PHPWord

 

 

 

حِرَاسَةُ التَّوحِيدِ

 

KARE TAUHIDI

 

 

 

 

 

لِسَمَاحَةِ الشَّيْخِ العَلَّامَةِ

عَبْدِ العَزِيزِ بْنِ عَبْدِ اللهِ بْنِ بَازٍ

رَحِمَهُ اللهُ

 

Wallafar: Babban Malami

AbdulAzeez Bin Abdullahi Bin Baaz

Allah Yayi masa rahama

 

 

 


بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ

SAƘO NA FARKO

Aƙida ingantacciya da abinda yake kishiyantarta

Wallafar: Babban Malami

AbdulAzeez Bin Abdullahi Bin Baaz

Godiya ta tabbata ga Allah Shi kaɗai, tsira da aminci su tabbata ga wanda babu wani annabi a bayansa, da alayen sa da sahabban sa.

Bayan haka: A yayin da ingantacciyar aƙidah ta kasance ita ce asalin Musulinci, kuma tushen addini, sai na ga cewa yana daga abu mai muhimmanci yin magana akan wannan batun, da kuma yin rubutu da wallafa domin bayaninsa da kuma fayyace shi.

Abu ne da yake sananne akan dalilai na shari’a daga Alƙur’ani da Hadisi: Cewa ayyuka da maganganu suna ingantane kuma a karɓe su idan suka kasance daga ingantacciyar aƙidah. Amma idan aƙidah ta kasance gurɓatacciya, to fa duk abinda ya rassantu daga gare ta na ayyuka da maganganu ya zama ɓatacce, kamar yadda Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿...وَمَن يَكۡفُرۡ بِٱلۡإِيمَٰنِ فَقَدۡ حَبِطَ عَمَلُهُۥ وَهُوَ فِي ٱلۡأٓخِرَةِ مِنَ ٱلۡخَٰسِرِينَ﴾

{Kuma wanda ya kãfirta da ĩmãni to, lalle ne aikinsa yã ɓãci, kuma shĩ, a cikin Lãhira, yanã daga mãsu hasãra.} [al-Ma'ida: 5].

Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿وَلَقَدۡ أُوحِيَ إِلَيۡكَ وَإِلَى ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِكَ لَئِنۡ أَشۡرَكۡتَ لَيَحۡبَطَنَّ عَمَلُكَ وَلَتَكُونَنَّ مِنَ ٱلۡخَٰسِرِينَ 65﴾

{Kuma hakika an yi wahayi zuwa gare ka da kuma zuwa ga waɗanda suke a gabãninka, "Lalle idan ka yi shirki haƙĩƙa aikinka zai ɓãci, kuma lalle zã ka kasance daga mãsu hasãra."} [al-Zumar: 65],

Kuma ayoyi da suka zo da wannan ma’anar suna da yawa. Kuma tabbas littafin Allah mabayyani da sunnar Manzon Sa amintacce - mafificin salati da aminci su tabbata a gare shi daga Ubangijin sa -; sun yi bayani akan aƙidah nagartacciya tana dunƙule ne a cikin abubuwa shida, su ne kamar haka: Imani da Allah, da Mala’iku da Littattafai da Manzanni da ranar lahira da kuma ƙaddara alkhairin ta da sharrin ta. To waɗannan abubuwa shida, su ne tushen aƙidah ingantacciya, waɗanda littafin Allah mai buwaya ya saukar da su, kuma Allah Ya aiko Manzon shi (Annabi) Muhammad - tsira da aminci su tabbata a gare shi - da ita.

Kuma tabbas dalilai masu yawa sun zo akan waɗannan tushen guda shida a cikin Alƙur’ani da kuma sunnah ingantacciya, daga cikin haka abinda zaizo domin buga misali:

Na farko: Dalilai daga Alƙur’ani; daga cikin su akwai faɗin Allah - Mai girma da ɗaukaka -:

﴿لَّيۡسَ ٱلۡبِرَّ أَن تُوَلُّواْ وُجُوهَكُمۡ قِبَلَ ٱلۡمَشۡرِقِ وَٱلۡمَغۡرِبِ وَلَٰكِنَّ ٱلۡبِرَّ مَنۡ ءَامَنَ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِ وَٱلۡمَلَٰٓئِكَةِ وَٱلۡكِتَٰبِ وَٱلنَّبِيِّـۧنَ...﴾

{Bai zama addini ba dõmin kun jũyar da fuskõkinku wajen gabas da yamma, kuma amma addini shi ne ga wanda ya yi ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira da malã'iku da Littattafan (sama) da Annabãwa.} [al-Baƙara: 177].

Da faɗinSa Allah - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka -:

﴿ءَامَنَ ٱلرَّسُولُ بِمَآ أُنزِلَ إِلَيۡهِ مِن رَّبِّهِۦ وَٱلۡمُؤۡمِنُونَۚ كُلٌّ ءَامَنَ بِٱللَّهِ وَمَلَٰٓئِكَتِهِۦ وَكُتُبِهِۦ وَرُسُلِهِۦ لَا نُفَرِّقُ بَيۡنَ أَحَدٖ مِّن رُّسُلِهِ...﴾

{Manzon Allah yã yi ĩmãni da abin da aka saukar zuwa gare shi daga Ubangijinsa, da mũminai. Kõwanensu yã yi ĩmãni da Allah, da mala'ikunSa, da littattafanSa, da manzanninSa. Bã mu rarrabẽwa a tsakãnin ɗaya daga ManzanninSa".} [al-Baƙara: 285].

Da faɗinSa - tsarki ya tabbatar maSa -:

﴿يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ ءَامِنُواْ بِٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦ وَٱلۡكِتَٰبِ ٱلَّذِي نَزَّلَ عَلَىٰ رَسُولِهِۦ وَٱلۡكِتَٰبِ ٱلَّذِيٓ أَنزَلَ مِن قَبۡلُۚ وَمَن يَكۡفُرۡ بِٱللَّهِ وَمَلَٰٓئِكَتِهِۦ وَكُتُبِهِۦ وَرُسُلِهِۦ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِ فَقَدۡ ضَلَّ ضَلَٰلَۢا بَعِيدًا 136﴾

{Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi ĩmãni da Allah da Manzonsa, da Littãfin da Ya sassaukar ga ManzonSa da Littãfin nan wanda Ya saukar daga gabãni. To, wanda ya kãfirta da Allah da malã'ikunSa, da LittattafanSa, da ManzanninSa, da Rãnar Lãhira, to, lalle ne yã ɓace, ɓata mai nĩsa.} [al-Nisa'i: 136].

Da faɗinSa - tsarki ya tabbatar maSa -:

﴿أَلَمۡ تَعۡلَمۡ أَنَّ ٱللَّهَ يَعۡلَمُ مَا فِي ٱلسَّمَآءِ وَٱلۡأَرۡضِۚ إِنَّ ذَٰلِكَ فِي كِتَٰبٍۚ إِنَّ ذَٰلِكَ عَلَى ٱللَّهِ يَسِيرٞ 70﴾

{Ashe, ba ka sani ba, lalle ne Allah Yanã sanin abin da yake a cikin sama da ƙasa? Lalle ne wancan yanã cikin Littafi, lalle wancan ga Allah mai sauƙi ne.} [al- Hajj: 70].

Na biyu: Dalilai daga Sunnah; Daga ciki akwai hadisi ingantacce shahararre wanda Muslim ya ruwaito shi a Sahihin ɗinsa cikin hadisin sarkin muminai Umar ɗan al-Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi -, cewa (Mala’ika) Jibrilu - aminci ya tabbata a gare shi - ya tambayi annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - dangane da imani, sai ya ce da shi: «Imani: (shi ne) ka yi imani da Allah, da mala'ikunSa da littattafanSa, da ManzanninSa, da ranar lahira, kuma ka yi imani da ƙaddara: alkhairinta da sharrinta»1. Hadisi, Kuma Bukhari da Muslim- tare da banbanci kaɗan - sun fitar da shi cikin hadisin Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -.

Kuma yana karkasuwa daga cikin waɗannan tushan guda shida: Dukkan abinda yake wajaba musulmi ya ƙudurce shi, ya kuma yi imani da shi, na haƙƙin Allah - Mai girma da ɗaukaka -, da al’amarin lahira, da wanin haka na al'amuran gaibu, wanda Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya bada labarin sa, da ManzonSa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -

Bayanin waɗannan asali guda shida shi ne kamar haka:

ASALI NA FARKO: Imani da Allah - Maɗaukakin Sarki -, hakan kuma yana ƙunsar abubuwa da dama; daga cikinsu akwai:

Shi imani (da Allah) yana ƙunsar al'amurra da dama; daga cikinsu: Imani da cewa Shi ne Ubangiji na gaskiya wanda Ya cancanci bauta banda waninSa; saboda kasantuwar Sa Mahaliccin bayi, Mai kyautata musu, Mai tsayuwa akan arzuƙansu, Masanin sirrin su da kuma zahirin su, kuma Mai iko akan bada lada ga mai biyayya a cikin su da kuma yin uƙuba ga wanda ya saɓa a cikin su.

Haƙiƙa Allah Ya halicci mutum da aljan saboda wannan bautar, kuma Ya umarce su da ita, kamar yadda Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya faɗa:

﴿وَمَا خَلَقۡتُ ٱلۡجِنَّ وَٱلۡإِنسَ إِلَّا لِيَعۡبُدُونِ 56 مَآ أُرِيدُ مِنۡهُم مِّن رِّزۡقٖ وَمَآ أُرِيدُ أَن يُطۡعِمُونِ 57 إِنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلرَّزَّاقُ ذُو ٱلۡقُوَّةِ ٱلۡمَتِينُ 58﴾

{Kuma Ban halitta aljannu da mutãne ba sai dõmin su bauta Mini,

Ba na nufin wani arziƙi daga garesu, kuma ba na nufin su ciyar dani,

{Lalle Allah, Shĩ ne Mai azurtãwa, Mai ĩkon yi, Mai cikakken ƙarfi.} [al-Zariyāt: 56-58].

Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ ٱعۡبُدُواْ رَبَّكُمُ ٱلَّذِي خَلَقَكُمۡ وَٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِكُمۡ لَعَلَّكُمۡ تَتَّقُونَ 21 ٱلَّذِي جَعَلَ لَكُمُ ٱلۡأَرۡضَ فِرَٰشٗا وَٱلسَّمَآءَ بِنَآءٗ وَأَنزَلَ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءٗ فَأَخۡرَجَ بِهِۦ مِنَ ٱلثَّمَرَٰتِ رِزۡقٗا لَّكُمۡۖ فَلَا تَجۡعَلُواْ لِلَّهِ أَندَادٗا وَأَنتُمۡ تَعۡلَمُونَ 22﴾

{Yã ku mutãne! Ku bauta wa Ubangjinku, Wanda Ya halicce ku, kũ da waɗanda suke daga gabãninku, tsammãninku ku kãre kanku!,

{Wanda Ya sanya muku ƙasa shimfiɗa, kuma sama gini, kuma Ya saukar da ruwa daga sama, sa'an nan Ya fitar da abinci daga 'ya'yan itãce game da shi, sabõda ku. Sabõda haka kada ku sanya wa Allah wasu kĩshiyõyi, alhãli kuwa kuna sane.} [al-Baƙara: 21-22].

Haƙiƙa Allah Ya aiko Manzanni, kuma Ya saukar da littattafai, domin bayanin wannan gaskiyar, da kuma kira zuwa gare ta da kuma tsawatarwa daga abinda yake kishiyantar ta, kamar yadda Allah - tsarki ya tabbata a gare Shi - Ya ce:

﴿وَلَقَدۡ بَعَثۡنَا فِي كُلِّ أُمَّةٖ رَّسُولًا أَنِ ٱعۡبُدُواْ ٱللَّهَ وَٱجۡتَنِبُواْ ٱلطَّٰغُوتَ...﴾

{Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun aika a cikin kõwace al'umma da wani Manzo (ya ce): "Ku bauta wa Allah, kuma ku nĩsanci ɗãgũtu."} [al-Nahl: 36].

Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿وَمَآ أَرۡسَلۡنَا مِن قَبۡلِكَ مِن رَّسُولٍ إِلَّا نُوحِيٓ إِلَيۡهِ أَنَّهُۥ لَآ إِلَٰهَ إِلَّآ أَنَا۠ فَٱعۡبُدُونِ25﴾

{Kuma ba Mu aiki wani Manzo ba a gabãninka fãce Munã yin wahayi zuwa gare shi, cẽwa "Lalle ne Shi, bãbu abin bautãwa fãce Nĩ, sai ku bauta Mini."} [al-Anbiya: 25].

Kuma Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya ce

﴿الر كِتَابٌ أُحْكِمَتْ آيَاتُهُ ثُمَّ فُصِّلَتْ مِنْ لَدُنْ حَكِيمٍ خَبِيرٍ1 أَلَّا تَعْبُدُوا إِلَّا اللَّهَ إِنَّنِي لَكُمْ مِنْهُ نَذِيرٌ وَبَشِيرٌ2﴾

{A. L̃.R. Littãfi ne an kyautata ãyõyinsa, sa'an nan an bayyanã su daki-daki, daga wurin Mai hikima, Mai ƙididdigewa,

{Kada ku bautã wa kõwa fãce Allah. Lalle ne ni a gare ku mai gargaɗi ne kuma mai bushãrã daga gare Shi} [Hud: 1, 2].

Kuma haƙiƙanin wannan ibadar: Ita ce kaɗaita Allah - tsarki ya tabbata a gare Shi- da dukkanin abinda bayi suke bauta da shi; na addu’a, da tsoro, da ƙauna, da sallah, da azumi, da yanka, da bakance, da wanin haka na nau’ukan ibada, ta fuskar ƙanƙan da kai gare Shi da kwaɗayin lada, da kuma tsoron uƙubar Sa tare da cikakken so gare Shi da ƙasƙantar da kai ga girman Sa.

Wanda ya yi la’akari da Alƙur’ani mai girma zai samu mafi yawan sa ya sauka ne akan wannan asali mai girma; kamar faɗin Allah - Mai tsarki da ɗaukaka -:

﴿إِنَّآ أَنزَلۡنَآ إِلَيۡكَ ٱلۡكِتَٰبَ بِٱلۡحَقِّ فَٱعۡبُدِ ٱللَّهَ مُخۡلِصٗا لَّهُ ٱلدِّينَ فَاعْبُدِ اللَّهَ مُخْلِصًا لَهُ الدِّينَ 2 أَلَا لِلَّهِ الدِّينُ الْخَالِصُ وَٱلَّذِينَ ٱتَّخَذُواْ مِن دُونِهِۦٓ أَوۡلِيَآءَ مَا نَعۡبُدُهُمۡ إِلَّا لِيُقَرِّبُونَآ إِلَى ٱللَّهِ زُلۡفَىٰٓ إِنَّ ٱللَّهَ يَحۡكُمُ بَيۡنَهُمۡ فِي مَا هُمۡ فِيهِ يَخۡتَلِفُونَۗ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَهۡدِي مَنۡ هُوَ كَٰذِبٞ كَفَّارٞ3﴾

{Mun saukar da littafi a gareka da gaskiya to sai ka bautawa Allah kana mai tsarkake Addini a gare Shi}

{To, addini tsarkakakke na Allah ne, kuma waɗanda suka riƙi waɗansu majibinta, bã Shi ba, (sunã cẽwa) "Ba mu bauta musu ba fãce dõmin su kusantar da mu zuwa ga Allah, kusantar daraja." Lalle Allah nã yin hukunci a tsakãninsu ga abin da suka zama sunã sãɓãwa a cikinsa. Lalle Allah ba Ya shiryar da wanda yake mai ƙarya, mai kãfirci} [al-Zumar: 2-3].

Da faɗinSa Allah - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka -:

﴿وَقَضَىٰ رَبُّكَ أَلَّا تَعۡبُدُوٓاْ إِلَّآ إِيَّاهُ...﴾

{Kuma Ubangijinka Ya hukunta kada ku bauta wa kõwa fãce Shi} [al-Isra'a: 23].

Da faɗinSa - Mai girma da ɗaukaka -

﴿فَٱدۡعُواْ ٱللَّهَ مُخۡلِصِينَ لَهُ ٱلدِّينَ وَلَوۡ كَرِهَ ٱلۡكَٰفِرُونَ14﴾

{Sabõda haka ku kirãyi Allah, kunã mãsu tsarkake addini a gare Shi, kuma kõ dã kãfirai sun ƙi.} [Gafir: 14].

Haka kuma, wanda yayi la’akari da sunna ta Annabta zai sami kulawa ta musamman ga wannan asalin mai girma, daga wannan: Abinda aka ruwaito a cikin Bukhari da Muslim daga Mu’az - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Haƙƙin Allah akan bayinSa shi ne su bauta maSa kada su haɗa Shi da komai"2.

Yana shiga ƙarƙashin imani da Allah kuma: Imani da duk abinda Ya wajabta shi akan bayinSa, Ya kuma farlanta shi a kan su, na shika-shikan Musulinci biyar na zahiri.

Su ne: Shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Annabi Muhammad bawan Allah ne, da tsaida sallah, da bayar da zakkah, da azumin watan Ramadan da Hajjin Ɗakin Allah mai alfarma ga wanda ya sami ikon tafarki zuwa gare shi, da wanin haka na farillai, waɗanda shari’a tsarkakiyya ta zo da su.

Mafi muhimmancin waɗannan rukunan shine: Shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma (Annabi) Muhammad Manzon Allah ne. Wannan shaidawar tana hukunta: Tsarkake ibada ga Allah Shi kaɗai, da kuma kore ta ga duk wanda ba Shi ba, wannan shi ne ma’anar: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, wato ma’anar ta - kamar yadda malamai suka ce - Allah Yayi musu rahama -: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma gini akan hakan shine: Duk abinda aka bautawa bayan Allah- mutum ne ko mala’ika ko aljan ko wanin wannan -, to abin bautawa ne ba na gaskiya ba, abin bauta na gaskiya Shi ne Allah Shi kaɗai, kuma babu abokin tarayya a tare da Shi, kamar yadda Allah - Mai tsarki da ɗaukaka - Ya ce:

﴿ذَٰلِكَ بِأَنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلۡحَقُّ وَأَنَّ مَا يَدۡعُونَ مِن دُونِهِۦ هُوَ ٱلۡبَٰطِلُ...﴾

{Wancan! sabõda lalle ne Allah, shĩ ne Gaskiya, kuma lalle ne, abin da suke kira waninSa shi ne ƙarya.} [al-Hajj: 62].

Kuma haƙiƙa bayani ya gabata: Cewa lalle Allah - tsarki ya tabbata a gare Shi Ya ɗaukaka -, Ya halicci mutum da aljan ne domin wannan asali mai tushe, kuma Ya umarce su da shi, kuma Ya aiko ManzanninSa da shi, kuma Ya saukar da littattafanSa da shi; to ya zama wajibi ga bawa ya yi la’akari da wannan sosai, ya kuma yi tadabburinsa sosai; domin jahilci mai girma na wannan asalin da musulmai suka faɗa ya bayyana a gare shi; har ya kai sun bautawa Allah tare da waninSa, suka juyar da tsantsar haƙƙinSa ga waninSa, Allah Shi ne Abin neman taimako.

Yana daga cikin imani da Allah - tsarki ya tabba a gare Shi - imani da cewar Shi ne Mahalicci Masani kuma Mai juya lamuransu kuma Mai tasarrufi a cikinsu da iliminSa da ikonSa, kamar yadda Ya ga dama - tsarki ya tabbata a gare Shi -, kuma lalle Shine Mamallakin duniya da lahira, kuma Ubangijin talikai baki ɗaya, babu Mahalicci in ba Shi ba, kuma babu Ubangiji in ba Shi ba. Kuma Ya aiko Manzanni Ya kuma saukar da littattafai; domin gyara bayi, da kuma kiransu ga abinda yake tsira ne gare su da kuma gyara gare su a nan duniya da kuma lahira. Kuma lalle Shi Allah - tsarki ya tabbata a gare Shi -, ba Shi da abokin tarayya a dukkanin hakan, Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿ٱللَّهُ خَٰلِقُ كُلِّ شَيۡءٖۖ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ وَكِيلٞ 62﴾

{Allah ne Mai halittan dukkan kõme, kuma Shĩ ne Wakĩli a kan kõme.} [al-Zumar: 62].

Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿إِنَّ رَبَّكُمُ ٱللَّهُ ٱلَّذِي خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ فِي سِتَّةِ أَيَّامٖ ثُمَّ ٱسۡتَوَىٰ عَلَى ٱلۡعَرۡشِۖ يُغۡشِي ٱلَّيۡلَ ٱلنَّهَارَ يَطۡلُبُهُۥ حَثِيثٗا وَٱلشَّمۡسَ وَٱلۡقَمَرَ وَٱلنُّجُومَ مُسَخَّرَٰتِۭ بِأَمۡرِهِۦٓۗ أَلَا لَهُ ٱلۡخَلۡقُ وَٱلۡأَمۡرُۗ تَبَارَكَ ٱللَّهُ رَبُّ ٱلۡعَٰلَمِينَ54﴾

{Lalle ne Ubangijinku Allah ne, wanda Ya halicci sammai da ƙasa a cikin kwãnaki shida, sa'an nan kuma Ya daidaita a kan Al'arshi, Yanã sanya dare ya rufa yini, yanã nẽman sa da gaggawa, kuma rãnã da watã da taurãri hõrarru ne da umurninSa. To, Shĩ ne da halittar kuma da umurnin. Albarkar Allah Ubangijin halittu tã bayyana!.} [al-A'araf: 54].

Yana daga cikin imani da Allah - Maɗaukakin Sarki -: Imani da sunayansSa kyawawa da kuma siffofinSa maɗaukaka a littafinSa mabuwayi, kuma waɗanda suka tabbata daga ManzonSa amintacce, ba tare juyarwa ko korewa ba, kuma ba tare da surantawa ko kamantawa ba,

﴿...لَيۡسَ كَمِثۡلِهِۦ شَيۡءٞۖ وَهُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡبَصِيرُ﴾

{Wani abu bai zama kamar tamkarSa ba, kuma Shĩ ne Mai ji, Mai gani.} [al-Shura:11].

To yana wajaba a tafiyar da su ba tare da surantawa ba, tare da imani da abinda suka yi nuni akan sa na ma’anoni masu girma, waɗanda suke su ne siffofin Allah - Mai girma da ɗaukaka -, da kuma wajibcin siffanta Shi - Maɗaukakin Sarki - da su a fuskar da ta dace da Shi, ba tare da an kamanta halittun Sa a wani abu daga siffofinSa ba, kamar yadda Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce: Kuma Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya ce

﴿فَلَا تَضۡرِبُواْ لِلَّهِ ٱلۡأَمۡثَالَۚ إِنَّ ٱللَّهَ يَعۡلَمُ وَأَنتُمۡ لَا تَعۡلَمُونَ74﴾

{Sa'an nan kada ku bãyar da waɗansu misãlai ga Allah. Lalle ne Allah Yanã sani, kuma kũ, ba ku sani ba.} [al-Nahl: 74].

Wannan ita ce aƙidar Ahlussunna wal Jama’a daga sahabban Ma’aikin Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da mabiyansu da kyautatawa; a sunayan Allah da kuma siffofinSa, ita ce kuma wadda Imam: Abul Hasan al’Ash’ari - Allah Ya yi masa rahama - ya naƙalto ta a cikin littafin: “al-Maƙālat”, daga malaman hadisi da Ahlussunna, kuma wasun sa daga cikin ma'abota ilimi da imani suka naƙalto ta.

Al-Auza’i - Allah Ya yi masa rahama - ya ce: An tambayi az-Zuhri da Makhul, dangane da ayoyin da suke bayanin siffofin Allah, sai suka ce: Ku wuce su kamar yadda suka zo.3

Kuma al-Auza’i - Allah Ya yi masa rahama - ya faɗa dai: Mun kasance mu da tabi'ai mun haɗu muna cewa: Allah - tsarki ya tabbata a gare Shi -, Yana kan al’arshinSa, kuma muna imani da abinda ya zo a sunna, na Siffofi"4.

Kuma al-Walidu ɗan Muslim - Allah Ya yi masa rahama - ya ce: (An tambayi Maliku da al-Awza’i da al-Laisu ɗan Sa’ad, da Sufyan al-Thauri - Allah Ya yi musu rahama -, dangane da bayanan da suka zo akan siffofin Allah, sai baki ɗayansu suka ce: Ku wuce su kamar yadda suka zo, ba tare da faɗin yadda kaifiyyarsu take ba)5.

A lokacin da aka tambayi Rabi’atu bn Abdurrahman - malamin Maliku - Allah Ya yi musu rahama - dangane da al-Istiwa’u (daidaituwar Allah a akan Al-arshi), sai ya ce: al-Istiwa'u aba ce da aka santa, amma yadda take ba za’a iya hankalta ba, saƙo daga Allah yake, isarwa mabayyaniya ce akan Manzo, mu kuma gasgatawa ce a kan mu6. Kuma a lokacin da aka tambayi Imamu Malik - Allah Ya yi masa rahama - dangane da hakan, sai ya ce: (Istiwa'i sanannen abu ce, yadda ya ke kuma ba’a sani ba, imani da hakan wajibi ne, tambaya akan hakan kuma bidi’a ce.)

Sannan ya cewa wanda ya yi tambayar: Ba ni ganinka face mugun mutum! Sai ya yi umarnin a fitar da shi.7. Kuma haƙiƙa an ruwaito wannan ma’anar daga Uwar muminai Ummu Salamah, - Allah Ya yarda da ita -8.

Imam Abu Abdurrahman bn al-Mubarak - Allah Ya yi masa rahama ya ce -:(Muna sanin Ubangijin mu - Maɗaukakin Sarki - da cewar Shi Yana saman samman Sa akan al’arahin Sa nesa da halittun Sa9.

Magaganun manyan malamai a wannan babin yana da yawa sosai, ba zai yi wu akawo duka a wannan lakcar ba, wanda yake son yasan mafi yawa daga wannan, sai ya koma ga abinda malaman sunnah suka rubuta a wannan babin, kamar : Littafin "al-Sunnah", na Abdullahi bn Imam Ahmad, da littafin "al-Tauhid" na babban malami Muhammad bn Khuzaimah, da littafin "al-Sunnah" na Abubakar bn Abu Asim, da amsar da IbnTaimiyya ya bayar ga mutanen Hamah (Hamawiyyah). Shi amsa ce mai girma, mai yawan fa'idodi, - Allah Ya yi masa rahama -, ya yi bayanin aƙidar Ahlussunna wal Jama’ah a fayyace, kuma ya kawo da yawa daga maganganun su, da dalilai na shari'ah da na hankali akan ingancin abinda da yawa daga Ahlussunah suka faɗa, da ɓata abinda masu husumar su suka faɗa.

Haka nan littafin sa mai suna al-Tadmuriyyah; haƙiƙa ya shimfiɗa (bayanin) matsaya, ya kuma bayyana aƙidar Ahlussunnah da dalilanta waɗanda aka cirato da kuma na hankali, ya kuma yi raddi ga waɗanda suka saɓa da abinda yake bayyanar da gaskiya, kuma yana turmushe ƙarya ga dukkan wanda ya yi nazari ga wannan cikin ma'abota ilimi; da kyakkyawan nufi, da kuma kwaɗayin sanin gaskiya. A taƙaice: Ita aƙidar Ahlussunnah wal jama'a a babin sunayen Allah da siffofinSa; cewa su sun tabbatar wa Allah - tsarki ya tabbata a gare Shi - abinda Ya tabbatarwa kanSa a cikin littafinSa, ko kuma ManzonSa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya tabbatar maSa a cikin sunnar sa, tabbatarwa ba tare da kamantawa ba, suka tsarkake Shi - tsarki ya tabbata a gare Shi -, daga barin kamaceceniya da halittarSa, tsarkakewar da ta barranta daga korewa Allah siffah; sai suka rabauta da amincewa daga cin karo da juna. Kuma suka yi aiki da dukkanin dalilai, domin dacewa daga Allah; domin yana daga cikin sunnar Allah - tsarki ya tabbata a gare Shi - ga wanda ya yi ruƙo da gaskiya wacce ya aiko ManzanninSa da ita, ya kuma yi ƙoƙari akan hakan, ya tsarkake niyya wurin neman ta; da Ya datar da shi ga gaskiya, Ya kuma bayyana hujjar sa, kamar yadda Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿بَلۡ نَقۡذِفُ بِٱلۡحَقِّ عَلَى ٱلۡبَٰطِلِ فَيَدۡمَغُهُۥ فَإِذَا هُوَ زَاهِقٞ...﴾

{Ã'a, Munã jĩfa da gaskiya a kan ƙarya, sai ta darkãke ta, sai ga tã halakakka.} [al-Anbiya:18].

Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿وَلَا يَأۡتُونَكَ بِمَثَلٍ إِلَّا جِئۡنَٰكَ بِٱلۡحَقِّ وَأَحۡسَنَ تَفۡسِيرًا33﴾

{Kuma bã zã su zo maka da wani misãli ba, fãce Mun je maka da gaskiya da mafi kyau ga fassara.} [al-Furƙan: 33].

Amma wanda ya saɓa wa Ahlussunnah: A cikin abinda suka ƙudirce a babin sunaye da siffofi; to haƙiƙa babu makawa cikin saɓawa dalilan da aka cirato da kuma na hankali; tare tufka da warwara a bayyane a duk abinda zai tabbatar da shi ko ya kore shi. Haƙiƙa al-Hafiz Ibn Kasir - Allah Ya yi masa rahama - a Tafsirin sa shahararre, ya ambaci magana mai kyau a wannan batu, wannan kuwa a zancen sa a daidai faɗin Allah

- Mai girma da ɗaukaka -:

﴿إِنَّ رَبَّكُمُ ٱللَّهُ ٱلَّذِي خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ فِي سِتَّةِ أَيَّامٖ ثُمَّ ٱسۡتَوَىٰ عَلَى ٱلۡعَرۡشِ...﴾

{Lalle ne Ubangijinku Allah ne, wanda Ya halitta sammai da ƙasa a cikin kwãnaki shida, sa'an nan kuma Ya daidaita a kan Al'arshi.} [al-A'araf: 54].

Zai kyautu mu kawo maganar a nan; saboda girman fa'idar ta, sai ya faɗa - Allah Ya yi masa rahama - abinda ya nassanto shi:

Mutane a wannan gaɓar tamu suna da abin cewa da yawa sosai, wannan ba gurin bayanin bane a shimfiɗe, sai a kan wannan matsayar zamu bi mabiya magabata na gari: Malik da al-Auza;i da al-Thauri da al-Lais bn Sa`ad, da al-Shafi`i da Ahmad bn Hambal da Ishaƙ bn Rahuwaihi, dama wasu daga cikin malaman musulmai na da da na yanzu, kuma shine: Shuɗar da su kamar yadda suka zo ba tare da kaifiyya ko kamantawa ko ɓatawa ba, abinda ke a bayyane kuma mai gaggawa a cikin tunanin masu kamantawa to shi abin korewa ne ga Allah, domin Allah wani abu baya kamanceceniya da Shi daga halittarSa haka kuma

﴿...لَيۡسَ كَمِثۡلِهِۦ شَيۡءٞۖ وَهُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡبَصِيرُ﴾

{Wani abu bai zama kamar tamkarSa ba, kuma Shĩ ne Mai ji, Mai gani}, [al-Shura:11]. Bari dai, al’amarin fa kamar yadda manyan malamai suka faɗa ne, daga cikin su akwai Nu’aim bn Hammad al-khuza’i malamin Imam al-Bukhari, ya ce: Wanda ya kamanta Allah da halittarSa to ya kafirta, wanda kuma ya yi musun abinda Allah Ya siffanta kanSa da shi to ya kafirta10, babu kamanceceniya a abinda Allah - Maɗaukakin sarki - Ya siffanta kanSa da shi ko da abinda Manzon Sa ya siffanta Shi da shi. Wanda ya tabbatar wa Allah - Maɗaukakin Sarki - abinda ayoyi fayyatattu da hadisai ingantattu sukazo da shi; a yadda suka dace da girman Allah, ya kuma kore wa Allah dukkanin tawaya; to haƙiƙa ya bi tafarkin shiriya11.

Maganar Ibn Kasir ta ƙare, - Allah Ya yi masa rahama -.

Yana shiga cikin imani da Allah shine: Ƙudircewa cewa imani magana ne da aiki, yana ƙaruwa da ɗa'a kuma yana raguwa da saɓo, kuma ba ya halatta a kafirta wani a cikin musulmai saboda wani laifi da ya yi wanda yake bai kai shirka da kafirci ba; kamar zina, da sata, da cin riba, da shan kayan maye, da saɓawa iyaye da wanin haka daga manyan laifuka, muddin dai bai halatta su ba, saboda faɗin Allah - Mai tsarki da ɗaukaka -:

﴿إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَغۡفِرُ أَن يُشۡرَكَ بِهِۦ وَيَغۡفِرُ مَا دُونَ ذَٰلِكَ لِمَن يَشَآءُ...﴾

{Lalle ne, Allah ba Ya gãfarta a yi shirki da Shi, kuma Yana gãfarta abin da yake bãyan wannan, ga wanda Yake so.} [al-Nisa'a: 48]. Kuma saboda abinda ya tabbata a hadisai mutawatirai daga Ma’aikin Allah, - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, daga cikin su akwai: faɗin sa: "Lalle Allah Yana fitar da wanda ya kasance a zuciyar sa akwai kwatankwacin ƙwayar zarra daga wuta"12.

Asali na biyu

Imani da Mala’iku

Shi kuma yana ƙunsar al'amurra guda biyu:

Hakan yana ƙunsar al'amurra guda biyu: Lamari na farko: Imani da mala’iku a dunƙule; wannan kuwa shine muyi imani da cewa Allah Yana da mala’iku, Ya halicce su domin suyi maSa ɗa'a, Ya kuma siffanta su da cewa:

﴿وَقَالُواْ ٱتَّخَذَ ٱلرَّحۡمَٰنُ وَلَدٗاۗ سُبۡحَٰنَهُۥۚ بَلۡ عِبَادٞ مُّكۡرَمُونَ 26 لَا يَسۡبِقُونَهُۥ بِٱلۡقَوۡلِ وَهُم بِأَمۡرِهِۦ يَعۡمَلُونَ27 يَعۡلَمُ مَا بَيۡنَ أَيۡدِيهِمۡ وَمَا خَلۡفَهُمۡ وَلَا يَشۡفَعُونَ إِلَّا لِمَنِ ٱرۡتَضَىٰ وَهُم مِّنۡ خَشۡيَتِهِۦ مُشۡفِقُونَ28﴾

{Kuma suka ce: "Mai rahama ya riƙi ɗã." Tsarkinsa, ya tabbata! Ã'a, (malã'iku) bãyi ne mãsu daraja,

Bã su gabãtarSa da magana, kuma su da umurninSa suke aiki,

Yanã sanin abin da yake gaba gare su da abin da yake a bãyansu, kuma bã su yin cẽto fãce ga wanda Ya yarda, kuma sũmasu sauna ne sabõda tsõronSa.} [al-Anbiya'u: 26-28].

Su kuma nau’ika ne masu yawa; daga cikin su akwai waɗanda aka wakilta da ɗaukar al-Arshi, daga cikin su kuma akwai masu tsaron aljanna da wuta, kuma daga cikinsu akwai waɗanda aka wakilta domin kiyaye ayyukan bayi. Lamari na biyu: Imani da mala’iku a fayyace, wannan, hakan shine muyi imani da waɗanda Allah da ManzonSa suka faɗa mana sunayan su, kamar Jibrilu wanda aka wakilta shi ga wahayi, da Mika’ilu da aka wakilta ga ruwan sama, da Maliku mai tsaran wuta, da Israfilu da aka wakilta da busa ƙaho. Kamar yadda anbaton su ya zo a hadisai ingantattu, daga cikin su: Akwai abinda ya tabbata a Sahih (na al-Bukhari), daga Nana Aisha - Allah Ya yarda da ita -, lalle Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «An halicci mala'iku daga haske, kuma an halicci aljannu daga bira daga wuta, kuma an halicci (Annabi) Adam daga abinda aka siffanta muku»13. Muslim ne ya fitar da shi a Sahihinsa.

Asali na uku

Imani da littattafai shima yana ƙunsar al'amura guda biyu:

Lamari na farko: Imani da littattafai a dunƙule; hakan kuwa, domin lalle Allah Ya saukar da littattafai ga annabawanSa da ManzanninSa domin bayanin haƙƙinSa, da kira zuwa gare shi, kamar yadda - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿لَقَدۡ أَرۡسَلۡنَا رُسُلَنَا بِٱلۡبَيِّنَٰتِ وَأَنزَلۡنَا مَعَهُمُ ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡمِيزَانَ لِيَقُومَ ٱلنَّاسُ بِٱلۡقِسۡطِ...﴾

{Haƙĩƙa, lalle Mun aiko Manzannin Mu da hujjõji bayyanannu, kuma Muka saukar da Littãfi da sikẽli tãre da su dõmin mutãne su tsayu da ãdalci.} [al-Hadid: 25]. Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿كَانَ ٱلنَّاسُ أُمَّةٗ وَٰحِدَةٗ فَبَعَثَ ٱللَّهُ ٱلنَّبِيِّـۧنَ مُبَشِّرِينَ وَمُنذِرِينَ وَأَنزَلَ مَعَهُمُ ٱلۡكِتَٰبَ بِٱلۡحَقِّ لِيَحۡكُمَ بَيۡنَ ٱلنَّاسِ فِيمَا ٱخۡتَلَفُواْ فِيهِ...﴾

{Mutãne sun kasance al'umma guda. Sai Allah Ya aiki annabãwa suna mãsu bãyar da bishãra kuma mãsu gargaɗi; kuma Ya saukar da Littãfi da gaskiya tãre da su dõmin (Littãfin) ya yi hukunci a tsakãnin mutãnen a cikin abin da suka sãɓã wa jũna a cikinsa.} [al-Baƙara: 213].

Lamari na biyu: Imani da littattafai a rarrabe; hakan kuwa, shine muyi imani da waɗanda Allah Ya ambata daga cikin su: Kamar Attaura da Injila da Zabura da Alƙur’ani. Kuma mu ƙudurce cewa Alƙur'ani shi ne mafificin su, kuma cikamakin su, mai rinjaye akan su, mai kuma gasgata su. Shine wanda ya zama wajibi akan dukkan al’umma su bi shi, su kuma yi hukunci da shi; tare da abinda sunnah ta inganta daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -; domin Allah - tsarki ya tabbata a gare Shi -,Ya aiko ManzonSa (Annabi) Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi Manzo zuwa gaba ɗayan mutane da aljanu. Ya kuma saukar masa da Alƙur'ani domin ya yi hukunci da shi a tsakanin su, kuma ya sanya shi waraka a abinda yake cikin zukata, kuma bayani na kowanne abu, kuma shiriya da rahama ga muminai, kamar yadda Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿وَهَٰذَا كِتَٰبٌ أَنزَلۡنَٰهُ مُبَارَكٞ فَٱتَّبِعُوهُ وَٱتَّقُواْ لَعَلَّكُمۡ تُرۡحَمُونَ155﴾

{Kuma wannan Littãfi ne, Mun saukar da shi, mai albarka ne, sai ku bĩ shi kuma ku yi taƙawa, tsammãninku, anã jin ƙanku.} [al-An'am: 155]. Kuma - tsarki ya tabbatar maSa - Ya ce:

﴿...وَنَزَّلۡنَا عَلَيۡكَ ٱلۡكِتَٰبَ تِبۡيَٰنٗا لِّكُلِّ شَيۡءٖ وَهُدٗى وَرَحۡمَةٗ وَبُشۡرَىٰ لِلۡمُسۡلِمِينَ﴾

{Kuma Mun saussaukar da Littãfi a kanka dõmin yin bãyani ga dukkan kõme da shiriya da rahama da bushãra ga mãsu mĩƙa wuya (Musulmi).} [al- Nahl 89]. Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿قُلۡ يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ إِنِّي رَسُولُ ٱللَّهِ إِلَيۡكُمۡ جَمِيعًا ٱلَّذِي لَهُۥ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۖ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ يُحۡيِۦ وَيُمِيتُۖ فَـَٔامِنُواْ بِٱللَّهِ وَرَسُولِهِ ٱلنَّبِيِّ ٱلۡأُمِّيِّ ٱلَّذِي يُؤۡمِنُ بِٱللَّهِ وَكَلِمَٰتِهِۦ وَٱتَّبِعُوهُ لَعَلَّكُمۡ تَهۡتَدُونَ158﴾

{Ka ce: "Yã kũ mutãne! Lalle ne manzon Allah ne zuwa gare ku, gabã ɗaya. (Allah) Wanda Yake Shĩ ne da mulkin sammai da ƙasa; Bãbu wani abin bautawa fãce Shi, Yanã rãyarwa, kuma Yanã matarwa, sai ku yi ĩmãni da Allah da ManzonSa, Annabi, Ummiyyi, wanda yake yin ĩmãni da Allah da kalmominSa; ku bĩ shi, tsammãninku, kunã shiryuwa."} [al-A’araf, 158]. Kuma ayoyi da suka zo da wannan ma’anar suna da yawa.

Asali na huɗu Imani da manzanni

Shima yana ƙunsar al'amurra guda biyu: Lamari na farko: Imani da Manzanni a dunƙule; hakan kuwa shine mu yi imani da cewa Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya aiko Manzanni zuwa ga bayinSa daga cikin su, masu bushara da gargaɗi, kuma masu kira zuwa ga gaskiya, duk wanda ya amsa musu to ya rabauta da dacewa, wanda kuma ya saɓa musu to ya komo da taɓewa da nadama, kuma cikamakin su kuma mafificin su shi ne Annabin mu Muhammad ɗan Abdullahi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, kamar yadda Allah - tsarki ya tabbata a gare Shi - Ya ce:

﴿وَلَقَدۡ بَعَثۡنَا فِي كُلِّ أُمَّةٖ رَّسُولًا أَنِ ٱعۡبُدُواْ ٱللَّهَ وَٱجۡتَنِبُواْ ٱلطَّٰغُوتَ...﴾

{Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun aika a cikin kõwace al'umma da wani Manzo (ya ce): "Ku bauta wa Allah, kuma ku nĩsanci ɗãgũtu."} [al-Nahl: 36]. Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿رُّسُلٗا مُّبَشِّرِينَ وَمُنذِرِينَ لِئَلَّا يَكُونَ لِلنَّاسِ عَلَى ٱللَّهِ حُجَّةُۢ بَعۡدَ ٱلرُّسُلِ...﴾

{Manzanni mãsu bãyar da bushãra kuma mãsu gargaɗi dõmin kada wata hujja ta kasance ga mutãne a kan Allah bãyan Manzannin.} [al-Nisa'a: 165]. Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿مَّا كَانَ مُحَمَّدٌ أَبَآ أَحَدٖ مِّن رِّجَالِكُمۡ وَلَٰكِن رَّسُولَ ٱللَّهِ وَخَاتَمَ ٱلنَّبِيِّـۧنَ...﴾

{Muhammadu bai kasance uban kõwa ba daga mazanku, kuma amma shĩ yã kasance Manzon Allah kuma cikon Annabãwa.} [al-Ahzab: 40].

Lamari na biyu: Imani da Manzanni a fayyace, hakan shine muyi imani da wanda Allah - Maɗaukakin Sarki Ya ambata daga cikin su a fayyace kuma a ayyane, ko ambaton sa ya tabbata daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, kamar (Annabi) Nuhu da Hud da Salihu da Ibrahim da wasun su - tsira da amincin Allah su tabbata a gare su - da alayen su da mabiyansu.

Asali na biyar: Imani da ranar lahira

Shi yana ƙunsar:

Imani da dukkanin abinda Allah Ya bada labarin sa da Manzon sa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - na abinda zai kasance bayan mutuwa kamar fitinar ƙabari da azabar sa da kuma ni’imar sa, da kuma abinda zai kasance a ranar lahira na tsorace-tsorace da tsanance-tsanance da siraɗi da awo (na ayyuka) da hisabi da sakamako da yaɗa littattafai tsakanin mutane; akwai wanda zai karɓi littafin sa da hannun sa na dama, akwai kuma wanda zai karɓa da hagu ko kuma daga bayan bayan sa.

Yana shiga cikin wannan kuma: Imani da tafki abin gangarowa ga Annabin mu Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da imani da aljanna da wuta, da ganin muminai ga Ubangijin su - Mai tsarki da ɗaukaka -, da kuma maganar da Zai yi da su, da wanin haka daga abinda yazo a cikin Alƙur'ani mai girma da Sunnah ingantacciya daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -; to ya wajaba ga bawa yayi imani da waɗannan baki ɗaya, ya kuma gasgata su a yadda Allah da Manzon sa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - suka bayyana shi.

Asali na shida: Imani da ƙaddara

Yana ƙunsar al'amurra guda huɗu:

Lamari na farko: Imani da cewa Allah - Maɗaukakin Sarki - haƙiƙa Ya san abinda ya kasance da wanda zai kasance nan gaba, kuma Ya san halayen bayinSa, da arzuƙan su da ajalillikan su da ayyukan su, da wanin haka na sha’anonin su, saboda haka babu wani abinda yake ɓoyuwa ga Allah - Maɗaukakin Sarki - na hakan, kamar yadda - tsarki ya tabbata a gare Shi - Ya ce:

﴿...وَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ بِكُلِّ شَيۡءٍ عَلِيمٞ﴾

{Kuma ku sani, Allah Masani ne ga dukkan komai.} [al-Baƙara: 231]. Kuma (Allah) - Mai girma da ɗaukaka - Ya ce

﴿...لِتَعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ وَأَنَّ ٱللَّهَ قَدۡ أَحَاطَ بِكُلِّ شَيۡءٍ عِلۡمَۢا﴾

{Dõmin ku san lalle Allah Mai ĩkon yi ne akan dukan kõmai, kuma lalle Allah, haƙĩƙa Ya kẽwaye ga dukan kõmai da sani.} [al-Ɗalak: 12].

Lamari na biyu: Imani da cewa lalle Allah Ya rubuta dukkan abinda Ya ƙaddara shi kuma Ya hukunta shi, kamar yadda Allah - Mai tsarki da ɗaukaka - Ya ce:

﴿قَدۡ عَلِمۡنَا مَا تَنقُصُ ٱلۡأَرۡضُ مِنۡهُمۡۖ وَعِندَنَا كِتَٰبٌ حَفِيظُۢ 4﴾

{Lalle ne Mun san abin da ƙasã ke ragẽwa daga gare su, kuma wurinMu akwai wani littãfi mai tsarẽwa.} [Qaf: 4]. Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿...وَكُلَّ شَيۡءٍ أَحۡصَيۡنَٰهُ فِيٓ إِمَامٖ مُّبِينٖ﴾

{Kuma kõwane abu Mun ƙididdige shi, a cikin babban Littãfi Mabayyani.} [Yaseen: 12]. Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿أَلَمۡ تَعۡلَمۡ أَنَّ ٱللَّهَ يَعۡلَمُ مَا فِي ٱلسَّمَآءِ وَٱلۡأَرۡضِۚ إِنَّ ذَٰلِكَ فِي كِتَٰبٍۚ إِنَّ ذَٰلِكَ عَلَى ٱللَّهِ يَسِيرٞ70﴾

{Ashe, ba ka sani ba, lalle ne Allah Yanã sanin abin da yake a cikin sama da ƙasa? Lalle ne hakan yanã cikin Littafi lalle wancan ga Allah mai sauƙi ne.} [al- Hajj: 70].

Lamari na uku: Imani da mashi'ar Allah abar zartarwa, abinda Ya so yake kasancewa, wanda kuwa bai so ba, to ba ya kasancewa, kamar yadda Allah - tsarki ya tabbaga a gare Shi -Ya ce:

﴿...إِنَّ ٱللَّهَ يَفۡعَلُ مَا يَشَآءُ﴾

{Lalle ne Allah Yanã aikata abin da Yake so.} [al-Hajj: 18]. Kuma (Allah) - Mai girma da ɗaukaka - Ya ce

﴿إِنَّمَآ أَمۡرُهُۥٓ إِذَآ أَرَادَ شَيۡـًٔا أَن يَقُولَ لَهُۥ كُن فَيَكُونُ82﴾

{UmurninSa idan Yã yi nufin wani abu sai Ya ce masa kawai, "Ka kasance," sai yana kasancewa (kamar yadda Yake nufi).}

. [Yaseen: 82]. Kuma - tsarki ya tabbatar maSa - Ya ce:

﴿وَمَا تَشَآءُونَ إِلَّآ أَن يَشَآءَ ٱللَّهُ رَبُّ ٱلۡعَٰلَمِينَ29﴾

{Kuma bã zã ku so ba sai idan Allah Ubangijin halitta Yã yarda.} [al-Takweer: 29].

Lamari na huɗu: Imani da halittar Allah Maɗaukakin Sarki ga dukkanin samammu; babu wani Mahalicci in ba Shi ba, kuma babu wani Ubangiji idan ba Shi ba, kamar yadda - tsarki ya tabbata a gare Shi - Ya ce:

﴿ٱللَّهُ خَٰلِقُ كُلِّ شَيۡءٖۖ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ وَكِيلٞ62﴾

{Allah ne Mahaliccin dukkan kõme, kuma Shĩ ne Wakĩli a kan kõme.} [al-Zumar: 62]. Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ ٱذۡكُرُواْ نِعۡمَتَ ٱللَّهِ عَلَيۡكُمۡۚ هَلۡ مِنۡ خَٰلِقٍ غَيۡرُ ٱللَّهِ يَرۡزُقُكُم مِّنَ ٱلسَّمَآءِ وَٱلۡأَرۡضِۚ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۖ فَأَنَّىٰ تُؤۡفَكُونَ3﴾

{Yã kũ mutãne! Ku tuna ni'imar Allah a kanku. Shin, akwai wani mai halitta wanin Allah da zai azurta ku daga sama da, ƙasã? Bãbu wani abin bautãwa, fãce Shi. To, yãya ake karkatar da ku?.} [Faɗir: 3].

To shi imani da ƙaddara yana ƙunsar waɗannan lamura ne guda huɗu baki ɗayan su, kamar yadda yake shi ne aƙidar Ahlussunnah wal Jama’a; saɓanin waɗanda suka musunta wasu daga cikin waɗannan daga ‘yan bidi’a.

Yana cikin lamura masu muhimmanci a ingantacciyar aƙidah wacce Ahlussunnah suke ƙudirce ta: So saboda Allah, da kuma ƙi saboda Allah, da jiɓinta saboda Allah, da ƙiyayya saboda Allah, wannan ita ce: Aƙidar Alwala’u wal Bara’u, kuma ita tana cikin imani da Allah - Maɗaukakin Sarki -.

Shi mumini yana son muminai yana kuma jiɓintar su, yana kuma ƙin kafirai yana adawa da su, kuma waɗanda suke a kan gaba a cikin muminai a wannan al’ummar su ne sahabban Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, kamar yadda yake a tabbace a wurin Ahlussunnah wal Jama’a; domin su (Ahlussunnah) suna son su (sahabbai) kuma suna jiɓintar su, kuma suna ƙudirce cewa sune mafi alherin mutane bayan Annabawa, saboda faɗin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: «Mafificin mutane (su ne) ‘yan zamani na, sannan waɗanda suka biyo su, sannan waɗanda suka biyo su»14. Bukhari Da Muslim sun haɗu akan ingancinsa,

Suna kuma ƙudurcewa lallai mafificin su: Abubakar al-Siddiƙ, sannan Umar al-Faruƙ, sannan Usman ma’abocin haske biyu, sannan Aliyu yardajje, - Allah Ya yarda da su baki ɗaya -, sannan bayan su sauran cikon goma, sannan sauran sahabbai - Allah Ya yarda da su baki ɗaya -, kuma suna kamewa daga abinda ya gudana na saɓani a tsakaninsu - wato sahabban -, kuma suna ƙudirce cewa su akan hakan masu ijtihadi ne, wanda ya yi daidai yana da lada biyu, wanda kuma ya kuskure yana lada ɗaya.

Suna kuma son Ahlul Baitin Ma’aikin Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -,waɗanda suka yi imani da shi, kuma suna jiɓintar su, kuma suna jiɓintar matan Ma’aikin Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - waɗanda sune uwayen muminai, kuma suna nema musu yardar Allah baki ɗayan su. Kuma suna barranta daga tsarin ‘yan Shi’a Rafidawa waɗanda suke ƙin sahabban Ma’aikin Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, suna zagin su, suna wuce iyaka akan Ahlul Baiti, suna ɗaga su sama da matsayin su wanda Allah -Mai girma da ɗaukaka -Ya yi musu, kamar yadda suke barranta daga tafarkin Nasibawa waɗanda suke cutar da Ahlul Baiti da magana ko aiki.

To wannan abin da muka ambata: Baki ɗayan sa yana shiga cikin ingantacciyar aƙidah, wacce Allah Ya aiko Manzon sa (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da ita, kuma ita ce aƙidar da ya wajaba a ƙudirce ta a yi riƙo da ita, a kuma tsayu a kanta, a kuma kiyayi abinda ya saɓa mata, ita ce kuma aƙidar tawagar da ta tsira ta Ahlussunna wal Jama’a, wacce Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya faɗa dangane da ita: «Wata tawaga ba zata gushe ba a cikin al’umma ta suna masu taimako a kan gaskiya, wanda ya taɓar da su ba zai cutar da su ba, har sai al’amarin Allah ya zo alhali su suna a kan hakan»15. A cikin wata riwayar: «Wata tawaga daga cikin al’umma ta ba zata gushe ba akan gaskiya tana abar taimakawa»16. Kuma - tsira da aminci su tabbata a gare shi - ya ce: «Yahudawa sun kasu kashi saba’in da ɗaya, Nasara kuma sun kasu kashi saba’in da biyu, kuma da sannu wannan al’ummar zata rabu kashi saba’in da uku, duka suna wuta sai kashi ɗaya, sai sahabbai suka ce: Wacce ce ita ya Ma’aikin Allah? Sai ya ce: Wanda ya kasance akan irin abinda na kasance akan sa ni da sahabbai na»17.

AƘIDUN DA SUKE KISHIYANTAR INGANTACCIYAR AƘIDA

Waɗanda suka karkacewa wannan aƙidar, masu tafiya akan saɓanin ta, su kuma kashi-kashi ne; daga cikinsu: Akwai masu bautar gumaka da Mala’iku da waliyyai da aljanu da bishiyoyi da duwatsu da wasun su. To waɗan nan ba su amsa kiran Manzanni ba, bari dai sun saɓa musu sun nuna musu taurin kai, kamar yadda Ƙuraishawa suka yi da kuma dangogin Larabawa dangane da Annabin mu Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -; sun kasance suna roƙon abubuwan bautar su, don biyan buƙatun su, da kuma warakar da marasa lafiyar su, da taimako akan maƙiya, kuma suna yi musu yanka, suna yi musu alwashi, lokacin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, ya yi musu inkarin hakan, ya umarce su da tsarkake ibada domin Allah Shi kaɗai, sai suka ga hakan wani baƙon abu, suka yi inkarin sa, suka ce:

﴿أَجَعَلَ ٱلۡأٓلِهَةَ إِلَٰهٗا وَٰحِدًاۖ إِنَّ هَٰذَا لَشَيۡءٌ عُجَابٞ5﴾

{Shin, yã sanya gumãka duka su zama abin bautawa guda? Lalle wannan, haƙĩƙa, abu ne mai ban mãmaki!} [Saad: 5].

(Annabi) - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, bai gushe ba yana kiran su izuwa ga Allah, kuma yana gargaɗar da su daga shirka, yana yi musu bayanin haƙiƙanin abinda ake kiran su zuwa gare shi; har Allah Ya shiryar da wanda Ya shiryar, sannan bayan haka suka shiga addinin Allah jama’a jama’a, sai Addinin Allah ya ɗaukaka akan sauran addinai bayan kira mai saduwa da aka dinga yi, da kuma jihadi mai tsawo tun daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da kuma sahabban sa - Allah Ya yarda da su - da masu bin su da kyautatawa. Sannan lamura suka canza, jahilci ya rinjayi mafi yawan halittu; sai da yawa suka koma addinin Jahilyyah, ta hanyar wuce iyaka ga Annabawa da waliyyai, da roƙon su da kuma neman agajin su, da wanin haka na nau’ikan shirka, basu ma san mece ce ma’anar: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah ba; kamar yadda kafiran Larabawa suka sani, ga Allah muke neman taimako.

Wannan shirkar ba ta gushe ba tana watsuwa a cikin mutane har zuwa wannan lokacin na mu; ta sanadiyyar rinjayar jahilci da kuma nesa da zamanin Annabta.

Shubuhar waɗannan ‘yan bayan ita ce shubuhar mutanan farko, ita ce faɗin su:

﴿...هَٰٓؤُلَآءِ شُفَعَٰٓؤُنَا عِندَ ٱللَّهِ...﴾

{Waɗannan ne macẽtanmu a wurin Allah}. [Yunus: 18], Da kuma faɗin su:

﴿...مَا نَعۡبُدُهُمۡ إِلَّا لِيُقَرِّبُونَآ إِلَى ٱللَّهِ زُلۡفَىٰٓ...﴾

{"Ba mu bauta musu ba fãce dõmin su kusantar da mu zuwa ga Allah, kusantar daraja."} [al-Zumar: 3] Kuma haƙiƙa Allah Ya ɓata wannan shubuhar, Ya yi bayanin duk wanda aka bautawa ko waye, to haƙiƙa yayi wa Allah shirka da shi, kuma ya kafirta, kamar yadda Allah - Maɗaukakin Sarki -Ya ce:

﴿وَيَعۡبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ مَا لَا يَضُرُّهُمۡ وَلَا يَنفَعُهُمۡ وَيَقُولُونَ هَٰٓؤُلَآءِ شُفَعَٰٓؤُنَا عِندَ ٱللَّهِ...﴾

{Kuma sunã bautã wa, baicin Allah, abin da bã ya cũtar dasu kuma bã ya amfãninsu, kuma sunã cẽwa: "Waɗannan ne macẽtanmu a wurin Allah".} [Yunus: 18]. Sai (Allah) - tsarki ya tabbata a gare Shi - Ya mayar musu da martani da faɗin Sa:

﴿قُلۡ أَتُنَبِّـُٔونَ ٱللَّهَ بِمَا لَا يَعۡلَمُ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَلَا فِي ٱلۡأَرۡضِۚ سُبۡحَٰنَهُۥ وَتَعَٰلَىٰ عَمَّا يُشۡرِكُونَ18﴾

{Ka ce: "Shin, kunã bai wa Allah lãbãri ne, ga abin da bai sani ba, a cikin sammai ko a cikin ƙasa? TsarkinSa ya tabbata kuma ɗaukaka daga gabin da duk suke yin shirki da Shi."} [Yunus: 18].

Sai Allah a cikin wannan ayar Ya bayyana cewa: Lalle bautawa wanin Sa daga Annabawa da waliyyai da wasun su, shi ne babbar shirka, ko da masu yin ta sun kirata da wanin hakan, Allah

- Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿...وَٱلَّذِينَ ٱتَّخَذُواْ مِن دُونِهِۦٓ أَوۡلِيَآءَ مَا نَعۡبُدُهُمۡ إِلَّا لِيُقَرِّبُونَآ إِلَى ٱللَّهِ زُلۡفَىٰٓ...﴾

{Kuma waɗanda suka riƙi waɗansu majiɓinta waɗanda bã Shĩ ba Allah ne Mai tsaro a kansu, kuma kai, bã wakili ne a kansu ba.} [al-Zumar: 3]. Sannan (Allah) - Maɗaukakin Sarki - Ya yi musu raddi da faɗin Sa:

﴿...إِنَّ ٱللَّهَ يَحۡكُمُ بَيۡنَهُمۡ فِي مَا هُمۡ فِيهِ يَخۡتَلِفُونَۗ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَهۡدِي مَنۡ هُوَ كَٰذِبٞ كَفَّارٞ﴾

{Lalle Allah nã yin hukunci a tsakãninsu ga abin da suka zama sunã sãɓãwa a cikinsa. Lalle Allah ba Ya shiryar da wanda yake mai ƙarya, mai kãfirci} [al-Zumar: 3].

Sai Allah - tsarki ya tabbatar a gare Shi -,Ya yi bayani akan bautar su ga wani wanda ba Shi ba ta hanyar addu’a, da tsoro da kwaɗayi, da makamantan haka; kafircewa Allah ne - tsarki ya tabbata a gare Shi -, kuma (Allah) Ya ƙaryata su akan maganar su: Lalle uwayengijin su suna kusantar da su izuwa gare Shi kusasntarwa.

Akwai daga cikin aƙidu na kafirci waɗanda suke kishiyantar ingantacciyar aƙidah, kuma masu saɓawa da abinda Manzanni

- tsira da amincin Allah su tabbata agare su - suka zo da shi: abinda mulhidai suke ƙudircewa a wannan zamanin cikin mabiya Marx da Lenin da wasun su, cikin masu kira zuwa ga ilhadi da kafirci, daidai ne an kira hakan da sunan Ishtirakiyya ne ko Shuyu'iyyah ko Ba’athiyyah ko ma wanin haka na sunaye, domin yana cikin tushan waɗannan mulhidan cewa: Babu Allah, kuma rayuwa Maddah ce kawai (maƙunshin wanzuwa),

Yana daga cikin Usul ɗin su kuma: Musun tashi bayan mutuwa, da musun akwai aljanna da wuta, da kafircewa addinai baki ɗayan su, wanda ya yi nazarin littattafan su ya kuma karanta abinda suke akan sa, zai sani, sani na yaƙini, kuma babu shakka wannan aƙidar (ta su) tana kishiyantar dukkanin addinai da suka zo daga sama, kuma za ta kai masu ita zuwa ga mafi munin makoma a duniya da lahira.

Daga cikin waɗannan aƙidu masu kishiyantar gaskiya: Abinda wasu daga sufaye suke ƙudurcewa cewa wasu daga cikin waɗanda suke cewa waliyyai suna tarayya da Allah a jujjuya lamurra, kuma suna tasarrufi a sha’anin talikai, ana kiran su Khuɗubai da Autadu da Agwasu, da wanin haka na sunayan da suka ƙage su ga abubuwan bautar su, wannan kuwa shirka ce a Rububiyyah, kuma tana cikin mafi munin nau’ikan shirka ga Allah - Maɗaukakin Sarki -.

Wanda ya yi la’akari a shirkar mutanen farko na Jahilyyah, ya kuma kwatanta ta da shirkar da take yaɗuwa tsakanin ‘yan baya; zai samu lalle shirkar ‘yan baya ita ce mafi girman shirka kuma mafi muni, bayanin haka kuwa shi ne kamar haka: Lalle kafiran larabawa a zamanin Jahilyyah sun banbanta da abubuwa biyu: Lamari na farko: Su ba su kasance suna shirka da Allah ba a Rububiyyah (ayyukan Allah), kaɗai suna shirkar su a ibada ne, sun kasance sun yi i'itirafin Rububiyyah (ayyukan Allah) ga Allah - Mai girma da ɗaukaka - Shi kaɗai, kamar yadda Allah - Mai tsarki da ɗaukaka - Ya ce:

﴿وَلَئِن سَأَلۡتَهُم مَّنۡ خَلَقَهُمۡ لَيَقُولُنَّ ٱللَّهُ...﴾

{Kuma lalle idan ka tambaye su: "Wãne ne ya halitta su?" Lalle ne zã su ce Allah ne.} [al-Zukhruf: 87]. Kuma - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿قُلۡ مَن يَرۡزُقُكُم مِّنَ ٱلسَّمَآءِ وَٱلۡأَرۡضِ أَمَّن يَمۡلِكُ ٱلسَّمۡعَ وَٱلۡأَبۡصَٰرَ وَمَن يُخۡرِجُ ٱلۡحَيَّ مِنَ ٱلۡمَيِّتِ وَيُخۡرِجُ ٱلۡمَيِّتَ مِنَ ٱلۡحَيِّ وَمَن يُدَبِّرُ ٱلۡأَمۡرَۚ فَسَيَقُولُونَ ٱللَّهُۚ فَقُلۡ أَفَلَا تَتَّقُونَ31﴾

{Ka ce: "Wãne ne Yake azurtã ku daga sama da ƙasa? Shin kõ kuma Wãne ne Yake mallakar jĩ da ganĩ, kuma Wãne ne Yake fitar da mai rai daga mamaci, kuma Ya fitar da mamaci daga mai rai, Kuma Wãne ne Yake shirya al'amari?" To, zã su ce: "Allah ne." To, ka ce: "Shin fa, bã zã ku yi taƙawa ba?".} [Yunus: 31]. Ayoyi da suka zo a wannan ma’anar suna da yawa sosai.

Lamari na biyu: Cewa shirkar su a ibadah ba ta kasance dawwamammiya ba, kawai tana kasancewa ne a lokacin yalwa, amma a lokacin tsanani to su sun kasance suna tsarkake ibada ga Allah, kamar yadda Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿فَإِذَا رَكِبُواْ فِي ٱلۡفُلۡكِ دَعَوُاْ ٱللَّهَ مُخۡلِصِينَ لَهُ ٱلدِّينَ فَلَمَّا نَجَّىٰهُمۡ إِلَى ٱلۡبَرِّ إِذَا هُمۡ يُشۡرِكُونَ65﴾

{To, a lõkacin da suka shiga cikin jirgin ruwa, sun kirãyi Allah sunã mãsu tsarkake addini a gare shi, to, a lõkacin da Ya tsĩrar da su zuwa ga tudun ƙasã, sai gã su sunã shirki.} [al-Ankabut: 65].

Amma mushirikai ‘yan baya, to su sun ƙara akan mutanan farko ta fuskoki biyu: Fuska ta farko: Yadda wasun su suke shirka a cikin Rububiyyah. Fuska ta biyu: Shirkar su a lokacin yalwa da tsanani, kamar yadda wanda ya cuɗanya da su kuma ya karanci halayen su zai san hakan, ya ga kuma irin abinda suke aikatawa a ƙabarin al-Husaini da al-Badawi da wasun su a Masar, da ƙabarin al-Aidurus a Adan, da al-Hadi a Yaman da Ibn Arabi a Sham da Sheikh Abdulƙadir al-Jilani a Iraƙ da sauran su na ƙaburbura shahararru waɗanda jama’a suka wuce iyaka akansu, suka juyar da da yawa daga haƙƙin Allah - Maɗaukakin Sarki - zuwa can. Da ƙyar ka sami mai yi musu inkari akan hakan, ya yi musu bayanin haƙiƙanin Tauhidin da Allah Ya aiko AnnabinSa Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, da Manzanni da suka zo kafin shi - tsira da aminci su tabbata gare su -, to fa lalle mu ga Allah muke kuma gare Shi zamu koma.

Akwai daga cikin aƙidun da suke kishiyantar ingantacciyar aƙidah a babin sunayen Allah da siffofinSa: Akidun ‘yan bidi’a, irin su Jahamiyyah da Mu’utazilah da duk wanda ya bi hanyar su a kore siffofin Allah - Mai girma da ɗaukaka -, da soke abinda aka ambata ga Allah - tsarki ya tabbata a gare Shi - na siffofin cika, da kuma siffanta shi (Allah) da siffofin abubuwan da babu su da daskararrun abubuwa da ma abubuwan da ba za su yiwu ba. Allah Ya ɗaukaka daga maganar su, ɗaukaka mai girma.

Yana kuma shiga ƙarƙashin wannan: Wanda ya kore sashen siffofin da kuma tabbatar da wasu sashen; kamar yadda wannan ita ce aƙidar Asha’irah, kuma waɗannan abinda suka tabbatar da shi zai lazimce su, na siffofi irin wanda suka gujewa akan siffofin da suka kore, suka yi tawilin dalilan su, sai suka saɓa da waɗannan dalilan na ruwaya da hankali, suka yi tufka da warwara bayyananne a cikin hakan.

Amma su Ahlussunnah wal Jama’a, to haƙiƙa sun tabbatarwa Allah - Maɗaukakin Sarki - abinda Ya tabbatar wa kanSa ko ManzonSa (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya tabbatar maSa na sunaye da siffofi, ta fuskar cika, kuma suka tsarkake shi daga barin kamanceceniya da halittarSa, tsarkakewa da ta barranta daga birbishin sokewa, sai suka yi aiki da dalilan baki ɗaya, ba su jirkita ba, kuma ba su soke ba, sun kuɓuta daga tufka da warwara wanda wasun su suka afka cikin sa, - kamar yadda bayani akan hakan ya gabata -.

Wannan kuwa ita ce hanyar tsira, da kuma rabauta a duniya lahira, kuma shi ne tafarki miƙaƙƙe wanda magabata na ƙwarai na wannan al'umma suka bi shi, kuma babu abinda zai gyara ƙarshen wannan al’ummar sai abinda ya gyara na farkon ta, wanda yake shine bin littafin Allah da sunnar ManzonSa da kuma barin abinda ya saɓa musu. Muna roƙon Allah - Maɗaukakin Sarki -, Ya mayar da wannan al’ummar kan shiriyar ta, Ya kuma yawaita masu kira zuwa shiriya a cikin ta, Ya datar da shugabannin ta da malaman ta akan yaƙar shirka da yin hukunci akan ta, da kuma tsawatarwa daga (bin) hanyoyin ta… lalle Shi Mai ji ne kuma Makusanci. Allah shi ne Majiɓincin datarwa, kuma Ya isar mana, kuma madalla da wakili, kuma babu dabara babu ƙarfi face da (taimakon) Sa. Allah Ya yi daɗi tsira ga bawanSa kuma ManzonSa, Annabin mu Muhammad da alayen sa da sahabban sa.

 

 

***

 


بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ

SAƘO NA BIYU

Akan hukuncin neman agaji da Annabi

-tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -.

Godiya ta tabbata ga Allah, tsira da amincin Allah su tabbata ga Manzon Allah, da alayen sa da sahabban sa da waɗanda suka shiryu da shiriyar sa.

Bayan haka: haƙiƙa jaridar zamantakewa ta ƙasar Kuwait a fitowa ta 15, ranar 19/4/1390 bayan hijira, ta buga wani bayani a ƙarƙashin matashiyar: (Tunawa da mauludin Annanbi mai daraja), to waɗannan baitukan sun kasance suna ƙunshe da neman agajin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da neman taimakon sa; domin ya kawowa wannan al’umma ɗauki, ya taimaketa ya tsamar da ita daga inda ta afka na rarrabuwa da saɓani. Wacce ta rattaba hannu ita ce: (Amina), ga nassin baitocin da aka yi maganar a cikin su:

Ya Manzon Allah, ka ceci wani malami... yana rura wutar yaƙi kuma yana ƙonewa daga wutarta

Ya Manzon Allah, ka ceci wata al'umma... cikin duhun shakka, da sirrin ta ya tsawaita.

Ya Manzon Allah, ka ceci wata al'umma... a cikin ruɗanin baƙin da hangen nesanta ya ɓace

Har zuwa inda tace:

Ka gaggauta taimako, kamar yadda Ka gaggauta shi... a ranar Badar lokacin da ka kira Allah.

Sabõda haka, ƙasƙanci ya koma taimako mai ban mamaki... Lalle ne Allah Yana da rundunõni waɗanda ba ka ganinsu.

(Haka mai wannan rubutun take fuskantar da kiran ta da neman agajin ta zuwa ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, tana neman ya kawowa wannan al’umma ɗauki ta hanyar gaggauto da nasara -.Ta manta - ko ta jahilci - cewa nasara tana hannun Allah ne Shi kaɗai, ba tana hannun Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ba ne, ko wanin sa a cikin halittu, kamar yanda Allah - tsarki ya tabbata a gare Shi - Ya ce a littafin Sa mabayyani:

﴿...وَمَا النَّصْرُ إِلَّا مِنْ عِنْدِ اللَّهِ الْعَزِيزِ الْحَكِيمِ﴾

{Taimako bai kasance ba fãce daga wurin Allah, Mabuwãyi, Mai hikima} [Aali- Imran: 126], Kuma Allah - Maɗaukaki - Ya ce:

﴿إِنْ يَنْصُرْكُمُ اللَّهُ فَلَا غَالِبَ لَكُمْ وَإِنْ يَخْذُلْكُمْ فَمَنْ ذَا الَّذِي يَنْصُرُكُمْ مِنْ بَعْدِهِ...﴾

{Idan Allah Ya taimake ku, to, bãbu marinjayi a gare ku. Kuma idan Ya yarɓe ku, to, wãnẽ ne wanda yake taimakon ku a bāyanSa} [Aali- Imran: 160].

Wannan aiki na roƙo da neman agaji, shi ne: juyar da nau’i daga cikin nau’ikan ibada ga wanin Allah - Maɗaukakin Sarki -; Haƙiƙa an sani da Nassi da kuma Ijima’i: Lalle hakan bai halatta ba, kuma Allah - tsarki ya tabbata a gare Shi - Ya halicci halitta ne domin su bauta maSa, kuma Ya aiko da Manzanni, Ya kuma saukar da littattafai domin bayanin wannan ibadar da kuma kira zuwa gare ta, kamar yadda (Allah) - tsarki ya tabbata a gare shi - Ya ce:

﴿وَمَا خَلَقْتُ الْجِنَّ وَالْإِنْسَ إِلَّا لِيَعْبُدُونِ56﴾

{Kuma Ban halitta aljannu da mutãne ba sai dõmin su bauta Mini} [al-Zariyat: 56], Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿وَلَقَدْ بَعَثْنَا فِي كُلِّ أُمَّةٍ رَسُولًا أَنِ اُعْبُدُوا اللَّهَ وَاجْتَنِبُوا الطَّاغُوتَ...﴾

{Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun aika a cikin kõwace al'umma da wani Manzo (ya ce): "Ku bauta wa Allah, kuma ku nĩsanci ɗãgũtu} [al-Nahl: 36], Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿وَمَا أَرْسَلْنَا مِنْ قَبْلِكَ مِنْ رَسُولٍ إِلَّا نُوحِي إِلَيْهِ أَنَّهُ لَا إِلَهَ إِلَّا أَنَا فَاعْبُدُونِ25﴾

{Kuma ba Mu aiki wani Manzo ba a gabãninka fãce Munã yin wahayi zuwa gare shi, cẽwa "Lalle ne Shi, bãbu abin bautãwa fãce Nĩ, sai ku bauta Mini} [al-Anbiya'a: 25], Kuma Allah - Maɗaukaki - Ya ce:

﴿الر كِتَابٌ أُحْكِمَتْ آيَاتُهُ ثُمَّ فُصِّلَتْ مِنْ لَدُنْ حَكِيمٍ خَبِيرٍ1 أَلَّا تَعْبُدُوا إِلَّا اللَّهَ إِنَّنِي لَكُمْ مِنْهُ نَذِيرٌ وَبَشِيرٌ2﴾

{A. L̃.R. Littãfi ne an kyautata ãyõyinsa, sa'an nan an bayyanã su daki-daki, daga wurin Mai hikima, Mai ƙididdigewa}

{Kada ku bautã wa kõwa fãce Allah. Lalle ne ni a gare ku mai gargaɗi ne kuma mai bushãrã daga gare Shi} [Hud: 1, 2].

Sai (Allah) - Maɗaukakin Sarki - Ya yi bayani a waɗannan ayoyin bayyanannu cewa, bai halicci mutum da aljan ba sai domin su bauta maSa Shi kaɗai, ba Shi da abokin tarayya, kuma Ya bayyana cewa Ya aiko manzanni ne - tsira da aminci ya tabbata a gare su - domin umarni da wannan ibadar, da kuma hani daga kishiyar ta, kuma Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya bada labarin cewa Ya kyautata ayoyin littafinSa, kuma Ya rabe su daki-daki domin kada a bautawa wani wanda ba Shi ba - tsarki ya tabbata a gare Shi -.

Sananne ne ibada tana nufin: Kaɗaita Allah da kuma Yi maSa ɗa'a, ta yin ruƙo da umarninSa da kuma barin abubuwan da Ya hana, kuma haƙiƙa Allah Ya yi umarni Ya kuma bada labari da hakan a ayoyi masu yawa, daga cikin su: FaɗinSa - tsarki ya tabbata a gare Shi -:

﴿وَمَا أُمِرُوا إِلَّا لِيَعْبُدُوا اللَّهَ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ حُنَفَاءَ...﴾

{Kuma ba a umarce su da kome ba fãce bauta wa Allah suna mãsu tsarkake addinin gare Shi, mãsu karkata zuwa ga addinin gaskiya} [al-Bayyinah: 5], Da faɗinSa - Mai girma da ɗaukaka -:

﴿وَقَضَى رَبُّكَ أَلَّا تَعْبُدُوا إِلَّا إِيَّاهُ...﴾

{Kuma Ubangijinka Ya hukunta kada ku bauta wa kõwa fãce Shi} [al-Isra'a: 23], Da faɗinSa - tsarki ya tabbatar maSa -:

﴿إِنَّآ أَنزَلۡنَآ إِلَيۡكَ ٱلۡكِتَٰبَ بِٱلۡحَقِّ فَٱعۡبُدِ ٱللَّهَ مُخۡلِصٗا لَّهُ ٱلدِّينَ2 أَلَا لِلَّهِ ٱلدِّينُ ٱلۡخَالِصُۚ وَٱلَّذِينَ ٱتَّخَذُواْ مِن دُونِهِۦٓ أَوۡلِيَآءَ مَا نَعۡبُدُهُمۡ إِلَّا لِيُقَرِّبُونَآ إِلَى ٱللَّهِ زُلۡفَىٰٓ إِنَّ ٱللَّهَ يَحۡكُمُ بَيۡنَهُمۡ فِي مَا هُمۡ فِيهِ يَخۡتَلِفُونَۗ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَهۡدِي مَنۡ هُوَ كَٰذِبٞ كَفَّارٞ3﴾

{Mun saukar da littafi a gareka da Gaskiya ka bautawa Allah kana mai tsarkake Addini a gare shi}

{To, addini tsarkakakke na Allah ne, kuma waɗanda suka riƙi waɗansu majibinta, bã Shi ba, (sunã cẽwa) "Ba mu bauta musu ba fãce dõmin su kusantar da mu zuwa ga Allah, kusantar daraja." Lalle Allah nã yin hukunci a tsakãninsu ga abin da suka zama sunã sãɓãwa a cikinsa. Lalle Allah ba Ya shiryar da wanda yake mai ƙarya, mai kãfirci} [al-Zumar: 2-3].

Ayoyi a wannan ma’anar suna da yawa, kuma dukkan su suna nuni akan wajabcin tsarkake ibada domin Allah Shi kaɗai, da barin bautawa wanda ba Shi ba cikin Annabawa da wasun su.

Babu shakka, ita addu’a tana daga muhimman nau’ikan ibada kuma mafi tattarar su, sai ya wajaba a tsarkake ta domin Allah Shi kaɗai, kamar yadda Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya ce:

﴿فَادْعُوا اللَّهَ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ وَلَوْ كَرِهَ الْكَافِرُونَ14﴾

{Sabõda haka ku kirãyi Allah, kunã mãsu tsarkake addini a gare Shi, kuma kõ dã kãfirai sun ƙi} [Ghafir: 14], Kuma (Allah) - Mai girma da ɗaukaka - Ya ce-:

﴿وَأَنَّ الْمَسَاجِدَ لِلَّهِ فَلَا تَدْعُوا مَعَ اللَّهِ أَحَدًا18﴾

{Kuma lalle ne wurãren sujada na Allah ne, saboda haka kada ku kira kõwa tãre da Allah (da su, a cikinsu)} [al-Jinn: 18], Wannan fuskantarwar, ta kaɗaita Allah da addu’a tana game dukkanin halitta daga Annabawa da wasunsu, fadinSa (Allah):

﴿وَلَا تَدْعُ مِنْ دُونِ اللَّهِ مَا لَا يَنْفَعُكَ وَلَا يَضُرُّكَ فَإِن فَعَلۡتَ فَإِنَّكَ إِذٗا مِّنَ ٱلظَّٰلِمِينَ106﴾

{Kuma kada ka kirãyi, baicin Allah, abin da bã ya amfãnin ka kuma bã ya cũtar ka. To, idan ka aikata haka, sa'an nan lalle kai, a lõkacin, kanã daga mãsu zãlunci.} [Yunus: 106], Wannan magana ce ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, kuma sanannen abu ne cewa Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya tsare shi daga shirka, kawai dai abin nufi da wannan shine tsoratar da waninsa. Sannan Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿وَلَا تَدۡعُ مِن دُونِ ٱللَّهِ مَا لَا يَنفَعُكَ وَلَا يَضُرُّكَ فَإِنْ فَعَلْتَ فَإِنَّكَ إِذًا مِنَ الظَّالِمِينَ106﴾

{"Kuma kada ka kirãyi, baicin Allah, abin da bã ya amfãnin ka kuma bã ya cũtar ka. To, idan ka aikata haka, sa'an nan lalle kai, a lõkacin, kanã daga mãsu zãlunci."} [Yunus: 106], Kuma wannan kira ne ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, kuma abin nufi shi ne: Tsawatar da waninsa; domin sanannen abu ne, Allah - Maɗaukakin Sarki - haƙiƙa ya tsare Manzon sa daga shirka, sannan kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya kausasa hanin da tsawatarwar, sai Ya ce:

﴿...فَإِنْ فَعَلْتَ فَإِنَّكَ إِذًا مِنَ الظَّالِمِينَ﴾

{To idan ka aikata, to lalle kai a lokacin kana cikin azzalumai} Shi zalunci idan aka faɗe shi a sake, to ana nufin: Babbar shirka, kamar yadda (Allah) - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿...وَالْكَافِرُونَ هُمُ الظَّالِمُونَ﴾

{Kuma kãfirai sũ ne azzãlumai} [al-Baƙara: 254] Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿...إِنَّ الشِّرْكَ لَظُلْمٌ عَظِيمٌ﴾

{Lalle shirki wani zãlunci ne mai girma} [Luƙman: 13]. Har idan shugaban ‘yan Adam - tsira da aminci su tabbata a gare shi -, da zai kira wanin Allah zai kasance cikin azzalumai, to ina ga wanda ba shi ba?!.

Sai aka sani da waɗannan ayoyin da wasunsu, lalle kiran wanin Allah - daga matattu da bishiyoyi da gumaka da wasunsu -, shirka ne da Allah - Maɗaukakin Sarki -, kuma yana kore kaɗaita Allah a ibada wacce take ita ce manufar halittar mutum da aljan, da kuma aiko Manzanni da saukar da littattafai, kuma mai cin karo ce ga ma’anar: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, wacce take kore bautawa wanin Allah, take kuma tabbatar da ita ga Allah Shi kaɗai, kamar yadda Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿ذَٰلِكَ بِأَنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلۡحَقُّ وَأَنَّ مَا يَدۡعُونَ مِن دُونِهِۦ هُوَ ٱلۡبَٰطِلُ وَأَنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلۡعَلِيُّ ٱلۡكَبِيرُ62﴾

{Wancan! sabõda lalle ne Allah, shĩ ne Gaskiya, kuma lalle ne, abin da suke kira waninSa shi ne ƙarya. Kuma lalle ne Allah, Shĩ ne Maɗaukaki, Mai girma} [al-Hajj: 62].

Wannan shi ne asalin Addini kuma tushen al'umma, kuma ibadu ba zasu inganta ba sai bayan ingancin wannan asali, kamar yadda

- Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿وَلَقَدْ أُوحِيَ إِلَيْكَ وَإِلَى الَّذِينَ مِنْ قَبْلِكَ لَئِنْ أَشْرَكْتَ لَيَحْبَطَنَّ عَمَلُكَ وَلَتَكُونَنَّ مِنَ الْخَاسِرِينَ65﴾

{Kuma an yi wahayi zuwa gare ka da kuma zuwa ga waɗanda suke a gabãninka, "Lalle idan ka yi shirki haƙĩƙa aikinka zai ɓãci, kuma lalle zã ka kasance daga mãsu hasãra} [al-Zumar: 65], (Allah) - Mai tsarki da ɗaukaka - Ya ce:

﴿...وَلَوْ أَشْرَكُوا لَحَبِطَ عَنْهُمْ مَا كَانُوا يَعْمَلُونَ﴾

{Kuma dã sun yi shirki dã haƙĩƙa abin da suka kasance sunã, aikatãwa yã lãlãce} [al-An'am: 88].

Daga cikin abinda ya gabata, yana bayyana cewa Addinin Musulinci da shaidawa (Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah), suna da tushe guda biyu masu girma:

Na farkon su: Kada abautawa kowa sai Allah Shi kaɗai, ba Shi da abokin tarayya; wanda ya kira matattu daga cikin Annabawa da wasunsu, ko ya kira gumaka ko bishiyoyi ko duwatsu ko wasunsu cikin halittu, ko ya nemi agajin su ko ya nemi kusanci zuwa gare su ta hanyar yanka ko bakance, ko ya yi musu sallah ko ya yi musu sujjada; to haƙiƙa ya ɗauke su abubuwan bauta koma bayan Allah, ya kuma sanya su kishiyoyi gare Shi - Mai tsarki da ɗaukaka -, ya kuma warware da kore ma’anar: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah.

Na biyu: Kada a bautawa Allah saida shari’ar AnnabinSa kuma ManzonSa, - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, duk wanda ya ƙirƙiro wata bidi’a a addini wacce Allah Bai yi izini da ita ba; to bai tabbatar da ma’anar shaidawa cewa (Annabi) Muhammad Manzon Allah ne ba, kuma aikin sa ba zai anfane shi ba, kuma ba za’a karɓi aikin daga wurin sa ba, Allah - girman Sa ya ɗaukaka - Ya ce:

﴿وَقَدِمْنَا إِلَى مَا عَمِلُوا مِنْ عَمَلٍ فَجَعَلْنَاهُ هَبَاءً مَنْثُورًا23﴾

{Kuma Muka gabãta zuwa ga abin da suka aikata daga aiki, sai Muka sanya shi ƙũra wãtsattsiya} [al-Furƙan: 23], Abin nufi da waɗannan ayyukan da aka ambata a ayar: Ayyukan wanda ya mutu yana shirka da Allah - Mai girma da ɗaukaka -.

Yana shiga ciki kuma: Ayyukan da aka ƙirƙira, waɗanda Allah Bai bada izini ba, domin za su kasance ranar lahira tamkar ƙura watsattsiya, saboda kasantuwar su ba su yi daidai da Shari’a tsarkakkiya ba, kamar yadda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Duk wanda ya farar da wani sabon abu a cikin wannan addinin namu wanda ba ya ciki, to shi abun mayarwa ne». Bukhari da Muslim sun haɗu akan ingancinsa.

A taƙaice dai: Wannan mai rubutun ta nemi ta fuskantar da neman agajin ta ne da roƙon ta ga Ma’aikin - Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, ta kau da kai daga Allah Ubangijin talikai, wanda a hannunSa taimako da cuta da amfani yake, babu wani abu daga wannan da yake a hannun wani wanda ba shi ba.

Babu shakka lalle wannan zalunci ne mai girma kuma mai muni, haƙiƙa Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya yi umarni da a roƙe Shi, kuma ya yiwa wanda ya roƙe Shi alƙawarin amsawa, Ya kuma yi alƙawarin narkon azaba ga wanda ya yi girman kai daga barin hakan (roƙon Shi) da shiga Jahannama, kamar yadda Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya ce:

﴿وَقَالَ رَبُّكُمُ ادْعُونِي أَسْتَجِبْ لَكُمْ إِنَّ الَّذِينَ يَسْتَكْبِرُونَ عَنْ عِبَادَتِي سَيَدْخُلُونَ جَهَنَّمَ دَاخِرِينَ 60

{Kuma Ubangijinku ya ce: "Ku kira Ni in karɓa muku. Lalle waɗannan da ke kangara daga barin bauta Mini, za su shiga Jahannama sunã ƙasƙantattu} [Gafir: 60], Wato: ƙasƙantattu wulaƙantattu, Sai waɗannan ayoyin masu karamci suka yi nuni akan lalle addu’a ibada ce, kuma duk wanda ya yi girman kai daga gare ta, to makomar sa Jahannama ce, idan wannan shi ne halin wanda ya yi girman kai daga roƙon Allah, to ya halin wanda ya roƙi waninSa, ya bijire maSa (Allah), alhali Shi - tsarki ya tabbata a gare Shi - Makusanci ne, Mamallakin kowanne abu, Mai iko ne akan komai, kamar yadda Allah - tsarki ya tabbata a gare Shi - Ya ce:

﴿وَإِذَا سَأَلَكَ عِبَادِي عَنِّي فَإِنِّي قَرِيبٌ أُجِيبُ دَعْوَةَ الدَّاعِ إِذَا دَعَانِ فَلْيَسْتَجِيبُوا لِي وَلْيُؤْمِنُوا بِي لَعَلَّهُمْ يَرْشُدُونَ 186﴾

{Kuma idan bãyiNa suka tambaye ka daga gare Ni, to, lalle Ni Makusanci ne. Ina karɓa kiran mai kira idan ya kirã Ni. Sabõda haka su nẽmi karɓawaTa, kuma su yi ĩmãni da Ni: tsammãninsu, su shiryu} [al-Baƙara: 186], Kuma Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ba da labari a cikin hadisi sahihi cewa addu'a ita ce ibada, kuma ya ce wa ɗan kawunsa Abdullahi bin Abbas - yardar Allah ta tabbata a gare su: «Ka kiyaye Allah sai Allah Ya kiyaye ka, ka kiyaye Allah sai ka same Shi duk halin da kasamu kanka, kuma idan zakayi roƙo, to, ka roƙi Allah, kuma idan zaka nemi taimako to ka nemi taimakon Allah». Tirmizi da wanin sa ne suka fitar da shi.

Kuma - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Duk wanda ya mutu yana kiran wani kini ga Allah, to zai shiga wuta». Bukhari ne ya rawaito shi, A cikin Sahih Bukhari da Muslim, an rawaito daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - cewa an tambaye shi: Wanne zunubi ne ya fi girma? Ya ce: «Ka sanyawa Allah kini alhali kuwa shi ne ya halliceka?». Al-Niddu: Shine makamanci da mamisalci, don haka duk wanda ya kira wanin Allah, ko ya nemi taimako daga gare shi ko yayi bakance saboda shi, ko yayi masa yanka, ko ya juya wata ibada zuwa gare shi banda abin da ya gabata; to ya ɗauke shi a matsayin abokin tarayya, daidai ne ya kasance Annabi ne, ko waliyi, ko mala'ika, ko aljani, ko gunki, ko wanin haka daga cikin halittu.

A nan kuma takan yi wu mai tambaya ya ce: To menene hukuncin roƙon wanda yake a raye mahalarci akan abinda yake da iko akai, da kuma neman taimakon sa a kan abubuwan da ake gani ko ake taɓawa waɗanda yake da iko akan su; Amsa a nan: Wannan ba shi daga cikin shirka, kawai yana cikin lamurra na al’ada da suke halas ne tsakanin musulmai, kamar yadda Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya faɗa a ƙissar Annabi Musa:

﴿...فَاسْتَغَاثَهُ الَّذِي مِنْ شِيعَتِهِ عَلَى الَّذِي مِنْ عَدُوِّهِ...﴾

{Sai wannan da yake daga ƙungiyarsa ya nẽmi ãgajinsa akan wanda yake daga maƙiyansa} [al-Ƙasas: 15], Kuma kamar yadda - Maɗaukakin Sarki - Ya ce a cikin labarin Musa ma:

﴿فَخَرَجَ مِنْهَا خَائِفًا يَتَرَقَّبُ...﴾

{Sai ya fita daga gare ta,* yanã mai jin tsõro yanã sauna} [al-Ƙasas: 21], Kuma kamar yadda mutum yake neman agajin abokan sa a yaƙi, da wanin hakan na lamuran da suke bujurowa mutane, ya zama sashen su yana buƙatar sashe.

Kuma haƙiƙa Allah Ya umarci AnnabinSa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da ya baiwa al’ummar sa labarin shi fa ba ya mallakar amfani ko cuta ga kowa, sai (Allah) - Mai tsarki da ɗaukaka - Ya ce:

﴿قُلْ إِنَّمَا أَدْعُو رَبِّي وَلَا أُشْرِكُ بِهِ أَحَدًا21 قُلْ إِنِّي لَا أَمْلِكُ لَكُمْ ضَرًّا وَلَا رَشَدًا22﴾

{Ka ce: "lna kiran Ubangijina ne kawai, kuma bã zan tãra kowa da Shi ba. Ka ce: "Lalle ne, nĩ bã ni mallakar wata cũta gare ku, kuma bã ni mallakar wani alhẽri."}

Ka ce: "Lalle ne, nĩ bã ni mallakar wata cũta gare ku, kuma bã ni mallakar wani alhẽri. [al-Jinn: 21,22], Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿قُلْ لَا أَمْلِكُ لِنَفْسِي نَفْعًا وَلَا ضَرًّا إِلَّا مَا شَاءَ اللَّهُ وَلَوْ كُنْتُ أَعْلَمُ الْغَيْبَ لَاسْتَكْثَرْتُ مِنَ الْخَيْرِ وَمَا مَسَّنِيَ السُّوءُ إِنْ أَنَا إِلَّا نَذِيرٌ وَبَشِيرٌ لِقَوْمٍ يُؤْمِنُونَ188﴾

{Ka ce: "Bã ni mallaka wa raina wani amfãni, kuma haka ban tunkuɗe wata cũta, fãceabin da Allah Ya so. Kuma dã na kasance inã sanin gaibi, dã lalle ne, nã yawaita daga alhẽri kuma cũta bã zã ta shãfe ni ba, nĩ ban zama ba fĩce mai gargaɗi, kumamai bãyar da bishãra ga mutãne waɗanda suke yin ĩmãni} [al-A'araf: 188].

Kuma ayoyi da suka zo da wannan ma’anar suna da yawa.

Kuma sanannen abu ne, lalle Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, ba ya kiran kowa sai Ubangijin sa, kamar yadda ya tabbata daga gare shi ya kasance a ranar (yaƙin) Badar yana neman agajin Allah ne, yana neman taimakon Sa akan abokan gabar sa, yana marairaicewa akan hakan, yana cewa: «Ya Ubangiji! Ka zartar min abinda Ka yi min alƙawarin sa». Har ya kai babban abokin sa, Abubakar - Allah Ya yarda da shi - Ya ce: Allah Ya isar maka Ya Ma’aikin Allah, lalle Allah Zai zartar maka alƙawarin da Ya yi maka, kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya saukar da faɗinSa a akan hakan:

﴿إِذۡ تَسۡتَغِيثُونَ رَبَّكُمۡ فَٱسۡتَجَابَ لَكُمۡ أَنِّي مُمِدُّكُم بِأَلۡفٖ مِّنَ ٱلۡمَلَٰٓئِكَةِ مُرۡدِفِينَ9﴾

{A lõkacin da kuke nẽman Ubangijinku taimako, sai Ya karɓa muku cẽwa: "Lalle ne Nĩ, Mai taimakon ku ne da dubu daga malã'iku, jẽre} [al-Anfal: 9]. Sai (Allah) - Maɗaukakin Sarki - Ya ambata musu neman agajin su a wannan ayar, Ya kuma labarta cewa Ya amsa musu, Sai ya ƙarfafe su da Mala’iku; domin bada bushara da nasara da kuma kwanciyar hankali, kuma (Allah) - tsarki ya tabbata a gare shi -Ya yi bayanin lalle ita nasarar ba daga Mala’iku take ba, ita nasara daga wurin Allah take, sai (Allah) - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿وَمَا النَّصْرُ إِلَّا مِنْ عِنْدِ اللَّهِ...﴾

{Taimako bai kasance ba fãce daga wurin Allah} [Aali- Imran: 126], Kuma Allah - Maɗaukaki - Ya ce:

﴿وَلَقَدْ نَصَرَكُمُ اللَّهُ بِبَدْرٍ وَأَنْتُمْ أَذِلَّةٌ فَاتَّقُوا اللَّهَ لَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ123﴾

{Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Allah Yã taimake ku a Badar, alhãli kuwa kunã mafiya rauni, sabõda haka ku bi Allah da taƙawa tsammãninku, kuna gõdẽwa} [Aal- Imran: 123]. Sai (Allah) - tsarki ya tabbata a gare Shi - Ya yi bayani a cikin waɗannan ayoyin, Shi ne Mai basu nasara a ranar (yaƙin) Badar, sai aka sani da wannan cewa, abinda Ya ba su na makamai da ƙarfi, da kuma abinda Ya ƙarfafe su da shi na Mala’iku, duka yana cikin sabubba ne na samun nasara da bushara da natsuwa, ba wai nasara daga Mala’ikun ba ne, kawai ita nasara daga wurin Allah take shi kaɗai. To, ta yaya wannan mai rubutun ta yi ƙarfin hali ko ma wanin ta, ta fuskantar da neman agajin ta da neman nasarar ta daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, ta juya baya daga Ubangijin talikai, Mamallakin kowanne abu, Mai iko akan dukkan komai?!

Babu shakka lallai wannan yana cikin mafi munin jahilci, kai yana cikin mafi munin shirka ma, to abinda ya zama wajibi ga ita mai wannan rubutun shi ne ta tuba zuwa ga Allah - tsarki ya tabbata a agare Shi -, tuba na gaskiya, tuba na gaskiya kuwa shi ne wanda ya ƙunshi abubuwa da dama, su ne kamar haka: Na farko: Nadama akan abinda ya afku daga garesu. Na biyu: Cirata daga abinda ya afka ɗin. Na uku: Niyyar ba zai sake komawa ga saɓon ba, domin girmama Allah da tsarkake addini gare Shi, da kuma kamantawa da umarnin Sa, da kiyayewa akan abinda Ya hana, wannan shi ne tuba mai kyau, Akwai kuma wani lamari na huɗu, shi na daban ne, idan saɓon ya kasance a haƙƙin halittu ne, shi ne:

Na hudu: Mayar da haƙƙi ga masu haƙƙin su, ko ya warware shi daga gare shi.

Kuma haƙiƙa Allah Ya umarci bayinSa da (su) tuba, kuma Ya yi musu alkawarin karɓar ta, kamar yadda Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿وَتُوبُوا إِلَى اللَّهِ جَمِيعًا أَيُّهَ الْمُؤْمِنُونَ لَعَلَّكُمْ تُفْلِحُونَ31﴾

{Kuma ku tũba zuwa ga Allah gabã ɗaya, yã ku mũminai! Tsammãninku, ku sãmi babban rabo} [al-Nur: 31], Kuma (Allah - Madaukakin Sarki -) Yace game da kiristoci:

﴿أَفَلَا يَتُوبُونَ إِلَى اللَّهِ وَيَسْتَغْفِرُونَهُ وَاللَّهُ غَفُورٌ رَحِيمٌ74﴾

{Shin fã, bã su tuba zuwa ga Allah, kuma su neme Shi gãfara, alhãli kuwa Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai?} [al-Ma'ida: 74], Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿وَالَّذِينَ لَا يَدْعُونَ مَعَ اللَّهِ إِلَهًا آخَرَ وَلَا يَقْتُلُونَ النَّفْسَ الَّتِي حَرَّمَ اللَّهُ إِلَّا بِالْحَقِّ وَلَا يَزْنُونَ وَمَنْ يَفْعَلْ ذَلِكَ يَلْقَ أَثَامًا68 يُضَاعَفْ لَهُ الْعَذَابُ يَوْمَ الْقِيَامَةِ وَيَخْلُدْ فِيهِ مُهَانًا69 إِلَّا مَنْ تَابَ وَآمَنَ وَعَمِلَ عَمَلًا صَالِحًا فَأُولَئِكَ يُبَدِّلُ اللَّهُ سَيِّئَاتِهِمْ حَسَنَاتٍ وَكَانَ اللَّهُ غَفُورًا رَحِيمًا70﴾

{Kuma waɗanda bã su kiran wani ubangiji tãre da Allah, kuma bã su kashe rai wanda Allah Ya haramta fãce da haƙƙi kuma bã su yin zina. Kuma wanda ya aikata wancan, zai gamu da laifuffuka}

{A riɓanya masa azãba a Rãnar al-ƙiyãma. Kuma ya tabbata a cikinta yanã wulakantacce}

{Sai wanda ya tũba, kuma ya yi ĩmãni, kuma ya aikata aiki na ƙwarai to, waɗancan Allah Yanã musanya miyãgun ayyukansu da mãsu kyau. Allah Ya kasance Mai gãfara Mai jin ƙai} [al-Furƙan: 68-70], Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿وَهُوَ الَّذِي يَقْبَلُ التَّوْبَةَ عَنْ عِبَادِهِ وَيَعْفُو عَنِ السَّيِّئَاتِ وَيَعْلَمُ مَا تَفْعَلُونَ25﴾

{Kuma Shi ne ke karɓar tũba daga bãyinSa, kuma Yanã Yafe ƙananan laifuffuka, alhãli kuwa Yanã sanin abin da kuke aikatãwa} [al-Shura: 25].

Kuma ya inganta daga Manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- cewa ya ce: «Musulunci yana rusa abin da ya gabace shi, kuma tuba tana kankare abin da ya gabace ta».

Haƙiƙa na tace waɗannan kalmomin a taƙaice, saboda girman hatsarin shirka, da kuma kasancewar ta mafi girman zunubai, da kuma tsoron ruɗuwa da abinda ya fito daga wannan mai rubutun, kuma saboda wajibcin nasiha saboda Allah da kuma bayinSa. Ina roƙon Allah - girman Sa ya ɗaukaka -, Ya anfanar da wannan (bayani), kuma Ya kyautata halayan mu da halayan musulmai baki ɗaya, kuma Ya yi mana baiwa da fahimtar Addini da tabbata a kan sa, Ya kuma tsare mu da musulmai daga sharrukan kawunan mu da munanan ayyukan mu, Shi Majiɓincin hakan ne, kuma mai iko ne akan hakan.

Allah Yayi tsira da aminci da albarka ga bawanSa kuma ManzonSa Annabin mu Muhammad da alayensa da aahabbansa.

 

***

 


بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ

SAƘO NA UKU

A cikin hukuncin neman taimako da aljanu da shaiɗanu da yin bakance gare su

Daga AbdulAzeez Bn Abdullahi Bn Baaz zuwa ga duk wanda ya gani daga cikin musulmai, Allah Ya datar da ni da su dan yin riƙo da addininSa da kuma tabbatuwa a kansa amin.

Amincin Allah a gareku da rahamarSa da albarkatunSa.

Bayan haka, haƙiƙa wani cikin ‘yan uwa ya tambaye ni akan wani abu da wasu jahilai suke aikatawa, na roƙon wanin Allah - tsarki ya tabbata a gare Shi -, da neman taimakon sa a muhimman abubuwa; kamar roƙon aljanu da neman agajin su, da yi musu alwashi da yi musu yanka. Daga wannan kuma zancen sashen su: (Ya Sab'atah), wato bakwai daga cikin shugabannin aljanu ku riƙe shi, ku karya ƙashin sa, ku sha jinin sa, ku daddatsa shi, Ya Sab’atah, ku aikata kaza da kaza da shi. Ko faɗin sashen su: (Ku kama shi ya ku aljanun tsakar rana, Ya ku aljanun la’asar), wannan akan same shi da yawa a ɓangaran kudanci. Yana kuma cikin abinda yake haɗuwa da wannan lamarin, kiran matattu daga cikin Annabawa da salihai da wasunsu, da kiran Mala’iku da kuma neman agajin su, Wannan fa gabaɗayan sa da ma ire-iren sa yana faruwa ne daga cikin masu jingina kansu da Musulinci, saboda sun jahilce shi, don kuma koyi da waɗanda suka gabace su, kuma akan sami wani daga sashen su ya ɗauki abin da sauƙi, har ma ya yi hujja akan hakan da cewa: Ai wannan abu ne da ke gudana a harshe, bamu nufatarsa, kuma bama ƙudurce shi.

Kuma ya tambaye ni: Game da hukuncin auran wanda aka san yana aikata waɗannan abubuwa, da (cin) yankan su, da yi musu sallah (idan sun mutu), haka (yin sallah) a bayan su, da kuma gaskata 'yan tsibbu da 'yan duba, kamar wanda yake da'awar sanin cuta da dalilanta ta hanyar kawai kallon wani abu daga cikin abinda ya taɓa jikin mara lafiya; kamar rawani da wando da mayafi da makamantan su.

Amsa ita ce: Godiya ta tabbata ga Allah Shi kaɗai, tsira da aminci su tabbata ga wanda babu wani Annabi a bayansa, da alayensa da sahabbansa da waɗanda suka shiriya da shiriyarsu har zuwa ranar sakamako.

Bayan haka: Lallai Allah - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka - Ya halicci mutane da aljanu don su bauta maSa, ba tare da bautawa waninSa ba, kuma su keɓance Shi da addu'a da neman taimako, da yanka da bakance da sauran ibadu, kuma Ya aiko Manzanni da wannan, kuma Ya umarce su da shi, Ya saukar da littattafan sama wanda mafi girma daga cikinsu shine Alƙur'ani mai girma da bayanin hakan da kuma kira zuwa gare shi, da gargaɗin mutane daga shirka da Allah da bautar waninSa. Wannan kuma shi ne asalin dukkan asalai, kuma tushen hanyar gaskiya da addini, kuma shi ne ma’anar shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma haƙiƙanin: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah. Ita kalmar shahada tana kore allantaka da ibadah ga wanin Allah, tana kuma tabbatar da ita - ai ibadah - ga Allah Shi kaɗai, banda waninSa daga sauran halittu, Dalilai akan wannan daga cikin littafin Allah da Sunnar ManzonSa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - suna da matuƙar yawa, daga ciki: Faɗin Allah - girman Sa ya ɗaukaka -:

﴿وَمَا خَلَقْتُ الْجِنَّ وَالْإِنْسَ إِلَّا لِيَعْبُدُونِ56﴾

{Kuma Ban halitta aljannu da mutãne ba sai dõmin su bauta Mini} [al-Zariyat: 56], Da faɗinSa - tsarki ya tabbatar maSa -:

﴿وَقَضَى رَبُّكَ أَلَّا تَعْبُدُوا إِلَّا إِيَّاهُ...﴾

{Kuma Ubangijinka Ya hukunta kada ku bauta wa kõwa fãce Shi} [al-Isra'a: 23], Da faɗinSa - Maɗaukakin Sarki -:

﴿وَمَا أُمِرُوا إِلَّا لِيَعْبُدُوا اللَّهَ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ حُنَفَاءَ...﴾

{Kuma ba a umarce su da kome ba fãce bauta wa Allah suna mãsu tsarkake addinin gare Shi, mãsu karkata zuwa ga addinin gaskiya} [al-Bayyinah: 5]. Da faɗinSa - Maɗaukakin Sarki -:

﴿وَقَالَ رَبُّكُمُ ادْعُونِي أَسْتَجِبْ لَكُمْ إِنَّ الَّذِينَ يَسْتَكْبِرُونَ عَنْ عِبَادَتِي سَيَدْخُلُونَ جَهَنَّمَ دَاخِرِينَ60﴾

{Kuma Ubangijinku ya ce: "Ku kira Ni in karɓa muku. Lalle waɗannan da ke kangara daga barin bauta Mini, za su shiga Jahannama sunã ƙasƙantattu} [Gafir: 60], Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿وَإِذَا سَأَلَكَ عِبَادِي عَنِّي فَإِنِّي قَرِيبٌ أُجِيبُ دَعْوَةَ الدَّاعِ إِذَا دَعَانِ...﴾

{Kuma idan bãyiNa suka tambaye ka daga gare Ni, to, lalle Ni Makusanci ne. Ina karɓa kiran mai kira idan ya kirā Ni} [al-Baƙara: 186].

Sai - tsarki ya tabbata a gare Shi - Ya bayyana a cikin waɗannan ayoyin cewa, Allah Ya halicci mutum da aljan ne domin su bauta masa, kuma Ya hukunta wato: Ya yi umarni da wasiyya ga bayinSa a ayoyin Alƙur'ani ingantattu, haka kuma akan harshen Manzo - tsira da aminci su tabbata a gare shi - cewa kada a bautawa kowa sai Ubangijin su.

Kuma (Allah) - Mai girma da ɗaukaka - Ya bayyana cewa addu'a ibada ce mai girma, wanda ya kangare daga gare ta zai shiga wuta, kuma ya umarci bayinsa su roƙe shi Shi kaɗai, kuma ya ba da labari cewa Yana kusa Yana amsa addu'arsu, don haka ya zama wajibi a kan dukkan bayi su keɓe Ubangijinsu da addu'a; domin ita nau'in ibada ce da aka halicce su don ta, kuma aka umarce su da ita, kuma (Allah) - Mai girma da ɗaukaka - Ya ce:

﴿قُلْ إِنَّ صَلَاتِي وَنُسُكِي وَمَحْيَايَ وَمَمَاتِي لِلَّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ162 لَا شَرِيكَ لَهُ وَبِذَلِكَ أُمِرْتُ وَأَنَا أَوَّلُ الْمُسْلِمِينَ163﴾

{Ka ce: "Lalle ne sallãta, da baikõna, da rãyuwãta, da mutuwãta, na Allah ne Ubangijin tãlikai"}

{Bãbu abõkin tãrayya a gare Shi. Kuma da wancan aka umurce ni, kuma ni ne farkon mãsu sallamãwa} [al-An'am: 162, 163].

Sai Allah Ya umarci AnnabinSa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, akan ya baiwa mutane labarin cewa sallar sa da baikon sa - shine yanka - da rayuwar sa da kuma mutuwar sa na Allah ne Ubangijin talikai ba Shi da abokin tarayya, gini akan hakan, duk wanda ya yi yanka ga wanin Allah to haƙiƙa ya yi wa Allah shirka, kamar da ace yayi sallah ga wanin Allah - Maɗaukakin Sarki -.; domin Allah - tsarki ya tabbata a gare Shi - Ya sanya sallah da yanka a tare, Ya kuma bada labarin cewa su din nan biyu na Allah ne Shi kadai, ba Shi da abokin tarayya. To duk wanda ya yi yanka ga wanin Allah daga aljanu, Mala’iku, matattu da sauransu, yana neman kusanci gare su, to kamar wanda ya yi sallah ne ga wanin Allah. Ya zo a cikin hadisi ingantacce cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Allah Ya tsinewa wanda yayi yanka dan wanin Allah». Imam Ahmad ya fitar (da hadisi) da isnadi mai kyau daga Ɗariƙ ɗan Shihab - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - cewa shi ya ce: «Wasu mutum biyu sun wuce ta wurin wasu mutane da suke da wani gunki da ba wanda zai wuce shi sai ya miƙa masa wani abu dan neman kusanci, sai suka ce wa ɗaya daga cikinsu: Miƙa. Sai ya ce: Bani da wani abu da zan bayar, sai suka ce: Miƙo ko da ƙuda ne, sai ya bada wani ƙuda, sai suka barshi ya tafi, sai ya shiga wuta. Kuma suka ce wa ɗayan: Miƙo. Sai ya ce: Bazan miƙawa kowa wani abuba sai Allah - Mai girma da ɗaukaka - sai suka sare kansa, sai ya shiga Aljanna».

To idan wanda ya kasance yana neman kusanci ga gunki da makamancin shi da ƙuda da makamancin sa, yana zama mushriki, yana cancantar shiga wuta, to ya kake ganin wanda yake kiran aljanu da Mala’iku da waliyyai, to ya wanda yake neman agajin su yana musu bakance yana neman kusanta gare su da yanke-yanke, yana fatan tsarin dukiyarsa ko warakar da mara lafiyarsa ko amincin dabbobinsa da gonarsa, kuma ya ga wanda yake aikata hakan dan tsoron sharrin aljanu ko abinda ya yi kama da hakan.?!

Babu shakka duk wanda ya aikata haka da abubuwan da suke kama da hakan, shi ya fi cancantar zama mushiriki da ya cancanci shiga wuta akan wannan mutumin da ya gabatar da ƙuda ga gunki dan neman kusanci.

Daga cikin abinda ya zo a cikin wannan - kuma - faɗinSa - Maɗaukakin Sarki -:

﴿إِنَّآ أَنزَلۡنَآ إِلَيۡكَ ٱلۡكِتَٰبَ بِٱلۡحَقِّ فَٱعۡبُدِ ٱللَّهَ مُخۡلِصٗا لَّهُ ٱلدِّينَ2 أَلَا لِلَّهِ ٱلدِّينُ ٱلۡخَالِصُۚ وَٱلَّذِينَ ٱتَّخَذُواْ مِن دُونِهِۦٓ أَوۡلِيَآءَ مَا نَعۡبُدُهُمۡ إِلَّا لِيُقَرِّبُونَآ إِلَى ٱللَّهِ زُلۡفَىٰٓ إِنَّ ٱللَّهَ يَحۡكُمُ بَيۡنَهُمۡ فِي مَا هُمۡ فِيهِ يَخۡتَلِفُونَۗ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَهۡدِي مَنۡ هُوَ كَٰذِبٞ كَفَّارٞ3﴾

{Mun saukar da littafi a gareka da gaskiya sai ka bautawa Allah kana mai tsarkake Addini a gare Shi}

{To, addini tsarkakakke na Allah ne, kuma waɗanda suka riƙi waɗansu majibinta, bã Shi ba, (sunã cẽwa) "Ba mu bauta musu ba fãce dõmin su kusantar da mu zuwa ga Allah, kusantar daraja." Lalle Allah nã yin hukunci a tsakãninsu ga abin da suka zama sunã sãɓãwa a cikinsa. Lalle Allah ba Ya shiryar da wanda yake mai ƙarya, mai kãfirci} [al-Zumar: 1-3], Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿وَيَعْبُدُونَ مِنْ دُونِ اللَّهِ مَا لَا يَضُرُّهُمْ وَلَا يَنْفَعُهُمْ وَيَقُولُونَ هَؤُلَاءِ شُفَعَاؤُنَا عِنْدَ اللَّهِ قُلْ أَتُنَبِّئُونَ اللَّهَ بِمَا لَا يَعْلَمُ فِي السَّمَاوَاتِ وَلَا فِي الْأَرْضِ سُبْحَانَهُ وَتَعَالَى عَمَّا يُشْرِكُونَ18﴾

{Kuma sunã bautã wa, baicin Allah, abin da bã ya cũtar dasu kuma bã ya amfãninsu, kuma sunã cẽwa: "Waɗannan ne macẽtanmu a wurin Allah."Ka ce: "Shin, kunã bai wa Allah lãbãri ne, ga abin da bai sani ba, a cikin sammai ko a cikin ƙasa? TsarkinSa ya tabbata kuma ɗaukaka daga abin da duk suke yin shirki da Shi."} [Yunus: 18].

Sai Allah - tsarki ya tabbata a gare Shi - Ya bada labari a cikin waɗannan ayoyi biyu, cewa mushirikai sun ɗauki wasu ba Allah ba majiɓinta daga cikin halittu, suna bauta musu tare da Shi (Allah) akan tsoro da fata da yanka da bakance da addu’a da makamancin haka, suna raya cewa waɗannan majiɓintan suna kusantar da waɗanda suka bauta musu zuwa ga Allah, kuma suna cetonsu a wurinSa. Sai Allah - tsarki ya tabbata a gare Shi - Ya ƙaryata su, Ya fayyace ƙaryarsu, Ya kuma kirasu maƙaryata, kafirai kuma mushirikai, Ya kuma tsarkake kanSa daga barin tarayya da Shi, sai Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya ce:

﴿...سُبْحَانَهُ وَتَعَالَى عَمَّا يُشْرِكُونَ﴾

{TsarkinSa ya tabbata kuma ɗaukaka daga abin da duk suke yin shirki da Shi} [al-Nahl: 1]. Sai aka sani da wannan cewa, duk wanda ya riƙi wani mala'ika, ko Annabi ko aljani ko itace ko dutse yana kiransa tare da Allah, kuma yake neman taimakonsa, yana neman kusanci gare shi, da bakance da kuma yanka, da fatan samun cetonsa a wurin Allah, da kusantar da shi gare Shi, ko fatan warkar da mara lafiya, ko kiyaye dukiya, ko kuɓutar da wanda baya nan, ko makamancin haka; to haƙiƙa ya faɗa cikin shirka mai girma saboda wannan, da bala'i mai tsanani, wanda Allah Ya ce game da shi:

﴿إِنَّ اللَّهَ لَا يَغْفِرُ أَنْ يُشْرَكَ بِهِ وَيَغْفِرُ مَا دُونَ ذَلِكَ لِمَنْ يَشَاءُ وَمَنْ يُشْرِكْ بِاللَّهِ فَقَدِ افْتَرَى إِثْمًا عَظِيمًا48﴾

{Lalle ne, Allah ba Ya gãfarta a yi shirki game da Shi, kuma Yana gãfarta abin da yake bãyan wannan ga wanda Yake so, kuma wanda ya yi shirki da Allah, to, lalle ne ya ƙirƙiri zunubi mai girma} [al-Nisa'a: 48], Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿إِنَّهُ مَنْ يُشْرِكْ بِاللَّهِ فَقَدْ حَرَّمَ اللَّهُ عَلَيْهِ الْجَنَّةَ وَمَأْوَاهُ النَّارُ وَمَا لِلظَّالِمِينَ مِنْ أَنْصَارٍ72﴾

{Lalle ne shĩ, wanda ya yi shirki da Allah, to, lalle ne, Allah Yã haramta masa Aljanna. Kuma bãbu wasu mataimaka ga azzãlumai} [al-Ma'ida: 72].

Kuma ceto yana samuwa ne kawai a ranar Alƙiyama ga ma'abota tauhidi da ikhlasi, ba ga masu shirka ba, kamar yadda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce lokacin da aka ce masa: Ya Manzon Allah, waye mafi arziƙin mutane da samun cetonka? sai ya ce: «Wanda ya ce: (Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah) yana mai ikhlasi daga zuciyarsa». Kuma - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Kowane Annabi yana da addu'ar da aka amsa masa, sai kowanne Annabi ya gaggauta addu'arsa, amma ni na ɓoye addu'a ta ta zama ceto ga al'ummata ranar Alƙiyama, kuma - in sha Allah - zata samu duk wanda ya mutu daga al'ummata ba tare da yayi shirka da Allah ba».

Kuma mushrikai na farko sun kasance suna imani da cewa Allah ne Ubangijinsu kuma Mahaliccinsu kuma Mai azurtarsu, kaɗai sun jingina ne ga annabawa da waliyyai da mala'iku da itatuwa da duwatsu da makamantan haka, suna fatan cetonsu a wurin Allah, da kusantar da su zuwa gare Shi, kamar yadda ya rigaya a cikin ayoyi, Allah Baiyi musu uzuri da hakan ba, bari ma dai, Allah Ya yi musu inkari a cikin littafinSa mai girma, Ya kuma kirasu kafirai da mushirikai, Ya kuma ƙaryata su a riyawar da suka yi akan cewar waɗannan allolin za su cecesu kuma za su kusantar da su ga Allah kusantarwa ta daraja. Haka Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - bai yi musu uzuri ba, bari ma dai, Manzon - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, ya yaƙe su ne akan wannan shirkar har sai sun tsarkake ibada domin Allah shi kaɗai, don aiki da faɗinSa - tsarki ya tabbata a gare shi -:

﴿وَقَاتِلُوهُمْ حَتَّى لَا تَكُونَ فِتْنَةٌ وَيَكُونَ الدِّينُ لِلَّهِ...﴾

{Kuma ku yãƙe su har ya zama wata fitina bã zã ta kasance ba, kuma addini ya zama na Allah} [al-Baƙara: 193]. Kuma Manzo- tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «An umurce ni da in yãƙi mutane har sai sun shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma cewa (Annabi) Muhammadu Manzon Allah ne, kuma su tsaida sallah, kuma su bayar da zakkah, to idan suka aikata haka sun tsare jinanansu da dukiyoyinsu daga gareni, sai dai bisa haƙƙin musulunci, kuma hisabinsu yana ga Allah». Ma'anar faɗin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: «Har sai sun shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah» Wato: Har sai sun keɓe Allah da bauta, ba tare da waninSa ba.

Kuma haƙiƙa mushirikan sun kasance suna tsoron aljanu suna kuma neman tsari da su, sai Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya saukar da faɗinSa akan hakan:

﴿وَأَنَّهُ كَانَ رِجَالٌ مِنَ الْإِنْسِ يَعُوذُونَ بِرِجَالٍ مِنَ الْجِنِّ فَزَادُوهُمْ رَهَقًا6﴾

{"Kuma lalle ne shi wasu maza daga cikin mutãne, sun kasance sunã nẽman tsari da wasu maza daga cikin aljannu, sabõda haka suka ƙara musu girman kai"} [al-Jin: 6]. Malaman tafsiri sun faɗi ma'anar faɗinSa: Akan wannan ayar mai girma:

﴿...فَزَادُوهُمْ رَهَقًا﴾

{"Sabõda haka suka ƙara musu girman kai"} Wato: firgici da tsoro; domin aljanu suna jin izza a kansu da girman kai, idan suka ga mutane suna neman tsari da su, a lokacin sai su ƙara musu tsoro da firgici, har sai sun ƙara yawan bautarsu, da fakewa gare su.

Kuma haƙiƙa Allah Ya mayar wa musulmai hakan ta hanyar neman tsari da Shi - tsarki ya tabbatar maSa -, da kuma cikakkun kalmominSa, kuma Ya saukar da wannan a cikin zancenSa - Maɗaukaki Sarki - inda Ya ce:

﴿وَإِمَّا يَنْزَغَنَّكَ مِنَ الشَّيْطَانِ نَزْغٌ فَاسْتَعِذْ بِاللَّهِ إِنَّهُ سَمِيعٌ عَلِيمٌ200﴾

{Kuma imma wata fizga daga Shaiɗan ta fizge ka, sai ka nẽmi tsari ga Allah. Lalle ne shi, Mai jĩ ne, Masani} [al-A'araf: 200], Da faɗinSa - Maɗaukakin Sarki -:

﴿قُلْ أَعُوذُ بِرَبِّ الْفَلَقِ1﴾

{Ka ce "ina neman tsari ga Ubangijin safiya"}, Kuma ya inganta daga annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa ya ce: «Duk wanda ya sauka a wani masauki sai ya ce: (Ina neman tsari da kalmomin Allah cikakku daga sharrin abin da Ya halitta); wani babu bazai cutar da shi ba har ya bar masaukinsa wannan».

Daga cikin ayoyi da hadisan da suka gabata, mai neman tsira zai sani, kuma mai burin kiyaye Addininsa, da samun tsira daga shirka, zuzzurfinta da bayyanennenta, zai fahimci cewa dogaro da matattu da mala'iku da aljannu da wasunsu daga halittu, da kiran su da neman tsari da su da makamantan haka; yana daga cikin ayyukan mutanen Jahiliyya mushrikai, kuma yana daga cikin mafi munin shirka da Allah - tsarki ya tabbatar maSa -, don haka wajibi ne a bar shi, da kiyayewa daga wannan, da yiwa juna wasiyya da barin sa, da yin Allah wadai ga wanda ya aikata shi.

Amma wanda aka san shi a cikin mutane da irin waɗannan ayyukan na shirka, to ba ya halitta a aurar masa, haka ba ya halitta a ci yankansa haka yi masa sallah haka kuma sallah a bayansa, har sai ya bayyanar da tubansa ga Allah - Maɗaukakin sarki - akan hakan, ya tsarkake addu’ar sa da kuma tsarkake ibada ga Allah Shi kaɗai. Addu’a kuma ita ce ibada, a’a ita ce ma ɓargon (jigon) ta, kamar yadda Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Addu'a itace ibada». Kuma an ruwaito daga gare shi (Annabi) - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a wani lafazin daban cewa ya ce: «Addu'a ita ce ɓargon (jigon) ibada». Amma aurar mushirikai: to haƙiƙa Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿وَلَا تَنْكِحُوا الْمُشْرِكَاتِ حَتَّى يُؤْمِنَّ وَلَأَمَةٌ مُؤْمِنَةٌ خَيْرٌ مِنْ مُشْرِكَةٍ وَلَوْ أَعْجَبَتْكُمْ وَلَا تُنْكِحُوا الْمُشْرِكِينَ حَتَّى يُؤْمِنُوا وَلَعَبْدٌ مُؤْمِنٌ خَيْرٌ مِنْ مُشْرِكٍ وَلَوْ أَعْجَبَكُمْ أُولَئِكَ يَدْعُونَ إِلَى النَّارِ وَاللَّهُ يَدْعُو إِلَى الْجَنَّةِ وَالْمَغْفِرَةِ بِإِذْنِهِ وَيُبَيِّنُ آيَاتِهِ لِلنَّاسِ لَعَلَّهُمْ يَتَذَكَّرُونَ221﴾

{Kuma kada ku auri mãtã mushirikai sai sun yi ĩmãni: Kuma lalle ne baiwa mũmina ita ce mafi alhẽri daga ɗiya kãfira, kuma kõ da tã bã ku sha'awa. Kuma kada ku aurar wa maza mushirikai sai sun yi ĩmãni, kuma lalle ne bãwa mũmini shi ne mafi alhẽri daga da mushiriki, kuma kõ da yã bã ku sha'awa, waɗannan suna kira ne zuwa ga wuta kuma Allah Yana kira zuwa ga Aljanna da gãfara da izninsa. Kuma Yana bayyana ãyõyinsa ga mutãne; tsammãninsu suna tunãwa} [al-Baƙara: 221], Sai Allah - tsarki ya tabbatar maSa -, Ya hana musulmai daga auren mãtã mushirikai, daga masu bautar gumãka da aljannu da mala'iku da sauran su, sai sunyi ĩmãni da tsarkake ibãda ga Allah Shi kaɗai, da gasgata Manzo, - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a cikin abin da yazo da shi, da bin hanyar sa, kuma ya hana aurar mãza mushirikai ga mãtã Musulmai, sai sun yi ĩmãni da tsarkake ibãda ga Allah Shi kaɗai, da gasgata Manzo - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, da kuma binsa.

Allah - tsarki ya tabbatar maSa - Ya bada labari cewa baiwa mumina tafi alheri daga 'yantacciyar mushrika, ko da ta burge wanda yake kalle ta, yake ji maganarta, saboda kyawunta da kyawun maganarta, kuma bawa mumini ya fi alheri daga 'yantaccen mushriki, ko da ya burge mai sauraro da mai kallon sa, saboda kyawunsa da fasaharsa da jarumtarsa da sauran su, sannan Ya bayyana dalilan wannan fifiko da fadinSa - tsarki ya tabbatar maSa -:

﴿...أُولَئِكَ يَدْعُونَ إِلَى النَّارِ...﴾

{Waɗannan suna kira ne zuwa ga wuta} [al-Baƙara: 221]. Yana nufin da wannan: Mushirikai maza da mushirikai mata; domin su na daga masu kira zuwa wuta da maganganunsu da ayyukansu da halayensu da ɗabi'unsu, amma muminai maza da muminai mata su na daga masu kira zuwa aljanna da ɗabi'unsu da ayyukansu da halayensu, to yaya waɗannan da waɗannan za su daidaita!

Amma yin sallah ga mushirikai (bayan mutuwarsu): to haƙiƙa Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya ce:

﴿وَلَا تُصَلِّ عَلَى أَحَدٍ مِنْهُمْ مَاتَ أَبَدًا وَلَا تَقُمْ عَلَى قَبْرِهِ إِنَّهُمْ كَفَرُوا بِاللَّهِ وَرَسُولِهِ وَمَاتُوا وَهُمْ فَاسِقُونَ84﴾

{Kuma kada ka yi salla a kan kõwa daga cikinsu wanda ya mutu, har abada, kuma kada ka tsaya a kan kabarinsa. Lalle ne sũ, sun kãfirta da Allah da ManzonSa, kuma sun mutu alhãli kuwa sunã fãsiƙai} [al-Taubah: 84], Sai (Allah) - Mai girma da ɗaukaka - Ya bayyana cikin wannan aya mai girma cewa ba za ayi sallah ga munafuki da kafiri ba; saboda kafircinsu ga Allah da ManzonSa, haka kuma ba za ayi sallah a bayansu, kuma ba za a sanya su shugabanni ga musulmai ba; saboda kafircinsu da rashin amincinsu, da kuma babbar adawa da ke tsakaninsu da musulmai, kuma saboda ba su daga cikin masu sallah da ibada; domin aiki baya wanzuwa a tare da kafirci da shirka, muna roƙon Allah Ya ba mu lafiya daga hakan. Amma kuma cin yankan mushirikai: to haƙiƙa Allah - girman Sa ya ɗaukaka - ya ce, Yana mai bayyana haramcin mushe da yankan mushirikai:

﴿وَلَا تَأْكُلُوا مِمَّا لَمْ يُذْكَرِ اسْمُ اللَّهِ عَلَيْهِ وَإِنَّهُ لَفِسْقٌ وَإِنَّ الشَّيَاطِينَ لَيُوحُونَ إِلَى أَوْلِيَائِهِمْ لِيُجَادِلُوكُمْ وَإِنْ أَطَعْتُمُوهُمْ إِنَّكُمْ لَمُشْرِكُونَ121﴾

{Kada ku ci daga abin da ba a ambaci sũnan Allah ba a kansa.* Kuma lalle ne shĩ fãsiƙanci ne. Kuma lalle ne, shaiɗãnu, haƙĩƙa, suna yin ishãra zuwa ga masõyansu, dõmin su yi jãyayya da ku. Kuma idan kuka yi musu ɗã'a, lalle ne kũ, haƙĩƙa, mãsu shirki ne} [al-An'am: 121], Sai Allah - girman Sa ya ɗaukaka - Ya hana musulmai cin mushe da yankan mushiriki; domin najasa ce, to yankansa yana da hukuncin mushe ne, ko da ya ambaci sunan Allah a yankan, domin ambaton Allah da ya yi a yankan ɓatacce ne ba shi da wani tasiri, domin hakan ibada ce, shirka kuma tana ɓata ibada ta lalata ta, har sai mushiriki ya tuba ya koma ga Allah - tsarki ya tabbata a gare shi -. Kaɗai - Maɗaukakin Sarki - Ya halatta abincin ma'abota littafi a cikin faɗinSa - tsarki ya tabbatar maSa -:

﴿...وَطَعَامُ الَّذِينَ أُوتُوا الْكِتَابَ حِلٌّ لَكُمْ وَطَعَامُكُمْ حِلٌّ لَهُمْ...﴾

{Kuma abincin waɗanda aka bai wa Littãfi halal ne a gare ku, kuma abincinku halal ne a gare su} [al-Ma'ida: 5], Saboda suna danganta kansu da Addini na sama, suna raya cewa su mabiyan Musa da Isa ne, duk da cewa ƙarya suke, kuma haƙiƙa Allah Ya shafe Addininsu Ya kuma soke shi da aiko Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ga mutane baki ɗaya, amma Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya halatta mana abincin Ahlul kitabi da (auren) matansu; saboda hikima mai girma da sirrika masu daraja, lallai malamai sun bayyana su, saɓanin mushrikai daga masu bautar gumaka da matattu, daga Annabawa da waliyyai da sauransu; domin Addininsu ba shi da asali, kuma babu shubha a cikin sa, bar dai, shi ɓatacce ne tun daga tushen sa, sai yankan mutanensa ya zama mushe, kuma cin sa ba ya halatta.

Amma faɗin mutum ga wanda yake yi wa magana: (Aljan ya same ka), (Aljan ya ɗauke ka), (Shaiɗan ya tashi da kai), da makamancin haka, wannan yana daga cikin zagi da tsinuwa, kuma hakan bai halatta tsakanin musulmi ba, kamar sauran nau'ikan zagi da tsinuwa, kuma wannan ba daga cikin shirka bane, sai dai idan mai faɗin hakan yana ƙudurcewa cewa aljanu suna tasarrafi a cikin mutane ba tare da izinin Allah da nufinSa ba. To duk wanda ya ƙudurce hakan a sha'anin aljannu ko waninsu daga cikin halittu, to kafiri ne da wannan ƙudurcewar, domin Allah - tsarki ya tabbatar maSa - Shine Mai mulki ga dukkan komai, kuma Mai iko akan dukkan komai, Shine Mai amfannarwa da cutarwa, kuma babu wani abu da za'a samar sai da izininSa da sonSa da ƙaddararSa mai gabatuwa, kamar yadda - Maɗaukakin sarki - Ya ce, yana mai umartar AnnabinSa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da ya sanar da mutane wannan babban asali:

﴿قُلْ لَا أَمْلِكُ لِنَفْسِي نَفْعًا وَلَا ضَرًّا إِلَّا مَا شَاءَ اللَّهُ وَلَوْ كُنْتُ أَعْلَمُ الْغَيْبَ لَاسْتَكْثَرْتُ مِنَ الْخَيْرِ وَمَا مَسَّنِيَ السُّوءُ إِنْ أَنَا إِلَّا نَذِيرٌ وَبَشِيرٌ لِقَوْمٍ يُؤْمِنُونَ188﴾

{Ka ce: "Bã ni mallaka wa raina wani amfãni, kuma haka ban tunkuɗe wata cũta, fãce abin da Allah Ya so. Kuma dã na kasance inã sanin gaibi, dã lalle ne, nã yawaita daga alhẽri kuma cũta bã zã ta shãfe ni ba, nĩ ban zama ba fĩce mai gargaɗi, kumamai bãyar da bishãra ga mutãne waɗanda suke yin ĩmãni} [al-A'araf: 188], Idan shugaban halitta kuma mafi alherinsu - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ba ya mallakawa kansa wani amfani ko cuta, sai abinda Allah Ya ga dama, to ta yaya ga waninSa daga cikin halitta?! Kuma ayoyi masu yawa suna cikin wannan ma'ana.

Kuma tambayar ƴan duba da masu tsibbu da masana taurari da makamantansu, waɗanda suke da'awar bayar da labari akan abubuwan da suke ɓoye, to wannan abin ƙi ne da ba ya halatta, kuma gaskata su ya fi muni kuma ya fi zama abin ƙyama, har ma yana daga cikin rassan kafirci; saboda faɗin Annabi

- tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: «Wanda ya je wurin ɗan duba ya tambaye shi wani abu; ba za a karɓi Sallarsa ta kwana arba’in ba». Muslim ne ya rawaito shi a cikin Sahih ɗin sa, Ya zo a cikin Sahihin sa - kuma - daga Mu'awiya bin al-Hakam al-Sulami -Allah Ya yarda da shi: «Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya hana zuwa wajen bokaye da tambayar su».

Masu (littattafan) Sunan sun ruwaito daga annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa shi ya ce: «Duk wanda yaje wajen boka, sai ya gasgata shi cikin abinda yake cewa; to haƙiƙa ya kafirta da abinda aka saukarwa (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -». Hadisai da suka zo da wannan ma’anar suna da yawa. Abinda yake wajibi a kan musulmi: Su yi hattara daga tambayar bokaye da masu duba, da sauran masu tsibbu, waɗanda suka shagala da bada labari game da gaibu, da yaudarar musulmi, ko da sunan magani ko wani abu daban, saboda abin da ya gabata na hani daga - Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, da kuma tsawatarwar sa daga gare shi, Yana kuma shiga cikin hakan: Abinda wasu cikin mutane suke cewa da sunan ɗibbu (magani), na wasu lamurra na gaibu. Idan ya shinshina rawanin mara lafiya ko kallabin mara lafiya ko makamantan haka, sai ya ce: Wannan mara lafiyan ko mara lafiyar ya aikata abu kaza ko ya yi abu kaza, na abubuwan gaibu wanda ba ya jikin rawanin mara lafiyar da makamantan haka domin nuni akan hakan, kawai manufa akan hakan ita ce rikitar da mutane har ya kai ga mutane suke cewa: Ai masanin magunguna ne, da nau’ukan cututtuka da sabubban su, wataƙil ya ba su wasu abubuwa daga magunguna, kuma wataƙil ya dace da wannan warakar da ƙaddarar Allah, sai su yi tsmammanin ta sanadiyyar waɗannan magungunan nasa ne. Wataƙila rashin lafiya yana zuwa ne ta dalilin wasu aljanu da shaiɗanu, waɗanda suke hidimtawa wannan mai iƙirarin likitancin, kuma suna sanar da shi wasu daga cikin abubuwan gaibu waɗanda suke tsinkaye akan su, sai ya dogara da hakan, kuma ya gamsar da aljanu da shaiɗanu da abin da ya dace da su na ibada, sai su ɗauke kansu daga wannan mara lafiya, su bar abin da suka cuɗanya shi da shi yi na cutarwar, wannan sanannen abu ne game da aljanu da shaiɗanu da masu amfani da su.

Abinda yake wajibi akan musulmai kuma shi ne: A kiyayi haka, kuma a hana juna hakan, a kuma dogara ga Allah - tsarki ya tabbata a gare Shi -, da kuma dogaro gare Shi a dukkanin lamurra, babu laifi idan mutum ya yi Ruƙya (tofi na shari’a) da halastattun magunguna, da magani wurin likitoci waɗanda suke bincike ga mara lafiya da kuma tabbatarwa akan rashin lafiyar ta sa, ta hanyar zahiri da hankali, haƙiƙa ya inganta daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - cewa ya ce : «Allah bai saukar da wata cuta ba, face ya saukar da waraka gare ta, wanda ya sani ya sani, wanda bai sani ba bai sani ba». Kuma - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Ga kowacce cuta an sanya mata magani, idan maganin ya haɗu da cutar, sai ya warke da izinin Allah». Kuma - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Ya bãyin Allah, ku nemi magani amma kada ku nemi mãgani da haram». Hadisai da suka zo da wannan ma’anar suna da yawa.

To muna roƙon Allah - girmanSa ya ɗaukaka -, da Ya gyara halayan musulmai baki ɗaya, Ya kuma warkar da zukatansu da jikinsu daga kowanne mugun abu, Ya kuma tara su akan shiriya, Ya kuma tsaremu da su daga fitintinu masu ɓatarwa, haka kuma ya tsare daga yi wa shaiɗan biyayya da majiɓantansa, lalle Shi (Allah) Mai iko ne akan komai, kuma babu ƙarfi babu dabara sai da (nufin) Allah - Mai ɗaukaka Mai girma -.

Allah Yayi tsira da aminci da albarka ga bawanSa kuma ManzonSa Annabin mu Muhammad da alayensa da aahabbansa.

 

 

***

 


بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ

SAƘO NA HUƊU:

Akan hukuncin yin ibadah da wasu wuridai na bidi’a da na shirka

Daga AbdulAzeez Bn Abdullahi Bn Baaz zuwa ga ɗan'uwa mai daraja (.........), Allah Ya datar da shi ga dukkan alheri, amin.

Amincin Allah ya tabbata a gareku da rahamarSa da albarkatunSa.

Bayan haka: Haƙiƙa littafina mai daraja ya iso gare ku, Allah Ya haɗa ku da shiriyarSa, da abinda ya ƙunsa na fa'ida cewa akwai mutane waɗanda suke riƙon waɗansu wuridan da Allah bai saukar da wani dalili ba a kansu ba, daga cikinsu akwai wanda bidi'a ne, kuma akwai wanda shirka ne, kuma suna danganta hakan zuwa ga Amirul Muminin: Aliyu ɗan Abu Ɗalib - Allah Ya yarda da shi - da waninsa. Kuma suna karanta waɗannan zikiran a majalisai na zikiri, ko a masallatai bayan sallar magariba, suna zaton cewa hakan kusanci ne ga Allah, kamar faɗin su: Don haƙƙin Allah, Ya ku bayin Allah, ku taimake mu da taimakon Allah, kuma ku kasance taimakon mu don Allah. Kuma kamar faɗin su: Ya ƙuɗubai, ya shuwagabanni, ku amsa, ya masu madadi a cikinmu, ku yi ceto zuwa ga Allah, wannan bawan ku ne a tsaye, kuma a ƙofar ku yana mai kifuwa, kuma yana mai jin tsoro daga gazawarsa, ka taimake mu ya Manzon Allah, ba inda zanje in ba wurinku ba, kuma daga gare ku ne ake samun buƙata, kuma ku ne mutanen Allah, don Hamza shugaban shahidai, ya mamakin madadain da ake samu daga gurinku, ka taimake mu ya Manzon Allah. Kuma kamar faɗin su: Ya Allah Kayi salati ga wanda Ka sanya shi sanadiyyar buɗewar asiranKa na Aljabarut, kuma haskaka fitilun rahamarKa, har ya zama wakili daga halarar Ubangiji, kuma halifan asiranKa na zati.

Da kuma kwaɗayinku akan bayanin mecece bidi’a, kuma mecece shirka, kuma shin sallah ta yi idan aka yi ta bayan limamin da yake yin wannan addu’ar, dukkan wannan ya kasance sananne ne?.

Amsa ita ce: Godiya ta tabbata ga Allah Shi kaɗai, tsira da aminci su tabbata ga wanda babu wani Annabi a bayansa, da alayensa da sahabbansa, da kuma duk wanda ya shiryu da shiriyarsa har zuwa ranar sakamako.

Bayan haka: Ka sani - Allah Ya datar da kai - lallai Allah - tsarki ya tabbata a gareShi - kaɗai, Ya halicci halitta kuma Ya aiko manzanni - tsira da aminci su tabbata a gare su - dan a bauta maSa Shi kaɗai, ba Shi da abokin tarayya, banda dukkan waninSa, kamar yadda Allah - Maɗaukaki - Ya ce:

﴿وَمَا خَلَقْتُ الْجِنَّ وَالْإِنْسَ إِلَّا لِيَعْبُدُونِ56﴾

{Kuma Ban halitta aljannu da mutãne ba sai dõmin su bauta Mini} [al-Zariyat: 56].

Ibadah, - kamar yadda bayani ya gabata - ita ce: Biyayya ga Allah tsarki ya tabbata a gare Shi - da kuma biyayya ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, ta hanyar aikata abinda Allah da ManzonSa suka yi umarni da shi, da kuma barin abinda Allah da Manzon Sa suka hana, na daga imani da Allah da ManzonSa, da tsarkake ibadah domin Allah a aiki, tare da kai ƙoli a son Allah, da cikar ƙanƙan da kai ga Allah Shi kaɗai banda wani wanda ba Shi ba; kamar yadda Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿وَقَضَى رَبُّكَ أَلَّا تَعْبُدُوا إِلَّا إِيَّاهُ...﴾

{Kuma Ubangijinka Ya hukunta kada ku bauta wa kõwa fãce Shi} [al-Isra'a: 23] Wato: Ya yi umarni kuma Ya yi wasiyya da a bauta maSa Shi kaɗai, Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿الْحَمْدُ لِلَّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ2 الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ3 مَالِكِ يَوْمِ الدِّينِ4 إِيَّاكَ نَعْبُدُ وَإِيَّاكَ نَسْتَعِينُ5﴾

{Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu,

Mai rahama, Mai jin ƙai,

Mai nuna Mulkin Rãnar Sakamako,

{Kai kaɗai muke bautawa, kuma Kai kaɗai muke neman taimakonKa} [al-Fatiha: 2-5]. Sai Allah - Mai tsarki da ɗaukaka - Ya yi bayani a waɗannan ayoyin: Cewar Shine wanda Ya cancanci da a bauta masa Shi kaɗai, kuma a nemi taimakonSa Shi kaɗai. Allah - girmanSa ya ɗaukaka - Ya ce:

﴿إِنَّآ أَنزَلۡنَآ إِلَيۡكَ ٱلۡكِتَٰبَ بِٱلۡحَقِّ فَٱعۡبُدِ ٱللَّهَ مُخۡلِصٗا لَّهُ ٱلدِّينَ2 أَلَا لِلَّهِ ٱلدِّينُ ٱلۡخَالِصُۚ...﴾

{Mun saukar da littafi a gareka da gaskiya ka bautawa Allah kana mai tsarkake Addini a gare Shi.To, addini tsarkakakke na Allah ne}

To, addini tsarkakakke na Allah ne... [al-Zumar: 2-3]. Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿فَادْعُوا اللَّهَ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ وَلَوْ كَرِهَ الْكَافِرُونَ14﴾

{Sabõda haka ku kirãyi Allah, kunã mãsu tsarkake addini a gare Shi, kuma kõ dã kãfirai sun ƙi} [Ghafir: 14], Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿وَأَنَّ الْمَسَاجِدَ لِلَّهِ فَلَا تَدْعُوا مَعَ اللَّهِ أَحَدًا18﴾

{Kuma lalle ne wurãren sujada na Allah ne, saboda haka kada ku kira kõwa tãre da Allah (da su, a cikinsu)} [al-Jinn: 18], Ayoyi a cikin wannan ma'ana suna da yawa, kuma dukkansu suna nuna wajabcin kaɗaita Allah da ibada.

Sanannen abu ne cewa ita addu’a da dukkanin nau’ukan ta ibadah ce, ba ya halatta ga wani daga mutane ya roƙi kowa face UbangijinSa, kuma ba zai roƙi wani ko ya nemi agajin wani ba saidai Allah (shi kaɗai), domin yin aiki da waɗannan ayoyin masu daraja, da kuma abinda ya zo a ma’anonin su. Wannan yana bayan abubuwan al'ada, da dalilan zahiri, wanda halitta mai rai gamu-ga-shi ke da iko akansu, domin waɗannan basa daga ibada, bari dai yana halatta da nassi da ijma'i cewa mutum zai iya neman taimako daga mutum mai rai mai iko, a cikin abubuwan al'ada da yake da iko akansu; kamar ya nemi taimako daga gareshi ko ya nemi agaji daga gareshi wajen kawar da sharri daga ɗansa ko bawansa ko karensa da makamantan haka, Kamar mutum ya neman agajin mutumin da yake a raye ne, yake a wurin kuma yake da iko (na yin agajin), ko wanda ba ya nan amma ta hanya da ake gani kamar rubutu da makamantansa, domin gina gidan sa ko gyaran motar sa ko abinda ya yi kama da haka. Yana daga hakan kuma: Neman agajin mutum da mutanen sa a jihadi da yaƙi da makamantan haka. Yana daga wannan babin kuma, faɗin Allah - Maɗaukakin Sarki - a ƙissar Annabi Musa -tsaira da aminci su tabbata a agare shi -:

﴿...فَاسْتَغَاثَهُ الَّذِي مِنْ شِيعَتِهِ عَلَى الَّذِي مِنْ عَدُوِّهِ...﴾

{Sai wannan da yake daga ƙungiyarsa ya nẽmi ãgajinsa akan wanda yake daga maƙiyansa} [al-Kasas: 15].

Amma neman agaji wurin matattu da aljan da Mala’iku da bishiyoyi da duwatsu, to duka wannan yana cikin babbar shirka, kuma yana cikin irin ayyukan mushirikan farko tare da allolinsu; kamar Uzza da Lata da wasunsu. Haka kuma neman agaji da taimako daga waɗanda ake ƙudircewa cewa waliyyai ne cikin rayayyu, a abinda babu mai iko a kansa sai Allah, kamar warkar da mara lafiya, shiryar da zukata, shiga aljannah da kuma tseratarwa daga wuta da makamantan haka.

Ayoyin da suka gabata da kuma abinda ya zo akan ma’anonisu na ayoyi da hadisai: Dukkan su suna nuni ne akan wajabcin fuskantar da zukata zuwa ga Allah a dukkanin lamurra, da kuma tsarkake ibadah domin Allah Shi kaɗai, domin an halicci bayi ne domin wannan, kuma da shine aka umarce su, - kamar yadda bayani ya gabata a ayoyin -, haka kuma kamar yadda Allah - tsarki ya tabbata a gare Shi - Ya ce:

﴿وَاعْبُدُوا اللَّهَ وَلَا تُشْرِكُوا بِهِ شَيْئًا...﴾

{Kuma ku bauta wa Allah kuma kada ku haɗa wani da Shi} [al-Nisa'a: 36], Da faɗinSa - tsarki ya tabbatar maSa -:

﴿وَمَا أُمِرُوا إِلَّا لِيَعْبُدُوا اللَّهَ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ...﴾

{Kuma ba a umarce su da kome ba fãce bauta wa Allah suna mãsu tsarkake addinin gare Shi} [al-Bayyinah: 5], Da faɗin Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- a cikin Hadisin Mu'az -Allah Ya yarda da shi-: «Haƙƙin Allah a bisa bayi, su bauta maSa kada kuma su haɗa wani da Shi». Bukhari Da Muslim sun haɗu akan ingancinsa, Da faɗin sa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce a cikin hadisin Ibn Mas'ud - Allah Ya yarda dashi -: «Duk wanda ya mutu yana kiran wani kishiya ga Allah, to zai shiga wuta». Bukhari ne ya rawaito shi. A cikin sahihai biyu (Bukhari da Muslim) daga hadisin ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - lokacin da ya tura Mu'az zuwa Yamen, ya ce masa: «Lalle kai zaka je gun wasu mutane ma'abota littafi, to farkon abinda zaka fara kiransu zuwa garesa shine ya kasance; Shaidawa babu wani abin bauta da gaskiya sai Allah». A wani lafazin kuma: «Ka kira su zuwa ga shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma lalle ni Manzon Allah ne». A wata riwayar ta Bukhari: «Sai ya kasance farkon abinda zaka kira su shi ne su kaɗaita Allah». Kuma a Sahih Muslim daga Ɗariƙ ɗan Ashyam al’Ashja’i, - Allah Ya yarda da shi -, cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Duk wanda ya ce: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, ya kuma kafircewa abin da ake bautawa ba Allah ba; dukiyarsa da jininsa sun haramta, kuma hisabinsa yana ga Allah». Hadisai da suka zo da wannan ma’anar suna da yawa.

Kuma wannan TAUHIDIN shi ne asalin Addinin Musulinci kuma shi ne tushen aƙidah, shi ne kuma kan lamari kuma mafi girman farillai, shi ne kuma hikimar halittar mutum da aljan, da hikimar aiko Manzanni baki ɗaya -tsira da aminci su tabbata a gare su -, kamar yadda ayoyi masu nuni akan hakan suka gabata. Daga cikinsu: Faɗinsa - tsarki ya tabbata a gare Shi -:

﴿وَمَا خَلَقْتُ الْجِنَّ وَالْإِنْسَ إِلَّا لِيَعْبُدُونِ56﴾

{Kuma Ban halitta aljannu da mutãne ba sai dõmin su bauta Mini} [al-Zariyat: 56], Daga cikin dalilan haka - kuma -: FaɗinSa - Maɗaukakin Sarki -:

﴿وَلَقَدْ بَعَثْنَا فِي كُلِّ أُمَّةٍ رَسُولًا أَنِ اعْبُدُوا اللَّهَ وَاجْتَنِبُوا الطَّاغُوتَ...﴾

{Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun aika a cikin kõwace al'umma da wani Manzo (ya ce): "Ku bauta wa Allah, kuma ku nĩsanci ɗãgũtu} [al-Nahl: 36], da faɗinSa Allah - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka -:

﴿وَمَا أَرْسَلْنَا مِنْ قَبْلِكَ مِنْ رَسُولٍ إِلَّا نُوحِي إِلَيْهِ أَنَّهُ لَا إِلَهَ إِلَّا أَنَا فَاعْبُدُونِ25﴾

{Kuma ba Mu aiki wani Manzo ba a gabãninka fãce Munã yin wahayi zuwa gare shi, cẽwa "Lalle ne Shi, bãbu abin bautãwa fãce Nĩ, sai ku bauta Mini} [al-Anbiya: 25]. Kuma Allah - girmanSa ya ɗaukaka - Ya ce dangane da (Annabi) Nuhu da Hudu da Salihu da Shu’aibu - tsira da aminci su tabbata a gare su, cewa sun ce wa mutanensu:

﴿...اعْبُدُوا اللَّهَ مَا لَكُمْ مِنْ إِلَهٍ غَيْرُهُ...﴾

{Ku bauta wa Allah! Bã ku da wani abin bautãwa waninSa} [al-A'araf: 59], Wannan kuma ita ce da’awar Annabawa baki ɗaya, kamar yadda ayoyi biyun da suka gabata suka yi nuni akan hakan. Haƙiƙa maƙiya Manzanni sunyi iƙirari akan cewa Manzanni sun umarce su da su kaɗaita Allah da bauta, da yin watsi da duk wasu alloli da ake bautawa ba Allah ba, kamar yadda Allah - girmanSa ya ɗaukaka - Ya ce a cikin ƙissar Adawa, cewa sun faɗawa (Annabi) Hudu - tsira da aminci su tabbata a gare shi -:

﴿...أَجِئْتَنَا لِنَعْبُدَ اللَّهَ وَحْدَهُ وَنَذَرَ مَا كَانَ يَعْبُدُ آبَاؤُنَا...﴾

{Shin, kã zo mana ne dõmin mu bauta wa Allah Shi kaɗai, kuma mu bar abin da ubanninmu suka kasance sunã bauta wa} [al-A'araf: 70], Kuma (Allah) - tsarki ya taabata a gare Shi - Ya ce dangane da Ƙuraishawa a lokacin da Annabimmu Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kira su akan su kaɗaita Allah da bauta, su kuma bar abinda suke bautawa ba Allah ba daga Mala’iku da waliyyai da gumaka da bishiyoyi da wanin haka:

﴿أَجَعَلَ الْآلِهَةَ إِلَهًا وَاحِدًا إِنَّ هَذَا لَشَيْءٌ عُجَابٌ5﴾

{Shin, yã sanya gumãka duka su zama abin bautawa guda? Lalle wannan, haƙĩƙa, abu ne mai ban mãmaki} [Saad: 5], Allah - Mai tsarki da ɗaukaka - Ya ce dangane da su:

﴿إِنَّهُمْ كَانُوا إِذَا قِيلَ لَهُمْ لَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ يَسْتَكْبِرُونَ35 وَيَقُولُونَ أَئِنَّا لَتَارِكُوٓاْ ءَالِهَتِنَا لِشَاعِرٖ مَّجۡنُونِۭ36﴾

{Lalle sũ, sun kasance idan an ce musu: "Bãbu abin bautãwa, fãce Allah," sai su ɗõra girman kai}

Kuma sunã cẽwa, "Shin, mũ lalle mãsu barin gumãkanmu ne, sabõda maganar wani mawãƙi mahaukaci?) [al-Sāffāt: 35-36], Ayoyi masu nuni akan wannan ma’anar suna da yawa.

Daga cikin abinda muka ambata na ayoyi da hadisai, zai bayyana a gareka - Allah Ya datar da ni da kai ga fahimatar addini da kuma basira a haƙƙin Allah Ubangijin talikai - lalle waɗannan addu’o’in da nau’ikan neman agaji -, waɗanda na bayyana su a cikin tambayar ka, duka suna cikin nau’ikan babbar shirka; domin bauta ce ga wanin Allah, kuma neman wani abu ne da babu mai iko akansa in ba Shi ba, cikin matattu da waɗanda ba sa nan, wannan kuwa ta fi shirkar mutanen farko muni, domin mutanen farko suna shirka ne a lokacin wadata, Amma a lokacin tsanani, sai su tsarkake ibada ga Allah; domin su basa sanin cewa Shi - tsarki ya tabbatar maSa - shine mai ikon tsamosu daga tsanani ba wanin sa ba, kamar yadda Maɗaukakin Sarki Ya faɗa a cikin littafinSa mai bayyanawa game da waɗannan mushrikai:

﴿فَإِذَا رَكِبُواْ فِي ٱلۡفُلۡكِ دَعَوُاْ ٱللَّهَ مُخۡلِصِينَ لَهُ ٱلدِّينَ فَلَمَّا نَجَّىٰهُمۡ إِلَى ٱلۡبَرِّ إِذَا هُمۡ يُشۡرِكُونَ65﴾

{To, a lõkacin da suka shiga cikin jirgin ruwa, sun kirãyi Allah sunã mãsu tsarkake addini a gare shi, to, a lõkacin da Ya tsĩrar da su zuwa ga tudun ƙasã, sai gã su sunã shirki} [al-Ankabut: 65], Kuma - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka - Ya faɗa Yana yi musu magana a cikin wata ayar daban:

﴿وَإِذَا مَسَّكُمُ ٱلضُّرُّ فِي ٱلۡبَحۡرِ ضَلَّ مَن تَدۡعُونَ إِلَّآ إِيَّاهُۖ فَلَمَّا نَجَّىٰكُمۡ إِلَى ٱلۡبَرِّ أَعۡرَضۡتُمۡۚ وَكَانَ ٱلۡإِنسَٰنُ كَفُورًا67﴾

{Kuma idan cũta ta shãfe ku, a cikin tẽku, sai wanda kuke kira ya ɓace fãce Shi. To, a lõkacin da Ya tsira da ku zuwa, ga tudu sai kuka bijire. Kuma mutum ya kasance mai yawan butulci} [al-Isra'a: 67].

Idan mai magana ya ce, suwaye waɗannan mushirikan ‘yan baya: Lalle mu ba ma nufin waɗannan suna fa'idantarwa a karan kansu, kuma suna warkar da marasa lafiyarmu a karan kansu, ko suna amfanar damu a karan kansu, ko suna cutar damu a karan kansu ba, kawai abinda muke nufi shine cetansu a wurin Allah - Maɗaukakin Sarki - a cikin hakan?

Amsa: Ita ce, a ce masa: Wannan ai shi ne abin nufin kafiran farko kuma abin nemansu, ba wai suna nufin allolinsu suna halitta ne ko suna azurtawa ba, ko suna amfanarwa ko suna cutarwa ba a karan kansu, domin wannan abinda Allah Ya faɗa a cikin Alƙur'ani game da su yana ɓata shi. Lalle su sun nemi cetonsu ne da alfarmar su da kusantar da su ga Allah kusantarwa ta daraja, kamar yadda Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿وَيَعۡبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ مَا لَا يَضُرُّهُمۡ وَلَا يَنفَعُهُمۡ وَيَقُولُونَ هَٰٓؤُلَآءِ شُفَعَٰٓؤُنَا عِندَ ٱللَّهِ...﴾

{Kuma sunã bautã wa, baicin Allah, abin da bã ya cũtar dasu kuma bã ya amfãninsu, kuma sunã cẽwa: "Waɗannan ne macẽtanmu a wurin Allah} [Yunus: 18], Sai Ya yi musu raddin wannan da faɗinSa:

﴿...قُلۡ أَتُنَبِّـُٔونَ ٱللَّهَ بِمَا لَا يَعۡلَمُ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَلَا فِي ٱلۡأَرۡضِۚ سُبۡحَٰنَهُۥ وَتَعَٰلَىٰ عَمَّا يُشۡرِكُونَ﴾

{Ka ce: "Shin, kunã bai wa Allah lãbãri ne, ga abin da bai sani ba, a cikin sammai ko a cikin ƙasa? TsarkinSa ya tabbata kuma Yã ɗaukaka daga gabin da duk suke yin shirki da Shi"} [Yunus: 18], Sai (Allah) - tsarki ya tabbata a gare Shi - Ya yi bayanin cewa Shi Bai san wani mai ceto a wurinSa ba a cikin sammai da ƙasa ta wannan hanyar da mushirikai suke nufi. Kuma abinda Allah bai san shi ba to wannan abin ai babu shi; domin Shi (Allah) - tsarki ya tabbata a gare Shi - babu abinda yake ɓoyuwa a gare Shi. Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿تَنزِيلُ ٱلۡكِتَٰبِ مِنَ ٱللَّهِ ٱلۡعَزِيزِ ٱلۡحَكِيمِ 1 إِنَّآ أَنزَلۡنَآ إِلَيۡكَ ٱلۡكِتَٰبَ بِٱلۡحَقِّ فَٱعۡبُدِ ٱللَّهَ مُخۡلِصٗا لَّهُ ٱلدِّينَ2 أَلَا لِلَّهِ ٱلدِّينُ ٱلۡخَالِصُۚ وَٱلَّذِينَ ٱتَّخَذُواْ مِن دُونِهِۦٓ أَوۡلِيَآءَ مَا نَعۡبُدُهُمۡ إِلَّا لِيُقَرِّبُونَآ إِلَى ٱللَّهِ زُلۡفَىٰٓ إِنَّ ٱللَّهَ يَحۡكُمُ بَيۡنَهُمۡ فِي مَا هُمۡ فِيهِ يَخۡتَلِفُونَۗ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَهۡدِي مَنۡ هُوَ كَٰذِبٞ كَفَّارٞ3﴾

{Saukar da Littafin daga Allah ne, Mabuwãyi, Mai hikima,

Mun saukar da littafi a gareka da Gaskiya ka bautawa Allah kana mai tsarkake Addini a gare Shi,

To, addini tsarkakakke na Allah ne, kuma waɗanda suka riƙi waɗansu majibinta, bã Shi ba, (sunã cẽwa) "Ba mu bauta musu ba fãce dõmin su kusantar da mu zuwa ga Allah, kusantar daraja." Lalle Allah nã yin hukunci a tsakãninsu ga abin da suka zama sunã sãɓãwa a cikinsa. Lalle Allah ba Ya shiryar da wanda yake mai ƙarya, mai kãfirci} [al-Zumar: 1-3].

Kuma abinda ake nufi da addini anan: Ibada, kuma ita ce: ɗa'a ga Allah da ManzonSa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - kamar yadda ya gabata. - Kuma yana shiga cikin ta: Addu’a da neman agaji da tsoro da ƙauna da yanka da alwashi, kamar kuma yadda sallah take shiga da azumi da wanin haka, cikin abinda Allah da ManzonSa suka yi umarni. Sai (Allah) - tsarki ya tabbata a gare shi - Ya yi bayanin lalle ita ibada, ta sa ce Shi kaɗai, kuma ya wajaba ga bayi su tsarkake ta gare Shi - girmanSa ya ɗaukaka -; domin umarninSa ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi - da tsarkake ibada gare Shi, umarni ne da ya shafi dukkan 'ya'yan wannan al’ummar.

Sannan Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya yi bayani bayan hakan dangane da kafirai, sai Ya ce:

﴿...وَٱلَّذِينَ ٱتَّخَذُواْ مِن دُونِهِۦٓ أَوۡلِيَآءَ مَا نَعۡبُدُهُمۡ إِلَّا لِيُقَرِّبُونَآ إِلَى ٱللَّهِ زُلۡفَىٰٓ...

{Kuma waɗanda suka riƙi waɗansu majibinta, bã Shi ba, (sunã cẽwa) "Ba mu bauta musu ba fãce dõmin su kusantar da mu zuwa ga Allah, kusantar daraja} [al-Zumar: 3]. Sai Allah tsarki ya tabbata a gare shi - Ya yi musu raddi da faɗinSa - tsarki ya tabbata a gare Shi -:

﴿...إِنَّ ٱللَّهَ يَحۡكُمُ بَيۡنَهُمۡ فِي مَا هُمۡ فِيهِ يَخۡتَلِفُونَۗ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَهۡدِي مَنۡ هُوَ كَٰذِبٞ كَفَّارٞ﴾

{Lalle Allah nã yin hukunci a tsakãninsu ga abin da suka zama sunã sãɓãwa a cikinsa. Lalle Allah ba Ya shiryar da wanda yake mai ƙarya, mai kãfirci} [al-Zumar: 3], Sai Allah - tsarki ya tabbata a gare shi - Ya bayar da labari a cikin wannan ayar mai daraja: Cewa kafirai, ba su bautawa waliyyai ba koma bayan Allah sai domin su kusantar da su zuwa ga Allah kusantar daraja, wannan kuwa ita ce manufar na da, da na yanzu. Haƙiƙa Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ɓata hakan da faɗinSa:

﴿...إِنَّ ٱللَّهَ يَحۡكُمُ بَيۡنَهُمۡ فِي مَا هُمۡ فِيهِ يَخۡتَلِفُونَۗ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَهۡدِي مَنۡ هُوَ كَٰذِبٞ كَفَّارٞ﴾

{Lalle Allah nã yin hukunci a tsakãninsu ga abin da suka zama sunã sãɓãwa a cikinsa. Lalle Allah ba Ya shiryar da wanda yake mai ƙarya, mai kãfirci} [al-Zumar: 3], Sai Allah - tsarki ya tabbata a gare Shi - Ya bayyana ƙaryar su a rayawar su cewa, allolinsu zasu kusantar da su ga Allah kusantar daraja, kuma Ya kafirta su akan yadda suka karkatar musu da ibada, da wannan ne duk mai mafi ƙarancin fahimta zai san cewa kafiran farko kafircin su ya kasance ne ta ɗaukar Annabawa da waliyyai da itatuwa da duwatsu da wanin haka cikin halittu; dan nema masu ceto tsakaninsu da Allah, Da kuma ƙudircewarsu cewa suna biya musu buƙatunsu ba tare da izininSa da yardarSa - Maɗaukakin Sarki - ba, kamar yadda wazirai suke neman ceto a wurin shugabanni. Sai suka ƙiyasta Allah - Maɗaukakin sarki - da sarakuna da shuwagabanni. Suka kuma ce: Kamar yadda wanda yake da buƙata a wurin sarki da shugaba yake neman ceto izuwa gare shi ta hanyar keɓantattun mutanen sa da mataimakan sa, sai su ce to muma muna neman kusanci ga Allah ne da bautawa AnnabawanSa da WaliyyanSa, wannan kuwa yanan cikin mafi girman ɓarna; domin Shi (Allah) - tsarki ya tabbata a gare Shi - babu abinda ya yi kama da Shi, ba kuma a yin ƙiyasinSa da halittarSa, kuma babu wanda zai yi ceto a wurinSa sai da izinin Sa a ceton, kuma ba Ya yin izini sai ga masu Tauhidi, kuma shi tsarki ya tabbata a gare Shi - Mai iko ne akan komai, kuma Masani ne akan komai, Shine kuma mafi jinƙan masu jinƙai, ba Ya tsoron kowa babu mai razana shi; domin Shi (Allah) - tsarki ya tabbata a gare Shi -, Shi ne Mai iko akan bayinSa, kuma Shi ne Mai juya su kamar yadda Yake so. Saɓanin sarakuna da shuwagabanni, domin su ba su da iko akan komai, saboda haka suke buƙatar waɗanda zasu taimaka musu akan abinda suka kasa; cikin mataimakansu, da keɓantattun mutanensu da jami’an tsaron su, kamar yadda suke buƙatar isar musu da buƙatun wanda ba su san buƙatarsa ba, sai su buƙaci wanda zai tausaya musu, ya kwantar musu da hankali cikin mataimakansu da keɓantattun mutanensu, Amma Ubangiji - Mai girma da ɗaukaka -, Shi Mawadaci ne daga dukkan halittarSa, Shi ne Mafi jin kai a gare su fiye da iyayensu, Shi ne Mai adalci, Yana sanya ayoyi a wuraren da suka dace, bisa ga hikimarSa da iliminSa da ikonSa' Don haka, ba ya halatta a ƙiyasta Shi da halittarSa ta kowacce irin fuska. Saboda wannan ne (Allah) - tsarki ya tabbata a gare Shi - Ya fayyace a cikin littafinSa: Lalle mushirikai sun tabbatar da cewa shi ne Mahalicci Mai azurtawa Mai jujjuya lamurra, kuma Shi ne wanda Yake amsa addu’ar mabuƙaci, kuma Yake yaye damuwa, Ya ke rayawa kuma Yake kashewa, da wanin hakan daga ayyukanSa - tsarki ya tabbata a gare Shi -. Haƙiƙa husuma ta kasance tsakanin mushirikai da Manzanni akan tsarkake ibada domin Allah shi kaɗai, kamar yadda Allah -tsarki ya tabbata a gare Shi - Ya ce:

﴿وَلَئِن سَأَلۡتَهُم مَّنۡ خَلَقَهُمۡ لَيَقُولُنَّ ٱللَّهُ...﴾

{Kuma lalle idan ka tambaye su: "Wãne ne ya halitta su?" Lalle ne zã su ce Allah ne} [al-Zukhruf: 87], Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿قُلۡ مَن يَرۡزُقُكُم مِّنَ ٱلسَّمَآءِ وَٱلۡأَرۡضِ أَمَّن يَمۡلِكُ ٱلسَّمۡعَ وَٱلۡأَبۡصَٰرَ وَمَن يُخۡرِجُ ٱلۡحَيَّ مِنَ ٱلۡمَيِّتِ وَيُخۡرِجُ ٱلۡمَيِّتَ مِنَ ٱلۡحَيِّ وَمَن يُدَبِّرُ ٱلۡأَمۡرَۚ فَسَيَقُولُونَ ٱللَّهُۚ فَقُلۡ أَفَلَا تَتَّقُونَ31﴾

{Ka ce: "Wãne ne Yake azurtã ku daga sama da ƙasa? Shin kõ kuma Wãne ne Yake mallakar jĩ da ganĩ, kuma Wãne ne Yake fitar da mai rai daga mamaci, kuma Ya fitar da mamaci daga mai rai, Kuma Wãne ne Yake shirya al'amari?" To, zã su ce: "Allah ne." To, ka ce: "Shin fa, bã zã ku yi taƙawa ba?"} [Yunus: 31], Kuma ayoyi da suka zo da wannan ma’anar suna da yawa.

Haƙiƙa ya gabata: Ambton ayoyi masu nuni akan rikici tsakanin Annabawa da al’ummu abin sani kawai ya kasance ne akan tsarkake ibada ga Allah Shi kaɗai, kamar fadinSa Allah - tsarki ya tabbatar maSa -:

﴿وَلَقَدۡ بَعَثۡنَا فِي كُلِّ أُمَّةٖ رَّسُولًا أَنِ ٱعۡبُدُواْ ٱللَّهَ وَٱجۡتَنِبُواْ ٱلطَّٰغُوتَ...﴾

{Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun aika a cikin kõwace al'umma da wani Manzo (ya ce): "Ku bauta wa Allah, kuma ku nĩsanci ɗãgũtu} [al-Nahl: 36], Da kuma abinda ya zo a cikin ma’anarta na ayoyi. Kuma Allah - tsarki ya tabbata a gare Shi - Yayi bayanin sha'anin ceto a wurare masu yawa cikin littafinSa mai daraja, sai (Allah) - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿َ...مَن ذَا ٱلَّذِي يَشۡفَعُ عِندَهُۥٓ إِلَّا بِإِذۡنِهِ...﴾

{Wane ne wanda yake yin cẽto a wurinSa, fãce da izninSa?} [al-Baƙara: 255], Kuma (Allah) - Mai girma da ɗaukaka - Ya ce-:

﴿وَكَم مِّن مَّلَكٖ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ لَا تُغۡنِي شَفَٰعَتُهُمۡ شَيۡـًٔا إِلَّا مِنۢ بَعۡدِ أَن يَأۡذَنَ ٱللَّهُ لِمَن يَشَآءُ وَيَرۡضَىٰٓ26﴾

{Akwai malã'iku da yawa a cikin sammai cẽtonsu bã ya wadãtar da kõme fãce bãyan Allah Yã yi izni (da shi) ga wanda Yake so, kuma Yake yarda.} [al-Najm: 26].

Ya kuma ce a siffar Mala’iku:

﴿...وَلَا يَشۡفَعُونَ إِلَّا لِمَنِ ٱرۡتَضَىٰ وَهُم مِّنۡ خَشۡيَتِهِۦ مُشۡفِقُونَ﴾

{Kuma sũmasu sauna ne sabõda tsõron Sa} [al-Anbiya'a: 28].

Ya kuma bada labari - girmanSa ya ɗaukaka -, cewa Shi bai yardarwa bayinSa kafirci ba, abinda kawai Yake yarda da shi daga gare su shine godiya, godiyar kuma ita ce kaɗaita Shi da ibada da kuma yin aiki da biyayyar Sa, sai Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿إِن تَكۡفُرُواْ فَإِنَّ ٱللَّهَ غَنِيٌّ عَنكُمۡۖ وَلَا يَرۡضَىٰ لِعِبَادِهِ ٱلۡكُفۡرَۖ وَإِن تَشۡكُرُواْ يَرۡضَهُ لَكُمۡ...﴾

{Idan kun kãfirta to, lalle Allah Wadãtacce ne daga barinku, kuma bã Shi yarda da kãfirci ga bãyin Sa, kuma idan kun gõde, Zai yarda da ita (gõdiyar)} [al-Zumar: 7].

Kuma Bukhari ya ruwaito a cikin a sahihinsa daga Abu Hurairah - Allah Ya yarda da shi -, cewa ya ce: Ya Ma’aikin Allah! waye mafi rabauta da ceton ka a cikin mutane? (sai) ya ce: «Wanda ya ce: (Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah) yana mai ikhlasi daga zuciyarsa». Ko ya ce: «Daga ransa».

Kuma ya zo a cikin sahih (na Bukhari) daga Anas - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - cewa ya ce: «Kowane Annabi yana da addu'ar da aka amsa masa, sai kowanne Annabi ya gaggauta addu'ar sa, amma na ɓoye addu'a ta ta zama ceto ga al'umma ta ranar alƙiyama, kuma za ta samu - in sha Allah - duk wanda ya mutu daga al'umma ta ba tare da ya shirkanta komai da Allah ba». Hadisai da suka zo da wannan ma’anar suna da yawa.

Gabaɗayan abinda muka anbata na ayoyi da hadisai suna nuni ne akan ita ibada haƙƙin Allah ce Shi kaɗai, kuma ba ya halatta a karkatar da wani abu nata ga wanin Allah, ba ga Annabawa ba ko ga waninsu, kuma shi ceto mallakar Allah ne, kamar yadda Allah - tsarki ya tabbata a gare Shi - Ya faɗa:

﴿قُل لِّلَّهِ ٱلشَّفَٰعَةُ جَمِيعٗا...﴾

{Ka ce: "Cẽto gabã ɗaya ga Allah yake} [al-Zumar: 44] Babu wani da ya cancanci ceto sai bayan izinin Sa ga wanda zai yi ceton, da kuma yardarSa akan wanda za’a ceta, Shi kuma - tsarki ya tabbata a gare Shi - ba Ya yarda sai da Tauhidi, - kamar yadda ya gabata -. Gini akan hakan, lalle su mushirikai ba su da kaso a ceto, kuma haƙiƙa Allah Ya fayyace hakan a faɗinSa -Maɗaukakin Sarki -:

﴿فَمَا تَنفَعُهُمۡ شَفَٰعَةُ ٱلشَّٰفِعِينَ 48﴾

{Sabõda haka cẽton mãsu cẽto bã zai amfãne su ba} [al-Mudaththir: 48], Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿...مَا لِلظَّٰلِمِينَ مِنۡ حَمِيمٖ وَلَا شَفِيعٖ يُطَاعُ﴾

{Bãbu wani masõyi ga azzãlumai, kuma bãbu wani mai cẽto da zã a yi wa dã'a (ga cẽtonsu)} [Gafir: 18].

Kuma sananne ne cewa idan aka ambaci zalinci a sake, to shirka da Allah ake nufi, kamar yadda Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya faɗa:

﴿...وَٱلۡكَٰفِرُونَ هُمُ ٱلظَّٰلِمُونَ﴾

{Kuma kãfirai sũ ne azzãlumai} [al-Baƙara: 254], Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿...إِنَّ ٱلشِّرۡكَ لَظُلۡمٌ عَظِيمٞ﴾

{Lalle shirki wani zãlunci ne mai girma} [Luƙman: 13].

Amma abinda ka ambata a cikin tambayar: Daga zancen wasu daga cikin Sufaye a cikin masallatai da waninsu: Ya Allah Ka yi salati ga wanda Ka sanya shi sababi na yayewar sirrikan Ka na Jabruti, kuma yayewa ga hasken Ka Rahamaniyya, sai ya kasance a madadin halartar Rabbaniyya, kuma halifan sirrikan Ka na zati…. izuwa ƙarshe.

Amsa: a ce: Lalle wannan maganar da ire irenta suna cikin zubin ɗorawa kai da shisshigi; wanda Annabinmu - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya hana; a abinda Muslim ya ruwaito a Sahih daga Abdullah ɗan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi -, Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Masu tsattsauran ra'ayi sun halaka, ya faɗe ta sau uku.

Imam al-Khaɗɗabi - Allah Ya yi masa rahama - ya ce: Mai shisshigi: Mai kutsawa cikin abu, mai ɗorawa kai abu, mai ƙwaƙulo abun; akan tsarin ma'abota ilimin Kalam, masu shiga cikin abinda ba zai amfane su ba, masu kutsawa inda hakalinsu bai kaiba.

Abu al-Sa'adat Ibn al-Athir ya ce: Su ne masu zurfafawa masu guluwwi cikin magana, masu magana daga ƙololuwar maƙogwaron su, an samo shi ne daga kalmar 'Nuɗ'u' wanda shine rami mafi ɗaukaka a baki, sannan aka yi amfani da shi ga duk mai zurfafawa a magana da aiki.

Da kuma abinda waɗannan malaman biyu daga malaman Lugga suka ambata, zai bayyana a gareka da duk wanda yake da mafi ƙarancin hankali, lallai wannan tsari na salati da sallama ga Annabinmu kuma shugabanmu, Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cikin jumallar ɗorawa kai da shisshigi wanda aka hana. Abinda aka shar’antawa musulmi a wannan batu shi ne, ya kardadi kaifiyya tabbatacciya daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, a siffar yin salati da sallama a gare shi, wannan kuwa ya wadatar daga waninsa.

Daga cikin hakan: Abinda Bukhari da Muslim suka ruwaito a Sahihaini (Sahih al-Bukhari da Sahih Muslim) daga Ka’ab bn Ujrah - Allah Ya yarda da shi -, cewa sahabbai - Allah Ya yarda da su - sun ce: Ya Ma’aikin Allah, Allah Ya umarce mu mu yi maka salati; to yaya za mu yi maka salatin? Sai ya ce: «Ku ce:Ya Allah Kayi salati ga (Annabi) Muhammad da alayen (Annabi) Muhammad, kamar yanda Kayi salati ga (Annabi) Ibrahim da alayen (Annabi) Ibrahim, kuma Kayi albarka ga (Annabi) Muhammad da alayen (Annabi) Muhammad kamar yanda Kayi albarka ga (Annabi) Ibrahim da alayen (Annabi) Ibrahim, lallai Kai Abin yabo ne Mai girma».

Ya zo a cikin Sahihaini, daga Abu Humaid al-Sa’idi - Allah Ya yarda da shi -: Cewa sun ce: Ya Manzon Allah! Yaya za mu yi maka salati? (Sai) ya ce: «Ku ce: Ya Allah Kayi salati ga (Annabi) Muhammad da matayen sa da zuri'ar sa, kamar yanda Kayi salati ga alayen (Annabi) Ibrahim, kuma Kayi albarka ga (Annabi) Muhammad da matayen sa da zuri'ar sa, kamar yanda Kayi albarka ga alayen (Annabi) Ibrahim, lallai Kai Abin yabo ne Mai girma».

A cikin Sahih Muslim daga Abu Mas’ud al-Ansari, - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Bashir bn Sa’ad ya ce: Ya Ma’aikin Allah! Allah Ya umarce mu mu yi salati a gareka, to yaya za mu yi maka salatin? Sai ya yi shiru, sannan sai ya ce: «Ku ce: Ya Allah Ka yi salati ga (Annabi) Muhammad da alayen (Annabi) Muhammad; kamar yanda Ka yi salati ga alayen (Annabi) Ibrahim, kuma Ka yi albarka ga (Annabi) Muhammad, da alayen (Annabi) Muhammad; kamar yanda Ka yi albarka ga alayen (Annabi) Ibrahim. Lalle Kai abin yabo ne, Mai girma. Sai kuma sallama kamar yadda kuka sani».

To waɗannan lafuza da makamantansu da wasunsu, - daga abinda ya tabbata daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, su ne waɗanda suka kamata mutum musulmi ya yi amfani da su a salatinsa da sallmarsa ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, domin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, shi ne mafi sanin mutane da abinda ya cancanta a yi anfani da shi a haƙƙin sa, kamar kuma yanda yake mafi sanin mutane da abinda ya cancanta a yi amfani da shi na lafuza a haƙƙin Ubangijinsa da lafuza.

Amma lafuzan da aka ƙera da kuma sabbin lafuzai, da lafuzan da ke iya ɗaukar ma'ana mara inganci; kamar lafuzan da aka ambata a cikin tambaya, to bai kamata a yi amfani da su ba; saboda akwai sarƙaƙiya a cikin su, da kuma kasancewar ana iya fassara su da ma'anoni ɓatattu, tare da kasancewar su saɓanin lafuzan da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya zaɓa, kuma ya shiryar da al'ummar sa izuwa gare su. Shi ne mafi sanin halitta kuma mafi nasihar su kuma mafi nisantar su daga sarƙaƙiya, - mafificin salati da aminci su tabbata a gare shi - daga Ubangijin sa.

Wannan kenan, ina fatan abinda muka ambata na dalilai a bayanin haƙiƙanin Tauhidi, da haƙiƙanin shirka, da kuma bambancin abinda mushirikan farko suke akai da mushirikai na baya a wannan babin, da bayanin kaifiyyar salati da aka shar’anta ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, ya wadatar kuma ya gamsar da mai neman gaskiya. Amma wanda ba shi da kwaɗayin sanin gaskiya; wannan mai bin son ransa ne, Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿فَإِن لَّمۡ يَسۡتَجِيبُواْ لَكَ فَٱعۡلَمۡ أَنَّمَا يَتَّبِعُونَ أَهۡوَآءَهُمۡۚ وَمَنۡ أَضَلُّ مِمَّنِ ٱتَّبَعَ هَوَىٰهُ بِغَيۡرِ هُدٗى مِّنَ ٱللَّهِۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَهۡدِي ٱلۡقَوۡمَ ٱلظَّٰلِمِينَ50﴾

{To, idan ba su karɓa maka ba to sai ka sani sunã bin son zuciyarsu ne kawai, kuma wãne ne mafi ɓata daga wanda ya bi son zuciyarsa, bã tãre da wata shiriya daga Allah ba? Lalle ne, Allah bã ya shiryar da mutãne azzãlumai} [al-Ƙasas: 50].

Sai Allah - tsarki ya tabbta a gare Shi -, Ya yi bayani a cikin wannan ayar mai daraja: Cewa mutane dangane da abinda Allah Ya aiko Annabinsa Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - na shiriya da addinin gaskiya, sun kasu kashi biyu:

Na farkonsu: Mai amsa wa Allah da ManzonSa ne.

Na biyu: Mai bin son zuciyarsa; sannan (Allah) - tsarki ya tabbata a gare Shi - Ya bada labarin cewa babu ɓatacce sama da wanda ya bi son zuciyar sa, ba tare da wata shiriya daga Allah ba.

Don haka muna roƙon Allah - girmanSa ya ɗaukaka - kiyayewa daga bin son zuciya, Ya kuma sanya mu da ku da sauran ‘yan uwanmu cikin waɗanda suka amsawa Allah da ManzonSa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, kuma masu girmama shari’arSa, kuma masu tsawatarwa daga duk abinda ya saɓawa shari’arSa na bidi’a da son zuciya. Lalle Allah Mai kyauta ne kuma Mai karamci.

Allah Ya yi salati ga bawanSa kuma ManzonSa; Annabimmu Muhammad da alayensa da da sahabbansa da masu binsa da kyautatawa har izuwa ranar sakamako.

 

***

 


بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ

SAƘO NA BIYAR:

Hukuncin taron maulidin Annabi da sauran mauludai

Godiya ta tabbata ga Allah, tsira da amincin Allah su tabbata ga Manzon Allah, da alayen sa da sahabban sa da waɗanda suka shiryu da shiriyar sa.

Bayan haka: An sha tambayar mutane da dama game da hukuncin taron bikin haihuwar Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi-, da tsayuwa saboda shi a lokacin yin hakan, da yi masa sallama, da sauran abubuwan da ake yi a maulidi.

Amsa sai a ce: Ba ya halatta yin bikin mauludin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, haka ma na wanin sa; domin hakan bidi’a ne wacce aka ƙirƙira a cikin addini; domin Manzo - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - bai yi ba, haka halifofin sa shiryayyu, haka sauran sahabbai - Allah Ya yarda da su -, haka waɗanda suka bi su da kyautatawa a mafifitan ƙarni, alhali su suka fi kowa sanin sunnah, su suka fi cikar son Ma’aikin Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, kuma suka fi bin shari’ar sa akan waɗanda suka zo a bayan su, Kuma haƙiƙa Allah - Mai tsarki da ɗaukaka - Ya faɗa a cikin littafin Sa mabayyani:

﴿...وَمَآ ءَاتَىٰكُمُ ٱلرَّسُولُ فَخُذُوهُ وَمَا نَهَىٰكُمۡ عَنۡهُ فَٱنتَهُواْ...﴾

{Abinda manzo ya zo muku (da shi) to ku riƙe shi abinda kuma ya haneku to ku hanu}

[al-Hashr: 7]. Kuma Allah - Maɗaukaki - Ya ce:

﴿...فَلۡيَحۡذَرِ ٱلَّذِينَ يُخَالِفُونَ عَنۡ أَمۡرِهِۦٓ أَن تُصِيبَهُمۡ فِتۡنَةٌ أَوۡ يُصِيبَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٌ﴾

{To waɗanda suke saɓa umarninsa su kiyayi kansu kada musiba ko fitina ta sauka a kansu ko kuma azaba mai raɗaɗi ta same su} [al-Nnur: 63], Kuma - tsarki ya tabbatar maSa - Ya ce:

﴿لَّقَدۡ كَانَ لَكُمۡ فِي رَسُولِ ٱللَّهِ أُسۡوَةٌ حَسَنَةٞ لِّمَن كَانَ يَرۡجُواْ ٱللَّهَ وَٱلۡيَوۡمَ ٱلۡأٓخِرَ وَذَكَرَ ٱللَّهَ كَثِيرٗا21﴾

{Lalle, abin kõyi mai kyau ya kasance gare ku daga Manzon Allah, ga wanda ya kasanee yanã fãtan rahamar Allah da Rãnar Lãhira, kuma ya ambaci Allah da yawa} [al-Ahzab: 21], Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿وَٱلسَّٰبِقُونَ ٱلۡأَوَّلُونَ مِنَ ٱلۡمُهَٰجِرِينَ وَٱلۡأَنصَارِ وَٱلَّذِينَ ٱتَّبَعُوهُم بِإِحۡسَٰنٖ رَّضِيَ ٱللَّهُ عَنۡهُمۡ وَرَضُواْ عَنۡهُ وَأَعَدَّ لَهُمۡ جَنَّٰتٖ تَجۡرِي تَحۡتَهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَآ أَبَدٗاۚ ذَٰلِكَ ٱلۡفَوۡزُ ٱلۡعَظِيمُ100﴾

{Kuma mãsu tsẽrẽwa na farko daga Muhãjirina da Ansar da waɗanda suka bi su da kyautatãwa, Allah Ya yarda daga gare su su kuma sun yarda daga gare Shi, kuma Ya yi mãsu tattalin gidãjen Aljanna; ƙõramu sunã gudãna a ƙarƙashinsu, suna madawwamã a cikinsu har abada. Wancan ne babban rabo mai girma} [al-Taubah: 100], Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿...ٱلۡيَوۡمَ أَكۡمَلۡتُ لَكُمۡ دِينَكُمۡ وَأَتۡمَمۡتُ عَلَيۡكُمۡ نِعۡمَتِي وَرَضِيتُ لَكُمُ ٱلۡإِسۡلَٰمَ دِينٗا...﴾

{Kuma yaune Na cika muku addininku, kuma Na cika muku ni'imaTa kuma Na yarje muku musulunci a matsayin addini} [al-Ma'ida: 3]. Kuma ayoyi da suka zo da wannan ma’anar suna da yawa. Kuma haƙiƙa ya tabbata daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Duk wanda ya farar da wani abu a cikin wannan Addinin namu wanda ba ya ciki, to shi abun mayarwa ne». Wato: Za’a mayar masa, Kuma ya faɗa a wani hadisin daban: «Na hore ku da bin sunnata da sunnar halifofi shiryayyu masu shiryarwa a baya na, ku yi riƙo da ita, kuma ku riƙeta da fiƙoƙinku, kuma na hane ku da fararrun abubuwa; saboda kowane fararren abu bidi'a ne; kuma kowace bidi'a ɓata ce». To a cikin waɗannan hadisai biyu, akwai tsawatarwa mai tsanani akan farar da bidi’a, da kuma aiki da ita.

Kuma farar da ire-iren waɗannan mauludan, ana fahimta daga gare shi cewa, Allah - tsarki ya tabbata a gare Shi - bai cika wa wannan al’ummar Addini ba, kuma Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - bai isarwa al’umma abinda ya kamata ta aikata ba, har sai da waɗannan ’yan baya bayan suka zo, sai suka ƙirƙira a shari'ar Allah abinda bai bada izini ba; suna masu riya cewa hakan yana cikin abinda zai kusantar da su ga Allah. Kuma wannan babu shakka yana da babban haɗari, kuma ƙalubalantar Allah ne - tsarki ya tabbatar maSa - da ManzonSa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, kuma Allah - tsarki ya tabbatar maSa - Ya cika addini ga bayinSa, kuma Ya cika ni’imarSa a gare su, kuma Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya isar da isarwa bayyananniya, bai bar wata hanya da zata kai zuwa Aljanna, kuma ta nisantar daga wuta ba face ya bayyana ta ga al’umma, kamar yadda aka tabbatar a cikin hadisi sahihi daga Abdullahi ɗan Amru - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Allah bai aiko wani Annabi ba sai ya zama wajibi a gare shi ya nuna wa al'ummarsa mafi alherin abinda ya sani a gare su, kuma ya gargaɗe su daga mafi sharrin abinda ya sani a gare su». Muslim ne ya rawaito shi a cikin Sahih ɗin sa.

Sanannen abu ne, lalle Annabimmu - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, shi ne mafificin Annabawa kuma cika makinsu, kuma mafi cikarsu a isarwa da nasiha. Da bikin maulidai yana cikin Addinin da Allah tsarki ya tabbata a gare Shi - Ya yarda da shi da ManzonSa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya bayyana shi ga al’umma ko ya aikata shi a rayuwarsa ko sahabbansa sun aikata shi a bayansa, - Allah Ya yarda da su -.To a yayin da babu abinda ya faru cikin waɗannan, sai aka sani cewa shi ba ya cikin Musulinci ta ko’ina, bari dai, yana cikin fararrun abubuwan da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya tsawatar da al’ummarsa a kansu, kamar yadda ambaton hakan ya gabata a cikin hadisai. Ayoyi da hadisai a wannan babin suna da yawa.

Kuma haƙiƙa jama’a masu yawa cikin malamai sun bayyana inkarinsu ga maulidai da kuma tsawatarwa akan su; domin yin aiki da dalilan da aka ambata da wasunsu. Sai wasu cikin ‘yan baya bayan nan suka saɓa (akan hakan): Sai suka halasta shi idan bai ƙunshi abubuwan ƙi ba; kamar wuce iyaka a (sha'anin) Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, kamar kuma haɗuwar mata da maza, da amfani da kayan kiɗa, da wasunsu, na abinda shari’a tsarkakakkiya ba ta yarda da shi ba, suka yi zaton hakan yana cikin bidi’a kyakkyawa.

Ka'idar shari'a ita ce: Mayar da abinda mutane suka yi saɓani a kai zuwa ga Littafin Allah da sunnar ManzonSa annabi Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - kamar yadda Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya ce:

﴿يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ أَطِيعُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُواْ ٱلرَّسُولَ وَأُوْلِي ٱلۡأَمۡرِ مِنكُمۡۖ فَإِن تَنَٰزَعۡتُمۡ فِي شَيۡءٖ فَرُدُّوهُ إِلَى ٱللَّهِ وَٱلرَّسُولِ إِن كُنتُمۡ تُؤۡمِنُونَ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِۚ ذَٰلِكَ خَيۡرٞ وَأَحۡسَنُ تَأۡوِيلًا59﴾

{Yã kũ waɗanda suka yiĩmãni! Ku yi ɗã'a ga Allah, kuma ku yi ɗã'a ga ManzonSa, da ma'abũta al'amari daga cikinku. Idan kun yi jãyayya a cikin wani abu, to ku mayar da shi zuwa ga Allah da ManzonSa idan kun kasance kunã ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira. wannan ne mafi alhẽri, kuma mafi kyau ga fassara} [al-Nisa'a: 59], Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿وَمَا ٱخۡتَلَفۡتُمۡ فِيهِ مِن شَيۡءٖ فَحُكۡمُهُۥٓ إِلَى ٱللَّهِ ...﴾

{Kuma abin da kuka yi saɓani a cikinsa na daga wani abu to hukuncinsa zuwa ga Allah yake} [al-Shura: 10].

Haƙiƙa mun maida wannan mas’alar: Shi ne: (Hujjar) bikin maulidai zuwa littafin Allah - tsarki ya tabbata a gare Shi - , sai muka samu yana umartarmu da bin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a abinda ya zo da shi, yana kuma hanamu aikata abinda ya hana, yana kuma ba mu labarin cewa Allah - tsarki ya tabbata a gare Shi - haƙiƙa Ya cikawa wannan al’umma Addininta, wannan bikin kuma ba ya cikin abinda Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya zo da shi, sai ya zama ba ya cikin Addinin da Allah Ya cika mana, kuma Ya umarce mu da bin Manzo a cikinsa.

Haƙiƙa mun maida wannan - shima -: Zuwa ga Sunnar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -; ba mu samu ya aikata shi ba a cikinta, kuma bai yi umarni da shi ba, kuma sahabbansa ba su aikata shi ba - Allah Ya yarda da su-; sai muka sani da hakan cewa hakan ba ya cikin Addini, bari dai, yana cikin bidi’a ƙagaggiya, kuma yana cikin koyi da ma’abota littafi Yahudu da Nasara a bukukuwansu.

Da wannan ne zai bayyana ga dukkan wanda yake da mafi ƙarancin basira da kwaɗayin gaskiya da kuwala wurin nemanta: Lalle taron mauludai ba ya cikin Addinin Musulinci, bari dai yana cikin bidi’o’i da aka ƙago, waɗanda Allah - tsarki ya tabbata a gare Shi - da ManzonSa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - suka yi umarni da barinsu, suka kuma tsawatar daga garesu. Kuma ba ya kamata ga mai hankali ya ruɗu da yawan masu aikata shi cikin mutane a sassan duniya, domin ita gaskiya ba’a saninta da yawan masu yinta, kaɗai ana sanin gaskiya ne da dalilai na shari’a, kamar yadda Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya faɗa akan Yahudu da Nasara:

﴿وَقَالُواْ لَن يَدۡخُلَ ٱلۡجَنَّةَ إِلَّا مَن كَانَ هُودًا أَوۡ نَصَٰرَىٰۗ تِلۡكَ أَمَانِيُّهُمۡۗ قُلۡ هَاتُواْ بُرۡهَٰنَكُمۡ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ111﴾

{Kuma suka ce: "Bãbu mai shiga Aljanna fãce waɗanda suka zama Yahũdu ko Nasãra." Waɗancan tãtsũniyõyinsu ne. Ka ce: "Ku kãwo dalilinku idan kun kasance mãsu gaskiya} [al-Baƙara: 111], Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿وَإِنْ تُطِعْ أَكْثَرَ مَنْ فِي الْأَرْضِ يُضِلُّوكَ عَنْ سَبِيلِ اللَّهِ...﴾

{Kuma idan ka bi mafiya yawan waɗanda suke a cikin ƙasa da ɗã'a sunã ɓatar da kai daga hanyar Allah} [al-An'am: 116],

Sannan lallai mafi yawancin waɗannan bukukwawa na maulidai tare da kasancewarsu bidi’a ne, suna ƙunshe ma da munanan ayyuka na daban; kamar cakuɗuwar mata da maza, amfani da waƙoƙi da kayan kaɗe-kaɗe, da shan abubuwa masu sa maye da masu bugarwa da wanin haka na abubuwan sharri. Kuma wani abu yakan faru wanda ya fi haka muni, itace babbar shirka, wannan kuwa, ta hanyar wuce iyaka a sha'anin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, ko waninsa cikin waliyyai da roƙonsa da neman agajinsa da neman madadi daga gare shi, da ƙudurce cewa ya san gaibu , da wanin haka cikin abubuwan da suke na kafirci waɗanda da yawa cikin mutane suke ta’ammuli da su a lokacin bikin da suke yi na maulidin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da waninsa cikin waɗanda ake cewa waliyyai. Haƙiƙa ya inganta daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Kashedinku da wuce iyaka a cikin addini, don abinda ya halakar da waɗanda suke kafinku shi ne wuce iyaka a cikin addini» Kuma - tsira da aminci su tabbata a gare shi - ya ce: «Kada ku wuce gona da iri wajen yabona kamar yadda Nasara suka wuce gona da iri ga Ɗan Maryam, ni kawai bawa ne, to ku ce Bawan Allah ne kuma ManzonSa ne». Bukhari ya fitar da shi a cikin Sahihinsa, daga hadisin Umar - Allah Ya yarda da shi -.

Daga cikin abubuwan mamaki da al'ajabi: Yadda mutane da dama ke himma da ƙoƙari wajen halartar waɗannan bukukuwan na bidi'a, suna kare su, kuma suna kaucewa abin da Allah Ya wajabta musu na halartar Juma'a da jam'i, ba su ɗauki hakan wani abu ba, kuma ba su ga cewa sun aikata wani babban mummunan abu ba, babu shakka wannan yana daga cikin raunin imani, da ƙarancin basira, da yawan abin da ya rufe zukata daga nau'o'in zunubai da saɓo, muna roƙon Allah Ya bamu lafiya da sauran musulmai.

Yana daga hakan: Lalle wasu daga cikinsu suna zaton cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana zuwa wurin da ake yin maulidi; saboda haka ne suke miƙewa don nuna soyayya da kuma marhaban. Wannan kuwa yana daga cikin mafi girman ɓarna da mafi munin jahilci, domin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, ba ya fitowa daga ƙabarinsa kafin ranar alƙiyama, ba ya haɗuwa da kowa cikin mutane kuma ba ya zuwa taronsu, bari dai yana nan a ƙabarinsa har zuwa ranar alƙiyama, kuma ransa yana mafi ɗaukakar Illiyyun a wurin Ubangijinsa a gida na karamci kamar yadda Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya faɗa:

﴿ثُمَّ إِنَّكُمْ بَعْدَ ذَلِكَ لَمَيِّتُونَ15 ثُمَّ إِنَّكُمْ يَوْمَ الْقِيَامَةِ تُبْعَثُونَ16﴾

{Sa'an nan kuma ku, bãyan wannan, lalle ne masu mutuwa ne.

Sannan kuma ku a Ranar Alƙiyama za’a tayar da ku} [al-Mua'Minun: 15 - 16].

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Ni ne farkon wanda ƙabari zai tsagewa ranar Alƙiyama, kuma farkon mai ceto, kuma farkon wanda za'a bawa ceto». Mafificin Salati da aminci daga Ubangijinsa su tabbata a gareshi.

To waɗannan ayoyi guda biyu masu girma da hadisin maɗaukaki, da kuma abinda ya zo akan ma’anoninsu na ayoyi da hadisai: Dukkansu suna nuni ne akan lalle Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da waninsa cikin waɗanda suka rasu, kaɗai zasu fito ne daga ƙaburburansu ne a ranar alƙiyama, wannan kuwa lamari ne da aka yi ijima’i a kansa a tsakanin malamai musulmai; babu wata jayayya a tsakaninsu a cikinsa. Don haka yana kamata ga kowanne musulmi ya faɗaka da waɗannan abubuwan, kuma ya kiyayi abinda jahilai da ire-irensu suka ƙago na bidi’o’i da shaci faɗi; waɗanda Allah bai saukar da wani dalili kansu ba. Allah Shi ne abin neman taimako, kuma gare Shi muka dogara, kuma babu ƙarfi babu dabara ba face gareShi.

Amma salati da sallama ga Manzon Allah- tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: to wannan yana cikin manyan abubuwa masu kusantarwa kuma suna cikin ayyuka na gari, kamar yadda Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya faɗa:

﴿إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِيِّۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ صَلُّواْ عَلَيۡهِ وَسَلِّمُواْ تَسۡلِيمًا56﴾

{Lallai Allah da Mala'ikunSa su na salati ga Annabi ya ku waɗanda sukayi imani kuyi salati a gareshi kuma kuyi sallama mai yawa}. [al-Ahzab: 56], Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Wanda yayi salati a gareni sau ɗaya, Allah Zai masa salati sau goma». Kuma shi abin shara'antawa ce a dukkan lokuta, kuma ya fi ƙarfi a ƙarshen sallah, kai wajibi ne ma a wurin wasu malaman a Tahiyar ƙarshe ta kowacce sallah. Kuma sunnantuwar ta tana ƙara ƙarfafa a wurare masu yawa; daga ciki: Bayan kiran sallah da lokacin ambaton sa (Annabi) - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da yinin Juma’a da kuma darensa, kamar yadda hadisai masu yawa suka yi nuni akan hakan.

Allah ne wanda ake roƙa Ya datar damu da sauran musulmai fahimtar AddininSa da tabbata a kansa, kuma Yayi wa kowa baiwa da bin sunnah, da kiyaye bidi'a, lallai cewa Shi Mai yawan kyauta ne kuma Mai karamci.

Allah Ya Yi tsira da aminci ga Annabinmu Muhammadu da alayansa da sahabbansa.

 

 

***

 


بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ

SAƘO NA SHIDA:

Hukuncin taron bikin daren Isra'i da Mi'iraji

Godiya ta tabbata ga Allah, tsira da amincin Allah su tabbata ga Manzon Allah, da alayansa da sahabbansa.

Bayan haka: Babu shakka cewa Isira'i da Mi'iraji suna daga cikin ayoyin Allah masu girma masu nuni akan gaskiyar ManzonSa annabi Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, da kuma girman matsayinsa a wajen Allah - Mai girma da ɗaukaka-, kamar yadda suke daga cikin dalilai akan ikon Allah mai ban mamaki, da kuma ɗaukakarSa - Subhanahu wa Ta'ala - akan dukkan halittunSa, Allah - Subhanahu wa Ta'ala - Ya ce:

﴿سُبۡحَٰنَ ٱلَّذِيٓ أَسۡرَىٰ بِعَبۡدِهِۦ لَيۡلٗا مِّنَ ٱلۡمَسۡجِدِ ٱلۡحَرَامِ إِلَى ٱلۡمَسۡجِدِ ٱلۡأَقۡصَا ٱلَّذِي بَٰرَكۡنَا حَوۡلَهُۥ لِنُرِيَهُۥ مِنۡ ءَايَٰتِنَآۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡبَصِيرُ1﴾

{Tsarki ya tabbata ga wanda Ya yi tafiyar dare da bãwanSa da dare daga Masallaci mai alfarma zuwa ga Masallaci mafi nĩsa wanda Muka sanya albarka a gefensa dõmin Mu nũna masa daga ãyõyinMu. Lalle ne Shi shĩ ne Mai ji, Mai gani} [al-Isra'a: 1].

An samu Hadisan da yawa daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - cewa an ɗauke shi zuwa sammai, kuma an buɗe masa ƙofofinsu har ya wuce sama ta bakwai, sai Ubangijinsa - Mai girma da ɗaukaka - Yayi masa magana da abin da Ya so, kuma Ya farlanta masa salloli biyar, kuma Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya farlanta su da farko hamsin, Annabinmu Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -bai gushe ba yana koma maSa yana roƙon sauƙi, har Ya maida su biyar, to su biyar ne a farilla, hamsin ne a lada; domin kyakkyawa tana da lada goma, godiya ta tabbata ga Allah bisa dukkan ni'imominSa.

Wannan daren da a cikinsa ne aka yi Isra’ila da Mi’iraji, hadisai ingantattu ba su zo da ayyana daren ba, ba wai a Rajab ba, ba kuma a waninsa ba, duk abinda ya zo na ayyana daren to bai tabbata ba daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a wurin malamai ma’abota ilimin hadisi. Allah Yana da cikakkiyar hikima a mantar da mutane wannan daren, da ace ayyanashi ya tabbata to da baya halatta ga mutane su keɓanceshi da wani abu na ibadodi, kuma ba ya halatta gare su suyi bukukuwa saboda (daren); domin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, da sahabbansa - Allah Ya yarda da su - basu yi bukukuwa saboda (daren) ba, kuma ba su ware shi da wani abu ba. Da a ce bukukuwan abu ne shar’antacce da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi bayaninsa ga al’umma; ko dai ta magana ko kuma ta aiki, da wani abu ya faru na hakan da an sani, kuma da ya shahara, da kuma sahabbai - Allah Ya yarda da su - sun naƙalto mana. Don haƙiƙa sun ruwaito duk wani abu da al’umma take buƙatarsa daga Annabin na su, basu yi sakaci a wani abu da ya shafi Addini ba, a’a su ne ma na farko a duk wani alheri. To da taron bikin wannan daren shar’antacce ne da sun riga kowa aikata shi. Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - shi ya fi kowa yi wa mutane nasiha, kuma tabbas ya isar da manzanci matuƙar isarwa, kuma ya bayar da amana. Da ace girmama wannan daren da yin biki saboda shi yana cikin Addinin Allah da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - bai gafala daga aikata shi ba, kuma ba zai ɓoye shi ba. A sanda babu wani abu da ya faru cikin waɗannan sai aka sani cewa yin bikin daren da girmama shi ba sa cikin Musulinci ta kowanne ɓangare, domin tabbas Allah Ya cikawa wannan al’ummar Addininta, kuma Ya cika mata ni’ima, kuma Ya yi inkari ga duk wanda ya shar’anta wani abu a Addini da Allah bai bada izini akai ba, sai (Allah) Mai tsarki da ɗaukaka - Ya ce a cikin littafinS mai bayyanawa:

﴿...ٱلۡيَوۡمَ أَكۡمَلۡتُ لَكُمۡ دِينَكُمۡ وَأَتۡمَمۡتُ عَلَيۡكُمۡ نِعۡمَتِي وَرَضِيتُ لَكُمُ ٱلۡإِسۡلَٰمَ دِينٗا...﴾

{Kuma yaune Na cika muku addininku, kuma Na cika muku ni'imaTa kuma Na yarje muku musulunci a matsayin addini} [Ma'ida: 3], Kuma Allah - Maɗaukaki - Ya ce:

﴿أَمۡ لَهُمۡ شُرَكَٰٓؤُاْ شَرَعُواْ لَهُم مِّنَ ٱلدِّينِ مَا لَمۡ يَأۡذَنۢ بِهِ ٱللَّهُۚ وَلَوۡلَا كَلِمَةُ ٱلۡفَصۡلِ لَقُضِيَ بَيۡنَهُمۡۗ وَإِنَّ ٱلظَّٰلِمِينَ لَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٞ21﴾

{Kõ sunã da waɗansu abõkan tãrayya (da Allah) waɗanda suka shar'anta musu, game da addini, abin da Allah bai Yi izni da shi ba? Kuma bã dõmin kalmar hukunci (a lahira ba), da lalle, an yi hukunci (tun anan duniya) a tsakãninsu. Kuma lalle azzãlumai sunã da azãba mai raɗaɗi} [al-Shura: 21].

Kuma ya tabbata daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a hadisai ingantattu: Tsawatarwa akan bidi’a da kuma bayani ƙarara cewa bidi’a ɓata ce, don faɗakar da wannan al’ummar akan girman hatsarinta (ita bidi’ar) da nesantasu daga kusantarta daga cikin hakan: Abinda ya tabbata a cikin Sahihaini (Sahih al-Bukhari da Sahih Muslim) daga Nana Aisha - Allah Ya yarda da ita - daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - cewa ya ce: «Duk wanda ya farar da wani sabon abu a cikin wannan Addinin namu wanda baya ciki to shi abun mayar masa ne». A cikin wata riwayar ta Muslim: «Duk wanda yayi wani aiki wanda babu umarninmu a cikinsa to wannan aikin abin mayar masa ne». A cikin Sahihu Muslim daga Jabir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana faɗa a cikin huɗubarsa ranar Juma'a: «Bayan haka, to lallai cewa mafificin zance (shi ne) Littafin Allah, kuma mafificiyar shiriya (ita ce) shiriyar (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, kuma mafi sharrin al'amura abubuwan da aka farar, dukkanin bidi'a ɓata ce». Nasa'i ya ƙara da sanadi kyakkyawa: «Kuma kowacce ɓata tana cikin wuta». Ya zo a cikin Sunan daga Irbad bn Sariyah - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi mana wa’azi, wa’azi mai shiga jiki, zukata suka firgita, idanuwa suka zub da hawaye, muka ce: Ya Ma’aikin Allah! Kamar wa’azin mai bankwana, Ka yi mana wasiyya, sai ya ce: Ina yi muku wasicci da tsoron Allah, da ji da bi, koda bawa ne ya shugabance ku, domin cewa wanda ya rayu daga cikinku zai ga saɓani mai yawa, to na hore ku da sunnata da sunnar halifofina shiryayyu a bayana, ku riƙe su da turamen haƙoranku, na haneku da fararrun al'amura, domin cewa kowanne fararran abu bidi'a ce, kuma kowacce bidi'a ɓata ce. Hadisai da suka zo da wannan ma’anar suna da yawa.

Haƙiƙa ya tabbata daga sahabban Ma’aikin Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, haka kuma daga maganata na ƙwarai bayansu; tsawatarwa daga bidi’a da tsoratarwa akanta; ba komai ya sa haka ba sai domin ita ƙari ce a cikin Addini, kuma shari’a ce da Allah bai bada izini a kanta ba, kuma koyi ce da maƙiya Allah cikin Yahudu da Nasara, a yadda suke yin ƙari a Addininsu, da kuma yadda suke ƙirƙiro bidi’a a cikinsa na abinda Allah bai bada izini ba, kuma don lazimtarta tawaya ce ga Addinin Musulinci, kuma tuhumarsa ce da rashin cika, kuma sananne ne abinda yake cikin haka na ɓarna mai girma, da mummunan abin ƙi mai girma, kuma ya ci karo da faɗin Allah - girmanSa ya ɗaukaka -:

﴿...ٱلۡيَوۡمَ أَكۡمَلۡتُ لَكُمۡ دِينَكُمۡ...﴾

{Kuma yaune Na cika muku addininku, kuma Na cika muku ni'imaTa kuma Na yarje muku musulunci a matsayin addini} [Ma'ida: 3], da saɓawa bayyananniya ga hadisan Manzo - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - masu tsawatarwa daga bidi'o'i da kuma tsoratarwa daga gare su.

Wannan kenan, ina fatan abinda muka ambata na dalilai sun wadatar, kuma sun gamsar da mai neman gaskiya a inkarin wannan bidi’ar; ina nufin: Bidi’ar bikin daren Isra’i da Mi’iraj, da kuma tsawatarwa akan ta alhali ita ba ta cikin Addinin Musulinci ta ko’ina.

Saboda abin da Allah Ya wajabta na yin nasiha ga musulmai, da bayyana abin da Allah Ya shar'anta musu na addini, da haramcin ɓoye ilimi; na ga dacewar faɗakar da 'yan uwa musulmai kan wannan bidi'a, wadda ta yaɗu a cikin yawancin garuruwa, har wasu mutane suka ɗauka cewa a cikin addini take.

Allah nake roƙo da Ya gyara halayen musulmai baki ɗaya, kuma Ya basu fahimta a cikin addini, Ya datar damu da su don riƙe gaskiya da tsayawa a kanta, da barin duk abin da ya saɓa mata, lalle ne Shi ne Majiɓincin hakan kuma Mai iko a kansa.

Allah Yayi tsira da aminci da albarka ga bawanSa kuma ManzonSa Annabin mu Muhammad da alayensa da aahabbansa.

 

***

 


بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ

SAƘO NA BAKWAI:

Hukuncin yin biki a daren rabin watan Sha'aban

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah wanda Ya cika mana addini, kuma Ya cika ni’ima a kanmu, tsira da amincin Allah su tabbata ga AnnabinSa kuma ManzonSa (annabi) Muhammad Annabin tuba da rahama.

Bayan haka: Haƙiƙa Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce:

﴿...ٱلۡيَوۡمَ أَكۡمَلۡتُ لَكُمۡ دِينَكُمۡ وَأَتۡمَمۡتُ عَلَيۡكُمۡ نِعۡمَتِي وَرَضِيتُ لَكُمُ ٱلۡإِسۡلَٰمَ دِينٗا...﴾

{Kuma yaune Na cika muku addininku, kuma Na cika muku ni'imaTa kuma Na yarje muku musulunci a matsayin addini} [Ma'ida: 3], Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿أَمۡ لَهُمۡ شُرَكَٰٓؤُاْ شَرَعُواْ لَهُم مِّنَ ٱلدِّينِ مَا لَمۡ يَأۡذَنۢ بِهِ ٱللَّهُ...﴾

{Ko suna da wasu abokan tarayya ne da suke shar'anta musu addini abin da Allah bai musu izini da shi ba} [al-Shura: 21], Kuma ya zo a cikin Sahihil Bukari da Muslim daga Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Duk wanda ya farar da wani sabon abu a cikin wannan Addinin namu wanda ba ya ciki to shi abun mayarwa ne». Acikin Sahih Muslim daga Jabir - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa a cikin huɗubar Jumu'a: «Bayan haka, to lallai cewa mafificin zance (shi ne) littafin Allah, kuma mafificiyar shiriya (ita ce) shiriyar (annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, kuma mafi sharrin al'amura abubuwan da aka farar, dukkanin bidi'a ɓata ce». Ayoyi da hadisai masu yawa akan wannan ma’ana suna nan, kuma suna nuni a fili cewa Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya cikawa wannan al’umma addininta, kuma Ya cika ni’imarSa a gare ta, kuma bai karɓi ran AnnabinSa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ba sai bayan ya isar, isarwa bayyananniya, kuma ya bayyana wa al’umma duk abin da Allah Ya shar’anta mata na maganganu da ayyuka, Kuma Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare - shi ya fayyace duk abinda mutane suke ƙirƙira su jingina shi ga Addinin Musulinci na magana ko ayyuka; to gabaɗayan sa bidi’a ne abin mayarwa ga wanda ya ƙirƙire shi, ko da kuwa niyyar sa kyakkyawa ce, kuma haƙiƙa sahabban Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sun san hakan, haka kuma malaman Musulinci da suka zo bayansu, sai suka yi musun bidi’o’in, suka kuma tsawatar akan hakan, kamar yadda duk wanda ya yi rubutu akan girmama sunnah da inkarin bidi’a ya ambata; kamar Ibn Waddah da Ɗarɗushi da Abu Shamah da wasunsu.

Kuma lalle yana daga bidi’o’in da wasu mutane suka ƙirƙira: Bidi’ar bikin daren Nisfu Sha’aban (wato daren da watan Sha’aban yayi rabi) da keɓance yinin da yin azumi, kuma babu wani dalili da ya halatta ayi dogaro da shi, kuma hadisai masu rauni sun zo akan falalarsa, ba ya halatta a dogara a kan su.

Amma abin da ya zo akan falalar sallah a cikinta; dukkanin sa ƙarya ne, kamar yadda masana ilimi da yawa suka yi nuni da hakan, kuma za a zo da ambaton wasu daga cikin maganganunsu in Allah Ya so.

Haƙiƙa kuma, akwai bayanai daga wasu cikin Salaf (magabata) na mutanen Sham da wasun su.

Abinda jamhurun malamai suka yi ijima’i a kansa shi ne wannan taron bikin bidi’a ne, kuma dukkkan hadisan da suka zo akan falalarsa da’ifai ne (masu rauni), wasu hadisan ma maudu'ai (na ƙarya ne), daga cikin waɗanda suka yi tambihi akan hakan: al-Hafiz Ibn Rajab, a littafinsa: (Laɗa’iful Ma’arif), da waninsa, kuma sananne ne cewa hadisai da'ifai kaɗai ana aiki da su ne a ibadun da asalinsu ya tabbata da dalilai ingantattu, Amma bikin daren Nisfu Sha’aban to ba shi da wani asali ingantacce har da za'a iya dogaro gare shi da hadisai da'ifai. Haƙiƙa Imam Abul Abbas Shaikhul Islam Ibn Taimiya - Allah Ya yi masa rahama - ya ambaci wannnan babbar ƙa’idar:

Kuma ina isar maka - ya kai mai karatu - abin da wasu ma'abota ilimi suka faɗa a cikin wannan al'amari, domin ka kasance shaida a cikin hakan.

Haƙiƙa malamai sun yi ijma’i - Allah Ya yi musu rahma - akan abinda yake wajibi shine: Mayar da abinda mutane suka yi jayayya a kansa na mas’aloli zuwa ga littafin Allah (Alƙur'ani) da kuma sunnar ManzonSa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, to abinda su biyun suka yi hukunci da shi ko ɗayansu to shi ne shari’ar da ta zama wajibi a bi ta, abin da kuma ya saɓa musu to ya wajaba a yi watsi da shi, abin da kuma bai zo a cikinsu ba (Alƙur'ani da Sunnah) na ibada to bidi’a ne ba ya halasta a aikata shi balle ma a yi kira zuwa gare shi, ko a ga dacewarsa, Allah Mai tsarki da ɗaukaka - Ya ce:

﴿يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ أَطِيعُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُواْ ٱلرَّسُولَ وَأُوْلِي ٱلۡأَمۡرِ مِنكُمۡۖ فَإِن تَنَٰزَعۡتُمۡ فِي شَيۡءٖ فَرُدُّوهُ إِلَى ٱللَّهِ وَٱلرَّسُولِ إِن كُنتُمۡ تُؤۡمِنُونَ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِۚ ذَٰلِكَ خَيۡرٞ وَأَحۡسَنُ تَأۡوِيلًا59﴾

{Yã kũ waɗanda suka yiĩmãni! Ku yi ɗã'a ga Allah, kuma ku yi ɗã'a ga ManzonSa, da ma'abũta al'amari daga cikinku. Idan kun yi jãyayya a cikin wani abu, to ku mayar da shi zuwa ga Allah da ManzonSa idan kun kasance kunã ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira. wannan ne mafi alhẽri, kuma mafi kyau ga fassara}. [al-Nisa'a: 59], Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿وَمَا ٱخۡتَلَفۡتُمۡ فِيهِ مِن شَيۡءٖ فَحُكۡمُهُۥٓ إِلَى ٱللَّهِ...﴾

{Kuma abin da kuka yi saɓani a cikinsa na daga wani abu to hukuncinsa zuwa Allah yake} [al-Shura: 10] Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿قُلۡ إِن كُنتُمۡ تُحِبُّونَ ٱللَّهَ فَٱتَّبِعُونِي يُحۡبِبۡكُمُ ٱللَّهُ وَيَغۡفِرۡ لَكُمۡ ذُنُوبَكُمۡ...﴾

{Ka ce: "Idan kun kasance kunã son Allah to, ku bĩ ni, Allah Ya sõ ku, kuma Ya gãfarta muku zunubanku} [Aal- Imran: 31]. Kuma Allah - Maɗaukaki - Ya ce:

﴿فَلَا وَرَبِّكَ لَا يُؤۡمِنُونَ حَتَّىٰ يُحَكِّمُوكَ فِيمَا شَجَرَ بَيۡنَهُمۡ ثُمَّ لَا يَجِدُواْ فِيٓ أَنفُسِهِمۡ حَرَجٗا مِّمَّا قَضَيۡتَ وَيُسَلِّمُواْ تَسۡلِيمٗا65﴾

{To, a'aha! Ina rantsuwa da Ubangijinka, ba za su yi ĩmãni ba, sai sun yarda da hukuncinka ga abin da ya sãɓa a tsakãninsu, sa'an nan kuma ba su sãmi wani ƙunci a cikin zukãtansu ba, daga abin da ka hukunta, kuma su sallama sallamãwa} [al-Nisa'a: 65], kuma ayoyi a cikin wannan ma'ana suna da yawa, kuma suna nuni da wajabcin mayar da al'amuran da ake saɓani zuwa ga Littafi (AlKur’ani) da Sunnah, da kuma wajabcin yarda da hukuncinsu, kuma cewa hakan shi ne abin da imani ke buƙata, kuma mafi alheri ga bayi a nan duniya da lahira, kuma mafi kyawun fassara: wato kyakkyawan ƙarshe.

Masanin Hadisi Ibn Rajab -Allah Yayi masa rahama- ya ce a cikin littafinsa: (Laɗa'if al-Ma'arif) a cikin wannan mas'ala -bayan maganar da ta gabata- abin da ya ce:

«Kuma daren rabin Sha'aban, Tabi'ai daga mutanen Sham; kamar Khalid bin Ma'dan, da Mak'hul, da Luƙman bin Amir da sauransu, suna girmama shi kuma suna ƙoƙari a cikinsa wajen bauta, kuma daga gare su ne mutane suka ɗauki falalarsa da girmamawarsa, Kuma an ce: Wasu hadisai na Isra'iliyyat sun kai garesu, to a yayin da waɗannan abubwan suka yaɗu a garuruwa daga gare su, sai mutane suka rarrabu akan hakan; daga cikinsu akwai wanda ya karɓe su kuma ya yi tarayya da su akansu cikin girmama su, daga cikinsu kuma akwai wasu jama'a daga masu bauta a mutanen Basrah da wasunsu. Yawancin malaman Hijaz sun yi inkari akan hakan, daga cikinsu akwai: Aɗa’au, da Ibn Abi Mulaika, kuma Abdulrahman ɗan Zaid dan Aslam ya ruwaito daga malaman fiƙihun Madina, kuma shi ne faɗin almajiran Malik da wasu, kuma suka ce: wannan duka bidi'a ce.

Malamai na Sham sun yi saɓani a kan siffar rayawar a kan maganganu guda biyu:

Na farko: An so a rayar da ita a cikin masallatai a cikin jama'a, Khalid bin Ma'dan da Luƙman bin Amir da wasu sun kasance suna sanya mafi kyawun tufafinsu, suna sanya turare da yin tozali, suna tsayawa a cikin masallaci a daren su, kuma Ishaƙ dan Rahuwaih ya yarda da su akan hakan, Kuma ya ce game da tsayuwarta a masallatai cikin jam'i: wannan ba bidi'a ba ce, Harb al-Karmani ya ruwaito a cikin mas'alolinsa.

Na biyu: Ana ƙyamatar taruwa a bikin Nisfu Sha’aban a masallatai don sallah da labarai da addu'a, amma ba a ƙyamatar mutum ya yi sallah a daran don kansa, wannan shi ne ra'ayin al-Auza'i, limamin mutanen Sham kuma malamin su, kuma wannan shi ne mafi kusanci insha Allah Ta'ala». Har zuwa inda ya ce: «Ba’a san Imam Ahmad yana da wata magana ba akan daren Nisfu Sha’aban ba, za’a fitar da mustahabbacin tsayuwarsa ne daga gare shi ta riwayoyi biyu cikin riwayoyi daga gare shi a tsayuwar darare biyu na idi, domin (a cikin wata riwayar) ba’a so a yi nafilfilin a cikin jam’i a cikinsa; domin ba’a samo hakan daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ba haka kuma sahabbansa, An so ta (a cikin wata ruwayar), saboda abin da Abdurrahman ɗan Yazid ɗan Aswad ya yi, wanda shi ne daga cikin tabi'ai, haka ma tsayuwar daren tsakiyar Sha'aban, ba ta tabbata daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ko daga sahabbansa ba, amma ta tabbata daga wasu daga cikin tabi'ai daga manyan malaman fiƙihu na mutanen Sham».

Abin nufi a maganar al-Hafiz Ibn Rajab - Allah Ya yi masa rahama - ya ƙare, kuma a cikinsa akwai bayani a bayyane cewa wani abu na daren Nisfu Sha'aban bai tabbata daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ba - ko sahabbansa - Allah Ya yarda da su -.

Amma abinda al-Auza’i - Allah Ya yi masa rahama - ya zaɓa na son tsayuwarta ga mutum ɗaya, da kuma zaɓin al-Hafiz Ibn Rajab ga wannan magana, to wannan abu ne mai ban mamaki kuma mai rauni; domin dukkanin abubuwan basu tabbata da hujjojin shari’a ba cewa yana daga cikin shari’a, to bai halatta ga musulmi ya ƙirƙire shi a cikin addinin Allah ba, ko ya aikata shi shi kaɗai ko a cikin jama’a, ko ya ɓoye shi ko ya bayyana shi; saboda gamewar faɗin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: «Duk wanda ya yi wani aiki wanda babu umarninmu a cikinsa to wannan aikin abun mayarwa ne». Da wasun su daga hujjoji masu nunin ƙin bidi'a da tsawatarwa daga gare ta.

Kuma Imam Abu Bakar al'Ɗarɗusi - Allah Yayi masa rahama - ya ce a cikin littafinsa: "Al'hawadith wal bid'aa" abin da ya ce:

«Ibnu Waddah ya ruwaito daga Zaid ɗan Aslam, ya ce: Ba mu samu kowa daga cikin dattawanmu ko malaman fiƙihunmu suna mai da hankali ga rabin Sha'aban ba, kuma ba su mai da hankali ga hadisin Mak'hul ba, kuma ba su ganin yana da falala akan sauran kwanaki ba».

Kuma aka ce wa ɗan Abi Mulaika: Lallai Ziyad an-Namiri yana cewa: «Lallai ladar daren tsakiyar Sha'aban yana daidai da Lailatul ƙadari», Sai ya ce: "Da na ji shi kuma a hannuna akwai sanda da na buge shi». Ziyad ya kasance mai labari ne (wa’azin turmi) manufar ta ƙare.

Babban malami al-Shaukani,- Allah Ya yi masa rahama - a littafinsa «Alfawa’idul Majmu’ah» ya faɗi abinda nassinsa shine:

Hadisi: «Ya Ali, duk wanda ya yi sallah raka'a ɗari a daren tsakiyar Sha'aban, yana karanta wa a kowacce raka'a da Fatiha da Qul huwa Allahu Ahad sau goma; Allah zai biya masa dukkan wata buƙata». Hadisin Maudu'i ne, kuma a lafuzansa da ke bayyana abin da mai aikata shi zai samu na lada babu wanda ke da hankali zai yi shakka a cikin ƙaryarsa, kuma maruwaitansa ba a san su ba, an kuma ruwaito shi ta wata hanya ta biyu da ta uku dukkan su ƙarya ne kuma masu rawaiton su ba a san su ba, Ya ce a cikin: «al-Mukhtasar»: Hadisin sallar rabin Sha'aban ba shi da inganci, kuma daga Ibnu Hibban daga hadisin Ali: «Idan dare na rabin Sha'aban ya kasance, ku yi tsayuwar dare, kuma ku yi azumin ranar sa», mai rauni ne. Ya ce a cikin: «Al-La'ali»: «Raka'a ɗari a cikin rabin Sha'aban da Ikhlasi sau goma» tare da tsawon falalarsa, ga Dailami da wasu, Hadisin ƙarya ne, kuma mafi yawan masu ruwaitawa a cikin hanyoyi uku ba a san su ba kuma raunana ne, Ya ce: "Raka'o'i goma sha biyu da ikhlasi sau talatin". Mauru'i ne, "da raka'o'i goma sha huɗu" Mauru'i ne.

Kuma wasu daga cikin malamai sun ruɗu da wannan hadisi; kamar mai littafin (Ihya) da sauransu haka nan daga cikin masu tafsiri, an kuma ruwaito sallar wannan daren - wato: daren rabin Sha'aban - a hanyoyi daban-daban dukkan su ba su da inganci kuma an ƙirƙiro su ne, Wannan kuma ba ya kore riwayar Tirmizi cikin hadisin Nana Aisha - Allah Ya yarda da ita - na tafiyar da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - zuwa Baƙi’a, da kuma saukar Ubangiji a daren Nisfu zuwa saman duniya, kuma Shi (Ubangiji) yana gafartawa sama da adadin gashin dabbobin Kalb, to wannan maganar kawai akan wannan sallar ce da aka ƙaga wannan daren. Amma hadisin Nana Aisha yana da rauni da katsewa, kamar yadda hadisin Ali da aka ambata a baya game da tsayuwar da daddare, ba ya kore cewa wannan sallar ƙagaggiya ce, duk da raunin da ke ciki kamar yadda muka ambata.

Al-Hafiz al-Iraƙi ya ce: «Hadisin sallar daren rabin dare (na Sha’aban) an ƙirƙire shi ne ga Manzon Allah -tisira da amincin Allah su tabbata a gareshi- kuma ƙarya ce aka yi masa», Kuma Imam al-Nawawi ya ce a cikin littafin: (al-Majmu'): "Sallar da aka sani da Sallar Ragha'ib, wato raka'o'i goma sha biyu tsakanin Magriba da Isha, a daren Juma'a ta farkon Rajab, da sallar daren rabin Sha'aban raka'o'i ɗari, waɗannan salloli biyu bidi'a ce mummuna, kada a yaudareka da ambatonsu a cikin littafin: (Kutul ƙulub), da (Ihya Ulumuddin), ko da hadisin da aka ambata a cikinsu, domin duk wannan ba daidai ba ne, kada a yaudareka da wasu daga cikin malamai da suka rikice a kan hukuncinsu suka rubuta takardu a kan soyyayarsu, domin sun yi kuskure a cikin wannan.

Haƙiƙa babban malami Imam Abu Muhammad Abdurrahman bn Isma’il al-Maƙdasi ya wallafa littafi mai kyau akan ɓatansu su biyun, kuma ya yi bayani mai kyau a cikinsa ya kyautata, maganar malamai a wannan mas’alar tana da yawa, da zamu dinga kawo duk abinda muka gani a wannan mas’alar to da maganar ta yi yawa, muna fatan wannan da muka ambata ya isa kuma ya gamsar ga mai neman gaskiya.

Daga cikin abinda ya gabata na ayoyi da hadisai da kuma maganar malamai; zai bayyana ga mai neman gaskiya, lalle bikin daren Nisfu Sha’aban ko waninsa, da kuma ware yininsa da azumi; to wannan bidi’a ce mummuna a wurin mafi yawan malamai, kuma ba shi da wani asali a shari’a mai tsarki, kawai yana cikin abinda aka ƙirƙira a cikin Musulinci bayan zamanin sahabbai - Allah Ya yarda da su -, kuma faɗin Allah - girmanSa ya ɗaukaka - ya ishi mai neman gaskiya a wannan babin da waninsa:

﴿...ٱلۡيَوۡمَ أَكۡمَلۡتُ لَكُمۡ دِينَكُمۡ...﴾

(A yau na cika muku addininku) [al-Ma'ida: 3]. Da abinda ya zo a cikin ma'anarsu na ayoyin, da faɗin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: «Duk wanda ya farar da wani abu a cikin wannan Addinin namu wanda ba ya ciki. to shi abun mayarwa ne». Da abinda ya zo a cikin ma'anarsa daga hadisai.

Ya zo cikin Sahihin Muslim daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Kada ku ware daren Juma'a da tsayuwar dare daga cikin sauran darare, kuma kada ku ware ranar da azumi daga cikin sauran ranaku, sai dai idan yana cikin azumin da ɗayanku yake yi». Da ace keɓance wani abu cikin darare da wani nau’i na ibada ya halatta, da daren Juma'a ya fi cancanta akan sauran darare; domin yinin ta shi ne mafi alherin yini da rana ta ɓullo a cikinsa, bisa nassosin hadisai sahihai daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, Bayan da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi gargaɗi akan keɓance daren da tsayuwa daga cikin sauran darare, hakan ya nuna cewa sauran darare ma sun fi dacewa, baya halatta a keɓance wani abu daga cikinsu da wani abu na ibada ba, sai dai da hujja sahihiya da ke nuna keɓancewar.

Kuma da yake daren Lailatul Ƙadr da dararen Ramadan an shar'anta tsayuwa da ƙoƙari a cikinsu, Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yayi nuni da hakan, kuma ya kwaɗaitar da al'umma akan tsayuwa a cikinsu, kuma ya aikata hakan da kansa, kamar yadda yake a cikin Bukhari da Muslim daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Duk wanda ya yi tsayuwar daren Ramadana yana mai imani da kuma neman lada; an gafarta masa abinda ya gabata na zunubinsa, kuma duk wanda ya tsayuwa a daren Lailatul Qadari yana mai imani da kuma neman lada, an gafarta masa abinda ya gabata na zunubinsa». Da ace daren tsakiyar Sha'aban, ko daren Juma'a na farko a Rajab ko daren Isra'i da Mi'iraji an shar'anta keɓance su da wani biki ko wani abu na ibada, da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yayiwa al'umma jagora zuwa gare shi, ko ya aikata shi da kansa, kuma da ace wani abu daga cikin wannan ya faru da sahabbai - Allah Ya yarda da su - sun isar da shi ga al'umma, ba su ɓoye shi ba, alhalin su ne mafi alkhairi na mutane, kuma mafi nasihar mutane bayan Annabawa - aminci ya tabbata agare su -, kuma Allah - Ya yarda ga ahabban Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -kuma ya yarda da su.

Kuma haƙiƙa mun sani a abinda ya gabata na maganganun malamai, cewa wani abu ba na falalar daren Juma’a ta farkon watan Rajab haka kuma daren Nisfu Sha’aban bai tabbata daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ba -, haka kuma bai tabbata daga sahabbansa ba, - Allah Ya yarda da su -. Saboda haka sai aka sani yin bikinsa bidi’a ce da aka ƙirƙira a cikin Musulinci, haka kuma keɓance ta da wasu ibadu duka bidi’a ce abar ƙi. Kuma haka daren ashirin da bakwai na watan Rajab, wanda wasu mutane ke tunanin cewa shi ne daren Isra'i da Mi'iraji, ba ya halatta a keɓance shi da wani abu na ibada, kamar yadda ba ya halatta a yi biki da shi; saboda hujjojin da suka gabata, wannan fa idan an san shi kenan, to yaya kuma a ingantaccen zance daga maganganun malamai shi ne ba a ma san shi ba, Kuma maganar wanda ya ce: Shi ne daren ashirin da bakwai na Rajab, magana ce mara tushe a cikin hadisai sahihai, kuma haƙiƙa ya kyautata wanda ya ce:

Mafificin al'amura (su ne) waɗanda suka gabata akan shiriya... kuma mafi sharrin al'amura (su ne) abubuwan da aka farar, bidi'o'i.

Allah ne abin roƙo Ya datar damu da sauran musulmai don riƙe sunnah da tabbata a kanta, da kuma tsarewa daga abin da ya saɓa mata, lallai cewa Shi Allah Mai yawan kyauta ne kuma Mai girma.

Tsira da amincin Allah su tabbata ga bawanSa kuma ManzonSa Annabinmu Muhammad da alayensa da sahabbansa baki ɗaya.

 

***

 


بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ

SAƘO NA TAKWAS:

Muhimmiyar Sanarwa akan ƙaryar wasiyyar da aka dangantawa

Shiekh Ahmad mai Hidimar Haramin Annabi maɗaukaki

Daga AbdulAzeez ɗan Abdullahi ɗan Baaz zuwa ga duk wanda zai karanta cikin musulmai, Allah Ya kiyaye su da addinin Musulunci, kuma Ya tsare mu da su daga sharrin ƙaryar jahilai, amin.

Amincin Allah ya tabbata a gareku da rahamarSa da albarkatunSa.

Bayan haka: To haƙiƙa na karanta wani jawabi da aka danganta ga Sheikh Ahmad maiyiwa Haramin Annabi mai daraja hidima, mai taken: «Wannan wasiyya ce daga Madina Munawwara daga Sheikh Ahmad Khadimul Haramin Nabawi al-Sharif», inda ya ce:

«Na kasace a farke a daren Juma’a ina karanta Alƙur'ani mai girma, bayan na karanta sunayen Allah kyawawa, to a lokacin da na kammala hakan sai na yi shirin bacci, kawai sai na ga ma’abocin hasken fuska, Ma’aikin Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - wanda ya zo da ayoyi na Alƙur'ani da hukunce-hukunce masu daraja; don rahma ga talikai, shugabammu (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -,ya ce: Ya Shaikh Ahmad, sai na ce: Amsawarka ya Ma’aikin Allah, ya mafi karamcin halittar Allah. Sai ya ce mini: Ina jin kunya daga munanan ayyukan mutane, ba zan iya haɗuwa da Ubangijina ba haka ma da Mala’iku; domin daga Juma’a zuwa Juma’a, mutum dubu ɗari da sittin ne suka mutu a tafarkin da ba na Musulinci ba, - sannan sai ya ambaci abinda mutane suka faɗa cikinsa na saɓo. Sannan sai ya ce: Wannan wasiyyar rahma ce gare su daga (Allah) Mabuwayi Mai tilastawa: Sannan ya ambaci wani sashe na alamomin tashin alƙiyama, har dai inda ya ce: - Sai ka sanar musu da wannan wasiyyar ya Shaikh Ahmad, domin an cirota ne daga Lauhul Mahfuz da alƙalamin ƙudura, duk wanda ya rubuta ta ya kuma aikata daga wani gari zuwa wani garin, haka daga wani wuri zuwa wani wurin to za’a gina masa katafaran gida a aljanna, wanda kuma bai rubuta ta ba kuma bai aikata ba, to cetona ya haramta a gare shi a ranar alƙiyama. Ko wanda ya rubuta ta kuma yana cikin talauci, Allah zai wadata shi, ko yana da bashi, Allah zai biya masa bashinsa, ko yana da wani zunubi, Allah zai gafarta masa da iyayensa saboda albarkar wannan wasiyyar, Wanda kuma bai rubuta ta daga cikin bayin Allah ba, fuskarsa zata yi baƙi a duniya da Lãhira, Kuma ya ce: Na rantse da Allah Mai girma sau uku wannan gaskiya ce, kuma idan na kasance maƙaryaci(Allah) Yasa in bar duniya ba tare da Musulunci ba, kuma wanda ya gaskata ta zai tsira daga azabar wuta, kuma wanda ya ƙaryata ta ya kafirta».

Wannan shi ne taƙaitaccen abin da ke cikin wasiyyar ƙarya da aka jinginawa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - kuma mun ji wannan wasiyyar ƙarya sau da yawa tun shekaru da dama, ana yaɗa ta tsakanin mutane lokaci zuwa lokaci, kuma ana tallata ta tsakanin yawancin talakawa, kuma a cikin lafuzanta akwai bambanci, Kuma maƙaryacin yana cewa:

Ya ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a cikin bacci, ya ɗauki wannan wasiyya, kuma a cikin wannan sanarwa ta ƙarshe da muka ambata maka ya mai karatu, mai ƙirƙirar ƙaryar yayi iƙirarin cewa yaga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - lokacin da ya shirya yin bacci, don haka ma'anar: ya gan shi a farke!

Wannan da ya ƙirƙiri wannan ƙaryar yana riya abubuwa masu yawa a cikin wannan wasiyyar; waɗanda suna cikin mafi bayyanar ƙarya, kuma mafi bayyanar ɓarna, da sannu zan faɗakar da kai game da su a waɗannan kalmomin da yardar Allah. Haƙiƙa na faɗakar a kansu a shekarun da suka gabata, na kuma yi wa mutane bayanin cewa suna daga mafi bayyanar ƙarya, kuma mafi bayyanar ɓarna. To a lokacin da na ga wannan bugun na ƙarshe, sai na yi kai ka wo a rubutata, domin ɓacinta a fili yake, da kuma girman ƙarfin halin wanda ya ƙirƙiro ƙaryar, bana zaton ɓarnarsa za ta sake ruruwa ga wanda yake da mafi ƙarancin basira ko cikakken tunani. Saidai da yawa daga ‘yan uwa sun bani labarin cewa ta rurutar da da yawa daga cikin mutane, kuma sun dinga yaɗa ta a tsakaninsu, wasu kuma sun gasgata ta; to saboda haka na ga yin rubutu a kanta ya wajaba ga ire-ire na, domin yin bayanin ɓacinta, da ƙaryata wannan abinda aka ƙaga ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, don kada wani ya ruɗu da ita. To, duk wanda ya yi nazari daga cikin masu ilimi da imani, ko kuma masu kyakkyawar ɗabi'a da hankali mai kyau; zai gane cewa ita ƙarya ce da ƙirƙira daga ɓangarori da yawa.

Na tambayi wasu daga cikin dangin Sheikh Ahmad da ake jingina wannan ƙarya gare shi, game da wannan wasiyya, sai suka amsa mini: cewa an ƙirƙira wannan magana ga Sheikh Ahmad ne, kuma bai faɗe ta ba tun asali ma, Shehin da aka ambata, Ahmad, ya rasu tun tsawon lokaci, kuma idan muka yi zato cewa shehin da aka ambata, Ahmad, ko wanda yafi shi girma, yayi iƙirarin cewa ya ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a cikin bacci ko a farke, kuma yayi masa wannan wasiyyar, da mun san da tabbaci cewa maƙaryaci ne, ko kuma wanda ya faɗa masa hakan Shaiɗan ne, ba shi ne Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ba saboda dalilai da yawa, daga cikinsu:

Na farko: Lalle Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, ba a ganin shi a farke bayan rasuwarsa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -. Duk wanda ya riya daga cikin jahilan Sufaye cewa wai ya ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a farke ko ya ce yana zuwa wurin maulidi ko abinda ya yi kama da haka; to haƙiƙa ya tafka kuskure mafi munin kuskure, kuma lamurra sun rikice masa matuƙar rikicewa, kuma ya afka cikin kuskure mai girma, ya kuma saɓawa littafi (Alƙur'ani) da sunnah da ijma’in malamai; domin mamata kaɗai za'a fito da su ne daga ƙaburburansu ranar alƙiyama ne ba a nan duniya ba. To, wanda ya faɗi akasin haka to shi maƙaryaci ne kuma ya yi ƙarya bayyananniya, ko kuma mai kuskure wanda aka ruɗe shi, bai san gaskiyar da salihan magabata suka sani ba, kuma sahabban Manzon Allah - taira da amincin Allah su tabbata a gare shid - da mabiyansu da kyautatawa suka bi, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce:

﴿ثُمَّ إِنَّكُم بَعۡدَ ذَٰلِكَ لَمَيِّتُونَ15 ثُمَّ إِنَّكُمْ يَوْمَ الْقِيَامَةِ تُبْعَثُونَ16﴾

{Sa'an nan kuma ku, bãyan wannan, lalle ne masu mutuwa ne.Sa'an nan kuma lalle ne kũ a Rãnar alƙiyãma, za a tãyar da ku}

Sannan kuma lalle ne kũ a Rãnar alkiyãma, za a iãyar da ku, [al-Mua'Minun: 15 - 16], Kuma Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Ni ne farkon wanda ƙasa za ta tsage masa ranar Alƙiyama, kuma farkon mai ceto farkon wanda za'a bawa ceto». Ayoyi da hadisai da suka zo da wannan ma’anar suna da yawa.

Na biyu: Lalle Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ba ya faɗin saɓanin gaskiya, ko yana raye ko bayan rasuwarsa. Wannan wasiyyar ta saɓawa shari’ar sa, saɓawa ta zahiri, hakan kuwa ta fuskoki da yawa - kamar yadda bayani zai zo -, kuma shi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - takan yi wu a gan shi a cikin bacci. Kuma duk wanda ya gan shi a cikin mafarki a kan surarsa mai daraja to ya gan shi; domin Shaiɗan ba ya kwaikwayon surarsa, kamar yadda ya zo a cikin hadisi sahihi mai daraja, amma abin dubawa duka yana cikin imanin mai ganin da gaskiyarsa da adalcinsa da tsarewarsa da addininsa da amincinsa, kuma shin ya ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a cikin surarsa ko a cikin wata surar.

Da a ce wani hadisi zai zo daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da ya faɗe shi a rayuwar sa, ba ta hanyar amintattu adalai masu kaifin hadda ba, to da ba za’a dogara da shi ba, ba kuma za’a yi hujja da shi ba, ko kuma ya zo ta hanyar amintattu masu kaifin hadda, saidai ya saɓawa riwayar wanda ya fi shi hadda kuma mafi aminci daga cikinsu, saɓawar da ba zai yi wu a haɗa riwayoyin biyu ba, to da ɗaya ya zama an shafe shi ba za’a yi aiki da shi ba, na biyun kuma ya zama shi ya shafe saboda haka za’a yi aiki da shi in dai hakan zai yi wu da sharuɗɗansa. Idan kuma haɗa su ba zai yi wu ba, kuma shafe wa ma ba zata yi wu ba, to ya zama dole a yi watsi da riwayar wanda baida ƙarfin hadda kuma adalarsa take koma baya, sai ayi mata hukuncin cewa ta zama Shazzah ba za yi aiki da ita ba.

To ya wasiyyar da ba’a san wanda ya yi ta ba, wanda ya karɓo ta daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, ba’a san adalarsa da amanarsa ba, to a wannan halin ita tafi cancantar a yi watsi da ita, ba za a kula da ita ba, ko da babu wani abu a cikinta da ya saɓawa shari’a, to ya wasiyyar za ta kasance idan a cikinta akwai abubuwan da suka saɓawa shari’a, kuma ita ƙarya ce aka yi wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, kuma tana ƙunshe da wata shari'ar da Allah bai bada izini akai ba?!

Haƙiƙa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yace: «Wanda ya (danganta mini) abin da ban faɗa ba; to ya tanadi mazauninsa a wuta». Kuma haƙiƙa wanda ya ƙirƙiri wannan ƙaryar ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, ya faɗi abinda (Annabi) bai faɗa ba, kuma yayi masa ƙarya a bayyane mai hatsari. Mamakin dacewarsa ga wannan narko (na azaba) mai girma, mamakin cancantarsa da shi idan bai yi gaggawar tuba ba, ya kuma yaɗawa mutane ƙaryar wannan wasiyyar da ya yi ta akan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -; domin duk wanda ya yaɗa ɓarna a cikin mutane ya kuma jinginata ga Addini; to tuban shi ba ya inganta har sai ya sanar (da ƙaryar) kuma ya bayyanar, har mutane su tabbatar da ya bar wannan ƙaryar ya kuma ƙaryata kansa; saboda faɗin Allah - girmanSa ya ɗaukaka -:

﴿إِنَّ ٱلَّذِينَ يَكۡتُمُونَ مَآ أَنزَلۡنَا مِنَ ٱلۡبَيِّنَٰتِ وَٱلۡهُدَىٰ مِنۢ بَعۡدِ مَا بَيَّنَّٰهُ لِلنَّاسِ فِي ٱلۡكِتَٰبِ أُوْلَٰٓئِكَ يَلۡعَنُهُمُ ٱللَّهُ وَيَلۡعَنُهُمُ ٱللَّٰعِنُونَ159 إِلَّا ٱلَّذِينَ تَابُواْ وَأَصۡلَحُواْ وَبَيَّنُواْ فَأُوْلَٰٓئِكَ أَتُوبُ عَلَيۡهِمۡ وَأَنَا ٱلتَّوَّابُ ٱلرَّحِيمُ160﴾

{Lalle ne waɗanda suke ɓõyẽwar abin da Allah Ya saukar da ga hujjõji bayyanannu, da shiriya, daga bãyan Mun bayyana shi ga mutãne, a cikin Littãfi (Alƙur'ãni), waɗannan Allah Yana la'anar su, kuma mãsu la'ana suna la'anar su.

Sai waɗanda suka tũba, kuma suka gyãra, kuma suka bayyana, to waɗannan Ina karɓar tũba a kansu kuma Nĩ ne Mai karɓar tũba, Mai jin ƙai) [al-Bakara: 159, 160], Allah - Maɗaukakin sarki - Ya bayyana a cikin wannan aya mai girma: Cewa duk wanda ya ɓoye wani abu daga gaskiya ba to tubansa bai inganta ba sai bayan gyara da bayyanawa, kuma Allah - Maɗaukakin sarki - haƙiƙa Ya cika wa bayinSa addini, kuma Ya cika musu ni'ima da aiko ManzonSa (annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, da abin da Allah Ya yi wahayi zuwa gare shi na shari’a cikakkiya, kuma bai karɓe shi zuwa gare Shi ba sai bayan cikawa da bayyanawa, kamar yadda Ya ce - tsarki ya tabbatar maSa:

﴿...ٱلۡيَوۡمَ أَكۡمَلۡتُ لَكُمۡ دِينَكُمۡ وَأَتۡمَمۡتُ عَلَيۡكُمۡ نِعۡمَتِي وَرَضِيتُ لَكُمُ ٱلۡإِسۡلَٰمَ دِينٗا...﴾

{Kuma yaune Na cika muku addininku, kuma Na cika muku ni'imaTa kuma Na yarje muku musulunci a matsayin addini} [al-Ma'ida: 3]

Mai ƙirƙirar wannan wasiyya ya zo a ƙarni na goma sha huɗu, yana son ya jefa mutane cikin wani sabon addini, wanda ya sanya shiga Aljanna ga wanda ya karɓi shari'arsa, da kuma haramta Aljanna da shiga wuta ga wanda bai karɓi shari'arsa ba, Yana so ya sanya wannan wasiyyar da ya ƙirƙira ta fi Alƙur'ani girma da falala, inda ya ƙirƙira a cikinta: cewa duk wanda ya rubuta ta ya aika ta daga gari zuwa gari, ko daga wuri zuwa wuri; za a gina masa gida a Aljanna, kuma wanda bai rubuta ta ba ya aika ta, za a haramta masa ceto na Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a ranar Alƙiyama, Wannan yana daga cikin munanar ƙarya, kuma daga cikin bayyanannun dalilai akan ƙaryar wannan wasiyya, da ƙarancin kunyar wanda ya ƙirƙira ta, da girman jarumtar sa akan ƙarya; domin wanda ya rubuta Alƙur'ani mai girma kuma ya aika shi daga gari zuwa gari, ko daga wuri zuwa wuri; ba zai samu wannan falalar ba idan bai yi aiki da Alƙur'ani mai girma ba, to yaya za a samu ga wanda ya rubuta wannan ƙarya kuma ya yaɗa ta daga gari zuwa gari. Waɗanda ba su rubuta AlKur’ani ba kuma ba su aika shi daga gari zuwa gari ba, ba za a haramta musu ceto na Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - idan sun kasance masu imani da shi, masu bin shari'arsa, Da wannan ƙarya guda ɗaya a cikin wannan wasiyya, tana isa da kanta don nuna ɓatancinta da ƙaryar wanda ya yaɗa ta, da rashin kunya da wawancinsa da nisansa daga sanin abin da Manzo - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zo da shi na shiriya ba.

A dai cikin wannan wasiyyar - ban da abinda aka ambata - akwai wasu abubuwa kuma daban da suke nuna ɓacinta da kuma ƙaryarta. Da wanda ya ƙirƙireta zai rantse sau dubu ko sama da haka akan ingancinta, haka da ace zai kirawa kansa mafi girman azaba da mafi tsananin uƙuba akan cewa shi mai gaskiya ne; da ba zai zama mai gaskiya ba, ba kuma zata taɓa zama ingantacciya ba, bari dai, ita wallahi thumma wallahi tana cikin mafi girma da mafi munin ɓarna, mu kuma muna shaidawa Allah - tsarki ya tabbata a gare Shi - da duk Mala’ikun da suke tare da mu. Duk wanda ya karanta wannan rubutu daga cikin musulmai - shaida ce da za mu gabatar da ita ga Ubangijinmu - Maɗaukakin sarki -: Cewa wannan wasiyya ƙarya ce da ƙirƙira akan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - Allah Ya kunyatar da wanda ya ƙirƙireta kuma Yayi masa hukunci da abinda ya cancanta.

Bayan abinda aka ambata, al'amurra da dama a cikin abinda aka ambata a nassinta (wasiyyar) suna nuni akan ƙaryar wannan wasiyya da kuma ɓacinta, daga ciki:

Lamari na farko: Maganarsa a cikinta (Domin daga Juma’a zuwa Juma’a mutum dubu ɗari da sittin ne suka rasu ba akan addinin Musulinci ba); domin wannan yana cikin ilimin gaibu, kuma Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabata a gare shi -wahayi ya yanke masa bayan rasuwarsa, kuma a rayuwarsa bai san gaibu ba, to ya bayan mutuwarsa; saboda faɗin Allah - tsarki ya tabbata a gare Shi -:

﴿قُل لَّآ أَقُولُ لَكُمۡ عِندِي خَزَآئِنُ ٱللَّهِ وَلَآ أَعۡلَمُ ٱلۡغَيۡبَ...﴾

{Ka ce: Ba zance muku ina da taskokin Allah ba kuma ban san gaibu ba} [al-An'am: 50] Da faɗinSa - Maɗaukakin Sarki -:

﴿قُل لَّا يَعۡلَمُ مَن فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ ٱلۡغَيۡبَ إِلَّا ٱللَّهُ...﴾

{Ka ce: wanda suke sammai da ƙassai basu san gaibu ba sai Allah} [al-Naml: 65], Ya zo cikin ingantaccen hadisi daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: Ya ce: Za a kore wasu mutane daga tafkina a ranar Alƙiyama, sai in ce: Ya Ubangiji! Abokaina, abokaina, sai a ce mini: Lallai ba ka san abin da suka aikata a bayanka ba. Sai in ce kamar yadda bawan kirki ya ce: 'Kuma nã kasance mai shaida a kansu matuƙar nã dawwama a cikinsu, sa'an nan a lõkacin da Ka karɓi raina Kã kasance Kai ne mai tsaro a kansu, kuma Kai a kan dukkan kõme, Halartacce ne.' [Al-Ma'ida: 117]

Lamari na biyu: - Daga lamurran da suke nuna ɓacin wannan wasiyya da kuma cewa ita ɗin ƙage ce -: Faɗinsa a cikinta: (wanda ya rubuta ta yana talaka, Allah zai wadata shi, ko yana fama da bashi, Allah zai biya masa bashinsa, ko yana da zunubi Allah zai masa gafara da iyayen sa saboda albarkar wannan wasiyya) zuwa ƙarshenta. Wannan ma yana cikin manyan ƙarairayi, kuma dalilai sun bayyana ƙaryar wanda ya ƙirƙireta da kuma ƙarancin kunyarsa ga Allah da bayinSa; domin waɗannan lamurra uku ba sa samuwa da zarar an rubuta Alƙur'ani mai girma, to ta yaya zasu samu ga wanda ya rubuta wannan ɓataciyyar wasiyyar?! Kawai wannan mugun yana son ya yaudari mutane ne, da kuma jingina su da wannan wasiyya; har su rubuta ta kuma su jingina kansu da wannan falalar da ake iƙirari, su bar hanyoyin da Allah Ya shara'anta ga bayinSa, kuma Ya sanya su masu sadarwa zuwa ga wadatar zuci da biyan bashi, da gafarar zunubai, don haka muna neman tsari da Allah daga hanyoyin wulaƙanci da biyayya ga son zuciya da Shaiɗan.

Lamari na uku: - Daga lamurran da suke nuni akan ɓacin wannan wasiyyar -, faɗinsa a cikin wasiyyar: (wanda kuma bai rubuta ta ba cikin bayin Allah; fuskarta za ta yi baƙi a duniya da lahira). Wannan kuma yana daga cikin munanar ƙarya, kuma yana daga cikin bayyanannun hujjoji akan ɓacin wannan wasiyyar, da kuma ƙaryar wanda ya ƙirƙireta, ta yaya zai yiwu a hankalin mai hankali ya rubuta wannan wasiyyar da wani mutum wanda ba’a san shi ba a ƙarni na goma sha huɗu yazo da ita, yana ƙirƙirar ta ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - kuma yana da'awar cewa wanda bai rubuta ta ba fuskarsa za ta yi baƙi a duniya da lahira, kuma wanda ya rubuta ta zai zama mai arziƙi bayan talauci, kuma zai tsira daga bashi bayan ya taru a kansa, kuma za a gafarta masa abin da ya aikata na zunubai!!

Tsarki ya tabbata gareka! wannan ƙarya ce babba!! Lallai hujjoji na gaskiya suna shaidawa da ƙaryar wannan maƙaryaci, da girman ƙarfin zuciyarsa akan Allah, da ƙarancin kunyarsa ga Allah da mutane, ga waɗannan al'ummai masu yawa ba su rubuta ta ba, fuskarsu ba ta yi baƙi ba, kuma ga wannan taro mai yawa wanda babu mai ƙirga su sai Allah sun rubuta ta sau da yawa, amma ba a biya basussukansu ba, kuma talaucinsu bai gushe ba, muna neman tsarin Allah ga karkacewar zukata, da ɓarnar zunubai, Waɗannan siffofi da sakamakon shari'a mai daraja ba ta zo da su ba ga wanda ya rubuta mafi kyawun littafi kuma mafi girma wato Alƙur'ani mai girma, to yaya zasu samu ga wanda ya rubuta wasiyya ta ƙarya mai ɗauke da nau'o'in ƙarya, da jimloli masu yawa daga nau'o'in kafirci, tsarki ya tabbata ga Allah!! Ya mamakin haƙurinSa ga wanda Yayi masa ƙarya.

Lamari na huɗu: - Daga lamurran da suke nuni akan cewa wannan wasiyyar tana daga mafi girman ɓarna, kuma mafi bayyanar ƙarya -: Faɗinsa a cikinta (wanda kuma gasgata ta to zai tsira daga azabar wuta, wanda kuma ya ƙaryata ta ya kafirta), Wannan - kuma - yana daga cikin mafi girman jarumtar yin ƙarya, da kuma mafi munin ɓata, wannan maƙaryaci yana kiran dukkan mutane, da su gaskata da ƙaryarsa, yana iƙirarin cewa da hakan za su tsira daga azabar wuta, kuma cewa duk wanda ya ƙaryata ta zai kafirta, Haƙiƙa - Wallahi- wannan maƙaryacin ya yi ƙage mai girma ga Allah, kuma - Wallahi - ya faɗi abinda ba gaskiya ba ne. Lalle wanda ya gasgata ta shi ne wanda ya cancanci ya kasance kafiri ba wai wanda ya ƙaryata ta ba; domin ita (wasiyyar) fa ƙage ce kuma ɓarna ce kuma ƙarya ce da ba ta da tushe na inganci. Kuma mu muna shaidawa Allah akan cewa wasiyyar ƙarya ce, kuma wanda ya ƙirƙire ta maƙaryaci ne, yana son ya shar’anta wa mutane ne abinda Allah bai yi izini ba. Ya shigar musu abinda baya cikin addininsu, kuma haƙiƙa Allah Ya cika addinin, Ya kuma cika shi ga wannan al’ummar tun kafin wannan ƙirƙiren da ƙarni goma sha huɗu. Ku faɗaka: Ya ku masu karatu da ‘yan uwa, kada ku kuskura ku gasgata irin waɗannan ƙirkire-ƙirƙiren, kada a samu masu rurutata a cikinku, domin ita gaskiya tana da haske ba ya rikicewa mai nemanta, ku nemi gaskiya da dalilinta, ku tambayi malamai akan abinda ya shige muku duhu, kada ku ruɗu da rantsuwar maƙaryata. Haƙiƙa shaiɗan la’ananne ya rantsewa iyayenku (Annabi) Adamu da (Nana) Hauwa'u akan cewar shi mai nasiha ne a gare su, alhali kuwa shine ne mafi girman maha’inta kuma mafi ƙaryar maƙaryata, kamar yadda Allah Ya hakaito hakan daga gare shi, sai (Allah) - Mai tsarki da ɗaukaka - Ya ce:

﴿وَقَاسَمَهُمَآ إِنِّي لَكُمَا لَمِنَ ٱلنَّٰصِحِينَ21﴾

{Kuma ya yi musu rantsuwa; Lalle ne , a gare ku, haƙĩƙa, daga mãsu nasĩha ne} [al-A'araf: 21]. Ku kiyaye shi, ku kiyayi mabiyansa daga masu ƙirƙire-ƙirƙire, sau nawa shi da su suke ta rantse-rantse na ƙarya da alƙawura na yaudara da maganganu da aka ƙawata, domin ruɗarwa da ɓatarwa! Amma abinda wannan me ƙirƙiren ya ambata na bayyanar munanan abubuwa; to wannan al’amari ne da yake a waƙi'i, Alƙur'ani mai girma da Sunnah mai tsarki tabbas sun tsawatar a kansu matuƙar tsawatarwa, kuma a cikinsu ne (Alƙur’ani da Sunnah) shiriya take da kuma wadatarwa.

Amma abinda ya anbata na alamomi alƙiyama, to haƙiƙa hadisai sun yi bayani dalla dalla na abinda zai kasance na alamomin alƙiyama, kuma Alƙur'ani mai girma ya yi nuni akan wasu daga ciki, duk wanda yake son ya san haka zai same shi a mahallinsa a cikin littattafan Sunnah, da littattafan ma'abota ilimi da imani, mutane ba su da buƙatar bayanin irin wannan me ƙirƙiren ƙaryar da kuma ruɗarwarsa da yadda ya cuɗa gaskiya da ƙarya. Allah Ya tsare ni Ya tsare ku da sauran musulmai daga sharrin shaiɗanu, da fitinar masu ɓatarwa, da karkacewar karkatattu, da ruɗarwar maƙiya Allah maɓarnata, waɗanda suke son su bice hasken Allah da bakunansu, su rikitarwa mutane addinin su, alhali kuwa Allah Mai cika haskenSa ne, kuma Mai taimakon addininSa ne, koda kuwa maƙiya Allah sun ƙi daga cikin shaiɗanu da mabiyansu cikin kafirai da mulhidai. Muna roƙon Allah Ya kyautata halayan musulmai, Ya kuma yi musu baiwa da bin gaskiya da kuma tsayuwa a kanta, da kuma tuba ga Allah - tsarki ya tabbata a gare Shi - daga sauran zunubai, domin Shi Mai yawan karɓar tuba ne, kuma Mai yawan jin ƙai ne, kuma Mai iko ne akan dukkan komai. Kuma Allah Ya isar mana, kuma madalla da Wakili, babu dabara babu ƙarfi face da (nufin) Allah Maɗaukaki Mai girma.

Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, tsira da amincin Allah su tabbata ga bawanSa kuma ManzonSa mai gaskiya amintacce, da alayensa da sahabbansa da mabiyansa da kyautatawa har zuwa ranar sakamako.

 

***

 


بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ

SAƘO NA TARA

Hukuncin sihiri da bokanci da abinda yake da alaƙa da su18

Godiya ta tabbata ga Allah Shi kaɗai, tsira da aminci su tabbata ga wanda babu wani Annabi a bayansa, bayan haka:

Duba da yawaitar ‘yan tsibbu a shekarun baya bayan nan waɗanda suke da'awar cewar suna bada magani, sunayin magani ta hanyar sihiri ko bokanci, da kuma yadda suka watsu a wasu garuruwan, da kuma yadda suke ribatar duhun kai na waɗanda jahilci ya rinjaye su, sai na ga yana daga babin nasiha ga Allah da bayinSa da in yi bayanin abinda hakan na daga da hatsari mai girma ga Musulinci da musulmai, saboda abinda yake cikin sa na dogaro ga wanin Allah - Maɗaukakin Sarki -da saɓawa umarninSa da umarnin ManzonSa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -.

Sai nake cewa, ina mai neman taimakon Allah - Maɗaukakin Sarki -: Neman magani ya halatta da ittifaƙin malamai. Saboda haka ya halatta musulmi ya je wurin likitan ciki ko tiyata ko jijiya ko makamantan haka domin ya duba shi ya kuma ba shi magani irin wanda ya dace da shi na magunguna da shari'ah ta halatta, gwargwadon iliminsa na likitancin; domin hakan yana ɓangaren riƙo da sabubba da aka saba, kuma baya kore tawakkali ga Allah. Haƙiƙa Allah - Mai tsarki da ɗaukaka - Ya saukar da cuta kuma ya saukar da magani a tare da ita; wanda ya sani ya sani, wanda kuma bai sani ba to bai sani ba. Sai dai Shi (Allah) - tsarki ta tabbatar maSa - Bai sanya warakar bayinSa ba cikin abinda Ya haramta musu .

Ba ya halatta ga mara lafiya ya tafi wurin bokaye waɗanda suke da'awar wai sun san abubuwan gaibu; domin ya san rashin lafiyar sa daga gare su, kamar yadda bai halatta ya gasgata su cikin abinda suke bashi labari da shi ba, domin su suna magana ne a fagauniyar gaibu, ko su kirawo aljanu domin su nemi taimakon su akan abinda suka nufata, waɗannan hukuncinsu shine kafirci da ɓata idan suka yi da'awar sanin gaibu,

Haƙiƙa Muslim ya ruwaito a Sahihinsa cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: (Duk wanda ya je wajan ɗan duba kuma ya tambaye shi game da wani abu, ba za’a karɓi sallarsa ta kwana arba’in ba)

(Duk wanda yaje wajen boka, sai ya gasgata shi cikin abinda yake cewa; to haƙiƙa ya kafirta da abinda aka saukarwa (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -) «Duk wanda yaje wajen boka, sai ya gasgata shi cikin abinda yake cewa; to haƙiƙa ya kafirta da abinda aka saukarwa (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -» Abu Dawud ne ya ruwaito shi, kuma ma'abota (littattafan) Sunan su huɗu sun fitar da shi, kuma Hakim ya inganta shi daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da lafazin: Duk wanda ya je wajen ɗan duba ko boka sai ya gasgata shi akan abinda yake cewa; to haƙiƙa ya kafirta da abinda aka saukarwa (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -.

Daga Imran ɗan Husain - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: (Baya tare da mu duk wanda ya yi camfi ko aka yi masa, ko yayi bokanci ko aka yi masa, ko yayi sihiri (asiri) ko aka yi masa; kuma duk wanda yaje wajen boka kuma ya gasgata shi akan abinda ya ke faɗa; to haƙiƙa ya kafircewa abinda aka saukarwa Annabi Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -) Bazzar ne ya ruwaito shi da isnadi mai kyau.

A cikin waɗannan hadisan masu daraja: akwai hani akan zuwa wurin ƴan duba da bokaye da matsafa da ire irensu, da tambayarsu da gasgata su, kuma a cikin su akwai narkon azaba akan hakan;

Don haka, ba ya halatta a ruɗu da gaskiyar su a wasu abubuwa, ko yawan jama'ar da suke zuwa zuwa wurinsu, domin jahilai ne ba ya halatta a ruɗu da su, domin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - tabbas ya hana zuwa wurin su da tambayar su da gaskata su, saboda abinda yake cikin hakan daga mummunan abu mai girma, da kuma hatsari babba da kuma mummunan ƙarshe, kuma domin cewa su maƙaryata ne fajirai,

Kamar yadda yake a cikin waɗannan hadisan: Akwai dalilai akan kafircin boka da matsafi; domin suna da'awar sanin gaibu; hakan kuma kafirci ne, da kuma cewa ba sa kaiwa inda suke so sai sun yi anfani da aljanu da kuma bauta musu koma bayan Allah; wannan kuwa kafircewa Allah ne kuma shirka ne da shi - tsarki ya tabbatar maSa -.

Wanda yake gasgata maganarsu ta sanin gaibu yana kasancewa irinsu ne, da duk wanda ya karɓi waɗannan al’amurra daga wanda yake ta’ammuli da su; to haƙiƙa Manzon Allah ya barranta da shi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -.

Kamar yadda bai halatta ga musulmi: Ya sallamawa abinda suke raya cewa magani ne ba, kamar surƙulle da ɗalasimai ko zuba harsashi, da makamancin haka na camfe-camfe da suke yi, domin hakan yana cikin bokanci da rikitar da mutane, to duk wanda ya yarda da hakan to haƙiƙa ya taimaka musu akan ɓarnar su da kuma kafircinsu.

Kamar yadda bai halatta ga kowanne musulmi ya je wurinsu ba; dan ya tambayesu wanda zai auri ɗan sa ko wani mukusancin sa, ko mai zai kasance tsakanin ma’auratan da iyalan su na daga so da aminci, ko ƙiyayya da rabuwa da makamantan haka; Domin wannan na daga gaibu wanda babu wanda ya san shi sai Allah - Mai tsarki da ɗaukaka -.

Abinda yake wajibi akan shugabanni da ‘yan Hisbah da sauran jama'a da suke da iko da mulki: Su hana zuwa wurin bokaye da ‘yan duba da makamantansu, su kuma hana wanda yake aikata wani abu na hakan a kasuwanni da sauransu, da yi musu inkarin hakan mafi tsananin inkarin, da kuma hana wanda yake zuwa wurinsu.

Haka nan sihiri: Domin shima yana cikin abubuwan da aka haramta na kafirc; kamar yadda Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya ce dangane da Mala’iku biyun nan:

﴿...وَمَا يُعَلِّمَانِ مِنۡ أَحَدٍ حَتَّىٰ يَقُولَآ إِنَّمَا نَحۡنُ فِتۡنَةٞ فَلَا تَكۡفُرۡۖ فَيَتَعَلَّمُونَ مِنۡهُمَا مَا يُفَرِّقُونَ بِهِۦ بَيۡنَ ٱلۡمَرۡءِ وَزَوۡجِهِۦۚ وَمَا هُم بِضَآرِّينَ بِهِۦ مِنۡ أَحَدٍ إِلَّا بِإِذۡنِ ٱللَّهِۚ وَيَتَعَلَّمُونَ مَا يَضُرُّهُمۡ وَلَا يَنفَعُهُمۡۚ وَلَقَدۡ عَلِمُواْ لَمَنِ ٱشۡتَرَىٰهُ مَا لَهُۥ فِي ٱلۡأٓخِرَةِ مِنۡ خَلَٰقٖۚ وَلَبِئۡسَ مَا شَرَوۡاْ بِهِۦٓ أَنفُسَهُمۡۚ لَوۡ كَانُواْ يَعۡلَمُونَ﴾

{Kuma ba su sanar da kõwa ba har sai sun ce: "Mũ fitina kawai ne, sabõda haka kada ka kãfirta," balle har su yi ta nẽman ilmin abin da suke rarrabẽwa tsakãnin mutum da mãtarsa da shi daga gare su. Kuma su (mãsu yin sihirin) ba su zama mãsu cũtar da kõwa da shi ba, fãce da iznin Allah. Kuma suna nẽman ilmin abin da yake cũtar da su, kuma bã ya amfaninsu. Kuma lalle ne, haƙiƙa, sun sani, tabbas, wanda ya saye shi, bã ya da wani rabo a cikin Lãhira. Kuma tir da abin da suka sayar da rãyukansu da shi, dã sun kasance suna sani}. [al-Baƙara: 102].

Sai waɗannan ayoyi masu daraja suka yi nuni akan sihiri kafirci ne kuma matsafa suna raba mutum da matarsa, kamar yadda ayar ta yi nuni akan asiri ba ya tasiri da kansa a anfanarwa ko cutarwa, kawai yana tasiri ne da izinin Allah na kaunu abin ƙaddarawa; domin Allah -Mai tsarki da ɗaukaka - Shi ne Wanda Ya halicci alheri da sharri.

Kamar yadda ayar mai daraja ta yi nuni akan waɗanda suke koyon sihiri, kaɗai suna koyon abinda yake cutar da su ne ba ya anfanar da su, kuma ba su da kowanne rabo a wurin Allah, (wato kowanne kaso ko nasibi), wannan kuwa narko ne na azaba mai girma da yake nuni akan tsananin asarar su a duniya da lahira, kuma su sun sayar da kawunansu da mafi ƙarancin farashi, saboda haka ne Allah - Mai tsarki da ɗaukaka - Ya aibata su da faɗinSa:

﴿...وَلَبِئۡسَ مَا شَرَوۡاْ بِهِۦٓ أَنفُسَهُمۡۚ لَوۡ كَانُواْ يَعۡلَمُونَ﴾

{Kuma tir da abin da suka sayar da rãyukansu da shi, dã sun kasance suna sani}, [al-Baƙara: 102]. 'Shira’u' anan ma’anarsa sayarwa.

Kuma haƙiƙa cutarwar ta girmama, kuma lamarin yayi tsanani ga waɗannan maƙaryatan, waɗanda suka gaji wannan ilimin daga mushirikai, suka rikitar da masu raunin hankula, da su, to lalle mu ga Allah muke, kuma mu zuwa gare Shi muke komawa, Allah Ya isar mana kuma madalla da Shi abin wakiltawa.

Muna rokon Allah lafiya da aminci daga sharrin matsafa da bokaye da sauran masu surƙulle, kuma muna rokon Shi - tsarki ya tabbatar maSa - Ya tsare musulmai daga sharrin su, kuma Ya datar da shugabannin musulmai da tsawatarwa daga gare su, da zartar da hukuncin Allah a kansu har bayi su huta daga cutarwar su da munanan ayyukan su, lalle Shi Mai yawan kyauta ne kuma Mai karamci.

Kuma lallai Allah - tsarki ya tabbatar maSa - Ya shar’antawa bayinSa abinda za su kare kansu da shi daga sharrin sihiri kafin afkuwar sa, kuma Ya yi musu bayanin abinda za su yi magani da shi bayan afkuwar sa, wannan rahamar Sa ce gare su, da kuma kyautatawar Sa gare su, da kuma cika ni’imar Sa a gare su.

Ga bayanin waɗansu abubuwa da mutum zai kaucewa haɗarin asiri kafin afkuwar sa, da kuma abubuwan da za’a yi magani da su bayan afkuwar sa na halastattun abubuwa a shari'ah, ga bayanin nan kamar haka:

Na farko: Abinda za’a kaucewa haɗarin asiri kafin faruwarsa: Mafi muhimmanci kuma wanda ya fi amfani shi ne: Kariya ta hanyar yin zikirai shar’antattu, da addu’o’i da kuma abubuwan neman tsari da aka ruwaito, daga cikin haka: Karatun Ayatul Kursiyy, - ita ce aya mafi girma a cikin Alƙur’ani mai girma -, bayan sallamewa daga kowacce sallah ta farilla, ita ce faɗinSa - tsarki ya tabbatar maSa:

﴿ٱللَّهُ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ ٱلۡحَيُّ ٱلۡقَيُّومُۚ لَا تَأۡخُذُهُۥ سِنَةٞ وَلَا نَوۡمٞۚ لَّهُۥ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِۗ مَن ذَا ٱلَّذِي يَشۡفَعُ عِندَهُۥٓ إِلَّا بِإِذۡنِهِۦۚ يَعۡلَمُ مَا بَيۡنَ أَيۡدِيهِمۡ وَمَا خَلۡفَهُمۡۖ وَلَا يُحِيطُونَ بِشَيۡءٖ مِّنۡ عِلۡمِهِۦٓ إِلَّا بِمَا شَآءَۚ وَسِعَ كُرۡسِيُّهُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَۖ وَلَا يَـُٔودُهُۥ حِفۡظُهُمَاۚ وَهُوَ ٱلۡعَلِيُّ ٱلۡعَظِيمُ255﴾

{Allah, bãbu wani Ubangiji fãce Shi, Rãyayye, Mai tsayuwa da kõme, gyangyaɗi bã ya kãma Shi, kuma barci bã ya kãma Shi, Shi ne da abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasa. Wanene wanda yake yin cẽto a wurinSa, fãce da izninSa? Yana sanin abin da yake a gaba gare su da abin da yake a bãyansu. Kuma bã su kẽwayẽwa da kõme daga ilminSa, fãce da abin da Ya so. KursiyyunSa ya yalwaci sammai da ƙasa. Kuma tsare su bã ya nauyayarSa. Kuma Shi ne Maɗaukaki, Mai girma}. [al-Baƙara: 255], Da kuma karanta ta dai a lokacin barci, haƙiƙa ya inganta daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: (Wanda ya Karanta Ayatul Kursiyy da daddare, to mai kiyayewa daga Allah ba zai gushe ba a gare shi, kuma shaiɗani ba zai zo kusa da shi ba har ya wayi gari).

Akwai daga cikin hakan karanta:

﴿قُلۡ هُوَ ٱللَّهُ أَحَدٌ1﴾

{Ka ce: "Shi ne Allah Makaɗaĩci."},

﴿قُلۡ أَعُوذُ بِرَبِّ ٱلۡفَلَقِ1﴾

{"Ka ce "ina neman tsari ga Ubangijin safiya"},

﴿قُلۡ أَعُوذُ بِرَبِّ ٱلنَّاسِ1﴾

{"Ka ce "Ina nẽman tsari ga Ubangijin mutãne."}, [al-Nas: 1]. A bayan kowacce sallah ta farilla. Da kuma karatun waɗannan surorin uku, sau uku da a farkon rana bayan sallar asuba, da kuma farkon dare bayan sallar magariba.

Yana daga cikin hakan: Karanta ayoyi biyu na ƙarshen suratul Baƙarah a farkon dare, su ne faɗinSa - Maɗaukakin Sarki -:

﴿ءَامَنَ ٱلرَّسُولُ بِمَآ أُنزِلَ إِلَيۡهِ مِن رَّبِّهِۦ وَٱلۡمُؤۡمِنُونَۚ كُلٌّ ءَامَنَ بِٱللَّهِ وَمَلَٰٓئِكَتِهِۦ وَكُتُبِهِۦ وَرُسُلِهِۦ لَا نُفَرِّقُ بَيۡنَ أَحَدٖ مِّن رُّسُلِهِۦۚ وَقَالُواْ سَمِعۡنَا وَأَطَعۡنَاۖ غُفۡرَانَكَ رَبَّنَا وَإِلَيۡكَ ٱلۡمَصِيرُ285﴾

[Manzon Allah yã yi ĩmãni da abin da aka saukar zuwa gare shi daga Ubangijinsa, da mũminai. Kõwanensu yã yi ĩmãni da Allah, da mala'ikunSa, da littattafanSa, da manzanninSa. Bã mu rarrabẽwa a tsakãnin daya daga manzanninSa. Kuma (mũminai) suka ce: "Mun ji kuma mun yi dã'a; (Muna nẽman) gãfararKa, yã Ubangijinmu, kuma zuwa a gare Ka makõma take." Har zuwa ƙarshen surar.

Saboda abinda ya inganta daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - cewa shi ya ce: (Wanda ya karanta ayoyi biyu na ƙarshen Suratul Baƙara da daddare sun ishe shi), Abin nufi, Allah ne Masani: Sun ishe shi daga dukkan mummunan abu. Yana daga cikin hakan yawaita neman tsari da (Kalmomin Allah cikakku daga sharrin Abinda Ya halitta), a dare da rana, da lokacin sauka a kowanne irin masauki, a gini ne ko a sahara, ko a sararin samaniya ne ko a teku, saboda faɗin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: (Duk wanda ya sauka a wani masauki sai ya ce: Ina neman tsari da kalmomin Allah cikakku daga sharrin abinda Ya halitta, babu abunda zai cuce shi har sai ya tashi daga wannan masaukin).

Yana daga cikin wannan: Shine Musulmi ya ce a farkon rana (da safe) da kuma farkon dare (da daddare) ya faɗa sau uku: (Da sunan Allah, wanda da sunanSa wani abu a sama ko a ƙasa bazai cutu ba, Shi ne Mai ji kuma Masani)

Saboda ingancin kwaɗaitarwa akan hakan, daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, kuma hakan dalili ne na samun kuɓuta daga dukkan mummunan abu.

Na biyu: Abinda za’a magance sihiri da shi bayan afkuwar sa, to wannan shi ma yana kasancewa ne da abubuwa kamar haka:

Na daya: Yawaita ƙanƙan dakai ga Allah, da kuma roƙonSa - tsarki ya tabbatar maSa - da Ya yaye cutar Ya kuma kawar da tsananin.

Na biyu: Yin kokari wurin sanin inda aka sanya asirin a ƙasa ne ko dutse ko wani wuri, idan aka sani sai a fito da shi sai a warware shi, to an lalata sihirin, wannan kuwa yana cikin mafi anfanin maganin sihiri,

Na uku: Yin ruƙyah da zikirai da wuridai shar’antattu, kuma suna da yawa; daga ciki:

Abinda ya tabbata a maganar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: (Ya Allah, Ubangijin mutane Ka tafiyar da tsananin, Ka warkar, Kai ne Mai warkarwa, babu waraka sai warakarKa, warakar da ba ta barin wata larura) Zai faɗa sau uku,

Akwai daga cikin hakan: (Addu’ar) ruƙya wacce Mala’ika Jibirilu ya yi wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ruƙya da ita. Itace faɗin sa: (Da sunan Allah nake maka ruƙya, daga dukkan wani abu da zai cutar da kai, daga sharrin kowane irin rai ko idon mai hassada, Allah Ya warkar da kai, da sunan Allah nake maka ruƙya) Ya kuma maimaita hakan sau uku.

Yana daga cikin hakan - Kuma wannan magani ne mai anfani ga mutum wanda aka hana masa kusantar iyalin sa -: ya sami ganyen magarya koraye guda bakwai, sai ya dandaƙa su da dutse ko makamancin sa sai ya zuba a cikin ƙwarya sai kuma ya zuba ruwa akan sa wanda zai ishe shi yin wanka, sai ya karanta a ciki:

Ayatul-kursiyyi

﴿قُلۡ يَٰٓأَيُّهَا ٱلۡكَٰفِرُونَ1﴾

{Ka ce: "Ya kũ kãfirai!"}, [al-Kafirun: 1], da kuma

﴿قُلۡ هُوَ ٱللَّهُ أَحَدٌ1﴾

{Ka ce: "Shi ne Allah Makaɗaĩci."}, [al-Ikhlas: 1], da kuma

﴿قُلۡ أَعُوذُ بِرَبِّ ٱلۡفَلَقِ1﴾

{"Ka ce "ina neman tsari ga Ubangijin safiya"}, [al-Falaƙ: 1], da

﴿قُلۡ أَعُوذُ بِرَبِّ ٱلنَّاسِ1﴾

{"Ka ce "Ina nẽman tsari ga Ubangijin mutãne."}, [al-Nas: 1].

Da ayoyi da suke maganar sihiri a Suratul A’araf, su ne faɗinSa -tsarki ya tabbatar maSa -:

﴿وَأَوۡحَيۡنَآ إِلَىٰ مُوسَىٰٓ أَنۡ أَلۡقِ عَصَاكَۖ فَإِذَا هِيَ تَلۡقَفُ مَا يَأۡفِكُونَ117 فَوَقَعَ ٱلۡحَقُّ وَبَطَلَ مَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ118 فَغُلِبُواْ هُنَالِكَ وَٱنقَلَبُواْ صَٰغِرِينَ119﴾

{Kuma Muka yi wahayi zuwa ga Mũsã cẽwa: "Ka jẽfa sandarka." Sai gã ta tanã lãƙumar abin da suke ƙarya da shi!.Gaskiya ta auku, kuma abin da suke aikatãwa ya ɓãci.Sai aka rinjãye su a can, kuma suka jũya sunã ƙasƙantattu.},

Gaskiya ta auku, kuma abin da suke aikatãwa ya ɓãci.

Sai aka rinjãye su a can, kuma suka jũya sunã ƙasƙantattu. [al-A'araf: 117-119].

Da kuma ayoyi a Suratu Yunus, su ne faɗinSa - tsarki ya tabbatar maSa -:

﴿وَقَالَ فِرۡعَوۡنُ ٱئۡتُونِي بِكُلِّ سَٰحِرٍ عَلِيمٖ79 فَلَمَّا جَآءَ ٱلسَّحَرَةُ قَالَ لَهُم مُّوسَىٰٓ أَلۡقُواْ مَآ أَنتُم مُّلۡقُونَ80 فَلَمَّآ أَلۡقَوۡاْ قَالَ مُوسَىٰ مَا جِئۡتُم بِهِ ٱلسِّحۡرُۖ إِنَّ ٱللَّهَ سَيُبۡطِلُهُۥٓ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يُصۡلِحُ عَمَلَ ٱلۡمُفۡسِدِينَ81 وَيُحِقُّ ٱللَّهُ ٱلۡحَقَّ بِكَلِمَٰتِهِۦ وَلَوۡ كَرِهَ ٱلۡمُجۡرِمُونَ82﴾

{Kuma Fir'auna ya ce: "Ku zo mini da dukan masihirci, masani."To, a lõkacin da masihirta suka je, Mũsã ya ce musu,"Ku jẽfa abin da kuke jẽfãwa."To, a lõkacin da suka jẽfa, Mũsa ya ce: "Abin da kuka zo da shi sihiri ne. Lalle ne Allah zai ɓãta shi. Haƙĩƙa Allah bã Ya gyãra aikin maɓarnata."Kuma Allah Yanã tabbatar da gaskiya da kalmõmin Sa, kõ dã mãsu laifi sun ƙi."},

To, a lõkacin da masihirta suka je, Mũsã ya ce musu,"Ku jẽfa abin da kuke jẽfãwa."80

To, a lõkacin da suka jẽfa, Mũsa ya ce: 'Abin da kuka zo da shi sihiri ne. Lalle ne Allah zai ɓãta shi. Haƙĩƙa Allah bã Ya gyãra aikin maɓarnata.'

Kuma Allah Yanã tabbatar da gaskiya da kalmõmin Sa, kõ dã mãsu laifi sun ƙi. [Yunus: 79-82].

Da kuma ayoyi da suke cikin Suratu Ɗaha:

﴿قَالُواْ يَٰمُوسَىٰٓ إِمَّآ أَن تُلۡقِيَ وَإِمَّآ أَن نَّكُونَ أَوَّلَ مَنۡ أَلۡقَىٰ65 قَالَ بَلۡ أَلۡقُواْۖ فَإِذَا حِبَالُهُمۡ وَعِصِيُّهُمۡ يُخَيَّلُ إِلَيۡهِ مِن سِحۡرِهِمۡ أَنَّهَا تَسۡعَىٰ66 فَأَوۡجَسَ فِي نَفۡسِهِۦ خِيفَةٗ مُّوسَىٰ67 قُلۡنَا لَا تَخَفۡ إِنَّكَ أَنتَ ٱلۡأَعۡلَىٰ68 وَأَلۡقِ مَا فِي يَمِينِكَ تَلۡقَفۡ مَا صَنَعُوٓاْۖ إِنَّمَا صَنَعُواْ كَيۡدُ سَٰحِرٖۖ وَلَا يُفۡلِحُ ٱلسَّاحِرُ حَيۡثُ أَتَىٰ69﴾

{Suka ce: "Ya Mũsã! Imma ka jefa, ko kuma mu kasance farkon mai jẽfawa."Ya ce: "Ã'a, ku jẽfa." Sai gã igiyoyinsu da sandunansu anã sũranta su a gare shi, daga sihirinsu, lalle sunã tafiya da sauri.Sai Mũsã ya ji tsõro a cikin ransa.Muka ce: "Kada ka ji tsõro. lalle kai ne mafi ɗaukaka.""Kuma ka jẽfa abin da ke a cikin hannun dãmanka, ta cafe abin da suka aikata. Lalle ne abin da suka aikata mãkircin masihirci ne kuma masihirci bã ya cin nasara a duk inda ya je."}.

Ya ce: "Ã'a, ku jẽfa." Sai gã igiyoyinsu da sandunansu anã sũranta su a gare shi, daga sihirinsu, lalle sunã tafiya da sauri.

Sai Mũsã ya ji tsõro a cikin ransa.

Muka ce: "Kada ka ji tsõro. lalle kai ne mafi ɗaukaka.

Kuma ka jẽfa abin da ke a cikin hannun dãmanka, ta cafe abin da suka aikata. Lalle ne abin da suka aikata mãkircin masihirci ne kuma masihirci bã ya cin nasara a duk inda ya je. [Daha: 65-69].

Bayan karanta abinda aka ambata a cikin ruwa, sai a sha kanfata uku , sai a wanke jiki da sauran, da wannan cutar za ta gushe da yardar Allah. Idan kuma an buƙaci a sake yi ya zama na biyu ko sama da haka to babu wani laifi, har dai cutar ta kau.

Waɗannan zikiran da addu’o’in neman tsari da kuma hanyoyin suna daga cikin mafi girman sabubba na kaucewa sharrin sihiri da wanin sa na nau’ukan sharri, kuma shi ne mafi girman makami na kawar da sihiri bayan ya afku; ga duk wanda ya kiyaye akan hakan da gaskiya da kuma imani da amincewa da Allah da dogaro da Shi, da kuma samun yalwar ƙirji na abinda suka yi nuni akan sa.

Wannan shi ne abinda bayanin sa ya sawwaƙa na abubuwan da ake kaucewa sihiri da su, kuma ake maganin sa da su, Allah Shine Mai datarwa.

Anan ne kuma za’a zo da wata mas’ala mai muhimmanci, wato magance sihiri ta hanyar matsafa, wanda yake cika ta hanyar kusanta ga aljanu ta hanyar yi musu yanka ko makamantan hakan na abubuwan kusanci; to wannan bai halatta ba; domin yana cikin aikin shaiɗan; kai yana ma cikin babbar shirka; Kamar yadda baya halatta a yi magani ba ta hanyar tambayar bokaye da masu duba da ‘yan tsibbu ba, da kuma aiki da abinda suke faɗa; domin ba sa yin imani, kuma su maƙaryata ne fajirai, suna da'awar sanin gaibu, suna ruɗar da mutane, kuma haƙiƙa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya tsoratar daga zuwa wurin su da tambayar su da kuma gasgata su, kamar yadda bayani ya gabata akan hakan a farkon wannan saƙon. Abinda yake wajibi kiyaye wa akan haka, domin ya inganta daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, an tambaye shi dangane al-Nushrah' sai ya ce: (Ita yana cikin aikin shaiɗan) Ahmad ne ya ruwaito shi da Abu Dawud da isnadi mai kyau.

Al-Nushrah: Ita ce warware sihiri daga wanda aka yi wa sihirin. Abinda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yake nufi a wannan maganar ta shi shine: al-Nushrah wacce mutanan Jahilyyah suke yi, itace: Neman matsafi da ya warware sihiri ko ya warware shi da wani sihirin irinsa daga wani mai sihirin daban.

To Amma warware shi ta hanyar ruƙyah da addu’o’in neman tsari da aka shar’anta da magunguna na halas to babu laifi akan hakan, kamar yadda ya gabata. Haƙiƙa babban malami Ibn al- Ƙayyim ya nassanta hakan, da Shaikh Abdurrahman ɗan Hassan a Fathul Majid - Allah Yayi musu rahama su biyun - , kuma da yawa wasu daban daga cikin ma'abota ilimi sun nassanta hakan.

Allah muke roƙo Ya datar da musulmai ga yayewa daga dukkan abin ƙi, Ya kuma tsare musu Addinin su, Ya azurta su fahimata a cikin sa, Ya kuma kare su daga dukkan abinda ya sabawa shari’ar Sa.

Tsira da amincin Allah su tabbata ga bawanSa kuma ManzonSa (Annabi) Muhammad da alayen sa da sahabban sa.

 

***

 


بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ

SAƘO NA GOMA:

Tsawatarwa akan gina masallatai a maƙabartu

Da sunan Allah, godiya ta tabbata ga Allah, tsira da aminci su tabbata ga Manzon Allah.

Bayan haka, haƙiƙa na ga wani abu da aka buga a fitowa ta uku a mujallar Rabiɗat al-Ulum al-Islamiyyah a babin: (Labaran Musulmai a wata): Lalle Rabiɗat al-Ulum al-Islamiyyah dake masarautar Hashimiyya ta ƙasar Jordan tana son gina wani masallaci a kan wani kogo da aka gano bada daɗewa ba a garin al-Raheeb, wanda shi ne kogon da ake cewa: Lalle (Ashabul kahf) mutanan kogo da bayaninsu ya zo a cikin Alƙur’ani mai girma sun kwanta a cikinsa.

Ya ƙare.

Duba da wajibcin nasiha ga Allah da kuma bayinSa, na ga in wajjahar da wata kalma a mujalla ɗin a karan kanta ta Rabiɗatul Ulumul Islamiyya dake masarautar Hashimiyya ta ƙasar Jodan, abinda ta ƙunsa: Nasihar Rabiɗah akan aikin da ta ƙuduri aniyar yi na gina masallaci a kogon da aka ambata; ba kuma komai ya kawo hakan ba sai domin yin gini akan ƙaburburan Annabawa da salihai da gurabensu na abinda shari’ar Musulinci cikakkiya tazo da shi na hani da kuma tsawatarwa akai, da kuma la’anar wanda ya aikata hakan; saboda kasantuwarsa hanyoyin shirka da wuce iyaka akan Annabawa da salihai. Abinda yake a waƙi'i mai shaida ne akan ingancin abinda shari’a ta zo da shi, kuma dalili ne akan lalle daga Allah - Maɗaukakin Sarki - take, kuma dalili ne maɗaukaki kuma hujja ta yankan shakku akan gaskiyar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - , a cikin abinda ya zo da shi daga wurin Allah ya kuma isarwa al’umma. Duk wanda yayi la’akari da halin da duniyar Musulinci take ciki, da kuma abinda ya faru na shirka da wuce iyaka; ta sanadiyar gina Masallatai a ƙaburbura, da girmamasu da yi musu shinfiɗa da kwalliya, da kuma samar da masu yi musu hidima, zai sami ilimi na yaƙini cewa hakan yana cikin hanyoyin shirka, kuma yana cikin kyawun shari'ar Musulinci hana hakan da kuma tsawatarwa akan ginin.

Yana daga cikin abinda yazo akan hakan, abinda Bukhari da Muslim suka ruwaito - Allah Yayi musu rahama -, daga Nana Aisha - Allah Ya yarda da ita ta ce: Ma’aikin Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Allah Ya tsinewa Yahudawa da Nasara, sun riƙi ƙaburburan annabawansu masallatai» Nana A'isha ta ce: Yana gargaɗi akan abin da suka aikata, ta ce: Badon haka ba da an fito da ƙabarinsa, banda ana jin tsoron a riƙe shi masallaci. Kuma acikin ingantattun littattafan hadisan nan biyu, cewa Ummu Salama da Ummu Habibah - Allah Ya yarda da su - sun ambatawa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - wata coci da suka gani a ƙasar Habasha, da kuma abinda yake cikinta na hotuna, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Waɗannan mutanan idan mutumin kirki ya mutu a cikinsu; sai su gina masallaci a kan ƙabarinsa, su kuma zana irin waɗancan hotunan a cikin sa, waɗancan su ne ashararan halitta a wajen Allah.

Da hadisin Jundub bin Abdullah - Allah Ya yarda ad shi - a cikin Sahih Muslim ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - kafin ya rasu da kwana biyar yana cewa: "Lalle ni ina barranta zuwa ga Allah ya kasance ina da badaɗayi daga cikinku, domin Allah - Madaukakin sarki - haƙiƙa Ya riƙe ni badaɗayi kamar yadda Ya riƙi (Annabi) Ibrahim badaɗayi da na kasance mai riƙon badaɗayi daga al'umma ta, da na riƙi Abubakar badaɗayi ku saurara, lallai waɗanda suka gabace ku sun kasance suna maida ƙaburburan Annabawan su da salihan su masallatai, ku saurara, kada ku maida kaburbura masallatai, lalle ni ina hanaku hakan". Hadisai a wannan babin suna da yawa.

Haƙiƙa manyan malaman Musulinci sun nassanto a fili daga dukkanin mazhabobi huɗu da wasun su akan hani na gina masallatai a maƙabartu kuma sun tsawatar akan hakan; domin aiki da sunnar Manzon Allah -tsira tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, da kuma nasiha da tsawatar da al’umma don kada ta faɗa a cikin abinda waɗanda suka gabace ta suka faɗa na masu wuce iyaka daga Yahuduwa da Nasara da makamantansu daga cikin ɓatattun wannan al’umma.

Abinda yake wajibi ga Rabiɗatul Ulumul Islamiyyah dake Jodan, da wanin su cikin musulmai shi ne ruƙo da sunnah, da kuma tafiya akan tsarin manyan malamai, da kuma tsawatarwa daga abinda Allah da ManzonSa suka tsawatar, to anan akwai gyaruwar bayi da rabautar su da kuma tsiran su a duniya da lahira. Haƙiƙa wasu daga cikin mutane sun alaƙanta faɗin Allah - Maɗaukakin Sarki - a wannan abin a ƙissar (Ashabul kagf) ƴan kogo:

﴿...قَالَ ٱلَّذِينَ غَلَبُواْ عَلَىٰٓ أَمۡرِهِمۡ لَنَتَّخِذَنَّ عَلَيۡهِم مَّسۡجِدٗا﴾

(Sai waɗanda suka yi rinjaye a kan lamarinsu suka ce lalle zamu riƙi masallaci a gare su) [Kahf: 21].

Amsa ga wannan: Shine a ce: Lallai Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ba da labari game da shugabanni da masu iko a wannan lokacin cewa sun faɗi wannan magana, kuma ba haka ba ne a matsayin yarda da tabbatarwa gare su, sai dai a matsayin zargi da aibu da kuma tsoratarwa daga aikinsu. Kuma yana nuni akan haka: Lalle Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - wanda shi aka saukarwa wannan ayar, kuma shi yafi kowa sanin fassarar ta, ya hana al’ummar sa riƙon masallatai a maƙabartu, ya tsawatar da su hakan, ya kuma la’anci gami da zargin wanda ya aikata hakan.

Inda hakan ya halatta, da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - bai kausasa ba, matuƙar kausasawa, ya kai matuƙa a hakan har ya la'anci wanda ya aikata hakan, ya kuma bada labarin cewa shi yana cikin ashararan halittu a wurin Allah - Mai girma da ɗaukaka -, to wannan kuwa akwai isa da wadatuwa a cikin sa ga duk mai neman gaskiya. Da zamu ƙaddara cewa riƙon masallatai a maƙabartu ya halatta ga waɗanda suka gabace mu; to ai bai halatta a garemu mu yi koyi da su ba akan hakan, domin shari’armu ta shafe shari’ar da ta gaba ce ta, kuma Manzommu - tsira da aminci su tabbata a gare shi -, shine cikamakin Manzanni, kuma shari’ar sa cikakkiya ce kuma gamammiya, kuma haƙiƙa ya hana mu mu riƙi masallatai akan maƙabartu, kuma baya halatta a garemu mu saɓa masa, ya wajaba muyi masa biyayya da ruƙo da abinda ya zo da shi da barin abinda ya saɓawa hakan na shari’o'in da suka gabata, da al’adu waɗanda masu aikatasu suke ganin kyawun su; domin babu abinda ya cika kamar shari’ar Allah, kuma babu wata shiriya mafi kyau kamar shiriyar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi-.

Allah nake roƙo da Ya datar damu da ɗaukacin musulmai da tabbata akan AddininSa, da kuma riƙo da Shari'ar ManzonSa (annabi) Muhammad - tsira da aminci su tabbata a gare shi -; a cikin maganganu da ayyuka, a bayyane da a ɓoye, da kuma a cikin dukkan al'amura har mu haɗu da Allah - Mai girma da ɗaukaka -, lallai Shi Mai ji ne kuma Makusanci.

Tsira da amincin Allah su tabbata ga bawanSa kuma ManzonSa (annabi) Muhammad da alayensa da sahabbansa da waɗanda suka bi shiriyarsa har zuwa ranar sakamako.

 

 

***

 


بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ

SAƘO NA GOMA SHA ƊAYA:

Binne matattu a cikin masallatai

Da sunan Alah, dukkan godiya ta tabbata ga Allah, tsira da amincin Allah su tabbata ga manzon Allah, da alayansa da duk wanda ya yi koyi da shiriyarsa. Bayan haka:

Haƙiƙa na gani a Jaridar Khartoum da aka buga a 17/4/1415 bayan hijira, sai na samu a cikinta an buga wani bayani game da binne Mallam Muhammad al-Hassan al-Idrisi a kusa da mahaifinsa a cikin masallacinsu a birnin Omdurman… izuwa ƙarshe.

Saboda abinda Allah Ya wajabta na yin nasiha ga musulmai da bayanin hana mummunan aiki, na ga dacewar in faɗakar akan binne mamata a cikin masallatai abune da bai halatta ba, kai yana ma cikin hanyoyin shirka, yana kuma cikin ayyukan Yahudawa da Nasara, waɗanda Allah Ya aibata su a kansu, kuma manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya la’ance su, kamar yadda yake a cikin Bukhari da Muslim daga Nana Aisha - Allah Ya yarda da ita - daga annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - cewa shi ya ce: «Allah Ya tsinewa Yahudawa da Nasara, sun riƙi ƙaburburan Annabawansu masallatai», Ya zo cikin Sahihin Muslim daga Jundub ɗan Abdullahi daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ku Saurara lallai cewa waɗanda suka gabace ku sun kasance suna riƙar ƙaburburan annabawansu da mutanen kirkinsu masallatai, ku saurara kada ku riƙi ƙaburbura masallatai, lallai ni na hanaku yin hakan". Hadisai da suka zo da wannan ma’anar suna da yawa.

Abinda yake wajibi akan musulmai a kowanne wuri- shugabanni da mabiya-: Suji tsoron Allah su kuma kiyayi abinda aka hana, su binne mamatansu a wajan masallaci (ba a ciki ba) kamar yadda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da sahabbansa - Allah Ya yarda da su - suka kasance suna binne mamatansu a wajan masallaci, haka nan waɗanda suka biyo su da kyautatawa.

Amma samun ƙabarin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da sahabbansa biyu Abubakar da Umar - Allah Ya yarda da su - a cikin masallacinsa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ba zai zama dalili na a binne mamata a cikin masallatai ba; domin shi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - an binne shi ne a ɗakin Nana Aisha - Allah Ya yarda da ita-, sannan aka binne sahabbansa biyu tare da shi, a lokacin da Walid ɗan AbdulMalik ya faɗaɗa masallacin, sai ya shigar da ɗakin a cikinsa a farkon shekara ta ɗari daga hijira, kuma malamai a lokacin sunyi masa inkarin hakan, sai dai shi ba ya ganin hakan zai hana faɗaɗawar, kuma al’amarin a fili yake babu wata shubuha a cikinsa.

Da wannan ne, zai bayyana ga kowanne musulmi, cewa shi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da sahabbansa biyu - Allah Ya yarda da su - ba’a binne su a cikin masallaci ba, kuma shigar da su da aka yi saboda faɗaɗawar masallacin ba hujja ba ce akan halaccin binne mamata a masallatai; domin su ba a cikin masallacin suke ba, kawai su suna cikin ɗakinsa ne - tsira da aminci su tabbata a gare shi-, kuma aikin Walid bazai inganta ya zama hujja ga kowa a kan hakan ba, kawai hujja tana cikin Alƙur’ani ne da hadisi da ijima’in magabata al'umma (na ƙwarai) - Allah Ya yarda da su -, Ya kuma sanyamu cikin mabiyansu da kyautatawa.

Don nasiha da kuɓutar da wuyaye an rubuta shi da tacewa a: 14/5/1415 bayan Hijira.

Allah Shi ne majiɓincin datarwa. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabin mu Muhammad, da alayansa da sahabban sa, da mabiyan su da kyautatawa.

 

***

 


بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ

SAƘO NA GOMA SHA BIYU

Bayanin kafirci da ɓatan duk wanda ya raya cewa ya halatta ga wani ya kauce daga shari'ar (Annabi) Muhammadu - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi-.

Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, tsira da aminci su tabbata ga cikamakin Annabawa da Manzanni Annabinmu Muhammad, da alayansa da sahabbansa baki ɗaya.

Bayan haka: Haƙiƙa na karanta maƙalar da aka wallafa a jaridar al-Sharƙ al-Awsaɗ a lamba ta (5824) da kwanan wata 5/6/1415 H, wanda ya rubuta shine wanda ya kira kansa: Abdul Fattah al-Hayik, a ƙarƙashin taken: (Fahimtar da ba daidai ba).

Taƙaitaccen bayanin: Musuntawar da ya yi na abinda aka sani daga addinin Musulunci da wajibi, da nass da kuma ijma'i; wato gamewar aiken (annabi) Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi zuwa ga dukkan mutane, da iƙirarin cewa wanda bai bi (annabi) Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ba kuma bai yi masa biyayya ba kawai ya tsaya ya kasance Bayahude ko Banasara to yana kan addini na gaskiya, sannan ya yi suka ga Allah Ubangijin talikai - Tsarkakakke - a cikin hikimarsa na azabtar da kafirai da masu saɓo, ya sanya hakan cikin abinda ba shi da amfani.

Haƙiƙa ya tsayu wurin canza nassoshi na shari’a da sanya su ba'a bigiren su ba, ya kuma fassara su da son zuciyarsa, ya kuma kau da kai daga dalilai na shari’a da nassoshi da suke a bayyane waɗanda suke nuni akan gamewar manzancin (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, kuma suke nuni akan kafircin duk wanda ya ji shi kuma bai bi shi ba, kuma Allah ba Ya karɓar wani addini da ba Musulinci ba, da wanin haka na nassoshi fayyatattu waɗanda ya kau da kai daga gare su domin ya yaudari jahilai da maganarsa. Wannan abinda ya aikata kafirci ne kuma ridda ce daga Musulinci kuma ƙaryata Allah ne - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka -, kuma (ƙaryatawa ne) ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, kamar yadda duk wanda ya karanta maganar sa cikin malamai masu imani ya san hakan.

Abinda yake wajibi akan shugaba: Ya miƙa shi gaban kotu, domin ya tuba a kuma yi masa hukunci da abinda shari'ah mai tsarki ta hukunta.

Allah - Tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka - Ya bayyana gamewar saƙon annabi Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, da wajabcin binsa ga dukkan nauyaya biyu (mutum da aljann), kuma wannan ba zai ɓoyu ga wanda yake da ƙarancin ilimi cikin Musulmai ba.

Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce:

﴿قُلۡ يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ إِنِّي رَسُولُ ٱللَّهِ إِلَيۡكُمۡ جَمِيعًا ٱلَّذِي لَهُۥ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۖ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ يُحۡيِۦ وَيُمِيتُۖ فَـَٔامِنُواْ بِٱللَّهِ وَرَسُولِهِ ٱلنَّبِيِّ ٱلۡأُمِّيِّ ٱلَّذِي يُؤۡمِنُ بِٱللَّهِ وَكَلِمَٰتِهِۦ وَٱتَّبِعُوهُ لَعَلَّكُمۡ تَهۡتَدُونَ158﴾

{Ka ce: "Yã kũ mutãne! Lalle ne manzon Allah ne zuwa gare ku, gabã ɗaya. (Allah) Wanda Yake Shĩ ne da mulkin sammai da ƙasa; Bãbu wani abin bautawa da gaskiya fãce Shi, Yanã rãyarwa, kuma Yanã matarwa, sai ku yi ĩmãni da Allah da ManzonSa, Annabi, Ummiyyi, wanda yake yin ĩmãni da Allah da kalmominSa; ku bĩ shi, tsammãninku, kunã shiryuwa} [al-A'araf: 158]. Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿...وَأُوحِيَ إِلَيَّ هَٰذَا ٱلۡقُرۡءَانُ لِأُنذِرَكُم بِهِۦ وَمَنۢ بَلَغَ...﴾

{An saukar min da wannan Alƙur’anin dan na gargaɗe ku dashi da duk wanda zai isa zuwa gareshi} [al-An'am: 19]. Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿قُلۡ إِن كُنتُمۡ تُحِبُّونَ ٱللَّهَ فَٱتَّبِعُونِي يُحۡبِبۡكُمُ ٱللَّهُ وَيَغۡفِرۡ لَكُمۡ ذُنُوبَكُمۡۚ وَٱللَّهُ غَفُورٞ رَّحِيمٞ31﴾

{Ka ce: "Idan kun kasance kunã son Allah to, ku bĩ ni, Allah Ya sõ ku, kuma Ya gãfarta muku zunubanku} [Aal- Imran: 31]. Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿وَمَن يَبۡتَغِ غَيۡرَ ٱلۡإِسۡلَٰمِ دِينٗا فَلَن يُقۡبَلَ مِنۡهُ وَهُوَ فِي ٱلۡأٓخِرَةِ مِنَ ٱلۡخَٰسِرِينَ85﴾

{Kuma wanda ya nẽmi wanin Musulunci ya zama addini, to, bã zã a karɓa daga gare shi ba. Kuma shi a Lãhira yana daga cikin mãsu hasãra} [Aal- Imran: 85]. Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿وَمَآ أَرۡسَلۡنَٰكَ إِلَّا كَآفَّةٗ لِّلنَّاسِ بَشِيرٗا وَنَذِيرٗا...﴾

{Kuma ba Mu aika ka ba sai kana mai bãyar da bushãra, kuma mai gargaɗi} [Saba'i: 28]. Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿وَمَآ أَرۡسَلۡنَٰكَ إِلَّا رَحۡمَةٗ لِّلۡعَٰلَمِينَ107﴾

{Kuma Ba Mu aika ka ba sai kana mai rahama ga talikai} [al-Anbiyaa: 107]. Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿...وَقُل لِّلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡأُمِّيِّـۧنَ ءَأَسۡلَمۡتُمۡۚ فَإِنۡ أَسۡلَمُواْ فَقَدِ ٱهۡتَدَواْۖ وَّإِن تَوَلَّوۡاْ فَإِنَّمَا عَلَيۡكَ ٱلۡبَلَٰغُۗ وَٱللَّهُ بَصِيرُۢ بِٱلۡعِبَادِ﴾

{Kuma ka ce wa waɗanda aka bai wa littãfi da Ummiyyai: "Shin kun sallama?" To, idan sun sallama, haƙĩƙa, sun shiryu kuma idan sun jũya, to, kawai abinda ke kanka, shi ne iyarwa. Kuma Allah Mai gani ne ga bãyinSa}. [Aal Imran: 20]. Kuma - tsarki ya tabbatar maSa - Ya ce:

﴿تَبَارَكَ ٱلَّذِي نَزَّلَ ٱلۡفُرۡقَانَ عَلَىٰ عَبۡدِهِۦ لِيَكُونَ لِلۡعَٰلَمِينَ نَذِيرًا1﴾

{Albarka ta tabbata ga wanda Ya saukar da (Littãfi) mai rarrabẽwa a kan bãwanSa, dõmin ya kasance mai gargaɗi ga halitta} [al-Furƙan: 1].

Bukhari da Muslim sun ruwaito daga Jabir - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «An bani abubuwa biyar, waɗanda ba a baiwa wani daga cikin Annabawa a gabani na ba: An bani cin nasara ta hanyar tsoro (da ake jefawa abokan gaba) wata ɗaya gabanin haɗuwar mu, kuma aka sanya mini ƙasa ta zama wajen yin sallah na kuma abar yin tsarki, don haka duk wanda sallah ta riske shi cikin al'umma ta to sai ya yi ta, kuma an halarta min ganima, ba'a taɓa halartawa wani kafin ni ba, kuma an bani ceto, ya kasance ana aiko Annabi zuwa ga mutanensa kaɗai, ni kuwa an aiko ni zuwa ga mutane gaba ɗaya».

Wannan bayani ne fayyatacce da yake nuni akan gamewar manzancin (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - zuwa ga dukkan mutane, kuma manzancinsa ya share dukkanin shari’o’i da suka gabata, kuma duk wanda bai bi (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ba - kuma baiyi masa biyayyaba to kafiri ne mai laifi wanda ya cancanci uƙuba, (Allah) Maɗaukakin Sarki ya ce:

﴿...وَمَن يَكۡفُرۡ بِهِۦ مِنَ ٱلۡأَحۡزَابِ فَٱلنَّارُ مَوۡعِدُهُۥ...﴾

{Kuma wanda ya kafirta da shi daga jama'a to wuta ita ce makomarsa} [Hud: 17]. Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿...فَلۡيَحۡذَرِ ٱلَّذِينَ يُخَالِفُونَ عَنۡ أَمۡرِهِۦٓ أَن تُصِيبَهُمۡ فِتۡنَةٌ أَوۡ يُصِيبَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٌ﴾

{To waɗanda suke saɓa umarninsa su kiyayi kansu kada musiba ko fitina ta sauka a kansu ko kuma azaba mai raɗaɗi ta same su} [al-Nur: 63]. Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿وَمَن يَعۡصِ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ وَيَتَعَدَّ حُدُودَهُۥ يُدۡخِلۡهُ نَارًا خَٰلِدٗا فِيهَا وَلَهُۥ عَذَابٞ مُّهِينٞ14﴾

{Kuma wanda ya sãɓã wa Allah da ManzonSa, kuma ya ƙẽtare iyãkõkinSa, zai shigarda shi wuta, yana madawwami a cikinta, kuma yana da wata azãba mai walãƙantarwa} [al-Nisa'a: 14], Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿...وَمَن يَتَبَدَّلِ ٱلۡكُفۡرَ بِٱلۡإِيمَٰنِ فَقَدۡ ضَلَّ سَوَآءَ ٱلسَّبِيلِ﴾

{Kuma wanda ya musanya kãfirci da ĩmãni, to, lalle ne yã ɓace tsakar hanya} [al-Baƙara: 108], Kuma ayoyi da suka zo da wannan ma’anar suna da yawa.

Allah - tsarki ya tabbatar maSa - Ya haɗa biyayyar Manzo - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da biyayyarSa, kuma Ya bayyana cewa wanda ya yi imani da wanin Musulunci to shi mai hasara ne, ba za'a karɓa daga gareshi ba ko da sadaka ko fansa, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce:

﴿وَمَنْ يَبْتَغِ غَيْرَ الْإِسْلَامِ دِينًا فَلَنْ يُقْبَلَ مِنْهُ وَهُوَ فِي الْآخِرَةِ مِنَ الْخَاسِرِينَ85

{Kuma wanda ya nẽmi wanin Musulunci ya zama addini, to, bã zã a karɓa daga gare shi ba. Kuma shi a Lãhira yana daga cikin mãsu hasãra} [Aal- Imran: 85]. Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿مَنْ يُطِعِ الرَّسُولَ فَقَدْ أَطَاعَ اللَّهَ...

{Wanda ya yi ɗã'a ga Manzo, to, haƙĩƙa, yã yi ɗã'a ga Allah} [al-Nisa'a: 80]. Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿قُلْ أَطِيعُوا اللَّهَ وَأَطِيعُوا الرَّسُولَ فَإِنْ تَوَلَّوْا فَإِنَّمَا عَلَيْهِ مَا حُمِّلَ وَعَلَيْكُمْ مَا حُمِّلْتُمْ وَإِنْ تُطِيعُوهُ تَهْتَدُوا...

{Ka ce: "Ku yi ɗã'ã ga Allah kuma ku yi ɗã'ã ga Manzo. To, idan kun jũya, to, a kansa akwai abin da aka aza masa kawai, kuma a kanku akwai abin da aka aza muku kawai, Kuma idan kun yi masa ɗã'ã za ku shiryu} [al-Nur: 54]. Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿إِنَّ الَّذِينَ كَفَرُوا مِنْ أَهْلِ الْكِتَابِ وَالْمُشْرِكِينَ فِي نَارِ جَهَنَّمَ خَالِدِينَ فِيهَا أُولَئِكَ هُمْ شَرُّ الْبَرِيَّةِ 6

{Lalle ne waɗanda suka kafirta daga mutanen Littafi da mushirikai sana cikin wutar Jahannama suna madawwama a cikinta. Waɗannan su ne mafi ashararancin tãlikai} [al-Bayyinah: 6].

Muslim ya ruwaito a cikin Sahihinsa cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Na rantse da wanda raina yake a hannunSa, babu wani daga wannan al'umma Bayahude ko Nasara da zai ji wani abu game dani, sannan ya mutu bai yi imani da abinda aka aiko ni da shi ba, face sai ya kasance daga cikin 'yan wuta».

Kuma haƙiƙa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya bayyana da aikinsa da maganarsa ɓacin addinin wanda bai shiga addinin Musulunci ba, domin ya yaƙi Yahudawa da Nasara, kamar yadda ya yaƙi sauran kafirai, kuma ya karɓi jiziya daga wanda ya bayar daga cikinsu; har sai ba su hana isar da saƙo zuwa ga sauran su ba, muddin dai ba su hana wanda yake son shiga Musulinci ba daga cikinsu ba tare da tsoron mutanensa za su hana shi ko su tsare shi ko su kashe shi ba.

Bukhari da Muslim sun suwaito, daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Yayin da muke cikin masallaci sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya fito ya ce: Ku tafi zuwa ga Yahudawa". Sai muka fita tare da shi har muka zo gidan karatu, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya tashi, ya kira su sai ya ce: "Ya ku jama'ar Yahudawa, ku musulunta za ku tsira". Sai suka ce: Ka isar ya Abal Kasim. Sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wannan nake so, ku musulunta za ku tsira". Sai suka ce: Ka isar ya Abal Kasim. Sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wannan nake so". Sannan ya faɗa a karo na uku...» Hadisi.

Manufar ita ce: Cewa shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tafi zuwa ga masu addini cikin Yahudawa a cikin gidan karatunsu, sai ya kira su zuwa musulunci, kuma ya ce musu: «Ku musulunta za ku tsira». Ya kuma maimaita hakan a gare su.

Haka kuma: Ya aika da wasiƙa zuwa ga Hiraƙlu yana kiransa izuwa Musulinci, kuma yana ba shi labarin cewa idan ya ƙi, to zai ɗauki laifin duk waɗanda suka ƙi (shiga) musulunci saboda ƙin da ya yi. Haƙiƙa Bukhari da Muslim sun ruwaito a ingantattun littattafan su biyu, cewa Hiraƙlu ya ce, a kawo masa wasiƙar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, sai ya karanta, sai gashi a ciƙin wasiƙar: «Da sunan Allah Mai yawan rahama Mai yawan jin ƙai.

Daga Muhammad Manzon Allah zuwa ga Hiraƙlu sarkin Roma, aminci ya tabbata ga duk wanda yabi shiriya.

Bayan haka: Lalle ni ina kiranka da kira na Musulinci, ka musulunta za ka tsira, ka musulunta, Allah zai baka ladan ka sau biyu, idan kuma ka ƙi to laifukan Arisiyyun yana kanka. Kuma

﴿يَٰٓأَهۡلَ ٱلۡكِتَٰبِ تَعَالَوۡاْ إِلَىٰ كَلِمَةٖ سَوَآءِۭ بَيۡنَنَا وَبَيۡنَكُمۡ أَلَّا نَعۡبُدَ إِلَّا ٱللَّهَ وَلَا نُشۡرِكَ بِهِۦ شَيۡـٔٗا وَلَا يَتَّخِذَ بَعۡضُنَا بَعۡضًا أَرۡبَابٗا مِّن دُونِ ٱللَّهِۚ فَإِن تَوَلَّوۡاْ فَقُولُواْ ٱشۡهَدُواْ بِأَنَّا مُسۡلِمُونَ64﴾

Ka ce: 9Yã ku Mutãnen Littãfi! Ku taho zuwa ga kalma mai daidaitãwa a tsakã ninmu da ku; kada mu bauta wa kõwa fã ce Allah. Kuma kada mu haɗa kõme da Shi, kuma kada sãshenmu ya riƙi sãshe Ubangiji, baicin Allah." To, idan sun jũya bã ya sai ku ce: "ku yi shaida cẽwa, lalle ne mu masu sallamã wa ne) [Aal- Imran: 64.

Sannan lokacin da suka ƙi, suka juya baya suka ƙi shiga Musulinci, sai (Annabi) -tsira da aminci Allah su tabbata gare shi- ya yaƙe su shi da sahabbansa - Allah Ya yarda da su - kuma (ma’aikin Allah) ya ɗora musu jiziya.

Domin tabbatar da ɓatan su da cewa suna kan addini na ƙarya bayan an shafe shi da addinin (Annabi) Muhammad -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi-; Allah Ya umarci musulmi da ya roƙi Allah a kowace rana da kowace sallah da kowace raka'a da Ya shiryar da shi hanya madaidaiciya ta gaskiya abar karɓa, wato shine: Musulunci, kuma Ya nisantar da shi daga hanyar waɗanda aka yi fushi da su, wato: Yahudawa da makamantansu waɗanda suka san suna kan kuskure kuma suka nace a kansa, Ya nisantar da shi daga hanyar ɓatattu waɗanda suke bautã ba tare da ilimi ba, kuma suna zaton suna kan hanyar shiriya, alhãli kuwa suna kan hanyar ɓatasũ ne: Kiristoci, da waɗanda suka yi kama da su daga sauran al'ummatai waɗanda suke bautã a kan ɓata da jahilci, Duka wannan: Domin Musulmi ya sani, sani na yaƙini cewa duk wani addini da ba Musulinci ba to ɓatacce ne, kuma duk wanda yake bautawa Allah ba ta (hanyar) Musulinci ba to ɓatacce ne, duk wanda bai ƙudirce hakan ba to baya cikin musulmai. Dalilai a kan wannan babi suna da yawa daga AlKur’ani da kuma Sunnah.

Ya zama wajibi a kan mai wannan maƙala - Abdul Fattah - ya gaggauta tuba, tuba tsaftacce, kuma ya rubuta maƙala inda zai bayyana tubansa, wanda ya tuba zuwa ga Allah tuba na gaskiya; Allah zai karɓi tubansa; saboda faɗin Allah - Maɗaukakin sarki -:

﴿...وَتُوبُوٓاْ إِلَى ٱللَّهِ جَمِيعًا أَيُّهَ ٱلۡمُؤۡمِنُونَ لَعَلَّكُمۡ تُفۡلِحُونَ﴾

{Kuma ku tuba zuwa ga Allah ya ku muminai baki ɗayanku ko kwa rabauta} [al-Nur: 31], Da faɗinSa - tsarki ya tabbatar maSa -:

﴿وَٱلَّذِينَ لَا يَدۡعُونَ مَعَ ٱللَّهِ إِلَٰهًا ءَاخَرَ وَلَا يَقۡتُلُونَ ٱلنَّفۡسَ ٱلَّتِي حَرَّمَ ٱللَّهُ إِلَّا بِٱلۡحَقِّ وَلَا يَزۡنُونَۚ وَمَن يَفۡعَلۡ ذَٰلِكَ يَلۡقَ أَثَامٗا68 يُضَٰعَفۡ لَهُ ٱلۡعَذَابُ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ وَيَخۡلُدۡ فِيهِۦ مُهَانًا69 إِلَّا مَن تَابَ وَءَامَنَ وَعَمِلَ عَمَلٗا صَٰلِحٗا فَأُوْلَٰٓئِكَ يُبَدِّلُ ٱللَّهُ سَيِّـَٔاتِهِمۡ حَسَنَٰتٖۗ وَكَانَ ٱللَّهُ غَفُورٗا رَّحِيمٗا70﴾

{Kuma waɗanda bã su kiran wani ubangiji tãre da Allah, kuma bã su kashe rai wanda Allah Ya haramta fãce da haƙƙi kuma bã su yin zina. Kuma wanda ya aikata wancan, zai gamu da laifuffuka,

A riɓanya masa azãba a Rãnar ƙiyãma. Kuma ya tabbata a cikinta yanã wulaƙantacce,

Sai wanda ya tũba, kuma ya yi ĩmãni, kuma ya aikata aiki na ƙwarai to, waɗancan Allah Yanã musanya miyãgun ayyukansu da mãsu kyau. Allah Ya kasance Mai gãfara Mai jin ƙai} [al-Furƙan: 68-70]. Kuma Saboda faɗin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: «Musulunci yana rusa abin da ya kasance gabaninsa, kuma tuba yana rusa abin da ya kasance gabaninsa». Kuma da faɗinsa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: «Mai tuba daga zunubi kamar wanda ba shi da zunubi ne».

Ayoyi da hadisai da suka zo da wannan ma’anar suna da yawa.

Ina roƙon Allah - subhanahu wa ta'ala - Ya nuna mana gaskiya gaskiya ce, Ya azurta mu bin ta, Ya kuma nuna mana ƙarya ƙarya ce Ya azurta mu nisantar ta, Ya kuma yi baiwa a gare mu da marubuci Abdul Fattah da dukkan musulmai da tuba na gaskiya, Ya kuma kare mu duka daga fitintinu masu ɓata da bin son zuciya da Shaiɗan, lalle Shi ne Majiɓincin wannan kuma Mai iko a kansa.

Allah Ya yi tsira da aminci ga Annabinmu Muhammad, da alayansa da sahabbansa, da wanda ya biyo bayansu da kyautatawa har zuwa ranar Alƙiyama.

***

TEBURIN BAYANI

 

Aƙida ingantacciya da abinda yake kishiyantarta 2

ASALI NA FARKO: Imani da Allah - Maɗaukakin Sarki -, hakan kuma yana ƙunsar abubuwa da dama; daga cikinsu akwai: 6

ASALI NA BIYU: Imani da mala’iku. 21

Shi kuma yana ƙunsar al'amurra guda biyu: 21

ASALI NA UKU: Imani da littattafai, shima yana ƙunsar al'lamurra guda biyu: 22

ASALI NA HUƊU: Imani da manzanni 25

ASALI NA BIYAR: Imani da ranar lahira 26

ASALI NA SHIDA: Imani da ƙaddara 27

Aƙidun da suke kishiyantar ingantacciyar aƙida 33

SAƘO NA BIYU: Akan hukuncin neman agaji da annabi 43

-tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -. 43

SAƘO NA UKU 62

A cikin hukuncin neman taimako da aljana da shaiɗanu da yin bakance gare su 62

SAƘO NA HUƊU: 83

Akan hukuncin yin ibadah da wasu wuridai na bidi’a da na shirka 83

SAƘO NA BIYAR: 109

Hukuncin taron maulidin annabi da sauran mauludai 109

SAƘO NA SHIDA: 121

Hukuncin taron bikin daren Isra'i da Mi'iraji 121

SAƘO NA BAKWAI: 128

Hukuncin yin biki a daren rabin watan Sha'aban 128

SAƘO NA TAKWAS: 143

Muhimmiyar Sanarwa akan ƙaryar wasiyyar da aka dangantawa

Shiekh Ahmad mai Hidimar Haramin Annabi maɗaukaki 143

SAƘO NA TARA: Hukuncin sihiri da bokanci da abinda yake da alaƙa da su 160

SAƘO NA GOMA: 177

Tsawatarwa akan gina masallatai a maƙabartu 177

SAƘO NA GOMA SHA ƊAYA: Binne matattu a cikin masallatai 183

SAƘO NA GOMA SHA BIYU: Bayanin kafirci da ɓatan duk wanda ya raya cewa ya halatta ga wani ya kauce daga shari'ar (Annabi) Muhammadu - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi-. 185

 

 

 

***


Bukhari ne ya fitar da shi (2856), da Muslim (30).

Lālaka'i ne ya fitar da shi a Sharhu Usul al-I’itiƙad, (735), da Ibnu Abdul Barr a Jami’i al-Ulum wa fadlihi (1801), saidai da lafazin hadisan maimakon ayoyin siffofin, kuma lafazin sa shine: “Ku ruwaito waɗannan hadisan kamar yanda suka zo, kada ku yi jayayya akan su”.

Al-Baihaƙi ne ya ruwaito shi a Al’asma’u Wal Sifāt (865), Ibn Taimiya ya Inganta isnadin sa a cikin Hamawiyya (shafi na 269), al-Zahabi ya ce a (littafin) al’Ard (2/223), maruwaitan sa shuwagabanni ne, amintattu ne.

Al-Lalaka’i ne ya fitar da shi a cikin Sharhu Usul al-I'itiƙad I(930), da al-Baihaƙi a cikin al’Asmau Was Sifat, (955).

Al- Lalaka’i ne ya fitar da shi a cikin Sharhu Usulil I'itiƙad (665), da al-Baihaƙi a cikin al’Asma'u Was Sifat, (868).

Al-Lalaka'i ne ya fitar da shi a cikin Sharhu Usulil I'itiƙad (664), da Abu Nu’aim a cikin Hilyatul Auliya'u (6/325), da al-Baihaƙi a cikin al’Asma'u Was Sifat (867).

Al-Muzakki ya fitar da shi a cikin al’Muzakkiyat (29), da Ibn Baɗɗah a cikin al’Ibanah (120), da al-Lalaka’i a cikin Sharhu Usul al-I'itiƙad (663).

Al-Darimi ne ya fitar da shi a cikin al-Raddu alal Jahmiyyah (67), da al-Baihaƙi a cikin al’Asma'u Was Sifat (903).

Al-Zahabi ne ya ruwaito shi a cikin al’Uluwwu (464), kuma Albani ya ce a cikin Mukhtasarul Uluwwu (shafi na: 184), wannan isnadin ingantacce ne, kuma maruwaitan sa amintattu ne sanannu.

Tafsir Ibn Kathir (3/426 ,427).

. Bukhari ne ya fitar da shi (22), daga hadisin Abu Sa’id al-Khudri - Allah Ya yarda da shi -.

Muslim ne ya fitar da shi (2996), daga hadisin Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita -.

Bukhari ne ya fitar da shi (3651), da Muslim (2533), daga hadisin Abdullahi ɗan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi -.

Muslim ne ya fitar da shi (1920), daga hadisin Thauban, - Allah Ya yarda da shi -.

Ibn Majah ne ya fitar da shi (3952), daga hadisin Thauban, - Allah Ya yarda da shi -, kuma Ibn Hibban ya inganta shi (6714), da al-Hakim (8653).

Tirmizi ne ya fitar da shi (2641), daga hadisin Abdullahi ɗan Amr - Allah Ya yarda da shi -, al-Munawi ya ce a cikin Faidhul ƙadir (5/347): "A cikin sa akwai Abdurrahman ɗan Ziyad al-Ifriƙi, al-Zahabi ya ce: Sun raunana shi". Kuma Albani ya inganta shi a cikin Sahihul Jami’i (5343).

Muslim ne ya fitar da shi (8).

Bukhari ne ya fitar da shi (2856), da Muslim (30).