PHPWord

 

 

مِنْ أَحْكَامِ الصِّيَامِ

 

 

Daga Hukunce-Hukuncen Azumi

 

 

اللَّجْنَةُ العِلْمِيَّةُ

بِرِئَاسَةِ الشُّؤُونِ الدِّينِيَّةِ بِالمَسْجِدِ الحَرَامِ وَالمَسْجِدِ النَّبَوِيِّ

 

Kwamitin ilimi a jagorancin harkokin addini a Masallacin Harami da Masallacin Annabi

 

 


بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ

Daga Hukunce-Hukuncen Azumi

MABHASI NA FARKO

Ma'anar azumi, da kuma wajibcin azumin Ramadan

Na farko: Ma'anar azumi:

Azumi shi ne: Ibada ga Allah - Maɗaukakin Sarki - ta hanyar kamewa daga abubuwa masu karya azumi, tun daga ɓullowar alfijir har zuwa faɗuwar rana.

Na biyu: Wajibcin azumin Ramadan:

Azumin watan Ramadan rukuni ne daga rukunan Musulunci, waɗanda addinin Musulunci ba ya tsayuwa sai da su. Kuma azumi farilla ne akan dukkanin al'ummatai, koda yake kaifiyyar sa da lokacin sa sun sha banban; kamar yadda Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ كُتِبَ عَلَيۡكُمُ ٱلصِّيَامُ كَمَا كُتِبَ عَلَى ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِكُمۡ لَعَلَّكُمۡ تَتَّقُونَ 183

{Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! An wajabta azumi a kanku kamar yadda aka wajabta shi a kan waɗanda suke daga gabãninku, tsammãninku, zã ku yi taƙawa} (al-Baƙarah:183), (Kutiba) ma'ana an farlanta.

Haƙiƙa Alƙur'ani da sunnah da ijma'i (na malamai) sun yi nuni akan wajibcin sa:

• Amma Alƙur'ani: to faɗin Sa - Maɗaukakin Sarki -:

﴿يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ كُتِبَ عَلَيۡكُمُ ٱلصِّيَامُ كَمَا كُتِبَ عَلَى ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِكُمۡ لَعَلَّكُمۡ تَتَّقُونَ 183 أَيَّامٗا مَّعۡدُودَٰتٖ...

{Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! An wajabta azumi a kanku kamar yadda aka wajabta shi a kan waɗanda suke daga gabãninku, tsammãninku, zã ku yi taƙawa}

{Kwanuka ne ƙidãyayyu} (al-Baƙarah:183-184).

• Amma sunnah: to faɗin sa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: «An gina Musulunci akan abubuwa biyar: Shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma lalle (Annabi) Muhammad Manzon Allah ne, da tsaida sallah, da bada zakkah, da azumin Ramadan, da Hajjin ɗaki »1.

• Amma ijma'i: Haƙiƙa musulmai sun haɗu akan wajibcin azumtar azumin Ramadan, kuma lalle wanda ya yi musun wajibcin azumtar sa, to shi kafiri ne.

MABHASI NA BIYU

Falalolin watan Ramadan

Akwai darajoji masu girma da faloli ga wannan wata mai girma, da suka banbanta shi da sauran watanni, daga cikin su:

1) Saukar da Alƙur'ani mai girma a cikin sa, kamar yadda Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿شَهۡرُ رَمَضَانَ ٱلَّذِيٓ أُنزِلَ فِيهِ ٱلۡقُرۡءَانُ...

{Watan Ramalãna ne wanda aka saukar da Alƙur'ãni a cikinsa} (al-Baƙarah: 185).

2) Cewa lalle ana buɗe ƙofofin aljannah; wannan kuma saboda yawan ayyuka na gari ne a cikin sa.

3) Kulle ƙofofin wuta a wannan watan; wannan kuma saboda ƙarancin saɓo.

Haƙiƙa wannan ya zo a cikin faɗin sa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: «Idan Ramadan ya zo za'a buɗe ƙofofin aljannah, kuma a rufe ƙofofin wuta, kuma a ɗaure shaiɗanu»2.

4) Daga cikin falalolin sa kuma: faɗin sa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: «Babu wani kyakkyawan aiki da ɗan Adam zai aikata face an rubuta masa kyawawa goma zuwa ninki ɗari bakwai, Allah Ya ce: Sai fa azumi domin shi Nawa ne, kuma Ni zan yi sakayya da shi, zai bar sha'awar sa da abincin sa saboda Ni. Azumi garkuwa ne, kuma mai azumi yana da farin ciki biyu: Farin ciki a yayin buɗa bakin sa da farin ciki a yayin haɗuwa da Ubangijin sa, kuma lalle bashin bakin mai azumi yafi daɗi a wurin Allah fiye da ƙamshin almiski».3 Don haka, (ladan) ninkuwar azumi ba ya taƙaituwa da wani adadi.

5) Cewa ikhlasi a azumi ya fi yawa daga shi fiye da wanin sa; saboda faɗinSa: «Ya bar sha'awar sa da abincin sa sasboda Ni»4.

6) Cewa Allah Ya keɓanci wata ƙofa ga masu azumi daga ƙofofin aljannah, ita ce Arrayyan, wasunsu ba zasu shiga ta ƙofar ba.

7) Cewa akwai wata addu'a karɓaɓɓiya ga mai azumi; saboda faɗin sa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: «Akwai wata addu'ah ga mai azumi a lokacin buɗa bakin sa da ba'a juyarwa»5.

8) Faɗinsa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: «Wanda ya azumumci Ramadan yana mai imani da neman lada, za'a gafarta masa abinda ya gabata na zunuban sa»6.

To ya cancanta ga musulmi ya azumce shi da imani da kuma neman lada, har ya sami lada da gafarar zunubai.

 


MABHASI NA UKU

Abinda shigar watan Ramadan yake tabbatuwa da shi

Shigar watan Ramadan yana tabbatuwa da ɗaya daga al'amurra biyu:

1) Da ganin jinjirin wata (na Ramadan); saboda faɗinsa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: «Idan kunga jinjirin wata, to ku yi azumi, idan kuma kun gan shi (watan Shawwal), to ku yi buɗa baki (ƙaramar sallah). idan watan ya ɓoye muku, to ku ƙaddara (kwanukansa)»7, da kuma faɗinsa: «Kada ku yi azumi har sai kun ga jinjirin wata, kada kuma ku yi buɗa baki har sai kun gan shi (watan Shawwal)»8.

2) Idan ba su ga jinijirin wata ba, su cika ƙirgen watan Sha'aban kwana talatin; saboda faɗinsa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: «Wata dare ashirin da tara ne, kada ku yi azumi har sai kun gan shi, idan ya ɓuyar muku, to ku cika ƙirgen (kwana) talatin»9.

 

MABHASI NA HUƊU

Niyyah a azumi

Niyyah sharaɗi ce ga ingancin kowane aiki, babu makawa sai mai Azumi ya yi niyyar azumin Ramadan da daddare; saboda faɗinsa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: «Duk wanda bai kwana da niyyar azumi ba kafin alfijir, to ba shi da azumi»10.

Shaikhul Islam ibn Taimiyyah - Allah Ya yi masa rahma - ya ce: "Duk wanda ya san cewa gobe ne Ramadan, kuma yana da niyyar azumtar sa, to haƙiƙa ya yi niyyar azumin sa, daidai ne ya furta niyyar, ko bai furta ba, wannan kuwa shi ne aikin gabaɗayan musulmai, dukkan su suna yin niyyar azumi"11.

MABHASI NA BIYAR

Akan wa azumi yake wajaba?

Azumi yana wajaba akan dukkan: Musulmi, baligi, mai hankali.

Idan ya kasance mai lafiya mazaunin gida: Yinsa a kan lokaci yana wajaba. Idan ya kasance mara lafiya ne (sai ya ajiye): To rama shi yana wajaba.

Idan kuma ya kasance mai lafiya ne matafiyi: An ba shi zaɓi tsakanin azumi ko ajiyewa, amma ajiyewar ita ta fi falala.

• Azumi ba ya wajaba akan kafiri, kuma ba ya inganta daga gare shi, idan ya tuba a tsakiyar watan, zai azumci sauran kwanakin, kuma ba zai rama abinda ya wuce a lokacin yana kafirci ba.

• Kuma ba ya wajaba akan yaro ƙarami, yana inganta daga yaro mai iya bambance abubuwa, kuma zai zama nafila ne a haƙƙin sa.

• Kuma ba ya wajaba akan mahaukaci, ko da ya yi azumin a lokacin haukan sa, to azumin bai inganta daga gare shi ba: saboda rashin niyya.

MABHASI NA SHIDA

Suwa ake wa uzurin barin azumi?

Ana yin uzuri na barin azumi a watan Ramadan ga:

1) Mara lafiyan da azumi zai masa wahala, to an so ya sha azumi.

2) Matafiyin da (watan) Ramadan ya kama alhali yana kan tafiya, ko ya fara tafiya a tsakiyar watan da tafiyar sa ta kai kilomita tamanin ko sama da haka.

3) Mai al’ada da biƙi azumi yana haramta a kansu a lokacin (jinin) hailar da biƙin: saboda faɗin Nana Aisha - Allah Ya yarda da ita -: «Hakan yana samun mu (jinin al’ada da biƙi), sai a umarce mu da rama azumi, amma ba'a umartar mu da rama sallah»12.

4) Mara lafiya, rashin lafiyar da ke da wuyar magani da aka yanke ƙaunar warakar sa, kuma yake wahalar da shi daga yin azumin, wahalarwa mai ɗorewa to wannan zai sha azumi kuma zai ciyar da miskini ɗaya rabin sa'i na alkama ko wanin ta a madadin kowace rana, kuma babu ramuwa a kansa.

5) Tsoho gajiyayye da ba ya iya yin azumi, to zai sha azumi, zai ciyar da miskini ɗaya ga kowace rana, kuma babu ramuwa a kansa.

6) Mai ciki da mai shayarwa idan sun ji tsoro ga kawunan su ko ga ɗansu daga cutuwar azumin, to zasu sha azumin kuma su rama. Idan shan azumin nasu ya kasance saboda tsoro ne ga ɗansu kaɗai, to lalle zasu rama kuma zasu ciyar da miskini a madadin kowace rana.

MABHASI NA BAKWAI

Abubuwan da Suke ɓata azumi:

1-Jima'i:

Wanda ya yi jima'i a tsakar rana a Ramadan azumin sa ya ɓaci, kuma kamewa ya wajaba a kansa a ragowar yinin, kuma akwai tuba a kansa da neman gafara. Zai rama wannan yinin da ya yi jima'in a cikin sa, kuma akwai kaffara a kansa. Ita ce: 'Yanta wuyaye, idan bai samu ba to ya yi azumin watanni biyu a jere, idan bai da ikon yin azumin watanni biyu a jere, to sai ya ciyar da miskinai sittin, ga kowanne miskini rabin sa'i na alkama ko waninta daga abinda yake kasancewa abincin garin.

2) fitar da maniyyi saboda sumbata ko runguma ko istimna'i ko maimaita kallo:

Idan mai azumin ya yi inzali saboda ɗaya daga waɗannan sabubban, to azumin sa ya ɓaci, kuma akwai kamewa a kansa, kuma zai rama azumin wannan ranar amma babu kaffara a kansa. Sai dai akwai tuba da nadama da neman gafara a kansa, da kuma nisanta daga waɗannan abubuwan masu tada sha'awah; domin yana cikin ibada mai girma.

3) Ci da sha da gangan.

4- Fitar da jini daga mai azumi, saboda ƙaho ko tsaga jijiya ko janyo jini don bayarwa.

Asalin wannan shine faɗinsa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a (sha'anin) ƙaho: «Mai yin ƙaho da wanda aka yiwa sun karya azumi»13.

Shaikhul Islam Ibn Taymiyyah - Allah Yayi masa rahma - ya ce: " Zancen cewa ƙaho yana karya azumi shi ne mazhabar mafi yawancin malaman Hadisi; kamar Ahmad bn Hambal da Ishaƙ bn Rahuwaihi da Ibn Khuzaimah da ibn al-Munzhir, da wasun su"14.

Amma fitar jini daga mai azumi ba tare da nufi ba kamar haɓo, da jinin rauni, da cire haƙori da makamantan sa, to ba ya shafar azumi.

5- ƙaƙaro amai:

Shi ne fitar da abinda yake cikin uwar hanji na daga abinci ko abin sha ta baki da gangan, amma idan amai ne ya rinjaye shi ya fita ba tare da zaɓin sa ba, to ba ya shafar azumin sa; saboda faɗinsa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: «Wanda amai ya rinjaye shi to babu ramuwa a kansa, wanda kuma ya ƙaƙaro amai to sai ya rama»15. Ma'anar 'zara'ahu': Ya rinjaye shi.

MABHASI NA TAKWAS

Mustahabban azumi

1) Sahur; saboda Hadisin Anas dan Malik - Allah Ya yarda da shi - cewa ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Ku yi sahur; domin a cikin sahur akwai albarka»16.

2/ Jinkirta sahur; muddin dai bai ji tsoron ɓullowar alfijir ba.

3) Gaggauta buɗa baki, idan faɗuwar rana Ta tabbata. Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Al'umma ta ba zata gushe cikin alkhairi ba, muddin dai sun jinkirta sahur kuma sun gaggauta buɗa baki»17.

4) An so a yi buɗa baki da ɗanyen dabino, idan ba'a samu ba, to da busasshen dabino, idan ba'a samu ba, to da ruwa; saboda faɗin Anas - Allah Ya yarda da shi -: «Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana buɗa baki da ɗanyun dabinai kafin a yi sallah, idan babu ɗanyun dabinai, to da busasshun dabinai, idan babu to sai ya kurɓi 'yan kurɓe na ruwa»18.

5) An so ga mai azumi ya yi addu'a a yayin buɗa bakin sa da abinda yake so, Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Lalle akwai addu'a ga mai azumi a yayin buɗa bakin sa da ba a juyarwa da ita»19.

6) Yawaita dukkan nau'ikan ibadah; kamar karatun Alƙur'ani, ambaton Allah, tsayuwar dare, sallar Tarawihi da sunnoni ratibai, sadaka da bayarwa a tafarkin alheri; domin kyawawa suna share munana.

MABHASI NA TARA

Faɗakarwa

• Yana wajaba ga mai azumi ya nisanci ƙarya da giba da aibatawa, idan wani ya zage shi ko ya aibata shi, to ya ce: "Lalle ni mai azumi ne".

Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce -: «Azumi garkuwa ne, kada (mai azumi) ya yi batsa kuma kada ya yi jahilci. Idan mutum ya yaƙe shi ko ya aibata shi, to ya ce: "Lalle ni mai azumi ne, sau biyu"20.

• Daga abinda aka hana mai azumi: Kaiwa matuƙa a kurkurar baki da shaƙa ruwa; domin zai yi wu ruwa ya tafi zuwa cikin sa.

Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Kuma Ka kai matuƙa a shaƙa ruwa (lokacin alwalla), sai dai in Ka kasance mai azumi ne»21.

• Asuwaki ba ya shafar azumi, bari ma dai mustahabbi ne kuma abin kwaɗaitarwa ne ga mai azumi da waninsa a farkon yini da kuma ƙarshen sa akan zance mafi inganci.

MABHASI NA GOMA

Ramuwar Ramadan

Wanda ya sha azumi a Ramadan saboda dalili halastacce, kamar uzururruka na shari'ah waɗanda suke halasta ajiye azumi, ko saboda abin da aka haramta, kamar wanda ya ɓata azumin sa saboda yin jima'i ko waninsa, to ramuwa ta wajaba a kansa; saboda fadinSa Allah - Maɗaukakin sarki -:

﴿...فَعِدَّةٞ مِّنۡ أَيَّامٍ أُخَرَ...

{Sai (ya biya) adadi daga wasu kwanuka na daban} (al-Baƙarah: 184). Kuma an so gare shi ya gaggauta ramuwar; saboda sauke abinda ke a kansa (na ramuwar), kuma an so ramuwar ta kasance a jere; domin ramuwa tana kwaikwayar Ada'i ne( yin azumin a cikin watan Ramadan). Jinkirtawa kuma ta halasta a gare shi; domin lokacin ta yalwatacce ne.

Kamar yadda ya halasta a gare shi ya rama a rarrabe, sai dai idan babu abinda ya rage a sha'aban sai abinda ke a kansa, to lalle ya wajaba ya yi a jere a ijma'i (na malamai); saboda ƙarancin lokacin, kuma jinkirta shi zuwa bayan wani Ramadan ɗin na daban ba ya halasta idan babu wani uzuri.

• To wanda ya jinkirta ramuwa har zuwa ƙarshen Ramadan na gaba, to yana da halaye biyu:

Ya jinkirta saboda wani uzuri na shari'ah, misali: Rashin lafiya ta zarce da shi har zuwa wani Ramadan ɗin na daban, to wannnan ramuwa ce kawai a kansa.

Ya jinkirta shi ba tare da wani uzuri na shari'ah ba, to wannan akwai ramuwa a kansa tare da ciyar da miskini ɗaya rabin sa'i na abincin garin ga kowace rana.

• Azumin taɗawwu'i ga wanda akwai ramuwa a kansa: Wanda ya kasance akwai ramuwar wani abu na Ramadan a kansa, to abinda ya fi shine ya yi gaggawar yin sa kafin azumin taɗawwu'in, sai dai idan azumin nafilan ya kasance daga wanda lokacin sa zai wuce ne kamar (azumin) Arfah da Āshurah, to ya yi azumin kafin na ramuwar; domin lokacin ramuwa yalwatacce ne, amma Āshurah da Arfah yana wucewa, sai dai ba zai yi azumin kwana shida na Shawwal ba har sai bayan (ya yi) na ramuwa.

Wannan shi ne abinda tara shi ya sawwaƙa, Allah Ya yi Salati da aminci ga Annabinmu Muhammad da alayen sa da sahabban sa kuma Ya yi aminci, aminci mai yawa.

 

 

***

Teburin bayani

 

MABHASI NA FARKO 2

Ma'anar azumi, da kuma wajibcin azumin Ramadan 2

MABHASI NA BIYU 3

Falalolin watan Ramadan 3

MABHASI NA UKU 6

Abinda shigar watan Ramadan yake tabbatuwa da shi 6

MABHASI NA HUƊU 7

Niyyah a azumi 7

MABHASI NA BIYAR 7

Akan wa azumi yake wajaba? 7

MABHASI NA SHIDA 8

Suwa ake wa uzurin barin azumi? 8

MABHASI NA BAKWAI 9

Abubuwan da Suke ɓata azumi: 9

MABHASI NA TAKWAS 11

Mustahabban azumi 11

MABHASI NA TARA 12

Faɗakarwa 12

MABHASI NA GOMA 13

Ramuwar Ramadan 13

***

ha419v1.0 - 22/02/2026


An haɗu a kansa, al-Bukhari ne ya fitar da shi a lamba ta 1898 (3/25), da Muslim a lamba ta 1079 (2/758).

Al-Nasa'i ne ya fitar da shi cikin al-Kubrah a lamba ta 2536 (3/131).

Duba takhrijin da ya gabata.

Ibn Majah ne ya fitar da shi a lamba ta 1753 (1/775).

An haɗu a kansa, al-Bukhari ya fitar da shi a lamba ta 38 (1/16), da Muslim a lamba ta 760 (1/523).

Al-Imam Ahmad ne ya fitar da shi a Musnad a lamba ta 6323 (10/402), da al-Nasa'i a al-Kubrah a lamba ta 2446 (3/102).

An haɗu a kansa, al-Bukhari ne ya fitar da shi a lamba ta 1906 (3/27), da Muslim a lamba ta 1080 (2/759).

An haɗu a kansa, al-Bukhari ne ya fitar da shi a lamba ta 1907 (3/27), da Muslim a lamba ta 1081 (2/762)0

Al-Nasa'i ne ya fitar da shi a al-Kubrah a lamba ta 2652 (3/170).

Al-Fatawah al-Kubrah (2/469).

Muslim ne ya fitar da shi a Sahihin sa, a lamba ta 335 (1/265)0

Al-Bukhari ne ya fitar da shi a lamba ta 1937 (3/33), da Ahmad a Musnad ɗinsa a lamba ta 26217 (43/278).

Majmu al-Fatawah (25/252).

Imam Ahmad ne ya fitar da shi a Musnad ɗinsa a lamba ta 10463 (16/283), da al-Tirmizi a al-Jami'ul Kabir a lamba ta 720 (2/91).

An haɗu a kansa, al-Bukhari ne ya fitar da shi a lamba ta 1923 (3/29), da Muslim a lamba ta 1095 (2/770).

Ahmad ne ya fitar da shi a Musnad ɗinsa a lamba ta 12507 (35/399).

Abu Dawud ne ya fitar da shi a lamba ta 2356 (2/306).

Ibn Majah ne ya fitar da shi a lamba ta 1753 (1/775).

Bukhari ne ya fitar da shi a lamba ta 1894 (3/24).

Abu Dawud ne ya fitar da shi a lamba ta 2366 (2/308), da al-Tirmizi a al-Jami'ul Kabir a lamba ta 788 (2/147).

An haɗu a kansa, al-Bukhari ne ya fitar da shi a lamba ta 8(1/11), da Muslim a lamba ta 16 (1/34).