مَا لَا يَسَعُ المُسْلِمَ جَهْلُهُ
ABINDA BA ZAI YI WU MUSULMI YA JAHILCE SHI BA
اللَّجْنَةُ العِلْمِيَّةُ
بِرِئَاسَةِ الشُّؤُونِ الدِّينِيَّةِ بِالمَسْجِدِ الحَرَامِ وَالمَسْجِدِ النَّبَوِيِّ
Kwamitin ilimi a jagorancin harkokin addini a Masallacin Harami da Masallacin Annabi
بِسْمِ اللهِ الرَّحمَنِ الرَّحِيمِ
ABINDA BA ZAI YI WU MUSULMI YA JAHILCE SHI BA
GABATARWA
Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, tsira da aminci su tabbata ga wanda aka aiko domin rahama ga talikai, da alayensa da sahabbansa da waɗanda suka yi koyi da shi, suka shiryu da shiriyarsa, har zuwa ranar sakamako. Bayan haka:
Wannan wani takaitaccen sako ne, da ya ƙunshi muhimman abubuwan da musulmi yake bukata a imaninsa da ibadarsa da mu’amalolinsa. Mun tattaro su ne domin masu ziyarar Masallatai biyu masu alfarma maza da mata, domin su sami ilimi da fahimtar al’amuran addininsu.
Muna fatan (Allah) Mai karamci da baiwa Ya amfanar da shi, Ya kuma sanya shi ingatacce, kuma da ikhlasi saboda Shi. Shi ne mafificin abin roko, kuma mafi karamcin abin fata.
Kwamitin ilimi wanda harkokin addini a Masallacin Harami da Masallacin Annabi ke jagoranta.
Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin ƙai
***
FASALI NA FARKO:
ABINDA YAKE DA ALAKA DA AKIDA
Bincike na farko: Ma'anar musulunci da rukunansa:
Musulunci: Shi ne: Miƙa wuya ga Allah da kadaita shi da jawuwa agareShi da biyayya, da kuma barranta daga shirka da ma'abotanta.
Rukunansa biyar ne:
Na farko: Shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma cewa (Annabi) Muhammad manzon Allah ne.
Na biyu: Tsaida sallah.
Na uku: Bada zakka.
Na huɗu: Azimtar Ramadan
Na biyar: ziyartar ɗakin Allah mai alfarma ga wanda ya samu ikon zuwa gare shi (Hajji).
Muhimmancin Tauhidi (kadaita Allah):
Ka sani cewa Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya halicci halittu domin su bauta maSa, kuma kada su hada Shi da wani abu. Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce:
﴿وَمَا خَلَقۡتُ ٱلۡجِنَّ وَٱلۡإِنسَ إِلَّا لِيَعۡبُدُونِ 56﴾
{Kuma Ban halicci aljannu da mutãne ba sai dõmin su bauta Mini. 56} [Al-Zariyat: 56], wannan bautar saninta ba ya yi wu wa sai da ilimi, Kamar yadda Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce:
﴿فَٱعۡلَمۡ أَنَّهُۥ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا ٱللَّهُ وَٱسۡتَغۡفِرۡ لِذَنۢبِكَ وَلِلۡمُؤۡمِنِينَ وَٱلۡمُؤۡمِنَٰتِۗ وَٱللَّهُ يَعۡلَمُ مُتَقَلَّبَكُمۡ وَمَثۡوَىٰكُمۡ 19﴾
{Sabõda haka ka sani, cẽwa bãbu abin bautãwa fãce Allah, kuma ka nẽmi gãfara ga zunubin, ka, kuma (nemi gafara) ga mũminai maza da mũminai mãtã, kuma Allah Ya san majũyaiku da mazauninku.19} [Muhammad: 19], Sai Ya fara da ilimi kafin faɗa da aiki. Mafi muhimmancin abinda ke kan musulmi ya koya, shi ne kaɗaita Allah - Mai girma da ɗaukaka - da ibada; domin cewa shi ne asalin addini kuma tushensa, Addini ba ya tabbatuwa sai da tauhidi, wannan shi ne farkon wajibi akan musulmi, kuma shi ne ƙarshen wajibi. Tauhidi shi ne rukuni na farko a cikin rukunan musulunci, waɗanda saninsu da aiki da su yake wajaba akan kowanne musulmi, su ne rukunai biyar, kamar yad da ya zo a cikin hadisin Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: na ji manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "An gina musulunci a kan abubuwa biyar: Shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma (Annabi) Muhammad manzon Allah ne, da tsaida sallah, da bada zakka, da ziyartar ɗaki (Hajji), da azumin Ramadan".1
To, yana wajaba akan musulmi sanin ma'anar tauhidi; shi ne kaɗaita Allah da bauta, kada ya hada wani tare da Shi a cikin bautarSa; ba wani mala'ika makusanci ba, ba kuma wani Annabin da aka aiko ba.
Ma’anar "Shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah":
Shi ne bawa ya tabbatar da ƙudiri yankakke (a zuciyarsa) cewa, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah - Mai girma da ɗaukaka -, sai ya bautawa Allah Shi kaɗai, kuma ya keɓance shi - tsarki ya tabbatar maSa da dukkanin nau'ikan ibadu; na addu'a da tsoro da fata da dogaro da wanin hakan.
kuma kalmar shahada ba ta tabbata sai da rukunai biyu:
Na farko: kore Allantaka da bauta daga wanin Allah; na dukkan kishiyoyi da alloli da ɗagutai.
Na biyu: Tabbatar da Allantaka, da bauta ta gaskiya ga Allah Shi kaɗai banda waninSa, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce:
﴿وَلَقَدۡ بَعَثۡنَا فِي كُلِّ أُمَّةٖ رَّسُولًا أَنِ ٱعۡبُدُواْ ٱللَّهَ وَٱجۡتَنِبُواْ ٱلطَّٰغُوتَ...﴾
{Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun aika a cikin kõwace al'umma da wani Manzo (ya ce): "Ku bauta wa Allah, kuma ku nĩsanci ɗãgũtu."} [al-Nahl: 36].
Amma sharuɗɗan (babu abin bautawa dagaskiya sai Allah) to su ne:
Na farko: Ilimi mai kore jahilci.
Na biyu: Sakankancewa mai kore shakku.
Na uku: Ikhlasi (tsakake aiki ga Allah) mai kore shirka.
Na huɗu: Gaskiya mai kore ƙarya.
Na biyar: Soyayya mai kore ƙiyayya.
Na shida: Jawuwa mai kore bari.
Na bakwai: Karɓa mai kore juyarwa.
Na takwas: Kafircewa da abinda ake bautawa, wanda ba Allah - Maɗaukakin Sarki-ba.
Waɗannan sharuɗɗan aiki da su yana wajaba, haƙiƙa an tattarosu a cikin baituka biyun nan masu zuwa:
Sani, yaƙini da ikhlasi da gaskiyarka tare da *** soyayya da jawuwa da karɓarsu.
An ƙara na takwas ɗinsu, kafircewarka ga abinda *** ba Allah ba, daga abubuwan da aka allantar da su.
Tabbatar da Kalmar shahada, yana kasancewa ne da bautar Allah - Maɗaukakin Sarki - Shi kaɗai, ba Shi da abokin tarayya, da tsarkake bauta ga Allah Shi kaɗai. kada ya bautawa kowa sai Allah, kada ya dogara ga kowa sai ga Allah, kada ya ƙaunaci (wani abu daga wani) sai Allah, kada ya yi sallah sai ga Allah, kada ya yi yanka sai ga Allah - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka -.
Abinda wasu daga mutane suke aikatawa na ɗawafi (kewayawa) a ƙaburbura da neman taimakon ma'abotansu (ƙaburbura) da roƙonsu, koma bayan Allah; shirka ne a cikin bauta, to kiyayewa daga hakan yana wajaba, da kuma gargaɗarwa daga gare shi; domin cewa wannan yana daga jinsin abinda mushrikai suke aikatawa, na bautar gumaka da duwatsu da bishiyoyi koma bayan Allah - Maɗaukakin sarki -, Ita ce shirkar da aka saukar da littattafai kuma aka aiko manzanni don gargaɗarwa a gare ta, da kuma hani a kanta.
Ma'anar shaidawa cewa (Annabi) Muhammad manzon Allah ne:
Yi masa biyayya a cikin abinda ya yi umarni, da gasgata shi a abinda ya bada labari, da nisantar abinda ya yi hani a gare shi ya kuma tsawatar, kuma kada a butawa Allah sai da abinda Ya shara'anta, Sai musulmi ya tabbatar da cewa, (Annabi) Muhammad ɗan Abdullahi Baƙuraishe Bahashime: Manzon Allah ne - Mai girma da ɗaukaka - zuwa ga dukkan halitta; aljanu da mutane. Kamar yadda Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:
﴿قُلۡ يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ إِنِّي رَسُولُ ٱللَّهِ إِلَيۡكُمۡ جَمِيعًا...﴾
{Ka ce: "Yã kũ mutãne! Lalle ne nĩ manzon Allah ne, zuwa gare ku, gabã ɗaya...} [al-A'araf: 158].
Kuma cewa Allah Ya aiko shi dan isar da addininSa da shiryar da halitta, Kamar yadda Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:
﴿وَمَآ أَرۡسَلۡنَٰكَ إِلَّا كَآفَّةٗ لِّلنَّاسِ بَشِيرٗا وَنَذِيرٗا وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يَعۡلَمُونَ28﴾
{Kuma ba Mu aika ka ba fãce zuwa ga mutãne gabã ɗaya, kanã mai bãyar da bushãra kuma mai gargaɗi, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba. 28} [Saba'i: 28]. Kuma kamar yan da Maɗaukakin sarki Ya ce:
﴿وَمَآ أَرۡسَلۡنَٰكَ إِلَّا رَحۡمَةٗ لِّلۡعَٰلَمِينَ 107﴾
{Kuma ba Mu aike ka ba fãce dõmin wata rahama ga talikai. 107} [al-Anbiyaa: 107].
Abinda wannan shahadar take hukuntawa: Kada ka ƙudirce cewa manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana da wani haƙƙi a cikin Rububiyya, da tasarrufi a cikin halitta, ko wani haƙƙi a cikin bauta, bari dai, shi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - bawa ne, ba'a bauta masa, kuma manzo ne, ba'a ƙaryata shi, kuma ba ya mallakawa kansa ko waninsa wani abu na anfani da cuta ba, sai abinda Allah Ya ya ga dama, Kamar yadda Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:
﴿قُل لَّآ أَقُولُ لَكُمۡ عِندِي خَزَآئِنُ ٱللَّهِ وَلَآ أَعۡلَمُ ٱلۡغَيۡبَ وَلَآ أَقُولُ لَكُمۡ إِنِّي مَلَكٌۖ إِنۡ أَتَّبِعُ إِلَّا مَا يُوحَىٰٓ إِلَيَّ...﴾
{Ka ce: "Ba zan ce muku, a wurina akwai taskõkin Allah ba. Kuma ba ni sanin gaibi, kuma ba ni gaya muku cẽwa, ni malã'ika ne. Ba wani abu nake bi ba, fãce abin da ake yiwo wahayi zuwa gare ni..."} [al-An'am: 50].
MABHASI NA BIYU: MA'ANAR IMANI DA RUKUNANSA:
Imani: Shi ne tabbatarwa da zuciya, da furuci da harshe, da aiki da zuciya da kuma gaɓɓai, yana ƙaruwa da biyayya, kuma yana raguwa da saɓo.
Imani sharaɗi ne na ingancin (ayyuka) da karɓar ibadu, kamar yadda shirka da kafirci, masu ɓata dukkan ayyukan biyayya ne, kamar yadda Allah ba Ya karɓar sallah ba tare da alwala ba, haka ba Ya karɓar wata ibada ba tare da imani ba, Allah Maɗaukakin sarki Ya ce:
﴿وَمَن يَعۡمَلۡ مِنَ ٱلصَّٰلِحَٰتِ مِن ذَكَرٍ أَوۡ أُنثَىٰ وَهُوَ مُؤۡمِنٞ فَأُوْلَٰٓئِكَ يَدۡخُلُونَ ٱلۡجَنَّةَ وَلَا يُظۡلَمُونَ نَقِيرٗا 124﴾
{Kuma wanda ya yi aiki daga ayyukan ƙwarai, namiji ne ko kuwa mace, alhãli kuwa Yanã mũmini, to, waɗannan sunã shiga Aljanna, kuma bã zã a zãlunce su da gwargwadon hancin gurtsun dabĩ no ba. 124} [al-Nasa'i: 124].
Kuma Ya bayyana cewa, shirka mai ɓata aiki ce, Kamar yadda Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:
﴿وَلَقَدۡ أُوحِيَ إِلَيۡكَ وَإِلَى ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِكَ لَئِنۡ أَشۡرَكۡتَ لَيَحۡبَطَنَّ عَمَلُكَ وَلَتَكُونَنَّ مِنَ ٱلۡخَٰسِرِينَ 65﴾
{Kuma hakika an yi wahayi zuwa gare ka, da kuma zuwa ga waɗanda suke a gabãninka, "Lalle idan ka yi shirki haƙĩƙa aikinka zai ɓãci, kuma lalle zã ka kasance daga mãsu hasãra". 65} [Al-Zumar: 65].
Rukunan imani guda shida ne: Yin imani da Allah, da mala'ikunSa, da litattafanSa, da manzanninSa, da ranar lahira, da ƙaddara alherinta da sharrinta.
1) Yin imani da Allah - Maɗaukakin Sarki - yana ƙunsar al'amurra guda uku:
1- Yin imani da RububiyyarSa:
Shi ne kaɗaita Allah - Maɗaukakin sarki - da ayyukanSa; kamar halitta da azirtawa, da rayawa, da kashewa, Babu wani Mahalicci sai Allah, babu wani Mai azirtawa sai Allah, babu wani Mai rayawa sai Allah, babu wani Mai kashewa sai Allah, babu wani mai tasarrufi acikin kasantacce sai Shi - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka -
Kuma ba'a san cewa wani ɗaya daga halitta ya yi musun Rububiyyar Allah - tsarki ya tabbatar maSa - ba, sai dai in ya kasance mai girman kai ne, ba mai ƙudirce abinda yake faɗa ba, kamar yadda ya faru ga Fir'auna, lokacin daya cewa mutanensa:
﴿...أَنَا رَبُّكُمُ الْأَعْلَى﴾
{...Nĩ ne Ubangijinku mafi ɗaudaka} [al-Nazi'at: 24], Saidai hakan bai kasance akan aƙida ba (wato har zuciya), kamar yadda Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce game da (Annabi) Musa - aminci ya tabbata agare shi -:
﴿قَالَ لَقَدۡ عَلِمۡتَ مَآ أَنزَلَ هَٰٓؤُلَآءِ إِلَّا رَبُّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ بَصَآئِرَ وَإِنِّي لَأَظُنُّكَ يَٰفِرۡعَوۡنُ مَثۡبُورٗا 102﴾
{Ya ce: "lalle ne haƙĩƙa ka sani bãbu wanda ya saukar da waɗannan, fãce Ubangijin sammai da ƙasa dõmĩn su zama abũbuwan lũra. Kuma lalle ne ni, haƙĩƙa, ina zaton ka, yã Fir'auna, halakakke".102} [al-Isra'a: 102], Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:
﴿وَجَحَدُوا بِهَا وَاسْتَيْقَنَتْهَا أَنْفُسُهُمْ ظُلْمًا وَعُلُوًّا... ﴾
{Kuma suka yi musunsu, alhãli zukãtansu sun natsu da su dõmin zãlunci da girman kai...} [al-Naml: 14].
Hakika waɗannan halittun babu makawa suna da wani Mahalicci Don ba zai yi wu su samar da kansu ba; domin abu ba ya halittar kansa, kuma ba zai yi wu a samesu haka kawai ba; domin kowane fararre ba makawa akwai wanda ya farar (da shi), kuma domin cewa samuwarsu akan wannan tsarin ƙayatacce da tsarin da aka saba yana hana samuwarsu haka kawai, Sai ya tabbata cewa, suna da wanda ya samar da su, Shi ne Allah Ubangijin talikai. Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce:
﴿أَمۡ خُلِقُواْ مِنۡ غَيۡرِ شَيۡءٍ أَمۡ هُمُ ٱلۡخَٰلِقُونَ 35 أَمۡ خَلَقُواْ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَۚ بَل لَّا يُوقِنُونَ 36﴾
{Shin, an halicce su ne bã daga kõme ba, kõ kuwa sũ ne mãsu yin halitta? 35
Shin, sun halicci sammai da ƙasa ne? Ã'a ba su dai yi ĩmãnin yaƙĩni ba. 36} [al-Dur: 35-36].
Haƙiƙa mushrikai sun kasance, suna tabbatar da Rububiyyar Allah - Maɗaukakin sarki - tare da yin shirkarsu da Shi a cikin Uluhiyya, amma hakan bai shigar da su cikin musulunci ba, kuma annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya yaƙesu, ya halatta jinanensu da dukiyoyinsu; domin su sun yi shirka a cikin bauta, sai suka bauwa waninSa tare da Shi; kamar gumaka da duwatsu da mala'iku da wasunsu.
2- Imani da UluhiyyarSa:
Yin imani da UluhiyyarSa wato: Cewa Shi kaɗai ne Allah na gaskiya baShi da abokin tarayya, (Allah) da ma'anar (Abin bauta), wato (Abin bauta) dan so da girmamawa da miƙa wuya.
Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce:
﴿وَإِلَٰهُكُمۡ إِلَٰهٞ وَٰحِدٞۖ لَّآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ ٱلرَّحۡمَٰنُ ٱلرَّحِيمُ 163﴾
{Kuma Ubangijinku Ubangiji Guda ne. Bãbu wani Ubangiji fãce Shi, Mai rahama, Mai jin ƙai. 163} [al-Baƙara: 163].
Dukkan wanda ya riƙi wani Ubangiji tare da Allah, yana bauta masa koma bayanSa, to Uluhiyyarsa ɓatacciya ce, (kenan bai kaɗaita Allah da bauta ba). Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce:
﴿ذَٰلِكَ بِأَنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلۡحَقُّ وَأَنَّ مَا يَدۡعُونَ مِن دُونِهِۦ هُوَ ٱلۡبَٰطِلُ وَأَنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلۡعَلِيُّ ٱلۡكَبِيرُ 62﴾
{Wancan! sabõda lalle ne Allah, shĩ ne Gaskiya, kuma lalle ne, abin da suke kira waninSa shi ne ƙarya. Kuma lalle ne Allah, Shĩ ne Maɗaukaki, Mai girma. 62} [al-Hajj: 62].
Saboda haka, manzanni - aminci ya tabbata a gare su - sun kasance, tun daga (Annabi) Nuhu zuwa (Annabi) Muhammad - tsira da a mincin Allah su tabbata a gare shi - suna kiran mutanensu zuwa Tauhidi da kaɗaita Allah da bauta, banda waninSa. Haƙiƙa Allah - Maɗaukkain sarki - Ya ɓata riƙon da mushrikai suka yi wa alloli suna bauta musu tare da Allah - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka - suna neman taimakonsu, suna neman agajinsu, hakan kuwa da dalilai biyu na hankali:
Na farko: Cewa babu wani abu daga cikin abubuwan da suka keɓanci allantaka a tare da wannan alloli da suka riƙe, su halittarsu aka yi, basa halitta, basa jawo wani anfani ga mai bauta musu, kuma ba sa tunkuɗe wata cuta daga garesu, kuma basa mallakar rayuwa, ko mutuwa, ko tayarwa (tayar da halitta bayan mutuwa). Kamar yadda Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:
﴿وَٱتَّخَذُواْ مِن دُونِهِۦٓ ءَالِهَةٗ لَّا يَخۡلُقُونَ شَيۡـٔٗا وَهُمۡ يُخۡلَقُونَ وَلَا يَمۡلِكُونَ لِأَنفُسِهِمۡ ضَرّٗا وَلَا نَفۡعٗا وَلَا يَمۡلِكُونَ مَوۡتٗا وَلَا حَيَوٰةٗ وَلَا نُشُورٗا 3﴾
(Kuma suka riƙi abũbuwan bautawa, baicin Shi, bã su yin halittar kõme alhãli sũ ne ake halittãwa kuma bã su mallakar wa kansu wata cũta ko wani amfãni, kuma bã su mallakar mutuwa kuma bã su mallakar rãyarwa, kuma bã su mallakar tãyarwa. 3} [al-Furƙan: 3].
Na biyu: Cewa waɗannan mushirikan sun kasance suna tabbatar da cewa Allah - Maɗaukakin Sarki - Shi ne Mahalicci Mai jujjuya al'amaura Shi kaɗai banda waninSa, wannan yana lazimta musu kaɗaita Shi, da Uluhiyya kamar yadda suka kaɗaitaShi da Rububiyya, Kamar yadda Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:
﴿قُل لِّمَنِ ٱلۡأَرۡضُ وَمَن فِيهَآ إِن كُنتُمۡ تَعۡلَمُونَ 84 سَيَقُولُونَ لِلَّهِۚ قُلۡ أَفَلَا تَذَكَّرُونَ85 قُلۡ مَن رَّبُّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ ٱلسَّبۡعِ وَرَبُّ ٱلۡعَرۡشِ ٱلۡعَظِيمِ 86 سَيَقُولُونَ لِلَّهِۚ قُلۡ أَفَلَا تَتَّقُونَ 87 قُلْ مَنْ بِيَدِهِ مَلَكُوتُ كُلِّ شَيْءٍ وَهُوَ يُجِيرُ وَلَا يُجَارُ عَلَيْهِ إِنْ كُنْتُمْ تَعْلَمُونَ 88 سَيَقُولُونَ لِلَّهِ قُلْ فَأَنَّى تُسْحَرُونَ 89﴾
{Ka ce: "Wane ne da mulkin ƙasa da wanda ke a cikinta, idan kun kasance kunã sani?" 84
Zã su ce: "Na Allah ne." Ka ce, "Shin, to, bã zã ku yi tunãni ba?" 85
Ka ce: "Wãne ne Ubangijin sammai bakwai, kuma Ubangijin Al'arshi mai girma?" 86
Zã su ce: "Na Allah ne." Ka ce, "Shin, to, bã zã ku bĩ ji tsoran Allah ba?" 87
Ka ce: "Wãne ne ga hannunsa mallakar kõwane abu yake, alhãli kuwa shi yanã amintar (da wanda ya so), kuma ba a amintar da kõwa daga gare shi, idan kun kasance kunã sani?" 88
Zã su ce: "Ga Allah yake." Ka ce: "To, yãya ake juyar da ku (ga barin gaskiya)?" 89} [Al-Mu'uminun: 84 - 89] Idan sun tabbatar da Tauhidin Rububiyya; to ya wajaba akansu su keɓanceShi - tsarki ya tabbatar maSa - da bauta Shi kaɗai, kuma kada su hada shi da wani tare da Shi a cikin bautarSa.
3- Imani da sunaye da siffofi:
Wato: Tabbatar da abinda Allah Ya tabbatarwa kanSa a cikn littafinSa, ko manzanSa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tabbatar maSa a cikin sunnarsa; na sunaye da siffofi, ta fuskar da ta dace da Allah - Maɗaukakin sarki -, ba tare da canjawa ko korewa ba, ko kwatantawa, ko kamantawa ba, Allah Maɗaukakin sarki Ya ce:
﴿وَلِلَّهِ ٱلۡأَسۡمَآءُ ٱلۡحُسۡنَىٰ فَٱدۡعُوهُ بِهَاۖ وَذَرُواْ ٱلَّذِينَ يُلۡحِدُونَ فِيٓ أَسۡمَٰٓئِهِۦۚ سَيُجۡزَوۡنَ مَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ 180﴾
{Kuma Allah Yanã da sũnãye mãsu kyau. Sai ku rõƙe shi da su, kuma ku bar waɗanda suke yin ilhãdi a cikin sũnãyenSa: zã a sãka musu abin da suka kasance sunã aikatãwa. 180} [al-A'araf: 180], Allah Maɗaukakin sarki Ya ce:
﴿...لَيۡسَ كَمِثۡلِهِۦ شَيۡءٞۖ وَهُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡبَصِيرُ﴾
{...Wani abu bai zama kamar tamkarSa ba, kuma Shĩ Mai ji, Mai gani ne.} [al-Shura:11].
Rabe-raben shirka gida uku ne:
1- Babbar Shirka .
2- Shirka ƙarama.
3- Shirka ɓoyayya.
2- Babbar Shirka :
Yanda za'a ganeta: Daidaita wanin Allah da Allah a abinda Allah ya keɓanta da shi. Kamar yadda Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:
﴿إِذۡ نُسَوِّيكُم بِرَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ 98﴾
{"A lõkacin da muke daidaita ku da Ubangijin talikai. 98} [al-Shu'ara'u: 98].
Shi ne abinda yake ƙunsar: Juyar da bauta ga wanin Allah - Maɗaukakin sarki -, ko karkatar da sashinta ga waninSa - tsarki ya tabbatar maSa -; kamar addu'a da neman agaji da bakance da yanka, da wasunsu na nau'ikan ibada.
ko ya ƙunshi: Halatta abinda Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya haramta, ko haramta abinda Ya halatta, ko sarayar da abinda Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya wajabta, Kamar halatta abinda aka san haramcinsa, na addini da larura; kamar halatta zina, da giya, ko saɓawa iyaye, ko riba, ko abunda ke kama da hakan.
Ko haramta abinda Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya halatta na tsarkakan abubuwa, ko sarayar (kawar) da abinda Allah Ya wajabta ; kamar ƙudirce cewa sallah ba wajibi ba ce, ko azimi ba wajibi bane, ko zakka ba wajiba bace.
Shirka babba tana wajabta ɓata aiki, da dawwama a cikin wuta ga wanda ya mutu akanta, Kamar yadda Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:
﴿...وَلَوۡ أَشۡرَكُواْ لَحَبِطَ عَنۡهُم مَّا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ﴾
{...Da sun yi shirka, da abinda suka kasance suna aikatawa ya lalace.} [al-An'am: 88].
kuma cewa wanda ya mutu akanta; Allah ba zai gafarta masa ba, kuma aljanna haramun ce a gare shi, kamar yadda Maɗaukakin sarki Ya ce:
﴿إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَغۡفِرُ أَن يُشۡرَكَ بِهِۦ وَيَغۡفِرُ مَا دُونَ ذَٰلِكَ لِمَن يَشَآءُ...﴾
{Lalle ne, Allah ba Ya gãfarta a yi shirka (tarayya) da Shi, kuma Yana gãfarta abin da yake koma bãyan wannan, ga wanda Yake so....} [al-Nisa'i: 48], kuma Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce:
﴿إِنَّهُۥ مَن يُشۡرِكۡ بِٱللَّهِ فَقَدۡ حَرَّمَ ٱللَّهُ عَلَيۡهِ ٱلۡجَنَّةَ وَمَأۡوَىٰهُ ٱلنَّارُ...﴾
{Lalle ne shĩ, wanda ya yi shirka da Allah, to, lalle ne, Allah Yã haramta masa Aljanna, kuma makōmarsa wuta...} [al-Ma'ida: 72].
2- ƙaramar Shirka
Ita ce wacce ambatanta shirka ya tabbata a nassosi, sai dai ita bata kai matakin shirka babba ba, to wannan ana ambatanta shirka ƙarama; misalin rantsuwa da wanin Allah - Maɗaukakin sarki -; kamar rantsuwa da Ka'aba, da kuma annabawa, da amana, da rayuwar wane, da makamancin hakan, kamar yadda tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi ya ce: «Wanda ya rantse da wanin Allah, to hakika ya kafirta, ko ya yi shirka»2.
Zata iya zama babba gwargwadan abinda yake kasancewa a cikin zuciyar mai ita, Idan ya kasance a cikin zuciyar mai rantsuwa da Annabi, ko shehi wane, cewa shi tamkar Allah ne, ko ana kiran shi koma bayan Allah, ko shi yana tasarrufi a cikin kasantacce, to shi yana zama shirka babba. Amma idan mai rantsuwa da wanin Allah, bai yi nufin wannan nufin ba, kaɗai ya gudana ne akan harshensa, ba tare da wannan nufin ba, don kasancewarsa ya saba da hakan; to ya zama shirka ƙarama, wannan yana afkuwa da yawa a wasu ɓangarori, to abinda yake wajibi faɗakarwa akan hakan, da gargaɗarwa daga gare shi, dan kiyaye Tauhidi da kuma tsare shi.
3- Shirka ɓoyayya:
Ita ce abinda yake kasancewa a zuciya na riya; kamar wanda yake sallah ko yake karatu dan ya nunawa mutane, ko yake tasbihi har su yaba masa, ko ya yi sadaka dan su yabe shi , Wannan yana ɓata aikin da ya yi riya a cikinsa ne, banda ragowar aikin da ya tsarkake Allah - Maɗaukakin sarki - da shi.
Tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: «Shirka a cikin wannan al'ummar, ita ce mafi ɓoyuwa daga tafiyar baƙar tururuwa akan baƙin kurman dutse a cikin duhun dare, kaffararta ya ce: ("Allahumma inni a'uzu bika an ushrika bika shai'an wa ana a'alamu, wa astagfiruka minaz zambil lazi la a'alamu"). "Ya Allah ni ina neman tsarinKa da in yi maka tarayya da wani abu, alhali ni ina sani, kuma ina neman gafararKa daga zunubin da ban san shi ba"»3.
NAU'UKAN KAFIRCI:
Nau'i na farko: Kafirci babba:
Shi ke tabbatar da dawwama a cikin wuta ne, kuma shi nau'i biyar ne:
1- Kafircin ƙaryatawa:
Shi ne ƙudirce ƙaryar manzanni, wannan kaɗan ne a cikin kafirai; domin Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya ƙarfafi manzanninSa da hujjoji bayyananu, kaɗai halin waɗannan maƙaryatan kamar yadda Allah Ya siffanta su ne:
﴿وَجَحَدُوا بِهَا وَاسْتَيْقَنَتْهَا أَنْفُسُهُمْ ظُلْمًا وَعُلُوًّا...﴾
{Sun yi musun ta, kuma kawunansu sun tabbatar da ita, sabo da zalunci da girman kai...} [al-Nahl: 14].
2- Kafircin ƙi da girman kai:
Wannan misalin kafircin Iblis, cewa shi bai musanta umarnin Allah ba kuma bai yi inkarinSa ba, kaɗai ya fuskanci umarnin ne da ƙi da girman kai, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce:
﴿وَإِذۡ قُلۡنَا لِلۡمَلَٰٓئِكَةِ ٱسۡجُدُواْ لِأٓدَمَ فَسَجَدُوٓاْ إِلَّآ إِبۡلِيسَ أَبَىٰ وَٱسۡتَكۡبَرَ وَكَانَ مِنَ ٱلۡكَٰفِرِينَ 34﴾
{Kuma a lõkacin da Muka ce ga malã'iku: "Ku yi sujada ga Ãdam," Sai suka yi sujada, fãce Ibilĩsa ya ƙi, kuma ya yi girman kai, kuma ya kasance daga kãfirai". 34} [al-Baƙara: 34].
3- Kafircin bijirewa:
Hakan kuwa, ya kau da kansa, da jinsa, da zuciyarsa, daga bin gaskiya, ba ya waiwayawa zuwa ga gaskiya, kuma ba ya bata kulawa, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce:
﴿وَمَنۡ أَظۡلَمُ مِمَّن ذُكِّرَ بِـَٔايَٰتِ رَبِّهِۦ ثُمَّ أَعۡرَضَ عَنۡهَآۚ إِنَّا مِنَ ٱلۡمُجۡرِمِينَ مُنتَقِمُونَ22﴾
{Kuma babu wanda yafi zãlunci fiiye da wanda aka tunãtar da ãyõyin Ubangijinsa, sannan ya bijire daga barinsu? Lalle Mũ, Mãsu yin azãbar rãmuwa ne ga mãsu laifi. 22} [al-Sajda: 22].
Amma bijirewa na wani yanki; to shi fasiƙanci ne ba kafirci ba; kamar wanda yake bijirewa daga neman sanin sashin wajiban addini; na hukunce-hukuncen azimi ko hajji da makamancin hakan.
4- Kafircin kokwanto:
Hakan shi ne ya yi kaikomo, ba zai yanke da bin gaskiya ba, a'a yana kokwanto a cikinta, kamar yadda yake a cikin faɗinSa - Allah Maɗaukakin sarki -:
﴿وَدَخَلَ جَنَّتَهُ وَهُوَ ظَالِمٌ لِنَفْسِهِ قَالَ مَا أَظُنُّ أَنْ تَبِيدَ هَذِهِ أَبَدًا 35 وَمَا أَظُنُّ السَّاعَةَ قَائِمَةً وَلَئِنْ رُدِدْتُ إِلَى رَبِّي لَأَجِدَنَّ خَيْرًا مِنْهَا مُنْقَلَبًا 36﴾
{Kuma ya shiga gõnarsa, alhãli yanã mai zãlunci ga kansa, ya ce: "Bã ni zaton wannan zã ta halaka har abada." 35
"Kuma bã ni zaton Alkiyama mai tsayuwa ce, kuma lalle ne, idan an mayar da ni zuwa ga Ubangijiĩna, to, lalle ne, zan sãmi abin da yake mafi alhẽri daga gare ta ya zama makõma." 36} [al-Kahf: 36].
5- Kafircin munafurci:
Shi ne, ya bayyanar da imani da harshensa, kuma ya ɓoye ƙaryatawa a zuciyarsa, Allah Maɗaukakin sarki - Ya ce:
﴿وَمِنَ ٱلنَّاسِ مَن يَقُولُ ءَامَنَّا بِٱللَّهِ وَبِٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِ وَمَا هُم بِمُؤۡمِنِينَ 8﴾
{Kuma akwai daga mutãne wanda yake cewa: "Mun yi imani da Allah kuma da Yinin Lãhira." Alhãli kuwa su ba muminai ba ne. 8} [al-Baƙara: 8].
Waɗannan sune nau'ikan kafirci babba shi ke fitarwa daga Musulunci.
NAU'I NA BIYU: Kafirci ƙarami:
Wannan nau'in ba ya tabbatar da dawwama a cikin wuta, Shi ne wanda ambatansa kafirci ya zo a cikin Alƙur'ani da Sunnah, ba tare da an yi masa Ma'arifa da Alif da Lam ba, kawai ya zo abin yi wa Nakira, Misalansa suna da yawa, daga cikinsu: Hadisin Abu Hurairah - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Abu biyu a cikin mutane su kafirci ne a cikinsu: Sukar nasaba, da kukan kera ga mamaci»4.
2) Imani da Mala'iku:
Su duniya ce ta boye, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya halicce ne daga haske, su masu bautar Allah - Maɗaukakin sarki - ne, basu da wani abun da ya keɓanci Rububiyya da Uluhiyya, su ba su saɓawa abinda Allah Ya umarce su, kuma suna aikata abinda aka umarce su, Su wani adadi ne mai yawa, babu wanda zai (iya) ƙididdigesu sai Allah - Maɗaukakin Sarki -.
Imani da mala'iku yana ƙunsar al'amura huɗu:
1- Imani da samuwarsu.
2- Imani da wanda muka san sunansa daga cikinsu; kamar: (Mala’ika) Jibril da Mika'il da Israfil da wasunsu. Wanda kuma bamu san sunansa ba, muna imani da shi a dunƙule.
3- Imani da abinda muka sani na siffofinsu, waɗanda suka zo a cikin Alkur’ani da sunnah; Kamar siffar (Mala'ika) Jibril, haƙiƙa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya bada labarin cewa ya gan shi akan siffarsa wacce Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya halicce shi a kanta, yana da fukafukai ɗari shida, haƙiƙa sun toshe sasanni.
4- Imani da abinda muka sani na ayyukansu; kamar tasbihinsu ga Allah - Maɗaukakin sarki -, da bauta maSa dare da rana ba tare da ƙosawa ko rauni ba.
Misali: (Mala'ika) Jibril: Amintacce ne akan wahayi.
(Mala'ika) Israfil kuma: Shi aka wakilta da yin busa a cikin ƙaho.
Da mala'ikan mutuwa: Wanda aka wakilta da ɗaukan rayuka a lokacin mutuwa.
Da (Mala'ika) Malik: Mai tsaron wuta. Da (Mala'ika) Ridwan: Mai tsaron aljanna, da wasunsu.
3) Imani da Litattafai:
Abin nufi da littattafai: Sune littattafan sama, waɗanda Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya saukar da su ga manzanninSa, dan shiryarwa ga mutane, da kuma jin ƙansu, dan su kai da tsira a duniya da lahira.
Imani da littattafai yana ƙunsar al'amura huɗu:
1- Imani da cewa, tabbas su saukakku ne daga Allah.
2- Imani da wanda muka san sunansa daga cikinsu; kamar Alƙur'ani da aka saukar ga (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, da Attaurar da aka saukar da ita ga (Annabi) Musa - aminci ya tabbata a gare shi -, da Linjilar da aka saukar ga (Annabi) Isa - aminci ya tabbata agare shi -, da Zaburar da aka bawa (Annabi) Dawud - aminci ya tabbata agare shi -,
Amma wanda bamu san sunansa ba; muna imani da shi a dunƙule.
3- Gasgatawa da labarunsu; kamar labarun dake cikin Alkur’ani, da labarun abinda ba'a canza ba daga littattafan da suka gabata.
4- Aiki da hukunce-hukuncen abinda ba'a shafe ba dake cikinsu, da yarda da sallamawa da shi, daidai ne shin mun fahimci hikimarsa ko bamu fahimceta ba. Dukkanin littattafan da suka gabata an shafe su da Alkur’ani mai girma, Saboda haka, ba ya halatta a yi aiki da kowane hukunci daga hukunce-hukuncen littattafan da suka gabata, sai abinda ya inganta daga garesu, kuma Alƙur'ani ya tabbatar da shi ko sunnar Annabi.
4) Imani da manzanni - aminci ya tabbata agare su -:
manzanni: jam'i ne na manzo; shi ne wanda aka yi masa wahayi cikin mutane da wata shari'a, kuma aka umarce shi da ya isar da ita, na farkonsu shi ne (Annabi) Nuhu - aminci ya tabbata agare shi -, kuma na ƙarshensu shi ne (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, su mutanene waɗanda aka halitta, basu da wani abun da ya keɓanci Rububiyya da Uluhiyya,
Imani da manzanni ya ƙunshi:
1- Imani da cewa soƙonsu gaskiya ne daga Allah, wanda ya kafirce da saƙon ɗaya daga cikinsu to haƙiƙa, ya kafirce da dukkaninsu.
2- Imani da wanda muka san sunansa daga cikinsu, misalin: (annabi) Muhammad, da Ibrahim, da Musa, da Isa, da Nuhu, - aminci ya tabbata agare su -, sune Ulul azmi cikin manzanni.
Amma wanda bamu san sunansa ba daga cikinsu; to muna imani da shi a dunƙule. Allah Maɗaukakin sarki Ya ce:
﴿وَلَقَدۡ أَرۡسَلۡنَا رُسُلٗا مِّن قَبۡلِكَ مِنۡهُم مَّن قَصَصۡنَا عَلَيۡكَ وَمِنۡهُم مَّن لَّمۡ نَقۡصُصۡ عَلَيۡكَ...﴾
{Kuma lalle haƙĩƙa, Mun aika wasu Manzanni daga gabãninka, daga cikinsu akwai wanda Muka ƙissanta maka lãbãrinsa kuma daga cikinsu akwai wanda ba Mu ƙissanta lãbãrinsa ba a gare ka...} [Ghafir: 78].
3- Gasgata abinda ya inganta daga garesu - aminci ya tabbata agare su - na labarunsu.
4- Aiki da shari'ar wanda aka aiko zuwa garemu daga cikinsu, shi ne cikamakinsu (annabi) Muhammad - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi -.
5) Imani da Ranar Lahira:
Ita ce ranar Alƙiyama, wacce za'a tashi mutane a cikinta don yin hisabi da sakamako, an ambace ta da hakan: domin babu wata rana a bayanta, ta yadda 'yan Aljanna zasu tabbata gidajensu, 'yan wuta kuma (zasu tabbata) a cikin gidajensu.
Imani da ranar lahira yana ƙunsar al'amura uku:
A- Imani da tashi.
Shi ne rayar matattu, lokacin da za’a yi busa acikin ƙaho busa ta biyu, sai mutane su tashi ga Ubangijin talikai, marasa takalma, tsirara basu da sutura, marasa kaciya, Allah Maɗaukakin sarki Ya ce:
﴿كَمَا بَدَأْنَا أَوَّلَ خَلْقٍ نُعِيدُهُ وَعْدًا عَلَيْنَا إِنَّا كُنَّا فَاعِلِينَ 104﴾
{Kamar yadda Muka fãra a farKon halitta Muke mãyar da ita. Wa'adi ne a Kanmu. Lalle ne Mun kasance Mãsu aikatãwa. 104} [Al-Anbiya'u: 104].
B- Imani da hisabi da sakamako:
Lokacin da za’a yi wa bawa hisabi akan aikinsa, kuma a yi masa sakayya akansa, (Allah) - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:
﴿إِنَّ إِلَيۡنَآ إِيَابَهُمۡ 25 ثُمَّ إِنَّ عَلَيۡنَا حِسَابَهُم 26﴾
{Lalle ne, zuwa gare Mu kõmõwarsu take. 25
Sa'an nan lalle ne aikin Mu ne Mu yi musu hisãbi.} [Al-Gashiya: 25-26].
C- Imani da aljanna da wuta:
Kuma cewa, sune makoma ta har abada ga halitta; Aljanna gidan ni'ima ce, wacce Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya tanade ta ga muminai masu tsoron Allah, waɗanda suka tsayu da biyayya ga Allah da manzonSa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -. a cikinta akwai abinda ido bai taɓa gani ba, kuma kunne bai taɓa ji ba, kuma bai taɓa ɗarsuwa a zuciyar wani mutum ba.
Amma wuta; Ita ce gidan azaba, wacce Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya tanadeta ga kafirai, waɗanda suka kafircewa Allah suka saɓawa manzanninSa. A cikinta akwai daga nau'ikan azaba da uƙuba abinda bai taɓa ɗarsuwa a cikin zuciya ba.
6) Imani da kaddara dukkaninta alherinta da kuma sharrinta:
Abin nufi da ƙaddara: Kaddarawar Allah - Mai girma da ɗaukaka - ga abinda zai kasance gwargwadan abinda ya rigaya na IliminSa, kuma hikimarSa ta hukuntar.
Imani da ƙaddara yana ƙunsar al'amura huɗu:
1- Ilimi: Shi ne imani da ilimin Allah - Maɗaukakin sarki - , kuma cewa Shi ne Masani da abinda ya kasance da abinda zai kasance, da yanda zai kasance, a dunƙule da kuma a rarrabe, azali da kuma har abada. Shi ne Masani - tsarki ya tabbatar maSa - da abinda bai kasance ba, da a ce ya kasance ta yaya zai kasance, kamar yadda tsarki ya tabbatar maSa Ya ce:
﴿وَلَوۡ رُدُّواْ لَعَادُواْ لِمَا نُهُواْ عَنۡهُ ...﴾
{Da a ce an dawo da su da sun koma ga abinda aka hanesu daga gare shi...} [al-An'am: 28].
2- Rubutu: Shi ne cewa Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya rubuta gwargwadon kowane abu har zuwa ranar Alƙiyama, Kamar yadda Maɗaukakin Sarki Ya ce:
﴿أَلَمۡ تَعۡلَمۡ أَنَّ ٱللَّهَ يَعۡلَمُ مَا فِي ٱلسَّمَآءِ وَٱلۡأَرۡضِۚ إِنَّ ذَٰلِكَ فِي كِتَٰبٍۚ إِنَّ ذَٰلِكَ عَلَى ٱللَّهِ يَسِيرٞ 70﴾
{Ashe, ba ka sani ba, lalle ne Allah Yanã sanin abin da yake a cikin sama da ƙasa? Lalle ne hakan yanã cikin Littafi lalle wancan ga Allah mai sauƙi ne.} [al-Hajj: 70].
3- Mashi'ah: Ita ce imani da cewa babu abinda zai kasance a cikin wannan duniyar sai abinda Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya so, kuma ya ga dama. Allah Maɗaukakin sarki Ya ce:
﴿وَرَبُّكَ يَخۡلُقُ مَا يَشَآءُ وَيَخۡتَارُ ...﴾
{Ubangijinka Yana halittar abinda Yake so, kuma Yana zaɓa...} [al-Ƙasas: 68]. Mutum yana da ganin dama da bata fita daga ganin damar Allah, kamar yadda Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:
﴿وَمَا تَشَآءُونَ إِلَّآ أَن يَشَآءَ ٱللَّهُ رَبُّ ٱلۡعَٰلَمِينَ 29﴾
{Kuma bã zã ku so ba sai idan Allah Ubangijin halitta Yã yarda.} [al-Takweer: 29].
4- Halitta: Shi ne imani cewa Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya halicci halitta da ayyukansu na alheri da sharri, Allah Maɗaukakin sarki Ya ce:
﴿ٱللَّهُ خَٰلِقُ كُلِّ شَيۡءٖۖ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ وَكِيلٞ 62﴾
{Allah ne Mahaliccin dukkan kõme, kuma Shĩ ne Wakĩli a kan kõme.} [al-Zumar: 62].
Haƙiƙa an tattaro waɗan nan matakan acikin wannan baitin:
Ilimi rubutun Ubangijinmu Mashi'arSa *** da halittarsa shi ne samarwa da kasantarwa.
MABHASI NA UKU: IHSANI (KYAUTAYI):
Kyautatawa: Shi rukuni ɗaya ne; ka bautawa Allah kamar kai kana ganinSa, idan kai baka ganinSa, to Shi yana ganinka.
Wato: Mutum ya aikata abinda Allah Ya bautar da shi, kai ka ce shi yana tsaye a gaban Allah - Mai girma da ɗaukaka -, hakan yana lazimtar cikar tsoron Allah da komawa zuwa gareShi - tsarki ya tabbatar maSa -. Kuma yana lazimtar zuwa da bautar akan tsarin Sunnar manzo - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi -.
Kyautatawa mataki biyu ne: masu kyautatawa kuma suna kan matakai guda biyu masu wadanda suka fi juna
Mataki na farko: Shi ne mafi girmansu, matakin Mushahadah; Shi ne bawa ya yi aiki kai ka ce yana ganin Allah - Mai girma da ɗaukaka - da zuciyarsa, sai zuciya ta yi haske da imani, har gaibu ya zama kamar sarari ƙarara.
Mataki na biyu: Mataki na ikhalasi da Muraƙabah. Shi ne bawa ya yi aiki akan halarto da ganin Allah da tsinkaya gareShi, idan ya halarto wannan to shi mai tsarkakewa ne ga Allah - Maɗaukakin sarki -.
MADALABI NA HUDU: Taƙaitaccen bayani kan: Tushen Ahlus Sunnah Wal Jama'ah:
Na farko: Bin abinda ya zo a cikin Alƙur'ani da Sunnah a ɓoye da sarari, da rashin gabatar da zancen wani cikin mutane, akan zancen Allah - Mai girma da ɗaukaka - da zancen manzonSa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -.
Na biyu: Kuɓutar zukatansu, da harsunansu ga sahabban manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, suna ganin cewa, Halifa bayan manzon Allah - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi, shi ne-: Abubakar, sannan Umar, sannan Usman, sannan Aliyu - Allah Ya yarda da su - baki ɗaya.
Na uku: Son iyalan gidan manzon Allah - tsira da a mincin Allah su tabbata a gare shi -, da jiɓintar su. Iyalan gidansa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: Nagari a cikinsu kaɗai.
Na huɗu: Rashin fito na fito ga shugabanni, da majiɓinta al'amura, koda sun yi zalinci, kuma ana yi musu addu'a ta gyaruwa da waraka, kada a yi musu mummunar addu'a. Kuma yi musu biyayya yana daga yi wa Allah - Mai girma da ɗaukaka - biyayya wajibi ne, muddin dai ba su yi umarni da saɓo ba, idan sun yi umarni da saɓo; to ba za’a yi musu biyayya a cikinsa ba, kuma biyayya gare su zata wanzu a wanin wannan.
Na biyar: Gasgatawa da karamomin waliyyai: Ita ce abinda Allah yake gudanarwa a hannayensu na saɓanin abinda aka saba.
Na shida: Ba sa kafirta masu sallah, don saɓo dan manyan zunubai. kamar yad da Kawarij suke aikatawa, kawai 'yan uwantaka ta imani tabbatacciya ce tare da saɓo, suna cewa game da mai saɓo: Shi mumini ne da imaninsa, kuma fasiƙi ne da babban laifin sa.
Fasali na biyu: Abinda ke da alaƙa da ibadu.
Mabhasi na farko: Tsarki:
Dahara a harshen (laranci): Tsafta da tsarkaka daga ƙazanta ta fili da ta ma'ana.
A shari'ah kuma: Dauke kari da gusar da najasa Tsarki mabuɗin sallah ne, Saboda haka, hakika neman saninsa yana cikin mafi girman muhimman al'amurran addinin Musulunci da neman saninsu da kulawa da su yake wajaba akan kowane musulmi.
Na farko: Rabe-raben ruwa:
1- Mai tsarkakewa; ya inganta yin tsarki da shi, daidai ne ya kasance akan asalin halittarsa; kamar ruwan sama, ko ƙoramai, ko koguna, ko wani abu mai tsarki ya cakuɗa da shi, amma bai yi rinjaye akansa ba, kuma bai zare masa sunansa ba.
2- Mai najasa; anfani da shi ba ya halatta, ba ya ɗauke kari, kuma ba ya gusar da najasa, shi ne wanda launinsa ya canza ko ƙanshinsa ko ɗanɗanansa da najasa.
Na biyu: Najasa:
Najasa: Ita ƙazanta ce keɓantacciya, jinsinta yana hana sallah; kamar fitsari da bahaya da jini da wasunsu, kuma suna kasancewa a jiki da guri da kuma tufafi.
Asali a cikin abubuwa: Halacci da tsarki, wanda ya yi da'awar najasar ainihin wani abu to wajibi ne akansa ya zo da dalili. Ba ya daga cikin najasa: Kaki, da gumin mutum, da gumin jaki, a'a su tsarkaka ne, ko da sun kasance da ƙazanta tare da su. Dukkan najasa to ƙazanta ce banda sunkuyen hakan.
Najasa matakai uku ce:
Na farko: Najasa mai kaushi;
kamar: Najasar abinda kare ya yi lallagi a cikinsa, kuma hanyar tsarkaketa: A wanketa sau bakwai, na farkonsu da turɓaya.
Na biyu: Najasa sassauƙa:
Misalin fitsarin yaron da ake shayar da shi idan ya shafi tufa da makancinta. Hanyar tsarkaketa: A yayyafa ruwa a kanta, har sai ruwan ya game ko’ina, ba ya buƙatuwa zuwa kankarewa, ko matsewa.
Na uku: Najasa matsakaiciya:
Misalin fitsarin ɗan Adam da bahayansa, da mafiyawancin sauran najasa, idan sun faɗa akan ƙasa ko tufa ko makancinsu. Hanyar tsarkakesu: Shi ne a gusar da asalin najasar idan an ganta , da tsaftace bigiranta da ruwa ko waninsa daga hanyoyin tsaftacewa.
Daga abinda dalili ya tabbata akan najasarsa:
1- Fitsarin ɗan Adam da bahayansa.
2- Maziyyi da wadiyyi5.
3- Toroson abinda ba'a cin namansa.
4- Jinin al’ada da nifasi (biki).
5- Yawun kare.
6- Mushe, an toge daga gare shi :
A- Mutum idan ya mutu.
B- Mushen kifi da fara.
C- Mushen abinda ba shi da jini mai gudana; kamar ƙuda da tururuwa da ƙudan zuma da makamancin hakan.
D- Ƙashin mushe da ƙahonsa da farcensa da gashinsa da gashinsa wanda ke biye da fata.
Yadda ake tsarkake najasa yana kasancewa ne:
1- Da ruwa, shi ne asali a tsarkake najasa, ba'a kaucewa zuwa waninsa.
2- Abinda shari'a ta zo da shi a kan siffar tsarkake ainihin najasa ko abinda ya samu najasa:
A- Ana tsarkake fatar mushe da jemewa.
B- Tsarkake ƙwarya idan kare ya yi lallagi a cikinta; a wanketa sau bakwai; na farkonsu da turɓaya.
C- Tsarkake tufa, idan jinin al’ada ya same shi; da kankare shi, sannan matse shi da ruwa, sannan yi masa yayyafi, idan bayan nan gurbi (alama) ya ragu, to hakan ba ya cutarwa.
D- Tsarkake bezar rigar mace; da abinda ke bayansa na ƙasa mai tsarki.
E- Tsarkake tufa daga fitsarin yaron da ake shayar da shi; da yayyafi, da kuma wanke fitsarin ƙaramar yarinya.
F- Tsarkake tufa daga maziyyi; da yayyafa ruwa a wurin.
G- Tsarkake ƙasan takalmi; da goga shi a ƙasa mai tsarki.
G- Tsarkake ƙasa daga najasa; ta hanyar zuba guga na ruwa akan bigiren, ko barinta har sai rana ta busar da ita, ko iska, idan gurbin najasar ya tafi, to ta tsarkaka.
Na uku: Abinda aikata shi yake haramta akan mai kari (hadasi):
Abubuwan da suke haramta akan mai ƙaramin kari ko babba.
1- Sallah ta farilla ko nafila; saboda abinda ya zo daga Ibnu Umar - Allah Ya yarda da su - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Allah ba Ya karɓar sallah, ba tare da tsarki ba»6.
2- Taɓa AlKur'ani; saboda abinda ya zo a cikin littafin da manzo - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya rubuta shi ga Amr ɗan Hazm, a cikinsa akwai faɗinsa: «Ba mai taɓa AlKur'ani, sai mai tsarki»7.
3- Dawafi a ɗaki daɗaɗɗe (Ka’abah). saboda faɗinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Dawafi a ɗaki (ka'aba) sallah ne, sai dai Allah Ya halatta magana a cikinsa»8.. Haƙiƙa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi alwala domin ɗawafi. kuma ya inganta daga gare shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa shi ya hana mai al’ada ta yi ɗawafi a ɗaki (Ka’abah) har sai ta yi tsarki.
Amma abubuwan da suke haramta akan mai babban kari musamman sune:
1- Karatun AlKur'ani; saboda Hadisin Ali - Allah Ya yarda da shi -: "Babu wani abu da yake shamakance shi - yana nufin Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata a gare shi - daga Alƙur'ani, in banda janaba"9.
2- Zama a cikin masallaci, ba tare da alwala ba; saboda faɗinSa - Allah Maɗaukakin sarki -:
﴿يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَقۡرَبُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَأَنتُمۡ سُكَٰرَىٰ حَتَّىٰ تَعۡلَمُواْ مَا تَقُولُونَ وَلَا جُنُبًا إِلَّا عَابِرِي سَبِيلٍ حَتَّىٰ تَغۡتَسِلُواْ...﴾
{Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku kusanci sallah alhãli kuwa kuna mãsu mãye, sai kun san abin da kuke faɗa, kuma haka idan kuna mãsu janaba, fãce mai ƙẽtare hanya, har ku yi wanka...} [al-Nisa'a: 43].
Idan wanda ke da babban kari (hadasi) ya yi alwala; to zama a masallaci ya halatta agare shi, haka nan yana halatta ga mai kari babba ya wuce ta masallaci kawai dan ƙetarewa daga gare shi ba tare da zama a cikinsa ba.
NA HUDU: Ladubban biyan buƙata:
Ana so a yayin biyan buƙata:
1- Nisanta da suturta daga mutane a cikin bayan gida.
2- Faɗin addu'ar da tazo (daga annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi) yayin shiga, ita ce: «Ya Allah ina neman tsarinka daga shaiɗanu maza, da shaiɗanu mata»10.
Yana wajaba a yayin biyan buƙata:
1- Tsarkaka daga fitsari.
2- Boye al'aura.
Kuma yana haramta a yayin biyan buƙata:
1- Fuskantar alƙibla ko juya mata baya.
2- Biyan buƙata a hanyoyin mutane da gurarensu na kowa da kowa.
3- Fitsari a zaunannan ruwa.
An karhanta a yayin biyan buƙata:
1- Shafar azzakari da hannun dama a lokacin biyan buƙata.
2- Tsarkin ruwa da tsarkin hoge da hannun dama.
3- An karhanta zance, musamman ma ambatan Allah - Mai girma da ɗaukaka - a yayin biyan buƙata.
Na biyar: Hukunce-hukuncen tsarkin ruwa da tsarkin hoge:
Tsarkin ruwa: Gusar da gurbin abinda ke fita daga hanyoyi biyu (daga jikin mutum wato gaba da baya) da ruwa.
Tsarkin hoge: Gusar da abinda ya fita daga hanyoyi biyu ba tare da ruwa ba; kamar duwatsu da hankici (kyalle).
Sharuɗɗan abinda ake tsarkin hoge da shi:
1- Ya zama halastacce.
2- Ya zama mai tsarki.
3- Ya zama tsaftatacce.
4- Kada ya zama ƙashi ko toroson dabbobi.
5- Kada ya zama da wani abu abin girmamawa; kamar takardun da a jikinsu akwai sunan Allah - Mai girma da ɗaukaka -.
Wadatuwa da tsarkin hoge yana halatta da sharuɗɗa biyu:
1- Kada abinda ya fita ya ƙetare gurin al'ada.
2- Tsarkin hogen ya zama da duwatsu uku, ko sama da hakan, masu tsarkakewa.
Na shida: Hukunce-hukuncen alwala:
Alwala tana wajaba ibadu uku:
1- Sallah; daidai ne ta kasance farilla ce ko nafila.
2- Taɓa AlKur'ani;
3- Dawafi.
Sharuɗɗan alwala:
1- Musulunci.
2- Hankali.
3- Mayyazewa.
4- Niyya: Kuma bigirenta zuciya, furtata bidi'a ne. Dukkan wanda ya yi nufin alwala to haƙiƙa ya yi niyya, amma wanke gaɓɓan alwala da niyyar sanyaya jiki ko tsaftace jiki; to ba alwala bane.
5- Ci gaba da kasantuwa cikin hukuncinta: Kada ya yi niyyar yanke ta har sai tsarkin sa ya tabbata.
6- Yankewar abinda ke wajabta alwala, an togance daga hakan: Wanda a tare da shi akwai ɗigar (yoyan) fitsari na dindindin, da mai jninin cuta.
7- Tsarkin ruwa da tsarkin hoge kafinsa, ga wanda fitsari ko bahaya ya fita daga gare shi.
8- Tsarkakar ruwa, da kuma halaccinsa.
9- Gusar da abinda yake hana isar ruwa zuwa fata.
10- Shigar lokacin sallah a haƙƙin wanda karinsa (hadasin sa) yake na dindindin ne.
Farillan alwala:
1- Wanke fuska, daga cikinta: Kuskurar baki da shaƙa ruwa.
2- Wanke hannaye tare da gwiwowin hannaye.
3- Shafar dukkanin kai, kunnuwa suna daga cikinsa.
4- Wanke ƙafafuwa tare da idan sawu.
5- Jerantawa tsakanin gaɓɓan alwala.
6- Bibiya; kada ya raba ba tsakanin gaɓɓai ba kuma rabewa mai tsawo.
SIFFAR ALWALA;
1- Ambatan Allah.
2- Wanke tafuka sau uku.
3- Wanke fuska sau uku, kuskurar baki da shaƙa ruwa suna daga gare shi .
4- Wanke hannaye zuwa gwiwowin hannaye sau uku, da farawa da dama sannan hagu.
5- Shafar kai tare da kunnuwa biyu.
6- Wanke ƙafafuwa zuwa idan sawu sau uku, da farawa da ƙafar dama sannan hagu.
Masu warware alwala:
1- Mai fita daga hanyoyi biyu, kamar: Fitsari da iska (tusa) da bayan gida.
2- Mai fita wanda ya yi muni mai najasa daga jiki.
3- Gushewar hankali da bacci ko waninsa.
4- Shafar farji da hannu, gaba ne ko baya ne ba tare da makari ba.
5- Cin naman raƙumi.
6- Ridda (fita) daga musulunci, Allah Ya tsaremu da musulmai daga hakan.
Na bakwai: Huknce-hukuncen shafa akan huffi biyu da jaurabi biyu:
1- Huffi: Abinda ake sawa a ƙafafuwa na fata da makancinsa.
2- Jaurabi: Abinda ake sawa a ƙafauwa na suf ko auduga da makancinsu.
Sharuɗɗan shafa akansu:
1- Ya sanya su bayan cikar tsarki.
2- Ya rufe ƙafafuwa tare da idan sawu.
3- Su kasance masu tsarki.
4- Shafar ta zama a cikin iyakantaccen lokaci.
5- Shafar ta zama a alwala banda wanka.
6- Huffin da makancinsa ya zama halastacce, idan ya zama wanda aka ƙwata ne, ko alhariri dangane da namiji; to shafa akansa ba ta halatta; domin haramtaccen abu ba'a halatta rangwame da shi ba.
Lokacin shafar:
Ga mazaunin gida: Yini da dare, matafiyi kuma: Kwana uku da dararensu.
yadda ake shafar:
Za'a jika hannu da ruwa, kuma a yi shafa akan saman jauraban ko huffin, daga yatsun ƙafafuwa zuwa ƙwauri, sau ɗaya.
Masu ɓata shafa:
1- Karewar Lokacin shafar.
2- Tuɓe jauraban ko ɗayansu.
3- Faruwar babban kari.
Hukuncin shafa akan huffi:
Cewa shi rangwame ne, kuma aikata shi shi ne ya fi daga cire huffin da wanke ƙafafuwa; dan riƙo da rangwamin Allah - Mai girma da ɗaukaka -, da koyi da annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, da kuma saɓawa 'yan bidi'a.
3- Shafa akan karan dori da bandeji da gam (filistar magani):
Karan dori: Shi ne abinda ake ɗaurewa akan karaya; na sumunti ko karare da makamancinsu.
Bandeji kuma: Shi ne abinda ake ɗaurewa akan ciwo, ko maruru ko ƙuna; na tsumma ne, da makancinsa.
Gam kuwa: Abinda ake mannawa akan ciwo ko maruru dan magani.
Hukuncin shafa a kansu:
Yana halatta: A lokacin buƙatar wanzuwarsu, da sharaɗin kada ya ƙetare bigiren buƙata.
Ba ya halatta: Idan buƙatuwa zuwa gareshi ta ƙare, ko kuma wahala ko cuta basa tabbatuwa akan tuɓesu.
Yadda ake shafa akansu:
Ana wanke abinda ke gefansu, kuma ana shafa akansu daga dukkan sasanni Ba'a shafar abinda ya ƙaru akan wurin alwalar.
Na takwas: Hukence-hukuncen Taimama:
Taimama: Ita ce shafar fuska da tafuka a bigire, da nufin tsarki, ta keɓantacciyar fuska.
Hukuncinta:
Taimama tana wajaba maimakon alwala da wanka, a lokacin rashin ruwa, ko rashin iko akan anfani da shi ruwan.
Hikima akan shara'antata:
Taimama tana daga abubuwan da suka kebanci al'ummar (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, kuma ba ta kasance sananniya ba a cikin al'ummun da suka gabata, dan yalwatawa daga Allah ga wannan al'ummar, da kuma kyautatawa gareta daga gare shi.
Halayen da aka halatta taimama a cikinsu:
1- Idan ya rasa ruwa, daidai ne ya rasa shi ne a zaman gida, ko a halin tafiya, kuma ya neme shi bai same shi ba.
2- Idan ya kasance a tare da shi akwai ruwan da yake buƙatuwa don sha ko girki, to da zai yi tsarki da shi, da ya cutar da buƙatarsa, inda yake tsoron ƙishirwa akan kansa, ko ƙishirwar waninsa na ɗan Adam, ko dabba waɗanda suke ababen girmamawa.
3- Idan ya ji tsoron cuta a cikin jiknsa na rashin lafiyarsa ko jinkirin warkewa idan ya yi anfani da ruwa.
4- Idan ya kasa anfani da ruwan, don rashin lafiyar da ba zai iya motsi tare da ita ba, kuma babu wanda zai yi masa alwala, kuma ya ji tsoron fitar lokaci.
5- Idan ya ji tsoron sanyi, ta hanyar anfani da ruwa, kuma bai samu abinda zai dafa shi da shi ba, to sai ya yi taimama, ya yi sallah.
Siffar taimama:
Ya bugi turɓaya da hannayensa, yana mai buɗe yatsun, sannan ya shafi fuskarsa da cikin yatsunsa, ya shafi tafukansa da tafinsa, ya game fuska da tafuka da shafar.
Masu ɓata taimama:
1- Samun ruwa idan taimamar ta kasance dan rashinsa ne. ko iko akan yin anfani da shi idan taimamar ta kasance dan rashin iko akan anfani da shi ne.
2- Tana ɓaci da ɗaya daga cikin abubuwan da suke ɓata alwala, ko ɗaya daga abubuwan dake wajabta wanka, na janaba da al’ada da nifasi (haihuwa).
Hukuncin wanda ya gajiya daga anfani da ruwa da kuma taimama:
Wanda ya rasa ruwa da turɓaya, ko ya kai halin da ba zai iya taɓa fatar shi da ruwan ko da turɓayar ba; to cewa shi zai yi sallah akan gwargwdan halinsa, ba tare da alwala ko taimama ba; domin Allah baYa ɗorawa wata rai sai abinda zata iya. Da za'a ƙaddara cewa, ya samu ruwa ko turɓayar bayan haka, ko ya samu iko akan amfani da su; to ba zai maimaita abinda ya sallata ba; domin ya zo da abinda aka umarce shi da shi. saboda faɗinSa - Allah Maɗaukakin sarki -:
﴿...فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ مَا ٱسۡتَطَعۡتُمۡ...﴾
{...sai ku bi Allah da taƙawa (tsoran Allah) gwargwadon abin da kuka sãmi ĩko...} [al-Tagabun: 16], kuma saboda faɗinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: «Idan na umarceku da wani al'amari, to ku zo da shi daidai iyawarku»11.
Fa'ida: Idan ya yi taimama saboda janaba, sannan ya samu ruwa; to shi zai yi wanka.
Na tara: Hukunce-hukuncen al’ada da nifasi (jinin haihuwa):
Na farko: Al’ada:
Shi jinin al’ada ne da halitta, yana fita daga cikin mahaifa, a wasu sanannun lokuta. A galibi yana fita a kowanne wata kwana shida ko bakwai, yakan ƙaru ko ya ragu, Watan mace yana tsawaita, ko ya ragu; gwargwdan yadda Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya tsara shi na daga ɗabi'u.
Hukunce-hukuncen Al’ada:
1- Mai al’ada, ba ta sallah, ba ta azumi a lokacin al’adarta, kuma (idan ta yi) ba su inganta daga gareta ba.
2- Mai al’ada zata rama azumi banda sallah idan ta tsarkaka daga al’adarta.
3- Ɗawafi a Ka’aba, ba ya halatta a ga mai al’ada. ba zata karanta AlKur'ani ba, kuma ba zata zauna a cikin masallaci ba, 4- Jima'i da ita ta farji yana haramta akan mijinta, har sai al’adar ta yanke kuma ta yi wanka.
5- Yana halatta mijin mai al’ada, ya ji daɗi da ita ba tare da jima'i a farji ba, kamar sumbata, da shafa, da makamancin hakan.
6- Ba ya halatta ga mijinta ya saketa alhali tana al’ada.
Tsarki shi ne daukewar jini, idan jini ya yanke; to haƙiƙa ta yi tsarki, kuma kwanakin al’adarta sun ƙare, to wanka yana wajaba akanta, Sannan ta aikata abinda aka hanata daga gare shi saboda jinin al’ada.
Idan bayan ta yi tsarki, sai ta ga hanta-hanta, ko fatsi-fatsi; ba zata waiwaiya garesu ba.
Na biyu: Jinin biƙi:
Shi jini ne da mahaifa take zubo da shi, saboda haihuwa da bayan haihuwar, shi ne ragowar jinin da aka tsare a lokacin ɗaukar ciki.
Jinin biƙi kamar al’ada yake a cikin abinda yake halatta; kamar jin daɗi daga gareta ta koma bayan farji.
Da kuma abinda yake haramta; kamar jima'i a cikin farji, da hana azimi, da sallah, da saki, da ɗawafi, da karatun AlKur'ani, da zama a cikin masallaci. Da wajabcin wanka a yayin yankewar jininta kamar al’ada.
Kuma yana wajaba akanta ta rama azimi banda sallah, ba zata ramata ba kamar mai al’ada.
Mafi yawancin lokacinsa kwana arba'in ne. Idan jinin biƙi ya yanke kwana arba'in, to haƙiƙa jinin biƙinta ya ƙare, sai ta yi wanka, zata yi sallah, zata aikata abinda aka hanata aikata shi saboda jinin biƙin.
Mabhasi na biyu: Sallah:
Na farko: Hukunce-hukncen kiran sallah da iƙama:
An shar'anta kiran sallah a cikin shekara ta farko, daga hijirar Annabta. Dalilin shar’anta shi ne; lokacin da gane lokutan sallah ya tsananta a garesu, sai su ka yi shawara a kafa wa lokacin sallah alama, sai aka nunawa Abdullahi ɗan Zaid - Allah Ya yarda da shi - wannan kiran sallar a cikin mafarki, kuma wahayi ya tabbatar da shi.
Kiran sallah: Sanar da shigar lokacin sallah. Iƙama: Ita ce sanar da ta da sallah.
Kiran sallah da iƙama farilla ne na kifaya (wanda wani zai daukewa wani) akan jama'ar maza a sallolin farilla, Su suna daga alamomin musulunci na zahiri, barinsu ba ya halatta.
Sharuɗɗan kiran sallah:
1- Ladanin ya zama namiji ne.
2- Kiran sallar ya zama a jere.
3- Kiran sallar ya zama mai bibiyar juna ne .
4- Kiran sallar ya zama bayan shigar lokaci, an togance daga hakan: Kiran sallar farko a Asuba da kuma Juma'a.
Sunnonin kiran sallah:
1- Ya sanya yatsunsa a cikin kunnuwansa.
2- Kiran sallah a farkon lokaci.
3- Waiwaye tare da Hai'ala biyu dama da hagu.
4- Ya zama mai kyakkyawan sauti.
5- Yabi a hankali (a sannu) da lafazu kan kiran sallah, ba tare da yalwatawa ba, ba kuma madda (Ja) mai wuce gona da iri ba.
6- Ya tsaya akan kowace jumla daga gare shi .
7- Ya fuskanci alƙibla a halin kiran sallah.
Kiran sallah jumla goma sha biyar ne, kamar yadda Bilal - Allah Ya yarda da shi - ya kasance yana kiran sallah da shi a gaban manzon Allah - tsira daa mincin Allah su tabbata agare shi - a koda yaushe.
Lafuzzan kiran sallah:
(Allah ne mafi girma): sau huɗu.
(Ina shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah): Sau biyu.
(Ina shaida cewa (Annabi) muhammad manzon Allah ne): Sau biyu.
(Ku taho zuwa sallah): Sau biyu,
(Ku taho zuwa tsira): Sau biyu.
Sannan ya ce: (Allah ne mafi girma): sau biyu.
Sannan ya cika da (Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah): Sau ɗaya.
A Asuba sai ya ƙara bayan ku yi gaggawa zuwa tsira: (Sallah ita ce mafi alheri daga bacci) sau biyu; domin cewa lokaci ne da mutane a galibi suke bacci a cikinsa.
Iƙama jumla goma sha ɗaya ce zai yi ta a sake, wato: Zaiyi sauri a cikinta; domin cewa ita dan sanar da mahalarta ne, babu wani buƙatuwa da yinta a hankali, (kamar kiran Sallah).
Sigarta kamar yadda zai zo :
(Allah ne mafi girma): Sau biyu.
(Ina shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah): Sau ɗaya.
(Ina shaida cewa (Annabi) Muhammad manzon Allah ne): Sau ɗaya.
(Ku taho zuwa sallah): Sau ɗaya.
(Ku taho zuwa rabauta): Sau ɗaya.
(Haƙiƙa sallah ta tsayu): Sau biyu.
(Allah ne mafi girma): Sau biyu.
(Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah): Sau ɗaya.
Ana so ga wanda ya ji kiran sallah ya faɗi irin abinda mai kiran sallar yake faɗa, sai dai a (Ku taho zuwa sallah), da kuma (Ku taho zuwa rabauta) sai ya ce; (Babu wata dabara babu wani ƙarfi sai ga Allah). Sannan ya yi salati ga annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi -. Sannan bayan nan ya ce: «Ya Allah Ma’abocin (Ubangjin) wannan cikakkan kira, da sallah mai tsayawa, Ka bawa (Annabi) Muhammad wasila da fadila, Ka tashe shi a matsayi abin yabo, wanda Ka yi alƙawarinsa, lallai Kai ba Ka saɓa alƙawari»12.
Sai kuma ya ce: «Na yarda da Allah a matsayin Ubangiji, da musulunci a matsayin addini, da (Annabi) Muhammad-tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- a matsayin annabi»13.
Fita daga masallaci yana haramta bayan kiran sallah ba tare da wani uzuri ba, ko niyyar dawowa.
A lokacin haɗa wa tsakaknin salloli biyu, yana isuwa da kiran sallah ɗaya da iƙama ga kowace sallah.
Na biyu: Matsayin sallah da falalarta:
Sallah ita ce mafi ƙarfin rukunan musulunci bayan shahada biyu, tana da keɓantaccen matsayi, yayin da Allah Ya wajabta ta ga manzonSa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a daren mi'iraji a sama, Sai hakan ya yi nuni akan girmanta, da ƙarfafar wajabcinta, da matsayinta a wurin Allah - Mai girma da ɗaukaka -.
haƙiƙa Hadisai da yawa sun zo akan falalarta da wajabcinta akan kowa da kowa, wajabcinta sanannene da larura daga addinin musulunci.
Daga abinda yake nuni akan wajabcinta da ƙarfafarta: Nassosi masu yawa daga AlKur'ani da Sunna, daga cikinsu:
1- FaɗinSa - Allah Maɗaukakin sarki -:
﴿...إِنَّ ٱلصَّلَوٰةَ كَانَتۡ عَلَى ٱلۡمُؤۡمِنِينَ كِتَٰبٗا مَّوۡقُوتٗا﴾
{...lalle ne salla tã kasance a kan mũminai, farilla mai ƙayyadaddun lõkuta.} [al-Nisa'i: 103]. Wato: Abar farlantawa, a cikin lokutan da manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya bayyanasu.
2- Da faɗinSa - Allah Maɗaukakin sarki -:
﴿وَمَا أُمِرُوا إِلَّا لِيَعْبُدُوا اللَّهَ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ حُنَفَاءَ وَيُقِيمُوا الصَّلَاةَ...﴾
{Kuma ba'a umarcesu da komai ba, sai bautawa Allah, suna masu tsarkake addini gare Shi, masu karkata zuwa ga addinin gaskiya, kuma su tsaida sallah...} [al-Bayyinah: 5].
Da faɗinSa - Allah Maɗaukakin sarki -:
﴿فَإِنْ تَابُوا وَأَقَامُوا الصَّلَاةَ وَآتَوُا الزَّكَاةَ فَإِخْوَانُكُمْ فِي الدِّينِ...﴾
{Sannan idan sun tuba, kuma suka tsayar da Sallah, kuma suka bada zakka to ‘yan’uwanku ne a cikin addini...} [al-Taubah: 11].
4- Daga Jabir - Allah Ya yarda da su - cewa manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Lallai tsakanin mutum da shirka da kafirci (shi ne) barin sallah»14.
5- Daga Buraidah - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Lallai alƙawarin da ke tsakanin mu da su (shi ne) sallah, wanda ya barta, to, haƙiƙa ya kafirta»15
Malamai sun yi ijma'i akan kafircin wanda ya yi musun wajabcinta, Amma wanda ya barta don kasala (lalaci) da wulaƙantarwa, to magana mafi inganci (ita ce) kafircinsa, saboda hadisin da ya gabata, da kuma ijma'in sahabbai akan hakan.
Na uku: Sharuɗɗan sallah:
1- Shigar lokacinta:
saboda faɗinSa - Allah Maɗaukakin sarki -:
﴿...إِنَّ ٱلصَّلَوٰةَ كَانَتۡ عَلَى ٱلۡمُؤۡمِنِينَ كِتَٰبٗا مَّوۡقُوتٗا﴾
{...lalle ne salla tã kasance a kan mũminai, farilla mai ƙayyadaddun lõkuta.} [al-Nisa'i]. Wato: Abar wajabtawa a ƙayyadaddun lokuta.
Lokutan sallolin farilla kamar yanda yake tafe:
A- Asuba: Daga hudowar alfijir zuwa ɓullowar rana.
B- Azahar: Daga karkatar rana, zuwa inuwar kowane abu ta zama tamkarsa a tsawo.
J- La'asar: Daga ƙarshen lokacin Azzahar, zuwa fatsi-fatsin rana, kuma lokacinta na laruri zuwa faɗuwarta (rana).
D- Magariba: Daga faɗuwar rana zuwa ɓuyan jan shafaƙi.
E- Issha'i: Daga ƙarewar loacin magariba zuwa rabin dare.
2- Boye al'aura:
Ita ce abinda rufe shi yake wajaba kuma bayyanarsa yake muni ake jin kunya daga gare shi. Al'aurar namiji daga cibiya zuwa gwiwa. Mace kuwa dukkaninta al'aurace a cikin sallah sai fuskarta. Zata rufe fuskarta idan ta kasance a gaban maza manisantarta wato: Ba muharramanta ba.
3- Nisantar najasa:
Najasa: Ita ƙazanta ce keɓantacciya, jinsinta yana hana sallah, kamar fitasri da bahaya da jini da wasunsu, kuma tana kasancewa a jiki da guri da kuma tufafi.
4- Fuskantar alƙibla:
Alkibla ita ce Ka'aba mai daraja, an anbaceta alƙibala ne dan fuskantar mutane gareta.
Sallah bata inganta batare da fuskantar alƙibala ba, saboda faɗinSa - Allah Maɗaukakin sarki -:
﴿...وَحَيۡثُ مَا كُنتُمۡ فَوَلُّواْ وُجُوهَكُمۡ شَطۡرَهُ...﴾
{...kuma inda duk kuka kasance, to, ku jũyar da fuskõkinku jiharsa...} [al-Baƙara: 144].
5- Niyya:
Ita ce a luga: Nufi, a shari'a kuma: Kudirce niyya akan aikata wani aikin ibada dan neman kusanci zuwa ga Allah - Maɗaukakin sarki -. Kuma bigiranta zuciya ne, ba'a buƙatuwa zuwa ga furtatawa, kai shi bidi'a ce ma.
Na huɗu: Rukunan sallah:
Su rukunai goma sha huɗu ne:
Rukuni na farko: Tsayuwa tare da iko:
Saboda faɗinSa - Allah Maɗaukakin sarki -:
﴿...وَقُومُواْ لِلَّهِ قَٰنِتِينَ﴾
{...kuma ku tsayu kuna mãsu ƙanƙan da kai (biyayya) ga Allah.} [al-Baƙara; 238], da Hadisin Imran - Allah Ya yarda da shi - Marfu'i: «Ka yi sallah a tsaye, idan ba za ka iya ba, to, a zaune, idan ba za ka iya ba, to, a ɓarin jiki»16.
Idan ba zai iya tsayuwa ba, saboda rashin lafiya; to ya yi sallar gwargwadan halinsa, azune ne ko a ɓangaren jiki, misalin mara lafiya: Mai jin tsoro, da mara tufafi, da wanda yake buƙatuwa ga zama ko kwanciya dan maganin da yake buƙatar rashin tsayuwa. Haka nan ana yi wa wanda yake sallah a bayan liman ratibi uzuri na barin tsayuwa, idan liman ba zai iya tsayuwar ba, sai shi ma ya yi sallah a zaune, to wanda ke bayansa za su yi sallah a zaune don bin limaminsu. Yin nafilfili yana halatta a zaune, koda ya kasance mai iko a tsayuwa, sai dai ladan ba zai zama kamar ladan wanda ya yi a tsaye ba.
Rukuni na biyu: Kabbarar harama a farkonta:
Saboda faɗinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: «Sannan ka fuskanci alƙibla, ka yi kabbara»17.
Lafazinta shi ne ya ce: (Allah ne Mafi girma), waninsa ba ya halatta.
Rukuni na uku: Karatun Fatiha:
Saboda faɗinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: «Babu sallah ga wanda bai karanta Fatiha ba»18.
Rukuni na huɗu: Ruku'u a kowace raka'a:
Saboda faɗinSa - Maɗaukakin sarki -:
﴿يَاأَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا ارْكَعُوا وَاسْجُدُوا...﴾
{Yaku waɗanda suka yi imani, ku yi ruku'u ku yi sujjada...} [al-Hajj: 77].
Rukuni na biyar da na shida:
Dagowa daga ruku'u, da daidaito a tsaye kamar yadda yake kafinsa, domin cewa shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya dawwama akan aikata shi.
Tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya cewa mai munana sallarsa: «Sannan ka ɗago har sai ka daidaita a tsaye»19.
Rukuni na bakwai: Sujjada akan gaɓɓai bakwai.
Sune goshi hanci yana tare da shi, da hannaye biyu, da gwiwowi biyu, da gefunan diga-digai, Saboda faɗinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: «An umarce mu, mu yi sujjada akan ƙasusuwa bakwai: Goshi, sai ya yi nuni da hannunsa zuwa hancinsa, da tafuka biyu, da gwiwowi biyu, da gefunan diga-digai»20.
Rukuni na takwas: Dagowa daga sujjada da zama tsakanin sujjadu biyu;
Saboda Hadisin Aisha - Allah ya yarda da ita - «Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance idan ya ɗago kansa daga sujjada, ba ya yin sujjada har sai ya daidaita a zaune»21.
Rukuni na tara: Nutsuwa a dukkanin rukunai:
Ita ce nutsuwa koda ta ƙaranta, saboda faɗinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ga wanda ya munana sallarsa: «Har sai ka nutsu»22.
Rukuni biyu: Na goma da na goma sha ɗaya:
Tahiyar ƙarshe da zamanta: Saboda Hadisin Ibnu Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - Marfu'i: «Idan ɗayanku ya yi sallah, to, ya ce: At-tahiyyātu lillāhi was-salawātu wat-tayyibāt. As-salāmu ‘alayka ayyuha an-nabiyyu wa rahmatullāhi wa barakātuh. As-salāmu ‘alayna wa ‘ala ‘ibādillāhi as-sālihīn. Ash'hadu alla ilāha illallāh, wa ash'hadu anna Muhammadan ‘abduhu wa rasūluh» (Tsarkakan gaisuwa sun tabbata ga Allah, da salloli da tsarkakan abubuwa, aminci ya tabbata a gare ka ya kai wannan Annabi da rahamar Allah da albarkarSa, aminci ya tabbata agaremu da bayin Allah salihai, ina shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah ina shaida cewa (Annabi) Muhammadu bawanSa ne kuma manzanSa ne)23.
Rukuni na goma shabiyu: Salati ga annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - a tahiyar ƙarshe:
Shine ya ce: «Ya Allah Ka yi salati ga (Annabi) Muhammad»24. abinda ya ƙaru akan hakan, to shi sunna ne.
Rukuni na goma sha uku: Jerantawa tsakanin rukunai:
Domin annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana aikatasu a jere. Kuma ya ce: «Ku yi sallah, kamar yadda kuka ga ina yin sallah»25 Kuma ya sanar da mai munana sallarsa ita a jere da (lafazin) "Sannan".
Rukuni na goma sha huɗu: Sallama:
Saboda faɗinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: «Kuma ƙarshenta (cikarta) shi ne sallama», Da faɗiinSa: "Kuma cikawarta (fita daga gareta), shi ne yin sallama»26.
Na biyar: Wajiban sallah:
Su takwas ne:
1- Dukkanin kabbarori banda kabbarar harama.
2- Faɗin «Subhāna rabbiyal ‘azhīm» (Tsarki ya tabbata ga Ubangijina mai girma) a cikin ruku'u sau ɗaya, an sunnanta ƙarawa zuwa uku, hakan kuma shi ne mafi ƙarancin cika, zuwa kuma goma ita ce mafi ɗaukakarsa.
3- Faɗin: «Sami‘allāhu liman hamidah» (Allah Ya ji wanda ya gode maSa) a ɗagowa daga ruku'u; ga liman da mai yin sallah shi kaɗai.
4- Faɗin: «Rabbana wa lakal-hamd» (Ya Ubangijin mu, godiya ta tabbata gareKa) a daidaituwa daga ruku'u
5- Faɗin: «Subhāna rabbiyal a‘la» (Tsarki ya tabbata ga Ubangijina Mafi ɗaukaka) a cikin sujjada sau ɗaya, an sunnanta ƙarawa zuwa uku.
6- Faɗin: «Rabbigh firli» (Ya Ubangina Ka gafarta mini). Tsakanin sujjada biyu sau ɗaya, an sunnanta ƙarawa zuwa uku.
7- Tahiyar farko; ita ce ya ce: «At-Tahiyyātu lillāhi was-salawātu wa at-tayyibāt, as-Salāmu ‘alayka ayyuha an-nabiyyu wa rahmatullāhi wa barakātuh, as-salāmu ‘alayna wa ‘ala ‘ibādillāhi as-sālihīn. Ash'hadu alla ilāha illallāh, wa ash'hadu anna Muhammadan ‘abduhu wa rasūluh». Tsarkakan gaisuwa sun tabbata ga Allah, da salloli da tsarkakan abubuwa, aminci ya tabbata agareka ya kai wannan annabi da rahamar Allah da albarkarSa, aminci ya tabbata agaremu da bayin Allah salihai, ina shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah ina shaida cewa (Annabi) Muhammadu bawanSa ne kuma manzanSa ne"27.
8- Zama domin tahiyar farko.
Na shida: Sunnonin sallah:
Sunnonin sallah, sallah ba ta ɓaci saboda barinsu, Su sun rabu gida biyu: Sunnoni na faɗa, da sunnoni na aikatawa.
Na farko: Sunnoni na faɗa:
1- Addu'ar buɗe sallah, tana da sigogi, daga cikinsu: «Subhānak Allāhumma wa bihamdik, wa tabārak ismuk, wa ta‘āla jadduk, wa la ilāha ghayruk» (Tsarki ya tabbata a gareKa Ya Ubangiji haɗi da gode maKa, kuma albarkar sunanKa ta yawaita, girmanKa ya daukaka babu abin bautawa in ba Kai ba)28.
2- Ta'awwuzi kafin fatiha, Shi ne faɗin: «A‘ūdhu billāhi minash-shaytānir rajīm» (Ina neman tsarin Allah daga Shaiɗan abin jefewa).
3- Bisimillah kafin karatu, ita ce faɗin: "Da sunan Allah Mai rahama Mai jin ƙai".
4- Abinda ya ƙaru akan sau ɗaya a cikin tasbihi da sujjada.
5- Abinda ya ƙaru akan sau ɗaya daga faɗin: «Rabb ighfirli» (Ya Ubangiji Ka gafarta mini). tsakanin sujjada biyu.
6- Faɗin: «Mal’as-samāwāti wa mal’al-ardi wa mal’a ma baynahuma wa mal’a ma shi’ta min shay’in ba‘d» (Cikar sammai, da cikar ƙasa, da cikar abinda ke tsakaninsu, da cikar abinda Ka so daga wani abu bayan nan). Bayan faɗinsa: «Rabbana wa lakal-hamd» (Ubangijinmu godiya ta tabbata a gareKa)29.
7- Karatu bayan fatiha.
8- Faɗin: «Allāhumma inni a‘ūdhu bika min ‘adhābi jahannam wa min ‘adhābil-qabr, wa min fitnatil-mahya wal-mamāt, wa min fitnatil-masīh ad-dajjāl» (Ya Allah ni ina neman tsarinKa daga azabar Jahannama, da kuma azabar ƙabari, daga fitinar rayuwa, da ya mutuwa, daga kuma fitinar Masihul Dajjal)30. Abinda ya ƙaru akan hakan na addu'a a tahiyar ƙarshe.
Na biyu: Sunnoni na aikatawa:
1- Daga hannaye daura da kafaɗu biyu ko kunnuwa biyu a wurare huɗu:
A- A lokacin kabbarar harama.
B- A lokacin ruku'u.
C- A lokacin ɗagowa daga ruku'u.
D-A lokacin tashi zuwa raka'a ta uku.
2- Dora hannun dama akan hagu akan ƙirji a tsakiyar tsayuwa kafin ruku'u da bayansa.
3- Kallo zuwa wurin sujjada.
4- Nisantar da (buɗa) damuttsa biyu daga gefe biyu, a yayin sujjada.
5- Nisantar da ciki daga cinyoyi a yayin sujjada biyu.
6- Yin zaman iftirash a dukkanin zaman sallah, sai a cikin tahiyar ƙarshe, a sallah mai raka'a uku da mai raka'a huɗu.
7- Zaman tawarruk (wato ɗora mazauni a kasa) a cikin tahiyar ƙarshe a sallah, mai raka'a uku ko mai raka'a huɗu.
Na bakwai: Siffar sallah:
1- Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya tashi zuwa sallah, yana fuskantar alƙibla, yana ɗaga hannayensa, ya fuskanci alƙibla da cikin yatsunsu, sai ya ce: "Allah ne Mafi girma".
2- Sannan ya riƙe hagunsa da damnsa, ya ɗorasu a kan ƙirjinsa.
3- Sanna ya yi addu'ar buɗe sallah, bai kasance yana dawwama akan addu'ar buɗe sallah kala ɗaya ba, dukkanin addu'o'in buɗe sallah tabbatattu daga gare shi yana halatta a buɗe sallah da su, daga cikinsu: «Subhānak Allāhumma wa bihamdik, wa tabārak-asmuk, wa ta‘āla jadduk, wa la ilāha ghayruk» (Tsarki ya tabbatar maKa ya Allah da godiyarKa, alherin sunanka ya yawaita, girmanKa ya ɗaukaka, babu wani Ubangiji waninKa).
4- Sannan ya ce: «A‘ūdhu billāhi minash-shaytānir rajīm, bismillāhir rahmānir rahīm» (Ina neman tsarin Allah daga Shaiɗan abin jefewa, da sunan Allah Mai rahama Mai jin ƙai).
5- Sannan ya karanta fatiha, idan ya cikata: Ya ce: "Amin".
6- Sannan ya karanta abinda ya sawwaƙa daga Alkur’ani, Ya bayyanar da karatu a Asuba, da raka'a biyun farko a Magariba da Issha'i. Ya ɓoye karatu a koma bayan hakan. Ya tsawaita raka'a ta farko daga kowace sallah mafi tsayi daga ta biyu.
7- Sannan ya ɗaga hannayensa kamar yadda ya ɗaga su a addu'ar buɗe sallah, Sannan ya ce: (Allah ne mafi girma). Sai ya sunkuya yana mai ruku'u, ya ɗora hannayensa akan gwiwowinsa yana mai rarraba yatsu, yana mai tabbatar da su, yana miƙe bayansa, yana sanya kansa daura da shi; ba zai ɗagosu ba, ba kuma zai yi kasa da su ba, yana mai cewa: «Subhāna rabbiyyal-‘azhīm» (Tsarki ya tabbata ga Ubangijina Mai girma) sau ɗaya, mafi ƙasan cika: Sau uku, kamar yadda ya gabata.
8- Sannan ya ɗago kansa yana mai cewa: «Sami‘allāhu liman hamidah» (Allah Yana jin wanda ya gode maSa). yana ɗaga hannayensa kamar yadda yake ɗagosu a lokacin ruku'u.
9- Idan ya daidaita a tsaye ya ce: «Allāhumma rabbana wa lakal-hamd, hamdan kathīran tayyiban mubārakan fīh, mal’as-samāwāti wa mal’al-ardi wa mal’a ma baynahuma wa mal’a ma shi’ta min shay’in ba‘d, ahluth-thanā’i wal-majd, ahaƙƙu ma ƙālal-‘abd, wa kulluna laka ‘abd, la māni‘a lima a‘tayt, wala mu‘tiya lima mana‘t, wala yanfa‘u dhal-jaddi minkal-jaddYa».
(Allah Ubangijinmu godiya ta tabbata gareka, godiya mai yawa mai tsarki mai albarka a cikinta, cikar sama, da cikar ƙasa, da cikar abinda ke tsakaninsu, da cikar abinda Kaso daga wani abu bayan nan, ma'abocin yabo da girma, mafi cancantar abinda bawa ya faɗa, dukkaninmu bayinKa ne, ba mai hana abinda Ka bayar, kuma ba mai bada abinda Ka hana, kuma ƙoƙari ba ya anfanar mai ƙoƙarin daga gareKa)31 . Ya kasance yana tsawaita wannan daidaiton.
10- Sannan ya yi kabbara ya sunkuya yana mai sujjada, ba zai ɗaga hannayensa ba, ya yi sujjada akan goshinsa da hancinsa da hannayensa da gwiwowinsa da gefan diga-digansa, ya fuskanci alƙibla da yatsun hannayensa da ƙafafuwansa, ya daidaita a cikin sujjadarsa, ya tabbatar da goshinsa da hancinsa a ƙasa, ya dogara akan tafukansa, ya ɗaga gwiwowin hannayensa, yana nisantar da damuttsansa daga geffensa, ya ɗago cikinsa daga cinyoyinsa, da cinyoyinsa daga ƙwaurukansa, Zai faɗa a sujjadarsa: «Subhāna rabbiyyal-a‘la» (Tsarki ya tabbata ga Ubangijina mafi ɗaukaka). Sau ɗaya. mafi ƙarancin cika sau uku kamar yadda ya gabata, ya yi addu'a da abinda ya zo.
11- Sannan ya ɗago kansa yana mai cewa: "Allah ne Mafi girma". Sannan ya shinfiɗa ƙafarsa ta hagu, ya zauna akanta, ya kafa ta dama, ya ɗora hannayensa akan cinyoyinsa sannan ya ce: «Allāhumma ighfirli warhamni wajburni wahdini warzuƙni» (Ya Allah Ka gafarta mini, Ka yi mini rahama, Ka gyarani, Ka shiryar dani, Ka azirtani)32.
12- Sannan ya yi kabbara ya yi sujjada, yana aikatawa a raka'a ta biyu kamar yadda ya aikata a raka’a ta farko.
13- Sannan ya ɗago kansa yana mai kabbara, ya dago akan saman diga-digansa, yana mai dogara akan gwiwowinsa da cinyoyinsa.
14- Idan ya daidaita a tsaye; sai ya fara karatu, ya sallaci raka'a ta biyu kamar ta farko.
15- Sannan ya zauna dan tahiyar farko yana mai Iftirashi kamar yadda ya zauna tsakanin sujjada biyu, yana mai ɗora hannunsa na dama akan cinyarsa ta dama, da hannunsa na hagu akan cinyarsa ta hagu, yana ɗora babban ɗan yatsansa na dama akan ɗan yatsansa na tsakiya kamar siffar halƙa (kewayo). yana nuni da ɗan yatsansa sabbaba, yana kallonsa gare shi, yana cewa: «At-tahiyyātu lillāhi was-salawātu wat-tayyibāt, as-salāmu ‘alayka ayyuha an-nabiyyu wa rahmatullāhi wa barakātuh. As-salāmu ‘alayna wa ‘ala ‘ibādillāhi as-sālihīn. Ash'hadu alla ilāha illallāh, wa ash'hadu anna Muhammadan ‘abduhu wa rasūluh» (Tsarkakan gaisuwa sun tabbata ga Allah, da salloli da tsarkakan abubuwa, aminci ya tabbata agareka ya kai wannan annabi da rahamar Allah da albarkarSa, aminci ya tabbata a garemu da bayin Allah salihai, ina shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah ina shaida cewa (Annabi) Muhammadu bawanSa ne kuma manzanSa ne). Ya kasance yana sauƙaƙa wannan zaman.
16- Sannan ya yinkura yana mai kabbara, sai ya sallaci raka'a ta uku da ta huɗu, ya sauƙaƙasu daga na farko, yana karanta Fatihatul Kitab a cikinsu.
17- Sannan ya zauna a tahiyar ƙarshe yana mai Tawarruk, Tawarruk: shi ne ya shinfiɗa ƙafarsa ta hagu ya fitar da ita daga ɓangaren dama, ya kafa ta dama, ya sanya mazauninsa akan ƙasa.
18- Sannan ya yi tahiyar ƙarshe ita ce: Kamar tahiyar farko take, ya ƙara akan hakan: «Allāhumma salli ‘ala Muhammadin wa ‘ala āli Muhammadin kama sallayta ‘ala āli Ibrāhīm, innaka Hamīdun Majīd. Wa bārik ‘ala Muhammadin wa ‘ala āli Muhammadin kama bārakta ‘ala āli Ibrāhīm, innaka Hamīdun Majīd» (Ya Allah Ka yi salati ga (Annabi) Muhammad da alayen (Annabi) Muhammad, kamar yadda Ka yi salati ga alayen (Annabi) Ibrahim, lallai Kai godadde ne Mai girma ne, Ka yi albarka ga (Annabi) Muhammad da alayen (Annabi) Muhammad, kamar yanda Ka yi albarka ga alayen (Annabi) Ibrahim, lallai Kai abin godewa ne Mai girma".)
19- Ya nemi tsarin Allah daga azabar Jahannama, da azabar ƙabari, daga fitinar rayuwa da mutuwa, da kuma fitinar Masihul Dajjal. Ya yi addu'a da abinda ya zo daga addu'o'i a cikin AlKur'ani da Sunna.
20- Sannan ya yi sallama a daman sa, sai ya ce: «As-salāmu ‘alaykum wa rahmatullāh» (Amincin Allah a gareku da rahamar Allah). da kuma hagunsa kamar haka; Yana mai fara sallama, yana mai fuskantar alƙibla, yana mai ƙarewa tare da cika waiwaye.
Na takwas: Abubuwan da aka karhanta a sallah (abubuwan da ba'a son aikata su):
1- Waiwaye ba tare da buƙata ba.
2- Daga gani zuwa sama.
3- Rintse idanuwa ba tare da buƙata ba.
4- Shinfiɗa hannaye a cikin sujjada.
5- Rufe baki da hanci, ba tare da wata buƙata ba.
6- Sallah a halin matse fitsari ko bahaya, ko a gaban abincin da yake sha'awarsa.
7- Goge goshinsa da hancinsa daga abinda ya maƙale musu, na gurbin sujjada, babu laifi da goge hakan, bayan idar da sallah.
8- Jingina da gini da waninsa a halin tsayuwa ba tare da wata buƙata ba.
Na tara: Abubuwan da suke ɓata sallah:
1- Ci da sha.
2- Zance mai fita daga gareta (wanda ba ya daga jinsin sallah).
3- Dariya da ƙyaƙyatawa.
4- Gangancin barin ɗaya daga rukunanta ko wajibanta.
5- Gangancin ƙara wani rukuni ko raka'a.
6- Gangancin sallama kafin liman.
7- Motsi mai yawa a jere ba tare da jinsin sallah ba, ba kuma tare da wata ba.
8- Zuwa da abinda yake kore ɗaya daga sharuɗɗan sallah; kamar warware alwala, da yaye al'aura da gangan, da juyar da jiki da yawa daga alƙibla ba tare da wata larura ba, da yanke niyya.
Na goma: Sujjadar rafkanuwa:
Rafkanuwa: Mantuwa, haƙiƙa annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya yi rafkanuwa a cikin sallah; domin rafkanuwa tana daga ɗabi'ar mutuntaka, rafkanuwarsa ta kasance, daga cikar ni'imar Allah ga al'ummarsa, da cika addininsu, dan su yi koyi da shi a cikin abinda ya shara'anta musu, a lokacin rafkanuwa.
Dalilan da aka halatta sujjadar rafkanuwa garesu:
1- Hali na farko:
Kari a cikin sallah, shi ne kodai ƙara ayyuka, ko ƙara maganganu:
A- Kara ayyuka: Idan ƙari ya kasance daga jinsin sallah: Kamar tsayuwa a bigiren zama, da zama a bigiren tsayuwa, ko ya ƙara ruku'u ko sujjada, idan ya aikata hakan akan rafkanuwa; to shi zai yi sujjada dan rafkanuwa.
B- Kara maganganu: Kamar karatu a cikin ruku'u da sujjada,
Idan ya aikata hakan; an so ya yi sujjada don rafkanuwa.
2- Hali na biyu:
Ragi a sallah akan rafkanuwa, yana kasancewa da ɗaya daga al'amura biyu:
A- Barin wani rukuni: Idan wannan rukunin ya kasance kabbarar harama ce, to sallarsa ba ta ƙullu ba, kuma sujjadar rafkanuwa bata wadatarwa daga gareshi. Idan ya kasance wani rukuninne, ba kabbarar harama ba, kamar ruku'u ko sujjada, ya kuma tuna kafin fara karatun wata raka'ar daban; to shi zai dawo dole, sai ya zo da shi da abinda ke bayansa.
Idan ya tunashi bayan ya fara karatun wata raka'ar daban, to raka'ar da ya barshi (Ruku’i ko Sujjada) daga gareta ta ɓaci, raka'ar dake biye mata ta tsaya a matsayinta.
B- Barin wani wajibi: Kamar: Manta tahiyar farko, ko tasbihi a cikin ruku'u. A cikin wannan halin: Zai yi sujjada dan rafkanuwa.
3- Hali na uku: Kokwanto:
Misali: Da zai yi kokwanto shin ya yi sallaci raka'a uku ko huɗu a cikin sallar azahar, to a cikin wannan halin:
A- Idan wani abu ya rinjaya gare shi ; sai ya yi aiki da shi, ya yi sujjada dan rafkanuwa.
B- Idan wani abu bai yi rinjaye gare shi ba; to zai yi gini akan yaƙini, sai ya yi sujjada dan rafkanuwa.
Idan ya yi kokwanto bayan sallah, ko ya kasance mai yawan kokwanto ne; to ba zai juya ga wancan kokwantan ba.
Fa'idah: Sujjadar rafkanuwa tana kasancewa ne kafin sallama: Idan ya kasance daga ragi ne, ko daga kokwanto, kuma wani abu bai rinjaya a wurinsa ba. Kuma tana kasancewa bayan sallama: Idan ya kasance daga ƙari ne, ko daga kokwanto sai ya yi aiki a cikinsa da abinda ya rinjaya, Al'amari a hakan mai yalwa ne in Allah - Maɗaukakin sarki - Ya so.
Na goma sha ɗaya: Lokutan da aka hana yin sallah:
Asali shi ne halaccin sallah a dukkanin lokuta, saidai shari'a ta zo da haramcin sallah a wasu daga lokuta, sune kamar yadda yake tafe:
1- Daga bayan sallar Asuba zuwa ɓullowar rana, da ɗagowarta gwargwadan goron mashi daga ƙasa a ganin ido.
2- Lokacin da ta tsaya a tsakiyar sama, har sai ta karkace, shi ne mafi gajartar lokutan hani.
3- Daga sallar la'asar, har sai rana ta faɗi, shi ne mafi tsawon lokutan hani.
Sallolin da aikatasu yake halatta a cikin lokutan hani:
1- Rama farillan da suka wuce.
2- Salloli masu dalilai, kamar: Tahiyyatul masjid gaisuwar masallaci), da raka'o'i biyu na ɗawafi, da sallar kisfewar rana, da sallar jana'iza.
3- Rama sunnar alfijir bayan sallar asuba.
Na goma sha biyu: Sallar jam’i.
ita wata alama ce mai girma, daga alamomin musulunci, ita ce sallar jam'i a cikin masallatai, haƙiƙa musulmai sun haɗu akan cewa, yin salloli biyar a cikin masallatai yana daga mafi ƙarfin ayyukan biyayya, kuma mafi girman ayyukan kusanci, kai ita ce mafi girman alamomin musulunci.
1- Hukuncin sallar jam'i:
Sallar jam'i wajiba ce a cikin masallatai dan salloli biyar akan maza masu iko, a halin zaman gida da halin tafiya, a halin aminci, da halin tsoro wajabci na aini (wanda ya wajaba akan kowa da kowa).
Haƙiƙa AlKur’ani da sunnah, sun yi nuni akan wajabcin sallar jam'i: da aikin musulmai ƙarni bayan ƙarni, kalaf (mamaya) daga salaf (shudaddu).
Daga AlKur'ani: FaɗinSa - Allah Maɗaukakin sarki:
﴿وَإِذَا كُنتَ فِيهِمۡ فَأَقَمۡتَ لَهُمُ ٱلصَّلَوٰةَ فَلۡتَقُمۡ طَآئِفَةٞ مِّنۡهُم مَّعَكَ...﴾
{Idan ka kasance a cikinsu, sai ka tsayar musu da sallah, to wasu jama'a su tsaya tare da kai daga cikinsu...} [al-Nisa'i: 102]. Yayin da ayar ta yi nuni akan ƙarfafuwar wajabcin sallar jam'i, Inda ba'a yi wa musulmai rangwame ba a kan barin jam’i a halin tsoro ba, da ta kasance ba wajiba ba, da mafi cancatar uzuri da saryarta shi ne uzurin tsoro. Barin sallar jama'a, da nauyin yinta, yana daga mafi shaharar siffofin munafukai.
Yana daga Sunnah: Hadisai masu yawa, daga cikinsu:
Abinda ya zo a cikin Sahihu Muslim Cewa wani mutum makaho ya ce: Ya manzon Allah, banda jagoran da zai kai ni masallaci, sai ya tambaye shi, da ya yi masa rangwame ya yi sallah a gidansa, sai ya yi masa rangwamen, lokacin da ya juya baya (ya tafi), sai ya kira shi, sai ya ce: «Shin kana jin kairan sallah?» Ya ce: Eh, ya ce: «To ka amsa»33.
Sai annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi masa umarni da zuwa masallaci dan sallar jam’i da amsa kiran sallah, tare da cewa shi makaho ne duk da abinda yake gamuwa da shi na wahala, sai hakan ya yi nuni akan wajabcin sallar jam'i.
2- Abinda ake riskar jam’i da shi:
Ana riskar jam’i da riskar raka'a ɗaya daga sallah tare da liman, Saboda faɗinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: «Wanda ya riski raka'a ɗaya, daga cikin sallah, to, hakiƙa ya riski sallah»34.
3- Abinda ake riskar raka'a da shi:
Ana riskar raka'a da riskar ruku'u, idan masbuƙi (wanda aka tsere masa) ya riski limaminsa yana mai ruku'u: To yana wajaba ya yi kabbarar harama, alhali shi yana tsaye, sannan ya yi ruku'u yana mai kabbara karo na biyu dan yin ruku'u, idan ya taƙaita akan kabbarar harama a halin tsayuwarsa, to ta isar masa, daga kabbarar ruku'u.
4- Uzurin da yake halattawa mutum barin sallar jam'i:
1- Rashin lafiya idan ya kasance halartar jum’i da jama'a suna yi masa wahala.
2- Tunkuɗowar fitsari ko bayan gida; dan abinda yake jerantuwa akan tunkuɗosu na tafiyar da kushu'i a cikin sallah, dan kuma abinda ke cikinsa na cutarwa ga jiki.
3- Kawo abinci, alhali mutum yana jin yunwa, ko ransa yana sha'awar abin cin, akan cewa kada ya riƙe hakan al'ada, ko dabara ga barin halartar sallar jam’i.
4- Tabbataccen tsoro, ga rai ko dukiya, ko wasunsu.
Na goma sha uku: Sallar tsoro:
An shara'anta sallar tsoro a kowanne yaƙin da aka halatta, kamar yaƙar kafirai, da 'yan tawaye, da 'yan fashi, saboda faɗinSa - Allah Maɗaukakin Sarki -:
﴿...إِنۡ خِفۡتُمۡ أَن يَفۡتِنَكُمُ ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ...﴾
{...idan kun ji tsõron waɗanda suka kãfirta su fitine ku...} [al-Nisa'i: 101], Sai ka ƙiyasta ragowar akansa, cikin waɗanda yaƙarsu yake halatta.
kuma an shar'anta sallar tsoro da sharuɗɗa biyu:
1) Maƙiyin ya zama yaƙarsa ta halatta.
2) A ji tsoron farmakinsa akan musulmai a lokacin sallah.
Siffar sallar tsoro:
Tana da siffofi da yawa, mafi shahararsu kamar yadda ya zo a cikin hadisin Sahlu - Allah Ya yarda da shi -: Cewa wasu jama'a sun yi sawu tare da annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi -, wasu jama'ar kuma suna fuskantar maƙiya, sai ya yi sallah da wacce ke tare da shi raka'a ɗaya, sannan ya tabbata a tsaye, suka ciko da kansu, sannan suka juya, suka yi sawu suna masu fuskantar maƙiya, ɗaya jama'ar kuma suka zo , sai ya sallaci raka'ar data saura cikin sallarsa da su, sannan ya tabbata a zaune, suka cika da kansu, sannan ya yi musu sallama35.
Muna fa'idantuwa daga sallar tsoro:
1- Muhimmancin sallah a muslunci, da muhimmancin sallar jam’i, domin cewa ita bata faduwa, har a cikin waɗannan lokuta masu rintsi.
2- Kore ƙunci daga wannan al'ummar, da sauƙin shari'a da dacewarta ga kowanne zamani da wuri.
3- Cikar shari'ar musulunci, kuma cewa ita an shar'antata ne ga kowanne lokaci da ya dace da ita.
Na goma sha huɗu: Sallar Juma'a:
Na farko: Hukuncinta:
Sallar juma'a farilla ce ta aini (tilashi) akan kowanne musulmi namiji balligi mai hankali mazaunin gari da ba shi da wani uzuri.
Saboda faɗinSa - Allah Maɗaukakin sarki -:
﴿يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِذَا نُودِيَ لِلصَّلَوٰةِ مِن يَوۡمِ ٱلۡجُمُعَةِ فَٱسۡعَوۡاْ إِلَىٰ ذِكۡرِ ٱللَّهِ وَذَرُواْ ٱلۡبَيۡعَۚ ذَٰلِكُمۡ خَيۡرٞ لَّكُمۡ إِن كُنتُمۡ تَعۡلَمُونَ 9﴾
{Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Idan anyi kirã zuwã ga salla a rãnar Jumu'a, sai ku yi aiki zuwa ga ambaton Allah, kuma ku bar ciniki. Wancan ɗinku ne mafi alhẽri a gare ku idan kun kasance kunã sani. 9} [al-Juma'a: 9].
kuma saboda faɗinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: «Lallai wasu mutane kodai su hanu daga barinsu Juma'o'i, ko Allah Zai yi yumƙi akan zukatansu, sannan zasu kasance daga marafkana»36.
Na biyu: Sharuɗɗan ingancin sallar Juma'a:
1) Lokaci: Lokacinta kamar lokacin sallar azahar ne, bata inganta kafin lokacinta, ko bayan fitarsa.
2) Jama'a su halarceta, mafi ƙarancin jama'ar uku ne akan mafi inganci, bata inganta daga mutum ɗaya, ko mutum biyu.
3) Masu sallar su zama mazauna gari ne a ginannun gidajen da abinda al'ada ta gudana da gini da shi. daidai ne hakan ya kasance ne na siminti ne ko na duwatsu ko na taɓo da wasunsu, akan hakan bata inganta daga 'yan ƙauye masu zaune a hemomi da gidajen zana,, waɗanda basa zama a tabbataccen wuri, kawai suna tashi suna bibiyar ciyayi dan dabbobinsu.
4) Huɗubobi biyu su gabace ta, saboda lazimtar annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - akansu.
Na uku: Rukunan haɗubobi biyu na Juma'a:
1- Godewa Allah da shahada biyu.
2- Salati ga annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
3- Wasiyya da tsoron Allah.
4- Karanta wani abu daga AlKur'ani.
5- Wa'azi.
Na huɗu: Mustahabban huɗubobi biyu na Juma'a:
1- Yin huɗuba akan minbari.
2- Rabewa tsakanin huɗubobi biyu da zama sassauƙa. 3- Addu'a a cikinsu, ga musulmai da majiɓinta al'amuransu.
4- Taƙaitasu.
5- Sallamar mai huɗuba ga mutane a lokacin hawa minbari.
Na biyar: Mustahabban abubuwa (wadanda ake so) a ranar Juma'a:
1- Yin asuwaki.
2- Shafa tirare in an samu.
3- Sammakon fita zuwa sallar Juma'a.
4- Tafiya a ƙasa zuwa masallaci da rashin tafiya a abin hawa.
5- Kusantowa ga liman.
6- Yin addu'a.
7- Karanta Suratul Kahf.
8- Salati ga Annabi - tsira da amicin Allah su tabbata a gare shi -
Na shida: Abinda aka hana ga wanda ya halarci Juma'a:
1- Zance yana haramta, alhali liman yana huɗuba ranar juma'a, saboda faɗinsa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: «Idan ka ce wa abokinka: Yi shiru, a ranar Juma'a, a lokacin liman yana huɗuba, to, haƙiƙa ka yi yasasshen zance »37. Wato: ka yi lagawu, lagawu shi ne: Zunubi
2- An karhanta tsallaka mutane, sai dai in ya kasance liman ne, ko kuma ƙetarewa zuwa wata kafar da ba zai kai gareta ba sai da hakan.
Riskar sallar Juma'a:
Wanda ya riski ruku'u tare da liman, a cikin raka'a ta biyu daga sallar Juma'a; to haƙiƙa ya riski Juma'a, kuma ya cikata raka'o'i biyu, idan bai riski ruku'u ba, a raka'a ta biyu; to. haƙiƙa Juma'a ta wuce shi, kuma ya cika ta azahar raka'o'i huɗu, haka nan wanda Juma'a ta wuce shi don bacci ko waninsa; to ya sallace ta Azzahar.
Na goma sha biyar: Sallar masu uzurai:
Na farko: Sallar mara lafiya:
Na farko: Yana wajaba akan mara lafiya, ya yi sallah gwargwadan ikonsa, ba ya halatta gare shi ya jinkiratata daga lokaci muddin dai hankalinsa yana nan.
Na biyu: Yaya mara lafiya zai yi sallah?:
1- Yana wajaba akan mara lafiya ya yi sallah a tsaye, idan ya kasance yana da ikon tsayuwa ba tare da wata wahala ko cuta ba, ya yi riku'u ya yi sujjada.
2- Idan ya kasance yana cutuwa da yin riku'u ko sujjada tare da ikonsa akan tsayuwa; to sai ya yi nuni da ruku'u a tsaye, da sujjada kuma a zaune.
3- Idan ba zai iya sallah a tsaye ba; to, ya yi sallar a zaune. Sunnah ita ce ya zama mai harɗewa a wurin tsayuwa, kuma ya yi nuni da ruku'u, ya yi sujjada akan ƙasa in hakan ya sawwaƙa, in ba haka ba, to, ya yi nuni da sujjada, kuma ya zama ya fi sunkuyar da kai fiye da ruku'u.
4- idan ba zai iya sallah a zaune ba; to ya yi a ɓangaren jikinsa, fuskarsa tana fuskantar alƙibla. Gefen dama ya fi in ya sawwaƙa, kuma ya yi nuni da ruku'u da sujjada.
5- Idan ba zai iya sallah ta gefensa ba; to ya yi sallah yana rigingine ta bayansa, ƙafafuwansa suna fuskantar alƙibla, yana mai nuni da ruku'u da sujjada.
6- Idan nuni bai sawwaƙa gare shi da jikinsa ba a cikin ruku'u da sujjada; sai ya yi nuni da kansa, idan ya wahalar da shi; to nunin ya fadi gare shi, sai ya gudanar da ayyukan sallah da zuciyarsa, sai ya yi niyyar ayyukan sallah na ruku'u da sujjada da zama alhali shi yana kan halinsa, sai ya zo da zikiransu.
7- Mara lafiya zai aikata sharuɗɗan sallah abinda yake da iko akansa, misali: Fuskantar alƙibla, da alwala da ruwa, ko taimama a yayin gajiyawa, da tsarki daga najasa, idan ya gajiya daga wani abu daga hakan; to ya saraya daga gare shi, ya yi sallah gwargwadan halinsa, kada ya jinkirta sallah daga lokacinta.
8- Sunnah ita ce , mara lafiya ya zauna a harɗe a wurin tsayuwa da ruku'u, kuma yana mai iftirashi a wanin hakan (wato shinfida kafar tasa).
Na biyu: Sallar matafiyi :
1- Daga masu uzurai: Matafiyi, an shar'anta masa, yin ƙasarun (rage) sallah, mai raka'a huɗu daga huɗu zuwa biyu. Saboda faɗinSa - Allah Maɗaukakin sarki -:
﴿وَإِذَا ضَرَبۡتُمۡ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَلَيۡسَ عَلَيۡكُمۡ جُنَاحٌ أَن تَقۡصُرُواْ مِنَ ٱلصَّلَوٰةِ...﴾
{Kuma idan kun yi tafiya a doron ƙasa, to, bãbu laifi a kanku ku rage daga sallah, idan kun ji tsõron waɗanda suka kãfirta su fitine ku...} [al-Nisai: 101].
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: «Mun fita tare da annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - daga Madina zuwa Makka, ya kasance yana sallah raka'a biyu-biyu, har muka dawo zuwa Madina»38.
Ana fara ƙasaru da fitar matafiyi daga gine ginen garinsa; domin Allah Ya halatta ƙasaru ga wanda ya yi tafiya a cikin ƙasa, kuma aka ce kafin fita daga garinsa ba ya kasancewa mai tafiya a cikin ƙasa, ko matafiyi, domin annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kaɗai yana yin ƙasaru ne idan ya tafi.
2- Tafiyar da idan matafiyi ya yanketa to yin ƙasarun sallah ya halatta gare shi ita ce kwatankwacin kilo mita tamanin.
3- Matafiyi zai iya yin ƙasaru a dawowarsa har sai ya shiga garinsa, wanda ya fita daga gare shi.
4- Idan matafiyi ya kai wani gari, kuma ya yi nufin zama a cikinsa; to shi yana da halaye uku:
A) Yayi niyyar zama sama da kwana huɗu; to cika sallah yana wajaba akansa, daga farkon ranar da ya tabbata a cikinta, ba zai ribaci rangwamin matafiyi ba.
B) Yayi niyyar zama kwana huɗu ko mafi ƙaranci; to ƙasaru da rangwamin tafiya yana halatta gare shi .
C- Bai yi niyyar iyakantaccen zama ba, kawai zai iya wanzuwa yini ɗaya ko kwana goma gwargwadan dacewar gurin gare shi, ko yana da wata buƙata na magani ne ko ganin likita, duk lokacin da buƙatarsa ta ƙare zai koma garinsa; to wannan ƙasaru da rangwamin tafiya, sun halatta gare shi har sai ya dawo, koda hakan ya ƙaru akan kwana huɗu.
5- Idan matafiyi ya yi sallah a bayan liman mazaunin gida; to cika sallah ya wajaba gare shi, koda bai riski komai tare da shi ba sai tahiyar ƙarshe.
6- Idan mazaunin gida ya yi sallah a bayan matafiyin da zai yi ƙasarun sallah; to ya wajaba akan mazaunin gida ya cika sallarsa bayan sallamar liman.
Na goma sha shida: Sallolin idi biyu:
Idin al’ummar musulmai idi ne (guda biyu) na Ubangiji, Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya shar'antasu gare su (su Musulmai), ba su suka shar'anta su a kan kansu ba. basu da wasu iduka sai idi biyu kawai, sune: Idun ƙaramar sallah, da idun babbar sallah. Saɓanin bukukuwan kafirai, ko bukukuwan 'yan bidi'a waɗanda Allah - Maɗaukakin Sarki - Bai shar'antasu ba, kuma bai yi umarni da su ba, bari dai su suka shar'anta su da kansu.
Hukuncin sallar idu biyu:
Farillah ne na kifaya, annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya lazimcesu, kuma kalifofinsa shiryayyu - Allah Ya yarda da su baki ɗaya - sun lazimcesu. Su suna daga alamomin addini da kuma alamominsa na zahiri.
Lokacin sallar idu biyu:
Lokacin sallar idu biyu yana farawa ne daga ɗagawar rana gwargwadan goron mashi wato: Bayan kwatankwacin ɗaya bisa huɗu na awa daga ɓullowar rana, kuma lokacinta yana ƙarewa ne a lokacin karkacewar rana.
Siffar sallar idu biyu:
1- Zai yi kabbarar harama a raka'a ta farko, sannan ya karanta addu'ar buɗe sallah, sannan ya yi kabbara shida, yana ɗaga hannayensa tare da kowace kabbara, yana godewa Allah yana yabo gareShi, yana salati ga annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - tsakanin kabbarori, sannan ya yi Ta'awwuzi ya yi Bisimillah, sai ya fara karatu.
2- Zai yi kabbara a raka’a ta biyu bayan kabbarar dagowa kabbara biyar, sannan ya yi Ta'awwuzi ya yi Bisimillah, sai ya fara karatu, an so a raka'a ta farko ya karanta Suratul A'ala bayan Fatiha, a raka'a ta biyu Suratul Gashiyah.
3- Idan liman ya yi sallama; zai hau minbari, sai ya yi huɗuba, huɗuba biyu, ya zauna a tsakaninsu sassauƙan zama, kamar yadda ya aikata a huɗubar juma'a.
Sunnonin idi:
A- Wanka.
B- Tsafta da shafa tirare.
C- Ci kafin fita a idin ƙaramar sallah, da bayansa a idin babbar sallah daga abin layyarsa idan ya kasance yana da abin layya.
D- Tafiya a ƙasa.
E- Tafiya ta wata hanyar, da komawa ta wata hanyar daban.
F- Kabbara zuwa wurin sallah ga mamu banda liman.
Kabbara:
An sunnanta kabbara a dararen idu biyu, da goman Zulhijja, da kwanukan Tashriƙ, shi nau'i biyu ne:
Nau'i na farko: Kabbara kai tsaye: Ita ce wadda ba'a ƙayyadeta da wani iyakantaccen lokaci ba.
1- A ƙaramra sallah: Tun daga faɗuwar rana daren idi zuwa fara sallar idi.
- A babbar sallah: Tun daga faɗuwar rana daren farko na Zulhijja zuwa faɗuwar rana a ƙarshen kwanunkan Tashriƙ.
Nau'i na biyu: Kabbara abar ƙayyadewa:
1- Ban maniyyaci: Tun daga alfijir ɗin ranar Arfa zuwa la'asar ɗin kwanukan Tashriƙ.
2- Mai harama (da hajji) : Tun daga azahar ɗin ranar idin har zuwa la'asar ɗin kwanukan Tashriƙ.
Na goma sha bakwai: Sallolin kisfewar rana da wata:
Ma’anar kisfewar wata da kisfewar rana:
Kisfewar wata: Shi ne tafiyar hasken wata ko sashinsa a cikin dare.
Kisfewar rana: Shi ne tafiyar hasken rana ko sashinsa a cikin yini.
Hukuncin sallar kisfewar rana:
Sunna ce mai ƙarfi, aikin manzo - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya yi nuni akan hakan, inda ya sallaceta lokacin da rana ta yi kusufi a zamninsa - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi -, kamar yadda umarninsa ya yi nuni da ita, kuma malamai sun haɗu akan halaccinta.
Lokacinta:
Daga fara kusufin watan ko kusufin ranar har zuwa yayewa, shi ne gushewar kisfewar ranar ko kisfewar watan.
Siffarta:
Adadin raka'o'inta raka'a biyu ne, yana bayyanar da karatu a cikinsu, siffarta kamar yadda yake tafe ne:
A- Zai yi kabbarar harama, zai yi addu'ar buɗe sallah zai yi Ta'awwuzi zai yi Basmalah, zai karanta Fatiha, sannan ya yi karatu, karatu mai tsawo.
- Sannan ya yi ruku'u, ruku'u mai tsawo.
j- Sannan ya ɗago daga ruku'u, sai ya ce:"Sami‘allāhu liman hamidah" (Allah Ya ji wanda ya gode maSa), sannan ya karanta Fatiha, sannan ya yi karatu, karatu mai tsawo mafi gajarta daga na raka'ar farko.
D- Sannan ya yi ruku'u, ruku'u mai tsawo nafi gajarta daga ruku'un farko.
E- Sannan ya ɗago daga ruku'u, sai ya ce: "Sami‘allāhu liman hamidah" (Allah ya ji wanda ya gode maSa).
F- Sannan ya yi sujjada sujjadodi biyu masu tsawo.
G- Sannan ya ɗago dan yin raka'a ta biyu, ita kwatankwacin raka'a ta farko ce, sai dai ita bata kai ta farkon tsayi ba.
Sunnoninta:
A) Kira gareta da faɗin: (A halarto Sallah).
B) A yi ta a cikin jam'i.
C- Tsawaitawa a cikin sallar da tsayuwarta da ruku'unta da sujjadarta.
D) Raka'a ta biyu ta kasance mafi gajarta daga raka'a ta farko.
E) Yin wa'azi bayanta, da kwaɗaitarwa akan aikata ayyukan biyayya da barin ayyukan ƙi.
F) Yawan addu'a da ƙanƙar da kai da neman gafara da sadaka.
Na goma sha takwas: Sallar sha da fari (Sallar roƙon ruwa):
1) Sha da fari: Shi ne neman shayarwa daga Allah - Maɗaukakin Sarki - da saukar da ruwa a lokacin fari.
Lokacin da aka shar'anta sallar sha da fari:
An shara'anta sallar sha da fari, idan ƙasa ta yi fari, ruwan sama ya tsaya, cutarwa ta faru saboda yankewarsa, babu wani makoma garesu sai su ƙanƙar da kai ga Ubangijinsu, su nemi ya shayar da su, su nemi agajinSa da nau'ikan ƙanƙar da kai.
A- Wani lokaci da yin sallah a jama'a, ko ɗai-ɗai.
B- Wani lokaci kuma da yin addu'a a cikin huɗubar sallar juma'a, mai huɗuba yana addu'a, musulmai suna cewa amin akan addu'arsa.
C- Wani lokaci kuma da yin addu'a, a kowane lokaci, ba tare da yin sallah ko huɗuba ba.
Hukuncin sallar sha da far (roƙon ruwa):
Sunnah ce mai ƙarfi a yayin samun dalilinta, saboda aikin annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi, kamar yadda yake a cikin Hadisin Abdullahi ɗan Zaid - Allah Ya yarda da shi - ya ce: «Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya fita wurin sallah, sai ya nemi Allah ya shayar da su, ya fuskanci alƙibla, ya juyar da mayafi, ya yi sallah raka''o'i biyu»39.
Siffar sallar sha da fari:
Siffar sallar sha da fari a yadda take kamar sallar idi ce. An so aikatata a wurin sallah, kamar sallar idi, hukunce-hukuncenta kamar hukunce-hukuncen sallar idi ne; a adadin raka'o'i, da bayyana karatu, da kasancewarta ana yinta kafin huɗuba, da adadin kabbarorin ƙari a cikin raka'a ta farko da ta biyu kafin karatu, kamar yadda bayaninsa ya gabata a cikin sallar idi biyu. zai yi huɗuba ɗaya.
Na goma sha tara: Hukunce-hukuncen jana'iza:
Na farko: Ga wanda ya zo wajen wanda alamun mutuwa suka zo masa:
1- An sunnantawa wanda ya zo wa wanda ya zo gargara, ya laƙanta masa: «La ilāha illallāh« (Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah).
2- An kuma sunnanta da a fuskantar da wanda ya kusa rasuwa zuwa alƙibla.
3- An so rintse idanuwansa.
4- An sunnanta suturce mamaci bayan mutuwarsa da tufafi.
5- Yana kamata gaggauta shisshirya shi.
6- Gaggauta biyan basukansa yana wajaba.
7- Ana wanke mamaci, a sanya masa likkafani, yin hakan kuma farilla ne na kifaya (idan wasu suka yi ya sauka daga kan saura).
Na biyu: Hukunce-hukuncen sallah ga mamaci:
1- Hukuncinta: Farilla ce ta kifaya (idan wasu suka yi, ya sauka daga kan saura).
Sharuɗɗanta:
1- Fuskantar alƙibla.
2- Boye al'aura.
3- Nisantar najasa:
4) Tsarkin mai sallah da wanda akewa sallah.
5) Musuluncin mai sallar da wanda ake wa sallah.
6) Halartowar jana'iza in ta kasance a gari ne.
7) Ya zama mukallafi (wanda shari'ah ta hau kansa).
Rukunanta:
1) Tsayuwa a cikinta.
2) Kabbarori huɗu.
3) Karatun Fatiha.
4) Salati ga annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
5) Addu'a ga mamaci.
6) Jerantawa.
7) Sallama.
Sunnoninta:
1) Daga hannaye tare da kowace kabbara.
2) Ta'awwuzi.
3) Addu'a ga kansa da kuma musulmai.
4) Boye karatu.
5) Ya tsaya kaɗan, bayan kabbara ta huɗu kuma kafin sallama.
6) Dora hannun dama akan na hugu akan ƙirji.
7) Waiwaye ga dama a cikin sallama.
Siffarta:
Liman ya tsaya da mai sallah shi kaɗai a daidai ƙirjin namiji, da tsakiyar mace, ya yi kabbarar harama, ya yi Ta'awwuzi, kada ya yi addu'ar buɗe sallah, ya yi Basmalah, ya karanta Fatiha.
Sannan ya yi kabbara, ya yi salati ga annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a bayanta, sannan ya yi kabbara, ya yi addu'a ga mamaci da abinda ya zo: Misalin faɗinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: «Allāhumma ighfir lihayyina wa mayyitina wa saghīrina wa kabīrina wa dhakarina wa unthāna wa shāhidina wa ghā’ibina. Allāhumma man ahyaytahu minna fa’ahyhi ‘alal-īmān wa man tawaffaytahu minna fatawaffahu ‘alal-islām. Allāhumma la tahrimna ajrahu wa la tudillana ba‘dah».
(Ya Allah Ka gafarta wa rayayyunmu da mamatanmu, da yaranmu da tsofaffinmu, da mazanmu da matanmu, da waɗanda suke a nan da waɗanda basa nan, Ya Allah, wanda zaKa raya shi a cikinmu, to Ka raya shi akan imani, wanda zaKa kashe daga cikinmu, to Ka kashe shi akan musulunci, ya Allah, Kada Ka hana mu ladansa, kuma kada ka ɓatar da mu a bayansa)40.
da faɗinsa: «Allāhumma ighfir lahu warhamh, wa ‘āfihi wa‘fu ‘anh, wa akrim nuzulah, wa wassi‘ mudkhalah, waghsilhu bilmā’i wath-thalji wal-barad, wa naƙƙihi minal-khaɗāya kama naƙƙayta ath-thawb al-abyada minad-danas, wa abdilhu dāran khayran min dārih, wa ahlan khayran min ahlih, wa zawjan khayran min zawjih, wa adkhilhu al-jannah, wa a‘idh'hu min ‘adhābil-ƙabr wa min ‘adhābin-nārYa».
Ma’ana: (Allah Ka yi masa gafara Ka jiƙansa, Ka kare shi, Ka yi masa rangwami, Ka girmama masaukinsa, Ka yalwata kabarinsa, Ka wanke shi da ruwa da ƙanƙara da sanyi, Ka tsarkake shi daga kurakurai, kamar yadda ake tsarkake farin tufafi daga datti, Ka canja masa gida mafi alheri daga gidansa, da iyalai mafi alheri daga iyalansa, da mata mafi alheri daga matarsa, Ka shigar da shi aljanna, Ka tsare shi daga azabar ƙabari, da kuma azabar wuta)41. Sannan ya yi kabbara, ya tsaya a bayanta kaɗan, sannan ya yi sallama, sallama ɗaya a damansa.
MABHASI NA UKU: ZAKKAH:
1- Ta'arifin (bayanin) zakka da matsayinta:
Zakka a lugga: Daɗuwa da ƙaruwa.
Zakka a shari'a: wani haƙƙine na wajibi a shari' a cikin keɓantattun dukiyoyi, ga wasu keɓantattun mutane.
Ita ce rukuni na uku, daga rukunan musulunci, Ita abar gwamawar sallah ce, a cikin Alƙur'ani a awurare tamanin da biyu, abinda yake nuni akan girman sha'aninta.
Allah Maɗaukakin sarki Ya ce:
﴿وَأَقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتُواْ ٱلزَّكَوٰةَ...﴾
{Kuma ku tsayar da sallah, kuma ku bãyar da zakka...} [al-Baƙara: 43].
Tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi ya ce: «An gina musulunci abisa abubuwa biyar: Shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma (annabi) Muhammad manzon Allah ne, da tsaida sallah, da bada zakka, da ziyartar ɗaki (Hajji), da azumin Ramadan»42.
Kuma musulmai sun haɗu akan wajabcinta, da kafircin wanda ya musunta wajabcinta, da yakar wanda ya hana fitar da ita.
2- Sharuɗɗan wajabcin zakka:
A) 'Yantuwa: (Zakkah) ba ta wajaba akan bawa; domin shi ba shi da dukiya, abinda ke hannunsa mallakin shugabansa ne, sai zakkarsa ta zama akan mai shi.
B) Musulunci: Bata wajaba akan kafiri; domin cewa ita kusancice da ɗa'a, kafiri ba ya daga ma'abota kusanci da ɗa'a.
C- Mallakar nisabi: Bata wajaba a abinda baikai nisabi ba, shi wani gwargwado ne abin sani daga dukiya.
D) Cikar mallaka: Dukiyar ta zama abar mallaka ce ga wani mutum cikakken mallaka, saboda haka babu zakka a cikin wata dukiya da mallakinta bai tabbata ba, kamar bashin wanda aka dorawa fansa.
E) Shuɗewar shekara akan dukiya: Saboda Hadisin Aisha - Allah ya yarda da ita - Marfu'i: «Babu zakka a kowacce dukiya har sai shekara ta kewayo akanta»43.
3- Dukiyoyuin da zakka take wajaba a cikinsu:
Na ɗaya: Dabbobin ni'ima:
Sune raƙuma da shanu da tumakai, zakka tana wajaba a cikinsu da sharuɗɗa biyu:
1- A riƙesu don tatsar nono da haihuwa, ba dan aiki ba.
2- Su zama masu kiwo, Zakka ba ta wajaba a dabbobin da harawar da ake basu ta hanyar saya ce, ko ya tattara musu abin ci ko waninsa, babu zakka a cikin waɗanda suke kiwo a sashin shekara ba dukkaninta ba ko mafi yawanta.
4- Nisabobin zakkar dabbobin ni'ima:
1- Zakkar raƙuma:
Idan sharuɗɗa sun cika; Akuya tana wajaba a dukkanin raƙuma biyar, a goma kuma akuyoyi biyu, a goma sha biyar akuyoyi uku, a ashirin akuyoyi huɗu, kamar yanda Sunna da Ijma'i suka yi nuni akan haka. idan sun kai ashirin da biyar, to a cikinsu za'a bada 'yar mai naƙuda, ita ce wacce ta cika shekara ɗaya ta shiga cikin shekara ta biyu, idan ya rasata to ɗan mai shayar da nono ya isar daga gareta.
idan raƙuma suka kai talatin da shida; to 'yar mai ban nono ta wajaba, a cikinsu ita ce : wacce ta cika shekara biyu.
Idan sun kai arba'in da shida; to, Hiƙƙa ta wajaba acikinsu, ita ce wacce ta cika shekara uku.
Idan sun kai raƙuma sittin da ɗaya; to ƙiba-ƙiba ta wajaba acikinsu, ita ce wacce ta cika shekara huɗu.
idan sun kai saba'in da shida; to 'ya'yan mai ban nono biyu sun wajaba a cikinsu.
Idan sun kai casa'in da ɗaya; to hiƙƙa biyu sun wajaba a cikinsu.
Idan ɗaya ta ƙaru akan yawan raƙuman da suka kai ɗari da ashirin (121), to 'ya'yan mai ban nono uku sun wajaba a cikinsu, sannan a cikin kowane arba'in za'a bada 'yar mai ban nono, a kowane hamsin kuma hiƙƙah.
2- Zakkar shanu:
Tana wajaba a cikinsu, idan sun cika sharuɗɗa, idan sun kai talatin: za'a bada tabi'i namiji ko tabi'i mace (wanda yake bin iyayensa kiwo); shi ne wanda ya cika shekara ɗaya ya shiga shekara ta biyu.
Babu komai a koma bayan talatin.
Idan sun kai arba'in; saniya Musinnah ta wajaba a cikinsu, ita ce : wacce ta cika shekara biyu.
Idan dukkan shanun sun ƙaru akan arba'in; to a kowane talatin daga cikinsu za'a bada tabi'i namiji ko tabi'i mace, a dukkanin arba'in kuma musinnah.
3- Zakkar tumakai:
Idan dukkanin tumakan sun kai arba'in daidai ne tinkiyoyine ko akuyoyi, to acikinsu za'a bada akuya ɗaya, ita ce ƙiba-ƙibar tunkiya, ko macen akuya.
Babu zakka a tumakai idan adadinsu ya ragu daga arba'in. Idan dukkan tumakan sun kai ɗari da ashirin da ɗaya; to akuyoyi biyu sun wajaba a cikinsu. Idan sun kai ɗari biyu da ɗaya; to akuyoyi uku sun wajaba a cikinsu.
Sannan wajabci ya tabbata a cikinsu bayan wannan gwargwadan, sai akuya ta wajaba a dukkan ɗari, a ɗari huɗu akuyoyi huɗu, haka dai.
Na biyu: Zakkar abinda da yake fitowa daga ƙasa:
Mai fita daga ƙasa nau'i biyu ne:
1) Hatsi da 'ya'yan itatuwa.
2) Ma'adanai.
Nau'i na farko: Hatsi da 'ya'yan itatuwa:
Zakka tana wajaba a cikin ƙwayoyi (hatsi); kamar: alkama da sha'ir da shinkafa. A 'ya'yan itatuwa kuma; kamar: Dabino da zabibi, bata wajaba a wanin hakan, na tsirrai; kamar maɓungula ƙasa da korraen abubuwa.
Sharuɗɗan wajabcin zakka a cikin ƙwayoyi da 'ya'yan itatuwa:
1) Su zama waɗanda ake ajiyewa ne: Babu zakka a cikin abinda ba'a ajiye shi kamar kayan marmari da korren abubuwa.
2) Su zama aunasu ake yi: Babu zakka a abinda ake siyarwa da ƙirgawa ko awo (na nauyi); kamar kankana, da albasa, da rumman, da wasunsu.
3) Sukai nisabi: Shi ne Ausuƙi biyar, babu zakka a binda ke ƙasa daga hakan.
4) Nisabin ya zama abin mallaka a lokacin wajabcin zakka.
Wanda ya mallake shi bayan lokacin wajabcin zakka, to zakka bata wajaba akansa ba, kamar da a ce ya siyeshi ko an ba shi kyauta bayan girbe shi.
Lokacin wajibcin zakkarsu:
Zakka tana wajaba a cikin ƙwayoyi da 'ya'yan itatuwa idan nunarsu ta fara, alamar bayyanar nunar kamar yadda yake tafe:
A- A ƙwayoyi: Idan su ka yi tauri suka ƙeƙashe suka zama masu tsauri.
B- A cikin 'ya'yan dabinai: Shi ne su yi ja-ja ko su yi fatsi-fatsi.
C- A cikin inabi: Ya zama ya laushi ya yi zaƙi.
Nisabinsu:
Nisabin ƙwayoyi da 'ya'yan itatuwa: Ausuƙi biyar ne, Ausuƙ shi ne sa'i (kwano) sittin, Sai nisabin ya zama Sa’in annabta ɗari uku, nisabin da kilo grame yaa yi daidai da: Kwatankwaci kilo gramme 900.
Gwargwadan zakkar wajibi a cikinsu:
Ɗaya bisa goma yana wajaba, a cikin abinda aka shayar, ba tare da ɗawainiya ko wahala ba; kamar wanda ake shayarwa da ruwan sama (noman damina), da idaniyar ruwa.
Rabin ɗaya bisa goma yana wajaba, a cikin abinda aka shayar da ɗawainiya da wahala; kamar wanda ake shayar da shi, da ruwan da aka yayyafa daga rijiyoyi da ƙoramai, ta hanyar dabbobi ko kayayyakin zamani (noman rani).
Nau'i na biyu: Ma'adanai:
Daga na'uikan da yake fitowa daga ƙasa: Ma'adanai: Sune abinda ake fito dasu daga ƙasa, wanda ba jinsinta ba; kamar zinare da azirfa da ƙarfe da jauharai.
Lokacin wajabcin zakka a cikinsu:
Idan ya yi hauzi garesu ya mallakesu; zai fitar da zakkarsu kai tsaye, dan ba'a sharɗanta shuɗewar shekara garesu ba, nisabinsu shi ne nisabin zinari da azirfa, ana fitar da rubu'in ushuri daga ƙimarsa.
Na uku: Zakkar kuɗi:
Kuɗaɗe sune: Zinanre da azirfa da takardun kuɗi, zakkarsu dolene, dalili: Faɗinsa - Allah Maɗaukakin sarki -:
﴿وَالَّذِينَ يَكْنِزُونَ الذَّهَبَ وَالْفِضَّةَ وَلَا يُنْفِقُونَهَا فِي سَبِيلِ اللَّهِ فَبَشِّرْهُمْ بِعَذَابٍ أَلِيمٍ 34﴾
{Kuma waɗanda suke taskacẽwar zĩnãriya da azurfa, kuma bã su ciyar da ita a cikin hanyar Allah, to, ka yi musu bushãra da azãba mai raɗaɗi. 34}. [al-Taubah: 34].
A cikin hadisi: «Babu wani mai zinare, ko azirfa, da ba ya bada haƙƙinsu a cikinsu; sai ranar lahira an yi masa faranti da su da farantai na wuta»44.
Kuma ma'abota ilimi sun haɗu akan wajabcin zakka a zinare, da azirfa, kuma takardun kuɗi suna da hukuncin zinare da a zirfa; domin su (takardun kudin) sun maye gurbinsu ne a mu'amalar kuɗi.
Nisabin zakka a cikin kuɗi, da gwargwadan wajibi a cikinsu:
Shi ne nisabin zinare da azirfa; domin sun maye gurbinsa a mu'amalar kudi, idan nisabin dayansu (zinare ko azurfa) ya kai to zakka ta wajaba a cikinsu. Galibin ƙimanta nisabin kudin takardu a yau da azirfa ne; domin yafi sauki daga zinare, sai ya riga shi kaiwa nisabi. Idan musulmi ya mallaki abinda kimarsa ta kai nawin gram (595) na azirfa, kuma shekara ta kewayo akansa, to zakkah ta wajaba a cikinsa. Ƙimar gram na azirfa tana canjawa, lokaci zuwa lokaci, wanda yake da kuɗi kaɗan da bai sani ba, shin sun kai nisabi ko basu kaiba, to ya tambayi masu kasuwancin azirfa nawa ne ƙimar gram na azirfa, sannan ya buga shi a cikin (595), abinda lissafi ya bayar shi ne nisabi.
Fa'idah: Idan ya yi nufin fitar da zakkar dukiyarsa; sai ya raba nisabin akan arba'in, abinda ya fita to shi ne gwargwadan wajibi.
Na huɗu: Zakkar kayan cinikayya:
Su ne abinda aka tanada, don siyarwa da siye, saboda samun riba. Hajojin kasuwanci sun ƙunshi dukkan nau'ikan dukiyoyin da ba kuɗi ba; kamar motoci da tufafi da gwanjo da ƙarfe da katako da wasunsu daga abinda aka tanada dan kasuwanci.
Sharuɗɗan wajibcin zakkar kayayyakin kasuwanci:
1- Ya mallakesu ta hanyar aikinsa; kamar siye, da bada haya, da wanin haka, daga fuskokin kasuwanci.
2- Ya mallakesu da niyyar sayarwa; da ya yi nufin kasuwanci da su, domin ayyuka sai da niyya, kasuwanci kuwa aiki ne, to gwamna shi da niyya yana wajaba da shi kamar sauran ayyuka.
3- Kimarsu su kai nisabi daga ɗayan kuɗaɗen (zinare ko azurfa).
4- Cikar shekara akansu, shi ne shuɗewar shekara.
Yadda ake fitar da zakkar kayan sayarwa (hajoji):
Za’a yi wa hajojin ƙima, a lokacin cikar shekara da ɗayan kuɗaɗen biyu zinare ko azirfa, Idan an yi musu ƙima, kuma suka kai nisabi da ɗayan kuɗaɗe biyun (zinare ko azurfa); sai a afitar da rubu'in ushiri na ƙimarsu (wato ɗaya bisa hudun ɗaya bisa goma, daya bisa arba’in kenan a takaice).
Na biyar: Zakkar kono (fidda kai):
Ita ce sadaka ta wajibi a cikar watan Ramadan, haƙiƙa an wajabta ta a cikin shekara ta biyu da hijira.
Hukuncinta:
Zakkar kono wajiba ce, akan musulmin da ya mallaki abinci ƙari akan abinda zai ishe shi, kuma ya ishi iyalansa a ranar idi da darensa. Kuma tana wajaba akan kowane musulmi; namiji ne ko mace, ƙaramine ko babba, ɗa ne ko bawa, Saboda hadisin: «Manzon Allah- tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya wajabta zakkar kono (zakkar fidda kai) akan bawa da ɗa da namiji da mace, da ƙarami da babba, daga musulmai»45. An faralanta da ma'anar: An lazimta an wajabta.
Hikima daga shara'antata:
Dan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: «Manzon Allah - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya faralanta zakkar kono (zakkar fidda kai); don tsarkakewa ga mai azumi daga zance mara kyau, da kwarkwasa, kuma don ciyar da miskinai»46.
Lokacin wajabcinta da fitar da ita:
Zakkar kono tana wajaba ne, daga faɗuwar rana daga daren idi. An so fitar da ita ranar idi, kafin tafiya sallar idi. Kuma jinkirtar da ita daga sallar idi ba ya halatta. Idan ya jinkirta bai fitar da ita ba har aka yi sallar idi; to fitar da ita a matsayin ramuwa ya wajaba akansa, kuma zai zama mai laifi na jinkirtar da ita, daga lokaci iyakantacce.
Gabatar da ita kafin ranar idi da yini ɗaya ko yini biyu yana halatta.
Gwargwadanta da abin ake fitarwa daga gare shi:
Sa'i ne daga abin ci da mutanen garin suka saba da shi; kamar shinkafa, da dabino da alkama, ko wasunsu. Gwargwadan sa'i: Kwatankwacin kilo grame uku. Ba ya halatta a fitar da ƙima; Shi ne ya bada kuɗi canji daga garesu; domin cewa hakan saɓanin umarnin manzo - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ne.
Fitar da zakka, da waɗanda ake bawa:
Lokacin fitar da ita:
Fitar da zakka yana wajaba da gaggawa, idan lokacin wajabcinta ya yi, Ba ya halatta a jinkirtar da ita, sai da larura, kamar dukiyar ta zama a wani gari mai nisa daga gare shi kuma ba'a samu wanda zai wakilta ba.
Wurin fitar da ita:
Abin da yafi fitar da zakka a cikin garin da a cikinsa dukiyar take, kuma dauketa daga garin da dukiyar take zuwa wani garin daban yana halatta a wasu halaye:
A- Idan a garin babu wani mai buƙatar zakka.
B- Idan an samu wani ɗan uwa mabuƙaci a wani garin daban.
C- Idan an samu wata maslaha, ta shari'a da take kira zuwa dakkota, misali: Dakkota zuwa wasu garuruwan musulmai waɗanda ke cikin masifar yunwa da ambaliyar ruwa.
Zakka tana wajaba a cikin dukiyar yaro da mahaukaci, saboda gamewar dalilai, kuma waliyyinsu (mai kula) da dukiyar shi ne zai jiɓinci fitar da ita. Fitar da zakka ba ya halatta sai da niyya. Saboda faɗinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: «Dukkan ayyuka basa yi wuwa sai da niyyoyi»47.
Waɗanda ake bawa zakka:
Sinfofin wadanda ake baiwa zakka takwas ne:
Sinfi na farko: Talakawa:
Sune waɗanda basa samun gwargwadan abinda zai ishe su na gurin zama da abin ci da tufafi, gwargwadan abin da ake basu na zakka shi ne abinda zai ishesu, kuma ya ishi waɗanda suke kula da su ga tsawon shekara.
Nau'i na biyu: Miskinai:
Sune waɗanda suke samun sama da isuwarsu, sai dai basa samun cikarsa, misali: Dan albashi, sai dai baya isarsa ga tsawon shekara.
Gwargwadan abin da ake basu na zakka: Cikar isuwarsu da isuwar waɗamda suke kulawa da rayuwarsu har tsawon shekara.
Nau'i na uku: Masu aiki akanta:
Sune waɗanda shugaba yake ɗora musu nauyin tattaro zakka, ko suke jiɓintar kiyayeta, ko isar da ita ga mabuƙata.
Gwargwadan abinda ake basu na zakka: Gwargwadan ladansu akan aikinsu, muddin dai basu da lada ko albashi daga hukuma.
Nau'i na huɗu: Waɗanda ake jawo zukatansu (zuwa musulunci):
Sune dukkan wanda ake kauna ta hanyar bashi zakka: Musuluncinsa, ko ƙarfin imaninsa, ko kare sharrinsa daga musulmai.
Gwargwadan abinda ake basu na zakka: Gwargwadan abinda jawo hankalinsu zai tabbata da shi.
Nau'i na biyar: 'Yanta wuyaye:
Ana nufi da shi: 'Yanta bayi da waɗanda aka ɗaurawa fansa.
Wanda aka ɗaurawa fansa: Shi ne bawan da ya sayi kansa daga mamallakinsa, fansar ribatattun musulamai a cikin yaƙoƙa yana shiga cikinsa.
Nau'i na shida: Waɗanda suka ci bashi, su nau'i biyu ne:
Na farko: Wanda akansa akwai bashi dan buƙatar kansa, kuma bai samu abinda zai biya bashinsa da shi ba, za'a bashi abinda zai biya bashinsa.
Na biyu: Wanda akansa akwai bashi saboda yin sulhu tsakanain masu rigima, ana bashi abinda zai biya bashinsa ko da ya kasance mawadaci ne.
Nau'i na bakwai: a tafarkin Allah
Sune waɗanda suke yaƙi a tafarkin Allah.
Gwargwdan abinda ake basu na zakka: Abinda zai ishesu ga yaƙi a tafarkin Allah; na abin hawa, da makami, da abinci da wanin hakan.
Nau'i na takwas: Dan tafarki (matafiyi):
Shi ne matafiyin da abincinsa ya ƙare, ko aka sace masa, babu wani abu da ya rage da zai kai shi garinsa a tare da shi na dukiya.
Gwargwadan abinda ake basu na zakka: Gwargwadan abinda zai kaishi garinsa, koda ya kasance mawadaci ne a cikinsa.
MABHASI NA HUƊU: AZUMI:
Azumi shi ne:
Bautawa Allah - Maɗaukakin Sarki - ta hanyar kamewa daga abubuwan da suke karya azumi, daga ɓullowar alfijir, zuwa faɗuwar rana.
Shi rukuni ne daga rukunan musulunci, kuma farilla ne daga farillan Allah - Maɗaukakin sarki -, abin sani daga addini da larura. Kuma AlKur'ani da Sunna da ijma'in malamai sun yi nuni akan wajabcinsa.
Allah Maɗaukakin sarki Ya ce:
﴿شَهۡرُ رَمَضَانَ ٱلَّذِيٓ أُنزِلَ فِيهِ ٱلۡقُرۡءَانُ هُدٗى لِّلنَّاسِ وَبَيِّنَٰتٖ مِّنَ ٱلۡهُدَىٰ وَٱلۡفُرۡقَانِۚ فَمَن شَهِدَ مِنكُمُ ٱلشَّهۡرَ فَلۡيَصُمۡهُ...﴾
{Watan Ramalãna ne wanda aka saukar da Alƙur'ãni a cikinsa yana shiriya ga mutãne da hujjõji bayyanannu daga shiriya da rarrabẽwa. To, wanda ya halarta daga gare ku a watan, sai ya azumce shi...} [al-Baƙara: 185].
Sharuɗɗan wajabcin azumin Ramadan:
1- Musulunci, (Azumi) ba ya inganta daga kafiri.
2- Balaga, ba ya wajaba akan yaro, Azimi yana inganta daga yaro mumayyazi (wanda ya iya rabewa), kuma yana zama nafila a haƙƙinsa.
3- Hankali, azimi ba ba wajaba akan mahaukaci, kuma baya inganta daga gare shi, saboda rashin niyya.
4- Iko akansa, ba ya wajaba akan mara lafiyar da yake gajiyawa daga gare shi, ko akan matafiyi, kuma suna ramashi a halin gushewar uzurin: Rashin lafiyar da kuma tafiyar. Ana sharɗanta ingancinsa daga mace: Yankewar jinin al’ad da jinin biƙi.
Shigar watan Ramadan, yana tabbata da ɗaya daga al'amurra biyu, sune:
A- Ganin jinjirin watan Ramadan, Saboda faɗinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: «Ku yi azumi saboda ganinsa (watan Ramadan), kuma ku ajiye azumi saboda ganinsa (watan Shawwal)»48.
B- Cikar watan Sha'aban kwana talatin, hakan idan ba'a ga jinjirin watan Ramadan ba, ko girgije, ko ƙura ko wanin hakan sun tsare ta yadda ba’a gan shi ba, saboda faɗinsa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: «Idan aka lulluɓe muku; to ku cika ƙirgar Sha'aban kwana talatin»49.
Niyyah a azumi:
Azimi kamar waninsa ne daga ibadu ba ya inganta sai da niyya, kuma lokacin wajabcin niyyar a cikin azimi na wajibi yana saɓawa daga waninsa, bayanin hakan kamar yadda yake tafe:
Na farko: Azinmin wajibi; kamar azimin Ramadan. ko na ramuwa, ko na bakance, niyyarsa tana wajaba da daddare kafin ɓullowar alfijir, Saboda faɗinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: «Wanda bai kwana da niyyar azumi da daddare ba, to ba shi da azumi»50.
Na biyu: Azimin taɗawwu'i, yana inganta mutum ya yi niyyarsa da rana, da sharaɗin kada ya kasance ya ci wani abu mai karya azimi bayan ɓullowar alfijir.
Abubuwan da Suke ɓata azumi:
Na farko: Jima'i: A duk lokacin da ya yi jima',i to aziminsa ya ɓaci, kuma rama wannan ranar da ya yi jima'i a cikinta ya lazimce shi, kuma ramuwa tare da kaffara suna wajaba a kansa, ita ce : 'Yanta baiwa, idan bai samu ba to ya wajaba a kansa ya yi azimin wata biyu a jere, idan ba zai iya ba, wato cewa bai samu iko ba, saboda wani uzuri na shari'a, to ya wajaba akansa ya ciyar da miskinai sittin, kowane miskini rabin Sa’i na abinci da ake ci a gari.
Na biyu: Fitar da maniyyi: Saboda sunbata, ko shafa, ko jawo maniyyi, ko maimaita kallo, to ramuwa ta wajaba akan sa kawai ba tare da kaffara ba; domin cewa kaffara ta keɓanci jima'i ne kawai. amma mai bacci, idan ya yi mafarki, sai ya zubar da maniyyi; to babu komai a kansa; domin hakan, ba tare da zaɓinsa ba ne, sai ya yi wankan janaba.
Na uku: Ci da sha da gangan: Saboda faɗinSa - Allah Maɗaukakin sarki -:
﴿وَكُلُواْ وَٱشۡرَبُواْ حَتَّىٰ يَتَبَيَّنَ لَكُمُ ٱلۡخَيۡطُ ٱلۡأَبۡيَضُ مِنَ ٱلۡخَيۡطِ ٱلۡأَسۡوَدِ مِنَ ٱلۡفَجۡرِۖ ثُمَّ أَتِمُّواْ ٱلصِّيَامَ إِلَى ٱلَّيۡلِ...﴾
{Kuma ku ci kuma ku sha har sĩlĩlin fari ya bayyana a gare ku daga sĩlĩlin baƙi daga alfijiri, sa'an nan kuma ku cika azumi zuwa ga dare...} [al-Baƙara: 187].
Amma wanda ya ci ko ya sha. akan mantuwa; to babu komai akansa; Saboda hadisin: «Wanda ya manta alhali yana azumi, sai ya ci ko ya sha, to ya cike aziminsa, domin kaɗai Allah ne Ya ciyar da shi kuma Ya shayar da shi»51.
Na huɗu: Fitar da amai da gangan, amma wanda amai ya rinjaye shi, ba tare da zaɓinsa ba; to baya tasiri akan aziminsa, Saboda faɗinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: «Wanda amai ya zo masa, to babu ramuwa akansa, amma wanda ya jawo amai da gangan, to sai ya rama»52.
Na biyar: Fitar da jini daga jiki; ta hanyar ƙaho, ko tsaga, ko zuƙo jini don bada kyautarsa don kuɓutar da mara lafiya; to hakan gaba ɗayansa yana karya azumi. Amma fitar da jini kaɗan, wanda ake fitarwa dan gwaji; to wannan ba ya tasiri akan azimi, haka nan fitar jini ba tare da zaɓinsa ba; kamar haɓo ko ciwuka ko cire haƙori; to wannan ba ya tasiri akan azimi.
Waɗanda aka halasta musu ajiye azumi a watan Ramadan:
Kashi na farko: Waɗanda aka halarta musu ajiye azumi, kuma ramuwa tana wajaba akansu, su ne:
Na farko: Mara lafiya rashin lafiyar da ake fatan warkewarsa, kuma yana cutuwa daga azimi ko yana wahalar da shi.
Na biyu: Matafiyi; daidai ne ya sha wahala a cikin tafiyar, ko bai sha wata wahala ba.
Dalili akansu: Faɗinsa - Allah Maɗaukakin sarki -:
﴿...وَمَن كَانَ مَرِيضًا أَوۡ عَلَىٰ سَفَرٖ فَعِدَّةٞ مِّنۡ أَيَّامٍ أُخَرَ...﴾
{...To, wanda ya kasance daga gare ku mara lafiya, ko kuwa yana a kan tafiya, sai (ya biya) adadi daga wasu kwanuka na dabam...} [al-Baƙara: 185].
Na uku: Mace mai ciki ko mai shayarwa, idan azimi yana wahalar da su, ko zai cutar da su ko 'ya'yansu, to su suna cikin hukuncin mara lafiya, to waɗannan ajiye azumi yana halatta garesu, sai dai rama azimi a wani lokacin daban yana wajaba akansu.
Na huɗu: Mace mai al’ada da mai jinin biƙi, su ajiye azumi wajibi ne akansu, kuma aziminsu ba ya inganta, kuma ramuwa a wasu kwanuka daban yana wajaba akansu.
Kashi na biyu: Wanda aka halatta masa ajiye azumi, kuma kaffara ta wajaba akansa banda ramuwa, su ne:
Na farko: Mara lafiya rashin lafiyar da ba'a tunanin warkewarsa.
Na biyu: Mai yawan shekarun da ba zai iya azimi ba.
To waɗannan zasu ajiye azuminsu, zasu ciyar da miskini amadadin kowace rana daga watan Ramadan, amma idan mai yawan shekarun ya kai matsayin rikicewa, to cewa nauyin shari'a ya gushe daga gare shi; sai ya ci abin cin sa, babu komai akansa.
Lokacin ramuwa, da kuma hukuncin jinkirata shi:
Rama azimin Ramadan yana wajaba a tsakaninsa da tsakanin wani Ramadan ɗin da yake biye masa, abin da yafi shi ne gaggauta ramuwar, Jinkirta ramuwa zuwa bayan Ramadan ɗin da yake biye baya halatta. Daga A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: «Yana kasancewa akaina akwai (rama) azumin Ramadan, bana iya ramawa sai a Sha'aban saboda matsayin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi»53.
Wanda ya jinkirta ramuwa bayan Ramadan ɗin da yake biye, to shi yana da halaye biyu:
1- Ya jinkirta saboda wani uzuri na shari'a, kamar: Rashin lafiyar ta zarce masa, har zuwa wani Ramadan ɗin daban, to wannan ramuwa ce kawai a kansa.
2- Ya jinkirta shi
ba tare da wani uzuri na shari'a ba, to wannan zai yi laifi da jinkirtawar, kuma tuba ya wajaba akansa, da ramuwa, da ciyar da miskini daga kowace rana.
Azumin nafila ga wanda akwai ramuwa a kansa:
Wanda akansa akwai rama wani abu na Ramadan; to abinda ya fi shi ne gaggawa da shi kafin azimin nafila, Saidai idan azumin nafilar ya kasance daga wanda lokacinsa zai wuce ne - kamar azimin Arafa da Ashura -; to sai ya azimce su, kafin ramuwar; domin cewa ramuwa lokacinta mai yalwa ne, amma Ashura da Arafa zasu wuce, sai dai ba zai yi azimin shida ga Shawwal ba sai bayan ramuwa.
Abinda azumtarsa yake haramta:
1- Azimi ranar ƙaramar sallah, da idin babbar sallah; saboda hani daga gare shi.
2- Azimin kwanukan tashriƙ daga watan Zul hijja, sai dai ga wanda yake Tamattu'i, da wanda yake Kirani a hajji, idan bai samu hadaya ba, kwanukan Tashriƙ su ne: Rana ta goma sha ɗaya da ta goma sha biyu da ta goma sha uku na watan Zul hijja.
3- Ranar kokwanto saboda kokwanto, ita ce ranar talatin ga Sha'aban, idan daren ya kasance dare ne mai girgije ko ƙurar da zasu tsare ganin jinjirin wata,
Abinda aka karhanta azumimtarsa:
A- Keɓance watan Rajab da azumi. B- Keɓance ranar juma'a, da azumi, saboda hani game da hakan, idan ya yi azimin wani yinin kafinsa ko bayansa to karhancin ya gushe.
Abinda aka sunnanta azuminsa:
A- Kwana shida a watan Shawwal. (Watan karamar sallah). B- Azumin kwana taran farko na Zul-Hijja, mafi ƙarfinsu ranar Arfa, saidai ga mai yin aikin hajji; to ba'a sunnanta masa azumtarsa ba, kuma azumtarsa yana kankare (kusakuren) shekaru biyu. C- Azumin kwanaki uku a kowane wata, abinda ya fi, su zama ranakun fari, sune: sha uku, sha huɗu da kuma sha biyar. D- Azumin Litinin da Alhamis a kowanne sati, saboda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana azumtarsu; saboda ana bujuro da ayyukan ibadah a cikinsu.
Azumin nafila:
A- Azumin (Annabi) Dawuda - aminci ya tabbata a gare shi -, ya kasance yana yin azumin rana ɗaya ya sha rana ɗaya.
B- Azumin watan Muharram, shi ne mafificin watan da ake son azumtarsa, kuma mafi ƙarfafarsa: Azumin ranar Ashura, shi ne goma ga Muharram, ya azumci tara ga watan tare da shi, saboda faɗinsa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: «Wallahi in dai na kai baɗi, lallai sai na Azumci tara ga watan»54. Yana kankare (zunuban) shekarar data gabata.
MABHASI NA BIYAR: HAJJI DA UMARAH.
Hajji a lugah: Nufi. A shari'a kuma: Nufatar ɗakin Allah mai alfarma da wuraren ibadu, a wani lokaci abin ayyanawa don yin ibadu keɓantattu.
Umra kuma: A luga: Ziyara.
A shari'a: Ziyarar ɗaki mai alfarma a cikin kowane lokaci dan yin ibadu keɓantattu.
Hajji ɗaya ne daga rukunan musulunci kuma maginarsa masu girma, haƙiƙa an wajabta shi a shekara ta tara bayan hijira, kuma annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi hajji ɗaya, shi ne (Hajjin ban kwana).
Hajji yana wajaba ne a cikin rayuwa sau ɗaya ga mai iko, abinda ya ƙaru to shi nafila ne. Amma Umra to wajiba ce a maganar mafi yawa cikin malamai, da dalilin faɗinsa - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - lokacin da aka tambaye shi: Shin akwai wani yaƙi na wajibi akan mata? Ya ce: «Eh, a kansu akwai jihadin da babu yaki a cikinsa: Hajji da Umarah»55.
Sharuɗɗan wajabcin Hajji da Umarah Umra:
1- Musulunci
2- Hankali.
3- Balaga
4- 'Yantuwa
5- Iko
Mace tana ƙara wani sharaɗi na shida; shi ne samun maharrami wanda zai yi tafiya tare da ita don yi shi. domin tafaiya ba ta halatta gareta, dan Hajji ko waninsa ba tare da mahram ba, Saboda faɗinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: «Kada mace ta yi tafiya sai tare da muharrami, kuma kada wani namiji ya shigo wurinta sai a tare da ita akwai muhrrami»56.
Mahramin mace shi ne: Mijinta, ko wanda aurenta yake haramta akansa, haramci na har abada; Soboda nasaba; kamar ɗan'uwanta da babanta da baffanta da ɗan ɗan'uwanta da yakumbanta (kawunta), ko da daliln aure; kamar ɗan'uwa na shayarwa, ko da sukurtaka; kamar mijin babarta da ɗan mijinta.
Iko: Shi ne: Iko na kuɗi da jiki, da ya samu damar hawa abin hawa kuma ya juri tafiya, kuma ya samu guzirin da zai ishe shi tafiya da dawowa, kuma zai samu abinda zai ishi 'ya'yansa, da wanda ciyarwarsu take lazimtarsa har zuwa dawowarsa garesu.
kuma hanyar zuwa hajjin ta zama amintacciya a ransa da dukiyarsa.
Wanda ya kasance mai iko da dukiyarsa banda jikinsa, da ya kasance mai yawan shekaru tsoho, ko mara lafiya, rashin lafiyar mai shamajika, ba'a tinanin warkewarsa; to ya lazimce shi ya samar da wanda zai yi masa hajji kuma ya yi masa umra a maimakonsa.
An sharɗanta ga ingancin wanda zai yi wa wani hajji da umra sharuɗɗa biyu:
1- Ya ksance daga waɗanda yin aikin hajji ya inganta daga gareshi, shi ne musulmi baligi mai hankali.
2- Ya kasance haƙiƙa ya yi wa kansa hajjin farilla.
Miƙatan yin harama:
Miƙatai: Jam'i ne na miƙati, shi a luga: Iyaka. A shari'a kuma: Shi ne wurin ibada ko zamaninta.
Aikin hajji yana da miƙati na lokaci da na wuri:
A- Miƙatai na lokaci : Allah Ya ambacesu da faɗinSa:
﴿ٱلۡحَجُّ أَشۡهُرٞ مَّعۡلُومَٰتٞۚ فَمَن فَرَضَ فِيهِنَّ ٱلۡحَجَّ...﴾
{Hajji watanni ne sanannu. To, wanda ya yi niyyar hajji a cikinsu...} [al-Baƙara: 197].
Waɗannan watannin su ne: Shawwal, da Zulƙi'ida, da (Kwanaki) goma na ZulHijja.
B- Miƙatai na wuri: Su ne iyakokin da ba ya halatta ga mai aikin hajji ya ƙetaresu zuwa Makka ba tare da harama ba. Sune kamar yadda yake tafe:
1- Zul Hulaifa: Miƙatin mutanen Madina.
2- Juhfah: Miƙatin mutanen Sham da Misra da Marocco
3- Karnil Manazil; A yanzu an fi saninsa da Sail; Miƙatin mutanen Najd.
4- Zatu Irƙin: Miƙatin mutanen Iraƙ.
5- Yalamlam: Miƙatin mutanen Yaman.
Wanda gidansa ya kasance koma bayan waɗannan miƙatan; to shi zai yi haramar Hajji da Umarah ne daga gidan nasa. Wanda ya kasance cikin mutanen Makka; su za su yi harama ne daga Makka, ba sa buƙatar fita miƙati don yin harama. Amma Umarah; to cewa su zasu fita ne zuwa mafi kusa da wajen harami, su yi harama. Wanda ya yi nufin Hajji, ko Umarah to babu makawa sai ya yi harama da su daga wuraren da manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya iyakance su, su ne Miƙatai na wurare waɗanda bayaninsu ya gabata. ba ya halatta ga wanda ya yi nufin hajji ko Umarah ya ƙetaresu, ba tare da harama ba.
- Dukkan wanda zai wuce ta miƙatan da aka ambata kuma ba ya daga ahalinsu; to zai yi harama daga garesu.
- Wanda hanyarsa zuwa Makka, ta kasance, kuma ba zai wuce ɗaya daga miƙatan da aka ambata ba ta ƙasa ne ko ta ruwa ko ta sama; to shi zai yi harama idan ya yi daura da mafi kusancin miƙatan gare shi. saboda faɗin Umar ɗan Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi -: «Ku duba daura da ita daga hanyarku»57.
- Wanda tafiyarsa ta kasance, don yin ibadar Hajji, ko Umarah ta hanyar jirgi, to shi yana wajaba akansa ya yi harama idan jirgin ya iso daura da miƙatin da ke hanyarsa, ba ya halatta gare shi ya jinkirta harama zuwa saukar jirgi a tsasha.
Ihrami:
A- Shi ne niyyar shiga cikin ibadar; a Hajji shi ne: Niyyar shiga cikin Hajji, a Umarah kuma shi ne niyyar shiga aikin Umarah . ba ya kasancewa mai harama, sai dai idan ya yi niyyar shiga cikin ibadar. Amma kawai sanya tufafin harama ba tare da niyya ba to baya zamowa mai harama.
Mustahabban Harama:
1- Wanka kafin harama ga dukkan jikinsa.
2- Namiji ya shafa tirare a jikinsa, ba'a tufafin haramarsa ba.
3- Haramarsa a cikin gwafso (kwarjalle) da mayafi farare da takalma silifa.
4- Ya yi harama halin kasancewarsa a kan abin hawa yana mai fuskantar alƙibla.
Nau'ukan ibadun Hajji:
Mai harama yana zaɓar abinda ya so daga ibadu uku, su ne:
1- Tamattu'i; shi ne ya yi harama da Umarah a cikin watannin Hajji, sai ya gamata, sannan ya yi harama da Hajji a shekararsa.
2- Ifradi; shi ne ya yi harama da hajji kawai, daga miƙati, ya wanzu a haramarsa har sai ya yi ayyukan Hajji.
3- Kirani; shi ne ya yi harama da hajji da Umarah tare, ko ya yi harama da Umarah, sannan ya shigar da hajji kafin shigarsa cikin ɗawafin Umarar sai ya yi niyyar Umarah da Hajji daga miƙati, ko kafin shigarsa cikin ɗawafin Umarah, kuma ya yi musu ɗawafi ya yi sa'ayi.
Fidiya tana wajaba akan mai tammattu'i, da mai ƙirani, in bai kasance daga mazauna masallaci mai alfarma ba.
Mafi falalar waɗannan ibadu ukun: Tamattu'i; domin cewa annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya umarci sahabbansa da shi58. Sannan ƙirani; domin shi Hajji ne da Umarah, sannan ifradi.
C) Idan ya yi harama da ɗayan waɗannan ibadun; zai yi talbiyya bayan haramarsa, sai ya ce: «Labbayka allāhumma labbayk, labbayka la sharīka laka labbayk, innal-hamda wan-ni‘mata laka wal-mulk, la sharīka lak».
(AmsawarKa ya Allah AmsawarKa, amsawarKa, ba Ka da abokin tarayya amsawarKa, lallai godiya da ni'ima naKa ne mulki ma (naKa ne) ba Ka da abokin tarayya)59.
Talbiyya sunnah ce, an so yawaitata, kuma namiji ya bayyanar da ita, mace kuma ta ɓoye ta.
Lokacin talbiyya: Lokacinta yana farawa ne daga bayan harama, ƙarshen lokacinta kuma kamar haka:
Na farko: Mai Umarah zai yanketa kafin ya fara ɗawafi.
Na biyu: Mai aikin Hajji zai yanketa idan ya fara jifan Jamratul Aƙabah (Babban Shaiɗan) ranar idi.
ABUBUWAN DA YIN HARAMA KE HANAWA:
Abin da aka hana na farko: Aske gashi ko saisaye shi ko taige shi daga kowane wuri na jikinsa.
Abinda aka hana na biyu: Yanke farata ko ragesu, daga hannu ko ƙafa, ba tare da wani uzuri ba, idan wani farce ya karye, sai ya gusar da shi to babu fidiya akansa.
Abin da aka hana na uku: Rufe kan namiji da abinda yake ɗanfarewa gare shi , misali: Hula da shimag.
Abin da aka hana na huɗu: Namiji ya sanya tufa mai kewaye jiki a jikinsa ko sashinsa; na riga ne ko rawani ko wando. Ɗinkakke: Abinda aka yi gwargwdan gaɓa kamar huffi biyu da safar hannu da jaurabi, amma mace sai ta sanya abinda ta so na tufa a halin harama (niyya) dan buƙatuwarta zuwa suturcewa, saidai cewa ita ba za ta sa niƙabi ba, ta rufe fuskarta da waninsa, na mayafi da jallabiya idan maza ajnabai (wadanda ba maharramanta ba) suka wuce ta, ba zata sanya safar hannu ba a tafukanta.
Abinda aka hana na biyar: Turare; domin mai harama an nema daga gare shi ya yi ne sa da wadata da adon duniya da jin daɗinta, ya fuskanci lahira.
Abin haramtawa na shida: Kashe farautar tudu da farautarsa, mai harama ba ya farautar abin farauta na sarari, kuma ba zai yi taimako akan farautarsa ba, kuma ba zai yanka shi ba.
Yana haramta akan mai harama ya ci daga abinda ya yi farautarsa, ko aka yi farauta saboda shi, ko ya yi taimako akan farautarsa; domin shi kamar mushe ne a gare shi.
Amma farautar kogi; to baya haramta akan mai harama ya yi farautarsa. Kuma yanka dabbar gida ba ya haramta akansa kamar kaji da dabbobin ni'ima; domin ba farauta ba ce.
Abin haramtawa na bakwai: Daurawa kansa aure ko waninsa, ko ya zama mai shaida.
Abin haramtawa na takwas: Jima'i; wanda ya yi jima'i kafin warware ihrami na farko; to hajjinsa ya ɓaci, kuma ya wajaba ya cigaba ya cika ibadunsa, ya ramashi a shekara ta biyu, kuma wajibine ya yanka taguwa. Idan ya kasance bayan warware ihrami na farko ne; to ibadunsa basu ɓaci ba, kuma akansa akwai yanka.
Mace a hakan kamar namiji ne, idan ta kasance ta yi biyayya.
Abin hanawa na tara: Rungumemeniya koma bayan farji, ba ya halatta ga mai harama ya rungumi mace, domin cewa ita hanya ce ta jima'in da aka haramta, abin nufi da rungumemeniya: Shafar mace da sha'awa.
Umarah:
A- Rukunan Umarah:
1- Ihrami (Daukar Niyya).
2- Dawafi.
3- Sa'ayi.
B- Wajiban Umarah:
1- Harama daga Mikatin da aka yi la'akari da shi.
2- Aski ƙwal-ƙwal ko saisaye.
C- Siffar Umarah:
Farkon abinda mai Umarah yake farawa da shi, shi ne ya yi ɗawafi kewaye bakwai, zai fara daga alHajarul Aswad kuma zai tiƙe da shi. Ya zama mai alwala a ɗawafinsa, yana mai suturce al'aurarsa daga cibiya zuwa gwiwa, An sunnanta masa Iɗɗiba'i a dukkan ɗawafi; shi ne ya yaye kafaɗarsa ta dama, sai ya sanya mayafinsa a ƙarƙashinta, ya sanya gefunan mayafin biyu akan kafaɗarsa ta hagu, idan ya cika kewaye bakwan; sai ya bar Iɗɗiba'in, sai ya rufe kafaɗarsa da mayafinsa.
ya fuskanci Hajarul Aswad, idan ya samu damar sunbatarsa sai ya sunbace shi, in ba haka ba, sai ya taba shi da hannunsa na dama in hakan ya sawwaƙa, ya sunbaci hannun nasa. Idan sunbatar dutsen bata samu gare shi ba, sai ya yi nuni gare shi yana mai ɗaga hannunsa na dama yana mai cewa: "Allahu Akbar”. (Wato Allah ne Mafi girma). sau ɗaya, ba zai sumbanci hannun nasa ba, kuma ba zai tsaya ba, sannan ya ci gaba da ɗawafinsa; yana mai sanya Ka'aba a hagunsa, an sunnanta masa ya yi sassarfa a cikin kewaye ukun na farko, Sassarfa: Saurin tafiya ce tare da kusanto da taku.
Idan ya wuce Rukunul Yamani - shi ne rukuni na huɗu ga Ka'aba - idan ya sawwaƙa gare shi sai ya sunbace shi da hannunsa na dama batare da kabbara ko sunbanta ba, idan sunbatarsa ba ta samu gareshi ba sai ya wuce bazaiyi nuni gareshi ba kuma ba zai yi kabbara ba, sai ya ce tsakanin Rukunai biyu na Yamani da na Aswad:
﴿...رَبَّنَآ ءَاتِنَا فِي ٱلدُّنۡيَا حَسَنَةٗ وَفِي ٱلۡأٓخِرَةِ حَسَنَةٗ وَقِنَا عَذَابَ ٱلنَّارِ﴾
{Rabbana ãtina fid duniya hasanatan wafil ãkhiarti hasanatan waƙina azaban nãr}.
(Yã Ubangijinmu! Ka bã mu mai kyau a cikin dũniya da mai kyau a cikin Lãhira, kuma Ka tsare mana azãbar wuta). [al-Baƙara: 201].
Idan ya gama ɗawafi; sai ya yi sallah raka'o'i biyu a bayan Maƙami Ibrahim - aminci ya tabbata a gare shi - idan hakan ya sawwaƙa, inba haka ba kuma sai ya sallace su a kowanne guri a masallaci mai alfarma, an sunnanta ya karanata Suratul (Kafirun) bayan Fatiha. a cikin raka'a ta biyu kuma Suratul (Ikhlas) bayan Fatiha, sannan ya fuskanci wurin Sa'ayi, sai ya yi Sa'ayi tsakanin Safa da Marwa kewaye bakwai; tafiyarsa kewaye ne (daya kenan) kuma dawowarsa ma kewaye ne ( biyu kenan).
yana fara Sa'ayi a Safa, sai ya hau shi, ko ya tsaya a wurinsa, hawan Safa ɗin shi yafi in ya sawwaƙa, yana karanta faɗinSa - AllahMaɗaukakin sarki - a wurin:
﴿إِنَّ ٱلصَّفَا وَٱلۡمَرۡوَةَ مِن شَعَآئِرِ ٱللَّهِ...﴾
{Lalle ne Safã da Marwa suna daga wurãren ibãdar Allah...} [al-Baƙara: 158].
An so ya fuskanci Ka’aba, sai ya godewa Allah, ya girmamaShi, ya ce: «La ilāha illallāh wallāhu akbar, la ilāha illallāh wahdahu la sharīka lah, lahul mulku walahul hamd, yuhyi wayumīt wahuwa ‘ala kulli shay’in ƙadīr, la ilāha illallāh wahdah, anjaza wa‘dah, wa nasara ‘abdah, wa hazama al-ahzāba wahdah».
(Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Allah ne Mafi girma, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kaɗai yake ba Shi da abokin tarayya, mulki naSa ne, godiya ma tasa ce, Yana rayawa kuma Yana kashewa, Shi Mai iko ne akan dukkan komai, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kaɗai yake, Ya zartar da alƙawarinSa, kuma Ya taimaki bawanSa, Ya tarwatsa rundunar ƙawance Shi kaɗai)60. Sannan ya yi addu'a da abinda ya sawwaƙa yana mai ɗaga hannuwansa, ya maimaita wannan zikirin da addu'ar sau uku. Sannan ya sauka, sai ya tafi Marwa, har ya kai zuwa alama ta farko, sai namiji ya yi gaggawar tafiya har sai ya kai alama ta biyu. Amma mace ba'a shar’anta mata gaggawa ba, tsakanin alamomi biyu ba domin ita al'aura ce, kawai abin shar'antawa gare ta yin tafiya a Sa'ayi gaba ɗayansa. Sanna ya yi tafiya, sai ya hau Marwa, ko ya tsaya a wurinsa, amma hawan yafi in hakan ya sawwaƙa, yana faɗa kuma yana aikatawa akan Marwa kamar yadda ya faɗa kuma ya aikata akan Safa, banda karanta ayar, ita ce faɗinSa - Allah Maɗaukakin sarki -:
﴿إِنَّ ٱلصَّفَا وَٱلۡمَرۡوَةَ مِن شَعَآئِرِ ٱللَّهِ...﴾
{Lalle ne Safã da Marwa suna daga wurãren ibãdar Allah...} Wannan kawai an shara'ata ne a lokacin hawa zuwa Safa. a kewaye na farko kawai. Sannan ya sauka, sai ya yi tafiya a wurin tafiyarsa, kuma ya yi gaggawa (sassarfa) a wurin gaggawa, har ya kai zuwa Safa, yana aikata hakan sau bakwai, tafiyarsa kewaye ce kuma dawowarsa ma kewaye ce. An so ya yawaita zikiri da addu'ar abinda ya sawwaƙa a cikin Sa'ayinsa kuma ya zama mai tsarki daga babban kari da ƙarami, da zai yi Sa'ayi, ba tare da tsarki ba (alwala), to hakan ya isar masa. Hakanan da mace zata yi al’ada, ko ta yi jinin biƙi bayan ɗawafi; ta yi Sa'ayi, hakan ya isar mata; domin cewa tsarki ba sharaɗine a cikin Sa'ayi ba, kawai shi mustahabbi ne.
Idan ya cika Sa'ayi; sai ya aske kansa ƙwal-ƙwal ko ya saisaye shi, aski ƙwal-ƙwal ɗin ya fi.
Da haka ne zai zama ya cika ayyukan Umararsa.
Hajji:
A- Rukunan Hajji:
1- Ihrami (Daukar Niyya).
2- Tsayuwar Arfa.
3- Dawafin Ifadah.
4- Sa'ayi.
B- Wajiban Hajji:
1- Harama daga Miƙati.
2- Tsayuwar Arfa ranar tara ga Zul-Hjja har zuwa faɗuwar rana ga wanda ya tsaya da rana a nan.
3- Kwana a Muzdalifa, daren goma ga Zul-Hijja har zuwa rabin dare.
4- Kwana a Mina a dararen Tashriƙ.
5- Jifan Jamrori (Shaiɗanu).
6- Kwalƙwal ko saisaye.
7- Dawafi bankwana.
C- Siffar Hajji:
Musulmi ya yi Talbiya da Hajji idan ya kai ga miƙati yana mai yin (niyyar) Ifradi idan lokacin ya zama ƙuntatacce. Idan ya iso Makka sai ya yi ɗawafi da sa'ayi, ya kasance akan haramarsa har ya wuce Arfa a ranar Arfa, rana ta tara kenan, ya tsaya a nan har rana ta faɗi.
Sannan ya juyo daga nan zuwa Muzdalifa yana mai yin Talbiya, ya tsaya a nan har ya yi sallar Asubah, sannan ya kasance a nan yana ambaton Allah yana Talbiya yana addu'a har gari ya washe.
Idan gari ya washe, sai ya wuce zuwa Mina kafin fitowar rana, sai ya jefi Jamratul Aƙabah (babban Shaiɗan) da tsakwankwani bakwai, sannan ya aske kai ƙwalƙwal ko saisaye, amma ƙwalƙwal shi yafi falala.
Sannan ya yi ɗawafin Ifadah, sa'ayin farko, da ya yi, ya ishe shi, da wannan aikin Hajjinsa ya cika kuma ya warware harama cikakkiyar warwarewa.
Abinda ya rage masa shi ne Jifan Jamrori (Shaiɗanu) a rana ta goma sha ɗaya da sha biyu. Idan ya kasance mai yin gaggawa ne; sai ya jefi Jamrori uku, kowacce Jamrah da tsakwankwani bakwai, yana mai yin kabbara a tare da kowacce tsakuwa, yana farawa da ƙaramin wanda yake bin masallacin Khaif, sannan na tsakiya, sannan Jamratul Aƙabah (babban Shaiɗan), shi ne na ƙarshe, zai jefi kowacce Jamrah da tsakwankwani bakwai. Idan ya yi nufin jinkirtawa, bayan rana ta goma sha biyu; sai ya yi jifa a rana ta goma sha uku kamar sifar jifansa a rana ta goma sha biyu da ta goma sha ɗaya.
Lokacin jifan: Bayan karkacewar rana ne a duka kwananki ukun.
Idan ya tafi a rana ta goma sha biyu kafin faɗuwar rana, to babu laifi. Idan ya zauna har ya yi jifa a rana ta goma sha uku bayan karkacewar rana, to hakan shi ya fi, saboda fadinSa - Maɗaukakin Sarki -:
﴿...فَمَن تَعَجَّلَ فِي يَوۡمَيۡنِ فَلَآ إِثۡمَ عَلَيۡهِ وَمَن تَأَخَّرَ فَلَآ إِثۡمَ عَلَيۡهِۖ لِمَنِ ٱتَّقَىٰ...﴾
{To, wanda ya yi gaggawa a cikin kwana biyu, to, bãbu laifi a kansa, kuma wanda ya jinkirta, to, bãbu laifi a kansa, ga wanda ya yi taƙawa...}
[al-Baƙara: 203].
Idan ya yi nufin tafiya; zai yi ɗawafi don ban kwana kewaye bakwai amma banda Sa'ayi.
Abinda ya fi, idan babu abin hadaya a tare da shi; ya yi harama da Umarah yana mai yin Tamattu'i, sannan ya yi Talbiya da Hajji a rana ta takwas, ya aikata irin abinda ya gabata na ayyukan Hajji. Idan ya yi harama da Hajji da Umarah gaba ɗaya to babu laifi, ana kiran hakan da Ƙirani, shi ne ya yi harama da Umarah da Hajji a tare da ɗawafi da Sa'ayi ɗaya.
Fasali na uku:
Abinda ke da alaƙa da Mu'amaloli
Malamai - Allah Ya yi musu rahama - sun bayyana ilimin da neman sanainsa yake wajibin aini (Wato akan kowa da kowa). kuma sun yi magana agwargwadan da neman saninsa shi ne farilla na aini akan kowane musulmi, sun ambata daga gare shi : Neman sanin hukunce-hukuncen cinikayya ga wanda yake kasuwanci, dan kar ya afka cikin haram ko riba, alhali shi bai sani ba, Haƙiƙa abinda zai ƙarfafa hakan ya zo daga wasu daga sahabbai - Allah Ya yarda da su -.
Umar ɗan Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - ya ce: «Babu wanda zai yi kasuwanci a kasuwarmu, sai wanda ya fahimci addini»61.
Aliyu ɗan Abu Dalib - Allah Ya yarda da shi - ya ce: «Wanda ya yi kasuwanci kafin ya fahinci addini; ya kutsa cikin riba, sannan ya kutsa, sannan ya kutsa. Wato: Ya faɗa cikin riba»62.
Ibnu Abidin ya faɗa, ya ciro daga al-Alami: "Farilla ne akan kowanne mukallafi namiji da mukallafa mace, bayan saninsa ilimin addini da shiriya, ya san ilimin alwala da wanka da sallah da azumi da ilimin zakka ga wanda yake da abinda ya kai nisabi, da Hajji ga wanda ya wajaba akansa da siye da siyarwa akan 'yan kasuwa, don su kiyaye shubuhohi da abubuwan da aka karhanta a ragowar mu'amaloli, haka nan masu sana'o'i, da dukkan wanda ya shagalta da wani abu wanda aka farlanta masa saninsa da hukuncinsa don ya hanu daga haram a cikinsa"63.
Nawawi - Allah Maɗaukakin Sarki Ya yi masa rahama - ya ce: "Amma siye da siyarwa, da aure da mai kama da su, daga abinda asalinsa ba ya wajaba, to haramun ne afka masa sai bayan sanin sharaɗinsa"64.
Waɗannan wasu ne daga ƙa'idoji masu alaka da mu'amaloli na kuɗi, waɗanda shari'ar musulunci ta zo da su:
1- Halaccin dukkan abinda a cikinsa akwai maslaha tsantsa, ko maslaha rinjiha; kamar siyar da abubuwan da aka halatta da siyensu da haya da shufu'ah65.
2- Halaccin dukkan abinda a cikinsa akwai lamuni ga haƙƙoƙin mutane da kiyayesu; kamar jingina da kafa shaida.
3- Halaccin dukkan abinda a cikinsa akwai maslahar masu ƙulla ciniki; kamar Iƙala da zaɓi da sharuɗɗa a cikin ciniki.
4- Hana dukkan a binda yake ƙunsar zalintar mutane, da cin dukiyoyinsu akan ƙarya; kamar riba da ƙwace da Ihtikar (Boye abin anfani har lokacin tsada).
5- Halaccin dukkan abinda acikinsa akwai taimakekeniya akan alheri; kamar rance da aro da ajiya.
6- Hana dukkan abinda yake ƙunsar cin dukiya ba tare da aiki ko anfani ko gajiya ba; kamar caca da riba.
7- Hana dukkan mu'amalar da jahilci da ruɗu suke rinjaya a cikinsu; kamar mutum ya saida abinda bai mallake shi ba, da saida abinda ba'a sani ba.
8- Hana dukkan abinda a cikinsa akwai dabara akan haram; kamar cinikin Inah66.
9- Hana abinda yake shagaltarwa daga biyayya ga Allah; kamar ciniki bayan kiran sallar Juma'a na biyu.
10- Hana dukkan abinda a cikinsa akwai cuta, ko yana haifar da gaba tsakanin musulmai; kamar saida a bubuwan da aka haramta, da cinikin mutum akan cinikin ɗan uwansa.
A Lokacin da hukuncin wata mas'ala daga cikin mas'aloli ya rikitar akan musulmi; to ya tambayi malamai game da ita, kada ya afka mata sai bayan sanin hukuncin shari'a a cikinta. kamar yadda Maɗaukkain sarki Ya ce:
﴿...فَاسْأَلُوا أَهْلَ الذِّكْرِ إِنْ كُنْتُمْ لَا تَعْلَمُونَ﴾
{...Sai ku tambayi wadanda suka sani idan kun kasance ba ku sani ba.} [al-Nahl: 43].
Wannan shi ne abinda tattara shi ya sawwaƙa. Allah ne abin roko Ya azirtamu ilimi mai anfani, da aiki na gari, lallai cewa Shi Mai yawan kyauta ne kuma Mai girma. Allah Yayi tsira Yayi aminci ga annabinmu Muhammad da alayensa da sahabbansa, Yayi aminci aminci mai yawa.
***
Teburin bayani
GABATARWA 2
FASALI NA FARKO: 3
ABINDA YAKE DA ALAKA DA AKIDA 3
Bincike na farko: Ma'anar musulunci da rukunansa: 3
Muhimmancin Tauhidi (kadaita Allah): 3
Ma’anar "Shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah": 5
Amma sharuɗɗan (babu abin bautawa dagaskiya sai Allah) to su ne: 5
Ma'anar shaidawa cewa (Annabi) Muhammad manzon Allah ne: 7
MABHASI NA BIYU: MA'ANAR IMANI DA RUKUNANSA: 9
1) Yin imani da Allah - Maɗaukakin Sarki - yana ƙunsar al'amurra guda uku: 10
1- Yin imani da RububiyyarSa: 10
2- Imani da UluhiyyarSa: 12
3- Imani da sunaye da siffofi: 15
2) Imani da Mala'iku: 22
3) Imani da Litattafai: 23
4) Imani da manzanni - aminci ya tabbata agare su -: 24
5) Imani da Ranar Lahira: 25
A- Imani da tashi. 26
B- Imani da hisabi da sakamako: 26
C- Imani da aljanna da wuta: 26
6) Imani da kaddara dukkaninta alherinta da kuma sharrinta: 27
MABHASI NA UKU: IHSANI (KYAUTAYI): 29
MADALABI NA HUDU: Taƙaitaccen bayani kan: Tushen Ahlus Sunnah Wal Jama'ah: 30
Fasali na biyu: Abinda ke da alaƙa da ibadu. 31
Mabhasi na farko: Tsarki: 31
Na farko: Rabe-raben ruwa: 31
Na biyu: Najasa: 32
Na uku: Abinda aikata shi yake haramta akan mai kari (hadasi): 34
NA HUDU: Ladubban biyan buƙata: 36
Na biyar: Hukunce-hukuncen tsarkin ruwa da tsarkin hoge: 37
Na shida: Hukunce-hukuncen alwala: 38
Na bakwai: Huknce-hukuncen shafa akan huffi biyu da jaurabi biyu: 40
Na takwas: Hukence-hukuncen Taimama: 42
Na tara: Hukunce-hukuncen al’ada da nifasi (jinin haihuwa): 44
Mabhasi na biyu: Sallah: 46
Na farko: Hukunce-hukncen kiran sallah da iƙama: 46
Na biyu: Matsayin sallah da falalarta: 49
Na uku: Sharuɗɗan sallah: 51
Na huɗu: Rukunan sallah: 53
Na biyar: Wajiban sallah: 57
Na shida: Sunnonin sallah: 58
Na bakwai: Siffar sallah: 60
Na takwas: Abubuwan da aka karhanta a sallah (abubuwan da ba'a son aikata su): 66
Na tara: Abubuwan da suke ɓata sallah: 66
Na goma: Sujjadar rafkanuwa: 67
Na goma sha ɗaya: Lokutan da aka hana yin sallah: 69
Na goma sha biyu: Sallar jam’i. 69
Na goma sha uku: Sallar tsoro: 72
Siffar sallar tsoro: 72
Na goma sha huɗu: Sallar Juma'a: 73
Na biyar: Mustahabban abubuwa (wadanda ake so) a ranar Juma'a: 75
Riskar sallar Juma'a: 76
Na goma sha biyar: Sallar masu uzurai: 76
Na goma sha shida: Sallolin idi biyu: 80
Na goma sha bakwai: Sallolin kisfewar rana da wata: 82
Na goma sha takwas: Sallar sha da fari (Sallar roƙon ruwa): 84
Na goma sha tara: Hukunce-hukuncen jana'iza: 85
MABHASI NA UKU: ZAKKAH: 89
1- Ta'arifin (bayanin) zakka da matsayinta: 89
2- Sharuɗɗan wajabcin zakka: 89
3- Dukiyoyuin da zakka take wajaba a cikinsu: 90
MABHASI NA HUƊU: AZUMI: 102
Sharuɗɗan wajabcin azumin Ramadan: 102
MABHASI NA BIYAR: HAJJI DA UMARAH. 109
Sharuɗɗan wajabcin Hajji da Umarah Umra: 110
Miƙatan yin harama: 112
Ihrami: 113
Umarah: 117
Hajji: 121
Fasali na uku: 124
Abinda ke da alaƙa da Mu'amaloli 124
***
Ahmad ya fiar da shi a Musnadinsa, lamba ta (6072), da Tirmizi a lamba ta (1535), kuma ya ce: Hadisi ne kyakkyawa.
Bukhari ya fitar da shi a cikin al-Adabul Mufrad a lamba ta (716), da Ahmad a cikin al-Musnad a lamba ta (19606), da Diya'ul Maƙdasi a cikin al'Ahadisul Mukhtarah (1/150), kuma Albani ya ingantashi a cikin Sahihul Jami'il sagir a lamba ta (3731).
Muslim ya fitar da shi a lamba ta (121), da Ahmad a al-Musnad a lamba ta (10434).
(Maziyyi): Ruwa ne me taushi, mara launi, yana fita yayin wasa, ko tunanin jima'i, ko nufin yinsa, ko kallo (na sha'awa) ko wanin wannan. Yana fita a yanayin ɗige-dige, kuma sau da yawa ma ba'a jin fitowarsa. (Wadiyyi): Ruwa ne mai kauri, fari da yake fita a gurbin (bayan) fitsari, ko a yayin ɗaukar wani abu mai nauyi.
Muslim ne ya fitar da shi, a lamba ta (224).
Malik ya fitar da shi a cikin Al-Muwaɗɗa’, a lamba ta (219 da 680), Al-Darimi, a lamba ta (312), da Abdurrazaƙ a cikin Musannaf nasa, a lamba ta (1328), Albani ya inganta shi a cikin Irwa’u Al-Ghaleel, a lamba ta (122).
Nasa’i ne ya fitar da shi a lamba ta (12808), da Ahmad a lamba ta (15423), kuma Albani ya inganta shi a cikin Irwa’ Al-Ghaleel a lamba ta (121).
Ibn Majah ya fitar da shi a lamba ta (594), da Ibn Hibban a lamba ta (799), kuma Albani ya ce yana da rauni a cikin Da’if Sunan Al-Tirmizi a lamba ta (146).
Bukhari ya fitar da shi a lamba ta (142), da Muslim a lamba ta (122).
Bukhari ya fitar da shi, a lamba ta (7288), da Muslim a lamba ta (6066).
Babban malami Abdul'Aziz Ibnu Baz - Allah Ya yi masa rahama - ya faɗa a cikin Majmu'u Fatawansa (29/141): (al-Baihaƙi ya ƙara da sanadi mai kyau, daga Jabir bayan faɗinsa: «Wanda Ka yi alƙawarinsa»: «Lallai Kai baKa saɓa alƙawari»).
Tirmizi ya fitar da shi a lamba ta (2635).
Muslim ne ya fitar da shi a lamba ta (82).
Tirmizi ya fitar da shi a lamba ta (265), kuma ya ce: Hadisin Hasan ne Sahihi Garibi, kuma Albany ya inganta shi a Sahih al-Targib wa al-Tarhib.
Bukhari ya fitar da shi a lamba ta (1117).
Bukhari ya fitar da shi a lamba ta (6251), da Muslim a lamba ta (884).
Bukhari ya fitar da shi a lamba ta (756), da Muslim a lamba ta (872).
Bukhari ya fitar da shi a lamba ta (793), da Muslim a lamba ta (398).
Bukhari ne ya fitar da shi a lamba ta (812), da Muslim a lamba ta (490).
Muslim ne ya fitar da shi (498).
Bukhari ne ya fitar da shi a lamba ta (724), da Muslim a lamba ta (398).
Bukhari ya fitar da shi (797), da Muslim (402).
Tirmizi ya fitar da shi a lamba ta (839).
Bukhari ne ya fitar da shi a lamba ta (6008).
Bukhari ne ya fitar da shi a lamba ta (1110).
Bukhari ne ya fitar da shi a lamba ta (835).
Bukhari ne ya fitar da shi, a lamba ta (743), da Muslim a lamba ta (399).
Tirmizi ne ya fitar da shi, a lamba ta (266).
Muslim ne ya fitar da shi, a lamba ta (588).
Abu Dawud ne ya fitar da shi a lamba ta (5168).
Tirmizi ne ya fitar da shi, a lamba ta (284).
Muslim ne ya fitar da shi a lamba ta (1484).
Bukhari ne ya fitar da shi a lamba ta (609), da Muslim a lamba ta (602).
Bukhari ne ya fitar da shi a lamba ta (4130), da Muslim a lamba ta (842).
Muslim ne ya fitar da shi a lamba ta (865).
Bukhari ne ya fitar da shi a lamba ta (934), da Muslim a lamba ta (851).
Bukhari ya fitar da shi a lamba ta (1081), a Muslim da lamba ta (693).
Bukhari ne ya fitar da shi a lamba ta (1012), da Muslim a lamba ta (894).
Abu Dawud ne ya fitar da shi a lamba ta (3201), da Tirmizi a lamba ta (1024) kum ya ce: Hadisi ne Hasani Sahihi.
Muslim ne ya fitar da shi a lamba ta (962).
Bukhari ne ya fitar da shi a lamba ta (8), da Muslim a lamba TA (111).
Ibn Majah ya fitar da shi a lamba ta (1792), da Tirmizi a lamba ta (63) da (631).
Bukhari ne ya fitar da shi da lamba (1402), da Muslim da lamba (2287).
Bukhari ne ya fitar da shi a lamba ta (1432), da Muslim a lamba ta (984).
Abu Dawuda ne ya fitar da shi a lamba ta (1609), da Ibn Majah a lamba ta (1827), Albani ya inganta shi a cikin Sahih Abi Dawud, lamba ta (1609).
Bukhari ne ya fitar da shi a lamba ta (1), da Muslim a lamba ta (1907).
Bukhari ne ya fitar da shi a lamba ta (1810), da Muslim a lamba ta (1086).
Bukhari ne ya fitar da shi a lamba ta (1909).
Ahmad ne ya fitar da shi a hadisi mai lamba (26457), da Abu Dawud a lamba ta (2454), da Nasa’i a lamba ta (2331), kuma wannan lafazinsa ne:
Bukhari ne ya fitar da shi a lamba ta (6669), da Muslim a lamba ta (2709).
Abu Dawuda ne ya fitar da shi a lamba ta (2380), da Tirmizi a lamba ta (719), da Ibn Majah a lamba ta (676).
Bukhari ne ya fitar da shi a lamba ta (1849), da Muslim a lamba ta (1846).
Muslim ne ya fitar da shi a lamba ta (1134).
Ahmad ne ya fitar da shi a lamba ta(25198), da Nasa’i a lamba ta (2627), da Ibn Majah a lamba ta (2901).
Bukhari ne ya fitar da shi a lamba ta (1862), da Muslim a lamba ta (1341).
Bukhari ne ya fitar da shi a lamba ta (1531).
Muslim ne ya fitar da shi a lamba ta (1211).
Bukhari ne ya fitar da shi, a lamba ta (1549).
Muslim ne ya fitar da shi a lamba ta (1218).
Tirmizi ne ya fitar da shi a lamba ta (487), kuma ya ce: Hasani ne Garibi, kuma Albani ya Hassana shi.
A duba: Mugni al-Muhtaj (2/22).
Hashiyatu ibn Abideen (1/42).
A duba: al-Majmu'u (1/50).
al-Shufu'a: Ita ce cancantar abokin tarayya karɓar kason abokin tarayyarsa daga duk wanda ya cirata zuwa gare shi da biyan kudi.
Cinikin Inah: Shi ne mutum ya siyarwa da wani mutumin wani abu da kuɗi abun jinkirtawa, kuma ya miƙa masa, sannan ya siyi abun kafin karɓar kuɗin da mafi ƙaranci daga wannan kuɗin, kuɗi hannu.
Bukhari ne ya fitar da shi da lamba ta (8).