Hadisan Annabi (SAW) da aka zaɓa
Daga Abu Umamah – Allah Ya yarda da shi – ya ce: -Naji Manzon Allah yana cewa: "Ku karanta Alƙur’ani domin zaizo ranar alƙiyama yana mai ceto ga ma’abotansa". [Ingantacce ne] - [Muslim ne ya ruwaito shi]
Daga A'isha - Allah Ya yarda da ita - lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ku yi kirdadon lailatul-ƙadri a cikin mara daga goman ƙarshe na Ramadan". [Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka ruwaito shi] - [صحيح البخاري - 2017]
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ku yi sahur, domin lallai akwai albarka a cikin sahur". [Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka ruwaito shi] - [صحيح البخاري - 1923]
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Sallah a cikin masallacina wannan (ita ce) mafi alheri daga sallah dubu a cikin waninsa sai dai Masallaci mai alfarma". [Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi] - [صحيح البخاري - 1190]
Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: "Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance mafi kyauta cikin mutane, kuma ya kasance mafi kyutar da yake yi a Ramadan ne". [Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka ruwaito shi] - [صحيح البخاري - 6]
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Allah Ya ce: Dukkan aikin ɗan Adam nasa ne, sai azumi, lallai shi Nawa ne kuma Nine Zan Yi sakayya da shi ". [Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka ruwaito shi] - [صحيح البخاري - 1904]
Daga Sahl ɗan Sa'ad - Allah Ya yarda da shi - lallai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Mutane ba zasu gushe ba cikin alheri matuƙar sun gaggauta buɗa baki". [Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka ruwaito shi] - [صحيح مسلم - 1098]
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya azumci Ramadan yana mai imani da neman lada za'a gafarta masa abin da ya gabata daga zunubinsa". [Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka ruwaito shi] - [صحيح البخاري - 38]
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya yi tsayuwar lailatul-ƙadri yana mai imani da neman lada za'a gafarta masa abin da ya gabata daga zunubinsa" [Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka ruwaito shi] - [صحيح البخاري - 35]
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: "Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Allah - alherinSa ya yawaita kuma Ya ɗaukaka - Ya ce: Yakai ɗan Adam lallai cewa kai muddin ka roƙeNi, ka yi kwaɗayi gareNi zan gafarta maka abinda ya kasance gareka babu ruwaNa". [Hasan ne] - [al-Tirmithi ya ruwaito shi] - [سنن الترمذي - 3540]