PHPWord

 

 

 

حُكْمُ السِّحْرِ وَالكِهَانَةِ

وَمَا يَتَعَلَّقُ بِهَا

 

Hukuncin Sihiri da Bokanci da abinda yake da alaƙa da su

 

 

 

 

 

لِسَمَاحَةِ الشَّيْخِ العَلَّامَةِ

عَبْدِ العَزِيزِ بْنِ عَبْدِ اللهِ بْنِ بَازٍ

رَحِمَهُ اللهُ

 

Wallafar: Babban Malami

AbdulAzeez Bin Abdullahi Bin Baaz

Allah Yayi masa rahama

 

 

 


بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ

SAƘO NA TARA

Hukuncin sihiri da bokanci da abinda yake da alaƙa da su1

Godiya ta tabbata ga Allah Shi kaɗai, tsira da aminci su tabbata ga wanda babu wani Annabi a bayansa, bayan haka:

Duba da yawaitar ‘yan tsibbu a shekarun baya bayan nan waɗanda suke da'awar cewar suna bada magani, sunayin magani ta hanyar sihiri ko bokanci, da kuma yadda suka watsu a wasu garuruwan, da kuma yadda suke ribatar duhun kai na waɗanda jahilci ya rinjaye su, sai na ga yana daga babin nasiha ga Allah da bayinSa da in yi bayanin abinda hakan na daga da hatsari mai girma ga Musulinci da musulmai, saboda abinda yake cikin sa na dogaro ga wanin Allah - Maɗaukakin Sarki -da saɓawa umarninSa da umarnin ManzonSa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -.

Sai nake cewa, ina mai neman taimakon Allah - Maɗaukakin Sarki -: Neman magani ya halatta da ittifaƙin malamai. Saboda haka ya halatta musulmi ya je wurin likitan ciki ko tiyata ko jijiya ko makamantan haka domin ya duba shi ya kuma ba shi magani irin wanda ya dace da shi na magunguna da shari'ah ta halatta, gwargwadon iliminsa na likitancin; domin hakan yana ɓangaren riƙo da sabubba da aka saba, kuma baya kore tawakkali ga Allah. Haƙiƙa Allah - Mai tsarki da ɗaukaka - Ya saukar da cuta kuma ya saukar da magani a tare da ita; wanda ya sani ya sani, wanda kuma bai sani ba to bai sani ba. Sai dai Shi (Allah) - tsarki ta tabbatar maSa - Bai sanya warakar bayinSa ba cikin abinda Ya haramta musu .

Ba ya halatta ga mara lafiya ya tafi wurin bokaye waɗanda suke da'awar wai sun san abubuwan gaibu; domin ya san rashin lafiyar sa daga gare su, kamar yadda bai halatta ya gasgata su cikin abinda suke bashi labari da shi ba, domin su suna magana ne a fagauniyar gaibu, ko su kirawo aljanu domin su nemi taimakon su akan abinda suka nufata, waɗannan hukuncinsu shine kafirci da ɓata idan suka yi da'awar sanin gaibu,

Haƙiƙa Muslim ya ruwaito a Sahihinsa cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: (Duk wanda ya je wajan ɗan duba kuma ya tambaye shi game da wani abu, ba za’a karɓi sallarsa ta kwana arba’in ba)

(Duk wanda yaje wajen boka, sai ya gasgata shi cikin abinda yake cewa; to haƙiƙa ya kafirta da abinda aka saukarwa (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -) «Duk wanda yaje wajen boka, sai ya gasgata shi cikin abinda yake cewa; to haƙiƙa ya kafirta da abinda aka saukarwa (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -» Abu Dawud ne ya ruwaito shi, kuma ma'abota (littattafan) Sunan su huɗu sun fitar da shi, kuma Hakim ya inganta shi daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da lafazin: Duk wanda ya je wajen ɗan duba ko boka sai ya gasgata shi akan abinda yake cewa; to haƙiƙa ya kafirta da abinda aka saukarwa (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -.

Daga Imran ɗan Husain - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: (Baya tare da mu duk wanda ya yi camfi ko aka yi masa, ko yayi bokanci ko aka yi masa, ko yayi sihiri (asiri) ko aka yi masa; kuma duk wanda yaje wajen boka kuma ya gasgata shi akan abinda ya ke faɗa; to haƙiƙa ya kafircewa abinda aka saukarwa Annabi Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -) Bazzar ne ya ruwaito shi da isnadi mai kyau.

A cikin waɗannan hadisan masu daraja: akwai hani akan zuwa wurin ƴan duba da bokaye da matsafa da ire irensu, da tambayarsu da gasgata su, kuma a cikin su akwai narkon azaba akan hakan;

Don haka, ba ya halatta a ruɗu da gaskiyar su a wasu abubuwa, ko yawan jama'ar da suke zuwa zuwa wurinsu, domin jahilai ne ba ya halatta a ruɗu da su, domin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - tabbas ya hana zuwa wurin su da tambayar su da gaskata su, saboda abinda yake cikin hakan daga mummunan abu mai girma, da kuma hatsari babba da kuma mummunan ƙarshe, kuma domin cewa su maƙaryata ne fajirai,

Kamar yadda yake a cikin waɗannan hadisan: Akwai dalilai akan kafircin boka da matsafi; domin suna da'awar sanin gaibu; hakan kuma kafirci ne, da kuma cewa ba sa kaiwa inda suke so sai sun yi anfani da aljanu da kuma bauta musu koma bayan Allah; wannan kuwa kafircewa Allah ne kuma shirka ne da shi - tsarki ya tabbatar maSa -.

Wanda yake gasgata maganarsu ta sanin gaibu yana kasancewa irinsu ne, da duk wanda ya karɓi waɗannan al’amurra daga wanda yake ta’ammuli da su; to haƙiƙa Manzon Allah ya barranta da shi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -.

Kamar yadda bai halatta ga musulmi: Ya sallamawa abinda suke raya cewa magani ne ba, kamar surƙulle da ɗalasimai ko zuba harsashi, da makamancin haka na camfe-camfe da suke yi, domin hakan yana cikin bokanci da rikitar da mutane, to duk wanda ya yarda da hakan to haƙiƙa ya taimaka musu akan ɓarnar su da kuma kafircinsu.

Kamar yadda bai halatta ga kowanne musulmi ya je wurinsu ba; dan ya tambayesu wanda zai auri ɗan sa ko wani mukusancin sa, ko mai zai kasance tsakanin ma’auratan da iyalan su na daga so da aminci, ko ƙiyayya da rabuwa da makamantan haka; Domin wannan na daga gaibu wanda babu wanda ya san shi sai Allah - Mai tsarki da ɗaukaka -.

Abinda yake wajibi akan shugabanni da ‘yan Hisbah da sauran jama'a da suke da iko da mulki: Su hana zuwa wurin bokaye da ‘yan duba da makamantansu, su kuma hana wanda yake aikata wani abu na hakan a kasuwanni da sauransu, da yi musu inkarin hakan mafi tsananin inkarin, da kuma hana wanda yake zuwa wurinsu.

Haka nan sihiri: Domin shima yana cikin abubuwan da aka haramta na kafirc; kamar yadda Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya ce dangane da Mala’iku biyun nan:

﴿...وَمَا يُعَلِّمَانِ مِنۡ أَحَدٍ حَتَّىٰ يَقُولَآ إِنَّمَا نَحۡنُ فِتۡنَةٞ فَلَا تَكۡفُرۡۖ فَيَتَعَلَّمُونَ مِنۡهُمَا مَا يُفَرِّقُونَ بِهِۦ بَيۡنَ ٱلۡمَرۡءِ وَزَوۡجِهِۦۚ وَمَا هُم بِضَآرِّينَ بِهِۦ مِنۡ أَحَدٍ إِلَّا بِإِذۡنِ ٱللَّهِۚ وَيَتَعَلَّمُونَ مَا يَضُرُّهُمۡ وَلَا يَنفَعُهُمۡۚ وَلَقَدۡ عَلِمُواْ لَمَنِ ٱشۡتَرَىٰهُ مَا لَهُۥ فِي ٱلۡأٓخِرَةِ مِنۡ خَلَٰقٖۚ وَلَبِئۡسَ مَا شَرَوۡاْ بِهِۦٓ أَنفُسَهُمۡۚ لَوۡ كَانُواْ يَعۡلَمُونَ﴾

{Kuma ba su sanar da kõwa ba har sai sun ce: "Mũ fitina kawai ne, sabõda haka kada ka kãfirta," balle har su yi ta nẽman ilmin abin da suke rarrabẽwa tsakãnin mutum da mãtarsa da shi daga gare su. Kuma su (mãsu yin sihirin) ba su zama mãsu cũtar da kõwa da shi ba, fãce da iznin Allah. Kuma suna nẽman ilmin abin da yake cũtar da su, kuma bã ya amfaninsu. Kuma lalle ne, haƙiƙa, sun sani, tabbas, wanda ya saye shi, bã ya da wani rabo a cikin Lãhira. Kuma tir da abin da suka sayar da rãyukansu da shi, dã sun kasance suna sani}. [al-Baƙara: 102].

Sai waɗannan ayoyi masu daraja suka yi nuni akan sihiri kafirci ne kuma matsafa suna raba mutum da matarsa, kamar yadda ayar ta yi nuni akan asiri ba ya tasiri da kansa a anfanarwa ko cutarwa, kawai yana tasiri ne da izinin Allah na kaunu abin ƙaddarawa; domin Allah -Mai tsarki da ɗaukaka - Shi ne Wanda Ya halicci alheri da sharri.

Kamar yadda ayar mai daraja ta yi nuni akan waɗanda suke koyon sihiri, kaɗai suna koyon abinda yake cutar da su ne ba ya anfanar da su, kuma ba su da kowanne rabo a wurin Allah, (wato kowanne kaso ko nasibi), wannan kuwa narko ne na azaba mai girma da yake nuni akan tsananin asarar su a duniya da lahira, kuma su sun sayar da kawunansu da mafi ƙarancin farashi, saboda haka ne Allah - Mai tsarki da ɗaukaka - Ya aibata su da faɗinSa:

﴿...وَلَبِئۡسَ مَا شَرَوۡاْ بِهِۦٓ أَنفُسَهُمۡۚ لَوۡ كَانُواْ يَعۡلَمُونَ﴾

{Kuma tir da abin da suka sayar da rãyukansu da shi, dã sun kasance suna sani}, [al-Baƙara: 102]. 'Shira’u' anan ma’anarsa sayarwa.

Kuma haƙiƙa cutarwar ta girmama, kuma lamarin yayi tsanani ga waɗannan maƙaryatan, waɗanda suka gaji wannan ilimin daga mushirikai, suka rikitar da masu raunin hankula, da su, to lalle mu ga Allah muke, kuma mu zuwa gare Shi muke komawa, Allah Ya isar mana kuma madalla da Shi abin wakiltawa.

Muna rokon Allah lafiya da aminci daga sharrin matsafa da bokaye da sauran masu surƙulle, kuma muna rokon Shi - tsarki ya tabbatar maSa - Ya tsare musulmai daga sharrin su, kuma Ya datar da shugabannin musulmai da tsawatarwa daga gare su, da zartar da hukuncin Allah a kansu har bayi su huta daga cutarwar su da munanan ayyukan su, lalle Shi Mai yawan kyauta ne kuma Mai karamci.

Kuma lallai Allah - tsarki ya tabbatar maSa - Ya shar’antawa bayinSa abinda za su kare kansu da shi daga sharrin sihiri kafin afkuwar sa, kuma Ya yi musu bayanin abinda za su yi magani da shi bayan afkuwar sa, wannan rahamar Sa ce gare su, da kuma kyautatawar Sa gare su, da kuma cika ni’imar Sa a gare su.

Ga bayanin waɗansu abubuwa da mutum zai kaucewa haɗarin asiri kafin afkuwar sa, da kuma abubuwan da za’a yi magani da su bayan afkuwar sa na halastattun abubuwa a shari'ah, ga bayanin nan kamar haka:

Na farko: Abinda za’a kaucewa haɗarin asiri kafin faruwarsa: Mafi muhimmanci kuma wanda ya fi amfani shi ne: Kariya ta hanyar yin zikirai shar’antattu, da addu’o’i da kuma abubuwan neman tsari da aka ruwaito, daga cikin haka: Karatun Ayatul Kursiyy, - ita ce aya mafi girma a cikin Alƙur’ani mai girma -, bayan sallamewa daga kowacce sallah ta farilla, ita ce faɗinSa - tsarki ya tabbatar maSa:

﴿ٱللَّهُ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ ٱلۡحَيُّ ٱلۡقَيُّومُۚ لَا تَأۡخُذُهُۥ سِنَةٞ وَلَا نَوۡمٞۚ لَّهُۥ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِۗ مَن ذَا ٱلَّذِي يَشۡفَعُ عِندَهُۥٓ إِلَّا بِإِذۡنِهِۦۚ يَعۡلَمُ مَا بَيۡنَ أَيۡدِيهِمۡ وَمَا خَلۡفَهُمۡۖ وَلَا يُحِيطُونَ بِشَيۡءٖ مِّنۡ عِلۡمِهِۦٓ إِلَّا بِمَا شَآءَۚ وَسِعَ كُرۡسِيُّهُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَۖ وَلَا يَـُٔودُهُۥ حِفۡظُهُمَاۚ وَهُوَ ٱلۡعَلِيُّ ٱلۡعَظِيمُ255﴾

{Allah, bãbu wani Ubangiji fãce Shi, Rãyayye, Mai tsayuwa da kõme, gyangyaɗi bã ya kãma Shi, kuma barci bã ya kãma Shi, Shi ne da abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasa. Wanene wanda yake yin cẽto a wurinSa, fãce da izninSa? Yana sanin abin da yake a gaba gare su da abin da yake a bãyansu. Kuma bã su kẽwayẽwa da kõme daga ilminSa, fãce da abin da Ya so. KursiyyunSa ya yalwaci sammai da ƙasa. Kuma tsare su bã ya nauyayarSa. Kuma Shi ne Maɗaukaki, Mai girma}. [al-Baƙara: 255], Da kuma karanta ta dai a lokacin barci, haƙiƙa ya inganta daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: (Wanda ya Karanta Ayatul Kursiyy da daddare, to mai kiyayewa daga Allah ba zai gushe ba a gare shi, kuma shaiɗani ba zai zo kusa da shi ba har ya wayi gari).

Akwai daga cikin hakan karanta:

﴿قُلۡ هُوَ ٱللَّهُ أَحَدٌ1﴾

{Ka ce: "Shi ne Allah Makaɗaĩci."},

﴿قُلۡ أَعُوذُ بِرَبِّ ٱلۡفَلَقِ1﴾

{"Ka ce "ina neman tsari ga Ubangijin safiya"},

﴿قُلۡ أَعُوذُ بِرَبِّ ٱلنَّاسِ1﴾

{"Ka ce "Ina nẽman tsari ga Ubangijin mutãne."}, [al-Nas: 1]. A bayan kowacce sallah ta farilla. Da kuma karatun waɗannan surorin uku, sau uku da a farkon rana bayan sallar asuba, da kuma farkon dare bayan sallar magariba.

Yana daga cikin hakan: Karanta ayoyi biyu na ƙarshen suratul Baƙarah a farkon dare, su ne faɗinSa - Maɗaukakin Sarki -:

﴿ءَامَنَ ٱلرَّسُولُ بِمَآ أُنزِلَ إِلَيۡهِ مِن رَّبِّهِۦ وَٱلۡمُؤۡمِنُونَۚ كُلٌّ ءَامَنَ بِٱللَّهِ وَمَلَٰٓئِكَتِهِۦ وَكُتُبِهِۦ وَرُسُلِهِۦ لَا نُفَرِّقُ بَيۡنَ أَحَدٖ مِّن رُّسُلِهِۦۚ وَقَالُواْ سَمِعۡنَا وَأَطَعۡنَاۖ غُفۡرَانَكَ رَبَّنَا وَإِلَيۡكَ ٱلۡمَصِيرُ285﴾

[Manzon Allah yã yi ĩmãni da abin da aka saukar zuwa gare shi daga Ubangijinsa, da mũminai. Kõwanensu yã yi ĩmãni da Allah, da mala'ikunSa, da littattafanSa, da manzanninSa. Bã mu rarrabẽwa a tsakãnin daya daga manzanninSa. Kuma (mũminai) suka ce: "Mun ji kuma mun yi dã'a; (Muna nẽman) gãfararKa, yã Ubangijinmu, kuma zuwa a gare Ka makõma take." Har zuwa ƙarshen surar.

Saboda abinda ya inganta daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - cewa shi ya ce: (Wanda ya karanta ayoyi biyu na ƙarshen Suratul Baƙara da daddare sun ishe shi), Abin nufi, Allah ne Masani: Sun ishe shi daga dukkan mummunan abu. Yana daga cikin hakan yawaita neman tsari da (Kalmomin Allah cikakku daga sharrin Abinda Ya halitta), a dare da rana, da lokacin sauka a kowanne irin masauki, a gini ne ko a sahara, ko a sararin samaniya ne ko a teku, saboda faɗin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: (Duk wanda ya sauka a wani masauki sai ya ce: Ina neman tsari da kalmomin Allah cikakku daga sharrin abinda Ya halitta, babu abunda zai cuce shi har sai ya tashi daga wannan masaukin).

Yana daga cikin wannan: Shine Musulmi ya ce a farkon rana (da safe) da kuma farkon dare (da daddare) ya faɗa sau uku: (Da sunan Allah, wanda da sunanSa wani abu a sama ko a ƙasa bazai cutu ba, Shi ne Mai ji kuma Masani)

Saboda ingancin kwaɗaitarwa akan hakan, daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, kuma hakan dalili ne na samun kuɓuta daga dukkan mummunan abu.

Na biyu: Abinda za’a magance sihiri da shi bayan afkuwar sa, to wannan shi ma yana kasancewa ne da abubuwa kamar haka:

Na daya: Yawaita ƙanƙan dakai ga Allah, da kuma roƙonSa - tsarki ya tabbatar maSa - da Ya yaye cutar Ya kuma kawar da tsananin.

Na biyu: Yin kokari wurin sanin inda aka sanya asirin a ƙasa ne ko dutse ko wani wuri, idan aka sani sai a fito da shi sai a warware shi, to an lalata sihirin, wannan kuwa yana cikin mafi anfanin maganin sihiri,

Na uku: Yin ruƙyah da zikirai da wuridai shar’antattu, kuma suna da yawa; daga ciki:

Abinda ya tabbata a maganar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: (Ya Allah, Ubangijin mutane Ka tafiyar da tsananin, Ka warkar, Kai ne Mai warkarwa, babu waraka sai warakarKa, warakar da ba ta barin wata larura) Zai faɗa sau uku,

Akwai daga cikin hakan: (Addu’ar) ruƙya wacce Mala’ika Jibirilu ya yi wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ruƙya da ita. Itace faɗin sa: (Da sunan Allah nake maka ruƙya, daga dukkan wani abu da zai cutar da kai, daga sharrin kowane irin rai ko idon mai hassada, Allah Ya warkar da kai, da sunan Allah nake maka ruƙya) Ya kuma maimaita hakan sau uku.

Yana daga cikin hakan - Kuma wannan magani ne mai anfani ga mutum wanda aka hana masa kusantar iyalin sa -: ya sami ganyen magarya koraye guda bakwai, sai ya dandaƙa su da dutse ko makamancin sa sai ya zuba a cikin ƙwarya sai kuma ya zuba ruwa akan sa wanda zai ishe shi yin wanka, sai ya karanta a ciki:

Ayatul-kursiyyi

﴿قُلۡ يَٰٓأَيُّهَا ٱلۡكَٰفِرُونَ1﴾

{Ka ce: "Ya kũ kãfirai!"}, [al-Kafirun: 1], da kuma

﴿قُلۡ هُوَ ٱللَّهُ أَحَدٌ1﴾

{Ka ce: "Shi ne Allah Makaɗaĩci."}, [al-Ikhlas: 1], da kuma

﴿قُلۡ أَعُوذُ بِرَبِّ ٱلۡفَلَقِ1﴾

{"Ka ce "ina neman tsari ga Ubangijin safiya"}, [al-Falaƙ: 1], da

﴿قُلۡ أَعُوذُ بِرَبِّ ٱلنَّاسِ1﴾

{"Ka ce "Ina nẽman tsari ga Ubangijin mutãne."}, [al-Nas: 1].

Da ayoyi da suke maganar sihiri a Suratul A’araf, su ne faɗinSa -tsarki ya tabbatar maSa -:

﴿وَأَوۡحَيۡنَآ إِلَىٰ مُوسَىٰٓ أَنۡ أَلۡقِ عَصَاكَۖ فَإِذَا هِيَ تَلۡقَفُ مَا يَأۡفِكُونَ117 فَوَقَعَ ٱلۡحَقُّ وَبَطَلَ مَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ118 فَغُلِبُواْ هُنَالِكَ وَٱنقَلَبُواْ صَٰغِرِينَ119﴾

{Kuma Muka yi wahayi zuwa ga Mũsã cẽwa: "Ka jẽfa sandarka." Sai gã ta tanã lãƙumar abin da suke ƙarya da shi!.Gaskiya ta auku, kuma abin da suke aikatãwa ya ɓãci.Sai aka rinjãye su a can, kuma suka jũya sunã ƙasƙantattu.},

Gaskiya ta auku, kuma abin da suke aikatãwa ya ɓãci.

Sai aka rinjãye su a can, kuma suka jũya sunã ƙasƙantattu. [al-A'araf: 117-119].

Da kuma ayoyi a Suratu Yunus, su ne faɗinSa - tsarki ya tabbatar maSa -:

﴿وَقَالَ فِرۡعَوۡنُ ٱئۡتُونِي بِكُلِّ سَٰحِرٍ عَلِيمٖ79 فَلَمَّا جَآءَ ٱلسَّحَرَةُ قَالَ لَهُم مُّوسَىٰٓ أَلۡقُواْ مَآ أَنتُم مُّلۡقُونَ80 فَلَمَّآ أَلۡقَوۡاْ قَالَ مُوسَىٰ مَا جِئۡتُم بِهِ ٱلسِّحۡرُۖ إِنَّ ٱللَّهَ سَيُبۡطِلُهُۥٓ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يُصۡلِحُ عَمَلَ ٱلۡمُفۡسِدِينَ81 وَيُحِقُّ ٱللَّهُ ٱلۡحَقَّ بِكَلِمَٰتِهِۦ وَلَوۡ كَرِهَ ٱلۡمُجۡرِمُونَ82﴾

{Kuma Fir'auna ya ce: "Ku zo mini da dukan masihirci, masani."To, a lõkacin da masihirta suka je, Mũsã ya ce musu,"Ku jẽfa abin da kuke jẽfãwa."To, a lõkacin da suka jẽfa, Mũsa ya ce: "Abin da kuka zo da shi sihiri ne. Lalle ne Allah zai ɓãta shi. Haƙĩƙa Allah bã Ya gyãra aikin maɓarnata."Kuma Allah Yanã tabbatar da gaskiya da kalmõmin Sa, kõ dã mãsu laifi sun ƙi."},

To, a lõkacin da masihirta suka je, Mũsã ya ce musu,"Ku jẽfa abin da kuke jẽfãwa."80

To, a lõkacin da suka jẽfa, Mũsa ya ce: 'Abin da kuka zo da shi sihiri ne. Lalle ne Allah zai ɓãta shi. Haƙĩƙa Allah bã Ya gyãra aikin maɓarnata.'

Kuma Allah Yanã tabbatar da gaskiya da kalmõmin Sa, kõ dã mãsu laifi sun ƙi. [Yunus: 79-82].

Da kuma ayoyi da suke cikin Suratu Ɗaha:

﴿قَالُواْ يَٰمُوسَىٰٓ إِمَّآ أَن تُلۡقِيَ وَإِمَّآ أَن نَّكُونَ أَوَّلَ مَنۡ أَلۡقَىٰ65 قَالَ بَلۡ أَلۡقُواْۖ فَإِذَا حِبَالُهُمۡ وَعِصِيُّهُمۡ يُخَيَّلُ إِلَيۡهِ مِن سِحۡرِهِمۡ أَنَّهَا تَسۡعَىٰ66 فَأَوۡجَسَ فِي نَفۡسِهِۦ خِيفَةٗ مُّوسَىٰ67 قُلۡنَا لَا تَخَفۡ إِنَّكَ أَنتَ ٱلۡأَعۡلَىٰ68 وَأَلۡقِ مَا فِي يَمِينِكَ تَلۡقَفۡ مَا صَنَعُوٓاْۖ إِنَّمَا صَنَعُواْ كَيۡدُ سَٰحِرٖۖ وَلَا يُفۡلِحُ ٱلسَّاحِرُ حَيۡثُ أَتَىٰ69﴾

{Suka ce: "Ya Mũsã! Imma ka jefa, ko kuma mu kasance farkon mai jẽfawa."Ya ce: "Ã'a, ku jẽfa." Sai gã igiyoyinsu da sandunansu anã sũranta su a gare shi, daga sihirinsu, lalle sunã tafiya da sauri.Sai Mũsã ya ji tsõro a cikin ransa.Muka ce: "Kada ka ji tsõro. lalle kai ne mafi ɗaukaka.""Kuma ka jẽfa abin da ke a cikin hannun dãmanka, ta cafe abin da suka aikata. Lalle ne abin da suka aikata mãkircin masihirci ne kuma masihirci bã ya cin nasara a duk inda ya je."}.

Ya ce: "Ã'a, ku jẽfa." Sai gã igiyoyinsu da sandunansu anã sũranta su a gare shi, daga sihirinsu, lalle sunã tafiya da sauri.

Sai Mũsã ya ji tsõro a cikin ransa.

Muka ce: "Kada ka ji tsõro. lalle kai ne mafi ɗaukaka.

Kuma ka jẽfa abin da ke a cikin hannun dãmanka, ta cafe abin da suka aikata. Lalle ne abin da suka aikata mãkircin masihirci ne kuma masihirci bã ya cin nasara a duk inda ya je. [Daha: 65-69].

Bayan karanta abinda aka ambata a cikin ruwa, sai a sha kanfata uku , sai a wanke jiki da sauran, da wannan cutar za ta gushe da yardar Allah. Idan kuma an buƙaci a sake yi ya zama na biyu ko sama da haka to babu wani laifi, har dai cutar ta kau.

Waɗannan zikiran da addu’o’in neman tsari da kuma hanyoyin suna daga cikin mafi girman sabubba na kaucewa sharrin sihiri da wanin sa na nau’ukan sharri, kuma shi ne mafi girman makami na kawar da sihiri bayan ya afku; ga duk wanda ya kiyaye akan hakan da gaskiya da kuma imani da amincewa da Allah da dogaro da Shi, da kuma samun yalwar ƙirji na abinda suka yi nuni akan sa.

Wannan shi ne abinda bayanin sa ya sawwaƙa na abubuwan da ake kaucewa sihiri da su, kuma ake maganin sa da su, Allah Shine Mai datarwa.

Anan ne kuma za’a zo da wata mas’ala mai muhimmanci, wato magance sihiri ta hanyar matsafa, wanda yake cika ta hanyar kusanta ga aljanu ta hanyar yi musu yanka ko makamantan hakan na abubuwan kusanci; to wannan bai halatta ba; domin yana cikin aikin shaiɗan; kai yana ma cikin babbar shirka; Kamar yadda baya halatta a yi magani ba ta hanyar tambayar bokaye da masu duba da ‘yan tsibbu ba, da kuma aiki da abinda suke faɗa; domin ba sa yin imani, kuma su maƙaryata ne fajirai, suna da'awar sanin gaibu, suna ruɗar da mutane, kuma haƙiƙa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya tsoratar daga zuwa wurin su da tambayar su da kuma gasgata su, kamar yadda bayani ya gabata akan hakan a farkon wannan saƙon. Abinda yake wajibi kiyaye wa akan haka, domin ya inganta daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, an tambaye shi dangane al-Nushrah' sai ya ce: (Ita yana cikin aikin shaiɗan) Ahmad ne ya ruwaito shi da Abu Dawud da isnadi mai kyau.

Al-Nushrah: Ita ce warware sihiri daga wanda aka yi wa sihirin. Abinda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yake nufi a wannan maganar ta shi shine: al-Nushrah wacce mutanan Jahilyyah suke yi, itace: Neman matsafi da ya warware sihiri ko ya warware shi da wani sihirin irinsa daga wani mai sihirin daban.

To Amma warware shi ta hanyar ruƙyah da addu’o’in neman tsari da aka shar’anta da magunguna na halas to babu laifi akan hakan, kamar yadda ya gabata. Haƙiƙa babban malami Ibn al- Ƙayyim ya nassanta hakan, da Shaikh Abdurrahman ɗan Hassan a Fathul Majid - Allah Yayi musu rahama su biyun - , kuma da yawa wasu daban daga cikin ma'abota ilimi sun nassanta hakan.

Allah muke roƙo Ya datar da musulmai ga yayewa daga dukkan abin ƙi, Ya kuma tsare musu Addinin su, Ya azurta su fahimata a cikin sa, Ya kuma kare su daga dukkan abinda ya sabawa shari’ar Sa.

Tsira da amincin Allah su tabbata ga bawanSa kuma ManzonSa (Annabi) Muhammad da alayen sa da sahabban sa.

 

***