da a ce) tana buɗe aikin Shaiɗan". Muslim ne ya rawaita shi.

Na shida: Samar da al'umma mai ƙarfi, da take bada dukkanin (abu) mai tsada da mai sauƙi, a wajen tabbatar da Addininta, da kafa ginshiƙansa, ba tare da la'akari da abinda zai sameta ba, akan tafarkin haka, akan wannan ne Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ke cewa:

﴿إِنَّمَا ٱلۡمُؤۡمِنُونَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ بِٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦ ثُمَّ لَمۡ يَرۡتَابُواْ وَجَٰهَدُواْ بِأَمۡوَٰلِهِمۡ وَأَنفُسِهِمۡ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِۚ أُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلصَّٰدِقُونَ 15﴾

{Mũminan gaskiya kawai, ne waɗanda suka yi ĩmãni da Allah da ManzonSa, sa'an nan ba su yi shakka ba, kuma suka yi jihãdi da dũkiyarsu da kuma rãyukansu, cikin tafarkin Allah. Waɗannan ne mãsu gaskiya(15)} [al- Hujrat: 15].

Na bakwai: Saduwa zuwa arzƙin duniya da lahira, da gyara ɗaidaiku da jama'a, da samun lada da abubuwan girma, akan wannan ne Allah - Maɗaukakin sarki - Yake cewa:

﴿مَنۡ عَمِلَ صَٰلِحٗا مِّن ذَكَرٍ أَوۡ أُنثَىٰ وَهُوَ مُؤۡمِنٞ فَلَنُحۡيِيَنَّهُۥ حَيَوٰةٗ طَيِّبَةٗۖ وَلَنَجۡزِيَنَّهُمۡ أَجۡرَهُم بِأَحۡسَنِ مَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ 97﴾

{Wanda ya aikata aiki na gari daga namiji ko mace, alhalin shi yana mumini, to lalle Zamu raya shi rayuwa mai daɗi, kuma lalle zaMu saka musu ladansu da mafi kyan abinda suka kasnce suna aikatawa(97)} [al-Nahl: 97].

Waɗannan sune sashin manufofin aƙidar Musulunci, muna ƙauna daga Allah - Maɗaukakin sarki - Ya tabbatar mana da su, da dukkanin musulmai, haƙiƙa Shi Mai yawan kyauta ne kuma Mai karamci ne, godiya ta tabbata ga Ubangijin talikai.

Allah Ya yi tsira da aminci ga Annabinmu, da Alayensa da sahabbansa baki ɗaya.

Ta cika da alƙalamin mawallafinta

Muhammad Bin Saleh al-Usaimeen

 

***

Teburin bayani

 

GABATARWA 2

ADDININ MUSULUNCI 4

RUKUNAN MUSULUNCI 9

GINSHIKAN AKIDAR MUSULUNCI 13

IMANI DA ALLAH - MAƊAUKAKIN SARKI -: 14

IMANI DA MALA'IKU 32

IMANI DA LITTATTAFAI 38

IMANI DA MANZANNI 41

IMANI DA RANAR LAHIRA 49

IMANI DA KADDARA 69

MANUFOFIN AKIDAR MUSULINCI 82

 

***