دَفْنُ المَوتَى فِي المَسَاجِدِ
BINNE MATATTU A CIKIN MASALLATAI
لِسَمَاحَةِ الشَّيْخِ العَلَّامَةِ
عَبْدِ العَزِيزِ بْنِ عَبْدِ اللهِ بْنِ بَازٍ
رَحِمَهُ اللهُ
Wallafar: Babban Malami
AbdulAzeez Bin Abdullahi Bin Baaz
Allah Yayi masa rahama
بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ
SAƘO NA GOMA SHA ƊAYA:
Binne matattu a cikin masallatai
Da sunan Alah, dukkan godiya ta tabbata ga Allah, tsira da amincin Allah su tabbata ga manzon Allah, da alayansa da duk wanda ya yi koyi da shiriyarsa. Bayan haka:
Haƙiƙa na gani a Jaridar Khartoum da aka buga a 17/4/1415 bayan hijira, sai na samu a cikinta an buga wani bayani game da binne Mallam Muhammad al-Hassan al-Idrisi a kusa da mahaifinsa a cikin masallacinsu a birnin Omdurman… izuwa ƙarshe.
Saboda abinda Allah Ya wajabta na yin nasiha ga musulmai da bayanin hana mummunan aiki, na ga dacewar in faɗakar akan binne mamata a cikin masallatai abune da bai halatta ba, kai yana ma cikin hanyoyin shirka, yana kuma cikin ayyukan Yahudawa da Nasara, waɗanda Allah Ya aibata su a kansu, kuma manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya la’ance su, kamar yadda yake a cikin Bukhari da Muslim daga Nana Aisha - Allah Ya yarda da ita - daga annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - cewa shi ya ce: «Allah Ya tsinewa Yahudawa da Nasara, sun riƙi ƙaburburan Annabawansu masallatai», Ya zo cikin Sahihin Muslim daga Jundub ɗan Abdullahi daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ku Saurara lallai cewa waɗanda suka gabace ku sun kasance suna riƙar ƙaburburan annabawansu da mutanen kirkinsu masallatai, ku saurara kada ku riƙi ƙaburbura masallatai, lallai ni na hanaku yin hakan". Hadisai da suka zo da wannan ma’anar suna da yawa.
Abinda yake wajibi akan musulmai a kowanne wuri- shugabanni da mabiya-: Suji tsoron Allah su kuma kiyayi abinda aka hana, su binne mamatansu a wajan masallaci (ba a ciki ba) kamar yadda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da sahabbansa - Allah Ya yarda da su - suka kasance suna binne mamatansu a wajan masallaci, haka nan waɗanda suka biyo su da kyautatawa.
Amma samun ƙabarin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da sahabbansa biyu Abubakar da Umar - Allah Ya yarda da su - a cikin masallacinsa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ba zai zama dalili na a binne mamata a cikin masallatai ba; domin shi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - an binne shi ne a ɗakin Nana Aisha - Allah Ya yarda da ita-, sannan aka binne sahabbansa biyu tare da shi, a lokacin da Walid ɗan AbdulMalik ya faɗaɗa masallacin, sai ya shigar da ɗakin a cikinsa a farkon shekara ta ɗari daga hijira, kuma malamai a lokacin sunyi masa inkarin hakan, sai dai shi ba ya ganin hakan zai hana faɗaɗawar, kuma al’amarin a fili yake babu wata shubuha a cikinsa.
Da wannan ne, zai bayyana ga kowanne musulmi, cewa shi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da sahabbansa biyu - Allah Ya yarda da su - ba’a binne su a cikin masallaci ba, kuma shigar da su da aka yi saboda faɗaɗawar masallacin ba hujja ba ce akan halaccin binne mamata a masallatai; domin su ba a cikin masallacin suke ba, kawai su suna cikin ɗakinsa ne - tsira da aminci su tabbata a gare shi-, kuma aikin Walid bazai inganta ya zama hujja ga kowa a kan hakan ba, kawai hujja tana cikin Alƙur’ani ne da hadisi da ijima’in magabata al'umma (na ƙwarai) - Allah Ya yarda da su -, Ya kuma sanyamu cikin mabiyansu da kyautatawa.
Don nasiha da kuɓutar da wuyaye an rubuta shi da tacewa a: 14/5/1415 bayan Hijira.
Allah Shi ne majiɓincin datarwa. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabin mu Muhammad, da alayansa da sahabban sa, da mabiyan su da kyautatawa.
***