Ayoyin Al-Kur’anin da aka zaɓa
Lalle ne wannan Alƙur'ãni yanã shiryarwa ga (hãlayen) waɗanda suke mafi daidaita[1] kuma yanã bãyar da bushãra ga mũminai waɗanda suke aikata ayyuka na ƙwarai (cẽwa) "Lalle ne sunã da wata ijãra. mai girma."
Yã kũ mutãne![1] Lalle ne Mũ, Mun halitta ku daga namiji da mace, kuma Muka sanya ku dangõgi da kabĩlõli, dõmin ku san jũna. Lalle mafĩfĩcinku daraja a wurin Allah, (shĩ ne) wanda yake mafĩfĩcinku a taƙawa. Lalle nẽ Allah Masani ne, Mai ƙididdigẽwa.