العَقِيدَةُ الصَّحِيْحَةُ وَمَا يُضَادُّهَا
AƘIDA INGANTACCIYA DA
ABINDA YAKE KISHIYANTAR TA
لِسَمَاحَةِ الشَّيْخِ العَلَّامَةِ
عَبْدِ العَزِيزِ بْنِ عَبْدِ اللهِ بْنِ بَازٍ
رَحِمَهُ اللهُ
Wallafar: Babban Malami
AbdulAzeez Bin Abdullahi Bin Baaz
Allah Yayi masa rahama
بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ
SAƘO NA FARKO
Aƙida ingantacciya da abinda yake kishiyantarta
Wallafar: Babban Malami
AbdulAzeez Bin Abdullahi Bin Baaz
Godiya ta tabbata ga Allah Shi kaɗai, tsira da aminci su tabbata ga wanda babu wani annabi a bayansa, da alayen sa da sahabban sa.
Bayan haka: A yayin da ingantacciyar aƙidah ta kasance ita ce asalin Musulinci, kuma tushen addini, sai na ga cewa yana daga abu mai muhimmanci yin magana akan wannan batun, da kuma yin rubutu da wallafa domin bayaninsa da kuma fayyace shi.
Abu ne da yake sananne akan dalilai na shari’a daga Alƙur’ani da Hadisi: Cewa ayyuka da maganganu suna ingantane kuma a karɓe su idan suka kasance daga ingantacciyar aƙidah. Amma idan aƙidah ta kasance gurɓatacciya, to fa duk abinda ya rassantu daga gare ta na ayyuka da maganganu ya zama ɓatacce, kamar yadda Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:
﴿...وَمَن يَكۡفُرۡ بِٱلۡإِيمَٰنِ فَقَدۡ حَبِطَ عَمَلُهُۥ وَهُوَ فِي ٱلۡأٓخِرَةِ مِنَ ٱلۡخَٰسِرِينَ﴾
{Kuma wanda ya kãfirta da ĩmãni to, lalle ne aikinsa yã ɓãci, kuma shĩ, a cikin Lãhira, yanã daga mãsu hasãra.} [al-Ma'ida: 5].
Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:
﴿وَلَقَدۡ أُوحِيَ إِلَيۡكَ وَإِلَى ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِكَ لَئِنۡ أَشۡرَكۡتَ لَيَحۡبَطَنَّ عَمَلُكَ وَلَتَكُونَنَّ مِنَ ٱلۡخَٰسِرِينَ 65﴾
{Kuma hakika an yi wahayi zuwa gare ka da kuma zuwa ga waɗanda suke a gabãninka, "Lalle idan ka yi shirki haƙĩƙa aikinka zai ɓãci, kuma lalle zã ka kasance daga mãsu hasãra."} [al-Zumar: 65],
Kuma ayoyi da suka zo da wannan ma’anar suna da yawa. Kuma tabbas littafin Allah mabayyani da sunnar Manzon Sa amintacce - mafificin salati da aminci su tabbata a gare shi daga Ubangijin sa -; sun yi bayani akan aƙidah nagartacciya tana dunƙule ne a cikin abubuwa shida, su ne kamar haka: Imani da Allah, da Mala’iku da Littattafai da Manzanni da ranar lahira da kuma ƙaddara alkhairin ta da sharrin ta. To waɗannan abubuwa shida, su ne tushen aƙidah ingantacciya, waɗanda littafin Allah mai buwaya ya saukar da su, kuma Allah Ya aiko Manzon shi (Annabi) Muhammad - tsira da aminci su tabbata a gare shi - da ita.
Kuma tabbas dalilai masu yawa sun zo akan waɗannan tushen guda shida a cikin Alƙur’ani da kuma sunnah ingantacciya, daga cikin haka abinda zaizo domin buga misali:
Na farko: Dalilai daga Alƙur’ani; daga cikin su akwai faɗin Allah - Mai girma da ɗaukaka -:
﴿لَّيۡسَ ٱلۡبِرَّ أَن تُوَلُّواْ وُجُوهَكُمۡ قِبَلَ ٱلۡمَشۡرِقِ وَٱلۡمَغۡرِبِ وَلَٰكِنَّ ٱلۡبِرَّ مَنۡ ءَامَنَ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِ وَٱلۡمَلَٰٓئِكَةِ وَٱلۡكِتَٰبِ وَٱلنَّبِيِّـۧنَ...﴾
{Bai zama addini ba dõmin kun jũyar da fuskõkinku wajen gabas da yamma, kuma amma addini shi ne ga wanda ya yi ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira da malã'iku da Littattafan (sama) da Annabãwa.} [al-Baƙara: 177].
Da faɗinSa Allah - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka -:
﴿ءَامَنَ ٱلرَّسُولُ بِمَآ أُنزِلَ إِلَيۡهِ مِن رَّبِّهِۦ وَٱلۡمُؤۡمِنُونَۚ كُلٌّ ءَامَنَ بِٱللَّهِ وَمَلَٰٓئِكَتِهِۦ وَكُتُبِهِۦ وَرُسُلِهِۦ لَا نُفَرِّقُ بَيۡنَ أَحَدٖ مِّن رُّسُلِهِ...﴾
{Manzon Allah yã yi ĩmãni da abin da aka saukar zuwa gare shi daga Ubangijinsa, da mũminai. Kõwanensu yã yi ĩmãni da Allah, da mala'ikunSa, da littattafanSa, da manzanninSa. Bã mu rarrabẽwa a tsakãnin ɗaya daga ManzanninSa".} [al-Baƙara: 285].
Da faɗinSa - tsarki ya tabbatar maSa -:
﴿يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ ءَامِنُواْ بِٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦ وَٱلۡكِتَٰبِ ٱلَّذِي نَزَّلَ عَلَىٰ رَسُولِهِۦ وَٱلۡكِتَٰبِ ٱلَّذِيٓ أَنزَلَ مِن قَبۡلُۚ وَمَن يَكۡفُرۡ بِٱللَّهِ وَمَلَٰٓئِكَتِهِۦ وَكُتُبِهِۦ وَرُسُلِهِۦ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِ فَقَدۡ ضَلَّ ضَلَٰلَۢا بَعِيدًا 136﴾
{Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi ĩmãni da Allah da Manzonsa, da Littãfin da Ya sassaukar ga ManzonSa da Littãfin nan wanda Ya saukar daga gabãni. To, wanda ya kãfirta da Allah da malã'ikunSa, da LittattafanSa, da ManzanninSa, da Rãnar Lãhira, to, lalle ne yã ɓace, ɓata mai nĩsa.} [al-Nisa'i: 136].
Da faɗinSa - tsarki ya tabbatar maSa -:
﴿أَلَمۡ تَعۡلَمۡ أَنَّ ٱللَّهَ يَعۡلَمُ مَا فِي ٱلسَّمَآءِ وَٱلۡأَرۡضِۚ إِنَّ ذَٰلِكَ فِي كِتَٰبٍۚ إِنَّ ذَٰلِكَ عَلَى ٱللَّهِ يَسِيرٞ 70﴾
{Ashe, ba ka sani ba, lalle ne Allah Yanã sanin abin da yake a cikin sama da ƙasa? Lalle ne wancan yanã cikin Littafi, lalle wancan ga Allah mai sauƙi ne.} [al- Hajj: 70].
Na biyu: Dalilai daga Sunnah; Daga ciki akwai hadisi ingantacce shahararre wanda Muslim ya ruwaito shi a Sahihin ɗinsa cikin hadisin sarkin muminai Umar ɗan al-Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi -, cewa (Mala’ika) Jibrilu - aminci ya tabbata a gare shi - ya tambayi annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - dangane da imani, sai ya ce da shi: «Imani: (shi ne) ka yi imani da Allah, da mala'ikunSa da littattafanSa, da ManzanninSa, da ranar lahira, kuma ka yi imani da ƙaddara: alkhairinta da sharrinta»1. Hadisi, Kuma Bukhari da Muslim- tare da banbanci kaɗan - sun fitar da shi cikin hadisin Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -.
Kuma yana karkasuwa daga cikin waɗannan tushan guda shida: Dukkan abinda yake wajaba musulmi ya ƙudurce shi, ya kuma yi imani da shi, na haƙƙin Allah - Mai girma da ɗaukaka -, da al’amarin lahira, da wanin haka na al'amuran gaibu, wanda Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya bada labarin sa, da ManzonSa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -
Bayanin waɗannan asali guda shida shi ne kamar haka:
ASALI NA FARKO: Imani da Allah - Maɗaukakin Sarki -, hakan kuma yana ƙunsar abubuwa da dama; daga cikinsu akwai:
Shi imani (da Allah) yana ƙunsar al'amurra da dama; daga cikinsu: Imani da cewa Shi ne Ubangiji na gaskiya wanda Ya cancanci bauta banda waninSa; saboda kasantuwar Sa Mahaliccin bayi, Mai kyautata musu, Mai tsayuwa akan arzuƙansu, Masanin sirrin su da kuma zahirin su, kuma Mai iko akan bada lada ga mai biyayya a cikin su da kuma yin uƙuba ga wanda ya saɓa a cikin su.
Haƙiƙa Allah Ya halicci mutum da aljan saboda wannan bautar, kuma Ya umarce su da ita, kamar yadda Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya faɗa:
﴿وَمَا خَلَقۡتُ ٱلۡجِنَّ وَٱلۡإِنسَ إِلَّا لِيَعۡبُدُونِ 56 مَآ أُرِيدُ مِنۡهُم مِّن رِّزۡقٖ وَمَآ أُرِيدُ أَن يُطۡعِمُونِ 57 إِنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلرَّزَّاقُ ذُو ٱلۡقُوَّةِ ٱلۡمَتِينُ 58﴾
{Kuma Ban halitta aljannu da mutãne ba sai dõmin su bauta Mini,
Ba na nufin wani arziƙi daga garesu, kuma ba na nufin su ciyar dani,
{Lalle Allah, Shĩ ne Mai azurtãwa, Mai ĩkon yi, Mai cikakken ƙarfi.} [al-Zariyāt: 56-58].
Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:
﴿يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ ٱعۡبُدُواْ رَبَّكُمُ ٱلَّذِي خَلَقَكُمۡ وَٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِكُمۡ لَعَلَّكُمۡ تَتَّقُونَ 21 ٱلَّذِي جَعَلَ لَكُمُ ٱلۡأَرۡضَ فِرَٰشٗا وَٱلسَّمَآءَ بِنَآءٗ وَأَنزَلَ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءٗ فَأَخۡرَجَ بِهِۦ مِنَ ٱلثَّمَرَٰتِ رِزۡقٗا لَّكُمۡۖ فَلَا تَجۡعَلُواْ لِلَّهِ أَندَادٗا وَأَنتُمۡ تَعۡلَمُونَ 22﴾
{Yã ku mutãne! Ku bauta wa Ubangjinku, Wanda Ya halicce ku, kũ da waɗanda suke daga gabãninku, tsammãninku ku kãre kanku!,
{Wanda Ya sanya muku ƙasa shimfiɗa, kuma sama gini, kuma Ya saukar da ruwa daga sama, sa'an nan Ya fitar da abinci daga 'ya'yan itãce game da shi, sabõda ku. Sabõda haka kada ku sanya wa Allah wasu kĩshiyõyi, alhãli kuwa kuna sane.} [al-Baƙara: 21-22].
Haƙiƙa Allah Ya aiko Manzanni, kuma Ya saukar da littattafai, domin bayanin wannan gaskiyar, da kuma kira zuwa gare ta da kuma tsawatarwa daga abinda yake kishiyantar ta, kamar yadda Allah - tsarki ya tabbata a gare Shi - Ya ce:
﴿وَلَقَدۡ بَعَثۡنَا فِي كُلِّ أُمَّةٖ رَّسُولًا أَنِ ٱعۡبُدُواْ ٱللَّهَ وَٱجۡتَنِبُواْ ٱلطَّٰغُوتَ...﴾
{Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun aika a cikin kõwace al'umma da wani Manzo (ya ce): "Ku bauta wa Allah, kuma ku nĩsanci ɗãgũtu."} [al-Nahl: 36].
Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:
﴿وَمَآ أَرۡسَلۡنَا مِن قَبۡلِكَ مِن رَّسُولٍ إِلَّا نُوحِيٓ إِلَيۡهِ أَنَّهُۥ لَآ إِلَٰهَ إِلَّآ أَنَا۠ فَٱعۡبُدُونِ25﴾
{Kuma ba Mu aiki wani Manzo ba a gabãninka fãce Munã yin wahayi zuwa gare shi, cẽwa "Lalle ne Shi, bãbu abin bautãwa fãce Nĩ, sai ku bauta Mini."} [al-Anbiya: 25].
Kuma Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya ce
﴿الر كِتَابٌ أُحْكِمَتْ آيَاتُهُ ثُمَّ فُصِّلَتْ مِنْ لَدُنْ حَكِيمٍ خَبِيرٍ1 أَلَّا تَعْبُدُوا إِلَّا اللَّهَ إِنَّنِي لَكُمْ مِنْهُ نَذِيرٌ وَبَشِيرٌ2﴾
{A. L̃.R. Littãfi ne an kyautata ãyõyinsa, sa'an nan an bayyanã su daki-daki, daga wurin Mai hikima, Mai ƙididdigewa,
{Kada ku bautã wa kõwa fãce Allah. Lalle ne ni a gare ku mai gargaɗi ne kuma mai bushãrã daga gare Shi} [Hud: 1, 2].
Kuma haƙiƙanin wannan ibadar: Ita ce kaɗaita Allah - tsarki ya tabbata a gare Shi- da dukkanin abinda bayi suke bauta da shi; na addu’a, da tsoro, da ƙauna, da sallah, da azumi, da yanka, da bakance, da wanin haka na nau’ukan ibada, ta fuskar ƙanƙan da kai gare Shi da kwaɗayin lada, da kuma tsoron uƙubar Sa tare da cikakken so gare Shi da ƙasƙantar da kai ga girman Sa.
Wanda ya yi la’akari da Alƙur’ani mai girma zai samu mafi yawan sa ya sauka ne akan wannan asali mai girma; kamar faɗin Allah - Mai tsarki da ɗaukaka -:
﴿إِنَّآ أَنزَلۡنَآ إِلَيۡكَ ٱلۡكِتَٰبَ بِٱلۡحَقِّ فَٱعۡبُدِ ٱللَّهَ مُخۡلِصٗا لَّهُ ٱلدِّينَ فَاعْبُدِ اللَّهَ مُخْلِصًا لَهُ الدِّينَ 2 أَلَا لِلَّهِ الدِّينُ الْخَالِصُ وَٱلَّذِينَ ٱتَّخَذُواْ مِن دُونِهِۦٓ أَوۡلِيَآءَ مَا نَعۡبُدُهُمۡ إِلَّا لِيُقَرِّبُونَآ إِلَى ٱللَّهِ زُلۡفَىٰٓ إِنَّ ٱللَّهَ يَحۡكُمُ بَيۡنَهُمۡ فِي مَا هُمۡ فِيهِ يَخۡتَلِفُونَۗ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَهۡدِي مَنۡ هُوَ كَٰذِبٞ كَفَّارٞ3﴾
{Mun saukar da littafi a gareka da gaskiya to sai ka bautawa Allah kana mai tsarkake Addini a gare Shi}
{To, addini tsarkakakke na Allah ne, kuma waɗanda suka riƙi waɗansu majibinta, bã Shi ba, (sunã cẽwa) "Ba mu bauta musu ba fãce dõmin su kusantar da mu zuwa ga Allah, kusantar daraja." Lalle Allah nã yin hukunci a tsakãninsu ga abin da suka zama sunã sãɓãwa a cikinsa. Lalle Allah ba Ya shiryar da wanda yake mai ƙarya, mai kãfirci} [al-Zumar: 2-3].
Da faɗinSa Allah - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka -:
﴿وَقَضَىٰ رَبُّكَ أَلَّا تَعۡبُدُوٓاْ إِلَّآ إِيَّاهُ...﴾
{Kuma Ubangijinka Ya hukunta kada ku bauta wa kõwa fãce Shi} [al-Isra'a: 23].
Da faɗinSa - Mai girma da ɗaukaka -
﴿فَٱدۡعُواْ ٱللَّهَ مُخۡلِصِينَ لَهُ ٱلدِّينَ وَلَوۡ كَرِهَ ٱلۡكَٰفِرُونَ14﴾
{Sabõda haka ku kirãyi Allah, kunã mãsu tsarkake addini a gare Shi, kuma kõ dã kãfirai sun ƙi.} [Gafir: 14].
Haka kuma, wanda yayi la’akari da sunna ta Annabta zai sami kulawa ta musamman ga wannan asalin mai girma, daga wannan: Abinda aka ruwaito a cikin Bukhari da Muslim daga Mu’az - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Haƙƙin Allah akan bayinSa shi ne su bauta maSa kada su haɗa Shi da komai"2.
Yana shiga ƙarƙashin imani da Allah kuma: Imani da duk abinda Ya wajabta shi akan bayinSa, Ya kuma farlanta shi a kan su, na shika-shikan Musulinci biyar na zahiri.
Su ne: Shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Annabi Muhammad bawan Allah ne, da tsaida sallah, da bayar da zakkah, da azumin watan Ramadan da Hajjin Ɗakin Allah mai alfarma ga wanda ya sami ikon tafarki zuwa gare shi, da wanin haka na farillai, waɗanda shari’a tsarkakiyya ta zo da su.
Mafi muhimmancin waɗannan rukunan shine: Shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma (Annabi) Muhammad Manzon Allah ne. Wannan shaidawar tana hukunta: Tsarkake ibada ga Allah Shi kaɗai, da kuma kore ta ga duk wanda ba Shi ba, wannan shi ne ma’anar: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, wato ma’anar ta - kamar yadda malamai suka ce - Allah Yayi musu rahama -: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma gini akan hakan shine: Duk abinda aka bautawa bayan Allah- mutum ne ko mala’ika ko aljan ko wanin wannan -, to abin bautawa ne ba na gaskiya ba, abin bauta na gaskiya Shi ne Allah Shi kaɗai, kuma babu abokin tarayya a tare da Shi, kamar yadda Allah - Mai tsarki da ɗaukaka - Ya ce:
﴿ذَٰلِكَ بِأَنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلۡحَقُّ وَأَنَّ مَا يَدۡعُونَ مِن دُونِهِۦ هُوَ ٱلۡبَٰطِلُ...﴾
{Wancan! sabõda lalle ne Allah, shĩ ne Gaskiya, kuma lalle ne, abin da suke kira waninSa shi ne ƙarya.} [al-Hajj: 62].
Kuma haƙiƙa bayani ya gabata: Cewa lalle Allah - tsarki ya tabbata a gare Shi Ya ɗaukaka -, Ya halicci mutum da aljan ne domin wannan asali mai tushe, kuma Ya umarce su da shi, kuma Ya aiko ManzanninSa da shi, kuma Ya saukar da littattafanSa da shi; to ya zama wajibi ga bawa ya yi la’akari da wannan sosai, ya kuma yi tadabburinsa sosai; domin jahilci mai girma na wannan asalin da musulmai suka faɗa ya bayyana a gare shi; har ya kai sun bautawa Allah tare da waninSa, suka juyar da tsantsar haƙƙinSa ga waninSa, Allah Shi ne Abin neman taimako.
Yana daga cikin imani da Allah - tsarki ya tabba a gare Shi - imani da cewar Shi ne Mahalicci Masani kuma Mai juya lamuransu kuma Mai tasarrufi a cikinsu da iliminSa da ikonSa, kamar yadda Ya ga dama - tsarki ya tabbata a gare Shi -, kuma lalle Shine Mamallakin duniya da lahira, kuma Ubangijin talikai baki ɗaya, babu Mahalicci in ba Shi ba, kuma babu Ubangiji in ba Shi ba. Kuma Ya aiko Manzanni Ya kuma saukar da littattafai; domin gyara bayi, da kuma kiransu ga abinda yake tsira ne gare su da kuma gyara gare su a nan duniya da kuma lahira. Kuma lalle Shi Allah - tsarki ya tabbata a gare Shi -, ba Shi da abokin tarayya a dukkanin hakan, Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:
﴿ٱللَّهُ خَٰلِقُ كُلِّ شَيۡءٖۖ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ وَكِيلٞ 62﴾
{Allah ne Mai halittan dukkan kõme, kuma Shĩ ne Wakĩli a kan kõme.} [al-Zumar: 62].
Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:
﴿إِنَّ رَبَّكُمُ ٱللَّهُ ٱلَّذِي خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ فِي سِتَّةِ أَيَّامٖ ثُمَّ ٱسۡتَوَىٰ عَلَى ٱلۡعَرۡشِۖ يُغۡشِي ٱلَّيۡلَ ٱلنَّهَارَ يَطۡلُبُهُۥ حَثِيثٗا وَٱلشَّمۡسَ وَٱلۡقَمَرَ وَٱلنُّجُومَ مُسَخَّرَٰتِۭ بِأَمۡرِهِۦٓۗ أَلَا لَهُ ٱلۡخَلۡقُ وَٱلۡأَمۡرُۗ تَبَارَكَ ٱللَّهُ رَبُّ ٱلۡعَٰلَمِينَ54﴾
{Lalle ne Ubangijinku Allah ne, wanda Ya halicci sammai da ƙasa a cikin kwãnaki shida, sa'an nan kuma Ya daidaita a kan Al'arshi, Yanã sanya dare ya rufa yini, yanã nẽman sa da gaggawa, kuma rãnã da watã da taurãri hõrarru ne da umurninSa. To, Shĩ ne da halittar kuma da umurnin. Albarkar Allah Ubangijin halittu tã bayyana!.} [al-A'araf: 54].
Yana daga cikin imani da Allah - Maɗaukakin Sarki -: Imani da sunayansSa kyawawa da kuma siffofinSa maɗaukaka a littafinSa mabuwayi, kuma waɗanda suka tabbata daga ManzonSa amintacce, ba tare juyarwa ko korewa ba, kuma ba tare da surantawa ko kamantawa ba,
﴿...لَيۡسَ كَمِثۡلِهِۦ شَيۡءٞۖ وَهُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡبَصِيرُ﴾
{Wani abu bai zama kamar tamkarSa ba, kuma Shĩ ne Mai ji, Mai gani.} [al-Shura:11].
To yana wajaba a tafiyar da su ba tare da surantawa ba, tare da imani da abinda suka yi nuni akan sa na ma’anoni masu girma, waɗanda suke su ne siffofin Allah - Mai girma da ɗaukaka -, da kuma wajibcin siffanta Shi - Maɗaukakin Sarki - da su a fuskar da ta dace da Shi, ba tare da an kamanta halittun Sa a wani abu daga siffofinSa ba, kamar yadda Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce: Kuma Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya ce
﴿فَلَا تَضۡرِبُواْ لِلَّهِ ٱلۡأَمۡثَالَۚ إِنَّ ٱللَّهَ يَعۡلَمُ وَأَنتُمۡ لَا تَعۡلَمُونَ74﴾
{Sa'an nan kada ku bãyar da waɗansu misãlai ga Allah. Lalle ne Allah Yanã sani, kuma kũ, ba ku sani ba.} [al-Nahl: 74].
Wannan ita ce aƙidar Ahlussunna wal Jama’a daga sahabban Ma’aikin Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da mabiyansu da kyautatawa; a sunayan Allah da kuma siffofinSa, ita ce kuma wadda Imam: Abul Hasan al’Ash’ari - Allah Ya yi masa rahama - ya naƙalto ta a cikin littafin: “al-Maƙālat”, daga malaman hadisi da Ahlussunna, kuma wasun sa daga cikin ma'abota ilimi da imani suka naƙalto ta.
Al-Auza’i - Allah Ya yi masa rahama - ya ce: An tambayi az-Zuhri da Makhul, dangane da ayoyin da suke bayanin siffofin Allah, sai suka ce: Ku wuce su kamar yadda suka zo.3
Kuma al-Auza’i - Allah Ya yi masa rahama - ya faɗa dai: Mun kasance mu da tabi'ai mun haɗu muna cewa: Allah - tsarki ya tabbata a gare Shi -, Yana kan al’arshinSa, kuma muna imani da abinda ya zo a sunna, na Siffofi"4.
Kuma al-Walidu ɗan Muslim - Allah Ya yi masa rahama - ya ce: (An tambayi Maliku da al-Awza’i da al-Laisu ɗan Sa’ad, da Sufyan al-Thauri - Allah Ya yi musu rahama -, dangane da bayanan da suka zo akan siffofin Allah, sai baki ɗayansu suka ce: Ku wuce su kamar yadda suka zo, ba tare da faɗin yadda kaifiyyarsu take ba)5.
A lokacin da aka tambayi Rabi’atu bn Abdurrahman - malamin Maliku - Allah Ya yi musu rahama - dangane da al-Istiwa’u (daidaituwar Allah a akan Al-arshi), sai ya ce: al-Istiwa'u aba ce da aka santa, amma yadda take ba za’a iya hankalta ba, saƙo daga Allah yake, isarwa mabayyaniya ce akan Manzo, mu kuma gasgatawa ce a kan mu6. Kuma a lokacin da aka tambayi Imamu Malik - Allah Ya yi masa rahama - dangane da hakan, sai ya ce: (Istiwa'i sanannen abu ce, yadda ya ke kuma ba’a sani ba, imani da hakan wajibi ne, tambaya akan hakan kuma bidi’a ce.)
Sannan ya cewa wanda ya yi tambayar: Ba ni ganinka face mugun mutum! Sai ya yi umarnin a fitar da shi.7. Kuma haƙiƙa an ruwaito wannan ma’anar daga Uwar muminai Ummu Salamah, - Allah Ya yarda da ita -8.
Imam Abu Abdurrahman bn al-Mubarak - Allah Ya yi masa rahama ya ce -:(Muna sanin Ubangijin mu - Maɗaukakin Sarki - da cewar Shi Yana saman samman Sa akan al’arahin Sa nesa da halittun Sa9.
Magaganun manyan malamai a wannan babin yana da yawa sosai, ba zai yi wu akawo duka a wannan lakcar ba, wanda yake son yasan mafi yawa daga wannan, sai ya koma ga abinda malaman sunnah suka rubuta a wannan babin, kamar : Littafin "al-Sunnah", na Abdullahi bn Imam Ahmad, da littafin "al-Tauhid" na babban malami Muhammad bn Khuzaimah, da littafin "al-Sunnah" na Abubakar bn Abu Asim, da amsar da IbnTaimiyya ya bayar ga mutanen Hamah (Hamawiyyah). Shi amsa ce mai girma, mai yawan fa'idodi, - Allah Ya yi masa rahama -, ya yi bayanin aƙidar Ahlussunna wal Jama’ah a fayyace, kuma ya kawo da yawa daga maganganun su, da dalilai na shari'ah da na hankali akan ingancin abinda da yawa daga Ahlussunah suka faɗa, da ɓata abinda masu husumar su suka faɗa.
Haka nan littafin sa mai suna al-Tadmuriyyah; haƙiƙa ya shimfiɗa (bayanin) matsaya, ya kuma bayyana aƙidar Ahlussunnah da dalilanta waɗanda aka cirato da kuma na hankali, ya kuma yi raddi ga waɗanda suka saɓa da abinda yake bayyanar da gaskiya, kuma yana turmushe ƙarya ga dukkan wanda ya yi nazari ga wannan cikin ma'abota ilimi; da kyakkyawan nufi, da kuma kwaɗayin sanin gaskiya. A taƙaice: Ita aƙidar Ahlussunnah wal jama'a a babin sunayen Allah da siffofinSa; cewa su sun tabbatar wa Allah - tsarki ya tabbata a gare Shi - abinda Ya tabbatarwa kanSa a cikin littafinSa, ko kuma ManzonSa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya tabbatar maSa a cikin sunnar sa, tabbatarwa ba tare da kamantawa ba, suka tsarkake Shi - tsarki ya tabbata a gare Shi -, daga barin kamaceceniya da halittarSa, tsarkakewar da ta barranta daga korewa Allah siffah; sai suka rabauta da amincewa daga cin karo da juna. Kuma suka yi aiki da dukkanin dalilai, domin dacewa daga Allah; domin yana daga cikin sunnar Allah - tsarki ya tabbata a gare Shi - ga wanda ya yi ruƙo da gaskiya wacce ya aiko ManzanninSa da ita, ya kuma yi ƙoƙari akan hakan, ya tsarkake niyya wurin neman ta; da Ya datar da shi ga gaskiya, Ya kuma bayyana hujjar sa, kamar yadda Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:
﴿بَلۡ نَقۡذِفُ بِٱلۡحَقِّ عَلَى ٱلۡبَٰطِلِ فَيَدۡمَغُهُۥ فَإِذَا هُوَ زَاهِقٞ...﴾
{Ã'a, Munã jĩfa da gaskiya a kan ƙarya, sai ta darkãke ta, sai ga tã halakakka.} [al-Anbiya:18].
Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:
﴿وَلَا يَأۡتُونَكَ بِمَثَلٍ إِلَّا جِئۡنَٰكَ بِٱلۡحَقِّ وَأَحۡسَنَ تَفۡسِيرًا33﴾
{Kuma bã zã su zo maka da wani misãli ba, fãce Mun je maka da gaskiya da mafi kyau ga fassara.} [al-Furƙan: 33].
Amma wanda ya saɓa wa Ahlussunnah: A cikin abinda suka ƙudirce a babin sunaye da siffofi; to haƙiƙa babu makawa cikin saɓawa dalilan da aka cirato da kuma na hankali; tare tufka da warwara a bayyane a duk abinda zai tabbatar da shi ko ya kore shi. Haƙiƙa al-Hafiz Ibn Kasir - Allah Ya yi masa rahama - a Tafsirin sa shahararre, ya ambaci magana mai kyau a wannan batu, wannan kuwa a zancen sa a daidai faɗin Allah
- Mai girma da ɗaukaka -:
﴿إِنَّ رَبَّكُمُ ٱللَّهُ ٱلَّذِي خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ فِي سِتَّةِ أَيَّامٖ ثُمَّ ٱسۡتَوَىٰ عَلَى ٱلۡعَرۡشِ...﴾
{Lalle ne Ubangijinku Allah ne, wanda Ya halitta sammai da ƙasa a cikin kwãnaki shida, sa'an nan kuma Ya daidaita a kan Al'arshi.} [al-A'araf: 54].
Zai kyautu mu kawo maganar a nan; saboda girman fa'idar ta, sai ya faɗa - Allah Ya yi masa rahama - abinda ya nassanto shi:
Mutane a wannan gaɓar tamu suna da abin cewa da yawa sosai, wannan ba gurin bayanin bane a shimfiɗe, sai a kan wannan matsayar zamu bi mabiya magabata na gari: Malik da al-Auza;i da al-Thauri da al-Lais bn Sa`ad, da al-Shafi`i da Ahmad bn Hambal da Ishaƙ bn Rahuwaihi, dama wasu daga cikin malaman musulmai na da da na yanzu, kuma shine: Shuɗar da su kamar yadda suka zo ba tare da kaifiyya ko kamantawa ko ɓatawa ba, abinda ke a bayyane kuma mai gaggawa a cikin tunanin masu kamantawa to shi abin korewa ne ga Allah, domin Allah wani abu baya kamanceceniya da Shi daga halittarSa haka kuma
﴿...لَيۡسَ كَمِثۡلِهِۦ شَيۡءٞۖ وَهُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡبَصِيرُ﴾
{Wani abu bai zama kamar tamkarSa ba, kuma Shĩ ne Mai ji, Mai gani}, [al-Shura:11]. Bari dai, al’amarin fa kamar yadda manyan malamai suka faɗa ne, daga cikin su akwai Nu’aim bn Hammad al-khuza’i malamin Imam al-Bukhari, ya ce: Wanda ya kamanta Allah da halittarSa to ya kafirta, wanda kuma ya yi musun abinda Allah Ya siffanta kanSa da shi to ya kafirta10, babu kamanceceniya a abinda Allah - Maɗaukakin sarki - Ya siffanta kanSa da shi ko da abinda Manzon Sa ya siffanta Shi da shi. Wanda ya tabbatar wa Allah - Maɗaukakin Sarki - abinda ayoyi fayyatattu da hadisai ingantattu sukazo da shi; a yadda suka dace da girman Allah, ya kuma kore wa Allah dukkanin tawaya; to haƙiƙa ya bi tafarkin shiriya11.
Maganar Ibn Kasir ta ƙare, - Allah Ya yi masa rahama -.
Yana shiga cikin imani da Allah shine: Ƙudircewa cewa imani magana ne da aiki, yana ƙaruwa da ɗa'a kuma yana raguwa da saɓo, kuma ba ya halatta a kafirta wani a cikin musulmai saboda wani laifi da ya yi wanda yake bai kai shirka da kafirci ba; kamar zina, da sata, da cin riba, da shan kayan maye, da saɓawa iyaye da wanin haka daga manyan laifuka, muddin dai bai halatta su ba, saboda faɗin Allah - Mai tsarki da ɗaukaka -:
﴿إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَغۡفِرُ أَن يُشۡرَكَ بِهِۦ وَيَغۡفِرُ مَا دُونَ ذَٰلِكَ لِمَن يَشَآءُ...﴾
{Lalle ne, Allah ba Ya gãfarta a yi shirki da Shi, kuma Yana gãfarta abin da yake bãyan wannan, ga wanda Yake so.} [al-Nisa'a: 48]. Kuma saboda abinda ya tabbata a hadisai mutawatirai daga Ma’aikin Allah, - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, daga cikin su akwai: faɗin sa: "Lalle Allah Yana fitar da wanda ya kasance a zuciyar sa akwai kwatankwacin ƙwayar zarra daga wuta"12.
Asali na biyu
Imani da Mala’iku
Shi kuma yana ƙunsar al'amurra guda biyu:
Hakan yana ƙunsar al'amurra guda biyu: Lamari na farko: Imani da mala’iku a dunƙule; wannan kuwa shine muyi imani da cewa Allah Yana da mala’iku, Ya halicce su domin suyi maSa ɗa'a, Ya kuma siffanta su da cewa:
﴿وَقَالُواْ ٱتَّخَذَ ٱلرَّحۡمَٰنُ وَلَدٗاۗ سُبۡحَٰنَهُۥۚ بَلۡ عِبَادٞ مُّكۡرَمُونَ 26 لَا يَسۡبِقُونَهُۥ بِٱلۡقَوۡلِ وَهُم بِأَمۡرِهِۦ يَعۡمَلُونَ27 يَعۡلَمُ مَا بَيۡنَ أَيۡدِيهِمۡ وَمَا خَلۡفَهُمۡ وَلَا يَشۡفَعُونَ إِلَّا لِمَنِ ٱرۡتَضَىٰ وَهُم مِّنۡ خَشۡيَتِهِۦ مُشۡفِقُونَ28﴾
{Kuma suka ce: "Mai rahama ya riƙi ɗã." Tsarkinsa, ya tabbata! Ã'a, (malã'iku) bãyi ne mãsu daraja,
Bã su gabãtarSa da magana, kuma su da umurninSa suke aiki,
Yanã sanin abin da yake gaba gare su da abin da yake a bãyansu, kuma bã su yin cẽto fãce ga wanda Ya yarda, kuma sũmasu sauna ne sabõda tsõronSa.} [al-Anbiya'u: 26-28].
Su kuma nau’ika ne masu yawa; daga cikin su akwai waɗanda aka wakilta da ɗaukar al-Arshi, daga cikin su kuma akwai masu tsaron aljanna da wuta, kuma daga cikinsu akwai waɗanda aka wakilta domin kiyaye ayyukan bayi. Lamari na biyu: Imani da mala’iku a fayyace, wannan, hakan shine muyi imani da waɗanda Allah da ManzonSa suka faɗa mana sunayan su, kamar Jibrilu wanda aka wakilta shi ga wahayi, da Mika’ilu da aka wakilta ga ruwan sama, da Maliku mai tsaran wuta, da Israfilu da aka wakilta da busa ƙaho. Kamar yadda anbaton su ya zo a hadisai ingantattu, daga cikin su: Akwai abinda ya tabbata a Sahih (na al-Bukhari), daga Nana Aisha - Allah Ya yarda da ita -, lalle Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «An halicci mala'iku daga haske, kuma an halicci aljannu daga bira daga wuta, kuma an halicci (Annabi) Adam daga abinda aka siffanta muku»13. Muslim ne ya fitar da shi a Sahihinsa.
Asali na uku
Imani da littattafai shima yana ƙunsar al'amura guda biyu:
Lamari na farko: Imani da littattafai a dunƙule; hakan kuwa, domin lalle Allah Ya saukar da littattafai ga annabawanSa da ManzanninSa domin bayanin haƙƙinSa, da kira zuwa gare shi, kamar yadda - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:
﴿لَقَدۡ أَرۡسَلۡنَا رُسُلَنَا بِٱلۡبَيِّنَٰتِ وَأَنزَلۡنَا مَعَهُمُ ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡمِيزَانَ لِيَقُومَ ٱلنَّاسُ بِٱلۡقِسۡطِ...﴾
{Haƙĩƙa, lalle Mun aiko Manzannin Mu da hujjõji bayyanannu, kuma Muka saukar da Littãfi da sikẽli tãre da su dõmin mutãne su tsayu da ãdalci.} [al-Hadid: 25]. Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:
﴿كَانَ ٱلنَّاسُ أُمَّةٗ وَٰحِدَةٗ فَبَعَثَ ٱللَّهُ ٱلنَّبِيِّـۧنَ مُبَشِّرِينَ وَمُنذِرِينَ وَأَنزَلَ مَعَهُمُ ٱلۡكِتَٰبَ بِٱلۡحَقِّ لِيَحۡكُمَ بَيۡنَ ٱلنَّاسِ فِيمَا ٱخۡتَلَفُواْ فِيهِ...﴾
{Mutãne sun kasance al'umma guda. Sai Allah Ya aiki annabãwa suna mãsu bãyar da bishãra kuma mãsu gargaɗi; kuma Ya saukar da Littãfi da gaskiya tãre da su dõmin (Littãfin) ya yi hukunci a tsakãnin mutãnen a cikin abin da suka sãɓã wa jũna a cikinsa.} [al-Baƙara: 213].
Lamari na biyu: Imani da littattafai a rarrabe; hakan kuwa, shine muyi imani da waɗanda Allah Ya ambata daga cikin su: Kamar Attaura da Injila da Zabura da Alƙur’ani. Kuma mu ƙudurce cewa Alƙur'ani shi ne mafificin su, kuma cikamakin su, mai rinjaye akan su, mai kuma gasgata su. Shine wanda ya zama wajibi akan dukkan al’umma su bi shi, su kuma yi hukunci da shi; tare da abinda sunnah ta inganta daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -; domin Allah - tsarki ya tabbata a gare Shi -,Ya aiko ManzonSa (Annabi) Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi Manzo zuwa gaba ɗayan mutane da aljanu. Ya kuma saukar masa da Alƙur'ani domin ya yi hukunci da shi a tsakanin su, kuma ya sanya shi waraka a abinda yake cikin zukata, kuma bayani na kowanne abu, kuma shiriya da rahama ga muminai, kamar yadda Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:
﴿وَهَٰذَا كِتَٰبٌ أَنزَلۡنَٰهُ مُبَارَكٞ فَٱتَّبِعُوهُ وَٱتَّقُواْ لَعَلَّكُمۡ تُرۡحَمُونَ155﴾
{Kuma wannan Littãfi ne, Mun saukar da shi, mai albarka ne, sai ku bĩ shi kuma ku yi taƙawa, tsammãninku, anã jin ƙanku.} [al-An'am: 155]. Kuma - tsarki ya tabbatar maSa - Ya ce:
﴿...وَنَزَّلۡنَا عَلَيۡكَ ٱلۡكِتَٰبَ تِبۡيَٰنٗا لِّكُلِّ شَيۡءٖ وَهُدٗى وَرَحۡمَةٗ وَبُشۡرَىٰ لِلۡمُسۡلِمِينَ﴾
{Kuma Mun saussaukar da Littãfi a kanka dõmin yin bãyani ga dukkan kõme da shiriya da rahama da bushãra ga mãsu mĩƙa wuya (Musulmi).} [al- Nahl 89]. Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:
﴿قُلۡ يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ إِنِّي رَسُولُ ٱللَّهِ إِلَيۡكُمۡ جَمِيعًا ٱلَّذِي لَهُۥ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۖ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ يُحۡيِۦ وَيُمِيتُۖ فَـَٔامِنُواْ بِٱللَّهِ وَرَسُولِهِ ٱلنَّبِيِّ ٱلۡأُمِّيِّ ٱلَّذِي يُؤۡمِنُ بِٱللَّهِ وَكَلِمَٰتِهِۦ وَٱتَّبِعُوهُ لَعَلَّكُمۡ تَهۡتَدُونَ158﴾
{Ka ce: "Yã kũ mutãne! Lalle ne nĩ manzon Allah ne zuwa gare ku, gabã ɗaya. (Allah) Wanda Yake Shĩ ne da mulkin sammai da ƙasa; Bãbu wani abin bautawa fãce Shi, Yanã rãyarwa, kuma Yanã matarwa, sai ku yi ĩmãni da Allah da ManzonSa, Annabi, Ummiyyi, wanda yake yin ĩmãni da Allah da kalmominSa; ku bĩ shi, tsammãninku, kunã shiryuwa."} [al-A’araf, 158]. Kuma ayoyi da suka zo da wannan ma’anar suna da yawa.
Asali na huɗu Imani da manzanni
Shima yana ƙunsar al'amurra guda biyu: Lamari na farko: Imani da Manzanni a dunƙule; hakan kuwa shine mu yi imani da cewa Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya aiko Manzanni zuwa ga bayinSa daga cikin su, masu bushara da gargaɗi, kuma masu kira zuwa ga gaskiya, duk wanda ya amsa musu to ya rabauta da dacewa, wanda kuma ya saɓa musu to ya komo da taɓewa da nadama, kuma cikamakin su kuma mafificin su shi ne Annabin mu Muhammad ɗan Abdullahi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, kamar yadda Allah - tsarki ya tabbata a gare Shi - Ya ce:
﴿وَلَقَدۡ بَعَثۡنَا فِي كُلِّ أُمَّةٖ رَّسُولًا أَنِ ٱعۡبُدُواْ ٱللَّهَ وَٱجۡتَنِبُواْ ٱلطَّٰغُوتَ...﴾
{Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun aika a cikin kõwace al'umma da wani Manzo (ya ce): "Ku bauta wa Allah, kuma ku nĩsanci ɗãgũtu."} [al-Nahl: 36]. Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:
﴿رُّسُلٗا مُّبَشِّرِينَ وَمُنذِرِينَ لِئَلَّا يَكُونَ لِلنَّاسِ عَلَى ٱللَّهِ حُجَّةُۢ بَعۡدَ ٱلرُّسُلِ...﴾
{Manzanni mãsu bãyar da bushãra kuma mãsu gargaɗi dõmin kada wata hujja ta kasance ga mutãne a kan Allah bãyan Manzannin.} [al-Nisa'a: 165]. Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:
﴿مَّا كَانَ مُحَمَّدٌ أَبَآ أَحَدٖ مِّن رِّجَالِكُمۡ وَلَٰكِن رَّسُولَ ٱللَّهِ وَخَاتَمَ ٱلنَّبِيِّـۧنَ...﴾
{Muhammadu bai kasance uban kõwa ba daga mazanku, kuma amma shĩ yã kasance Manzon Allah kuma cikon Annabãwa.} [al-Ahzab: 40].
Lamari na biyu: Imani da Manzanni a fayyace, hakan shine muyi imani da wanda Allah - Maɗaukakin Sarki Ya ambata daga cikin su a fayyace kuma a ayyane, ko ambaton sa ya tabbata daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, kamar (Annabi) Nuhu da Hud da Salihu da Ibrahim da wasun su - tsira da amincin Allah su tabbata a gare su - da alayen su da mabiyansu.
Asali na biyar: Imani da ranar lahira
Shi yana ƙunsar:
Imani da dukkanin abinda Allah Ya bada labarin sa da Manzon sa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - na abinda zai kasance bayan mutuwa kamar fitinar ƙabari da azabar sa da kuma ni’imar sa, da kuma abinda zai kasance a ranar lahira na tsorace-tsorace da tsanance-tsanance da siraɗi da awo (na ayyuka) da hisabi da sakamako da yaɗa littattafai tsakanin mutane; akwai wanda zai karɓi littafin sa da hannun sa na dama, akwai kuma wanda zai karɓa da hagu ko kuma daga bayan bayan sa.
Yana shiga cikin wannan kuma: Imani da tafki abin gangarowa ga Annabin mu Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da imani da aljanna da wuta, da ganin muminai ga Ubangijin su - Mai tsarki da ɗaukaka -, da kuma maganar da Zai yi da su, da wanin haka daga abinda yazo a cikin Alƙur'ani mai girma da Sunnah ingantacciya daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -; to ya wajaba ga bawa yayi imani da waɗannan baki ɗaya, ya kuma gasgata su a yadda Allah da Manzon sa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - suka bayyana shi.
Asali na shida: Imani da ƙaddara
Yana ƙunsar al'amurra guda huɗu:
Lamari na farko: Imani da cewa Allah - Maɗaukakin Sarki - haƙiƙa Ya san abinda ya kasance da wanda zai kasance nan gaba, kuma Ya san halayen bayinSa, da arzuƙan su da ajalillikan su da ayyukan su, da wanin haka na sha’anonin su, saboda haka babu wani abinda yake ɓoyuwa ga Allah - Maɗaukakin Sarki - na hakan, kamar yadda - tsarki ya tabbata a gare Shi - Ya ce:
﴿...وَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ بِكُلِّ شَيۡءٍ عَلِيمٞ﴾
{Kuma ku sani, Allah Masani ne ga dukkan komai.} [al-Baƙara: 231]. Kuma (Allah) - Mai girma da ɗaukaka - Ya ce
﴿...لِتَعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ وَأَنَّ ٱللَّهَ قَدۡ أَحَاطَ بِكُلِّ شَيۡءٍ عِلۡمَۢا﴾
{Dõmin ku san lalle Allah Mai ĩkon yi ne akan dukan kõmai, kuma lalle Allah, haƙĩƙa Ya kẽwaye ga dukan kõmai da sani.} [al-Ɗalak: 12].
Lamari na biyu: Imani da cewa lalle Allah Ya rubuta dukkan abinda Ya ƙaddara shi kuma Ya hukunta shi, kamar yadda Allah - Mai tsarki da ɗaukaka - Ya ce:
﴿قَدۡ عَلِمۡنَا مَا تَنقُصُ ٱلۡأَرۡضُ مِنۡهُمۡۖ وَعِندَنَا كِتَٰبٌ حَفِيظُۢ 4﴾
{Lalle ne Mun san abin da ƙasã ke ragẽwa daga gare su, kuma wurinMu akwai wani littãfi mai tsarẽwa.} [Qaf: 4]. Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:
﴿...وَكُلَّ شَيۡءٍ أَحۡصَيۡنَٰهُ فِيٓ إِمَامٖ مُّبِينٖ﴾
{Kuma kõwane abu Mun ƙididdige shi, a cikin babban Littãfi Mabayyani.} [Yaseen: 12]. Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:
﴿أَلَمۡ تَعۡلَمۡ أَنَّ ٱللَّهَ يَعۡلَمُ مَا فِي ٱلسَّمَآءِ وَٱلۡأَرۡضِۚ إِنَّ ذَٰلِكَ فِي كِتَٰبٍۚ إِنَّ ذَٰلِكَ عَلَى ٱللَّهِ يَسِيرٞ70﴾
{Ashe, ba ka sani ba, lalle ne Allah Yanã sanin abin da yake a cikin sama da ƙasa? Lalle ne hakan yanã cikin Littafi lalle wancan ga Allah mai sauƙi ne.} [al- Hajj: 70].
Lamari na uku: Imani da mashi'ar Allah abar zartarwa, abinda Ya so yake kasancewa, wanda kuwa bai so ba, to ba ya kasancewa, kamar yadda Allah - tsarki ya tabbaga a gare Shi -Ya ce:
﴿...إِنَّ ٱللَّهَ يَفۡعَلُ مَا يَشَآءُ﴾
{Lalle ne Allah Yanã aikata abin da Yake so.} [al-Hajj: 18]. Kuma (Allah) - Mai girma da ɗaukaka - Ya ce
﴿إِنَّمَآ أَمۡرُهُۥٓ إِذَآ أَرَادَ شَيۡـًٔا أَن يَقُولَ لَهُۥ كُن فَيَكُونُ82﴾
{UmurninSa idan Yã yi nufin wani abu sai Ya ce masa kawai, "Ka kasance," sai yana kasancewa (kamar yadda Yake nufi).}
. [Yaseen: 82]. Kuma - tsarki ya tabbatar maSa - Ya ce:
﴿وَمَا تَشَآءُونَ إِلَّآ أَن يَشَآءَ ٱللَّهُ رَبُّ ٱلۡعَٰلَمِينَ29﴾
{Kuma bã zã ku so ba sai idan Allah Ubangijin halitta Yã yarda.} [al-Takweer: 29].
Lamari na huɗu: Imani da halittar Allah Maɗaukakin Sarki ga dukkanin samammu; babu wani Mahalicci in ba Shi ba, kuma babu wani Ubangiji idan ba Shi ba, kamar yadda - tsarki ya tabbata a gare Shi - Ya ce:
﴿ٱللَّهُ خَٰلِقُ كُلِّ شَيۡءٖۖ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ وَكِيلٞ62﴾
{Allah ne Mahaliccin dukkan kõme, kuma Shĩ ne Wakĩli a kan kõme.} [al-Zumar: 62]. Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:
﴿يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ ٱذۡكُرُواْ نِعۡمَتَ ٱللَّهِ عَلَيۡكُمۡۚ هَلۡ مِنۡ خَٰلِقٍ غَيۡرُ ٱللَّهِ يَرۡزُقُكُم مِّنَ ٱلسَّمَآءِ وَٱلۡأَرۡضِۚ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۖ فَأَنَّىٰ تُؤۡفَكُونَ3﴾
{Yã kũ mutãne! Ku tuna ni'imar Allah a kanku. Shin, akwai wani mai halitta wanin Allah da zai azurta ku daga sama da, ƙasã? Bãbu wani abin bautãwa, fãce Shi. To, yãya ake karkatar da ku?.} [Faɗir: 3].
To shi imani da ƙaddara yana ƙunsar waɗannan lamura ne guda huɗu baki ɗayan su, kamar yadda yake shi ne aƙidar Ahlussunnah wal Jama’a; saɓanin waɗanda suka musunta wasu daga cikin waɗannan daga ‘yan bidi’a.
Yana cikin lamura masu muhimmanci a ingantacciyar aƙidah wacce Ahlussunnah suke ƙudirce ta: So saboda Allah, da kuma ƙi saboda Allah, da jiɓinta saboda Allah, da ƙiyayya saboda Allah, wannan ita ce: Aƙidar Alwala’u wal Bara’u, kuma ita tana cikin imani da Allah - Maɗaukakin Sarki -.
Shi mumini yana son muminai yana kuma jiɓintar su, yana kuma ƙin kafirai yana adawa da su, kuma waɗanda suke a kan gaba a cikin muminai a wannan al’ummar su ne sahabban Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, kamar yadda yake a tabbace a wurin Ahlussunnah wal Jama’a; domin su (Ahlussunnah) suna son su (sahabbai) kuma suna jiɓintar su, kuma suna ƙudirce cewa sune mafi alherin mutane bayan Annabawa, saboda faɗin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: «Mafificin mutane (su ne) ‘yan zamani na, sannan waɗanda suka biyo su, sannan waɗanda suka biyo su»14. Bukhari Da Muslim sun haɗu akan ingancinsa,
Suna kuma ƙudurcewa lallai mafificin su: Abubakar al-Siddiƙ, sannan Umar al-Faruƙ, sannan Usman ma’abocin haske biyu, sannan Aliyu yardajje, - Allah Ya yarda da su baki ɗaya -, sannan bayan su sauran cikon goma, sannan sauran sahabbai - Allah Ya yarda da su baki ɗaya -, kuma suna kamewa daga abinda ya gudana na saɓani a tsakaninsu - wato sahabban -, kuma suna ƙudirce cewa su akan hakan masu ijtihadi ne, wanda ya yi daidai yana da lada biyu, wanda kuma ya kuskure yana lada ɗaya.
Suna kuma son Ahlul Baitin Ma’aikin Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -,waɗanda suka yi imani da shi, kuma suna jiɓintar su, kuma suna jiɓintar matan Ma’aikin Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - waɗanda sune uwayen muminai, kuma suna nema musu yardar Allah baki ɗayan su. Kuma suna barranta daga tsarin ‘yan Shi’a Rafidawa waɗanda suke ƙin sahabban Ma’aikin Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, suna zagin su, suna wuce iyaka akan Ahlul Baiti, suna ɗaga su sama da matsayin su wanda Allah -Mai girma da ɗaukaka -Ya yi musu, kamar yadda suke barranta daga tafarkin Nasibawa waɗanda suke cutar da Ahlul Baiti da magana ko aiki.
To wannan abin da muka ambata: Baki ɗayan sa yana shiga cikin ingantacciyar aƙidah, wacce Allah Ya aiko Manzon sa (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da ita, kuma ita ce aƙidar da ya wajaba a ƙudirce ta a yi riƙo da ita, a kuma tsayu a kanta, a kuma kiyayi abinda ya saɓa mata, ita ce kuma aƙidar tawagar da ta tsira ta Ahlussunna wal Jama’a, wacce Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya faɗa dangane da ita: «Wata tawaga ba zata gushe ba a cikin al’umma ta suna masu taimako a kan gaskiya, wanda ya taɓar da su ba zai cutar da su ba, har sai al’amarin Allah ya zo alhali su suna a kan hakan»15. A cikin wata riwayar: «Wata tawaga daga cikin al’umma ta ba zata gushe ba akan gaskiya tana abar taimakawa»16. Kuma - tsira da aminci su tabbata a gare shi - ya ce: «Yahudawa sun kasu kashi saba’in da ɗaya, Nasara kuma sun kasu kashi saba’in da biyu, kuma da sannu wannan al’ummar zata rabu kashi saba’in da uku, duka suna wuta sai kashi ɗaya, sai sahabbai suka ce: Wacce ce ita ya Ma’aikin Allah? Sai ya ce: Wanda ya kasance akan irin abinda na kasance akan sa ni da sahabbai na»17.
AƘIDUN DA SUKE KISHIYANTAR INGANTACCIYAR AƘIDA
Waɗanda suka karkacewa wannan aƙidar, masu tafiya akan saɓanin ta, su kuma kashi-kashi ne; daga cikinsu: Akwai masu bautar gumaka da Mala’iku da waliyyai da aljanu da bishiyoyi da duwatsu da wasun su. To waɗan nan ba su amsa kiran Manzanni ba, bari dai sun saɓa musu sun nuna musu taurin kai, kamar yadda Ƙuraishawa suka yi da kuma dangogin Larabawa dangane da Annabin mu Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -; sun kasance suna roƙon abubuwan bautar su, don biyan buƙatun su, da kuma warakar da marasa lafiyar su, da taimako akan maƙiya, kuma suna yi musu yanka, suna yi musu alwashi, lokacin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, ya yi musu inkarin hakan, ya umarce su da tsarkake ibada domin Allah Shi kaɗai, sai suka ga hakan wani baƙon abu, suka yi inkarin sa, suka ce:
﴿أَجَعَلَ ٱلۡأٓلِهَةَ إِلَٰهٗا وَٰحِدًاۖ إِنَّ هَٰذَا لَشَيۡءٌ عُجَابٞ5﴾
{Shin, yã sanya gumãka duka su zama abin bautawa guda? Lalle wannan, haƙĩƙa, abu ne mai ban mãmaki!} [Saad: 5].
(Annabi) - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, bai gushe ba yana kiran su izuwa ga Allah, kuma yana gargaɗar da su daga shirka, yana yi musu bayanin haƙiƙanin abinda ake kiran su zuwa gare shi; har Allah Ya shiryar da wanda Ya shiryar, sannan bayan haka suka shiga addinin Allah jama’a jama’a, sai Addinin Allah ya ɗaukaka akan sauran addinai bayan kira mai saduwa da aka dinga yi, da kuma jihadi mai tsawo tun daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da kuma sahabban sa - Allah Ya yarda da su - da masu bin su da kyautatawa. Sannan lamura suka canza, jahilci ya rinjayi mafi yawan halittu; sai da yawa suka koma addinin Jahilyyah, ta hanyar wuce iyaka ga Annabawa da waliyyai, da roƙon su da kuma neman agajin su, da wanin haka na nau’ikan shirka, basu ma san mece ce ma’anar: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah ba; kamar yadda kafiran Larabawa suka sani, ga Allah muke neman taimako.
Wannan shirkar ba ta gushe ba tana watsuwa a cikin mutane har zuwa wannan lokacin na mu; ta sanadiyyar rinjayar jahilci da kuma nesa da zamanin Annabta.
Shubuhar waɗannan ‘yan bayan ita ce shubuhar mutanan farko, ita ce faɗin su:
﴿...هَٰٓؤُلَآءِ شُفَعَٰٓؤُنَا عِندَ ٱللَّهِ...﴾
{Waɗannan ne macẽtanmu a wurin Allah}. [Yunus: 18], Da kuma faɗin su:
﴿...مَا نَعۡبُدُهُمۡ إِلَّا لِيُقَرِّبُونَآ إِلَى ٱللَّهِ زُلۡفَىٰٓ...﴾
{"Ba mu bauta musu ba fãce dõmin su kusantar da mu zuwa ga Allah, kusantar daraja."} [al-Zumar: 3] Kuma haƙiƙa Allah Ya ɓata wannan shubuhar, Ya yi bayanin duk wanda aka bautawa ko waye, to haƙiƙa yayi wa Allah shirka da shi, kuma ya kafirta, kamar yadda Allah - Maɗaukakin Sarki -Ya ce:
﴿وَيَعۡبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ مَا لَا يَضُرُّهُمۡ وَلَا يَنفَعُهُمۡ وَيَقُولُونَ هَٰٓؤُلَآءِ شُفَعَٰٓؤُنَا عِندَ ٱللَّهِ...﴾
{Kuma sunã bautã wa, baicin Allah, abin da bã ya cũtar dasu kuma bã ya amfãninsu, kuma sunã cẽwa: "Waɗannan ne macẽtanmu a wurin Allah".} [Yunus: 18]. Sai (Allah) - tsarki ya tabbata a gare Shi - Ya mayar musu da martani da faɗin Sa:
﴿قُلۡ أَتُنَبِّـُٔونَ ٱللَّهَ بِمَا لَا يَعۡلَمُ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَلَا فِي ٱلۡأَرۡضِۚ سُبۡحَٰنَهُۥ وَتَعَٰلَىٰ عَمَّا يُشۡرِكُونَ18﴾
{Ka ce: "Shin, kunã bai wa Allah lãbãri ne, ga abin da bai sani ba, a cikin sammai ko a cikin ƙasa? TsarkinSa ya tabbata kuma Yã ɗaukaka daga gabin da duk suke yin shirki da Shi."} [Yunus: 18].
Sai Allah a cikin wannan ayar Ya bayyana cewa: Lalle bautawa wanin Sa daga Annabawa da waliyyai da wasun su, shi ne babbar shirka, ko da masu yin ta sun kirata da wanin hakan, Allah
- Maɗaukakin Sarki - Ya ce:
﴿...وَٱلَّذِينَ ٱتَّخَذُواْ مِن دُونِهِۦٓ أَوۡلِيَآءَ مَا نَعۡبُدُهُمۡ إِلَّا لِيُقَرِّبُونَآ إِلَى ٱللَّهِ زُلۡفَىٰٓ...﴾
{Kuma waɗanda suka riƙi waɗansu majiɓinta waɗanda bã Shĩ ba Allah ne Mai tsaro a kansu, kuma kai, bã wakili ne a kansu ba.} [al-Zumar: 3]. Sannan (Allah) - Maɗaukakin Sarki - Ya yi musu raddi da faɗin Sa:
﴿...إِنَّ ٱللَّهَ يَحۡكُمُ بَيۡنَهُمۡ فِي مَا هُمۡ فِيهِ يَخۡتَلِفُونَۗ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَهۡدِي مَنۡ هُوَ كَٰذِبٞ كَفَّارٞ﴾
{Lalle Allah nã yin hukunci a tsakãninsu ga abin da suka zama sunã sãɓãwa a cikinsa. Lalle Allah ba Ya shiryar da wanda yake mai ƙarya, mai kãfirci} [al-Zumar: 3].
Sai Allah - tsarki ya tabbatar a gare Shi -,Ya yi bayani akan bautar su ga wani wanda ba Shi ba ta hanyar addu’a, da tsoro da kwaɗayi, da makamantan haka; kafircewa Allah ne - tsarki ya tabbata a gare Shi -, kuma (Allah) Ya ƙaryata su akan maganar su: Lalle uwayengijin su suna kusantar da su izuwa gare Shi kusasntarwa.
Akwai daga cikin aƙidu na kafirci waɗanda suke kishiyantar ingantacciyar aƙidah, kuma masu saɓawa da abinda Manzanni
- tsira da amincin Allah su tabbata agare su - suka zo da shi: abinda mulhidai suke ƙudircewa a wannan zamanin cikin mabiya Marx da Lenin da wasun su, cikin masu kira zuwa ga ilhadi da kafirci, daidai ne an kira hakan da sunan Ishtirakiyya ne ko Shuyu'iyyah ko Ba’athiyyah ko ma wanin haka na sunaye, domin yana cikin tushan waɗannan mulhidan cewa: Babu Allah, kuma rayuwa Maddah ce kawai (maƙunshin wanzuwa),
Yana daga cikin Usul ɗin su kuma: Musun tashi bayan mutuwa, da musun akwai aljanna da wuta, da kafircewa addinai baki ɗayan su, wanda ya yi nazarin littattafan su ya kuma karanta abinda suke akan sa, zai sani, sani na yaƙini, kuma babu shakka wannan aƙidar (ta su) tana kishiyantar dukkanin addinai da suka zo daga sama, kuma za ta kai masu ita zuwa ga mafi munin makoma a duniya da lahira.
Daga cikin waɗannan aƙidu masu kishiyantar gaskiya: Abinda wasu daga sufaye suke ƙudurcewa cewa wasu daga cikin waɗanda suke cewa waliyyai suna tarayya da Allah a jujjuya lamurra, kuma suna tasarrufi a sha’anin talikai, ana kiran su Khuɗubai da Autadu da Agwasu, da wanin haka na sunayan da suka ƙage su ga abubuwan bautar su, wannan kuwa shirka ce a Rububiyyah, kuma tana cikin mafi munin nau’ikan shirka ga Allah - Maɗaukakin Sarki -.
Wanda ya yi la’akari a shirkar mutanen farko na Jahilyyah, ya kuma kwatanta ta da shirkar da take yaɗuwa tsakanin ‘yan baya; zai samu lalle shirkar ‘yan baya ita ce mafi girman shirka kuma mafi muni, bayanin haka kuwa shi ne kamar haka: Lalle kafiran larabawa a zamanin Jahilyyah sun banbanta da abubuwa biyu: Lamari na farko: Su ba su kasance suna shirka da Allah ba a Rububiyyah (ayyukan Allah), kaɗai suna shirkar su a ibada ne, sun kasance sun yi i'itirafin Rububiyyah (ayyukan Allah) ga Allah - Mai girma da ɗaukaka - Shi kaɗai, kamar yadda Allah - Mai tsarki da ɗaukaka - Ya ce:
﴿وَلَئِن سَأَلۡتَهُم مَّنۡ خَلَقَهُمۡ لَيَقُولُنَّ ٱللَّهُ...﴾
{Kuma lalle idan ka tambaye su: "Wãne ne ya halitta su?" Lalle ne zã su ce Allah ne.} [al-Zukhruf: 87]. Kuma - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:
﴿قُلۡ مَن يَرۡزُقُكُم مِّنَ ٱلسَّمَآءِ وَٱلۡأَرۡضِ أَمَّن يَمۡلِكُ ٱلسَّمۡعَ وَٱلۡأَبۡصَٰرَ وَمَن يُخۡرِجُ ٱلۡحَيَّ مِنَ ٱلۡمَيِّتِ وَيُخۡرِجُ ٱلۡمَيِّتَ مِنَ ٱلۡحَيِّ وَمَن يُدَبِّرُ ٱلۡأَمۡرَۚ فَسَيَقُولُونَ ٱللَّهُۚ فَقُلۡ أَفَلَا تَتَّقُونَ31﴾
{Ka ce: "Wãne ne Yake azurtã ku daga sama da ƙasa? Shin kõ kuma Wãne ne Yake mallakar jĩ da ganĩ, kuma Wãne ne Yake fitar da mai rai daga mamaci, kuma Ya fitar da mamaci daga mai rai, Kuma Wãne ne Yake shirya al'amari?" To, zã su ce: "Allah ne." To, ka ce: "Shin fa, bã zã ku yi taƙawa ba?".} [Yunus: 31]. Ayoyi da suka zo a wannan ma’anar suna da yawa sosai.
Lamari na biyu: Cewa shirkar su a ibadah ba ta kasance dawwamammiya ba, kawai tana kasancewa ne a lokacin yalwa, amma a lokacin tsanani to su sun kasance suna tsarkake ibada ga Allah, kamar yadda Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:
﴿فَإِذَا رَكِبُواْ فِي ٱلۡفُلۡكِ دَعَوُاْ ٱللَّهَ مُخۡلِصِينَ لَهُ ٱلدِّينَ فَلَمَّا نَجَّىٰهُمۡ إِلَى ٱلۡبَرِّ إِذَا هُمۡ يُشۡرِكُونَ65﴾
{To, a lõkacin da suka shiga cikin jirgin ruwa, sun kirãyi Allah sunã mãsu tsarkake addini a gare shi, to, a lõkacin da Ya tsĩrar da su zuwa ga tudun ƙasã, sai gã su sunã shirki.} [al-Ankabut: 65].
Amma mushirikai ‘yan baya, to su sun ƙara akan mutanan farko ta fuskoki biyu: Fuska ta farko: Yadda wasun su suke shirka a cikin Rububiyyah. Fuska ta biyu: Shirkar su a lokacin yalwa da tsanani, kamar yadda wanda ya cuɗanya da su kuma ya karanci halayen su zai san hakan, ya ga kuma irin abinda suke aikatawa a ƙabarin al-Husaini da al-Badawi da wasun su a Masar, da ƙabarin al-Aidurus a Adan, da al-Hadi a Yaman da Ibn Arabi a Sham da Sheikh Abdulƙadir al-Jilani a Iraƙ da sauran su na ƙaburbura shahararru waɗanda jama’a suka wuce iyaka akansu, suka juyar da da yawa daga haƙƙin Allah - Maɗaukakin Sarki - zuwa can. Da ƙyar ka sami mai yi musu inkari akan hakan, ya yi musu bayanin haƙiƙanin Tauhidin da Allah Ya aiko AnnabinSa Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, da Manzanni da suka zo kafin shi - tsira da aminci su tabbata gare su -, to fa lalle mu ga Allah muke kuma gare Shi zamu koma.
Akwai daga cikin aƙidun da suke kishiyantar ingantacciyar aƙidah a babin sunayen Allah da siffofinSa: Akidun ‘yan bidi’a, irin su Jahamiyyah da Mu’utazilah da duk wanda ya bi hanyar su a kore siffofin Allah - Mai girma da ɗaukaka -, da soke abinda aka ambata ga Allah - tsarki ya tabbata a gare Shi - na siffofin cika, da kuma siffanta shi (Allah) da siffofin abubuwan da babu su da daskararrun abubuwa da ma abubuwan da ba za su yiwu ba. Allah Ya ɗaukaka daga maganar su, ɗaukaka mai girma.
Yana kuma shiga ƙarƙashin wannan: Wanda ya kore sashen siffofin da kuma tabbatar da wasu sashen; kamar yadda wannan ita ce aƙidar Asha’irah, kuma waɗannan abinda suka tabbatar da shi zai lazimce su, na siffofi irin wanda suka gujewa akan siffofin da suka kore, suka yi tawilin dalilan su, sai suka saɓa da waɗannan dalilan na ruwaya da hankali, suka yi tufka da warwara bayyananne a cikin hakan.
Amma su Ahlussunnah wal Jama’a, to haƙiƙa sun tabbatarwa Allah - Maɗaukakin Sarki - abinda Ya tabbatar wa kanSa ko ManzonSa (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya tabbatar maSa na sunaye da siffofi, ta fuskar cika, kuma suka tsarkake shi daga barin kamanceceniya da halittarSa, tsarkakewa da ta barranta daga birbishin sokewa, sai suka yi aiki da dalilan baki ɗaya, ba su jirkita ba, kuma ba su soke ba, sun kuɓuta daga tufka da warwara wanda wasun su suka afka cikin sa, - kamar yadda bayani akan hakan ya gabata -.
Wannan kuwa ita ce hanyar tsira, da kuma rabauta a duniya lahira, kuma shi ne tafarki miƙaƙƙe wanda magabata na ƙwarai na wannan al'umma suka bi shi, kuma babu abinda zai gyara ƙarshen wannan al’ummar sai abinda ya gyara na farkon ta, wanda yake shine bin littafin Allah da sunnar ManzonSa da kuma barin abinda ya saɓa musu. Muna roƙon Allah - Maɗaukakin Sarki -, Ya mayar da wannan al’ummar kan shiriyar ta, Ya kuma yawaita masu kira zuwa shiriya a cikin ta, Ya datar da shugabannin ta da malaman ta akan yaƙar shirka da yin hukunci akan ta, da kuma tsawatarwa daga (bin) hanyoyin ta… lalle Shi Mai ji ne kuma Makusanci. Allah shi ne Majiɓincin datarwa, kuma Ya isar mana, kuma madalla da wakili, kuma babu dabara babu ƙarfi face da (taimakon) Sa. Allah Ya yi daɗi tsira ga bawanSa kuma ManzonSa, Annabin mu Muhammad da alayen sa da sahabban sa.
***
Bukhari ne ya fitar da shi (2856), da Muslim (30).
Lālaka'i ne ya fitar da shi a Sharhu Usul al-I’itiƙad, (735), da Ibnu Abdul Barr a Jami’i al-Ulum wa fadlihi (1801), saidai da lafazin hadisan maimakon ayoyin siffofin, kuma lafazin sa shine: “Ku ruwaito waɗannan hadisan kamar yanda suka zo, kada ku yi jayayya akan su”.
Al-Baihaƙi ne ya ruwaito shi a Al’asma’u Wal Sifāt (865), Ibn Taimiya ya Inganta isnadin sa a cikin Hamawiyya (shafi na 269), al-Zahabi ya ce a (littafin) al’Ard (2/223), maruwaitan sa shuwagabanni ne, amintattu ne.
Al-Lalaka’i ne ya fitar da shi a cikin Sharhu Usul al-I'itiƙad I(930), da al-Baihaƙi a cikin al’Asmau Was Sifat, (955).
Al- Lalaka’i ne ya fitar da shi a cikin Sharhu Usulil I'itiƙad (665), da al-Baihaƙi a cikin al’Asma'u Was Sifat, (868).
Al-Lalaka'i ne ya fitar da shi a cikin Sharhu Usulil I'itiƙad (664), da Abu Nu’aim a cikin Hilyatul Auliya'u (6/325), da al-Baihaƙi a cikin al’Asma'u Was Sifat (867).
Al-Muzakki ya fitar da shi a cikin al’Muzakkiyat (29), da Ibn Baɗɗah a cikin al’Ibanah (120), da al-Lalaka’i a cikin Sharhu Usul al-I'itiƙad (663).
Al-Darimi ne ya fitar da shi a cikin al-Raddu alal Jahmiyyah (67), da al-Baihaƙi a cikin al’Asma'u Was Sifat (903).
Al-Zahabi ne ya ruwaito shi a cikin al’Uluwwu (464), kuma Albani ya ce a cikin Mukhtasarul Uluwwu (shafi na: 184), wannan isnadin ingantacce ne, kuma maruwaitan sa amintattu ne sanannu.
Tafsir Ibn Kathir (3/426 ,427).
. Bukhari ne ya fitar da shi (22), daga hadisin Abu Sa’id al-Khudri - Allah Ya yarda da shi -.
Muslim ne ya fitar da shi (2996), daga hadisin Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita -.
Bukhari ne ya fitar da shi (3651), da Muslim (2533), daga hadisin Abdullahi ɗan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi -.
Muslim ne ya fitar da shi (1920), daga hadisin Thauban, - Allah Ya yarda da shi -.
Ibn Majah ne ya fitar da shi (3952), daga hadisin Thauban, - Allah Ya yarda da shi -, kuma Ibn Hibban ya inganta shi (6714), da al-Hakim (8653).
Tirmizi ne ya fitar da shi (2641), daga hadisin Abdullahi ɗan Amr - Allah Ya yarda da shi -, al-Munawi ya ce a cikin Faidhul ƙadir (5/347): "A cikin sa akwai Abdurrahman ɗan Ziyad al-Ifriƙi, al-Zahabi ya ce: Sun raunana shi". Kuma Albani ya inganta shi a cikin Sahihul Jami’i (5343).
Muslim ne ya fitar da shi (8).