PHPWord

 

 

 

التَّحْذِيرُ مِنْ بِنَاءِ المَسَاجِدِ

عَلَى القُبُورِ

 

Tsawatarwa akan gina masallatai a maƙabartu

 

 

 

 

 

لِسَمَاحَةِ الشَّيْخِ العَلَّامَةِ

عَبْدِ العَزِيزِ بْنِ عَبْدِ اللهِ بْنِ بَازٍ

رَحِمَهُ اللهُ

 

Wallafar: Babban Malami

AbdulAzeez Bin Abdullahi Bin Baaz

Allah Yayi masa rahama

 

 


بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ

SAƘO NA GOMA:

Tsawatarwa akan gina masallatai a maƙabartu

Da sunan Allah, godiya ta tabbata ga Allah, tsira da aminci su tabbata ga Manzon Allah.

Bayan haka, haƙiƙa na ga wani abu da aka buga a fitowa ta uku a mujallar Rabiɗat al-Ulum al-Islamiyyah a babin: (Labaran Musulmai a wata): Lalle Rabiɗat al-Ulum al-Islamiyyah dake masarautar Hashimiyya ta ƙasar Jordan tana son gina wani masallaci a kan wani kogo da aka gano bada daɗewa ba a garin al-Raheeb, wanda shi ne kogon da ake cewa: Lalle (Ashabul kahf) mutanan kogo da bayaninsu ya zo a cikin Alƙur’ani mai girma sun kwanta a cikinsa.

Ya ƙare.

Duba da wajibcin nasiha ga Allah da kuma bayinSa, na ga in wajjahar da wata kalma a mujalla ɗin a karan kanta ta Rabiɗatul Ulumul Islamiyya dake masarautar Hashimiyya ta ƙasar Jodan, abinda ta ƙunsa: Nasihar Rabiɗah akan aikin da ta ƙuduri aniyar yi na gina masallaci a kogon da aka ambata; ba kuma komai ya kawo hakan ba sai domin yin gini akan ƙaburburan Annabawa da salihai da gurabensu na abinda shari’ar Musulinci cikakkiya tazo da shi na hani da kuma tsawatarwa akai, da kuma la’anar wanda ya aikata hakan; saboda kasantuwarsa hanyoyin shirka da wuce iyaka akan Annabawa da salihai. Abinda yake a waƙi'i mai shaida ne akan ingancin abinda shari’a ta zo da shi, kuma dalili ne akan lalle daga Allah - Maɗaukakin Sarki - take, kuma dalili ne maɗaukaki kuma hujja ta yankan shakku akan gaskiyar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - , a cikin abinda ya zo da shi daga wurin Allah ya kuma isarwa al’umma. Duk wanda yayi la’akari da halin da duniyar Musulinci take ciki, da kuma abinda ya faru na shirka da wuce iyaka; ta sanadiyar gina Masallatai a ƙaburbura, da girmamasu da yi musu shinfiɗa da kwalliya, da kuma samar da masu yi musu hidima, zai sami ilimi na yaƙini cewa hakan yana cikin hanyoyin shirka, kuma yana cikin kyawun shari'ar Musulinci hana hakan da kuma tsawatarwa akan ginin.

Yana daga cikin abinda yazo akan hakan, abinda Bukhari da Muslim suka ruwaito - Allah Yayi musu rahama -, daga Nana Aisha - Allah Ya yarda da ita ta ce: Ma’aikin Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Allah Ya tsinewa Yahudawa da Nasara, sun riƙi ƙaburburan annabawansu masallatai» Nana A'isha ta ce: Yana gargaɗi akan abin da suka aikata, ta ce: Badon haka ba da an fito da ƙabarinsa, banda ana jin tsoron a riƙe shi masallaci. Kuma acikin ingantattun littattafan hadisan nan biyu, cewa Ummu Salama da Ummu Habibah - Allah Ya yarda da su - sun ambatawa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - wata coci da suka gani a ƙasar Habasha, da kuma abinda yake cikinta na hotuna, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Waɗannan mutanan idan mutumin kirki ya mutu a cikinsu; sai su gina masallaci a kan ƙabarinsa, su kuma zana irin waɗancan hotunan a cikin sa, waɗancan su ne ashararan halitta a wajen Allah.

Da hadisin Jundub bin Abdullah - Allah Ya yarda ad shi - a cikin Sahih Muslim ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - kafin ya rasu da kwana biyar yana cewa: "Lalle ni ina barranta zuwa ga Allah ya kasance ina da badaɗayi daga cikinku, domin Allah - Madaukakin sarki - haƙiƙa Ya riƙe ni badaɗayi kamar yadda Ya riƙi (Annabi) Ibrahim badaɗayi da na kasance mai riƙon badaɗayi daga al'umma ta, da na riƙi Abubakar badaɗayi ku saurara, lallai waɗanda suka gabace ku sun kasance suna maida ƙaburburan Annabawan su da salihan su masallatai, ku saurara, kada ku maida kaburbura masallatai, lalle ni ina hanaku hakan". Hadisai a wannan babin suna da yawa.

Haƙiƙa manyan malaman Musulinci sun nassanto a fili daga dukkanin mazhabobi huɗu da wasun su akan hani na gina masallatai a maƙabartu kuma sun tsawatar akan hakan; domin aiki da sunnar Manzon Allah -tsira tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, da kuma nasiha da tsawatar da al’umma don kada ta faɗa a cikin abinda waɗanda suka gabace ta suka faɗa na masu wuce iyaka daga Yahuduwa da Nasara da makamantansu daga cikin ɓatattun wannan al’umma.

Abinda yake wajibi ga Rabiɗatul Ulumul Islamiyyah dake Jodan, da wanin su cikin musulmai shi ne ruƙo da sunnah, da kuma tafiya akan tsarin manyan malamai, da kuma tsawatarwa daga abinda Allah da ManzonSa suka tsawatar, to anan akwai gyaruwar bayi da rabautar su da kuma tsiran su a duniya da lahira. Haƙiƙa wasu daga cikin mutane sun alaƙanta faɗin Allah - Maɗaukakin Sarki - a wannan abin a ƙissar (Ashabul kagf) ƴan kogo:

﴿...قَالَ ٱلَّذِينَ غَلَبُواْ عَلَىٰٓ أَمۡرِهِمۡ لَنَتَّخِذَنَّ عَلَيۡهِم مَّسۡجِدٗا﴾

(Sai waɗanda suka yi rinjaye a kan lamarinsu suka ce lalle zamu riƙi masallaci a gare su) [Kahf: 21].

Amsa ga wannan: Shine a ce: Lallai Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ba da labari game da shugabanni da masu iko a wannan lokacin cewa sun faɗi wannan magana, kuma ba haka ba ne a matsayin yarda da tabbatarwa gare su, sai dai a matsayin zargi da aibu da kuma tsoratarwa daga aikinsu. Kuma yana nuni akan haka: Lalle Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - wanda shi aka saukarwa wannan ayar, kuma shi yafi kowa sanin fassarar ta, ya hana al’ummar sa riƙon masallatai a maƙabartu, ya tsawatar da su hakan, ya kuma la’anci gami da zargin wanda ya aikata hakan.

Inda hakan ya halatta, da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - bai kausasa ba, matuƙar kausasawa, ya kai matuƙa a hakan har ya la'anci wanda ya aikata hakan, ya kuma bada labarin cewa shi yana cikin ashararan halittu a wurin Allah - Mai girma da ɗaukaka -, to wannan kuwa akwai isa da wadatuwa a cikin sa ga duk mai neman gaskiya. Da zamu ƙaddara cewa riƙon masallatai a maƙabartu ya halatta ga waɗanda suka gabace mu; to ai bai halatta a garemu mu yi koyi da su ba akan hakan, domin shari’armu ta shafe shari’ar da ta gaba ce ta, kuma Manzommu - tsira da aminci su tabbata a gare shi -, shine cikamakin Manzanni, kuma shari’ar sa cikakkiya ce kuma gamammiya, kuma haƙiƙa ya hana mu mu riƙi masallatai akan maƙabartu, kuma baya halatta a garemu mu saɓa masa, ya wajaba muyi masa biyayya da ruƙo da abinda ya zo da shi da barin abinda ya saɓawa hakan na shari’o'in da suka gabata, da al’adu waɗanda masu aikatasu suke ganin kyawun su; domin babu abinda ya cika kamar shari’ar Allah, kuma babu wata shiriya mafi kyau kamar shiriyar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi-.

Allah nake roƙo da Ya datar damu da ɗaukacin musulmai da tabbata akan AddininSa, da kuma riƙo da Shari'ar ManzonSa (annabi) Muhammad - tsira da aminci su tabbata a gare shi -; a cikin maganganu da ayyuka, a bayyane da a ɓoye, da kuma a cikin dukkan al'amura har mu haɗu da Allah - Mai girma da ɗaukaka -, lallai Shi Mai ji ne kuma Makusanci.

Tsira da amincin Allah su tabbata ga bawanSa kuma ManzonSa (annabi) Muhammad da alayensa da sahabbansa da waɗanda suka bi shiriyarsa har zuwa ranar sakamako.

 

 

***