رسالة في الدماء الطبيعية للنساء (هوسا)

كتاب رِسَالَةٍ فِي الدِّمَاءِ الطَّبِيعِيَّةِ لِلنِّسَاءِ للشيخ العلامة محمد بن صالح العثيمين رحمه الله هو رسالة علمية رصينة تناولت بالبحث والتحقيق دماء النساء الطبيعية من الحيض والاستحاضة والنفاس، مستندةً إلى الكتاب العزيز والسنة المطهرة، مقرونةً بفهم دقيق لأقوال أهل العلم في هذه المسائل. وضعت فيها أحكام الدماء، مبينةً الفروق الدقيقة بين الحالات، ومقدمةً دليلاً شرعيًا لتحقيق الهداية والطمأنينة للمسلمة في فهم دينها.

  • earth Harshe
    (هوسا)
  • earth Wallafar:
    الشيخ محمد بن صالح العثيمين
PHPWord

 

 

رِسَالَةٌ فِي الدِّمَاءِ الطَّبِيعِيَّةِ لِلنِّسَاءِ

 

SAƘO A KAN JINAYEN ƊABI'A GA MATA

 

بِقَلَمِ فَضِيلَةِ الشَّيْخِ العَلَّامَةِ

مُحَمَّدِ بْنِ صَالِحٍ العُثَيْمِينِ

غَفَرَ اللَّهُ لَهُ وَلِوَالِدَيْهِ وَلِلمُسْلِمِينَ

 

Da alƙalamin babban malami mai yawan sani

Muhammad bin Salih Al-Usaimeen

Allah Yayi masa gafara shi da mahaifansa da musulmai

 

 


بِسْمِ اللهِ الرَّحمَنِ الرَّحِيمِ

SAƘO A KAN JINAYEN ƊABI'A GA MATA

Da sunan Allah Mai rahama Mai jin ƙai.

Dukkan godiya ta tabbata ga Allah, muna gode maSa, kuma muna neman taimakon Sa, muna neman gafarar Sa, kuma muna tuba izuwa gare Shi. Muna neman tsarin Allah daga sharrukan rayukanmu, da kuma munanan ayyukanmu. Duk wanda Allah Ya shiryar babu mai ɓatar da shi, kuma wanda ya ɓatar babu mai shiryar da shi. Kuma ina Shaida cewa babu wani abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kaɗai yake, ba Shi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa cewa, Annabi Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne. Tsiran Allah da amincinSa su tabbata agare shi, da alayensa, da sahabbansa, da wanda ya biyo su da kyautatawa, zuwa ranar sakamako.

Bayan haka: Lallai cewa jinayen da suke samun mace, sune haila da jinin cuta da jinin biƙi, suna daga muhimman al'amuran da buƙata take neman bayanin su, da kuma sanin hukunce-hukuncensu, da banbance kuskure daga daidai daga zantukan malamai a kansu. Kuma dogaro ya kasance dangane da abin da za'a rinjayar ko a raunana daga hakan, a kan mahangar abin da ya zo a cikin Al-ƙur'ani da Sunna.

1- Domin cewa sune tushe na asali waɗanda ake gina hukunce-hukuncen Allah - Maɗaukakin sarki - a kansu, waɗanda bayinSa za su yi bauta da su kuma Ya ɗora musu su.

2- Kuma domin cewa akwai nutsuwar zuciya, da yalwar ƙirji, da daɗin rai, da kuɓutar wuyaye,a kan dogara ga Al-ƙur'ani da Sunna.

3- Kuma domin cewa duk abin da ba su ba, to, kaɗai ana kafa masa hujja ne, amma ba'a kafa hujja da shi.

Domin babu wata hujja sai a zancen Allah - Maɗaukakin sarki - da kuma zancen ManzonSa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, haka nan da zancen ma'abota ilimi daga sahabbai a kan magana mafi rinjaye, da sharaɗin, kada a samu abin da yake saɓa masa a cikin Al-ƙur'ani da Sunna. Kuma kada wani faɗin sahabin daban, ya yi karo da shi. Idan ya kasance a cikin Al-ƙur'ani da Sunna akwai abin da yake saɓa masa, to ya wajaba a yi ruƙo da abin da yake a cikin Al-ƙur'ani da Sunna. Idan maganar wani sahabin daban ta yi karo da shi sai a nemi rinjaye tsakanin maganganun biyu, a yi kuma riƙo da mafi rinjaye daga gare su; saboda faɗinSa - Maɗaukakin sarki -:

﴿...فَإِن تَنَٰزَعۡتُمۡ فِي شَيۡءٖ فَرُدُّوهُ إِلَى ٱللَّهِ وَٱلرَّسُولِ إِن كُنتُمۡ تُؤۡمِنُونَ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِۚ ذَٰلِكَ خَيۡرٞ وَأَحۡسَنُ تَأۡوِيلًا﴾

{Idan ku ka sami saɓani cikin wani abu to ku mayar da shi zuwa ga Allah da ManzonSa in kun kasance masu imani da Allah da ranar Lahira, yin haka shi ne mafi alheri kuma shi ne mafi kyawun fassara}. [an-Nisa': 59].

Wannan taƙaitaccen saƙo ne a kan abin da buƙata take neman sa na daga bayanin waɗannan jinayen, da kuma hukunce-hukuncensu, ya tattaro fasalillikan nan masu zuwa:

Fasali na farko: A cikin ma'anar haila da hikimar ta.

Fasali na biyu: A kan zamanin haila da tsawon lokacin ta.

Fasali na uku: A kan abubuwan da suke bujirowa haila.

Fasali na huɗu: A kan hukunce-hukuncen haila.

Fasali na biyar A kan jinin cuta da hukunce-hukuncensa.

Fasali na shida: A kan jinin biƙi da hukunc-hukuncensa.

Fasali na bakwai: A kan yin amfani da abin da yake hana haila ko yake jawo shi, da abin da yake hana ɗaukar ciki, ko yake zubar da shi.

FASALI NA FARKO: A CIKIN MA'ANAR HAILA DA HIKIMAR SA

Haila a harshen Larabci: Shi ne zubar abu da kuma gudanar sa.

A shari'a kuma: Shi wani jini ne, da yake faruwa ga mace ta hanyar ɗabi'a, ba tare da wani dalili ba, a cikin wasu lokuta ababen sani. Shi jini ne na ɗabi'a ba na wata rashin lafiya ko rauni ko ɓari ko haihuwa ba ne. Duk da cewa shi jini ne na ɗabi'a to shi yana saɓawa gwargwadan halin mace da yanayin ta da kuma yanayin garin su; saboda haka mata suke saɓawa a cikinsa saɓawa mai bambanta a zahiri.

Kuma hikima a cikinsa: Cewa shi yayin da ɗan tayi ya kasance a cikin mahaifiyarsa, ba ya yiwuwa ya ci abincin da abin da wanda ke wajen cikin yake cin sa kuma ba zai yiwu ba ga mafi jin ƙan halitta a gare shi da ya sadar masa da wani abu na abinci, a yayin nan Allah - Maɗaukakin sarki - Ya sanya fesowar jini a mace wanda ɗan tayi yake cin abinci da su a cikin mahaifiyarsa ba tare da buƙatuwa zuwa ci ko haɗiya ba. Suna zarcewa zuwa jikinsa daga hanyar cibiya ta inda jini yake ratsa jijiyoyinsa sai yaci abinci da shi, girman Allah ya ɗaukaka, alherinSa ya yawaita mafi kyautatawar masu halitta.

Wannan ita ce hikima a wannan hailar; saboda haka idan mace ta ɗauki ciki sai haila ta yanke mata, ba za ta yi haila ba sai lokaci kaɗan, haka nan mai shayarwa 'yan kaɗan ne daga cikinsu suke haila musamman ma a farkon zamanin shayarwa.

 

FASALI NA BIYU: A KAN ZAMANIN HAILA DA TSAWON LOKACIN SA

Magana a cikin wannan fasalin yana kan matsayai biyu:

Matsayi na farko: Game da shekarun da haila yake zuwa a cikinsu.

Matsayi na biyu: Game da tsawon lokacin haila.

Amma matsayi na farko: To shekarar da yawancin haila take kasancewa a cikinsa, shi ne tsakaknin shekara goma sha biyu, zuwa shekara hamsin. Wataƙila mace ta yi haila kafin hakan ko bayan hakan, gwargwadan halinta da yanayinta da kuma yanayin ɗabi'ar garinta.

Haƙiƙa malamai - Allah Ya yi musu rahama - sun yi saɓani: Shin shekarar da zai yiwu a samu haila a cikinta tana da iyaka abar ayyanawa, ta yanda mace ba za ta yi haila kafin ta ba ko bayanta, kuma lallai cewa abin da yake zuwa kafinta ko a a bayanta ɓataccen jini ne ba haila ba?

Malamai sun yi saɓani a kan haka; Imam Darimi ya ce - bayan ya ambaci saɓaninnikan -: Dukkanin wannan a wuri na kuskurene! domin cewa makoma a dukkanin wannan zuwa samuwa ne, to kowane gwargwado aka samu a kowane hali da shekara ya wajaba a sanya shi a matsayin haila, Allah ne masani1.

Wannan abin da Darimi ya faɗa shi ne daidai, kuma shi ne zaɓin babban malamin Musulunci Ibn Taimiyya2. A duk lokacin da mace ta ga haila to, ita mai haila ce, ko da ta kasance ƙasa da shekara tara, ko sama da shekara hamsin. Hakan kuwa saboda cewa hukunce-hukuncen haila, Allah da ManzonSa sun rataya su a kan samuwarsa, kuma Allah da ManzonSa ba su iyakance wata shekara abar ayyanawa ga hakan ba, don haka ya wajaba a koma a sha'aninsa zuwa samuwar da aka rataya hukunce-hukunce a kanta, kuma iyakance shi da shekara abar ayyanawa yana buƙatuwa zuwa ga dalili daga Al-ƙur'ani ko Sunna, kuma babu wani dalili a hakan.

Amma matsayi na biyu shi ne tsawon lokacin haila, wato: Gwargwadan zamaninsa.

Haƙiƙa malamai sun yi saɓani a kansa, saɓani mai yawa kimanin maganganu shida ko bakwai. Ibn Munzir - Alllah Ya yi masa rahama ya ce: Wasu jama'a sun ce: Babu iyaka ga mafi ƙarancin haila ko mafi yawansa3.

Na ce: Wannan faɗar kamar faɗar (Imam) Darimi ce da ta gabata, kuma shi ne zaɓin babban malamin Musulunci Ibn Taimiyya, kuma shi ne daidai; domin cewa shi ne Al-ƙur'ani da Sunna da izina suke nuni a kansa.

Dalili na farko: FaɗinSa - Maɗaukakin sarki -:

﴿وَيَسۡـَٔلُونَكَ عَنِ ٱلۡمَحِيضِۖ قُلۡ هُوَ أَذٗى فَٱعۡتَزِلُواْ ٱلنِّسَآءَ فِي ٱلۡمَحِيضِ وَلَا تَقۡرَبُوهُنَّ حَتَّىٰ يَطۡهُرۡنَ...﴾

{Suna tambayarka game da haila to kace shi cuta ne don haka ku nisanci mata a cikin wurin haila kuma kada ku kusance su har sai sun yi tsarki...} [al-Baƙara: 222]. Sai Allah Ya sanya ƙololuwar hanin shi ne tsarki, bai sanya ƙololuwar shi ne shuɗewar kwana ɗaya, ko kwana uku, ko kwana goma sha biyar ba, sai wannan ya yi nuni a kan cewa illar hukuncin ita ce samuwar haila ko rashinta. A duk lokacin da aka samu hailar to hukuncin ya tabbata, kuma yayin da ta samu tsarki daga gare shi to hukunce-hukuncensa sun gushe.

Dalili na biyu: Abin da ya tabbata a cikin Sahihu Muslim cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya cewa Nana A'isha alhali ta yi haila kuma tana cikin Ihram da Umra: «Ki aikata abin da mahajjaci yake aikatawa, sai dai kada ki yi ɗawafi a Ɗaki har sai kin yi tsarki». Ta ce: To a lokacin da ranar babbar sallah ta zo, sai ta yi tsarki, sannan ta yi ɗawafin Ifadha. Hadisi4.

A cikin Bukhari da Muslim cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce mata: «Ki jira, idan kin yi tsarki, sai ki fita zuwa Tan'im»5. Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya sanya ƙololuwar hanin shi ne tsarki, bai sanya ƙololuwar wani zamani abin ayyanawa ba, sai wannan ya yi nuni a kan cewa hukuncin yana rataye ne da samuwar haila ko rashinsa.

Dalili na uku: Cewa waɗannan ƙiyasce-ƙiyascen da rarrabewar waɗanda wanda ya ambace su ya ambace su daga masana Fiƙihu a cikin wannan mas'alar ba samammu bane a cikin littafin Allah - Maɗaukakin sarki - ko Sunnar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - tare da cewa buƙata kai larura ma mai kira ce zuwa bayanin su. Da ace sun kasance fahimtar su da yin ibada dasu yana daga abin da ya wajaba a kan bayi, to, Allah da Manzon Sa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da sun bayyana su bayani ɓaro-ɓaro ga kowane ɗaya; saboda muhimmancin hukunce-hukuncen da suka tabbatu a kan hakan, na daga sallah da azumi da aure da saki da gado da wasunsu, na daga hukunce-hukunce. Kamar yanda Allah da Manzon Sa suka bayyana adadin salloli da lokutansu da ruku'insu da sujjadarsu, Da zakka: Dukiyoyin ta da nisabobin ta da gwargwadan ta da inda ake bada ita, da kuma azumi: Tsawonsa da zamaninsa, da kuma Hajji da abin da ke koma bayan hakan. Kai har ladubban ci da sha da bacci da jima'i da zama da shiga gida, da fitowa daga gareshi, da ladubban biyan buƙata, kai har adadin gogewar tsarkin hoge, zuwa wanin hakan daga zurfafan al'amura da maɗaukakan su, daga abin da Allah Ya cika Addini da shi, kuma Ya cika ni'ima ga muminai da shi, kamar yanda Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce:

﴿...وَنَزَّلۡنَا عَلَيۡكَ ٱلۡكِتَٰبَ تِبۡيَٰنٗا لِّكُلِّ شَيۡءٖ...﴾

{...Mun saukar ma da littafi don bayani ga kowane abu...} [al-Nahl: 89]. Kuma (Allah) - Maɗaukakin sarki - Ya ce:

﴿...مَا كَانَ حَدِيثًا يُفْتَرَى وَلَـكِن تَصْدِيقَ الَّذِي بَيْنَ يَدَيْهِ وَتَفْصِيلَ كُلَّ شَيْءٍ...﴾

{...Bai kasance wani ƙirƙiran lãbãri ba kuma amma shi gaskatãwa ne ga, abin da yake a gaba gare shi, da rarrabẽwar dukan abũbuwa...} [Yusuf: 111].

Yayin da ba'a samu waɗannan ƙiyasce-ƙiyascen ba, da kuma rarrabe-rarraben ba, a cikin littafin Allah - Maɗaukakin sarki -, ko a Sunnar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ba, sai ya bayyana cewa, babu dogaro a gare su, kaɗai madogara tana kan abin da ake ambato haila ne wanda aka rataya samuwar hukunce-hukuncen shari'a a kansu da kuma rashinsu, Wannan dalilin - ina nufin: Cewa rashin ambaton hukuncin a cikin Al-ƙur'ani da Sunna dalili ne a kan rashin izinantar sa - zai amfanar da kai a cikin wannan mas'alar da watanta, daga mas'alolin ilimi; domin cewa hukunce-hukuncen shari'a, basa tabbata sai da dalili daga shari'a daga littafin Allah, ko Sunnar ManzonSa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, ko wani Ijma'i abin sani, ko wani Ƙiyasi ingantacce. Babban malamin Musulunci Ibn Taimiyya ya faɗa a cikin wata ƙa'ida ta shi: "Yana daga haka sunan haila, Allah Ya rataya hukunce-hukunce da yawa a gare shi a cikin Littafi da Sunna, bai kuma ƙaddara mafi ƙarancinsa, ko mafi yawan sa ba, ko tsarki tsakanin haila biyu ba, tare da cewa sanin muhimmancin su yana game kowa da kowa, da kuma buƙatuwar su zuwa gare shi. Harshen Larabci ba ya bambancewa tsakanin gwargwado da gwargwado, duk wanda ya iyakance wani iyaka a cikin hakan to haƙiƙa ya saɓawa Littafi da Sunna"6. Zancensa ya ƙare.

Dalili na huɗu: Yin izina, wato: Ingantaccen Ƙiyasi madawwami ɗoɗar, hakan kuwa cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Ya illanta haila da kasancewar sa cuta ne. A duk lokacin da aka samu haila to cuta ta samu, babu bambanci tsakanin rana ta biyu da rana ta farko, ko tsakanin rana ta huɗu da ta uku. Babu bambanci tsakanin rana ta goma sha shida, da ta goma sha biyar, kuma babu bambanci tsakanin rana ta goma sha takwas da ta goma sha bakwai. Haila itac e haila, cuta kuma ita ce cuta, illa samammiyac e a ranakun biyu daidai wa daida, to yaya banbantawa zata inganta a hukuncin tsakanin ranaku biyun, tare da daidaituwarsu a cikin illa? Shin yanzu wannan ba saɓanin ingantaccen Ƙiyasi ba ne? Shin yanzu Ƙiyasi ingantacce ba shi ne daidaituwar ranaku biyun ba a wajen hukunci, sabo da daidaituwar su a cikin illa?

Dalili na biyar: Saɓanin maganganun masu iyakancewa da karo da junansu, lalle hakan yana nuni a kan cewa babu wani dalili a cikin mas'alar da ya wajaba a koma zuwa gare shi, kawai su hukunce-hukuncene na Ijtihadi ababen bujurowa ga kuskure da daidai ne, ɗayan su bai zama mafi cancanta da bi ba daga ɗayan, makoma yayin jayayya (tana) ga Littafi ne da Sunna.

dan har ƙarfin maganar cewa babu iyaka ga mafi ƙarancin haila ko mafi yawansa ya bayyana Kuma cewa shi ne zance marinjayi, to, ka sani dukkanin abin da mace ta gani na jinin ɗabi'a da ba shi da wani dalili na ciwo da makamancinsa, to shi jinin haila ne ba tare da ƙaddara wani lokaci ba, ko shekara, sai in ya kasance mai zarcewa ne ga mace ba ya yankewa kwata-kwata, ko yana yankewa lokaci sassauƙa kamar rana ɗaya ko ranaku biyu a wata, sai ya zama jinin cuta. Da sannu in Allah - Maɗaukakin sarki - Ya so bayanin jinin cuta da hukunce-hukuncensa za su zo.

Babban malamin Musulunci IbnTaimiyya ya ce: Asali a dukkanin abin da yake fitowa daga mahaifa cewa shi haila ne, har sai dalili ya tabbata akan cewa shi jinin cuta ne7.

Kuma ya ce: Duk abin da ya afku na jini, to shi haila ne, idan ba'a gane cewa shi jinin jijiya ba ne ko ciwo8. Ya ƙare.

Wannan zancen kamar yanda yake shi ne mafi rinjaye, ta ɓangaren dalili, kuma shi ne mafi kusanci a fahimta da riska, kuma mafi sauƙi a aiki da aiwatarwa daga abin da masu iyakancewa suka ambace shi, abin da ya kasance kamar haka, to shi ne mafi cancanta da karɓuwa; don dacewar sa ga ruhin Addinin Musulunci, da kuma ƙa'idar sa, ita ce sauƙi da rangwami. Allah - Maɗaukakin sarki -Ya ce:

﴿...وَمَا جَعَلَ عَلَيۡكُمۡ فِي ٱلدِّينِ مِنۡ حَرَجٖ...﴾

{...Bai sanya wani tsanani a kanku a cikin Addini ba...} [al- Hajj: 78]. Kuma (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Lallai Addini mai sauƙi ne, babu wanda zai tsananta cikinsa face sai ya rinjaye shi, saboda haka ku daidaita ku kusanto kuma ku yi bushara". Bukhari ne ya rawaito shi9.

Ya kasance daga ɗabi'un sa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: «Cewa shi ba'a taɓa bashi zaɓi tsakanin al'amura guda biyu ba, sai ya zaɓi mafi sauƙinsu mutuƙar dai bai zama zunubi bane»10.

HAILAR MAI CIKI:

Mafi yawan rinjaye, cewa mace idan ta ɗauki ciki sai jini ya yanke mata, Imam Ahmad - Allah Ya yi masa rahama - ya ce: "Kaɗai mata suna gane ɗaukar ciki ne, ta hanyar yankewar jini"11.

Idan mai ciki ta ga jini, idan ya kasance kafin haihuwa ne da wani lokaci ƙanƙani kamar rana biyu ko uku kuma a tare da shi akwai naƙuda, to shi jinin biƙi ne, Idan kuma ya kasance kafin haihuwa ne da lokaci mai tsayi, ko kafin haihuwa da ƙanƙanin lokaci sai dai babu naƙuda a tare da shi, to ba jinin biƙi ba ne, saidai shin zai iya zama hailar da hukunce-hukuncen haila za su tabbata gare shi ne, ko zai zama jinin cuta ba za'a iya yi masa hukunci da hukunce-hukuncen haila ba?

A cikin wannan akwai saɓani tsakanin ma'abota ilimi, amma daidai shine cewa shi haila ne, idan ya kasance a fuskar al'ada a hailarta; domin cewa asali a cikin abin da yake samun mace na jini cewa shi haila ne, idan ba shi da wani dalili da zai hana kasancewar sa haila, kuma a cikin Littafi da Sunna babu abin da zai hana hailar mai ciki.

Wannan ita ce mazahabar Imam malik12 da Imam al-shafi'i13, kuma zaɓin babban malamin Musulunci Ibn Taimiyya. Ya faɗa a cikin (Littafin) al-Ikhtiyarat (shafi: 30): Kuma Baihaƙi ya ruwaito shi riwaya daga Imam Ahmad, kai ya hakaito cewa shi ya dawo zuwa gare shi. Ya ƙare.

A kan wannan abin da yake tabbata ga hailar mara ciki yana tabbata ga hailar mai ciki sai a mas'ala biyu:

Mas'ala ta farko: Saki, sakin wacce idda take lazimtarta, a halin haila, yana haramta a haƙƙin mara ciki, amma ba ya haramta a haƙƙin mai ciki; Domin saki a halin haila ga mara ciki, mai saɓawa ne ga faɗinSa - Maɗaukakin sarki -:

﴿...فَطَلِّقُوهُنَّ لِعِدَّتِهِنَّ...﴾

{...Ku sake su ga iddarsu...} [aɗ-Ɗalak: 1]. Amma sakin mai ciki, a halin haila, ba ya saɓa masa; domin cewa wanda ya saki mai ciki, to, haƙiƙa ya sake ta ga iddarta, daidai ne ta kasance mai haila ce ko mai tsarki ce; domin iddarta da ciki ne; Saboda haka sakinta baya haramta, bayan jima'i saɓanin waninta.

Mas'ala ta biyu: Lallai cewa hailar mai ciki idda ba ta ƙarewa da shi, saɓanin hailar waninta; Domin cewa iddar mai ciki, ba ta ƙarewa sai da haife cikin, daidai ne ta kasance tana haila ne ko a'a; Saboda faɗinSa - Maɗaukakin sarki -:

﴿...وَأُوْلَاتُ الأَحْمَالِ أَجَلُهُنَّ أَن يَضَعْنَ حَمْلَهُنَّ...﴾

{...Kuma ma'abũta cikinna ajalinsu, (shi ne) cewa su haifi cikinnansu...} [aɗ-Ɗalaƙ: 4].

 

FASALI NA UKU: A ABUBUWAN DA SUKE BIJIROWA HAILA.

Masu bujirowa haila nau'o'i ne:

Nau'i na farko: Ƙari ko ragi, misalin al'adar mace ta kasance kwana shida, sai jini ya zarce mata zuwa kwana bakwai, ko al'adartata kasance kwana bakwai sai ta yi tsarki a kwana shida.

Nau'i na biyu: Ya gabata ko ya jinkirta, misalin al'adarta ta kasance a ƙarshen wata, sai ta ga haila a farkonsa, ko al'adarta ta kasance a farkon wata sai ta gan shi a ƙarshensa.

Haƙiƙa ma'abota ilimi sun yi saɓani a cikin hukuncin waɗannan nau'ukan biyu, amma daidai shine cewa, ita a duk lokacin da ta ga jini to ita mai haila ce, kuma a duk lokacin da ta ga tsarki, to ita mai tsarki ce, daidai ne ya ƙaru a kan al'adarta ko ya ragu, kuma daidai ne ta gabata ne ko ta jinkirta. Kuma ambaton dalili a kan haka ya gabata, a fasalin dake gabansa, inda mai shar'antawa ya rataya hukunce-hukuncen haila da samuwa sa.

Wannan ita ce mazahabar Imam al-Shafi'i14, kuma zaɓin babban malamin Musulunci Ibn Taimiyya15, kuma mai al-Mugni ya ƙarfafe shi a cikinsa, kuma ya taimake shi, ya ce: Da a ce al'ada ta kasance abar lura a kan fuskar da aka ambata a cikin mazahaba, da Annabinsa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya bayyana shi ga al'ummarsa, da jinkirta bayaninsa bai yalwace shi ba; Don jinkirta bayani daga lokacinsa, ba ya halatta, kuma matayensa da wasunsu, daga mata suna buƙatuwa zuwa bayanin hakan a kowane lokaci, kuma bai kasance zai rafkana a bisa bayaninsa ba. Kuma ambaton al'ada ko bayaninta bai zo ba daga gare shi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sai a haƙƙin mai jinin cuta, banda waninta16. Ya ƙare.

Nau'i na uku: Fatsi-fatsi ko hanta-hanta, ta inda za ta ga jini mai kalar fatsi-fatsi, kamar ruwan ciwo ko mai kalar hanta-hanta tsakanin fatsi-fatsi da baƙi. To, wannan in ya kasance a tsakiyar haila ne ko mai saduwa da shi kafin tsarki, to shi haila ne za mu tabbatar masa da hukunce-hukuncen haila, idan ya kasance bayan tsarki ne to ba haila ba ne; Saboda faɗin Ummu Aɗiyya - Allah Ya yarda da ita -: "Mun kasance bama ɗaukar fatsi-fatsi ko hanta-hanta wani abu bayan tsarki". Abu Dawud ne ya rawaito shi da Sanadi ingantacce17. Kuma Bukhari ya ruwaito shi, ba tare da faɗinta: (Bayan tsarki) ba, sai dai cewa shi ya yi masa take da faɗinsa: Babin fatsi-fatsi da hanta-hanta a wanin kwanankin haila18.

(Imam Ibn Hajar) ya faɗa a cikin sharhin Fathul Bari: "Yana nuni da hakan zuwa haɗawa tsakanin hadisin A'isha wanda ya gabata a cikin faɗinta: Har sai sun ga ƙassa fara. Da kuma tsakanin hadisin Ummu Aɗiyya wanda aka ambata a cikin babin, da cewa hakan - wato: Hadisin A'isha - abin ɗauka ne a kan idan taga fatsi-fatsi ko hanta-hanta a cikin kwanukan haila, amma a cikin waninsu, to ya tabbata a kan abin da Ummu Aɗiyya ta faɗa"19. Ya ƙare.

Hadisin Nana A'isha kuma wanda ya yi nuni zuwa gare shi shi ne abin da Bukhari ya ruwaito shi Mu'allaƙ yana mai yankewa da shi kafin wannan babin20, cewa mata sun kasance suna aiko mata da durja (wani abu ne wanda mace take amfani da shi don ta gane shin wani abu na gurbin jinin haila ya ragu) a cikinsa akwai kursuf (auduga), a cikinsa akwai fatsi-fatsi, sai ta ce: «Kada ku yi gaggawa har sai kun ga farar ruwa»21.

Ƙassa fara wani ruwane fari wanda mahaifa take tunkuɗo shi yayin yankewar jini haila.

Nau'i na huɗu: Yayyankewar jini a haila, ta inda za taga jini wata rana, wata rana kuma za taga tsarkaka da makamancin hakan to waɗannan halaye biyu ne:

Hali na farko: Wannan ya kasance kowane lokaci tare da mace, to wannan jinin cuta ne hukuncin jinin cuta ana tabbatarwa wacce ta gan shi hukuncin mai jinin cuta.

Hali na biyu: Kada ya zama mai zarcewa ne tare da mace, a'a yana zo mata a wani lokaci, wani lokacin kuma ya kasance tana da ingantaccen lokacin tsarki. To malamai - Allah Ya yi musu rahama - sun yi saɓani a wannan tsarkin, shin zai kasance tsarkine ko kuma za'a aiwatar da hukunce-hukuncen haila ne a kansa?

Mazahabar Imam al-Shafi'i a mafi ingancin maganganunsa biyu cewa shi za'a ɗabbaƙa hukunce-hukuncen haila a kansa, sai ya zama haila22, kuma shi ne zaɓin babban malamin Musulunci Ibn Taimiyya da mai littafin Alfa'iƙ23, kuma shi ne mazhabar Abu Hanifa24. Hakan kuwa domin cewa ƙassa fara ba'a ganinta a cikin shi; kuma domin cewa shi da an sanya shi tsarki da ya kasance abin da ke gabansa haila ne, kuma abin da ke bayansa ma haila ne, kuma babu mai faɗin haka, in ba haka ba fa da iddar ta ƙare da jini da kwanuka biyar; Kuma cewa shi da an sanya shi tsarki da ƙunci da wahala sun same shi, ta hanyar yin wanka da waninsa a kowane kwanuka biyu, kuma ƙunci abin korewane a wannan shari'ar, godiya ta tabbata ga Allah.

Zance mafi shahara daga mazahabr Hanabila, cewa jinin haila ne, kuma tsarkaka tsarki ne, sai dai idan su duka in an tara su sun wuce mafi yawan kwanukan haila, to sai jinin daya ƙetare ya zama jinin cuta25.

Ya faɗa a cikin al-Mugni: "Yana fuskantar cewa yankewar jini a duk lokacin da ya yi ƙasa da rana biyu, to, shi ba tsarki ba ne, don gini a kan ruwayar da muka hakaito ta game da jinin biƙi, cewa ita ba za ta waiwaya zuwa ƙasa da rana ɗaya ba, kuma shi ne ingantacce - in Allah Ya so - domin cewa jini yana gudana wani lokaci kuma yana yankewa a wani lokacin daban, kuma a cikin wajabta wanka a kan wacce take tsarkaka awa bayan awa ƙunci ne da yake koruwa; Saboda faɗinSa - Maɗaukakin sarki -:

﴿...وَمَا جَعَلَ عَلَيۡكُمۡ فِي ٱلدِّينِ مِنۡ حَرَجٖ...﴾

{...Bai sanya wani tsanani a kanku a cikin Addini ba...} [al-Hajj: 78]. Ya ce: A kan wannan, yankewar jini ƙasa da rana ɗaya ba ya kasancewa tsarki sai dai idan ta ga abin da yake nuni a kansa, kamar yankewar sa ya zama a ƙarshen al'adarta ne, ko ta ga ƙassa fara"26. Ya ƙare.

Sai faɗin mawallafin Al-Mugni ya zama shi ne tsaka-tsakiya, tsakanin maganganun biyu, Allah Shi ne mafi sanin daidai.

Nau'i na biyar: Bushewa a jini ta inda mace za ta ga danshi kawai, to, wannan in ya kasance a tsakiyar haila ko mai saduwa da ita kafin tsarki, to, wannan haila ce, idan ya kasance bayan tsarkine to ba haila ba ce; Domin cewa mafi matuƙar halinsa, ya risku da fatsi-fatsi da kuma hanta-hanta, wannan shi ne hukuncinta.

FASALI NA HUƊU: A CIKIN HUKUNCE-HUKUNCEN HAILA

Haila tana da wasu hukunce-hukunce masu yawa, sun haura ashirin, zamu ambaci wasu daga abin da muke ganin ana yawan buƙatarsu, yana daga hakan:

Na ɗaya: Sallah: To sallah tana haramta ga mai haila, farillarta da nafilarta, babu abin da yake inganta daga gare su, haka nan sallah ba ta wajaba a kanta sai dai idan ta riski gwargwadan raka'a ɗaya cikakkiya daga lokacinta, sai sallah ta wajaba a kanta a wannan lokacin, daidai ne ta riski hakan daga farkon lokaci ko daga ƙarshensa.

Misalin hakan daga farkonsa: Mace ce ta yi haila bayan faɗuwar rana, da gwargwadan raka'a ɗaya, to yana wajaba a kanta ta rama sallar Magariba idan ta yi tsarki; domin cewa ita ta riski gwargwdan raka'a ɗaya daga lokacinta kafin ta yi haila.

Kuma misalin haka a ƙarshensa: Mace ce ta tsarkaka daga haila, kafin huduwar rana da gwargwadan raka'a ɗaya to, yana wajaba a kanta ta rama sallar Asuba idan ta tsarkaka; domin cewa ita ta riski wani yanki da zai yalwatu ga raka'a ɗaya daga lokacinta.

Amma idan mai haila ta riski wani yanki na lokaci da ba zai yalwatu ga cikakkiyar raka'a ɗaya ba, misali ta yi haila a misali na farko bayan faɗuwar rana da ɗan lokaci, ko ta tsarkaka a misali na biyu kafin huduwar rana da ɗan lokaci. To lallai cewa sallah ba ta wajaba a kanta ba; saboda faɗin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: "Wanda ya riski raka'a ɗaya daga cikin sallah, to, ya riski sallah". An haɗu a kansa27. Domin cewa abin da aka fahimta daga hadisin cewa wanda ya riski mafi ƙaranci daga raka'a ɗaya bai kasance mai riskar sallah ba.

Idan ta riski raka'a ɗaya daga lokacin sallar La'asar to shin sallar Azahar ta wajaba a kanta, tare da La'asar, ko ta riski raka'a ɗaya daga lokacin sallar issha'in ƙarshe, to, shin sallar Magariba tare da Issha'i ta wajaba a kanta?

Akwai saɓani a cikin wannan, tsakanin malamai, amma daidai cewa ita babu abin da yake wajaba a kanta, sai abin da ta riski lokacinsa, ita ce sallar La'asar da Issha'in ƙarshe kawai; saboda faɗinsa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: "Wanda ya riski raka'a daga La'asar, kafin faɗuwar rana to, haƙiƙa ya riski La'asar". Bukhari da Muslim suka rawaito shi28. Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - bai ce: Haƙiƙa ya riski Azahar da La'asar ba.

Kuma bai ambaci wajabacin Azahar a kansa ba, asali shi ne kuɓutar wuyaye, wannan shi ne mazahabar Imam Abu Hanifa da Imam malik, ya hakaito daga gare su a cikin sharhin Al-Muhazzab29.

Amma zikiri da kabbara da tasbihi da tahmidi, da ambaton Allah ga abinci da waninsa, da karanta hadisi da fiƙihu da faɗin Aamin gare shi, da jin karatun Al-ƙur'ani, ko wani abu daga hakan ba ya haramta a gare ta. Haƙiƙa ya tabbata a cikin ingantattun littattafan hadisan nan biyu da wasunsu. "Lallai cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana dogara a ƙirjin Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - alhali tana haila, sai ya karanta Al-ƙur'ani"30.

Kuma acikin inagantattaun littattafan hadisan nan biyu cewa Ummu Aɗiyya - Allah Ya yarda da ita - cewa ita ta ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Yan matan da suka kusa balaga da budurwai da masu haila suna fita - yana nufin zuwa sallar idi - kuma su halarci alheri da kuma gayyatar muminai, kuma masu haila su nisanci wurin sallar"31.

Amma karatun mai haila Al-ƙur'ani a kankanta, idan ya kasance duba ne da ido ko lura da zuciya, ba tare da furuci da harshe ba, to babu laifi da hakan, kamar a sanya Mushafi ko allo sai ta dinga duba ayoyin ta kuma karantasu a zuciyarta. Imam Al-Nawawi ya ce a cikin sharhin Al-Muhazzab: "Ya halatta ba tare da wani saɓani ba"32.

Amma idan karatunta ya kasance furuci ne da harshe to jumhur ɗin malamai sun tafi a kan cewa shi abin hanawa ne kuma bai halatta ba. Imam al-Bukhari33 da Ibn Jarir al-Ɗabari34 da Ibn al-Munzir35 sun ce: Shi ya halatta.

An hakaito daga Imam Malik da Imam al-shafi'i a tsohuwar maganar sa36, ya hakaito daga gare su a cikin Fathul Bari37.

Al-Bukhari ya ambata Mu'allaƙ daga Ibrahim al-Nakha'i: Babu laifi ta karanta aya38.

Babban malamin Musulunci Ibn Taimiyya ya faɗa a cikin fatawa tattarowar Ibn Ƙasim: "Babu wata Sunna tun asali a cikin hanata karatun Al-ƙur'ani; domin cewa faɗin sa: "M «Kada mai haila ko mai janaba su karanta wani abu daga Alƙur'ani»39. Hadisi ne mai rauni bisa ga ittifaƙin Malaman Hadisi40.

Haƙiƙa mata sun kasance suna haila a zamanin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, da a ce karatu ya kasance abin haramtawa a kan su kamar sallah, da wannan ya kasance daga abin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - zai bayyana shi ga al'ummarsa, kuma iyayen muminai sun nemi saninsa, kuma hakan ya zama daga abin da mutane suke cirato shi. Yayin da wani ɗaya bai cirato wani hani daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ba to ba ya halatta a sanya shi haram tare da sanin cewa shi bai yi hani a bisa hakan ba. Idan bai yi hani daga gare shi ba tare da yawan masu haila a zamaninsa sai aka san cewa shi ba haramun bane"41. Ya ƙare.

Abin da yake kamata bayan mun san jayayyar ma'abota ilimi shine a ce: Abin da yafi ga mai haila kada ta karanta Al-ƙur'ani tana mai furuci da harshe sai yayin buƙata kamar ta kasance mai koyarwa, to tana buƙatuwa zuwa laƙƙanawa mata masu koyo, ko a cikin halin jarrabawa to mai neman sani tana buƙatuwa zuwa karatu don jarrabata ko makakamancin hakan.

Na biyu: Azumi: Azumi yana haramta ga mai haila farillarsa da nafilarsa, babya inganta daga gareta, sai dai rama farilla daga gare shi yana wajaba a kanta; saboda hadisin Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita -: "Wannan ya kasance yana samunmu - tana nufin haila - sai a umarce mu da rama azumi, kuma ba'a umartar mu da rama sallah". Bukhar42.

Idan ta yi haila, alhali tana azumi to aziminta ya ɓaci, koda hakan ya kasance daf da faɗuwar rana ne da ƙiftawar ido, kuma rama wannan ranar ya wajaba a kanta idan ya kasance farilla ne. Amma idan ta ji da tawowar haila kafin faɗuwar rana sai dai bai fito ba sai bayan faɗuwar rana, to, lallai azuminta cikakkene bai ɓaci ba a kan ingantacciyar magana; domin jini a cikin ciki ba shi da wani hukunci;

Kuma saboda an tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - game da macen da take ganin abin da namiji yake gani a cikin baccin ta: Shin a kanta akwai wanka? Ya ce: "Eh, idan taga ruwa" 43 Sai ya rataya hukuncin da ganin maniyyi ba da ciratowarsa ba, to haka nan haila hukunce-hukuncenta ba sa tabbata sai da ganinsa a waje ba don tawowarsa ba.

Idan alfijir ya keto, alhali ita tana haila to azumin wannan ranar bai inganta gare ta ba koda ta tsarkaka bayan alfijir da ƙiftawar ido.

Idan ta yi tsarki daf da alfijir, sai ta yi azumi to, azuminta ya inganta, ko da ba ta yi wanka ba sai bayan alfijir, kamar mai janaba idan ya yi niyyar azumi alhali shi yana mai janaba bai yi wanka ba sai bayan ɓullowar alfijir to azuminsa ingantacce ne; Saboda hadisin A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: "Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana wayar gari yana mai janaba daga jima'i ba na mafarki ba sannan ya yi azumi a Ramadan". An haɗu a kansa44.

Hukuncu na uku: Ɗawafi a ɗaki: To, ɗawafi a ɗaki yana haramta a kanta, farillarsa da naifilarsa, ba ya inganta daga gare ta; Amma ragowar ayyukan, kamar Sa'ayi tsakanin safa da Marwa, da tsayuwar Arfa, da kwana a Muzdalifa da Minna, da jifan jamarori da wasunsu daga ibadun Hajji da Umra to ba haramun ne a kanta ba, Saboda faɗin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ga A'isha lokacin da ta yi haila: «Ki aikata abinda mahajjaci yake aikatawa, sai dai kada ki yi Ɗawafi a Ɗaki har sai kin yi tsarki»45.

A kan wannan, da a ce mace ta yi ɗawafi alhali tana mai tsarki sannan haila ta fito bayan ɗawafin kai tsaye, ko a cikin tsakiyar Sa'ayi to babu laifi a hakan.

Hukunci na huɗu: Faɗuwar ɗawafin ban kwana gare ta: Idan mace ta cika ibadun Hajji da Umra sannan ta yi haila, kafin fita zuwa garinta kuma haila ta zarce da ita zuwa fitarta, to ita za ta fita ba tare da ban kwana ba; Saboda hadisin Abdullahi ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: "An umarci mutane da su yi dawafi ga ɗakin Allah a ƙarshe, sai dai an sauƙaƙa ga mace mai haila". [An haɗu a kansa]46.

Ba'a so mai haila ya yin ban kwana ta zo ƙofar masallaci mai alfarma ta yi addu'a; domin hakan bai zo daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ba, kuma ibadu ababen ginawa ne akan abin da ya zo. Kai abin da ya zo daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana hukuntar da saɓanin hakan. A cikin ƙissar Safiyya - Allah Ya yarda da ita - yayin da ta yi haila bayan ɗawafin ban kwana, cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce da ita: «To ku fita». An haɗu a kansa47.

Kuma bai yi umarni da zuwa ƙofar masallaci ba, da hakan ya kasance abin shara'antawa da ya bayyana shi. Amma ɗawafin Hajji da Umra ba ya saraya gare ta, kai za ta yi ɗawafi idan ta yi tsarki.

Hukunci na biyar: Zama a masallaci: To yana haramta ga mai haila ta zauna a cikin masallaci, har filin sallar idi yana haramta a gare ta ta zauna a cikinsa. Saboda hadisin Ummu Aɗiyya - Allah Ya yarda da ita -; Cewa ita ta ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa; «'Yan mata waɗanda suka balaga da budurwai da masu haila su fita». Kuma a cikinsa: «Masu haila su nisanci wurin salla». An haɗu a kansa48.

Hukunci na shida: Jima'i: Yana haramta ga mijinta ya yi jima'i da ita, kuma yana haramta a gare ta, da ta ba shi damar yin hakan; saboda faɗinSa - Maɗaukakin sarki -:

﴿وَيَسۡـَٔلُونَكَ عَنِ ٱلۡمَحِيضِۖ قُلۡ هُوَ أَذٗى فَٱعۡتَزِلُواْ ٱلنِّسَآءَ فِي ٱلۡمَحِيضِ وَلَا تَقۡرَبُوهُنَّ حَتَّىٰ يَطۡهُرۡنَ...﴾

{Suna tambayarka game da haila to ka ce shi cuta ne don haka ku nisanci mata a cikin wurin haila har sai sunyi tsarki...} [al-Baƙara: 222]. Abin nufi da wurin haila, shi ne lokacin haila, da kuma wurinsa, shi ne farji; Kuma saboda faɗin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: «Ku aikata kowane abu banda aure». Yana nufin: Jima'i. Muslim ne ya rawaito shi49; Kuma saboda musulmai sun haɗu a kan haramcin saduwa da mai haila a cikin farjinta.

Ba ya halatta ga wani mutum da ya yi imani da Allah da ranar Lahira da ya aikata wannan al'amarin abin ƙi, wanda littafin Allah - Maɗaukakin sarki - da Sunnar ManzonSa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da Ijma'in malamai suka yi nuni a kan hani a gare shi, sai ya zama daga waɗanda suka saɓawa Allah da manzonSa, kuma ya bi hanyar da ba ta muminai ba. Ya faɗa a cikin Al-Majmu sharhin Al-Muhazzab (shafi na: 274 juzu'i na 2), Imam Al-Shafi'i - Allah Ya jiƙan sa - ya ce: " Wanda ya aikata haka, to, haƙiƙa ya zo wa babban laifi". Malamammu da wasunsu sun ce: "Duk wanda ya halatta jima'i da mai haila za'a yi hukunci da kafircinsa" Zancen Imam Al-Nawawi ya ƙare.

Haƙiƙa an halatta masa - godiya ta tabbata ga Allah - abin da zai karya masa sha'awarsa, ba tare da jima'i ba, kamar sumbata da runguma a abin da bai kai ga farji ba, sai dai abin da yafi kada ya yi runguma a tsakanin cibiya da gwiwa sai ta bayan shamaki; Saboda faɗin Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita -; "Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana umarta ta sai in yi ƙunzugu, sai ya rungume ni, alhali ni ina haila". An haɗu a kansa50.

Hukunci na bakwai: Saki: Yana haramta ga miji da ya saki matar sa mai haila, a halin hailar ta, Saboda faɗinSa - Maɗaukakin sarki -:

﴿يَاأَيُّهَا النَّبِيُّ إِذَا طَلَّقْتُمُ النِّسَاء فَطَلِّقُوهُنَّ لِعِدَّتِهِنَّ...﴾

{Ya kai wannan Annabi idan zaku saki mata to ku sake su ga iddar su...} [al-Dalaƙ: 1]. Wato: A cikin halin da za su fuskanci idda abar sani da shi yayin saki, kuma hakan baya kasancewa sa idai idan ya sake ta tana mai ciki, ko tsarkakiyya ba tare da jima'i ba; Domin cewa ita idan an sake ta a halin haila, ba za ta fuskanci idda ba, yayin da cewa hailar da aka sake ta a cikinta, ba'a ƙirga ta daga idda, idan kuma aka sake ta tana cikin tsarki bayan jima'i, iddar da take fuskantar ta ba za ta kasance abar sani ba, ta yadda cewa ba za'a san cewa, shin ta ɗauki ciki daga wannan jima'in ba, sai ta yi idda da ciki, ko ba ta ɗauki ciki ba sai ta yi idda da haila. Yayin da yaƙini bai samu ba daga nau'in iddar to saki ya haramta a gare shi har sai al'amarin ya bayyana.

To sakin mai haila a halin hailar ta haramun ne saboda ayar da ta gabata; Kuma saboda abin da ya tabbata a cikin ingantattun littattafan nan biyu da wasunsu daga hadisin Ibn Umar: «Cewa shi ya saki matarsa alhali tana haila, sai Umar ya bawa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - labari da hakan, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi fushi a cikinsa kuma ya ce: «Ka umarce shi ya dawo da ita, sannan ya riƙe ta har sai ta yi tsarki, sannan ta yi haila, sannan ta yi tsarki, sannan in ya so ya riƙe ta bayan haka, kuma in ya so ya sake ta kafin ya shafe ta, to wancan ita ce iddar da Allah Ya yi umarni a saki mata a gare ta»51.

Da mutum zai saki matarsa alhali tana hakika to shi mai laifi ne, kuma akwai tuba zuwa ga Allah - Maɗaukakin sarki - a kansa, kuma ya maida matar zuwa ga igiyar aurensa domin ya sake ta saki na Shari'a wanda ya dace da umarnin Allah da Manzonsa, sai ya barta bayan maido da ita har sai ta yi tsarki daga hailar da ya sake ta a cikinta, sannan ta yi wata hailar, sannan idan ta yi tsarki, to idan ya so ya wanzar da ita idan kuma ya so ya sake ta kafin ya yi jima'i da ita.

Ana togance mas'aloli uku, daga haramcin saki a cikin haila:

Ta farko: Idan sakin ya kasance kafin ya kaɗaita da ita, ko ya shafeta, to babu laifi ya sake ta alhali tana haila; Domin cewa babu idda a kanta a wannan lokacin, don haka sakin ta ba zai zama mai saɓawa ba; Saboda faɗinSa - Maɗaukakin sarki -:

﴿...فَطَلِّقُوهُنَّ لِعِدَّتِهِنَّ...﴾

{...To ku sake su ga iddarsu...} [a-Dalaƙ: 1].

Ta biyu: Idan hailar ta kasance a halin ciki, bayanin dalilin hakan ya rigaya.

Ta uku: Idan sakin ya kasance a kan wani musaya ne, to cewa shi babu laifi ya sake ta alhali tana haila.

Misalin jayayya ta kasance tsakanin ma'aurata biyu da mummunar mu'amala, sai miji ya karɓi wani musaya, don ya sake ta, to yana halatta koda ta kasance mai haila ce; Saboda hadisin Ibnu Abbas - Allah Ya yarda dasu - cewa matar Sabit ibn Ƙais ta zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah sutabbata a gare shi - sai tace: Ya Manzon Allah, Sabit ibn Ƙais, ba na zargi a kansa a cikin ɗabi'u ko Addini, sai dai cewa ni ina ƙyamar kafirci a cikin Musulunci, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Shin za ki mayar masa gonarsa?» Ta ce: Eh. Sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Ka karɓi gonar ka sake ta saki ɗaya» [Bukhari ne ya rawaito shi]52.

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - bai tambayi cewa: Shin ta kasance mai haila ce ko mai tsarki ba? kuma domin cewa wannan sakin fansa ne, daga matar da kanta, sai ya halatta yayin buƙatuwa zuwa gare shi a bisa kowane halin da ya kasance.

Ya faɗa a cikin Al-Mugni yana mai kawo dalili a kan halaccin Khul'i a halin haila, (shafi na: 52 juzu'i na 7 Ɗ M): "Domin cewa hanin sakin a halin haila, saboda cutar da za ta riske ta ne, saboda tsawaituwar idda, shi ko Khul'i don gusar da cutar da zata riske ta ne saboda mummunar mu'amala, da zama tare da wanda take ƙin sa, wannan yana daga mafi girma daga cutar tsawon iddar, sai tunkuɗe mafi ɗaukakar su da mafi ƙasƙancin su ya halatta; saboda haka Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - bai tambayi wacce ta yi Khul'i a bisa halinta ba" Zancensa ya ƙare.

Amma ɗaura aure ga mace alhali tana haila, to, babu laifi gare shi; domin asali shi ne halacci, kuma babu wani dalili a kan hani daga gare shi, sai dai yin tarewar miji da ita, alhali tana haila za'a yi duba a cikinsa, idan ya kasance yana da amincin cewa ba zai yi jima'i da ita ba, to, babu laifi, in ba haka ba fa, to, ba zai tare da ita ba har sai ta yi tsarki don tsoro daga afkawa a cikin abin da aka hana.

Hukunci na takwas: Izinar iddar saki da shi - wato haila -: Idan mutum ya saki matarsa bayan ya shafe ta ko ya kaɗaita da ita, to ya wajaba a kanta ta yi idda da haila uku cikakku, idan ta kasance daga masu haila ce, kuma ba ta zama mai ciki ba; Saboda faɗinSa - Maɗaukakin sarki -:

﴿وَٱلۡمُطَلَّقَٰتُ يَتَرَبَّصۡنَ بِأَنفُسِهِنَّ ثَلَٰثَةَ قُرُوٓءٖۚ...﴾

{Kuma mata waɗanda aka saka suna jinkiri da kansu jini uku...} [al-Baƙara:228]. Wato: Haila uku. Idan ta kasance mai ciki ce, to iddarta zuwa haife cikin ne gaba ɗayansa, duk ɗayane lokacin ya yi tsawo ko ya taƙaita; saboda faɗinSa - Maɗaukakin sarki -:

﴿...وَأُوْلَاتُ الأَحْمَالِ أَجَلُهُنَّ أَن يَضَعْنَ حَمْلَهُنَّ...﴾

{...Ma'abota cikkkuna ajalinsu (shi ne) su haife cikkunan su...} [al-Dalaƙ: 4]. Kuma idan ta kasance ba daga masu ciki ba ce, kamar ƙaramar yarinyar da bata fara haila ba, da wacce ta yanke ƙauna daga haila don girma ko tiyatar da ta tunɓuke mahaifar ta ko makamancin hakan daga abin da ba ta ƙaunar dawowar haila tare da ita, to iddarta wata uku ce; Saboda faɗinSa - Maɗaukakin sarki -;

﴿وَاللَّائِي يَئِسْنَ مِنَ الْمَحِيضِ مِن نِّسَائِكُمْ إِنِ ارْتَبْتُمْ فَعِدَّتُهُنَّ ثَلَاثَةُ أَشْهُرٍ وَاللَّائِي لَمْ يَحِضْنَ...﴾

{Mata waɗanda suka yanke ƙauna daga haila daga matanku idan kun yi kokwanto to iddarsu wata uku ne, da waɗanda basu fara haila ba...} [al-Dalaƙ: 4]. Idan kuma ta kasance daga masu haila ce, sai dai hailar ta ta ɗauke saboda wani sanan nan dalili, kamar rashin lafiya da shayarwa, to ita zata wanzu a cikin idda, koda iddar ta tsawaita har hailar ta dawo sai tayi idda da ita. Idan dalilin ya gushe, kuma hailar bata dawo ba, wato cewa ta warke daga rashin lafiyar ko kuma ta gama shayarwar, kuma hailar ta wanzu a ɗauke to cewa ita za ta yi idda da shekara ɗaya cikakkiya daga gushewar dalilin. Wannan ita ce inagnatacciyar maganar da take dacewa da ƙa'idodin shari'a. To cewa shi idan dalilin ya gushe kuma hailar ba ta dawo ba, ta zama kamar wacce hailar ta ta ɗauke ba tare da wani dalili abin sani ba, kuma idan hailarta ta ɗauke ba tare da wani sanan nan dalili ba, to cewa ita za tayi idda da shekara ɗaya cikakkiya, wata tara ga ciki don kewayo; domin cewa shi ne mafi yawancin ciki, da kuma wata uku don idda.

Amma idan sakin ya kasance bayan ɗaura aure ne, kuma kafin shafa da kaɗaitaka, to babu wata idda a cikinsa kai tsaye, ba da haila ba, ba kuma da waninta ba; Sabda faɗinSa - Maɗaukakin sarki -:

﴿يَاأَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِذَا نَكَحْتُمُ الْمُؤْمِنَاتِ ثُمَّ طَلَّقْتُمُوهُنَّ مِن قَبْلِ أَن تَمَسُّوهُنَّ فَمَا لَكُمْ عَلَيْهِنَّ مِنْ عِدَّةٍ تَعْتَدُّونَهَا...﴾

{Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! idan kun auri mũminai mãtã, sa'an nan kuka sake su a gabãnin ku shãfe su, to, bã ku da wata idda da zã ku lissafa a kansu...} [al-Ahzab: 49].

Hukunci na tara: Hukunci da kuɓutar mahaifa, wato: Da kaɗaitakarta daga ciki, wannan ana buƙatuwa zuwa gare shi, duk lokacin da aka buƙata zuwa hukunci da kuɓutar mahaifa, kuma yana da mas'aloli:

Daga cikinsu: Idan mutum ya mutu ya bar mace to cikinta zai gaje shi, alhalin ita tana da miji, to cewa mijinta ba zai taɓeta ba har sai ta yi haila, ko cikinta ya bayyana. Idan cikinta ya bayyana sai mu yi hukunci da gadonsa don hukuncinmu da samuwarsa lokacin mutuwar wanda zai gada, kuma idan ta yi haila sai mu yi hukunci da rashin gadonsa don hukuncinmu da kuɓutar mahaifa saboda haila.

Hukunci na goma: Wajabcin wanka: To yana wajaba a kan mai haila idan ta sami tsarki ta yi wanka da wanke dukkanin jiki; Saboda faɗin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ga Faɗima 'yar Abu Hubaish; «Idan haila ta fuskanto to ki bar sallah, idan kuma ta ba da baya, to ki yi wanka ki yi sallah». {Bukhari ne ya rawaito shi}53.

Mafi ƙarancin wajibi ga wanka shine ta game dukkanin jikinta da shi har abin da ke ƙarƙashin gashi, amma abin da yafi ya kasance a kan siffar abin da ya zo a cikin hadisi: "Daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - lokacin da Asma'u 'yar Shakal ta tambaye shi game da wankan haila, sai - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Ɗayar ku ta ɗauki ruwanta da magaryarta sai ta yi tsarki ta kyautata tsarkin, sannan ta zuba a kanta sai ta cuɗa shi cuɗawa mai tsanani, har sai ta kai asalin kanta, sannan ta zuba ruwa a kansa, sannan ta ɗauki ƙyalle mai turare - wato: Wani yanki na ƙyalle wanda a cikinsa akwai almiski - sai ta yi tsarki da shi». Sai Asma'u ta ce: Ta yaya za ta yi tsarki da shi? Sai ya ce: «Subhānal-lāh!» (Tsarki ya tabbata ga Allah), Sai Nana Aisha - Allah Ya yarda da ita - ta ce mata: Ki bibiyi gurbin jinin. [Muslim ne ya rawaito shi]54.

Warware gashin kai baya wajaba, sai dai idan ya kasance a ɗaure da ƙarfi ta inda ake jin tsoron ruwa ba zai kai zuwa asalansa ba; Saboda abin da ke cikin Sahihu Muslim daga hadisin Ummu Salama - Allah Ya yarda da ita - cewa ita ta tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sai ta ce: Ni mace ce da nake ɗaure gashin kai na shin zan warware shi saboda wankan janaba? A cikin wata riwayar: Don wankan haila da janaba? Sai ya ce: «A'a, kaɗai ya ishe ki ki kamfaci cikin tafin hannu na ruwa a kanki sau uku sannan ki kwara ruwa a kanki sai ki tsarkaka»55.

Idan mai haila ta yi tsarki a tsakiyar lokacin sallah to ya wajaba a kanta ta yi gaggawa da yin wanka don ta riski sallah a lokacinta, idan ta kasance a halin tafiya ne kuma babu ruwa a wurinta sai dai tana jin tsoron cuta in ta yi amfani da shi, ko ta kasance mara lafiya ruwan zai cutar da ita to cewa ita ta yi taimama canji daga wanka har mai hanawan ya gushe sannan ta yi wanka.

Kuma lallai cewa wata daga cikin mata tana samun tsarki a tsakiyar lokacin sallah, sai ta jinkirta wankan zuwa wani lokacin daban tana cewa: Cikar tsarkin ba zai yiwu ba a wannan lokacin, sai dai wannan ba hujja ba ne kuma ba uzuri ba ne; Domin cewa ita zai yiwu gare ta ta taƙaita a kan mafi ƙarancin wajibi ga wanka, kuma ta yi sallah a cikin lokacinta, sannan idan yalwataccen lokaci ya samu gare ta sai ta yi tsarki cikakken tsarki.

FASALI NA BIYAR: A CIKIN JININ CUTA DA HUKUNCE-HUKUNCENSA

Jinin cuta: Shi ne zarcewar jini ga mace ta yanda ba zai yanke daga gare ta ba har abada, ko yana yankewa daga gare ta lokaci ƙanƙani, kamar kwana ɗaya da kwana biyu a cikin wata.

Dalilin hali na farko wanda jini ba ya yankewa daga gare ta har abada shi ne abin da ya tabbata a cikin Sahihul Bukhari daga A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: "Faɗima 'yar Abu Hubaish ta cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: "Ya Manzon Allah ni ba na tsarkaka". Kuma a cikin wata riwayar: "Ina jini ba na tsarkaka"56.

Dalilin hali na biyu kuma wanda jini ba ya yankewa a cikinsa sai lokaci ƙanƙani hadisin Himna 'yar Jahsh lokacin da ta zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sai ta ce: "Ya Manzon Allah ni ina jinin haila mai yawa mai tsanani". [Hadisin.. Ahmad da Abu Dawud da Tirmizi ne suka rawaito shi57 kuma ya inganta shi, kuma ya ruwaito daga Imam Ahmad cewa ya inganta shi, da kuma daga Bukhari cewa ya kyautata shi]58.

HALAYEN JININ CUTA:

Akwai halaye uku ga mai jinin cuta:

Hali na farko: Ya kasance tana da sananniyar haila kafin jinin cutar, to wannan za ta koma zuwa muddar hailar ta abar sani da ta gabata, sai ta zauna a cikinta, kuma hukunce-hukuncen haila za su tabbata gare ta, kuma abin da ke koma bayan wannan to jinin cuta ne, hukunce-hukuncen jinin cuta za su tabbata gare ta.

Misalin haka mace ce haila take zo mata kwana shida a farkon kowane wata, sannan jinin cuta ya faɗo mata sai jinin ya kasance yana zo mata da zarcewa, sai hailar ta ta zama kwana shida daga farkon kowane wata, abin da ba wannan ba to jinin cuta ne; Saboda hadisin A'isha - Allah Ya yarda da ita - cewa Fatima 'yar Abu Hubaish ta ce: Ya Manzon Allah, ina zubda jini ba na tsarkaka, shin zan bar sallah ne? sai ya ce: «A'a, Wancananki jijiya ce, sai dai ki bar sallah a gwargwadan kwanukan da kika kasance kina haila a cikinsu, sannan ki yi wanka ki yi sallah». Bukhari ne ya rawaito shi59.

A cikin Sahihu Muslim: Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya cewa Ummu Habiba 'yar Jahsh: «Ki zauna gwargwadan abin da hailar ki take tsare ki sannan ki yi wanka ki yi sallah»60.

A kan wannan mai jinin cutar da take da sananniyar haila ta zauna gwargwadan hailarta, sannan ta yi wanka ta yi sallah, kada ta damu da jinin a wannan lokacin.

Hali na biyu: Ya kasance ba ta da wata sananniyar haila kafin jinin cutar, shi ne cewa jinin cutar ya zama mai zarcewa ne da ita daga farkon lokacin da taga jini daga farkon al'amarinta, to wannan za ta yi aiki da bambancewa, sai hailar ta ta zama abin da take banbancewa da shi na baƙi ne, ko kauri ko wari hukunce-hukuncen haila za su tabbata gare shi, wanda ba shi ba kuma jinin cutane hukunce-hukuncen jinin cuta zai tabbata gare shi.

Misalin haka mace ce ta ga jini a farkon lokacin da tagan shi, kuma ya zarce da ita, sai dai tana ganinsa baƙi a kwana goma, a ragowar kwanukan kuma ja, ko tana ganinsa mai kauri a kwanuka goma ragowar kwanukan kuma siriri, ko tana ganinsa a kwana goma yana da warin haila, a ragowar watan kuma ba shi da wari, to hailarta shi ne baƙi a misali na farko, kuma mai kauri a misali na biyu, mai wari kuma a misali na uku, wanda ba wannan ba to shi jinin cuta ne; Saboda faɗin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ga Faɗima 'yar Hubaish: «Idan ya kasance jinin haila ne to cewa shi baƙi ne da ake gane shi, idan ya zama hakan to ki kame daga barin sallah, idan kuma ya zama ɗayan ne to ki yi alwala ki yi sallah; domin cewa shi cuta ne». [Abu Dawud ya rawaito shi da Nasa'i, kuma Ibnu Hibban da al-Hakim sun inganta shi]61.

Wannan hadisin duk da a cikin sanadinsa da mataninsa akwai shakkun inganci to haƙiƙa ma'abota ilimi - Allah Ya yi musu rahama - sun yi aiki da shi, kuma shi ne mafi cancanta daga maida ita zuwa al'adar mafi yawan mata.

Hali na uku: Ya zama kada ta kasance tana da wata sananniyar haila, kuma babu banbancewa da ya inganta, shine cewa jinin cutar ya kasance mai zarcewa ne daga farkon lokacin da taga jini, kuma jininta yana a siffa ɗaya, ko yana a siffa mai rikitarwa ba zai yiwu ya zama haila ba, To, wannan za ta yi aiki da al'adar mafi yawancin mata, sai hailar ta ta zama kwana shida ko kwana bakwai a kowane wata, yana farawa daga farkon lokacin da taga jini a cikinsa, wanda ba shi ba kuma to jinin cuta ne.

Misalin haka cewa ta ga jini a farkon lokacin da ta gan shi a kwana na biyar daga wata, kuma yana zarcewa da ita ba tare da ya kasance akwai ingantaccen bambancewa a cikinsa ba ga haila, ba da launi ba ko da waninsa, to, sai hailarta ta zama a kowane wata kwana shida ko kwana bakwai za ta fara daga kwana na biyar a kowane wata; Saboda hadisin Hamnah 'yar Jahsh - Allah Ya yarda da ita - cewa ita ta ce: Ya Manzon Allah ni ina haila mai yawa da tsanani, to me kake gani a cikinta? Haƙiƙa ta hana ni sallah da azumi, sai (Annabi)tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: «Zan siffanta miki (zan siffanta miki amfani da) auduga (ita ce auduga) da zaki sanyata akan farji, to cewa shi yana tafiyar da jini». Ta ce: Shi ne sama da hakan. Kuma a cikinsa ya ce: «Haƙiƙa wannan wani bugu ne daga cikin bugun Shaiɗan, sai ki yi haila kwana shida ko bakwai a cikin ilimin Allah - Maɗaukakin sarki -, sannan ki yi wanka, har idan kin ga cewa kin yi tsarki kuma kin tsarkaka, sai ki yi sallah kwana ashirin da huɗu ko ashirin da uku, kuma ki yi azumi». Hadisi. [Ahmad da Abu Daud da Tirmizi ne suka rawaito shi kuma ya inganta shi62, kuma an naƙalto daga Ahmad cewa ya inganta shi, da kuma daga Bukhari cewa ya kyautata shi]63.

Kuma faɗinsa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: «Kwana shida ko kwana bakwai" Ba don zaɓi ba ne, kawai shi don ƙoƙarine, sai ta yi duba a cikin abin da yake mafi kusa zuwa halinta daga wacce take kama da ita a halitta, kuma take kusanci da ita a shekaru da 'yan uwantaka, da kuma abin da shi ne mafi kusanci zuwa haila daga jininta, da makamancin haka daga izina. Idan ya kasance mafi kusanci shi ne kwana shida sai ta maida shi kwana shida, idan kuma ya kasance mafi kusanci shi ne kwana bakwai sai ta maida shi kwana bakwai.

 

HALIN WACCE TAKE KAMA DA MAI JININ CUTA:

Wani dalili zai iya faruwa ga mace, wanda yake wajabta zubar jini daga farjinta, kamar tiyata a mahaifa ko koma bayan hakan, wannan a kan nau'i biyu ne:

Nau'i na farko: A san cewa ba zai yiwu ta yi haila bayan tiyatar ba, kamar ace tiyatar tunɓuke mahaifa ne gaba ɗayanta, ko toshe ta ta yanda wani jini ba zai zuba daga gare ta ba, to wannan matar hukunce-hukuncen haila ba sa tabbata gare ta, kawai hukuncin ta shine hukuncin wacce take ganin fatsi-fatsi ko hanta-hanta ko danshi bayan tsarki, ba za ta bar sallah ko azumi ba, kuma ba zai hana tarawa da ita ba, kuma wanka ba ya wajaba daga wannan jinin, sai dai wanke jinin yana lazaimtarta a lokacin sallah, kuma ta sa ƙyalle ko waninsa a kan farjinta, don ta hana fitar jini, sannan ta yi alwala don yin sallah, kuma ba za ta yi alwala ba sai bayan shigar lokacinta in tana da lokaci ga sallar kamar salloli biyar, in ba haka ba fa to a lokacin yin sallar kamar nafiloli kai tsaye.

Nau'i na biyu: Ya zamana ba'a san hanin hailarta bayan tiyata ba, kai zai iya yiwuwa ta yi haila, to wannan hukuncinta shi ne hukuncin mai jinin cuta, faɗinsa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ga Faɗima 'yar Abu Hubaish yana nuni a kan hakan: «Kawai wancanan ki jijiyace ba haila ba ce, idan hailarki ta fuskanto to ki bar sallah»64.

Cewa faɗinsa: «Idan hailarki ta fuskanto» Yana fa'idantar da cewa hukuncin mai jinin cuta ga wacce take da haila tabbatacciya mai fuskantowa kuma mai bada baya, amma wacce take ba ta da haila tabbatacciya, to jininta jinin cuta ne a kowane hali.

HUKUNCE-HUKUNCEN MAI JININ CUTA:

Mun sani daga abin da ya gabata, yaushe ne jini yake zama haila, kuma yaushe ne yake zama jinin cuta, a duk lokacin da ya zama haila to hukunce-hukuncen haila zasu tabbata gare shi, kuma a duk lokacin da yazama jinin cuta to hukunce-hukuncen jinin cuta zasu tabbata gare shi.

Kuma haƙiƙa ambaton mai muhimmanci daga hukunce-hukuncen haila ya gabata.

Amma hukunce-hukuncen jinin cuta to kamar hukunce-hukuncen tsarki ne, babu bambanci tsakaknin mai jinin cuta da mai tsarki sai dai a abin da zai zo:

Na farko: Wajabcin alwala a kanta ga kowace sallah. Saboda faɗin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ga Faɗima 'yar Abu Hubaish: «Sannan ki yi alwala ga kowace sallah». Bukhari ne ya rawaito shi a babin wanke jini. Ma'anar hakan cewa ita ba za ta yi alwala ba don sallah abar iyakancewa lokaci sai bayan shigar lokacinta. Amma idan sallar ta kasance ba abar iyakancewa lokaci ba to cewa ita za ta yi alwala gare ta lokacin nufin aikatata.

Na biyu: Cewa ita idan ta yi nufin alwala to cewa ita ta wanke gurbin jinin,, sannan ta sanya ƙyalle a auduga don jinin ya tsane; Saboda faɗin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ga Hamnah: «Zan siffanta miki auduga domin cewa ita tana tafiyar da jini». Ta ce: To lallai shi yafi haka yawa. Ya ce: «To ki riƙi tufafi». Ta ce: Shi yafi haka yawa. Ya ce: «Ki ɗaure wurin jinin da tufafi». Hadisi. Duk abin da zai fita bayan hakan ba zai cutar da ita ba; saboda faɗin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ga Faɗima 'yar Abu Hubaish: «Ki nisanci sallah a kwanukan hailarki, sannan ki yi wanka ki yi alwala ga kowace sallah, sannan ki yi sallah, koda jinin ya ɗiga a kan tabarma». [Ahmad da Ibn Majah ne suka rawaito shi]65.

Na uku: Jima'i, haƙiƙa malamai sun yi saɓani a halarcinsa, idan ba ya jin tsoron zina da barinsa, amma daidai shine halarcinsa kai tsaye; domin cewa mata masu yawa sun kai goma ko sama da haka sun yi haila a zamanin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - amma Allah ko ManzonSa basu hana tarawa da su ba, Kai a cikin faɗinSa - Maɗaukakin sarki -:

﴿...فَاعْتَزِلُواْ النِّسَاء فِي الْمَحِيضِ...﴾

{Kuma ku nĩsanci mãta a cikin wurin haila...} [al-Baƙara: 222]. Daliline a kan cewa ƙaurace musu ba ya wajaba a cikin waninsa; kuma domin cewa sallah tana halarta daga gare ta, to jima'i shi ne mafi sauƙi, ƙiyasin jima'inta a kan jima'in mai haila ba ingantacce ba ne; domin cewa su basa daidaita har a wurin masu faɗin haramcin, kuma ƙiyasi ba ya inganta tare da mai banbatawa.

FASALI NA SHIDA: A KAN JININ BIƘI DA HUKUNCINSA

Jinin biƙi: Wani jini ne wanda mahaifa take zubo da shi saboda haihuwa, ko dai tare da ita ko kuma bayanta ko kafinta da yini biyu ko uku tare da naƙuda.

Babban Malamin Musulunci Ibn Taimiyya ya ce: «Abin da take ganin shi yayin da ta fara naƙuda, to, shi jinin biƙi ne». Bai iyakance shi da kwana biyu ko uku ba, manufarsa: Naƙuda ce da haihuwa take biye mata, in ba haka ba fa to ba jinin biƙi bane. Malamai sun yi saɓani: Shin yana da iyaka a mafi ƙarancinsa da mafi yawansa? Babban malami Taƙiyyund din ya faɗa a cikin saƙonsa a cikin Al'Asma Allati allaƙasshari'u alaiha (Shafi: 37): «Jinin biƙi babu iyaka ga mafi ƙarancinsa ko mafi yawansa, da za'a ƙaddara cewa wata mace ta ga jini sama da kwana arba'in ko sittin ko sabab'in sai ya yanke to shi jinin biƙi ne, sai dai idan ya zarce to shi jinin cuta ne, a wannan lokacin mafi ƙaranci shi ne kwana arba'in cewa shi ne ƙarshen mafi yawan abin da hadisai suka zo da shi». Ya ƙare.

Na ce: A kan haka ne idan jinita ya ƙaru a kan kwana arba'in, kuma ta kasance tana da wata al'ada ta yankewarsa bayan nan, ko wasu alamomi suka bayyana a cikinsa kusan yankewa to sai ta yi saurare har sai ya yanke in ba haka ba fa to ta yi wanka yayin cikar kwana arba'in; domin cewa shi ne mafi rinjaye sai dai idan ya dace da zamanin hailarta, sai ta zauna har lokacin hailar ya ƙare, idan ya yanke bayan nan, to, yana kamata ya zama kamar al'ada gare ta, sai ta yi aiki da gwargwadansa a gaba, idan ya ci gaba to ita mai jinin cuta ce, sai ta koma zuwa hukunce-gukuncen mai jinin cutar da ya gabata, Da za ta yi tsarki da yankewar jini daga gare ta, to ita mai tsarki ce, koda kafin kwana arba'in ne, sai ta yi wanka ta yi sallah ta yi azimi kuma mijinta ya tara da ita, sai dai idan yankewar ya zama ƙasa da yini ɗaya to babu hukunci gare shi, ya faɗe shi a cikin al-Mugni66.

Jinin biƙi ba ya tabbata sai idan ta haife abin da halittar mutum yake bayyana a cikinsa, da za ta haife ƙaramin ɓari halittar mutum ba ta bayyana gare shi ba, to, jininta bai zama jinin biƙi ba, kai shi jinin cuta ne, sai hukuncinsa ya zama hukuncin mai jinin cuta, kuma mafi ƙarancin muddar wacce halittar mutum take bayyana a cikinta kwana tamanin ne daga farkon ciki, kuma mafi rinjayensa kwana casa'in ne.

Al-Majd Ibnu Taimiyya ya ce: A duk lokacin da ta ga wani jini kwana ɗaya a kan naƙuda kafinsa to ba za ta juya zuwa gare shi ba, kuma a bayansa sai ta kame daga sallah da azumi, sannan idan al'amarin ya yaye bayan haihuwa a saɓanin zahiri sai ta dawo ta riska, idan kuma al'amarin bai yaye ba sai hukuncin zahiri ya zarce babu komawa gare ta. Ya cirato shi daga gare shi a cikin Sharhin al'Iƙna67.

HUKUNCE-HUKNCEN JININ BIƘI:

Hukunce-hukncen jinin biƙi kamar hukunce-hukuncen haila ne daidai wa daida, sai a abin da zai zo:

Na farko: Iddah sai ayi izina da saki bada jinin biƙi ba; domin cewa shi idan sakin ya kasance kafin haihuwa to iddar zata ƙare da zarar an haife shi bada jinin biƙi ba, kuma idan sakin ya kasance bayan haihuwa, to, sai ta saurari dawowar hailar kamar yanda ya gabata.

Na biyu: Tsawon lokacin Īlā'i ana ƙirga muddar haila daga gare shi, amma ba'a ƙirga muddar jinin biƙi daga gare shi.

Īlā'i: Shi ne mutum ya yi rantsuwa a kan barin tarawa da matarsa har abada, ko zuwa wata muddar ta zata ƙaru a kan wata huɗu, idan ya yi rantsuwa kuma ta neme shi da yin jima'i, sai a sanya masa tsawon wata huɗu daga rantsuwarsa, idan muddar ta cika sai a tilasta shi a kan yin jima'in ko rabuwa da buƙatar matar, to wannan muddar idan jinin biƙi ya shuɗe da mace ba za'a ƙirga shi a kan mijin ba, kuma a ƙara shi a kan watanni huɗu da gwargwadan muddarsa, saɓanin haila cewa muddar ta ana ƙirgata a kan mijin.

Na uku: Balaga tana tabbata da haila ne ba ta tabbata da jinin biƙi; domin cewa mace ba zai yiwu ba ta ɗauki ciki har sai maniyyi ya zuba daga gare ta, sai ya zama samuwar balagar da zubar maniyyin da ya gabata ne ga cikin.

Na huɗu: Cewa jinin haila idan ya yanke, sannan ya dawo a al'ada, to, shi haila ne tabbas, kamar al'adarta ta kasance kwana takwas, sai taga haila kwana huɗu, sannan ya yanke kwana biyu, sannan ya dawo a kwana na bakwai da na takwas, to wannan mai dawowar haila ne tabbas, hukunce-hukuncen haila zasu tabbata gare shi. Amma jinin biƙi idan ya yanke kafin kwana arba'in sannan ya dawo a rana ta arba'in to shi abin kokwanto ne a cikinsa, yana wajaba a kanta ta yi sallah ta yi azumin farilla, abin sanyawa lokaci a cikin lokacinsa, kuma abin da yake haramta a kan mai haila yana haramta a kanta banda wajibabbu, kuma za ta rama abin da ta aikata bayan tsarkinta a wannan jinin daga abin da rama shi yake wajaba a kan mai haila. Wannan shi ne mafi shahara a wurin malaman fiƙihu daga Mazahabar Hanbaliyya68.

Amma daidai shi ne cewa jini idan ya dawo mata a cikin zamanin da zai yiwu ya zama jinin biƙi to shi jinin biƙi ne, inba haka bafa to shi jinin haila ne sai dai idan in ya zarce mata to sai ya zama jinin cuta.

Wannan kusa ne daga abin da ya cirato shi a cikin al-Mugni69 daga Imam Malik - Allah Ya yi masa rahama - inda ya ce: Malik ya ce: «Idan taga jini bayan kwana biyu ko kwana uku - yana nufin: Daga yankewarsa - to shi jinin biƙi ne in ba haka ba fa to shi haila ne». Ya ƙare. Kuma shi ne zahirin zaɓin babban malamin Musulunci Ibnu Taimiyya - Allah Ya yi masa rahama -.

Kuma babu wani abu a cikin jini abin kokwanto a cikinsa gwargwadan abin da ke faruwa, sai dai kokwanto wani al'amari ne mai danganawa wanda mutane suke saɓani a cikinsa gwargwadan saninsu da kuma fahimtarsu. Al-ƙur'ani da Sunna a cikinsu akwai bayanin kowane abu, kuma Allah - Maɗaukakin sarki - bai wajabtawa wani mutum yin azumi sau biyu ba, ko ya yi ɗawafi sau biyu, sai dai in a na farkon akwai ɓaci wanda riskuwarsa ba zai yiwu ba sai dai ramuwa, amma yayin da bawa ya aikata abin da zai iya na abin da aka ɗora masa gwargwadan ikonsa, to. haƙiƙa wuyayensa ya kubuta. Kamar yanda Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce:

﴿لَا يُكَلِّفُ ٱللَّهُ نَفۡسًا إِلَّا وُسۡعَهَا...﴾

{Allah ba Ya ɗorawa wani rai sai abin da zai iya...} [al-Baƙara: 286]. Kuma Ya ce:

﴿فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ مَا ٱسۡتَطَعۡتُمۡ...﴾

{Sai ku bi Allah da taƙawa gwargwadon abin da kuka sãmi ĩko...} [at-Tagabun: 16].

Bambanci na biyar tsakanin haila da jinin biƙi: Cewa shi a haila, idan ta samu tsarki kafin al'ada to ya halatta ga mijinta saduwa da ita ba tare da wani karhanci ba, amma a jinin biƙi idan ta samu tsarki kafin kwana arba'in, to, an karhanta ga mijinta ya sadu da ita a kan zance mafi shahara a Mazahaba, amma daidai cewa shi ba'a karhanta masa tarawa da ita ba. Kuma shi ne faɗin mafi yawan malamai; domin karhanci hukuncine na shari'a yana buƙatuwa zuwa dalili na shari'a. Kuma a wannan mas'alar babu wani abu in ba abin da Imam Ahmad ya ambata ba daga Usman ibn Abul Ās cewa, ita ta zo masa kafin kwana arba'in, sai ya ce: Kada ki kusance ni70.

Wannan ba ya lazimtar karhanci; domin cewa shi zai iya kasancewa daga gare shi ne a kan tafarkin kewayo don tsoro daga cewa ita ba ta tabbatar da tsarkin ba, ko kuma daga jini ya motsa saboda jima'i, ko wanin hakan daga dalilai. Allah ne mafi sani.

Fasali na bakwai: A kan yin amfani da abin da yake hana haila ko yake jawo shi, da abin da yake hana ciki, ko yake zubar dashi.

Mace ta yi amfani da abin da yake hana hailarta ya halatta da sharuɗɗa biyu:

Na farko: Kada a ji tsoron cuta a kanta, idan aka ji tsoron cuta a kanta daga hakan, to, ba ya halatta; Saboda faɗinSa - Maɗaukakin sarki -:

﴿...وَلَا تُلۡقُواْ بِأَيۡدِيكُمۡ إِلَى ٱلتَّهۡلُكَةِ...﴾

{...Kada ku jefa kanku da hannayen ku zuwa ga halaka...} [al-Baƙara: 195].

﴿...وَلَا تَقۡتُلُوٓاْ أَنفُسَكُمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ بِكُمۡ رَحِيمٗا﴾

{...Kuma kada ku kashe kan ku lallai Allah Ya kasance Mai yawan jin ƙaine gare ku} [an-Nisa': 29].

Na biyu: Hakan ya kasance da izinin mijin in ya kasance yana rataye da shi, kamar ta kasance mai idda daga gare shi ta fuskar da ciyarwarta take wajaba a kansa, to sai ta yi amfani da abin da yake hana ɗaukar ciki; don iddarta ta tsawaita kuma ciyarwar ta ta ƙaru a kansa, to ba ya halatta a gare ta ta yi amfani da abin da yake hana ɗaukar ciki a wannan lokacin saida izininsa, Haka nan in ya tabbata cewa hana haila yana hana ɗaukar ciki, to babu makawa daga izinin miji, yayin da halacci ya wajaba to abin da yafi shi ne rashin yin amfani da shi sai da buƙata; domin barin ɗabi'a a kan abin da take a kansa shi ne mafi kusanci zuwa daidaituwar lafiya sai aminci.

Amma amfani da abin da yake jawo haila to ya halatta da sharuɗɗa biyu kuma:

Na farko: Kada ta yi dabara da shi a kan sarayar da abin da yake wajibi, kamar tayi amfani dashi kusa da Ramadan saboda ta sha azumi ko ta sarayar da sallah da shi, da makamancin hakan.

Na biyu: Hakan ya kasance da izinin miji; domin samuwar haila yana hani daga cikar jin daɗi, to amfani da abin da yake hana haƙƙinsa ba ya halatta sai da yardarsa ko da ta kasance sakakkiyace, domin a cikinsa akwai gaggauto da sarayar haƙƙin miji daga kome in ta kasance da kome a kanta.

Amma amfani da abin da yake hana ɗaukar ciki to ya kasu nau'i biyu:

Na farko: Shi ne ya hana shi hani mai zarcewa, to wannan ba ya halatta; domin cewa shi yana yanke ciki sai zuriya ta yi ƙaranci, kuma shi ne saɓanin manufar mai shara'antawa na yawaita al'ummar Musulunci; kuma cewa shi ba'a aminta mutuwar 'ya'yanta samammu sai ta wanzu mai wabiya mara 'ya'ya.

Na biyu: Shi ne ya hana shi hani na lokaci, misalin mace ta kasance mai yawan ciki ce, kuma cikin yana wahalar da ita, sai take son ta yi tsarin cikin ta kowace shekara biyu sau ɗaya, ko makamancin hakan to wannan ya halatta, da sharaɗin mijinta ya yi mata izini, kuma ya kasance babu cutarwa a kanta. Dalilinsa shi ne cewa sahabbai sun kasance suna azalu ga matansu a zamanin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - saboda kada matansu su ɗauki ciki71, amma ba'a hana su hakan ba. Azalu shi ne mutum ya tara da matar sa, kuma ya zare azzakarin sa a lokacin zubar maniyyi sai ya zuba a wajen farji.

Amma amfani da abin da yake zubar da ciki to shi nau'i biyu ne:

Na farko: Shi ne ya yi nufin ɓata shi ta hanyar zubar da shi. To wannan idan ya kasance bayan an busa masa rai ne, to shi haramun ne babu kokwanto; domin cewa shi kashe rai ne abin haramtawa ba tare da wani haƙƙi ba, kuma kashe ran da aka haramta haramun ne a Al-ƙur'ani da Sunna da Ijima'in musulmai. Idan ya kasance kafin busa rai ne a cikinsa, to, haƙiƙa malamai sun samu saɓani a cikin halaccin sa. Daga cikinsu akwai wanda ya hana shi, daga cikinsu akwai wanda ya ce: Yana halatta muddin dai bai zama gudan jini ba, wato: Muddin dai kwana arba'in basu shuɗe a kansa ba, daga cikin su akwai wanda ya ce: Yana halatta muddin dai halittar mutum ba ta bayyana a cikinsa ba.

Mafi kewayo shi ne hani daga zubar da shI sai don wata buƙata, kamar mahaifiyar ta kasance mara lafiyace ba za ta iya ɗaukar ciki ba ko makamancin hakan, to, sai zubar da shi ya halatta a wannan lokacin, sai dai idan wani lokaci ya shuɗe a kansa wanda zai yiwu halittar mutum ta bayyana a cikinsa sai ya hanu. Allah ne mafi sani.

Na biyu: Kada a nufi ɓata shi ta hanyar zubar da shi, shi ne ƙoƙarin zubar da shi ya kasance a lokacin ƙarewar muddar cikin ce da kuma kusancin haihuwa, to, wannan ya halatta da sharaɗin kada ya kasance akwai cutarwa a kan mahaifiyar ba a kan ɗan ba, kuma kada al'amarin ya buƙatu zuwa tiyata, idan ya buƙaci tiyata to shi yana da halaye huɗu:

Na farko: Shine mahaifiyar ta kasance mai rai ce kuma ɗan a raye yake, to, tiyata ba ta halatta sai da larura, shi ne haihuwar ta ta yi wahala, sai ta buƙaci tiyata, wannan domin cewa jiki amana ne a wurin bawa, ba zai yi tasarrufi a cikinsa ba da abin da ake jin tsoro gare shi sai don maslaha babba; kuma domin cewa shi wataƙila yana zatan cewa babu wata cuta a tiyatar sai cutarwar ta faru.

Na biyu: Shi ne mahaifiyar ta kasance matacciya kuma ɗan ma matacce, to yin tiyata ba ya halatta don fitar da shi saboda rashin wata fa'ida.

Na uku: Shi ne mahaifiyar ta kasance mai rai ce amma ɗan matacce ne, to yin tiyata yana halatta don fitar da shi, sai dai idan ana jin tsoron cutarwa a kan mahaifiyar; domin a zahiri - Allah ne mafi sani - cewa ciki idan ya mutu ba ya kusa ya fita ba tare da tiyata ba, to zarcewarsa a cikin ta zai hanata ɗaukar ciki na gaba, kuma zai wahalar da ita, wataƙila ta wanzu bazawara idan ta kasance mai idda ce daga mijin da ya gabata.

Na huɗu; Shi ne mahaifiyar ta kasance matacciya amma cikin rayayye ne, idan ya kasance ba'a ƙaunar rayuwarsa to yin tiyata ba ya halatta.

Idan kuma ya kasance ana ƙaunar rayuwarsa, idan ya kasance haƙiƙa sashinsa ya fita sai a tsaga cikin mahaifiyar don fitar da ragowar, idan kuma wani abu bai fita ba daga gare shi to haƙiƙa malummanmu - Allah Yayi musu rahama - sun ce; Ba'a tsaga cikin mahaifiya don fitar da ciki; domin hakan misla ne, amma dadai shi ne cewa za'a tsaga cikin idan fitar da shi ba ya kasancewa ba tare da shi ba. Wannan shi ne zaɓin Ibnu Hubaira, ya faɗa a cikin al'Insaf72: Kuma shi ne ya fi.

Na ce; Musamman ma a wannan lokacin na mu, domin yin tiyata ba misla ba ne; domin cewa shi ana tsaga ciki sannan a ɗinke shi, kuma domin cewa alfarmar rayayye ita ce mafi girma daga alfarmar matacce; kuma domin cewa tsamo abin tsarewa daga halaka dole ne, ciki kuma mutum ne abin tsarewa sai tsamo shi ya zama dole. Allah shi ne Mafi sani.

Faɗakarwa: A kan halayen da zubar da ciki yake halatta a cikin abin da ya gabata babu makawa daga izinin wanda yake da cikin a hakan kamar miji.

A nan ne abinda muka yi nufin rubuta shi ya zo ƙarshe, a wannan maudhu'in mai muhimmanci. Haƙiƙa mun taƙaita a cikinsa a kan tushen mas'aloli da kuma kiyaye su, in ba haka ba fa to rassansu da ɓangarorinsu da abin da yake faruwa ga mata daga hakan kogi ne ba shi da gaɓa. Sai dai mai basira zai sami ikon dawo da rassa zuwa tushensu, kuma ɓangarori zuwa gaba ɗayansu da ƙa'idodinsu, kuma ya ƙiyasta abubuwa da masu kamanceceniya da su.

Kuma mai bada fatawa ya san cewa shi tsani ne tsakaninsa da tsakanin Allah da halittarSa a wajen isar da abin da Manzanni suka zo dashi, da kuma bayaninsa ga halitta, kuma cewa shi abin tambaya ne daga abin da ke cikin Al-ƙur'ani da Sunna, domin cewa su ne tushe da aka ɗorawa bawa fahimtarsu, da kuma aiki da su. Dukkan abin da ya saɓawa Al-ƙur'ani da Sunna, to, shi kuskure ne, ya wajaba a mayarwa wanda ya faɗe shi, aiki da shi baya halatta, duk da cewa mai faɗar zai iya zama abin yiwa uzuri mai ƙoƙari sai a ba shi lada a kan ƙoƙarinsa, sai dai cewa waninsa wanda yake masani da kuskurensa karɓarsa ba ya halatta.

Kuma yana wajaba a kan mai bada fatawa ya tsarkake niyya saboda Allah - Maɗaukakin sarki -, ya nemi taimakonSa a dukkanin wani abu da ya taso gare shi, ya roƙi Allah - Maɗaukakin sarki - tabbata da dacewa ga daidai.

Kuma yana wajaba a kansa ya zama a bin lurarsa shi ne abin da ya zo a cikin Al-ƙur'ani da Sunna, sai ya yi duba ya yi bincike a cikin hakan ko a cikin abin da ake neman taimako da shi daga zancen ma'abota ilimi a kan fahimarsu.

Kuma cewa da yawa wata mas'ala zata faru daga mas'aloli, sai mutum ya yi bincike a cikinta a abin da yake da iko a kansa daga zancen ma'abota ilimi, sannan ba zai sami abin da zai nutsu zuwa gare shi ba a cikin hukuncinta, wataƙila ma ba zai sami wani ambato gare ta kwata-kwata ba. Idan ya koma zuwa Al-ƙur'ani da Sunna hukuncinsu zai bayyana gare shi a kusa a bayyane, hakan gwargwadan tsarkake niyya da ilimi da kuma fahimta.

Kuma yana wajaba a kan mai bada fatawa yabi a hankali a cikin hukunci a lokacin rikici, kada ya yi gaggawa, da yawa hukuncin da zai yi gaggawa a cikinsa, sannan bayan duba makusanci, sai ya bayyana gare shi cewa shi mai kuskure ne a cikinsa, sai ya yi nadama a kan hakan, wataƙila ba zai iya riskar abin da ya bada fatawa da shi ba!.

Mai bada fatawa idan mutane suka fahimci jinkiri da tabbatarwa, za su amince da faɗarsa, kuma za su yi la'akari da shi. Idan kuma suka gan shi mai gaggawa ne mai yawan kurakurai, amincinsu ba zai kasance gare shi ba a cikin abin da yake bada fatawa da shi, sai ya zama da gaggawarsa da kuskurensa ya haramtawa kansa kuma ya haramtawa waninsa abin da ke tare da shi na ilimi da kuma daidai.

Muna roƙon Allah - Maɗaukakin sarki - Ya shiryar damu da 'yan uwanmu musulmai hanyarSa madaidaiciya, kuma Ya jiɓintar damu da kulawarSa, ya kiyaye mu daga tuntuɓe da kiyayewarSa, lallai cewa Shi Mai kyauta ne, Mai yawan karamci. Allah Ya yi daɗin tsira da aminci ga Annabinmu Muhammad da alayensa da sahabbansa baki ɗaya. Godiya ta tabbata ga Allah wanda da ni'imarSa ne ayyuka na gari suke cika.

(Saƙon) ya cika da alƙalamin mabuƙaci zuwa ga Allah

Muhammad bIn Salih Al-Uthaimeen

A hantsin ranar Juma'a

14 Sha'aban shekara ta1392 H

 

 

***

Teburin bayani

 

FASALI NA FARKO: A CIKIN MA'ANAR HAILA DA HIKIMAR SA 4

FASALI NA BIYU: A KAN ZAMANIN HAILA DA TSAWON LOKACIN SA 6

FASALI NA UKU: A ABUBUWAN DA SUKE BIJIROWA HAILA. 17

FASALI NA HUƊU: A CIKIN HUKUNCE-HUKUNCEN HAILA 22

FASALI NA BIYAR: A CIKIN JININ CUTA DA HUKUNCE-HUKUNCENSA 42

HALAYEN JININ CUTA: 44

HALIN WACCE TAKE KAMA DA MAI JININ CUTA: 49

HUKUNCE-HUKUNCEN MAI JININ CUTA: 50

FASALI NA SHIDA: A KAN JININ BIƘI DA HUKUNCINSA 52

HUKUNCE-HUKNCEN JININ BIƘI: 54

Fasali na bakwai: A kan yin amfani da abin da yake hana haila ko yake jawo shi, da abin da yake hana ciki, ko yake zubar dashi. 58

 

***

 


Bukhari ne ya fitar da shi: Littafin Haila, babin mai haila tana aikata dukkan ayyukan Hajji sai dai ɗawafi a ɗakin, lamba ta (305), da Muslim: Littafin Hajji, babin bayanin fuskokin harama, lamba ta (1211).

Bukhari ne ya fitar da shi: Littafin Umra, babin ladan Umra gwargwadon wahala, lamba ta (1662), da Muslim: Littafin Hajji, babin bayanin nau'o'in Ihrami, lamba ta (1211).

Risalatul Asma allati allaƙash Shari'ul ahkam biha (shafi na: 35)

Littafin da ya gabata (shafi na: 36).

Littafin da ya gabata (s: 38).

Bukhari ne ya fitar da shi: Littafin imani, babin Addini sauƙi ne, lamba ta (39), daga hadisin Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -.

Bukhari ne ya fitar da shi a littafin darajoji, babin siffar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, lamba ta (3560), da Muslim a littafin falaloli, babin nisantarsa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - daga zunubai, lamba ta (77/2327).

Majmu al-Fatawah (238-239/19).

al-Awsaɗ, (2/356).

Ka duba: "al-Mugni" (405/1).

al-Mudawwana (1/155), da an-Nawadir waz-Ziyadat (1/136).

Ikhtilaf al-Fuƙaha na al-Marwazi (: 193), al-Awsaɗ (2/239).

al-Umm (82/1).

Majmu'u Fatāwa (238/-239/19).

al-Mugni (396/1)

Abu Dawud ne ya fitar da shi: Littafin Tsarki, Babi kan matar da ta ga hanta-hanta da fatsi-fatsi bayan tsarki, lamba ta (307).

Bukhari ne ya fitar da shi a littafin haila, babin fatsi-fatsi da hanta-hanta a wanin kwanakin haila, a lamba ta (326).

Fathul bari (1/426).

Sahih al-Bukhari (1/ 71).

Bukhari ne ya rataya shi: a littafin haila, babi na zuwan haila da komawarsa, kafin hadisi mai lamba (320).

al-Umm (1/ 83-84).

An naƙalto daga gare su a al-Insaf.

al-Asl (19/2-20)

al-Mugni (226/1).

al-Mugni (257/1).

Bukhari ne ya fitar da shi a littafin lokutan sallah, babin wanda ya riski raka'a daga sallah, lamba ta (580). Da Muslim a littafin masallatai da wuraren sallah, babin wanda ya riski raka'a daga sallah to lalle ya riski sallar, lamba ta (607), daga Hadisin Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -.

Bukhari ne ya fitar da shi a littafin lokutan sallah, babin wanda ya riski raka'a ta Alfijir, lamba ta (579). Da Muslim a littafin masallatai da wuraren sallah, babin wanda ya riski raka'a to ya riski waccan sallar, lamba ta (608), daga Hadisin Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -.

Al-Majmu'u Sharhu al-Muhadhdhab (3/70).

Bukhari ne ya fitar da shi: Littafin Haila, babin karatun mutum a cinyar matarsa alhali tana haila, lamba ta (297). da Muslim: Littafin Haila, babin jinginar mutum a cinyar matarsa alhali tana haila da karatun Alƙur'ani, lamba ta (301), daga hadisin A'isha - Allah Ya yarda da ita -.

Bukhari ne ya fitar da shi: Littafin Haila, babin halartar mai haila sallolin idi biyu da gayyatar musulmai, kuma su ware daga wurin sallah, lamba ta (324). Da Muslim: Littafin sallolin idi biyu, babin ambaton halaccin fitar mata a sallolin idi biyu zuwa filin sallah da halartar huɗuba, sune a ware daga maza, lamba ta (890).

Al-Majmu'u (2/357).

Duba Sahihul Bukhari: Littafin Haila, babin mai haila tana aikata dukkan ayyukan ibada sai dai ɗawafi a Ka'aba, da Fathul Bari (1/ 407-408).

Fathul Bari (1/ 408).

al-Awsaɗ (2/223).

al-Majmu'u (2/356).

Fathul Bari (1/ 408).

Bukhari ya kawo shi Mu'allaƙ: Littafin Haila, babin mai haila tana kammala dukkan Manasik sai dai ɗawafi a Ka'aba, kafin hadisi mai lamba ta (305).

Tirmizi ya fitar da shi: Littafin tsarki, Babi kan mai janaba da mai haila cewa ba sa karanta Alƙur'ani, lamba ta (131).

Ka duba: Al'ilal na al-Tirmizi (69), da Al-sunan al-kubra na Baihaƙi (1/309), da Al'ahkam al-shar'iyya na Ibn Abdulhaƙ(1/504), da Nasb al-rayah na al-zaila'i (1/195).

Majmu al-Fatawah (191/26).

Bukhari ne ya fitar da shi: Littafin Haila, babin mai haila ba ta rama sallah, lamba ta (321). Da Muslim: Littafin Haila, babin wajabcin rama azumi a kan mai haila banda sallah, lamba ta (335). Lafazin na Muslim ne.

Bukhari ne ya fitar da shi: Littafin ilimi, babin kunya a ilimi, lamba ta (130). da Muslim: Littafin Haila, babin wajibcin wanka akan mace..., lamba ta (313).

Bukhari ne ya fitar da shi: Littafin Azumi, Babin wankan mai azumi, lamba ta (1931). Da Muslim: Littafin Azumi, Babin ingancin azumin wanda alfijir ya keto masa alhali yana da janaba, lamba ta (1109).

Bukhari ne ya fitar da shi a littafin Haila, babin mai haila za ta yi dukkan ayyukan Hajji sai dai ɗawafi a Ɗakin Allah, lamba ta (305), da Muslim a littafin Hajji, babin bayanin nau'ikan yin harama, lamba ta (1211).

Bukhari ne ya fitar da shi: Littafin Hajji, babin ɗawafin ban kwana, lamba ta (1755). Da Muslim: Littafin Hajji, babin wajabcin ɗawafin ban kwana da saryarwarsa ga mai haila, lamba ta (1328).

Bukhari ne ya fitar da shi: Littafin Hajji, babin idan mace ta yi haila bayan ta yi ɗawafin Ifada, lamba ta (1757). Da Muslim: Littafin Hajji, babin wajabcin ɗawafin bankwana, lamba ta (1211).

Bukhari ne ya fitar da shi: Littafin Haila, babin halartar masu haila sallolin idi biyu da gayyatar musulmai, kuma su ware daga filin sallah, lamba ta (324). Da Muslim: Littafin sallolin idi biyu, babin ambaton halaccin fitar mata a sallolin idi biyu zuwa filin sallah da halartar huɗuba, suna masu warewa daga maza, lamba ta (890).

Muslim ne ya fitar da shi: Littafin haila, babin halaccin mai haila ta wanke kan mijinta, lamba ta (302).

Bukhari ne ya fitar da shi: Littafin haila, babin rungumar mai haila, lamba ta (301). Da Muslim: Littafin haila, babin rungumar mai haila a saman zani, lamba ta (293).

Bukhari ne ya fitar da shi: Littafin saki, lamba ta (5251). da Muslim: Littafin saki, babin haramcin sakin mai haila ba tare da yardarta ba, da cewa idan ya saɓa to sakin ya auku, kuma a umarce shi da ya mayar da ita, lamba ta (1471), daga hadisin Ibnu Umar - Allah Ya yarda da su -.

Bukhari ne ya fitar da shi: Littafin saki, babin Khul'i da yadda saki yake a cikinsa, lamba ta (5273), daga hadisin Ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su -.

Bukhari ne ya fitar da shi: Littafin Haila, babin zuwan haila da tafiyarta, lamba ta (320), da Muslim: Littafin Haila, babin mai jinin istihadha da wankanta da sallarta, lamba ta (333), daga hadisin Aisha - Allah Ya yarda da ita -.

Bukhari ne ya fitar da shi: Littafin haila, babin wankan haila, lamba ta (315), da Muslim: Littafin haila, babin mustahabbancin mai wanka daga haila ta yi amfani da ƙyalle mai almiski a gurbin jini, lamba ta (332), daga hadisin A'isha - Allah Ya yarda da ita -.

Muslim ne ya fitar da shi: Littafin Haila, babin hukuncin kitson mai yin wanka, lamba ta (330), daga hadisin Ummu Salama - Allah Ya yarda da ita -.

Bukhari ne ya fitar da shi: Littafin Alwala, babin wanke jini, lamba ta (228), da Muslim: Littafin Haila, babin mai jinin ciwo da wankanta da sallarta, lamba ta (333), daga hadisin Nana Aisha - Allah Ya yarda da ita -.

Ahmad ne ya fitar da shi (6/349), da Abu Dawud: Littafin ɗahara, babin wanda ya ce idan haila ta gabato a bar sallah, lamba ta (287), da Tirmizi: Babukan ɗahara, babin mace mai istihada cewa tana haɗa salloli biyu da wanka guda ɗaya, lamba ta (128), daga hadisin Himnah bint Jahsh - Allah Ya yarda da ita -.

Sunan al-Tirmizi: Littafin Tsarki, babin mai istihada wadda take haɗa salloli biyu da wanka guda, bayan hadisi lamba ta (128).

Bukhari ne ya fitar da shi: Littafin Haila, babin Haila, da abin da ake gaskata mata a kansa na haila da ciki, a cikin abin da zai yiwu na haila, lamba ta (325), daga hadisin Nana Aisha - Allah Ya yarda da ita -.

Muslim ne ya fitar da shi: Littafin Haila, babin mai istihadha da wankanta da sallarta, lamba ta (334), daga hadisin Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita -.

Abu Dawud ne ya ruwaito shi: a Littafin tsarki, Babin wanda ya ce idan haila ta zo a bar sallah, lamba (286); da Nasa'i: a Littafin tsarki, Babin abin da ya zo game da mai istihadha wacce ta san kwanakin hailarta kafin jini ya zarce mata, lamba ta (211); da Ibnu Majah: a Littafin tsarki da sunnoninsa, Babin abin da ya zo game da mai istihadha wacce ta san kwanakin hailar ta kafin jini ya zarce mata, lamba ta (620); da Ibnu Hibban a cikin Sahihinsa (1348), da Hakim a cikin Mustadrak (618), daga hadisin A'isha - Allah Ya yarda da ita -.

Ahmad ne ya fitar da shi (6/439), da Abu Dawud: Littafin tsarki, babin wanda ya ce idan haila ta gabato sai a bar sallah, lamba ta (287), da Tirmizi: Babukan tsarki, babin mace mai istihadha tana haɗa salloli biyu da wanka ɗaya, lamba ta (128), daga hadisin Himnatu bnt Jahsh - Allah Ya yarda da ita -.

Sunan Tirmizi: Littafin tsarki, babin mai jinin istihadha cewa tana haɗawa tsakanin salloli biyu da wanka ɗaya, bayan hadisi lamba ta (128).

Bukhari ne ya fitar da shi: Littafin Alwala, babin wanke jini, lamba ta (228), da Muslim: Littafin Haila, babin mai jinin istihadha da wankanta da sallarta, lamba ta (333), daga hadisin Nana Aisha - Allah Ya yarda da ita -.

Ahmad ne ya fitar da shi (6/204), da Ibnu Majah, Littafin tsarki da Sunnoninsa, Babi kan abin da ya zo game da mai istihadha wacce ta ƙididdige kwanakin al'adarta, kafin jinin ya zarce mata, lamba ta (624), daga hadisin Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita -.

al-Mugni (252/1-253).

Kasshaf al-Ƙina (219/1).

al-Mugni (253/1).

al-Mugni (253/1).

Al-Mugni (2/252), da kuma asar na Usman ɗan Abul Ās, Abdurrazaƙ ya fitar da shi a cikin al-Musannaf (1202), da Ibnu Abi Shaibah a cikin al-Musannaf (17450), da al-Darimi a cikin al-Sunan (990), da Ibnul Jarud a cikin al-Muntaƙa (118).

Bukhari ne ya fitar da shi: Littafin aure, babin Azalu, lamba ta (5209), da Muslim: Littafin aure, babin hukuncin Azalu, lamba ta (1440), daga hadisin Jabir - Allah Ya yarda da shi -.

al-Insaf (556/2).

Hukunce-hukuncen mai ruɗanin haila, na Darimi (sh: 17).