PHPWord

 

 

 

التَّحْذِيرُ مِنَ البِدَعِ

 

Tsawatarwa daga Bidi''o'i

 

 

 

 

 

 

لِسَمَاحَةِ الشَّيْخِ العَلَّامَةِ

عَبْدِ العَزِيزِ بْنِ عَبْدِ اللهِ بْنِ بَازٍ

رَحِمَهُ اللهُ

 

Wallafar: Babban Malami

AbdulAzeez Bin Abdullahi Bin Baaz

Allah Yayi masa rahama

 

 

 


بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ

SAƘO NA BIYAR:

Hukuncin taron maulidin Annabi da sauran mauludai

Godiya ta tabbata ga Allah, tsira da amincin Allah su tabbata ga Manzon Allah, da alayen sa da sahabban sa da waɗanda suka shiryu da shiriyar sa.

Bayan haka: An sha tambayar mutane da dama game da hukuncin taron bikin haihuwar Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi-, da tsayuwa saboda shi a lokacin yin hakan, da yi masa sallama, da sauran abubuwan da ake yi a maulidi.

Amsa sai a ce: Ba ya halatta yin bikin mauludin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, haka ma na wanin sa; domin hakan bidi’a ne wacce aka ƙirƙira a cikin addini; domin Manzo - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - bai yi ba, haka halifofin sa shiryayyu, haka sauran sahabbai - Allah Ya yarda da su -, haka waɗanda suka bi su da kyautatawa a mafifitan ƙarni, alhali su suka fi kowa sanin sunnah, su suka fi cikar son Ma’aikin Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, kuma suka fi bin shari’ar sa akan waɗanda suka zo a bayan su, Kuma haƙiƙa Allah - Mai tsarki da ɗaukaka - Ya faɗa a cikin littafin Sa mabayyani:

﴿...وَمَآ ءَاتَىٰكُمُ ٱلرَّسُولُ فَخُذُوهُ وَمَا نَهَىٰكُمۡ عَنۡهُ فَٱنتَهُواْ...﴾

{Abinda manzo ya zo muku (da shi) to ku riƙe shi abinda kuma ya haneku to ku hanu}

[al-Hashr: 7]. Kuma Allah - Maɗaukaki - Ya ce:

﴿...فَلۡيَحۡذَرِ ٱلَّذِينَ يُخَالِفُونَ عَنۡ أَمۡرِهِۦٓ أَن تُصِيبَهُمۡ فِتۡنَةٌ أَوۡ يُصِيبَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٌ﴾

{To waɗanda suke saɓa umarninsa su kiyayi kansu kada musiba ko fitina ta sauka a kansu ko kuma azaba mai raɗaɗi ta same su} [al-Nnur: 63], Kuma - tsarki ya tabbatar maSa - Ya ce:

﴿لَّقَدۡ كَانَ لَكُمۡ فِي رَسُولِ ٱللَّهِ أُسۡوَةٌ حَسَنَةٞ لِّمَن كَانَ يَرۡجُواْ ٱللَّهَ وَٱلۡيَوۡمَ ٱلۡأٓخِرَ وَذَكَرَ ٱللَّهَ كَثِيرٗا21﴾

{Lalle, abin kõyi mai kyau ya kasance gare ku daga Manzon Allah, ga wanda ya kasanee yanã fãtan rahamar Allah da Rãnar Lãhira, kuma ya ambaci Allah da yawa} [al-Ahzab: 21], Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿وَٱلسَّٰبِقُونَ ٱلۡأَوَّلُونَ مِنَ ٱلۡمُهَٰجِرِينَ وَٱلۡأَنصَارِ وَٱلَّذِينَ ٱتَّبَعُوهُم بِإِحۡسَٰنٖ رَّضِيَ ٱللَّهُ عَنۡهُمۡ وَرَضُواْ عَنۡهُ وَأَعَدَّ لَهُمۡ جَنَّٰتٖ تَجۡرِي تَحۡتَهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَآ أَبَدٗاۚ ذَٰلِكَ ٱلۡفَوۡزُ ٱلۡعَظِيمُ100﴾

{Kuma mãsu tsẽrẽwa na farko daga Muhãjirina da Ansar da waɗanda suka bi su da kyautatãwa, Allah Ya yarda daga gare su su kuma sun yarda daga gare Shi, kuma Ya yi mãsu tattalin gidãjen Aljanna; ƙõramu sunã gudãna a ƙarƙashinsu, suna madawwamã a cikinsu har abada. Wancan ne babban rabo mai girma} [al-Taubah: 100], Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿...ٱلۡيَوۡمَ أَكۡمَلۡتُ لَكُمۡ دِينَكُمۡ وَأَتۡمَمۡتُ عَلَيۡكُمۡ نِعۡمَتِي وَرَضِيتُ لَكُمُ ٱلۡإِسۡلَٰمَ دِينٗا...﴾

{Kuma yaune Na cika muku addininku, kuma Na cika muku ni'imaTa kuma Na yarje muku musulunci a matsayin addini} [al-Ma'ida: 3]. Kuma ayoyi da suka zo da wannan ma’anar suna da yawa. Kuma haƙiƙa ya tabbata daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Duk wanda ya farar da wani abu a cikin wannan Addinin namu wanda ba ya ciki, to shi abun mayarwa ne». Wato: Za’a mayar masa, Kuma ya faɗa a wani hadisin daban: «Na hore ku da bin sunnata da sunnar halifofi shiryayyu masu shiryarwa a baya na, ku yi riƙo da ita, kuma ku riƙeta da fiƙoƙinku, kuma na hane ku da fararrun abubuwa; saboda kowane fararren abu bidi'a ne; kuma kowace bidi'a ɓata ce». To a cikin waɗannan hadisai biyu, akwai tsawatarwa mai tsanani akan farar da bidi’a, da kuma aiki da ita.

Kuma farar da ire-iren waɗannan mauludan, ana fahimta daga gare shi cewa, Allah - tsarki ya tabbata a gare Shi - bai cika wa wannan al’ummar Addini ba, kuma Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - bai isarwa al’umma abinda ya kamata ta aikata ba, har sai da waɗannan ’yan baya bayan suka zo, sai suka ƙirƙira a shari'ar Allah abinda bai bada izini ba; suna masu riya cewa hakan yana cikin abinda zai kusantar da su ga Allah. Kuma wannan babu shakka yana da babban haɗari, kuma ƙalubalantar Allah ne - tsarki ya tabbatar maSa - da ManzonSa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, kuma Allah - tsarki ya tabbatar maSa - Ya cika addini ga bayinSa, kuma Ya cika ni’imarSa a gare su, kuma Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya isar da isarwa bayyananniya, bai bar wata hanya da zata kai zuwa Aljanna, kuma ta nisantar daga wuta ba face ya bayyana ta ga al’umma, kamar yadda aka tabbatar a cikin hadisi sahihi daga Abdullahi ɗan Amru - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Allah bai aiko wani Annabi ba sai ya zama wajibi a gare shi ya nuna wa al'ummarsa mafi alherin abinda ya sani a gare su, kuma ya gargaɗe su daga mafi sharrin abinda ya sani a gare su». Muslim ne ya rawaito shi a cikin Sahih ɗin sa.

Sanannen abu ne, lalle Annabimmu - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, shi ne mafificin Annabawa kuma cika makinsu, kuma mafi cikarsu a isarwa da nasiha. Da bikin maulidai yana cikin Addinin da Allah tsarki ya tabbata a gare Shi - Ya yarda da shi da ManzonSa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya bayyana shi ga al’umma ko ya aikata shi a rayuwarsa ko sahabbansa sun aikata shi a bayansa, - Allah Ya yarda da su -.To a yayin da babu abinda ya faru cikin waɗannan, sai aka sani cewa shi ba ya cikin Musulinci ta ko’ina, bari dai, yana cikin fararrun abubuwan da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya tsawatar da al’ummarsa a kansu, kamar yadda ambaton hakan ya gabata a cikin hadisai. Ayoyi da hadisai a wannan babin suna da yawa.

Kuma haƙiƙa jama’a masu yawa cikin malamai sun bayyana inkarinsu ga maulidai da kuma tsawatarwa akan su; domin yin aiki da dalilan da aka ambata da wasunsu. Sai wasu cikin ‘yan baya bayan nan suka saɓa (akan hakan): Sai suka halasta shi idan bai ƙunshi abubuwan ƙi ba; kamar wuce iyaka a (sha'anin) Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, kamar kuma haɗuwar mata da maza, da amfani da kayan kiɗa, da wasunsu, na abinda shari’a tsarkakakkiya ba ta yarda da shi ba, suka yi zaton hakan yana cikin bidi’a kyakkyawa.

Ka'idar shari'a ita ce: Mayar da abinda mutane suka yi saɓani a kai zuwa ga Littafin Allah da sunnar ManzonSa annabi Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - kamar yadda Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya ce:

﴿يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ أَطِيعُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُواْ ٱلرَّسُولَ وَأُوْلِي ٱلۡأَمۡرِ مِنكُمۡۖ فَإِن تَنَٰزَعۡتُمۡ فِي شَيۡءٖ فَرُدُّوهُ إِلَى ٱللَّهِ وَٱلرَّسُولِ إِن كُنتُمۡ تُؤۡمِنُونَ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِۚ ذَٰلِكَ خَيۡرٞ وَأَحۡسَنُ تَأۡوِيلًا59﴾

{Yã kũ waɗanda suka yiĩmãni! Ku yi ɗã'a ga Allah, kuma ku yi ɗã'a ga ManzonSa, da ma'abũta al'amari daga cikinku. Idan kun yi jãyayya a cikin wani abu, to ku mayar da shi zuwa ga Allah da ManzonSa idan kun kasance kunã ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira. wannan ne mafi alhẽri, kuma mafi kyau ga fassara} [al-Nisa'a: 59], Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿وَمَا ٱخۡتَلَفۡتُمۡ فِيهِ مِن شَيۡءٖ فَحُكۡمُهُۥٓ إِلَى ٱللَّهِ ...﴾

{Kuma abin da kuka yi saɓani a cikinsa na daga wani abu to hukuncinsa zuwa ga Allah yake} [al-Shura: 10].

Haƙiƙa mun maida wannan mas’alar: Shi ne: (Hujjar) bikin maulidai zuwa littafin Allah - tsarki ya tabbata a gare Shi - , sai muka samu yana umartarmu da bin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a abinda ya zo da shi, yana kuma hanamu aikata abinda ya hana, yana kuma ba mu labarin cewa Allah - tsarki ya tabbata a gare Shi - haƙiƙa Ya cikawa wannan al’umma Addininta, wannan bikin kuma ba ya cikin abinda Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya zo da shi, sai ya zama ba ya cikin Addinin da Allah Ya cika mana, kuma Ya umarce mu da bin Manzo a cikinsa.

Haƙiƙa mun maida wannan - shima -: Zuwa ga Sunnar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -; ba mu samu ya aikata shi ba a cikinta, kuma bai yi umarni da shi ba, kuma sahabbansa ba su aikata shi ba - Allah Ya yarda da su-; sai muka sani da hakan cewa hakan ba ya cikin Addini, bari dai, yana cikin bidi’a ƙagaggiya, kuma yana cikin koyi da ma’abota littafi Yahudu da Nasara a bukukuwansu.

Da wannan ne zai bayyana ga dukkan wanda yake da mafi ƙarancin basira da kwaɗayin gaskiya da kuwala wurin nemanta: Lalle taron mauludai ba ya cikin Addinin Musulinci, bari dai yana cikin bidi’o’i da aka ƙago, waɗanda Allah - tsarki ya tabbata a gare Shi - da ManzonSa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - suka yi umarni da barinsu, suka kuma tsawatar daga garesu. Kuma ba ya kamata ga mai hankali ya ruɗu da yawan masu aikata shi cikin mutane a sassan duniya, domin ita gaskiya ba’a saninta da yawan masu yinta, kaɗai ana sanin gaskiya ne da dalilai na shari’a, kamar yadda Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya faɗa akan Yahudu da Nasara:

﴿وَقَالُواْ لَن يَدۡخُلَ ٱلۡجَنَّةَ إِلَّا مَن كَانَ هُودًا أَوۡ نَصَٰرَىٰۗ تِلۡكَ أَمَانِيُّهُمۡۗ قُلۡ هَاتُواْ بُرۡهَٰنَكُمۡ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ111﴾

{Kuma suka ce: "Bãbu mai shiga Aljanna fãce waɗanda suka zama Yahũdu ko Nasãra." Waɗancan tãtsũniyõyinsu ne. Ka ce: "Ku kãwo dalilinku idan kun kasance mãsu gaskiya} [al-Baƙara: 111], Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿وَإِنْ تُطِعْ أَكْثَرَ مَنْ فِي الْأَرْضِ يُضِلُّوكَ عَنْ سَبِيلِ اللَّهِ...﴾

{Kuma idan ka bi mafiya yawan waɗanda suke a cikin ƙasa da ɗã'a sunã ɓatar da kai daga hanyar Allah} [al-An'am: 116],

Sannan lallai mafi yawancin waɗannan bukukwawa na maulidai tare da kasancewarsu bidi’a ne, suna ƙunshe ma da munanan ayyuka na daban; kamar cakuɗuwar mata da maza, amfani da waƙoƙi da kayan kaɗe-kaɗe, da shan abubuwa masu sa maye da masu bugarwa da wanin haka na abubuwan sharri. Kuma wani abu yakan faru wanda ya fi haka muni, itace babbar shirka, wannan kuwa, ta hanyar wuce iyaka a sha'anin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, ko waninsa cikin waliyyai da roƙonsa da neman agajinsa da neman madadi daga gare shi, da ƙudurce cewa ya san gaibu , da wanin haka cikin abubuwan da suke na kafirci waɗanda da yawa cikin mutane suke ta’ammuli da su a lokacin bikin da suke yi na maulidin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da waninsa cikin waɗanda ake cewa waliyyai. Haƙiƙa ya inganta daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Kashedinku da wuce iyaka a cikin addini, don abinda ya halakar da waɗanda suke kafinku shi ne wuce iyaka a cikin addini» Kuma - tsira da aminci su tabbata a gare shi - ya ce: «Kada ku wuce gona da iri wajen yabona kamar yadda Nasara suka wuce gona da iri ga Ɗan Maryam, ni kawai bawa ne, to ku ce Bawan Allah ne kuma ManzonSa ne». Bukhari ya fitar da shi a cikin Sahihinsa, daga hadisin Umar - Allah Ya yarda da shi -.

Daga cikin abubuwan mamaki da al'ajabi: Yadda mutane da dama ke himma da ƙoƙari wajen halartar waɗannan bukukuwan na bidi'a, suna kare su, kuma suna kaucewa abin da Allah Ya wajabta musu na halartar Juma'a da jam'i, ba su ɗauki hakan wani abu ba, kuma ba su ga cewa sun aikata wani babban mummunan abu ba, babu shakka wannan yana daga cikin raunin imani, da ƙarancin basira, da yawan abin da ya rufe zukata daga nau'o'in zunubai da saɓo, muna roƙon Allah Ya bamu lafiya da sauran musulmai.

Yana daga hakan: Lalle wasu daga cikinsu suna zaton cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana zuwa wurin da ake yin maulidi; saboda haka ne suke miƙewa don nuna soyayya da kuma marhaban. Wannan kuwa yana daga cikin mafi girman ɓarna da mafi munin jahilci, domin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, ba ya fitowa daga ƙabarinsa kafin ranar alƙiyama, ba ya haɗuwa da kowa cikin mutane kuma ba ya zuwa taronsu, bari dai yana nan a ƙabarinsa har zuwa ranar alƙiyama, kuma ransa yana mafi ɗaukakar Illiyyun a wurin Ubangijinsa a gida na karamci kamar yadda Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya faɗa:

﴿ثُمَّ إِنَّكُمْ بَعْدَ ذَلِكَ لَمَيِّتُونَ15 ثُمَّ إِنَّكُمْ يَوْمَ الْقِيَامَةِ تُبْعَثُونَ16﴾

{Sa'an nan kuma ku, bãyan wannan, lalle ne masu mutuwa ne.

Sannan kuma ku a Ranar Alƙiyama za’a tayar da ku} [al-Mua'Minun: 15 - 16].

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Ni ne farkon wanda ƙabari zai tsagewa ranar Alƙiyama, kuma farkon mai ceto, kuma farkon wanda za'a bawa ceto». Mafificin Salati da aminci daga Ubangijinsa su tabbata a gareshi.

To waɗannan ayoyi guda biyu masu girma da hadisin maɗaukaki, da kuma abinda ya zo akan ma’anoninsu na ayoyi da hadisai: Dukkansu suna nuni ne akan lalle Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da waninsa cikin waɗanda suka rasu, kaɗai zasu fito ne daga ƙaburburansu ne a ranar alƙiyama, wannan kuwa lamari ne da aka yi ijima’i a kansa a tsakanin malamai musulmai; babu wata jayayya a tsakaninsu a cikinsa. Don haka yana kamata ga kowanne musulmi ya faɗaka da waɗannan abubuwan, kuma ya kiyayi abinda jahilai da ire-irensu suka ƙago na bidi’o’i da shaci faɗi; waɗanda Allah bai saukar da wani dalili kansu ba. Allah Shi ne abin neman taimako, kuma gare Shi muka dogara, kuma babu ƙarfi babu dabara ba face gareShi.

Amma salati da sallama ga Manzon Allah- tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: to wannan yana cikin manyan abubuwa masu kusantarwa kuma suna cikin ayyuka na gari, kamar yadda Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya faɗa:

﴿إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِيِّۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ صَلُّواْ عَلَيۡهِ وَسَلِّمُواْ تَسۡلِيمًا56﴾

{Lallai Allah da Mala'ikunSa su na salati ga Annabi ya ku waɗanda sukayi imani kuyi salati a gareshi kuma kuyi sallama mai yawa}. [al-Ahzab: 56], Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Wanda yayi salati a gareni sau ɗaya, Allah Zai masa salati sau goma». Kuma shi abin shara'antawa ce a dukkan lokuta, kuma ya fi ƙarfi a ƙarshen sallah, kai wajibi ne ma a wurin wasu malaman a Tahiyar ƙarshe ta kowacce sallah. Kuma sunnantuwar ta tana ƙara ƙarfafa a wurare masu yawa; daga ciki: Bayan kiran sallah da lokacin ambaton sa (Annabi) - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da yinin Juma’a da kuma darensa, kamar yadda hadisai masu yawa suka yi nuni akan hakan.

Allah ne wanda ake roƙa Ya datar damu da sauran musulmai fahimtar AddininSa da tabbata a kansa, kuma Yayi wa kowa baiwa da bin sunnah, da kiyaye bidi'a, lallai cewa Shi Mai yawan kyauta ne kuma Mai karamci.

Allah Ya Yi tsira da aminci ga Annabinmu Muhammadu da alayansa da sahabbansa.

 

 

***

 


بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ

SAƘO NA SHIDA:

Hukuncin taron bikin daren Isra'i da Mi'iraji

Godiya ta tabbata ga Allah, tsira da amincin Allah su tabbata ga Manzon Allah, da alayansa da sahabbansa.

Bayan haka: Babu shakka cewa Isira'i da Mi'iraji suna daga cikin ayoyin Allah masu girma masu nuni akan gaskiyar ManzonSa annabi Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, da kuma girman matsayinsa a wajen Allah - Mai girma da ɗaukaka-, kamar yadda suke daga cikin dalilai akan ikon Allah mai ban mamaki, da kuma ɗaukakarSa - Subhanahu wa Ta'ala - akan dukkan halittunSa, Allah - Subhanahu wa Ta'ala - Ya ce:

﴿سُبۡحَٰنَ ٱلَّذِيٓ أَسۡرَىٰ بِعَبۡدِهِۦ لَيۡلٗا مِّنَ ٱلۡمَسۡجِدِ ٱلۡحَرَامِ إِلَى ٱلۡمَسۡجِدِ ٱلۡأَقۡصَا ٱلَّذِي بَٰرَكۡنَا حَوۡلَهُۥ لِنُرِيَهُۥ مِنۡ ءَايَٰتِنَآۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡبَصِيرُ1﴾

{Tsarki ya tabbata ga wanda Ya yi tafiyar dare da bãwanSa da dare daga Masallaci mai alfarma zuwa ga Masallaci mafi nĩsa wanda Muka sanya albarka a gefensa dõmin Mu nũna masa daga ãyõyinMu. Lalle ne Shi shĩ ne Mai ji, Mai gani} [al-Isra'a: 1].

An samu Hadisan da yawa daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - cewa an ɗauke shi zuwa sammai, kuma an buɗe masa ƙofofinsu har ya wuce sama ta bakwai, sai Ubangijinsa - Mai girma da ɗaukaka - Yayi masa magana da abin da Ya so, kuma Ya farlanta masa salloli biyar, kuma Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya farlanta su da farko hamsin, Annabinmu Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -bai gushe ba yana koma maSa yana roƙon sauƙi, har Ya maida su biyar, to su biyar ne a farilla, hamsin ne a lada; domin kyakkyawa tana da lada goma, godiya ta tabbata ga Allah bisa dukkan ni'imominSa.

Wannan daren da a cikinsa ne aka yi Isra’ila da Mi’iraji, hadisai ingantattu ba su zo da ayyana daren ba, ba wai a Rajab ba, ba kuma a waninsa ba, duk abinda ya zo na ayyana daren to bai tabbata ba daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a wurin malamai ma’abota ilimin hadisi. Allah Yana da cikakkiyar hikima a mantar da mutane wannan daren, da ace ayyanashi ya tabbata to da baya halatta ga mutane su keɓanceshi da wani abu na ibadodi, kuma ba ya halatta gare su suyi bukukuwa saboda (daren); domin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, da sahabbansa - Allah Ya yarda da su - basu yi bukukuwa saboda (daren) ba, kuma ba su ware shi da wani abu ba. Da a ce bukukuwan abu ne shar’antacce da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi bayaninsa ga al’umma; ko dai ta magana ko kuma ta aiki, da wani abu ya faru na hakan da an sani, kuma da ya shahara, da kuma sahabbai - Allah Ya yarda da su - sun naƙalto mana. Don haƙiƙa sun ruwaito duk wani abu da al’umma take buƙatarsa daga Annabin na su, basu yi sakaci a wani abu da ya shafi Addini ba, a’a su ne ma na farko a duk wani alheri. To da taron bikin wannan daren shar’antacce ne da sun riga kowa aikata shi. Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - shi ya fi kowa yi wa mutane nasiha, kuma tabbas ya isar da manzanci matuƙar isarwa, kuma ya bayar da amana. Da ace girmama wannan daren da yin biki saboda shi yana cikin Addinin Allah da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - bai gafala daga aikata shi ba, kuma ba zai ɓoye shi ba. A sanda babu wani abu da ya faru cikin waɗannan sai aka sani cewa yin bikin daren da girmama shi ba sa cikin Musulinci ta kowanne ɓangare, domin tabbas Allah Ya cikawa wannan al’ummar Addininta, kuma Ya cika mata ni’ima, kuma Ya yi inkari ga duk wanda ya shar’anta wani abu a Addini da Allah bai bada izini akai ba, sai (Allah) Mai tsarki da ɗaukaka - Ya ce a cikin littafinS mai bayyanawa:

﴿...ٱلۡيَوۡمَ أَكۡمَلۡتُ لَكُمۡ دِينَكُمۡ وَأَتۡمَمۡتُ عَلَيۡكُمۡ نِعۡمَتِي وَرَضِيتُ لَكُمُ ٱلۡإِسۡلَٰمَ دِينٗا...﴾

{Kuma yaune Na cika muku addininku, kuma Na cika muku ni'imaTa kuma Na yarje muku musulunci a matsayin addini} [Ma'ida: 3], Kuma Allah - Maɗaukaki - Ya ce:

﴿أَمۡ لَهُمۡ شُرَكَٰٓؤُاْ شَرَعُواْ لَهُم مِّنَ ٱلدِّينِ مَا لَمۡ يَأۡذَنۢ بِهِ ٱللَّهُۚ وَلَوۡلَا كَلِمَةُ ٱلۡفَصۡلِ لَقُضِيَ بَيۡنَهُمۡۗ وَإِنَّ ٱلظَّٰلِمِينَ لَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٞ21﴾

{Kõ sunã da waɗansu abõkan tãrayya (da Allah) waɗanda suka shar'anta musu, game da addini, abin da Allah bai Yi izni da shi ba? Kuma bã dõmin kalmar hukunci (a lahira ba), da lalle, an yi hukunci (tun anan duniya) a tsakãninsu. Kuma lalle azzãlumai sunã da azãba mai raɗaɗi} [al-Shura: 21].

Kuma ya tabbata daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a hadisai ingantattu: Tsawatarwa akan bidi’a da kuma bayani ƙarara cewa bidi’a ɓata ce, don faɗakar da wannan al’ummar akan girman hatsarinta (ita bidi’ar) da nesantasu daga kusantarta daga cikin hakan: Abinda ya tabbata a cikin Sahihaini (Sahih al-Bukhari da Sahih Muslim) daga Nana Aisha - Allah Ya yarda da ita - daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - cewa ya ce: «Duk wanda ya farar da wani sabon abu a cikin wannan Addinin namu wanda baya ciki to shi abun mayar masa ne». A cikin wata riwayar ta Muslim: «Duk wanda yayi wani aiki wanda babu umarninmu a cikinsa to wannan aikin abin mayar masa ne». A cikin Sahihu Muslim daga Jabir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana faɗa a cikin huɗubarsa ranar Juma'a: «Bayan haka, to lallai cewa mafificin zance (shi ne) Littafin Allah, kuma mafificiyar shiriya (ita ce) shiriyar (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, kuma mafi sharrin al'amura abubuwan da aka farar, dukkanin bidi'a ɓata ce». Nasa'i ya ƙara da sanadi kyakkyawa: «Kuma kowacce ɓata tana cikin wuta». Ya zo a cikin Sunan daga Irbad bn Sariyah - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi mana wa’azi, wa’azi mai shiga jiki, zukata suka firgita, idanuwa suka zub da hawaye, muka ce: Ya Ma’aikin Allah! Kamar wa’azin mai bankwana, Ka yi mana wasiyya, sai ya ce: Ina yi muku wasicci da tsoron Allah, da ji da bi, koda bawa ne ya shugabance ku, domin cewa wanda ya rayu daga cikinku zai ga saɓani mai yawa, to na hore ku da sunnata da sunnar halifofina shiryayyu a bayana, ku riƙe su da turamen haƙoranku, na haneku da fararrun al'amura, domin cewa kowanne fararran abu bidi'a ce, kuma kowacce bidi'a ɓata ce. Hadisai da suka zo da wannan ma’anar suna da yawa.

Haƙiƙa ya tabbata daga sahabban Ma’aikin Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, haka kuma daga maganata na ƙwarai bayansu; tsawatarwa daga bidi’a da tsoratarwa akanta; ba komai ya sa haka ba sai domin ita ƙari ce a cikin Addini, kuma shari’a ce da Allah bai bada izini a kanta ba, kuma koyi ce da maƙiya Allah cikin Yahudu da Nasara, a yadda suke yin ƙari a Addininsu, da kuma yadda suke ƙirƙiro bidi’a a cikinsa na abinda Allah bai bada izini ba, kuma don lazimtarta tawaya ce ga Addinin Musulinci, kuma tuhumarsa ce da rashin cika, kuma sananne ne abinda yake cikin haka na ɓarna mai girma, da mummunan abin ƙi mai girma, kuma ya ci karo da faɗin Allah - girmanSa ya ɗaukaka -:

﴿...ٱلۡيَوۡمَ أَكۡمَلۡتُ لَكُمۡ دِينَكُمۡ...﴾

{Kuma yaune Na cika muku addininku, kuma Na cika muku ni'imaTa kuma Na yarje muku musulunci a matsayin addini} [Ma'ida: 3], da saɓawa bayyananniya ga hadisan Manzo - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - masu tsawatarwa daga bidi'o'i da kuma tsoratarwa daga gare su.

Wannan kenan, ina fatan abinda muka ambata na dalilai sun wadatar, kuma sun gamsar da mai neman gaskiya a inkarin wannan bidi’ar; ina nufin: Bidi’ar bikin daren Isra’i da Mi’iraj, da kuma tsawatarwa akan ta alhali ita ba ta cikin Addinin Musulinci ta ko’ina.

Saboda abin da Allah Ya wajabta na yin nasiha ga musulmai, da bayyana abin da Allah Ya shar'anta musu na addini, da haramcin ɓoye ilimi; na ga dacewar faɗakar da 'yan uwa musulmai kan wannan bidi'a, wadda ta yaɗu a cikin yawancin garuruwa, har wasu mutane suka ɗauka cewa a cikin addini take.

Allah nake roƙo da Ya gyara halayen musulmai baki ɗaya, kuma Ya basu fahimta a cikin addini, Ya datar damu da su don riƙe gaskiya da tsayawa a kanta, da barin duk abin da ya saɓa mata, lalle ne Shi ne Majiɓincin hakan kuma Mai iko a kansa.

Allah Yayi tsira da aminci da albarka ga bawanSa kuma ManzonSa Annabin mu Muhammad da alayensa da aahabbansa.

 

***

 


بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ

SAƘO NA BAKWAI:

Hukuncin yin biki a daren rabin watan Sha'aban

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah wanda Ya cika mana addini, kuma Ya cika ni’ima a kanmu, tsira da amincin Allah su tabbata ga AnnabinSa kuma ManzonSa (annabi) Muhammad Annabin tuba da rahama.

Bayan haka: Haƙiƙa Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce:

﴿...ٱلۡيَوۡمَ أَكۡمَلۡتُ لَكُمۡ دِينَكُمۡ وَأَتۡمَمۡتُ عَلَيۡكُمۡ نِعۡمَتِي وَرَضِيتُ لَكُمُ ٱلۡإِسۡلَٰمَ دِينٗا...﴾

{Kuma yaune Na cika muku addininku, kuma Na cika muku ni'imaTa kuma Na yarje muku musulunci a matsayin addini} [Ma'ida: 3], Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿أَمۡ لَهُمۡ شُرَكَٰٓؤُاْ شَرَعُواْ لَهُم مِّنَ ٱلدِّينِ مَا لَمۡ يَأۡذَنۢ بِهِ ٱللَّهُ...﴾

{Ko suna da wasu abokan tarayya ne da suke shar'anta musu addini abin da Allah bai musu izini da shi ba} [al-Shura: 21], Kuma ya zo a cikin Sahihil Bukari da Muslim daga Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Duk wanda ya farar da wani sabon abu a cikin wannan Addinin namu wanda ba ya ciki to shi abun mayarwa ne». Acikin Sahih Muslim daga Jabir - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa a cikin huɗubar Jumu'a: «Bayan haka, to lallai cewa mafificin zance (shi ne) littafin Allah, kuma mafificiyar shiriya (ita ce) shiriyar (annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, kuma mafi sharrin al'amura abubuwan da aka farar, dukkanin bidi'a ɓata ce». Ayoyi da hadisai masu yawa akan wannan ma’ana suna nan, kuma suna nuni a fili cewa Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya cikawa wannan al’umma addininta, kuma Ya cika ni’imarSa a gare ta, kuma bai karɓi ran AnnabinSa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ba sai bayan ya isar, isarwa bayyananniya, kuma ya bayyana wa al’umma duk abin da Allah Ya shar’anta mata na maganganu da ayyuka, Kuma Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare - shi ya fayyace duk abinda mutane suke ƙirƙira su jingina shi ga Addinin Musulinci na magana ko ayyuka; to gabaɗayan sa bidi’a ne abin mayarwa ga wanda ya ƙirƙire shi, ko da kuwa niyyar sa kyakkyawa ce, kuma haƙiƙa sahabban Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sun san hakan, haka kuma malaman Musulinci da suka zo bayansu, sai suka yi musun bidi’o’in, suka kuma tsawatar akan hakan, kamar yadda duk wanda ya yi rubutu akan girmama sunnah da inkarin bidi’a ya ambata; kamar Ibn Waddah da Ɗarɗushi da Abu Shamah da wasunsu.

Kuma lalle yana daga bidi’o’in da wasu mutane suka ƙirƙira: Bidi’ar bikin daren Nisfu Sha’aban (wato daren da watan Sha’aban yayi rabi) da keɓance yinin da yin azumi, kuma babu wani dalili da ya halatta ayi dogaro da shi, kuma hadisai masu rauni sun zo akan falalarsa, ba ya halatta a dogara a kan su.

Amma abin da ya zo akan falalar sallah a cikinta; dukkanin sa ƙarya ne, kamar yadda masana ilimi da yawa suka yi nuni da hakan, kuma za a zo da ambaton wasu daga cikin maganganunsu in Allah Ya so.

Haƙiƙa kuma, akwai bayanai daga wasu cikin Salaf (magabata) na mutanen Sham da wasun su.

Abinda jamhurun malamai suka yi ijima’i a kansa shi ne wannan taron bikin bidi’a ne, kuma dukkkan hadisan da suka zo akan falalarsa da’ifai ne (masu rauni), wasu hadisan ma maudu'ai (na ƙarya ne), daga cikin waɗanda suka yi tambihi akan hakan: al-Hafiz Ibn Rajab, a littafinsa: (Laɗa’iful Ma’arif), da waninsa, kuma sananne ne cewa hadisai da'ifai kaɗai ana aiki da su ne a ibadun da asalinsu ya tabbata da dalilai ingantattu, Amma bikin daren Nisfu Sha’aban to ba shi da wani asali ingantacce har da za'a iya dogaro gare shi da hadisai da'ifai. Haƙiƙa Imam Abul Abbas Shaikhul Islam Ibn Taimiya - Allah Ya yi masa rahama - ya ambaci wannnan babbar ƙa’idar:

Kuma ina isar maka - ya kai mai karatu - abin da wasu ma'abota ilimi suka faɗa a cikin wannan al'amari, domin ka kasance shaida a cikin hakan.

Haƙiƙa malamai sun yi ijma’i - Allah Ya yi musu rahma - akan abinda yake wajibi shine: Mayar da abinda mutane suka yi jayayya a kansa na mas’aloli zuwa ga littafin Allah (Alƙur'ani) da kuma sunnar ManzonSa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, to abinda su biyun suka yi hukunci da shi ko ɗayansu to shi ne shari’ar da ta zama wajibi a bi ta, abin da kuma ya saɓa musu to ya wajaba a yi watsi da shi, abin da kuma bai zo a cikinsu ba (Alƙur'ani da Sunnah) na ibada to bidi’a ne ba ya halasta a aikata shi balle ma a yi kira zuwa gare shi, ko a ga dacewarsa, Allah Mai tsarki da ɗaukaka - Ya ce:

﴿يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ أَطِيعُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُواْ ٱلرَّسُولَ وَأُوْلِي ٱلۡأَمۡرِ مِنكُمۡۖ فَإِن تَنَٰزَعۡتُمۡ فِي شَيۡءٖ فَرُدُّوهُ إِلَى ٱللَّهِ وَٱلرَّسُولِ إِن كُنتُمۡ تُؤۡمِنُونَ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِۚ ذَٰلِكَ خَيۡرٞ وَأَحۡسَنُ تَأۡوِيلًا59﴾

{Yã kũ waɗanda suka yiĩmãni! Ku yi ɗã'a ga Allah, kuma ku yi ɗã'a ga ManzonSa, da ma'abũta al'amari daga cikinku. Idan kun yi jãyayya a cikin wani abu, to ku mayar da shi zuwa ga Allah da ManzonSa idan kun kasance kunã ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira. wannan ne mafi alhẽri, kuma mafi kyau ga fassara}. [al-Nisa'a: 59], Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿وَمَا ٱخۡتَلَفۡتُمۡ فِيهِ مِن شَيۡءٖ فَحُكۡمُهُۥٓ إِلَى ٱللَّهِ...﴾

{Kuma abin da kuka yi saɓani a cikinsa na daga wani abu to hukuncinsa zuwa Allah yake} [al-Shura: 10] Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿قُلۡ إِن كُنتُمۡ تُحِبُّونَ ٱللَّهَ فَٱتَّبِعُونِي يُحۡبِبۡكُمُ ٱللَّهُ وَيَغۡفِرۡ لَكُمۡ ذُنُوبَكُمۡ...﴾

{Ka ce: "Idan kun kasance kunã son Allah to, ku bĩ ni, Allah Ya sõ ku, kuma Ya gãfarta muku zunubanku} [Aal- Imran: 31]. Kuma Allah - Maɗaukaki - Ya ce:

﴿فَلَا وَرَبِّكَ لَا يُؤۡمِنُونَ حَتَّىٰ يُحَكِّمُوكَ فِيمَا شَجَرَ بَيۡنَهُمۡ ثُمَّ لَا يَجِدُواْ فِيٓ أَنفُسِهِمۡ حَرَجٗا مِّمَّا قَضَيۡتَ وَيُسَلِّمُواْ تَسۡلِيمٗا65﴾

{To, a'aha! Ina rantsuwa da Ubangijinka, ba za su yi ĩmãni ba, sai sun yarda da hukuncinka ga abin da ya sãɓa a tsakãninsu, sa'an nan kuma ba su sãmi wani ƙunci a cikin zukãtansu ba, daga abin da ka hukunta, kuma su sallama sallamãwa} [al-Nisa'a: 65], kuma ayoyi a cikin wannan ma'ana suna da yawa, kuma suna nuni da wajabcin mayar da al'amuran da ake saɓani zuwa ga Littafi (AlKur’ani) da Sunnah, da kuma wajabcin yarda da hukuncinsu, kuma cewa hakan shi ne abin da imani ke buƙata, kuma mafi alheri ga bayi a nan duniya da lahira, kuma mafi kyawun fassara: wato kyakkyawan ƙarshe.

Masanin Hadisi Ibn Rajab -Allah Yayi masa rahama- ya ce a cikin littafinsa: (Laɗa'if al-Ma'arif) a cikin wannan mas'ala -bayan maganar da ta gabata- abin da ya ce:

«Kuma daren rabin Sha'aban, Tabi'ai daga mutanen Sham; kamar Khalid bin Ma'dan, da Mak'hul, da Luƙman bin Amir da sauransu, suna girmama shi kuma suna ƙoƙari a cikinsa wajen bauta, kuma daga gare su ne mutane suka ɗauki falalarsa da girmamawarsa, Kuma an ce: Wasu hadisai na Isra'iliyyat sun kai garesu, to a yayin da waɗannan abubwan suka yaɗu a garuruwa daga gare su, sai mutane suka rarrabu akan hakan; daga cikinsu akwai wanda ya karɓe su kuma ya yi tarayya da su akansu cikin girmama su, daga cikinsu kuma akwai wasu jama'a daga masu bauta a mutanen Basrah da wasunsu. Yawancin malaman Hijaz sun yi inkari akan hakan, daga cikinsu akwai: Aɗa’au, da Ibn Abi Mulaika, kuma Abdulrahman ɗan Zaid dan Aslam ya ruwaito daga malaman fiƙihun Madina, kuma shi ne faɗin almajiran Malik da wasu, kuma suka ce: wannan duka bidi'a ce.

Malamai na Sham sun yi saɓani a kan siffar rayawar a kan maganganu guda biyu:

Na farko: An so a rayar da ita a cikin masallatai a cikin jama'a, Khalid bin Ma'dan da Luƙman bin Amir da wasu sun kasance suna sanya mafi kyawun tufafinsu, suna sanya turare da yin tozali, suna tsayawa a cikin masallaci a daren su, kuma Ishaƙ dan Rahuwaih ya yarda da su akan hakan, Kuma ya ce game da tsayuwarta a masallatai cikin jam'i: wannan ba bidi'a ba ce, Harb al-Karmani ya ruwaito a cikin mas'alolinsa.

Na biyu: Ana ƙyamatar taruwa a bikin Nisfu Sha’aban a masallatai don sallah da labarai da addu'a, amma ba a ƙyamatar mutum ya yi sallah a daran don kansa, wannan shi ne ra'ayin al-Auza'i, limamin mutanen Sham kuma malamin su, kuma wannan shi ne mafi kusanci insha Allah Ta'ala». Har zuwa inda ya ce: «Ba’a san Imam Ahmad yana da wata magana ba akan daren Nisfu Sha’aban ba, za’a fitar da mustahabbacin tsayuwarsa ne daga gare shi ta riwayoyi biyu cikin riwayoyi daga gare shi a tsayuwar darare biyu na idi, domin (a cikin wata riwayar) ba’a so a yi nafilfilin a cikin jam’i a cikinsa; domin ba’a samo hakan daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ba haka kuma sahabbansa, An so ta (a cikin wata ruwayar), saboda abin da Abdurrahman ɗan Yazid ɗan Aswad ya yi, wanda shi ne daga cikin tabi'ai, haka ma tsayuwar daren tsakiyar Sha'aban, ba ta tabbata daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ko daga sahabbansa ba, amma ta tabbata daga wasu daga cikin tabi'ai daga manyan malaman fiƙihu na mutanen Sham».

Abin nufi a maganar al-Hafiz Ibn Rajab - Allah Ya yi masa rahama - ya ƙare, kuma a cikinsa akwai bayani a bayyane cewa wani abu na daren Nisfu Sha'aban bai tabbata daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ba - ko sahabbansa - Allah Ya yarda da su -.

Amma abinda al-Auza’i - Allah Ya yi masa rahama - ya zaɓa na son tsayuwarta ga mutum ɗaya, da kuma zaɓin al-Hafiz Ibn Rajab ga wannan magana, to wannan abu ne mai ban mamaki kuma mai rauni; domin dukkanin abubuwan basu tabbata da hujjojin shari’a ba cewa yana daga cikin shari’a, to bai halatta ga musulmi ya ƙirƙire shi a cikin addinin Allah ba, ko ya aikata shi shi kaɗai ko a cikin jama’a, ko ya ɓoye shi ko ya bayyana shi; saboda gamewar faɗin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: «Duk wanda ya yi wani aiki wanda babu umarninmu a cikinsa to wannan aikin abun mayarwa ne». Da wasun su daga hujjoji masu nunin ƙin bidi'a da tsawatarwa daga gare ta.

Kuma Imam Abu Bakar al'Ɗarɗusi - Allah Yayi masa rahama - ya ce a cikin littafinsa: "Al'hawadith wal bid'aa" abin da ya ce:

«Ibnu Waddah ya ruwaito daga Zaid ɗan Aslam, ya ce: Ba mu samu kowa daga cikin dattawanmu ko malaman fiƙihunmu suna mai da hankali ga rabin Sha'aban ba, kuma ba su mai da hankali ga hadisin Mak'hul ba, kuma ba su ganin yana da falala akan sauran kwanaki ba».

Kuma aka ce wa ɗan Abi Mulaika: Lallai Ziyad an-Namiri yana cewa: «Lallai ladar daren tsakiyar Sha'aban yana daidai da Lailatul ƙadari», Sai ya ce: "Da na ji shi kuma a hannuna akwai sanda da na buge shi». Ziyad ya kasance mai labari ne (wa’azin turmi) manufar ta ƙare.

Babban malami al-Shaukani,- Allah Ya yi masa rahama - a littafinsa «Alfawa’idul Majmu’ah» ya faɗi abinda nassinsa shine:

Hadisi: «Ya Ali, duk wanda ya yi sallah raka'a ɗari a daren tsakiyar Sha'aban, yana karanta wa a kowacce raka'a da Fatiha da Qul huwa Allahu Ahad sau goma; Allah zai biya masa dukkan wata buƙata». Hadisin Maudu'i ne, kuma a lafuzansa da ke bayyana abin da mai aikata shi zai samu na lada babu wanda ke da hankali zai yi shakka a cikin ƙaryarsa, kuma maruwaitansa ba a san su ba, an kuma ruwaito shi ta wata hanya ta biyu da ta uku dukkan su ƙarya ne kuma masu rawaiton su ba a san su ba, Ya ce a cikin: «al-Mukhtasar»: Hadisin sallar rabin Sha'aban ba shi da inganci, kuma daga Ibnu Hibban daga hadisin Ali: «Idan dare na rabin Sha'aban ya kasance, ku yi tsayuwar dare, kuma ku yi azumin ranar sa», mai rauni ne. Ya ce a cikin: «Al-La'ali»: «Raka'a ɗari a cikin rabin Sha'aban da Ikhlasi sau goma» tare da tsawon falalarsa, ga Dailami da wasu, Hadisin ƙarya ne, kuma mafi yawan masu ruwaitawa a cikin hanyoyi uku ba a san su ba kuma raunana ne, Ya ce: "Raka'o'i goma sha biyu da ikhlasi sau talatin". Mauru'i ne, "da raka'o'i goma sha huɗu" Mauru'i ne.

Kuma wasu daga cikin malamai sun ruɗu da wannan hadisi; kamar mai littafin (Ihya) da sauransu haka nan daga cikin masu tafsiri, an kuma ruwaito sallar wannan daren - wato: daren rabin Sha'aban - a hanyoyi daban-daban dukkan su ba su da inganci kuma an ƙirƙiro su ne, Wannan kuma ba ya kore riwayar Tirmizi cikin hadisin Nana Aisha - Allah Ya yarda da ita - na tafiyar da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - zuwa Baƙi’a, da kuma saukar Ubangiji a daren Nisfu zuwa saman duniya, kuma Shi (Ubangiji) yana gafartawa sama da adadin gashin dabbobin Kalb, to wannan maganar kawai akan wannan sallar ce da aka ƙaga wannan daren. Amma hadisin Nana Aisha yana da rauni da katsewa, kamar yadda hadisin Ali da aka ambata a baya game da tsayuwar da daddare, ba ya kore cewa wannan sallar ƙagaggiya ce, duk da raunin da ke ciki kamar yadda muka ambata.

Al-Hafiz al-Iraƙi ya ce: «Hadisin sallar daren rabin dare (na Sha’aban) an ƙirƙire shi ne ga Manzon Allah -tisira da amincin Allah su tabbata a gareshi- kuma ƙarya ce aka yi masa», Kuma Imam al-Nawawi ya ce a cikin littafin: (al-Majmu'): "Sallar da aka sani da Sallar Ragha'ib, wato raka'o'i goma sha biyu tsakanin Magriba da Isha, a daren Juma'a ta farkon Rajab, da sallar daren rabin Sha'aban raka'o'i ɗari, waɗannan salloli biyu bidi'a ce mummuna, kada a yaudareka da ambatonsu a cikin littafin: (Kutul ƙulub), da (Ihya Ulumuddin), ko da hadisin da aka ambata a cikinsu, domin duk wannan ba daidai ba ne, kada a yaudareka da wasu daga cikin malamai da suka rikice a kan hukuncinsu suka rubuta takardu a kan soyyayarsu, domin sun yi kuskure a cikin wannan.

Haƙiƙa babban malami Imam Abu Muhammad Abdurrahman bn Isma’il al-Maƙdasi ya wallafa littafi mai kyau akan ɓatansu su biyun, kuma ya yi bayani mai kyau a cikinsa ya kyautata, maganar malamai a wannan mas’alar tana da yawa, da zamu dinga kawo duk abinda muka gani a wannan mas’alar to da maganar ta yi yawa, muna fatan wannan da muka ambata ya isa kuma ya gamsar ga mai neman gaskiya.

Daga cikin abinda ya gabata na ayoyi da hadisai da kuma maganar malamai; zai bayyana ga mai neman gaskiya, lalle bikin daren Nisfu Sha’aban ko waninsa, da kuma ware yininsa da azumi; to wannan bidi’a ce mummuna a wurin mafi yawan malamai, kuma ba shi da wani asali a shari’a mai tsarki, kawai yana cikin abinda aka ƙirƙira a cikin Musulinci bayan zamanin sahabbai - Allah Ya yarda da su -, kuma faɗin Allah - girmanSa ya ɗaukaka - ya ishi mai neman gaskiya a wannan babin da waninsa:

﴿...ٱلۡيَوۡمَ أَكۡمَلۡتُ لَكُمۡ دِينَكُمۡ...﴾

(A yau na cika muku addininku) [al-Ma'ida: 3]. Da abinda ya zo a cikin ma'anarsu na ayoyin, da faɗin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: «Duk wanda ya farar da wani abu a cikin wannan Addinin namu wanda ba ya ciki. to shi abun mayarwa ne». Da abinda ya zo a cikin ma'anarsa daga hadisai.

Ya zo cikin Sahihin Muslim daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Kada ku ware daren Juma'a da tsayuwar dare daga cikin sauran darare, kuma kada ku ware ranar da azumi daga cikin sauran ranaku, sai dai idan yana cikin azumin da ɗayanku yake yi». Da ace keɓance wani abu cikin darare da wani nau’i na ibada ya halatta, da daren Juma'a ya fi cancanta akan sauran darare; domin yinin ta shi ne mafi alherin yini da rana ta ɓullo a cikinsa, bisa nassosin hadisai sahihai daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, Bayan da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi gargaɗi akan keɓance daren da tsayuwa daga cikin sauran darare, hakan ya nuna cewa sauran darare ma sun fi dacewa, baya halatta a keɓance wani abu daga cikinsu da wani abu na ibada ba, sai dai da hujja sahihiya da ke nuna keɓancewar.

Kuma da yake daren Lailatul Ƙadr da dararen Ramadan an shar'anta tsayuwa da ƙoƙari a cikinsu, Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yayi nuni da hakan, kuma ya kwaɗaitar da al'umma akan tsayuwa a cikinsu, kuma ya aikata hakan da kansa, kamar yadda yake a cikin Bukhari da Muslim daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Duk wanda ya yi tsayuwar daren Ramadana yana mai imani da kuma neman lada; an gafarta masa abinda ya gabata na zunubinsa, kuma duk wanda ya tsayuwa a daren Lailatul Qadari yana mai imani da kuma neman lada, an gafarta masa abinda ya gabata na zunubinsa». Da ace daren tsakiyar Sha'aban, ko daren Juma'a na farko a Rajab ko daren Isra'i da Mi'iraji an shar'anta keɓance su da wani biki ko wani abu na ibada, da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yayiwa al'umma jagora zuwa gare shi, ko ya aikata shi da kansa, kuma da ace wani abu daga cikin wannan ya faru da sahabbai - Allah Ya yarda da su - sun isar da shi ga al'umma, ba su ɓoye shi ba, alhalin su ne mafi alkhairi na mutane, kuma mafi nasihar mutane bayan Annabawa - aminci ya tabbata agare su -, kuma Allah - Ya yarda ga ahabban Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -kuma ya yarda da su.

Kuma haƙiƙa mun sani a abinda ya gabata na maganganun malamai, cewa wani abu ba na falalar daren Juma’a ta farkon watan Rajab haka kuma daren Nisfu Sha’aban bai tabbata daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ba -, haka kuma bai tabbata daga sahabbansa ba, - Allah Ya yarda da su -. Saboda haka sai aka sani yin bikinsa bidi’a ce da aka ƙirƙira a cikin Musulinci, haka kuma keɓance ta da wasu ibadu duka bidi’a ce abar ƙi. Kuma haka daren ashirin da bakwai na watan Rajab, wanda wasu mutane ke tunanin cewa shi ne daren Isra'i da Mi'iraji, ba ya halatta a keɓance shi da wani abu na ibada, kamar yadda ba ya halatta a yi biki da shi; saboda hujjojin da suka gabata, wannan fa idan an san shi kenan, to yaya kuma a ingantaccen zance daga maganganun malamai shi ne ba a ma san shi ba, Kuma maganar wanda ya ce: Shi ne daren ashirin da bakwai na Rajab, magana ce mara tushe a cikin hadisai sahihai, kuma haƙiƙa ya kyautata wanda ya ce:

Mafificin al'amura (su ne) waɗanda suka gabata akan shiriya... kuma mafi sharrin al'amura (su ne) abubuwan da aka farar, bidi'o'i.

Allah ne abin roƙo Ya datar damu da sauran musulmai don riƙe sunnah da tabbata a kanta, da kuma tsarewa daga abin da ya saɓa mata, lallai cewa Shi Allah Mai yawan kyauta ne kuma Mai girma.

Tsira da amincin Allah su tabbata ga bawanSa kuma ManzonSa Annabinmu Muhammad da alayensa da sahabbansa baki ɗaya.

 

***

 


بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ

SAƘO NA TAKWAS:

Muhimmiyar Sanarwa akan ƙaryar wasiyyar da aka dangantawa

Shiekh Ahmad mai Hidimar Haramin Annabi maɗaukaki

Daga AbdulAzeez ɗan Abdullahi ɗan Baaz zuwa ga duk wanda zai karanta cikin musulmai, Allah Ya kiyaye su da addinin Musulunci, kuma Ya tsare mu da su daga sharrin ƙaryar jahilai, amin.

Amincin Allah ya tabbata a gareku da rahamarSa da albarkatunSa.

Bayan haka: To haƙiƙa na karanta wani jawabi da aka danganta ga Sheikh Ahmad maiyiwa Haramin Annabi mai daraja hidima, mai taken: «Wannan wasiyya ce daga Madina Munawwara daga Sheikh Ahmad Khadimul Haramin Nabawi al-Sharif», inda ya ce:

«Na kasace a farke a daren Juma’a ina karanta Alƙur'ani mai girma, bayan na karanta sunayen Allah kyawawa, to a lokacin da na kammala hakan sai na yi shirin bacci, kawai sai na ga ma’abocin hasken fuska, Ma’aikin Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - wanda ya zo da ayoyi na Alƙur'ani da hukunce-hukunce masu daraja; don rahma ga talikai, shugabammu (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -,ya ce: Ya Shaikh Ahmad, sai na ce: Amsawarka ya Ma’aikin Allah, ya mafi karamcin halittar Allah. Sai ya ce mini: Ina jin kunya daga munanan ayyukan mutane, ba zan iya haɗuwa da Ubangijina ba haka ma da Mala’iku; domin daga Juma’a zuwa Juma’a, mutum dubu ɗari da sittin ne suka mutu a tafarkin da ba na Musulinci ba, - sannan sai ya ambaci abinda mutane suka faɗa cikinsa na saɓo. Sannan sai ya ce: Wannan wasiyyar rahma ce gare su daga (Allah) Mabuwayi Mai tilastawa: Sannan ya ambaci wani sashe na alamomin tashin alƙiyama, har dai inda ya ce: - Sai ka sanar musu da wannan wasiyyar ya Shaikh Ahmad, domin an cirota ne daga Lauhul Mahfuz da alƙalamin ƙudura, duk wanda ya rubuta ta ya kuma aikata daga wani gari zuwa wani garin, haka daga wani wuri zuwa wani wurin to za’a gina masa katafaran gida a aljanna, wanda kuma bai rubuta ta ba kuma bai aikata ba, to cetona ya haramta a gare shi a ranar alƙiyama. Ko wanda ya rubuta ta kuma yana cikin talauci, Allah zai wadata shi, ko yana da bashi, Allah zai biya masa bashinsa, ko yana da wani zunubi, Allah zai gafarta masa da iyayensa saboda albarkar wannan wasiyyar, Wanda kuma bai rubuta ta daga cikin bayin Allah ba, fuskarsa zata yi baƙi a duniya da Lãhira, Kuma ya ce: Na rantse da Allah Mai girma sau uku wannan gaskiya ce, kuma idan na kasance maƙaryaci(Allah) Yasa in bar duniya ba tare da Musulunci ba, kuma wanda ya gaskata ta zai tsira daga azabar wuta, kuma wanda ya ƙaryata ta ya kafirta».

Wannan shi ne taƙaitaccen abin da ke cikin wasiyyar ƙarya da aka jinginawa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - kuma mun ji wannan wasiyyar ƙarya sau da yawa tun shekaru da dama, ana yaɗa ta tsakanin mutane lokaci zuwa lokaci, kuma ana tallata ta tsakanin yawancin talakawa, kuma a cikin lafuzanta akwai bambanci, Kuma maƙaryacin yana cewa:

Ya ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a cikin bacci, ya ɗauki wannan wasiyya, kuma a cikin wannan sanarwa ta ƙarshe da muka ambata maka ya mai karatu, mai ƙirƙirar ƙaryar yayi iƙirarin cewa yaga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - lokacin da ya shirya yin bacci, don haka ma'anar: ya gan shi a farke!

Wannan da ya ƙirƙiri wannan ƙaryar yana riya abubuwa masu yawa a cikin wannan wasiyyar; waɗanda suna cikin mafi bayyanar ƙarya, kuma mafi bayyanar ɓarna, da sannu zan faɗakar da kai game da su a waɗannan kalmomin da yardar Allah. Haƙiƙa na faɗakar a kansu a shekarun da suka gabata, na kuma yi wa mutane bayanin cewa suna daga mafi bayyanar ƙarya, kuma mafi bayyanar ɓarna. To a lokacin da na ga wannan bugun na ƙarshe, sai na yi kai ka wo a rubutata, domin ɓacinta a fili yake, da kuma girman ƙarfin halin wanda ya ƙirƙiro ƙaryar, bana zaton ɓarnarsa za ta sake ruruwa ga wanda yake da mafi ƙarancin basira ko cikakken tunani. Saidai da yawa daga ‘yan uwa sun bani labarin cewa ta rurutar da da yawa daga cikin mutane, kuma sun dinga yaɗa ta a tsakaninsu, wasu kuma sun gasgata ta; to saboda haka na ga yin rubutu a kanta ya wajaba ga ire-ire na, domin yin bayanin ɓacinta, da ƙaryata wannan abinda aka ƙaga ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, don kada wani ya ruɗu da ita. To, duk wanda ya yi nazari daga cikin masu ilimi da imani, ko kuma masu kyakkyawar ɗabi'a da hankali mai kyau; zai gane cewa ita ƙarya ce da ƙirƙira daga ɓangarori da yawa.

Na tambayi wasu daga cikin dangin Sheikh Ahmad da ake jingina wannan ƙarya gare shi, game da wannan wasiyya, sai suka amsa mini: cewa an ƙirƙira wannan magana ga Sheikh Ahmad ne, kuma bai faɗe ta ba tun asali ma, Shehin da aka ambata, Ahmad, ya rasu tun tsawon lokaci, kuma idan muka yi zato cewa shehin da aka ambata, Ahmad, ko wanda yafi shi girma, yayi iƙirarin cewa ya ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a cikin bacci ko a farke, kuma yayi masa wannan wasiyyar, da mun san da tabbaci cewa maƙaryaci ne, ko kuma wanda ya faɗa masa hakan Shaiɗan ne, ba shi ne Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ba saboda dalilai da yawa, daga cikinsu:

Na farko: Lalle Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, ba a ganin shi a farke bayan rasuwarsa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -. Duk wanda ya riya daga cikin jahilan Sufaye cewa wai ya ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a farke ko ya ce yana zuwa wurin maulidi ko abinda ya yi kama da haka; to haƙiƙa ya tafka kuskure mafi munin kuskure, kuma lamurra sun rikice masa matuƙar rikicewa, kuma ya afka cikin kuskure mai girma, ya kuma saɓawa littafi (Alƙur'ani) da sunnah da ijma’in malamai; domin mamata kaɗai za'a fito da su ne daga ƙaburburansu ranar alƙiyama ne ba a nan duniya ba. To, wanda ya faɗi akasin haka to shi maƙaryaci ne kuma ya yi ƙarya bayyananniya, ko kuma mai kuskure wanda aka ruɗe shi, bai san gaskiyar da salihan magabata suka sani ba, kuma sahabban Manzon Allah - taira da amincin Allah su tabbata a gare shid - da mabiyansu da kyautatawa suka bi, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce:

﴿ثُمَّ إِنَّكُم بَعۡدَ ذَٰلِكَ لَمَيِّتُونَ15 ثُمَّ إِنَّكُمْ يَوْمَ الْقِيَامَةِ تُبْعَثُونَ16﴾

{Sa'an nan kuma ku, bãyan wannan, lalle ne masu mutuwa ne.Sa'an nan kuma lalle ne kũ a Rãnar alƙiyãma, za a tãyar da ku}

Sannan kuma lalle ne kũ a Rãnar alkiyãma, za a iãyar da ku, [al-Mua'Minun: 15 - 16], Kuma Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Ni ne farkon wanda ƙasa za ta tsage masa ranar Alƙiyama, kuma farkon mai ceto farkon wanda za'a bawa ceto». Ayoyi da hadisai da suka zo da wannan ma’anar suna da yawa.

Na biyu: Lalle Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ba ya faɗin saɓanin gaskiya, ko yana raye ko bayan rasuwarsa. Wannan wasiyyar ta saɓawa shari’ar sa, saɓawa ta zahiri, hakan kuwa ta fuskoki da yawa - kamar yadda bayani zai zo -, kuma shi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - takan yi wu a gan shi a cikin bacci. Kuma duk wanda ya gan shi a cikin mafarki a kan surarsa mai daraja to ya gan shi; domin Shaiɗan ba ya kwaikwayon surarsa, kamar yadda ya zo a cikin hadisi sahihi mai daraja, amma abin dubawa duka yana cikin imanin mai ganin da gaskiyarsa da adalcinsa da tsarewarsa da addininsa da amincinsa, kuma shin ya ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a cikin surarsa ko a cikin wata surar.

Da a ce wani hadisi zai zo daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da ya faɗe shi a rayuwar sa, ba ta hanyar amintattu adalai masu kaifin hadda ba, to da ba za’a dogara da shi ba, ba kuma za’a yi hujja da shi ba, ko kuma ya zo ta hanyar amintattu masu kaifin hadda, saidai ya saɓawa riwayar wanda ya fi shi hadda kuma mafi aminci daga cikinsu, saɓawar da ba zai yi wu a haɗa riwayoyin biyu ba, to da ɗaya ya zama an shafe shi ba za’a yi aiki da shi ba, na biyun kuma ya zama shi ya shafe saboda haka za’a yi aiki da shi in dai hakan zai yi wu da sharuɗɗansa. Idan kuma haɗa su ba zai yi wu ba, kuma shafe wa ma ba zata yi wu ba, to ya zama dole a yi watsi da riwayar wanda baida ƙarfin hadda kuma adalarsa take koma baya, sai ayi mata hukuncin cewa ta zama Shazzah ba za yi aiki da ita ba.

To ya wasiyyar da ba’a san wanda ya yi ta ba, wanda ya karɓo ta daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, ba’a san adalarsa da amanarsa ba, to a wannan halin ita tafi cancantar a yi watsi da ita, ba za a kula da ita ba, ko da babu wani abu a cikinta da ya saɓawa shari’a, to ya wasiyyar za ta kasance idan a cikinta akwai abubuwan da suka saɓawa shari’a, kuma ita ƙarya ce aka yi wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, kuma tana ƙunshe da wata shari'ar da Allah bai bada izini akai ba?!

Haƙiƙa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yace: «Wanda ya (danganta mini) abin da ban faɗa ba; to ya tanadi mazauninsa a wuta». Kuma haƙiƙa wanda ya ƙirƙiri wannan ƙaryar ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, ya faɗi abinda (Annabi) bai faɗa ba, kuma yayi masa ƙarya a bayyane mai hatsari. Mamakin dacewarsa ga wannan narko (na azaba) mai girma, mamakin cancantarsa da shi idan bai yi gaggawar tuba ba, ya kuma yaɗawa mutane ƙaryar wannan wasiyyar da ya yi ta akan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -; domin duk wanda ya yaɗa ɓarna a cikin mutane ya kuma jinginata ga Addini; to tuban shi ba ya inganta har sai ya sanar (da ƙaryar) kuma ya bayyanar, har mutane su tabbatar da ya bar wannan ƙaryar ya kuma ƙaryata kansa; saboda faɗin Allah - girmanSa ya ɗaukaka -:

﴿إِنَّ ٱلَّذِينَ يَكۡتُمُونَ مَآ أَنزَلۡنَا مِنَ ٱلۡبَيِّنَٰتِ وَٱلۡهُدَىٰ مِنۢ بَعۡدِ مَا بَيَّنَّٰهُ لِلنَّاسِ فِي ٱلۡكِتَٰبِ أُوْلَٰٓئِكَ يَلۡعَنُهُمُ ٱللَّهُ وَيَلۡعَنُهُمُ ٱللَّٰعِنُونَ159 إِلَّا ٱلَّذِينَ تَابُواْ وَأَصۡلَحُواْ وَبَيَّنُواْ فَأُوْلَٰٓئِكَ أَتُوبُ عَلَيۡهِمۡ وَأَنَا ٱلتَّوَّابُ ٱلرَّحِيمُ160﴾

{Lalle ne waɗanda suke ɓõyẽwar abin da Allah Ya saukar da ga hujjõji bayyanannu, da shiriya, daga bãyan Mun bayyana shi ga mutãne, a cikin Littãfi (Alƙur'ãni), waɗannan Allah Yana la'anar su, kuma mãsu la'ana suna la'anar su.

Sai waɗanda suka tũba, kuma suka gyãra, kuma suka bayyana, to waɗannan Ina karɓar tũba a kansu kuma Nĩ ne Mai karɓar tũba, Mai jin ƙai) [al-Bakara: 159, 160], Allah - Maɗaukakin sarki - Ya bayyana a cikin wannan aya mai girma: Cewa duk wanda ya ɓoye wani abu daga gaskiya ba to tubansa bai inganta ba sai bayan gyara da bayyanawa, kuma Allah - Maɗaukakin sarki - haƙiƙa Ya cika wa bayinSa addini, kuma Ya cika musu ni'ima da aiko ManzonSa (annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, da abin da Allah Ya yi wahayi zuwa gare shi na shari’a cikakkiya, kuma bai karɓe shi zuwa gare Shi ba sai bayan cikawa da bayyanawa, kamar yadda Ya ce - tsarki ya tabbatar maSa:

﴿...ٱلۡيَوۡمَ أَكۡمَلۡتُ لَكُمۡ دِينَكُمۡ وَأَتۡمَمۡتُ عَلَيۡكُمۡ نِعۡمَتِي وَرَضِيتُ لَكُمُ ٱلۡإِسۡلَٰمَ دِينٗا...﴾

{Kuma yaune Na cika muku addininku, kuma Na cika muku ni'imaTa kuma Na yarje muku musulunci a matsayin addini} [al-Ma'ida: 3]

Mai ƙirƙirar wannan wasiyya ya zo a ƙarni na goma sha huɗu, yana son ya jefa mutane cikin wani sabon addini, wanda ya sanya shiga Aljanna ga wanda ya karɓi shari'arsa, da kuma haramta Aljanna da shiga wuta ga wanda bai karɓi shari'arsa ba, Yana so ya sanya wannan wasiyyar da ya ƙirƙira ta fi Alƙur'ani girma da falala, inda ya ƙirƙira a cikinta: cewa duk wanda ya rubuta ta ya aika ta daga gari zuwa gari, ko daga wuri zuwa wuri; za a gina masa gida a Aljanna, kuma wanda bai rubuta ta ba ya aika ta, za a haramta masa ceto na Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a ranar Alƙiyama, Wannan yana daga cikin munanar ƙarya, kuma daga cikin bayyanannun dalilai akan ƙaryar wannan wasiyya, da ƙarancin kunyar wanda ya ƙirƙira ta, da girman jarumtar sa akan ƙarya; domin wanda ya rubuta Alƙur'ani mai girma kuma ya aika shi daga gari zuwa gari, ko daga wuri zuwa wuri; ba zai samu wannan falalar ba idan bai yi aiki da Alƙur'ani mai girma ba, to yaya za a samu ga wanda ya rubuta wannan ƙarya kuma ya yaɗa ta daga gari zuwa gari. Waɗanda ba su rubuta AlKur’ani ba kuma ba su aika shi daga gari zuwa gari ba, ba za a haramta musu ceto na Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - idan sun kasance masu imani da shi, masu bin shari'arsa, Da wannan ƙarya guda ɗaya a cikin wannan wasiyya, tana isa da kanta don nuna ɓatancinta da ƙaryar wanda ya yaɗa ta, da rashin kunya da wawancinsa da nisansa daga sanin abin da Manzo - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zo da shi na shiriya ba.

A dai cikin wannan wasiyyar - ban da abinda aka ambata - akwai wasu abubuwa kuma daban da suke nuna ɓacinta da kuma ƙaryarta. Da wanda ya ƙirƙireta zai rantse sau dubu ko sama da haka akan ingancinta, haka da ace zai kirawa kansa mafi girman azaba da mafi tsananin uƙuba akan cewa shi mai gaskiya ne; da ba zai zama mai gaskiya ba, ba kuma zata taɓa zama ingantacciya ba, bari dai, ita wallahi thumma wallahi tana cikin mafi girma da mafi munin ɓarna, mu kuma muna shaidawa Allah - tsarki ya tabbata a gare Shi - da duk Mala’ikun da suke tare da mu. Duk wanda ya karanta wannan rubutu daga cikin musulmai - shaida ce da za mu gabatar da ita ga Ubangijinmu - Maɗaukakin sarki -: Cewa wannan wasiyya ƙarya ce da ƙirƙira akan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - Allah Ya kunyatar da wanda ya ƙirƙireta kuma Yayi masa hukunci da abinda ya cancanta.

Bayan abinda aka ambata, al'amurra da dama a cikin abinda aka ambata a nassinta (wasiyyar) suna nuni akan ƙaryar wannan wasiyya da kuma ɓacinta, daga ciki:

Lamari na farko: Maganarsa a cikinta (Domin daga Juma’a zuwa Juma’a mutum dubu ɗari da sittin ne suka rasu ba akan addinin Musulinci ba); domin wannan yana cikin ilimin gaibu, kuma Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabata a gare shi -wahayi ya yanke masa bayan rasuwarsa, kuma a rayuwarsa bai san gaibu ba, to ya bayan mutuwarsa; saboda faɗin Allah - tsarki ya tabbata a gare Shi -:

﴿قُل لَّآ أَقُولُ لَكُمۡ عِندِي خَزَآئِنُ ٱللَّهِ وَلَآ أَعۡلَمُ ٱلۡغَيۡبَ...﴾

{Ka ce: Ba zance muku ina da taskokin Allah ba kuma ban san gaibu ba} [al-An'am: 50] Da faɗinSa - Maɗaukakin Sarki -:

﴿قُل لَّا يَعۡلَمُ مَن فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ ٱلۡغَيۡبَ إِلَّا ٱللَّهُ...﴾

{Ka ce: wanda suke sammai da ƙassai basu san gaibu ba sai Allah} [al-Naml: 65], Ya zo cikin ingantaccen hadisi daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: Ya ce: Za a kore wasu mutane daga tafkina a ranar Alƙiyama, sai in ce: Ya Ubangiji! Abokaina, abokaina, sai a ce mini: Lallai ba ka san abin da suka aikata a bayanka ba. Sai in ce kamar yadda bawan kirki ya ce: 'Kuma nã kasance mai shaida a kansu matuƙar nã dawwama a cikinsu, sa'an nan a lõkacin da Ka karɓi raina Kã kasance Kai ne mai tsaro a kansu, kuma Kai a kan dukkan kõme, Halartacce ne.' [Al-Ma'ida: 117]

Lamari na biyu: - Daga lamurran da suke nuna ɓacin wannan wasiyya da kuma cewa ita ɗin ƙage ce -: Faɗinsa a cikinta: (wanda ya rubuta ta yana talaka, Allah zai wadata shi, ko yana fama da bashi, Allah zai biya masa bashinsa, ko yana da zunubi Allah zai masa gafara da iyayen sa saboda albarkar wannan wasiyya) zuwa ƙarshenta. Wannan ma yana cikin manyan ƙarairayi, kuma dalilai sun bayyana ƙaryar wanda ya ƙirƙireta da kuma ƙarancin kunyarsa ga Allah da bayinSa; domin waɗannan lamurra uku ba sa samuwa da zarar an rubuta Alƙur'ani mai girma, to ta yaya zasu samu ga wanda ya rubuta wannan ɓataciyyar wasiyyar?! Kawai wannan mugun yana son ya yaudari mutane ne, da kuma jingina su da wannan wasiyya; har su rubuta ta kuma su jingina kansu da wannan falalar da ake iƙirari, su bar hanyoyin da Allah Ya shara'anta ga bayinSa, kuma Ya sanya su masu sadarwa zuwa ga wadatar zuci da biyan bashi, da gafarar zunubai, don haka muna neman tsari da Allah daga hanyoyin wulaƙanci da biyayya ga son zuciya da Shaiɗan.

Lamari na uku: - Daga lamurran da suke nuni akan ɓacin wannan wasiyyar -, faɗinsa a cikin wasiyyar: (wanda kuma bai rubuta ta ba cikin bayin Allah; fuskarta za ta yi baƙi a duniya da lahira). Wannan kuma yana daga cikin munanar ƙarya, kuma yana daga cikin bayyanannun hujjoji akan ɓacin wannan wasiyyar, da kuma ƙaryar wanda ya ƙirƙireta, ta yaya zai yiwu a hankalin mai hankali ya rubuta wannan wasiyyar da wani mutum wanda ba’a san shi ba a ƙarni na goma sha huɗu yazo da ita, yana ƙirƙirar ta ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - kuma yana da'awar cewa wanda bai rubuta ta ba fuskarsa za ta yi baƙi a duniya da lahira, kuma wanda ya rubuta ta zai zama mai arziƙi bayan talauci, kuma zai tsira daga bashi bayan ya taru a kansa, kuma za a gafarta masa abin da ya aikata na zunubai!!

Tsarki ya tabbata gareka! wannan ƙarya ce babba!! Lallai hujjoji na gaskiya suna shaidawa da ƙaryar wannan maƙaryaci, da girman ƙarfin zuciyarsa akan Allah, da ƙarancin kunyarsa ga Allah da mutane, ga waɗannan al'ummai masu yawa ba su rubuta ta ba, fuskarsu ba ta yi baƙi ba, kuma ga wannan taro mai yawa wanda babu mai ƙirga su sai Allah sun rubuta ta sau da yawa, amma ba a biya basussukansu ba, kuma talaucinsu bai gushe ba, muna neman tsarin Allah ga karkacewar zukata, da ɓarnar zunubai, Waɗannan siffofi da sakamakon shari'a mai daraja ba ta zo da su ba ga wanda ya rubuta mafi kyawun littafi kuma mafi girma wato Alƙur'ani mai girma, to yaya zasu samu ga wanda ya rubuta wasiyya ta ƙarya mai ɗauke da nau'o'in ƙarya, da jimloli masu yawa daga nau'o'in kafirci, tsarki ya tabbata ga Allah!! Ya mamakin haƙurinSa ga wanda Yayi masa ƙarya.

Lamari na huɗu: - Daga lamurran da suke nuni akan cewa wannan wasiyyar tana daga mafi girman ɓarna, kuma mafi bayyanar ƙarya -: Faɗinsa a cikinta (wanda kuma gasgata ta to zai tsira daga azabar wuta, wanda kuma ya ƙaryata ta ya kafirta), Wannan - kuma - yana daga cikin mafi girman jarumtar yin ƙarya, da kuma mafi munin ɓata, wannan maƙaryaci yana kiran dukkan mutane, da su gaskata da ƙaryarsa, yana iƙirarin cewa da hakan za su tsira daga azabar wuta, kuma cewa duk wanda ya ƙaryata ta zai kafirta, Haƙiƙa - Wallahi- wannan maƙaryacin ya yi ƙage mai girma ga Allah, kuma - Wallahi - ya faɗi abinda ba gaskiya ba ne. Lalle wanda ya gasgata ta shi ne wanda ya cancanci ya kasance kafiri ba wai wanda ya ƙaryata ta ba; domin ita (wasiyyar) fa ƙage ce kuma ɓarna ce kuma ƙarya ce da ba ta da tushe na inganci. Kuma mu muna shaidawa Allah akan cewa wasiyyar ƙarya ce, kuma wanda ya ƙirƙire ta maƙaryaci ne, yana son ya shar’anta wa mutane ne abinda Allah bai yi izini ba. Ya shigar musu abinda baya cikin addininsu, kuma haƙiƙa Allah Ya cika addinin, Ya kuma cika shi ga wannan al’ummar tun kafin wannan ƙirƙiren da ƙarni goma sha huɗu. Ku faɗaka: Ya ku masu karatu da ‘yan uwa, kada ku kuskura ku gasgata irin waɗannan ƙirkire-ƙirƙiren, kada a samu masu rurutata a cikinku, domin ita gaskiya tana da haske ba ya rikicewa mai nemanta, ku nemi gaskiya da dalilinta, ku tambayi malamai akan abinda ya shige muku duhu, kada ku ruɗu da rantsuwar maƙaryata. Haƙiƙa shaiɗan la’ananne ya rantsewa iyayenku (Annabi) Adamu da (Nana) Hauwa'u akan cewar shi mai nasiha ne a gare su, alhali kuwa shine ne mafi girman maha’inta kuma mafi ƙaryar maƙaryata, kamar yadda Allah Ya hakaito hakan daga gare shi, sai (Allah) - Mai tsarki da ɗaukaka - Ya ce:

﴿وَقَاسَمَهُمَآ إِنِّي لَكُمَا لَمِنَ ٱلنَّٰصِحِينَ21﴾

{Kuma ya yi musu rantsuwa; Lalle ne nĩ, a gare ku, haƙĩƙa, daga mãsu nasĩha ne} [al-A'araf: 21]. Ku kiyaye shi, ku kiyayi mabiyansa daga masu ƙirƙire-ƙirƙire, sau nawa shi da su suke ta rantse-rantse na ƙarya da alƙawura na yaudara da maganganu da aka ƙawata, domin ruɗarwa da ɓatarwa! Amma abinda wannan me ƙirƙiren ya ambata na bayyanar munanan abubuwa; to wannan al’amari ne da yake a waƙi'i, Alƙur'ani mai girma da Sunnah mai tsarki tabbas sun tsawatar a kansu matuƙar tsawatarwa, kuma a cikinsu ne (Alƙur’ani da Sunnah) shiriya take da kuma wadatarwa.

Amma abinda ya anbata na alamomi alƙiyama, to haƙiƙa hadisai sun yi bayani dalla dalla na abinda zai kasance na alamomin alƙiyama, kuma Alƙur'ani mai girma ya yi nuni akan wasu daga ciki, duk wanda yake son ya san haka zai same shi a mahallinsa a cikin littattafan Sunnah, da littattafan ma'abota ilimi da imani, mutane ba su da buƙatar bayanin irin wannan me ƙirƙiren ƙaryar da kuma ruɗarwarsa da yadda ya cuɗa gaskiya da ƙarya. Allah Ya tsare ni Ya tsare ku da sauran musulmai daga sharrin shaiɗanu, da fitinar masu ɓatarwa, da karkacewar karkatattu, da ruɗarwar maƙiya Allah maɓarnata, waɗanda suke son su bice hasken Allah da bakunansu, su rikitarwa mutane addinin su, alhali kuwa Allah Mai cika haskenSa ne, kuma Mai taimakon addininSa ne, koda kuwa maƙiya Allah sun ƙi daga cikin shaiɗanu da mabiyansu cikin kafirai da mulhidai. Muna roƙon Allah Ya kyautata halayan musulmai, Ya kuma yi musu baiwa da bin gaskiya da kuma tsayuwa a kanta, da kuma tuba ga Allah - tsarki ya tabbata a gare Shi - daga sauran zunubai, domin Shi Mai yawan karɓar tuba ne, kuma Mai yawan jin ƙai ne, kuma Mai iko ne akan dukkan komai. Kuma Allah Ya isar mana, kuma madalla da Wakili, babu dabara babu ƙarfi face da (nufin) Allah Maɗaukaki Mai girma.

Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, tsira da amincin Allah su tabbata ga bawanSa kuma ManzonSa mai gaskiya amintacce, da alayensa da sahabbansa da mabiyansa da kyautatawa har zuwa ranar sakamako.

 

***