Hadisan Annabi (SAW) da aka zaɓa
Daga Nu'uman ɗan Bashir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Kwatankwacin muminai a soyayyarsu da jinkansu da tausayinsu tamkar jiki ne, idan wata gaɓa daga gare shi ta yi ciwo sai ragowar jikin ya ɗauka da rashin bacci da zazzaɓi". [Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka ruwaito shi] - [صحيح مسلم - 2586]
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Bala'i ba zai gushe ga mumini da mumina ba a kansa da ɗansa da dukiyarsa har sai ya gamu da Allah ba shi da wani laifi". [Hasan ne] - - [سنن الترمذي - 2399]
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ɗayanku ba zai yi imani ba, har sai ya sowa ɗan uwansa abinda yake sowa kansa". [Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka ruwaito shi] - [صحيح البخاري - 13]
Daga Anas - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Mafi yawan addu'ar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ta kasance: "Ya Allah Ubangijinmu Ka bamu kyakkyawa a duniya, a lahira ma (Ka bamu) kyakkyawa, kuma ka karemu azabar wuta". [Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [ صحيح البخاري - 6389].
Daga Abdullahi Ɗan Amr - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Dukkaninku masu kiwone to abin tambayane daga abinda yake kiwonta, shugaban mutane mai kiwo ne shi abin tambayane game da su, mutum mai kiwone ga iyalan gidansa kuma shi abin tambaya ne game da su, mace mai kiwo ce a dakin mijinta da ’yayansa kuma ita abar tambaya ce game da su,, bawa mai kiwo ne akan dukiyar shugabansa shi abin tambaya ne game da ita, ku saurara dukkaninku abin tambaya ne game da abin da aka ba shi kiwonsa". [Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 2554]
Daga Usman - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Babu wani mutum musulmi da sallar farilla zata halarto shi, sai ya kyautata alwalarta da khushu'inta da ruku'inta, sai ta zama kaffara ga abinda ke gabaninta na zunubai, muddin dai bai aikata babban laifi ba, hakan a zamani ne gaba ɗayansa". [Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 228].
Daga Abu sa'id AlKhudri - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Babu wani musulmi da zai yi wata addu'a wacce babu zunubi a cikinta, kuma babu yanke zumunci, face sai Allah Ya ba shi ɗayan abu uku: Kodai Ya gaggauto masa da (amsa) addu’ar sa, ko kuma Ya tanadar masa ita sai ranar alƙiyama, ko kuma Ya kawar masa da wani mummunan abu irinta". Sai (Sahabbai) suka ce: Kenan mu yawaita? Sai ya ce: "Allah Shi ne Mafi yawaitawa". [Ingantacce ne] - [Ahmad ne ya rawaito shi] - [مسند أحمد - 11133].
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya yi alwala sai ya kyautata alwala sannan ya zo Juma'a sai ya saurari huduba kuma ya yi shiru yayi saurare za'a gafarta masa abinda ke tsakaninsa da tsakanin Juma'a da ƙarin kwanaki uku, wanda ya taba tsakankwani to haƙiƙa ya yi yashasshiyar magana". [Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 857].
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -: Lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Idan (watan) Ramadan ya zo sai a buɗe ƙofofin aljanna, a kukkule ƙofofin wuta, kuma a ɗaɗɗaure shaiɗanu". [Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka ruwaito shi] - [صحيح مسلم - 1079]
Daga Abu Musa - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Lallai ne Allah - Maɗaukakin sarki - Yana shimfiɗa hannunSa da daddare domin mai laifi da rana ya tuba, kuma Yana shimfiɗa hannunSa da rana domin mai laifi da daddare ya tuba, har sai rana ta ɓullo daga yammacinta". [Ingantacce ne] - [Muslim ne ya ruwaito shi] - [صحيح مسلم - 2759]