PHPWord

 

 

صِفَةُ العُمْرَةِ

 

SIFFAR AIKIN UMARA

 

سَمَاحَةُ الشَّيْخِ

عَبْدِ الْعَزِيزِ بْنِ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ بَازٍ

رَحِمَهُ اللَّهُ

 

NA

Babbab malami

AbdulAzeez Bn Abdullahi Bn Baaz

Allah Yay i masa rahama

 

 

 


بِسْمِ اللهِ الرَّحمَنِ الرَّحِيمِ

SIFFAR AIKIN UMARA

Mawallafi

AbdulAzeez Bn Abdullahi Bn Baaz

Dukkanin godiya ta tabbata ga Allah shi kaɗai, bayan haka:

Waɗannan taƙaitattun bayanai ne akan ayyukan ibadun Umra Ga bayanin hakan ga mai karatu:

Idan wanda yake son yin Umarah ya isa miƙati, an so a gare shi yayi wanka, ya tsaftace jikinsa, haka ma mace zata yi, ko da tana al’ada ko biƙi, saidai kawai baza ta yi Ɗawafi ba har sai ta yi tsarki kuma tayi wanka.

Namiji yana sanya turare a jikinsa ba’a tufafinsa na ihrami ba, idan wankan bai samu ba a miƙati ba to babu laifi, kuma an so ya yi wanka idan ya isa Makkah, kafin yayi Ɗawafi, idan hakan ya sawwaƙa.

Namiji yana cire dukkanin kayan jikinsa ɗinkakku, sai ya sanya kwarjalle da mayafi, (ya yafa), an so su kasance farare masu tsafta.

Amma ita mace, za ta yi haramarta ne a tufafinta na gida (banda niƙabi da safa, sai ta cire su, tana rufe fuskarta da tafikanta daga barin maza waɗanda ba maharramanta ba da wasu tufafin da ba niƙab ba) waɗanda ba su da ado, ko nuna shahara.

Sannan ya yi niyyar shiga cikin ayyukan Umrah a zuciyarsa, yana mai cewa da harshansa: Labbaika Umarah”, ko kuma: “Allahumma Labbaika Umrah”. Idan mai harama yaji tsoron ba zai iya bada ayyukan ba, saboda bashi da lafiya, ko tsoron maƙiyi, ko makamancin haka, an shar’anta masa ya sanya sharaɗi a lokacin ihiramin na sa, sai ya ce: «Idan wani abu mai tsarewa ya tsareni to zan warware haramata a inda ya tsareni» Saboda hadisin Biba’a bint Zubair - Allah Ya yarda da ita -.1

Sannan yayi Talbiya da irin Talbiyar Annabi- tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ita ce: AmsawarKa Ya Ubangiji amsawarKa, amsawarKa baKa da abokin tarayya amsawarKa, dukkan godiya da ni’ima naKa ne mulki ma (naKa ne), baKa da abokin tarayya.

Zai yawaita faɗin wannan Talbiyar da kuma ambaton Allah - Mai girma da ɗaukaka - da roƙonSa (Addu’a) har ya kai ga Ka’aba. «‌AmsawarKa ya Allah amsawarKa, amsawarKa, ba Ka da abokin tarayya amsawarKa, lallai godiya da ni'ima naKa ne mulki ma (naKane) ba Ka da abokin tarayya». Ya kuma yawaita wannan Talbiyar, da kuma ambaton Allah -Maɗaukakin sarki - da roƙonSa har sai ya kai ga ɗaki "Ka’abah".

(Maza suna ɗaga muryarsu, mata kuma suna ƙasa da muryar ta su, kamar yadda sahabbai - Allah Ya yarda da su - suka aikata.

Idan ya isa Ka’aba sai ya dakatar da Talbiyar, sai ya nufi Hajarul Aswad ya kuma fuskance shi, sannan ya taɓa shi da damansa ya sumbance shi idan ya sami ikon hakan, kada ya cutar da mutane da cunkoso, ya ce a lokacin da yake taɓa shi: "Bismillahi wallahu Akbar".

Idan sumbantar tayi wahala, sai ya taɓa shi da hannunsa ko da sanda ko da wani abu, idan taɓawar tayi wahala sai ya nuna shi, ya ce: "Allahu Akbar". Kuma bazai sumbanci abinda ya nuna da shi ba.

An sharɗanta a ingancin Ɗawafi mai Ɗawafin ya kasance yana da tsarki na ƙaramin hadasi da babba; domin Ɗawafi kamar sallah yake saidai shi an yi rangwamin yin magana a cikinsa.

Ya sanya Ka’aba a hagunsa, sai yayi Ɗawafi zagaye bakwai, idan yazo kusa da Rukunul Yamani sai ya taɓa shi da damansa idan ya samu iko, sai ya ce: "Bismillahi wallahu Akbar".

Bazai sumbance shi ba, idan taɓawar tayi wahala sai ya barshi, yaci gaba da Ɗawafinsa, bazai nuna shi ba, kuma bazaiyi kabbara ba, domin yin hakan ba’a samo shi daga Annabi- tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ba.

Amma Hajarul Aswad to a duk lokacin da yazo daidai da shi, sai ya taɓa shi ya kuma sumbance shi, kamar yadda muka ambata a baya, idan hakan baiyiwu ba, sai ya nuna shi yayi kabbara.

An so yin sassarfa-wato tafiya da sauri- a zagaye na ukun farko a farkon Ɗawafinsa na shigowa, wannan kuma ga namiji ne kaɗai. Ana son sassarfa - ita ce yin sauri a tafiya tare da kusantuwar taku- a lokacin zagayen ukun farko, a ɗawafin isowa, wannan kuwa ga namiji kaɗai.

Kamar yadda aka so ga namiji yayi Ibɗiɓa a Ɗawafin isowa a dukkanin kewayen, abin nufi da Ibɗiba'u: Ya sanya tsakiyar mayafinsa a ƙasan kafaɗarsa ta dama, gefunan kuma suna kan kafaɗarsa ta hagu. Al-Idɗiba'u: Shine ya sanya tsakiyar mayafinsa a ƙarƙashin hammatarsa ta dama, gefunansa (mayafin) kuma akan kafaɗarsa ta hagu.

An so yawaita ambaton Allah da addu’a da abinda ya sawwaƙa a dukkanin zagayan.

Babu wata keɓantacciyar addu'a a Ɗawafi, ko wani zikiri keɓantacce, kawai ya roƙi Allah kuma ya ambaci Allah da abinda ya sawwaƙa a gare shi na addu’o'i da zikiri, kuma a tsakanin Rukunul Yamani da Hajarul Aswad ya ce::

﴿...رَبَّنَآ ءَاتِنَا فِي ٱلدُّنۡيَا حَسَنَةٗ وَفِي ٱلۡأٓخِرَةِ حَسَنَةٗ وَقِنَا عَذَابَ ٱلنَّارِ﴾

Ya Ubangijinmu Ka bamu mai kyau a duniya kuma a Lahira ma Ka bamu mai kyau, kuma Ka tsaremu azabar wuta [al-Baƙara: 201]. a kowanne zagaye; domin hakan ya tabbata daga Annabi- tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -.

Sai ya cika na bakwai da taɓa Hajarul Aswad, da sumbantar sa idan ya sami ikon hakan, ko yayi nuni gare shi tare da kabbara , gwargwadon yadda bayani ya gabata ɗazu. Bayan ya gama wannan Ɗawafin sai ya dawo da mayafinsa ya sanya shi akan kafaɗunsa, gefunansa biyu akan ƙirjinsa.

Sannan sai yayi sallah raka’a biyu a bayan Maƙamu Ibrahim, idan ya sami sararin hakan, idan kuma bai samu ba, sai ya yi raka’o'in a duk inda ya samu sarari a cikin masallacin, zai karanta a cikinsu bayan Fatiha: Kulya .. a raka’a ta farko, da kuma Kul huwallhu a raka’a ta biyu. Wannan shine abinda ya fi, idan ya karanta wasu babu wani laifi. Sannan bayan yayi sallama daga raka’oi biyun sai ya nufi Hajarul Aswad idan ya sami damar hakan.

﴿قُلۡ يَٰٓأَيُّهَا ٱلۡكَٰفِرُونَ 1﴾

{Ƙul yã ayyuhal kafirun 1 (Ka ce: "Ya kũ kãfirai 1). [al-Kafirun:1] A raka'a ta farko, da kuma:

﴿قُلۡ هُوَ ٱللَّهُ أَحَدٌ 1﴾

{Ka ce: "Shi ne Allah Makaɗaĩci. (1) [al-Ikhlas: 1]. A raka’a ta biyu, wannan shi ne abinda ya fi, idan kuma ya karanta waninsu babu wani laifi. Sannan bayan ya yi sallama daga raka’a biyun, sai ya nufi baƙin dutse, sai ya sumbance shi da (hannunsa) na dama, idan hakan ya sawwaƙa. An sunnanta shan ruwan Zamzam bayan sallah raka'a biyu ta ɗawafi idan hakan ya sawwaƙa.

Sannan sai ya fita zuwa Safa, sai ya hau ko ya tsaya daidai a wajensa, amma hawan ya fi idan akwai damar, sai kuma ya karanta faɗin Allah - Maɗaukakin sarki -:

﴿إِنَّ ٱلصَّفَا وَٱلۡمَرۡوَةَ مِن شَعَآئِرِ ٱللَّهِ... ﴾

(Lallai Safa da Marwa suna daga cikin alamomin bauta ga Allah..) [al-Baƙara: 158].

An so ya fuskanci alƙibla (Ka’aba) ya godewa Allah ya girmama Shi ya ce: "Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Allahu Akbar, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kaɗai Yake, ba Shi da abokin tarayya, mulki na Sa ne, kuma godiya tasa ce, kuma Shi Mai iko ne akan dukkan komai. Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Ya cika alƙawarinSa Ya taimaki bawanSa, Ya rinjayi ƙungiyoyin ƙawance Shi kaɗai".

Sannan ya roƙi duk abinda yake so, yana mai ɗaga hannuwansa, yana maimaita wannan zikirin da addu’ar sau uku. Allahu Akbar, Allahu Akbar, La’iha Illallahu, Allahu Akbar, Allahu Akbar, walillahil Hamd, la'ilaha illallahu wahdahu la sharika lahu, lahul mulk walaul hamd wahuwa ala kulli shai'in ƙadir, la'ilaha illallahu wahdahu anjaza wa'adah, wa nasara abdah, wa hazamal ahzaba wahdah.

Ma’ana: Allah Shi ne Mai girma, Allah Shi ne Mai girma, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Allah Shi ne Mai girma, Allah Shi ne Mai girma, godiya ta tabbata ga Allah. Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kaɗai yake ba Shi da abokin tarayya, mulki naSa ne, kuma godiya taSa ce, kuma Shi Mai iko ne akan komai.

Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kaɗai yake, Ya cika alƙawarinSa Ya kuma taimakawa bawanSa, Ya rinjayi rundunoni taron dangi Shi kaɗai2. Sai ya roƙi abinda ya sawwaƙa na addu’a, sannan ya maimaita zikirin da addu’ar sau uku. Wannan ita ce Sunnar da Annabi- tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya aikata, yana mai fuskantar alƙibla. Sannan ya sakko, sai ya tafi Marwa, har idan ya kai alama ta farko, sai namiji ya yi sauri a tafiyar, har sai ya kai alama ta biyu.

Amma mace ba a shar’anta mata yin sauri ba; domin ita al’aura ce, sannan sai ya tafi ya hau Marwa ko ya tsaya a wurin nata, amma hawan shi ya fi idan ya sami dama, zai faɗa kuma ya aikata a Marwa kamar yadda ya faɗa kuma ya aikata a Safa.

Sannan sai ya sakko sai yayi tafiya a wurin tafiyarsa, ya kuma yi sauri a wurin saurinsa har sai ya kai Safa, zai yi hakan sau bakwai, tafiyarsa lissafin ta daban, dawowarsa ma lissafin ta daban, idan kuma ya yi akan abin hawa babu laifi, musamman ma idan akwai buƙatar hakan. Wanda kuma ya yi Sa’ayi (Safa da Marwa) akan abin hawa, to babu laifi, musamman idan akwai buƙatar hakan. Kuma ana so ya yawaita zikiri da ambaton Allah da roƙon abinda ya sawwaƙa, a Sa’ayin nasa, ya kuma zama mai tsarki daga hadasi babba da ƙarami.

Kuma an so ya yawaita zikiri da addu'a da abinda ya sawwaƙa a Sa’ayinsa, kuma ya kasance mai tsarki daga babban hadasi da ƙaramin, da ace zaiyi Sa’ayi ba shi da tsarki to Sa’yin ya yi.

Idan ya cika Sa’ayin sai namiji ya aske kansa ko ya yi saisaye, askewar shi yafi, idan kuma shigowar shi Makka yayi kusa da fita Hajji, to yin saisaye shi ya fi a wurinsa, domin ya aske abinda ya saura na kansa a Hajji.

To Amma ita mace za ta tara gashinta ne sai ta yanki wani abu na shi gwargwadon kan yatsa ko ƙasa da hakan.

To idan mai harama ya aikata abinda aka ambata to haƙiƙa ya kammala Umrarsa, Alhamdulillah. Kuma duk abinda ya haramta a gare shi saboda Ihrami yanzu ya halatta gareshi. (Annabi- tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- bai yi wata sallah bayan kammala Umararsa raka’a biyu ba, wanda yake son sa, sai ya yi irin yadda ya yi).

﴿لَّقَدۡ كَانَ لَكُمۡ فِي رَسُولِ ٱللَّهِ أُسۡوَةٌ حَسَنَةٞ لِّمَن كَانَ يَرۡجُواْ ٱللَّهَ وَٱلۡيَوۡمَ ٱلۡأٓخِرَ وَذَكَرَ ٱللَّهَ كَثِيرٗا 21﴾

(Lalle, abin kõyi mai kyau ya kasance gare ku daga Manzon Allah, ga wanda ya kasanee yanã fãtan rahamar Allah da Rãnar Lãhira, kuma ya ambaci Allah da yawa). [al-Ahzab: 21].

Allah Ya datar da mu da ragowar ’yan uwammu musulmai ga fahimatar addini da tabbatuwa a kansa, kuma Ya karɓa daga garemu baki ɗaya; lalle Shi tsarki ya tabbatar maSa Mai kyauta ne kuma Mai karamci ne.

Tsira da amincin Allah su tabbata ga bawanSa kuma ManzanSa Annabimmu Muhammad da iyalansa da da sahabbansa da mabiyansa da kyautatawa zuwa ranar sakamako.

Taƙaitaccan bayani daga ayyukan ibadun Umrah, wanda ya zo daga ofishin mai daraja a 13/2/1416 H.

(Maj’mu’ul Fatawah da maganganun shehin malami Ibnu Baz, juzu’i na 27, shafi na 425).

 

***

 


Muslim ya fitar da shi, a lamba ta (1218).

Al-Sunanul Kuburah, na Baihaƙi, a lamba ta: (10117).