Hadisan Annabi (SAW) da aka zaɓa
Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Babu wasu kwanaki da aiki na ƙwarai a cikinsu ya fi soyuwa a wurin Allah sama da waɗannan kwanakin". Wato kwanaki goman, (Zul Hijja) Suka ce: Ya Ma’aikin Allah, Har jihadi domin ɗaukaka addinin Allah ? Ya ce: Har Jihadi domin ɗaukaka addinin Allah, sai dai mutumin da ya fita da kansa da dukiyarsa, kuma bai dawo da komai ba. [Ingantacce ne] - [Bakhari ne ya ruwato shi, da Abu Dawud, kuma lafazin nasa ne]
Daga Ummu Salama Uwar muminai matar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya kasance yana da abin yankan da zai yanka shi (na Layya) to idan jinjirin watan Zul-Hijja ya kama, to kada ya cire wani abu daga gashinsa ko faratansa har sai ya yi layya". [Ingantacce ne] - [Muslim ne ya ruwaito shi]
Daga Abdullahi Dan Abbas -Allah ya yarda da su- yace: "An umarci mutane dasu yi dawafi ga dakin Allah a karshe,sai dai anyi sauki ga mace mai haila". [Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]
Daga Aisha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya farar da (wani abu) daga al'amarinmu wannan abinda ba ya ciknsa to an mayar masa". Daga Muslim: "Wanda ya aikata wani aiki wanda ba ya kan al'amarinmu to shi abin an mayar masa". [Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]–
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - Ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Wanda ya yi Hajji bai yi kwarkwasaba, kuma bai yi fasikanciba zai dawo kamar ranar da mahaifiyarsa ta haife shi". [Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa:"Haƙƙin musulmi akan musulmi guda biyar ne: Maida sallama, da gaida mara lafiya, da bin jana'iza, da amsa gayyata, da gaida mai atishawa". [Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 1240].
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Mumini ƙaƙƙarfa ya fi alkairi da soyuwa a wajen Allah sama da mumini rarrauna, akwai alkairi a kowanne, ka yi kwaɗayin yin abinda zai amfane ka, kuma ka nemi taimakon Allah, kada ka gaza, idan wani abu ya sameka kada ka ce: Dana aikata da kaza da kaza ya kasance, sai dai ka ce : Kaddarar Allah abinda Ya so zai aikata, domin cewa (da a ce) tana buɗe aikin Shaidan". [Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2664].
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Salloli biyar, da Juma'a zuwa Juma'a, da Ramadan zuwa Ramadan, masu kankare a binda ke tsakaninsu ne idan ya nisanci manyan zunubai". [Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 233]