الوسائل المفيدة للحياة السعيدة (هوسا)

كتاب الوسائل المفيدة للحياة السعيدة للشيخ عبد الرحمن بن ناصر السعدي يعالج أسباب السعادة الحقيقية من منظور إيماني عميق، فيرشد القارئ إلى الطمأنينة القلبية من خلال الإيمان والعمل الصالح، وذكر الله، والقناعة، والتفكر في النعم، والإحسان، والتوكل، والصبر، وتقدير الأمور، بأسلوب جميل، يضع بين يديك خارطة لحياة مطمئنة، متزنة، وسعيدة رغم تقلبات الحياة.

  • earth Harshe
    (هوسا)
  • earth Wallafar:
    الشيخ عبدالرحمن بن ناصر السعدي

Wasu fassarorin daban 53

ta تاميلي- தமிழ் bn بنغالي- বাংলা tr تركي- Türkçe zh صيني- 中文 ha هوسا- Hausa ar عربي- العربية ur أردو- اردو hi هندي- हिन्दी ms ملايو- Melayu en إنجليزي- English ps بشتو- بشتو fr فرنسي- Français ru روسي- Русский sw سواحيلي- Kiswahili fa فارسي- فارسي uz أوزبكي- Ўзбек id إندونيسي- Indonesia tl فلبيني تجالوج- Tagalog gu غوجاراتية- ગુજરાતી te تلغو- తెలుగు si سنهالي- සිංහල as آسامي- অসমীয়া es إسباني- español bs بوسني- bosanski pt برتغالي- português ro روماني- română rw كينيارواندا- Kinyarwanda pl بولندي- polski ml مليالم- മലയാളം mg ملاغاشي- Malagasy lt ليتواني- lietuvių am أمهري- አማርኛ ka جورجي- ქართული ku كردي- Kurdî kn كنادي- ಕನ್ನಡ it إيطالي- italiano cs تشيكي- čeština prs دري- فارسی دری sr صربي- Српски lo لاو- ພາສາລາວ dv ديفهي- ދިވެހި jo جوالا- Jóola sx سوننكي- Soninke ky قرغيزي- Кыргызча nl هولندي- Nederlands pa بنجابي- ਪੰਜਾਬੀ th تايلندي- ไทย mk مقدوني- македонски vi فيتنامي- Tiếng Việt ceb بيسايا- Bisaya hu هنجاري مجري- magyar ne نيبالي- नेपाली yo يوربا- Èdè Yorùbá
PHPWord

 

 

 

الوَسَائِلُ المُفِيْدَةُ لِلحَيَاةِ السَّعِيْدَةِ

 

Hanyoyi Masu Amfani Don Samun Rayuwa Mai Dadi

 

 

الشَّيْخُ عَبْدُ الرَّحمَنِ بْنُ نَاصِرٍ السَّعْدِيُّ

رَحِمَهُ اللهُ

 

Shiekh Abdulrahman bn Nasir al-Sa'di (Allah Ya yi masa rahama)

 

 

 


بِسْمِ اللهِ الرَّحمَنِ الرَّحِيمِ

Hanyoyi Masu Amfani Don Samun Rayuwa Mai Dadi

Gabatarwa

Yabo ya tabbata Allah wanda Shi ne Ya cancanci dukkan yabo, kuma ina shaida cewa babu abin bautawa bisa cancanta sai Allah, Shi kaɗai yake ba Shi da abokin tarayya, kuma ina mai shaidawa Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa ne, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da alayansa da sahabban sa.

Bayan haka: Lallai hutun zuciya, da nutsunuwarta da farin cikinta da gushewar baƙin cikinta da ɓacin ranta, shi ne abin nema ga kowane mutum, kuma da shi ne tsarkakakkiyar rayuwa take tabbata, kuma farin ciki da annashuwa suke cika. Da hakan akwai sabubba na addini, da sabubba na ɗabi'a, da sabubba na aiki, amma haɗuwar waɗannan gaba ɗaya ba ya yi wuwa sai ga muminai, amma wasunsu, cewa koda sun tabbata gare su ta wata fuskar da wani sababi masu hankulansu zasu yaƙesu a kansa. Saboda haka mafi amfanuwa kuma mafi tabbata kuma mafi kyan hali da makoma zai wucesu ta wasu fuskokin.

Amma kuma ni (a cikin wannan littafin nawa) zan faɗi wasu sabubba da suka zo min don wannan babban abin neman, wanda kowa yake ƙoƙarin nemansa.

Daga cikin su akwai wanda ya samu da yawa daga cikinsu, sai ya rayu rayuwa ta farin ciki kuma mai daɗi, kuma daga cikinsu akwai wanda ya kasa samunsu gaba ɗayansu sai ya rayu irin rayuwar taɓewa, ya kuma rayu irin rayuwar wahalhalu, kuma daga cikinsu akwai wanda tsaka-tsakiya ne, gwargwadan yadda aka datar da shi. Kuma Allah shi ne mai datarwa wanda ake neman taimakonSa a kan dukkan alheri da kuma tunkuɗewa daga dukkanin sharri.

Fasali: Imani da aiki na gari.

Mafi girman sabubba ga hakan da kuma asalinsu da tushensu shi ne imani da aiki na gari, Maɗaukakin sarki Ya ce:

﴿مَنۡ عَمِلَ صَٰلِحٗا مِّن ذَكَرٍ أَوۡ أُنثَىٰ وَهُوَ مُؤۡمِنٞ فَلَنُحۡيِيَنَّهُۥ حَيَوٰةٗ طَيِّبَةٗۖ وَلَنَجۡزِيَنَّهُمۡ أَجۡرَهُم بِأَحۡسَنِ مَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ 97﴾

{Wanda ya aikata aiki na ƙwarai daga namiji kõ kuwa mace, alhãli yanã mũmini, to, haƙĩƙa Munã rãyar da shi, rãyuwa mai dãɗi. Kuma haƙĩƙa Munã sãkã musu lãdarsu da mafi kyãwun abin da suka kasance sunã aikatãwa. 97} [al-Nahl: 97].

Sai Allah Maɗaukakin Sarki Ya bada labari Ya kuma yi alƙawari ga duk wanda ya haɗa imani da kuma yin aiki nagari, zai ba shi rayuwa mai daɗi a wannan gidan (na duniya), da sakamako mai kyau a wannan gidan, da kuma a gidan tabbata (na lahira).

Kuma sababin hakan a bayyane yake: Haƙiƙa cewa muminai waɗanda suka yi imani da Allah, imani ingantacce, wanda yake jawuwa zuwa ga aiki nagari mai gyara zuciya da ɗabi’u yake gyara duniya da kuma lahira, tare da su akwai asali da tushe da suke karɓar duk wani abin da zai kai su ga samun farin ciki da annushuwa ko kuma sabubban damuwa da baƙin ciki da ɓacin rai.

Suna karɓar abin da suke so, da wanda ya faranta musu, su gode da samunsu, su yi amfani da su cikin abin da zai amfanar. Idan kuma suka yi amfani da su ta wannan hanyar, sai ya samar musu wasu al’amura manya na farin ciki da su, da kwaɗayin wanzuwarsu da kuma albarkarsu, da fatan sakamakon masu godiya, waɗanda alkhairansu da albarkatunsu suka zarce waɗannan ababen farin cikin waɗanda su ne ’ya’yan itatuwansu.

Suna karɓar abubuwan ƙi da masu cutarwa da na baƙin ciki da ɓacin rai da gogayya ga abin da za su iya gogayya da shi, da sauƙaƙa abin da za su iya sauƙaƙa shi, da haƙuri mai kyau kan abin da basu da makawa a kansa. Da haka ne suke samun daga tasirin abubuwan ƙi na gogayya mai amfani, da jarrabawa da ƙarfi, kuma daga haƙuri da neman lada da sakamako al’amura masu girma, waɗanda a tare da su abubuwan ƙi suke gushewa, kuma farin ciki da burace-burace masu kyau su maye gurbinsu, da kuma kwaɗayi na samun falalar Allah da sakamakonSa, kamar yadda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya bayyana game da wannan a cikin ingantaccen hadisi cewa ya ce: ’’Lamarin mumini da ban mamaki yake, dukkannin al’amuransa alheri ne, idan abin farin ciki ne ya same shi sai ya godewa Allah, sai ya zamar masa alheri, idan kuma na sharri ne ya same shi sai ya yi haƙuri, shi ma sai ya zamar masa alheri, sai dai hakan ba ya kasancewa ga kowa sai ga mumini’’. Muslim ne ya ruwaito shi.

Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya ba da labari cewa lallai mumini ana riɓanya ganimarsa da alherinsa da sakamakon ayyukansa a cikin dukkanin abin da yake samunsa na farin ciki da abubuwan ƙi; saboda haka za ka ga mutane biyu wani abu na alheri ko na sharri ya same su, sai a sami bambanci mai girma a cikin karɓarsu, hakan kuwa saboda banbancin su ne a cikin imani da aiki na gari. Wanda ya siffantu da waɗannan siffofi guda biyu, zaka samu ya karɓi alheri ko sharri da abin da muka ambata na godiya da haƙuri da abin da yake biye musu, sai ya samar masa da farin ciki da annushuwa, da yayewar baƙin ciki, da ɓacin rai, da damuwa, da ƙuncin rai da kuma wahalar rayuwa sai ya samu cikakkiyar rayuwa daddaɗa a wannan gida (na duniya). Ɗayan kuma zai karɓi abin da yake so da sharri da girman kai da shishshigi, sai ɗabi’unsa su canja ya kuma karɓesu kamar yadda dabbobi suke karɓarsu da haɗama da firgita, kuma a tare da hakan cewa shi zuciyarsa ba’a huce take ba, suna tsotsarsu ta fuskoki masu yawa, sun tsotsa ta fuskar tsoronsa daga gushewar abubuwan da yake so, da kuma yawan abubuwa masu tasowa masu karo da su a mafi yawancin lokuta, da kuma ta fuskar cewa rayuka basa tsayawa a wata iyaka, bari dai ba za su gushe ba suna shauƙin wasu abubuwan daban, da zasu iya samuwa, kuma wataƙila ba za su iya samuwa ba. Mu ƙaddara cewa abubuwan sun tabbata, to shi kuma ɓacin rai ne ta fuskokin da aka ambata kuma zai gamu da abubuwan ƙi da ɓacin rai da razani da tsoro da ƙosawa. Kada ka yi tambaya game da abin da yake faruwa gare shi na taɓewar rayuwa, haka kuma daga cutukan tinani da jijiyoyi, da kuma tsoron da zai iya kai shi zuwa mafi munin halaye da mafi razanar abubuwan cutarwa, domin cewa shi ba ya kwaɗayin lada, kuma ba shi da haƙurin da zai haƙurtar da shi kuma ya sawwaƙa masa shi.

Kuma dukkanin wannan an gan su ta hanyar jarrabawa, misalin ɗaya daga wannan nau'in idan ka lura da shi ka kuma ɗabbaƙa shi a kan halayen mutane, za ka ga bambanci mai girma tsakanin mumini mai aiki da abin da imaninsa ya hukunta, da kuma wanda ba haka yake ba. Shi addini yana kwaɗaitarwa - matuƙar kwaɗaitarwa - a kan wadatuwa da arziƙin Allah, da kuma abin da Ya baiwa bayi daga falalarSa da karamcinSa mabambanta.

Shi mumini idan aka jarabce shi da wata rashin lafiya ko talauci, ko wani abu makamancin haka waɗanda ka iya samun kowa, to lallai shi - da imanin sa da wadatar zucinsa da kuma yarda kan duk abin da Allah Ya tsaga masa -, sai ka same shi cikin farin ciki, ba ya neman wani abu daga zuciyar sa wanda ba'a ƙaddara masa ba, yana duba zuwa ga na ƙasansa, ba ya duba na sama da shi, da yawa ma sai ka same shi cikin farin ciki da annashuwa fiye da wanda Allah Ya bawa duk wani abu da yake buƙata na duniya, amma kuma ba'a ba shi wadatar zuci ba.

Kamar yadda zaka sami wanda ba ya aiki da abin da imani yake hukuntawa, idan aka jarabce shi da wani abu na talauci ko rasa wani abu da yake buƙata na duniya, sai ka same shi cikin matuƙar tashin hankali da taɓewa.

Kuma wani misalin daban: Idan sabubban tsoro suka faru, kuma abubuwa masu tsoratarwa suka sauka a kan mutum, zaka samu ingantaccen imani mai tabbata ne a zuciya, mai natsuwar rai ne, mai iya jujjuya shi da tafiyar da shi ga wannan al’amarin wanda ya ruɗar da shi da abin da ke cikin ikonsa na tunani da faɗa da kuma aiki. Haƙiƙa ransa ya saba da wannan abun mai tsoratarwa mai ban haushi, to waɗannan sune halayen da suke hutar da mutum kuma suke tabbatar da zuciyarsa.

Kamar yadda kake samun wanda ya rasa imani da akasin wannan halin idan abubuwan tsoro suka faru sai zuciyarsa ta razana da su, hankalinsa ya tashi, tunanikansa su tarwatse, tsoro da razani su shige shi, tsoro na waje da ɓacin rai na baɗini waɗanda ba zai yi wu a faɗi haƙiƙaninsa ba sai su haɗar masa. Waɗannan nau'in mutane idan wasu daga cikin sabubba na ɗabi'a waɗanda suke buƙatar jarrabawa mai yawa ba su faru gare su ba, sai ƙarfinsu ya ƙare kuma hankalinsa ya tashi, hakan saboda rashin imanin da zaisa su haƙuri ne, musamman ma dai a guri mai ƙunci, da halaye masu baƙanta rai masu tsoratarwa.

Mutumin kirki da kuma fajiri, mumini da kafiri dukkan su suna tarayya wajen koyon jarumta, da halayyar da zata tausasa musu duk wani abin da suke tsoro ko ta sauƙaƙa musu, sai dai mumini zai fita daban ta ƙarfin imaninsa da haƙurinsa da tawakkalinsa da dogaronsa ga Allah da neman ladan wasu al’amura da jarumtarsa zata ƙaru da su, kuma takun tsoro ya sauƙaƙa gare shi, kuma musibu su sauƙaƙa a gare shi, kamar yadda Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce:

﴿...إِن تَكُونُواْ تَأۡلَمُونَ فَإِنَّهُمۡ يَأۡلَمُونَ كَمَا تَأۡلَمُونَۖ وَتَرۡجُونَ مِنَ ٱللَّهِ مَا لَا يَرۡجُونَ...﴾

{Idan kun kasance kuna jin zõgi, to, lalle sũ ma, suna jin zõgi kamar yadda kuke jin zõgi. Kuma kuna tsammãni, daga Allah, abin da bã su tsammãni...} [al-Nisā': 104]. Kuma taimakon Allah na musamman zai tabbata a gare su da kuma ƙari wanda zai tarwatsa duk wani abin da suke tsoro, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce:

﴿...وَٱصۡبِرُوٓاْۚ إِنَّ ٱللَّهَ مَعَ ٱلصَّٰبِرِينَ﴾

{...kuma ku yi haƙuri. Lalle ne Allah Yanã tãre da mãsu haƙuri.} [al-Anfal: 46].

Kyautatawawa halitta da furuci da kuma aiki Daga cikin sabubban da suke kawar da baƙin ciki da ɓacin rai da damuwa, kyautatawa halittu ta hanyar magana da kuma aiki, da nau’ikan alheri, kuma dukkaninsu alheri ne da kuma kyautatawa, kuma da su ne Allah Yake tunkuɗewa mutumin kirki da fajiri baƙin ciki da ɓacin rai daidai gwargwadonsu, sai dai mumini ya fi samun cikakken rabo daga gare su, kuma yana bambanta da cewa kyautatawarsa mai bijirowa ce daga ikhlasi da kuma neman ladansa.

Sai Allah Ya sauƙaƙa masa aikata alheri saboda abin da yake fatansa na alheri, kuma Ya tunkuɗe masa abubuwan ƙi saboda ikhlasinsa da kuma neman ladansa. Allah - Maɗaukakain sarki - Ya ce:

﴿لَّا خَيۡرَ فِي كَثِيرٖ مِّن نَّجۡوَىٰهُمۡ إِلَّا مَنۡ أَمَرَ بِصَدَقَةٍ أَوۡ مَعۡرُوفٍ أَوۡ إِصۡلَٰحِۭ بَيۡنَ ٱلنَّاسِۚ وَمَن يَفۡعَلۡ ذَٰلِكَ ٱبۡتِغَآءَ مَرۡضَاتِ ٱللَّهِ فَسَوۡفَ نُؤۡتِيهِ أَجۡرًا عَظِيمٗا 114﴾

{Bãbu wani alhẽri a cikin mãsu yawa daga gãnawarsu fãce wanda ya yi umurni da wata sadaka kõ kuwa wani alhẽri kõ kuwa gyãra a tsakãnin mutãne. Wanda ya aikata haka dõmin nẽman yardõdin Allah to zã Mu bã shi lãda mai girma. 114} [al-Nisā': 114].

Sai (Allah) Maɗaukakin Sarki ya bada labari cewa duk waɗannan al’amuran alheri ne daga wanda ya aikata su, kuma alkairi shi yake jawo alkhairi, kuma yake tunkuɗe sharri. Sannan cewa mumini mai neman lada, Allah zai yi masa sakamako mai girma, daga cikin jumullar ladan mai girma akwai: gusar da baƙin ciki da ɓacin rai da kuma gurɓatattun abubuwa da makancinsu.

Fasali: Shagaltuwa da wani aiki daga ayyuka, ko wani Ilmi daga ilmai masu amfani.

Daga cikin sabubban da suke tunkuɗe ɓacin rai wanda yake faruwa saboda tashin hankali, da shagaltar da zuciya da wasu daga cikin abubuwa masu gurɓata farin ciki: Shagaltuwa da wani aiki daga cikin ayyuka ko wani ilimi daga cikin ilmai masu amfani; domin su suna shagaltar da zuciya daga shagaltuwa da wannan al’amarin wanda ya ɓata masa. Wani lokacin ya kan manta saboda waɗannan sabubban da suka dora masa baƙin ciki da ɓacin rai, sai ransa ya yi farin ciki, kuma nishaɗinsa ya ƙaru, wannan sababin shima abin yin tarayya ne tsakanin mumini da waninsa. Sai dai mumini yana bambanta saboda imaninsa da kuma ikhlasinsa da neman ladansa a cikin shagaltuwarsa da wannan ilimin da yake neman saninsa ko yake koyar da shi, haka kuma da aikin alherin da yake aikata shi. Idan ya kasance ibada ce to shi ibada ce, idan kuma wani abu ne na duniya ko na al'ada sai niyya ta gari ta kasance tare da shi. Da kuma nufin neman taimako da hakan a kan biyayya ga Allah, to hakan yana da tasiri mai aiki a cikin tunkuɗe baƙin ciki da ɓacin rai da kuma baƙin ciki. Da yawa mutumin da aka jarraba da ɓacin rai da kuma lazimtar gurɓacewar zuciya, sai cututtuka mabambanta su saukar masa, sai maganinsa mai tasiri ya zamo (mantuwar sa da sababin da ya gurɓata shi kuma ya sa shi ɓacin rai, da kuma shagaltuwarsa da wani aiki daga abubuwa masu muhimmanci).

Kuma ya kamata aikin da zai shagala da shi ya zamo ya ɗauke masa hankali ya kuma nutsu da shi, kuma yake da shauƙi a kansa; wannan zai sa ya kai ga abin da aka nufa mai amfani, Allah shi ne Mafi sani.

Tattaro tunani dukkaninsa a kan himmatuwa da aiki na wannan ranar. Daga cikin abubuwan da ake tunkuɗe baƙin ciki da ɓacin rai da su akwai tattaro tunani dukkaninsa a kan himmatuwa da aiki na wannan ranar, da kuma yanke shi daga himmatuwa a cikin lokaci mai fuskantowa, da kuma baƙin ciki a kan lokacin da ya wuce. Saboda haka ne Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya nemi tsari daga baƙin ciki da ɓacin rai, don haka baƙin ciki akan al’amuran da suka wuce waɗanda dawo da su ko riskarsu ba zai yiwu ba to ba shi da wani amfani, kuma damuwa wadda take faruwa saboda tsoron nan gaba na iya cutarwa, to ya wajaba a kan bawa ya zama ɗan yinin sa ne, yana mai tattaro ƙoƙarinsa domin gyara yininsa da kuma lokacinsa na yanzu, domin tattarowar zuciya a kan hakan yana wajabta cikar ayyuka, kuma bawa yana kawar da baƙin ciki da kuma ɓacin rai da shi. Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - idan zai yi wata addu'a ko zai shiryar da al'ummarsa zuwa ga wata addu'a, kaɗai yana kwaɗaitarwa ne tare da neman taimakon Allah da kwaɗayin falalarSa a kan ƙoƙari a cikin tabbatarwa don samun abin da yake roƙon samunsa. Da kuma barin abin da ya kasance yake roƙo dan tunkuɗe shi; domin cewa addu'a mai gwamuwa da aiki ce, bawa ya yi ƙoƙari kan abin da zai anfane shi a cikin addini da duniya, kuma ya roƙi Ubangijinsa samun abin nufinsa, kuma ya nemi taimakonSa a kan hakan, kamar yadda (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: (Ka kwaɗaitu kan abin da zai amfane ka, kuma ka nemi taimakon Allah kada ka gajiya, idan wani abu ya same ka kada ka ce: Da na aikata kaza da kaza ne zai kasance, sai dai ka ce: Haka Allah Ya ƙaddara, kuma abin da Ya so shi Yake aikatawa, domin ita kalmar dana sani kofar Shaiɗan take buɗewa). Muslim ne ya rawaito shi. Annabi tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi ya haɗa tsakanin umarni da kwaɗaitarwa kan abubuwa masu amfani a kowanne hali, da neman taimakon Allah, kada kuma ya bari karaya ko gajiyawa su rinjaye shi wanda ita ce kasala mai cutarwa, da sallamawa kan abubuwan da suka shuɗe waɗanda aka zartar, da shaidawa kan abin da Allah Ya hukunta kuma Ya ƙaddara.

Ya kuma sanya al'amura ɓangare biyu: Wani ɓangaren zai yiwu bawa ya yi ƙoƙari a cikin tabbatar da shi ko tabbatar da abin da zai yiwu daga gare shi, ko tunkuɗe shi, ko sauƙaƙa shi, to wannan bawa zai bayyana ƙoƙarinsa, kuma ya nemi taimako da abin bautarsa. Ɗaya ɓangaren kuma hakan ba za ta yiwu ba, in hakan ya faru mutum ya kwantar da hankalinsa ya yarda ya kuma miƙa wuya, babu shakka kiyaye wannan tushen dalili ne da zai kawo masa farin ciki da yayewar baƙin ciki da damuwa.

Fasali: Yawaita ambaton Allah - Maɗaukakin sarki -.

Kuma daga cikin mafi girman sabubba ga buɗewar ƙirji da kuma nutsuwarsa: yawaita ambaton Allah, domin hakan yana da tasiri mai ban mamaki a cikin buɗewar ƙirji da kuma nutsuwarsa, da gushewar baƙin ciki da damuwa. (Allah) Maɗaukakin sarki Ya ce:

﴿...أَلَا بِذِكۡرِ ٱللَّهِ تَطۡمَئِنُّ ٱلۡقُلُوبُ﴾

{To, da ambaton Allah zukãta suke natsuwa.} [al-Ra'ad: 28] Ambaton Allah yana da tasiri mai girma wajen cimma wannan abin nema a karan kansa , da kuma abin da bawa yake fata na sakamakonSa da ladanSa.

Zantarwa da ni'imomin Allah na zahiri da na boye. Haka nan ambaton ni’imomin Allah na zahiri da na baɗini, domin saninsu da bayanunsu, Allah Yana tunkuɗe baƙin ciki da ɓacin rai da shi, kuma Yana kwaɗaitar da bawa a kan godiyar da ita ce mafi girman matakai kuma mafi ƙololuwarsu, ko da ace bawan yana cikin halin talauci ko rashin lafiya ko wasunsu daga nau’o’in bala’o’i. Domin idan ya haɗa tsakanin ni’imomin Allah a kansa — waɗanda ba za a iya ƙididdige su ko ƙirga su ba — da abin ƙi da ya same shi, to ba za a sami wata dangantaka ga abin ƙi idan aka kwatanta shi da ni’imomin ba.

Idan aka jarabci bawa da wani abin ƙi da musibu, sai ya bi da su da haƙuri da yarda da ƙaddara tare da miƙa wuya, sai nawinsu da wahalarsu su sauƙaƙa a gare shi, kuma burin bawa shi ne samun ladansu da sakamakonsu da kuma bautawa Allah ta hanyar tsayuwa da aikin haƙuri da kuma yarda, sai yabar abubuwa masu ɗaci su zama masu zaƙi sai zaƙin ladansu ya mantar da shi ɗacin haƙurinsu.

Duba zuwa ga waɗanda suke ƙasa da mu. Kuma daga cikin mafi amfanin abubuwa a wannan bigiren, amfani da abin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya shiryar a cikin hadisi ingantacce inda ya ce: (Ku yi duba zuwa ga wanda yake ƙasa da ku, kada ku yi duba zuwa ga wanda yake sama da ku, hakan zai sa ku godewa Allah ba za ku raina ni’imominSa gareku ba.) Muslim ne ya rawaito shi. To lallai idan bawa ya sanya wannan muhimmin hararo tsakanin idanuwansa ya auna shi, zai gani haƙiƙa ya fi da yawa daga cikin bayin Allah ta ɓangaren lafiya da abin da yake da alaƙa da ita, da ta ɓangaren arziƙi da abin da yake da alaƙa da shi duk tsananin halin da yake ciki, sai baƙin cikinsa, tashin hankalinsa da damuwarsa su gushe, farin cikinsa da murnarsa su ƙaru ganin cewa ya wuce waninsa a cikinsu daga waɗanda suke ƙasansa wurin dacewa da ni’imomin Allah (subhanahu wa ta’ala).

Kuma duk lokacin da bawa ya zurfafa tunaninsa kan ni’imomin Allah na zahiri da baɗini, na addini da na duniya, zai ga haƙiƙa Ubangijinsa Ya yi masa ni’imomi masu yawa Ya kuma kawar masa da sharrori masu yawa, babu shakka wannan yana kawar da baƙin ciki da ɓacin rai, yana kuma wajabta farin ciki da jindaɗi.

 


FASALI: Ƙoƙari wajen gusar da dalilan da suke jawo baƙin ciki, da kuma cimma waɗanda suke jawo farin ciki.

Daga cikin sabubba masu wajabta farin ciki da gusar da baƙin ciki da ɓacin rai ƙoƙari wajen gusar da dalilan da suke jawo baƙin ciki da kuma cimma waɗanda suke jawo farin ciki; wannan kuwa ta hanyar mantawa da abin da ya riga ya same shi na abubuwan ƙi, wanda ya wuce ba kuma zai iya dawo da shi ba, da saninsa cewa shagaltar da tunaninsa a cikinsu yana daga babin wasa da abin da ba zai yiwu ba, kuma cewa hakan wauta ce da hauka, Sai ya yi ƙoƙari ya yaƙi zuciyarsa wajen daina tunanin su, ya kuma yaƙe ta wajen damuwa kan abin da zai zo daga abubuwan da yake rayawa waɗanda suka danganci talauci ko tsoro ko wanin haka na daga abubuwan ƙi waɗanda yake tsoron faruwar su a rayuwarsa ta nan gaba. Kuma ya san cewa lallai babu wanda ya san abin da zai faru a nan gaba a rayuwarsa na daga alheri ko na burin rayuwa ko na rashin daɗinta. Gabaki ɗayansu suna a hannun Allah Mabuwayi Mai hikima, babu wani abu a hannun bayi daga gare su sai ƙoƙarin su ga sun kai ga alkhairai sun kuma kawar da abubuwan da zasu cutar da su, kuma bawa ya sani idan ya daina ɓata lokacinsa wajen damuwa kan al’amuran da suka shafi rayuwarsa ta nan gaba, ya dogara ga Allah kan cewa shi zai daidaita masa komai, ya kuma kwantar da hankalinsa. Idan ya aikata haka zuciyarsa zata nutsu kuma al’amuransa zasu gyaru, baƙin ciki da damuwarsa za su gushe.

Amfani da Addu’a. Kuma daga mafi amfanin abin da yake kasancewa a cikin lura da al'amura masu fuskantowa (yin amfani da) wannan addu'ar wacce Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana yin addu'a da ita: "Ya Allah Ka gyara min addini na wanda shi ne ƙashin bayan al’amari na, kuma Ka gyara min duniya ta wacce nake rayuwa a cikinta, Ka kuma gyara min lahira ta wacce ita ce makoma ta. Ka sanya rayuwa ta zamo ƙarin duk wani alheri a gare ni, kuma Ka sanya mutuwa ta zamo hutu ce a gare ni daga dukkan wani sharri". Muslim ne ya rawaito shi. Haka kuma faɗarsa: "Ya Allah rahamarKa na ke fata, kar Ka bar ni da kaina daidai da ƙiftawar ido, Ka gyara min al’amura na dukkan su, ba bu wani abin bautawa da gaskiya sai Kai". Abu Dawud ne ya rawaito shi da isnadi ingantacce. Idan bawa ya mai da hankali kan wannan addu’a wacce take ƙunshe da gyaran rayuwarsa ta nan gaba ta ɓangaren addini da duniya da kuma halarto da zuciyarsa, da kyakkyawar niyya, tare da ƙoƙarinsa wajen tabbatar da hakan, Allah zai tabbatar masa da abin da ya roƙa yake kuma fata ya kuma yi aiki domin sa, sai ya juyar da baƙin cikinsa zuwa farin ciki da jin daɗi.

Fasali: Ƙaddarta mafi muni daga abubuwan da ka iya faruwa.

Kuma daga mafi amfanin sabubba na gusar da damuwa da baƙin ciki idan wani abu ya faru ga bawa na masifu, shi ne ya yi ƙoƙari a sauƙaƙa su ta hanyar ƙaddarta mafi munin sakamakon al'amarin, kuma ya sabawa kansa a kan hakan. Idan ya aikata haka, to sai ya yi ƙoƙari ga sauƙaƙa abin da sauƙaƙa shi zai yiwu gwargwadon iko. Da wannan sabawar da kuma wannan ƙoƙarin mai amfani, baƙin cikinsa da ɓace-ɓacen ransa za su gushe, sai wannan ƙoƙarin ya zama a cikin jawo amfani, kuma a cikin tunkuɗe cutar da aka sawwaƙawa bawa.

Idan sabubban tsoro, da sabubban cututtuka, da sabubban talauci da rashi akan abin da yake sonsa daga abubuwan da yake so daban-daban suka saukar masa, to sai ya karɓi hakan da nutsuwa da sabawa rai a kansu, kai a kan mafi tsananin abin da zai yiwu daga garesu, domin cewa sabawa rai a kan jurewa abubuwan ƙi, yana sauƙaƙasu kuma yana gusar da tsananinsu, musammanma dai idan ya shagaltar da kansa ga karesu gwargwadan ikonsa, sai sabawa rai da kuma ƙoƙari mai amfani wanda yake shagaltarwa a kan himmatuwa da masifu su haɗu a cikin haƙƙinsa, kuma ya yaƙi zuciyarsa a kan sabunta ƙarfin gogayya da abubuwan ƙi, tare da dogaronsa ga Allah a cikin hakan da kuma kyakkyawar natsuwa da Shi, kuma babu kokwanto cewa akwai fa'ida mai girma ga waɗannan al'amuran a cikin samuwar farin ciki da buɗewar ƙirji, tare da abin da bawa yake lura da shi na lada magaggauci da majinkirci, wannan angani kuma an jarraba, kuma waƙi'o'insa daga waɗanda suka jarraba shi yana da yawa sosai.

Fasali: Ƙarfin zuciya, da rashin damuwarsa, da fusatarsa

Kuma daga mafi girman magungunan cutukan zuciya na jijiya, kai da ma cutukan jiki: Ƙarfin zuciya da rashin tayar mata da hankali da fusatarsa ga baƙin ciki da raye-raye waɗanda munanan tunani suke jawo su. Da fushi da saƙe –saƙe kan abubuwa masu raɗaɗi da fargabar faruwar al’amura marasa kyau, da gushewar ababen so, hakan sai ya jefa mutum cikin ɓacin rai, da baƙin ciki da cututtukan zuciya da na jiki da rugujewar jijiya wanda yana da tasiri mummuna, wanda mutane sun shaida cutarwar hakan da yawa.

Dogaro ga Allah. A duk lokacin da zuciya ta dogara ga Allah, ta yi tawakkali da Shi, kuma bai miƙa wuya ga ɗimauce-ɗimauce ba, kuma raye-raye munana basu mallake shi ba, kuma ya amincewa Allah kuma ya yi kwaɗayi a samun falalarSa, sai baƙƙan ciki da ɓace-ɓacen rai su kau daga gare shi, kuma mafi yawa daga cututtuka na jiki da zuciya su gushe daga gare shi, sai ƙarfi da buɗewar ƙirji da farin cikin da ba za'a iya izinar su ba sai su tabbata ga zuciya. Da yawa asibitoci suka cika daga masu cututtukan ɗimuwa da munanan tunani, da yawa waɗannan al'amuran suka yi tasiri a kan zuciyar mafi yawa cikin ƙarfafa, ballantana kuma raunana, da yawa ma sukan kai zuwa ga wauta da hauka. Wanda ya samu lafiya shi ne wanda Allah Ya ba shi lafiya kuma Ya datar da shi ga yaƙar kansa don samun sabubba masu amfani masu ƙarfafa zuciya, masu kare damuwarta, (Allah) - Maɗaukakin sarki -Ya ce:

﴿...وَمَن يَتَوَكَّلۡ عَلَى ٱللَّهِ فَهُوَ حَسۡبُهُۥٓ...﴾

{Kuma wanda ya dõgara ga Allah, to, Allah ne Ma'ishinsa...} [al-Dalaƙ: 3] Wato Ya isar masa dukkan abin da yake damunsa na al'amarin addininsa da kuma duniyarsa.

Wanda ya dogara ga Allah mai ƙarfin zuciya ne, ɗimauce-ɗimauce ba zasu yi masa tasiri ba, kuma haɗarirrika ba zasu dame shi ba saboda saninsa cewa hakan yana daga raunin rai, da rauni da tsoron da ba shi da haƙiƙa, kuma tare da hakan zai san cewa Allah haƙiƙa Ya lamuncewa wanda ya dogara gare Shi da cikakkiyar isuwa, sai ya amincewa Allah kuma ya nutsu ga alƙawarinSa. Sai baƙin cikinsa da damuwarsa su gushe, kuma ya canja tsananinsa zuwa sauƙi, kuma baƙin cikinsa ya koma farin ciki (al-Tarhu ma'anarsa: Baƙin ciki), kuma tsoronsa ya koma aminci, muna roƙonSa (Allah) - Maɗaukakin sarki - kariya kuma Ya yi mana falala da ƙarfin zuciya da kuma tabbatar ta, da kuma cikakken dogaro wanda Allah Ya lamuncewa ma'abotansa da dukkan alheri, da kare dukkanin abin ƙi da cuta (alDair: Cuta).

Fasali: Sabawa rai da haƙuri da aibobin wasu.

Kuma cikin faɗin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: "Mumini ba ya ƙin mumina, in ya ƙi wata ɗabi’ar daga gare ta, zai so wata ɗabi’ar daga gare ta". Muslim ne ya rawaito shi.

Fa'idodi biyu masu girma:

Na farkonsu: Shiryarwa kan yadda zaka mu’amalanci mata da ɗan uwa, da aboki, da abokin mu’amala, da dukkanin wanda tsakaninka da shi akwai wata alaƙa ko cuɗanya; kuma ya kamata ka sawa ranka cewa dole ne wannan ɗin ya zamo yana da aibi ko wata tawaya ko wani abu da kake ƙinsa. Idan ka sami haka, sai ka haɗa tsakanin wannan da abin da ya wajaba a kanka ko ya kamata na ƙarfafa alaƙa da wanzar da soyayya, ta hanyar tunawa da abin da yake da shi na kyawawan ɗabi’u da manufofi keɓantattu da na gamewa. Da wannan kau da kan ne daga munanan abubuwa da lura da kyawawan abubuwa, abokantaka da alaƙa zasu dawwama, hutu ya cika, kuma hakan ya tabbata a gare ka.

Fa'ida ta biyu: Gusar da baƙin ciki da damuwa da kuma firgici, da wanzuwar tsarkin rai, haka kuma da tsayuwa kan haƙƙoƙi na wajibi da na mustahabai, da samun nutsuwa tsakanin ɓangarorin guda biyu. Wanda bai shiryu da wannan abin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ambata ba, sai ya juyar da al’amari akasinsa, ya lura da munana, ya rufe idonsa daga kyawawa, to babu makawa zai shiga cikin damuwa, babu makawa kuma soyayyar da ke tsakaninsa da wanda yake da alaƙa da shi za ta gurɓace, kuma da yawa daga cikin haƙƙoƙin da ke rataye a wuyansu na kiyaye su za su yanke.

Da yawa daga cikin mutane ma'abota himma babba, suna tanadawa kansu haƙuri da nutsuwa yayin afkuwar masifu da abubuwa masu ban tsoro. Sai dai suna damuwa a wurin ƙananan al'amura, sai amintaka ta gurɓace, kuma dalili akan haka shi ne cewa su sun sabawa kawunansu wurin tarbar manyan abubuwa amma basu shirya karɓar ƙananan ba, sai su cutar da su, su yi kuma tasiri akan hutunsu. Tsayayyen mutum shi ne a kullum yake sabawa kansa wajen tarbar manya da ƙananan abubuwa ya kuma roƙi Allah Ya taimake shi a kansu, kar Ya bar shi da kansa dai dai da ƙiftawar ido, to a wannan yanayin sai ƙananan abubuwan su sauƙaƙa a gare shi kamar yadda manyan suka sauƙaƙa gare shi. Sai ya wanzu yana mai nutsuwar rai mai nutsuwar zuciya, yana mai hutawa.

Fasali: Rashin zarcewa wajen biye wa damuwa.

Mai hankali shi ne wanda ya san cewa ingantacciyar rayuwarsa rayuwar jin daɗi da nutsuwa ce, kuma haƙiƙa ta gajarta ƙwarai; bai kamata ya gajarta ta da bacin rai da sakinta tare da gurbace-gurbace ba, domin hakan kishiyar ingantacciyar rayuwa ce. Saboda haka ya yi rowa da rayuwarsa, kada yawanta ya tafi ganima ga ɓacin rai da gurɓace-gurɓace. Kuma babu bambanci a wannan tsakanin mai biyayya da fajiri; sai dai mumini shi ne mafi yawan rabo wajen tabbatuwa da wannan siffa, da rabo mai amfani a nan kusa ko a jinkirta masa.

Kwatantawa tsakanin ni’imomin Allah da abin da ya same shi wanda baya so. Kuma ya kamata a gare shi, idan abin ƙi ya same shi ko na tsoro ya haɗa tsakanin ragowar ni’imomin da aka yi masa na Addini ko waɗanda suka shafi duniya, da abin da ya same shi na rashin jin daɗi, to a wurin haɗawar yawan abin da yake cikin sa na ni’imomi zai bayyana, da kuma dusashewar abin da ya same shi na rashin jin daɗi.

Haka nan, zai haɗa tsakanin abin da yake jin tsoron cutuwarsa, da kuma damammakin kuɓuta daga gare su. Ba zai bar raunin yiwuwar ya rinjayi damammaki masu ƙarfi ba, da hakan ne baƙin cikinsa da tsoronsa zasu gushe, kuma ya ƙaddara mafi girman abin da zai kasance daga damammakin da yake tunanin zasu same shi, sai ya tanadarwa kansa dan faruwarsu idan sun faru, kuma ya yi ƙoƙari a cikin tunkuɗe abin da bai faru daga gare su ba, haka kuma a cikin ɗauke abin da ya faru ko sauƙaƙa shi.

Cutarwar mutane tana kansu muddin ba ka shagaltar da kanka da ita ba. Kuma daga al’amura masu amfani shi ne ka sani cewa cutarwar mutane gare ka musamman ta ɓangaren munanan maganganu ba za su cutar da kai ba, sai dai su cutar da su. Sai dai in ka shagaltar da kanka wajen mai da hankalinka kansu ka sanya su cikin ranka, a wannan lokacin sai su cutar da kai kamar yadda ta cutar da su, idan kuwa ba ka kula da su ba to ba za su cutar da kai da komai ba.

Ka kyautata rayuwarka da tunani masu amfani. Ka sani cewa rayuwarka tana tafiya ne daidai da tunaninka; idan tunaninka ya kasance a kan abin da zai maka amfani a Addininka da rayuwarka ta duniya, rayuwarka ta zamo mai kyau mai ƙunshe da farin ciki; in ko ba haka ba, to sai al’amarin ya kasance akasin haka.

Kasancewar mu’amala domin Allah ba domin halitta ba. Daga mafi amfanin al'amura ga kore baƙin ciki shi ne ka sabawa kanka cewa kada ka nemi godiya a wajen kowa sai a wajen Allah. Idan ka kyautatawa wanda yake da haƙƙi a kanka ko wanda ba shi da shi, to ka sani cewa wannan mu’amala ce tsakaninka da Allah, kada ka damu da godiyar wanda ka kyautatawa, kamar yadda Allah - Maɗaukakin sarki - Yake cewa dangane da haƙƙin bayinSa na musamman:

﴿إِنَّمَا نُطۡعِمُكُمۡ لِوَجۡهِ ٱللَّهِ لَا نُرِيدُ مِنكُمۡ جَزَآءٗ وَلَا شُكُورًا 9﴾

{(Suna cẽwa): "Munã ciyar da ku ne dõmin nẽman yardar Allah kawai, bã mu nufin sãmun wani sakamako daga gare ku, kuma bã mu nufin gõdiya. 9} [al-Insan: 9].

Kuma wannan yana ƙara ƙarfafuwa a cikin mu'amalantar iyalai da 'ya'ya da ƙarfin alaƙar ka da su. A duk lokacin da ka sabawa kanka watsar da sharri daga gare su, to ka huta kuma ka hutar. Yana daga abubuwan da suke janyo hutu, ruƙo da falaloli da kuma aiki a kansu bisa manufa ta hankali ba tare da ɗorawa kai abin da zai dameka ba. Zaka koma a kan benanka kana a taɓe daga samun falala, inda ka shiga karkatacciyar hanya, wannan yana daga hikima, kuma ka zaɓi tatattun al'amura masu zaƙi daga gurɓatattun al'amura, da haka ne abubuwa masu kyau masu daɗi zasu ƙaru, kuma abubuwa gurɓatattu zasu gushe.

Shagaltuwa da abin da ke da amfani, ba da abin da ke da cutarwa ba. Ka sanya al’amura masu amfani a gabanka ka yi aiki don tabbatar da su, kada ka waiwayi abubuwa masu cutarwa saboda kar su jawo maka ɓacin rai da damuwa, kuma ka nemi taimako ta hanyar hutawa da tara hankalinka wuri guda wajen yin ayyuka masu muhimmanci.

Gamawa (kawad da) ayyuka a nan take. Daga cikin al’amura masu amfani akwai ƙarar da ayyuka a kan lokaci, da sadaukar da kai don abin da zai zo nan gaba; saboda ayyuka idan ba a ƙarar da su ba sai ragowar ayyukan da suka gabata su taru a kanka, kuma su haɗu da ayyukan da za su biyo baya. Sai nauyinsu ya tsananta; amma idan ka gama komai a lokacinsa sai ka fuskanci masu zuwa da ƙarfin tunani da ƙarfin aiki.

Jerantawa abubuwan da suka fi cancanta tare da neman shawara. Kuma yana kamata ka zaɓi ayyuka masu muhimmanci masu amfani, sannan a cikin masu muhimmancin ma ka zaɓi waɗanda suka fi muhimmanci, kuma ka mai da hankalinka kan waɗanda kafi karkata gare su, kuma ka zage damtse a kan su, domin kishiyar hakan yakan haifar da gajiyawa da ƙosawa da kuma taɓarɓarewa. Ka nemi taimako kan haka ta yin kyakkyawan tunani tare da neman shawara, saboda duk mai neman shawara ba ya yin da na sani. Ka yi nazari mai kyau kan abin da kake son aikatawa, idan ka tabbatar da maslahar kuma ka yi niyya to sai ka dogara ga Allah, haƙiƙa Allah Yana son masu tawakkali.

Dukkan yabo ya tabbata ga Allah Ubangijin talikai.

Allah Ya yi daɗin tsira da aminci ga shugabanmu (Annabi) Muhammad da alayensa da sahabbansa.

Teburin bayani

 

Gabatarwa 2

Fasali: Imani da aiki na gari. 3

Fasali: Shagaltuwa da wani aiki daga ayyuka, ko wani Ilmi daga ilmai masu amfani. 10

Fasali: Yawaita ambaton Allah - Maɗaukakin sarki -. 13

FASALI: Ƙoƙari wajen gusar da dalilan da suke jawo baƙin ciki, da kuma cimma waɗanda suke jawo farin ciki. 16

Fasali: Ƙaddarta mafi muni daga abubuwan da ka iya faruwa. 18

Fasali: Ƙarfin zuciya, da rashin damuwarsa, da fusatarsa 19

Fasali: Sabawa rai da haƙuri da aibobin wasu. 21

Fasali: Rashin zarcewa wajen biye wa damuwa. 23

 

***