من خلق الكون؟ ومن خلقني؟ ولماذا؟ (هوسا)

كتاب "من خلق الكون؟ ومن خلقني، ولماذا؟" يناقش أصل وجود الكون والإنسان، مؤكدًا أن الكون لم يأتِ بالصدفة أو من العدم، بل له خالق عظيم هو الله، الذي وضع قوانين دقيقة تحكم الحياة والكون. يوضح الكتاب صفات الله وأهمية الإيمان بالرسل والكتب السماوية، ويؤكد أن الإسلام هو الدين الحق الذي جمع رسالات الأنبياء، داعيًا للإيمان به لتحقيق السعادة الحقيقية في الدنيا والآخرة.

  • earth Harshe
    (هوسا)
  • earth Wallafar:
    اللجنة العلمية برئاسة الشؤون الدينية بالمسجد الحرام والمسجد النبوي
PHPWord

 

 

مَنْ خَلَقَ الكَونَ؟ وَمَنْ خَلَقَنِي؟ وَلِمَاذَا؟

 

 

WA YA HALICCI HALITTU? WA YA HALICCE NI ? KUMA SABODA ME ?

 

 

اللَّجْنَةُ العِلْمِيَّةُ

بِرِئَاسَةِ الشُّؤُونِ الدِّينِيَّةِ بِالمَسْجِدِ الحَرَامِ وَالمَسْجِدِ النَّبَوِيِّ

 

Kwamitin ilimi a jagorancin harkokin Addini a Masallacin Harami da Masallacin Annabi

 


بِسْمِ اللهِ الرَّحمَنِ الرَّحِيمِ

Wa Ya halicci halittu? wa Ya halicce ni ? kuma saboda me?

Kwamitin ilimi da jagorancin harkokin Addini a Masallacin Harami, da Masallacin Annabi

Shin ina kan hanya ta daidai?

Wa ya halicci sammai da ƙasa da abinda ke tsakanin su na halittu masu girma waɗanda ba’a iya gane yawansu?

Wa yaƙera wannan gwanannan tsarin a sama ko a ƙasa ?

Wa Ya halicci mutum ya kuma ba shi ji da gani da hankali? Ya sanya shi mai iko akan tsururutar wasu ilimai da gane haƙiƙanin abubuwa?

Wa Ya ƙagi wannan gwananniyar ƙira a gaɓɓan jikinka, Ya kuma surantaka sai Ya kyautata halittar ta ka?

Kayi la’akari da halittar halittu rayayyu a banbancin nau’ukan su, wa Ya ƙage su a wannan kyawun da ba shi da iyaka?

Ta yaya wannan kasantacce mai girma yake tsaruwa kuma yake tabbatuwa tare da ƙa’idojin sa, waɗanda suke kiyaye shi, kiyaye wa ta ƙwarewa tsawon waɗannan shekarun?

Wa Ya sanya waɗannan tsare-tsaren suke tafiyar da wannan halittar (rayuwa da mutuwa, bibikon rayuwa, dare da yini, da canjin lokuta …

Shin wannan halittar ita ta yi kanta? Koko ta samu ne daga rashi? Ko kuma kwatsam aka sameta?

Allah - Maɗaukakin sarki - Yana cewa:

﴿‌أَمۡ خُلِقُواْ مِنۡ غَيۡرِ شَيۡءٍ أَمۡ هُمُ ٱلۡخَٰلِقُونَ٣٥ أَمۡ خَلَقُواْ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَۚ بَل لَّا يُوقِنُونَ36﴾

{Shin, an halitta su ne bã daga kõme ba, kõ kuwa sũ ne mãsu yin halitta(35)

Shin, sun halitta sammai da ƙasa ne? Ã'a ba su dai yi ĩmãnin yaƙĩni ba}. {al-Ɗur: 35-36].

Idan ba mu halicci kammu ba, kuma ba zai taɓa kasancewa a ce mun zo ne daga babu ko kwatsam, to dole abinda yake gaskiya da ba kokonto a cikinta: Wannan halittar dole ne tana da Mahalicci Mai girma Mai iko, domin ba zai yiwu wannan duniyar ta halicci kanta ba, ko ta zo daga babu ko kuma kwatsam ba.

Saboda me mutum yake yin imani da abubuwan da ba ya ganinsu, kamar: (Tunani hankali, rai, ji a jika, da so.) ashe ba saboda yana ganin alomominsu ba ne? To tayaya mutum zai yi musun samuwar Mahaliccin waɗannan abubuwan masu girma, alhali yana ganin alamomi na halittarSa da aikinSa da kuma rahamarSa?

Babu mutumin da zai yarda a ce da shi: Ai wannan gidan kawai ya samu ne ba tare da wani ne ya gina shi ba. Ko a ce da shi: Ai babu ita ce ta samar da wannan gidan!. To, ta yaya wasu daga cikin mutane suke gasgata wanda yake cewa: Wannan duniyar mai girma ta zo ne ba tare da Mahalicci ba?. Ta yaya mai hankali zai yarda ace da shi: Wannan ginin (na sama da ƙasa) wanda ke cike da ƙwarewa ya samu ne haka kawai?

Duk wannan yana kaimu ne zuwa ga sakamako guda ɗaya cewa: Wannan duniyar (halittar) tana da Ubangiji Mai girma Mai iko da Yake kula da su, kuma Shi ne kaɗai Ya cancanci bauta, kuma duk abinda ake bautawa komabayan Shi to bautar ɓatacciya ce kuma shi bai cancanci a bauta masa ba.

Ubangiji Mahalicci Mai girma.

Akwai wani Ubangiji Mahalicci guda ɗaya, Shi ne Mamallaki Mai jujjuya lamura Mai azurtawa, wanda Yake rayawa Yake kashewa. Shi ne wanda Ya halllici ƙasa, Ya kuma sawwaƙeta, Ya sanyata daidai da halittunSa. Shi ne wanda Ya halicci sama da abinda yake cikinta na halittu masu girma. Ya sanya wa rana da wata da dare da yini wannan nagartaccan tsarin, wanda yake nuni a bisa girman Ubangijinsa.

Shi ne wanda Ya hore mana iska, wacce babu rayuwa a garemu idan babu ita, Shi ne wanda Yake saukar mana da ruwa, kuma Ya hore mana tekuna da ƙoramu. Shi ne wanda Yake ciyar da mu, Yake karemu alhali mu muna tayi a cikin mahaifaNmu, ba tare da muna da wani ƙarfi ba, Shi ne wanda Yake tafiyar da jini a cikin jijiyoyin mu, tun daga haihuwar mu har zuwa mutuwarmu.

Wannan Ubangijin Mahalicci Mai azirtawa, Shi ne Allah - tsarki da ɗaukaka sun tabbatar masa -

Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce:

﴿إِنَّ رَبَّكُمُ ٱللَّهُ ٱلَّذِي خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ فِي سِتَّةِ أَيَّامٖ ثُمَّ ٱسۡتَوَىٰ عَلَى ٱلۡعَرۡشِۖ يُغۡشِي ٱلَّيۡلَ ٱلنَّهَارَ يَطۡلُبُهُۥ حَثِيثٗا وَٱلشَّمۡسَ وَٱلۡقَمَرَ وَٱلنُّجُومَ مُسَخَّرَٰتِۭ بِأَمۡرِهِۦٓۗ أَلَا لَهُ ٱلۡخَلۡقُ وَٱلۡأَمۡرُۗ تَبَارَكَ ٱللَّهُ رَبُّ ٱلۡعَٰلَمِينَ54﴾

{Lalle ne Ubangijinku Allah ne, wanda Ya halitta sammai da ƙasa a cikin kwãnaki shida, sa'an nan kuma Ya daidaita a kan Al'arshi, Yanã sanya dare ya rufa yini, yanã nman sa da gaggawa, kuma rãnã da watã da taurãri hõrarru ne da umurninSa. To, Shĩ ne da halittar kuma da umurnin. Albarkar Allah Ubangijin halittu tã bayyana!} [al-A'araf: 54].

Allah ! Shi ne Ubangiji Mahalicci ga dukkan abinda ke cikin duniyar nan wanda muke gani da wanda ba ma gani, duk abinda ba Shi ba to halitta ne daga halittun Sa. Shi ne wanda Ya cancanci a bauta maSa Shi kaɗai, kuma kada a bautawa wani tare da Shi, ba Shi da abokin tarayya a mulkinSa ko halittarSa ko jujjuya lamura ko bauta maSa.

Da zamu ƙaddara cewa akwai wasu ababan bauta tare da Ubangiji - Maɗaukakin sarki - da halittu sun lalace; domin ba zai yiwu ba a ce alloli biyu ne suke jujjuya al’amarin halitta a lokaci guda, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce:

﴿لَوۡ كَانَ فِيهِمَآ ءَالِهَةٌ إِلَّا ٱللَّهُ لَفَسَدَتَا...﴾

{Da ya kasance a cikinsu (sama da ƙasa) akwai wasu allolin banda Allahu to da sun ɓaci} [al-Anbiya'a: 22].

Siffofin Ubangiji Mahalicci

Ubangiji - tsarki ya tabbata a gare Shi - Yana da sunaye masu kyau waɗanda ba a iya ƙididdige su, Yana kuma da siffofi maɗaukaka masu yawa masu girma waɗanda suke nuni akan cikarSa.

Daga cikin sunayan na Sa:

Mahalicci, Allah. Ma’anar sa: Abin bauta wanda Ya cancanci bautar Shi kaɗai, ba Shi da abokin tarayya. Rayayye, Tsayayye, Mai jin ƙai, Mai azirtawa, Mai karamci, Allah - Maɗaukakin sarki - a ckin AlKur'ani mai girma Ya ce:

﴿ٱللَّهُ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ ٱلۡحَيُّ ٱلۡقَيُّومُۚ لَا تَأۡخُذُهُۥ سِنَةٞ وَلَا نَوۡمٞۚ لَّهُۥ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِۗ مَن ذَا ٱلَّذِي يَشۡفَعُ عِندَهُۥٓ إِلَّا بِإِذۡنِهِۦۚ يَعۡلَمُ مَا بَيۡنَ أَيۡدِيهِمۡ وَمَا خَلۡفَهُمۡۖ وَلَا يُحِيطُونَ بِشَيۡءٖ مِّنۡ عِلۡمِهِۦٓ إِلَّا بِمَا شَآءَۚ وَسِعَ كُرۡسِيُّهُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَۖ وَلَا يَـُٔودُهُۥ حِفۡظُهُمَاۚ وَهُوَ ٱلۡعَلِيُّ ٱلۡعَظِيمُ255﴾

{Allah, bãbu wani Ubangiji fãce Shi, Rãyayye, Mai tsayuwa da kõme, gyangyaɗi bã ya kãma Shi, kuma barci bã ya kãma Shi, Shi ne da abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasa. Wane ne wanda yake yin cto a wurinSa, fãce da izninSa? Yana sanin abin da yake a gaba gare su da abin da yake a bãyansu. Kuma bã su kwaywa da kõme daga ilminSa, fãce da abin da Ya so. KursiyyunSa ya yalwaci sammai da ƙasa. Kuma tsare su bã ya nauyayarSa. Kuma Shi ne Maɗaukaki, Mai girma} [Suratul Baƙarah: 255].

Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce:

﴿قُلۡ هُوَ ٱللَّهُ أَحَدٌ١ ٱللَّهُ ٱلصَّمَدُ ٢ لَمۡ يَلِدۡ وَلَمۡ يُولَدۡ ٣ وَلَمۡ يَكُن لَّهُۥ كُفُوًا أَحَدُۢ4﴾

Ka ce: "Shi ne Allah Makaɗaĩci (1)

Allah shi ne abin nufi da Buƙata (2)

Bai haifa ba, kuma ba a haife Shi ba (3)

Kuma babu ɗaya da ya kasance kini a gare Shi(4) [al-Ikhlas: 1-4].

Ubangiji abin bauta wanda Ya siffantu da siffofin cika

Daga cikin siffofinSa Shi ne abin bauta, wanda ba Shi ba to abin halitta ne, kuma an ɗora masa hukunce- hukunce kuma abin umarta ne kuma abin rinjaya.

Daga cikin siffofinSa Shi Rayayye ne kuma Tsayayye ne, to duk wani samamme a wannan halittar Allah ne Ya rayar da shi, kuma Ya samar da shi daga babu, Allah ne ke kula da shi ta samar da shi da arziƙin shi, da kula da shi. Ubangiji Rayayye ne ba Ya mutuwa kuma ƙarewa ta koru gare shi, Tsayayye ne ba ya bacci, a’a gyangyaɗi ko bacci basa kama Shi.

Daga siffofinSa shi Masani ne, wanda babu wani abu da yake ɓoyuwa a gare Shi a ƙasa ko a sama.

Daga cikin siffofinsa cewa Shi Mai ji ne kuma Mai gani ne, wanda Yake jin kowanne abu, Yake ganin kowanne abin halitta, Yana sane da abinda zukatammu suke saƙawa da kuma abinda suke ɓoyewa, babu wani abu da yake boyuwa a gare Shi, tsarki ya tabbata a gare Shi a sama ko a ƙasa.

Daga cikin siffofinSa Shi Mai iko ne, babu wani abu da yake gagarar Allah, kuma babu abinda zai mayar da nufinSa, Yana aikata abinda Ya so, Yana kuma hana abinda Ya so, Yana ƙaddamarwa Yana kuma jinkirtarwa, Yana da cikakkiyar hikima.

Daga cikin siffofinSa Shine Mahalicci, Mai azurtawa, Mai juya lamura, wanda Ya halicci halittu Ya kuma juya su, halittu suna cikin damƙarSa, kuma ƙarƙashin rinjayenSa.

Daga cikin siffofinSa Shine Yake amsawa mai tsananin buƙata, Yana agazawa wanda yake cikin tsanani, Yana yaye baƙin ciki, duk wani abin halitta, to idan ya shiga damuwa da ƙunci, yana komawa ne gareShi don neman taimako.

Ita bauta ba ta kasancewa sai ga Allah - Maɗaukakin sarki -, Shi ne cikakke wanda Ya cancanci a bauta maSa Shi kaɗai banda wanda ba Shi ba, duk abinda aka bautawa da ba Shi ba to abin bautar ɓatacce ne kuma tawayayye ne, mai mutuwane mai ƙarewa ne.

Allah - tsarki ya tabbatar maSa - Ya azurta mu da hankulan da suke riskar wani abu na girmanSa, Ya kuma dasa mana ɗabi'ar da take son alheri, kuma take ƙin sharri, kuma take natsuwa idan ka fake ga Allah Ubangijin talikai, wannan ɗabi'ar tana nuni akan cikarSa kuma cewa bazaiyiwu a siffantaShi da tawaya ba - tsarki ya tabbatar maSa -.

Bai kamata ga mai hankali ya bautawa wani ba sai cikakke, to tayaya zai bautawa wanda aka halitta mai tawaya irinsa ko ma wanda bai kai shi ba!

Bazai yuwu ba abin bautawa ya kasance mutum, ko gunki ko bishiya ko dabba!

Ubangiji Yana saman sammanSa, Ya daidaitu a kan Al’arshinSa nesa da halittarSa, babu wani abu a zatinSa na halittarSa, haka kuma babu a cikin halittarSa wani abu na zatinSa, ba ya shiga ko ya narke a cikin halittarSa.

Ubangiji babu wani abu da ya yi kama da Shi, Shi Mai ji ne Mai gani ne, ba Shi da wani kini, Shi Mawadaci ne ga barin halittarSa, ba Ya bacci baYa cin abin ci, shi Mai girma ne, bazaiyiwu a ce Yana da mata ko ɗa ba; Malicci Yana da siffofin girma wanda ba zaiyi wu ba har abada ace Ya siffantu da buƙata ko tawaya.

Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce:

﴿يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ ضُرِبَ مَثَلٞ فَٱسۡتَمِعُواْ لَهُۥٓۚ إِنَّ ٱلَّذِينَ تَدۡعُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ لَن يَخۡلُقُواْ ذُبَابٗا وَلَوِ ٱجۡتَمَعُواْ لَهُۥۖ وَإِن يَسۡلُبۡهُمُ ٱلذُّبَابُ شَيۡـٔٗا لَّا يَسۡتَنقِذُوهُ مِنۡهُۚ ضَعُفَ ٱلطَّالِبُ وَٱلۡمَطۡلُوبُ ٧٣ مَا قَدَرُواْ ٱللَّهَ حَقَّ قَدۡرِهِۦٓۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَقَوِيٌّ عَزِيزٌ74﴾

{Ya ku mutãne! An buga wani misãli, sai ku saurãra zuwa gare shi. Lalle ne waɗanda kuke kira baicin Allah, bã zã su halitta ƙudã ba, kõ da sun tãru gare shi, kuma idan ƙudãn ya ƙwãce musu wani abu, bã zã su kuɓutar da shi ba daga gare shi. Mai nma da wanda ake nman gare shi sun raunana} (73)

Ba su ƙaddara wa Allah haƙƙin girmanSa ba. Lalle ne Allah, haƙĩƙa, Mai ƙarfi ne, Mabuwãyi} [al-Hajj: 73-74].

To saboda me wannan Mahalicci Mai girma Ya haliccemu? Kuma me Yake so daga garemu?

Shin zai yuwu a hankalce ace Allah Ya halicci duk waɗannan halittu, ba tare da wata manufa ba, shin Ya haliccesu ne don wasa alhali Shine Gwani Masani?

Shin zai yuwu a hankalce cewa wanda Ya halicce mu da wannan kyautataccen tsari, Ya kuma hore mana abinda ke cikin sammai da ƙasa ace Ya halicce mu ba tare da wata manufa ba, ko Ya barmu ba tare da amsa mafi mahimmancin tambayoyi ba waɗanda zasu ja hankalin mu, misali: Saboda me muke a nan? Menene zai kasnce bayan mutuwa? Menene manufar halittar mu?

Shin zai yiwu a hankalce cewa babu wata uƙuba ga azzalimi da kuma sakayya ga mai kyautatawa?

Allah - tsarki ya tabbatar maSa - Ya ce:

﴿أَفَحَسِبۡتُمۡ أَنَّمَا خَلَقۡنَٰكُمۡ عَبَثٗا وَأَنَّكُمۡ إِلَيۡنَا لَا تُرۡجَعُونَ115﴾

{Shin, to, kun yi zaton cwa Mun halitta ku ne da wãsa kuma lalle ku, zuwa gare Mu, bã zã ku kõmo ba} [al-Mua'Minun: 115].

A’a, Allah Ya aiko Manzanni domin musan abinda ya sa aka samar da mu, kuma Ya nuna mana yadda zamu bauta maSa, kuma mu nemi kusanci gare Shi, kuma me Yake so daga garemu, ta yaya zamu sami yardar Sa, Ya kuma bamu labarin makomar mu bayan mutuwa.?

Allah Ya aiko Manzanni domin su bamu labarin cewa Shi kaɗai Yake wanda Ya cancanci a bauta maSa, domin kuma musan ya zamu bauta maSa, domin su isar mana da umarninSa da kuma haninSa, kuma su sanar da mu kyawawan ɗabi’un da idan muka yi riƙo da su to rayuwar mu zata zama kyakkyawa, alhairai za su gameta da kuma albarkatai.

Haƙiƙa Allah Ya aiko Manzanni masu yawa misalin: (Annabi Nuhu, Ibrahim, Musa, da Isa), Ya ƙarfafe su da ayoyi da Mu’ujizojin da suke nuni akan gaskiyarsu, kuma cewa su Manzanni ne daga wurinSa - tsarki ya tabbatar maSa -, kuma na ƙarshansu ya kasance (Annabi) Muhammad ne - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -.

Kuma haƙiƙa Manzanni sun bamu labari a bayyane cewa wannan rayuwar jarrabawa ce, kuma lalle rayuwa ta haƙiƙa zata kasance ne bayan mutuwa

Kuma cewa a can (lahira) akwai aljanna ga muminai waɗanda suka bautawa Allah Shi kaɗai baShi da abokin tarayya, kuma suka yi imani da dukkanin manzanni, hakanan kuma a can (lahira) akwai wuta wacce Allah Ya tanadeta ga kafirai waɗanda suka bautawa wasu allolin tare da Allah, ko suka kafirce da kowane manzo daga cikin manzannin Allah.

Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce:

﴿يَٰبَنِيٓ ءَادَمَ إِمَّا يَأۡتِيَنَّكُمۡ رُسُلٞ مِّنكُمۡ يَقُصُّونَ عَلَيۡكُمۡ ءَايَٰتِي فَمَنِ ٱتَّقَىٰ وَأَصۡلَحَ فَلَا خَوۡفٌ عَلَيۡهِمۡ وَلَا هُمۡ يَحۡزَنُونَ ٣٥ وَٱلَّذِينَ كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَا وَٱسۡتَكۡبَرُواْ عَنۡهَآ أُوْلَٰٓئِكَ أَصۡحَٰبُ ٱلنَّارِۖ هُمۡ فِيهَا خَٰلِدُونَ36﴾

{Yã ɗiyan Ãdam! Ko dai wasu manzanni, daga cikinku, su j muku, sunã gaya muku ayõyiNa to, wanda ya yi taƙawa, kuma ya gyara aikinsa, to, bãbu tsoro a kansu, kuma bã su yin baƙin ciki (35)

Kuma waɗanda suka ƙaryatã game da ãyõyinMu, kuma suka yi girman kai daga gare su, waɗannan sũ ne abõkan wuta, sũ, a cikinta madawwama ne} [al-A'araf: 35-36].

Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce:

﴿يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ ٱعۡبُدُواْ رَبَّكُمُ ٱلَّذِي خَلَقَكُمۡ وَٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِكُمۡ لَعَلَّكُمۡ تَتَّقُونَ ٢١ ٱلَّذِي جَعَلَ لَكُمُ ٱلۡأَرۡضَ فِرَٰشٗا وَٱلسَّمَآءَ بِنَآءٗ وَأَنزَلَ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءٗ فَأَخۡرَجَ بِهِۦ مِنَ ٱلثَّمَرَٰتِ رِزۡقٗا لَّكُمۡۖ فَلَا تَجۡعَلُواْ لِلَّهِ أَندَادٗا وَأَنتُمۡ تَعۡلَمُونَ ٢٢ وَإِن كُنتُمۡ فِي رَيۡبٖ مِّمَّا نَزَّلۡنَا عَلَىٰ عَبۡدِنَا فَأۡتُواْ بِسُورَةٖ مِّن مِّثۡلِهِۦ وَٱدۡعُواْ شُهَدَآءَكُم مِّن دُونِ ٱللَّهِ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ ٢٣ فَإِن لَّمۡ تَفۡعَلُواْ وَلَن تَفۡعَلُواْ فَٱتَّقُواْ ٱلنَّارَ ٱلَّتِي وَقُودُهَا ٱلنَّاسُ وَٱلۡحِجَارَةُۖ أُعِدَّتۡ لِلۡكَٰفِرِينَ ٢٤ وَبَشِّرِ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ أَنَّ لَهُمۡ جَنَّٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُۖ كُلَّمَا رُزِقُواْ مِنۡهَا مِن ثَمَرَةٖ رِّزۡقٗا قَالُواْ هَٰذَا ٱلَّذِي رُزِقۡنَا مِن قَبۡلُۖ وَأُتُواْ بِهِۦ مُتَشَٰبِهٗاۖ وَلَهُمۡ فِيهَآ أَزۡوَٰجٞ مُّطَهَّرَةٞۖ وَهُمۡ فِيهَا خَٰلِدُونَ25﴾

{Yã ku mutãne! Ku bauta wa Ubangjinku, Wanda Ya halicce ku, kũ da waɗanda suke daga gabãninku, tsammãninku ku kãre kanku (21)

Wanda Ya sanya muku ƙasa shimfiɗa, kuma sama gini, kuma Ya saukar da ruwa daga sama, sa'an nan Ya fitar da abinci daga 'ya'yan itãce game da shi, sabõda ku. Sabõda haka kada ku sanya wa Allah wasu kĩshiyõyi, alhãli kuwa kuna sane (22)

Idan kun kasance a cikin kokwanto daga abinda muka saukar a bisa bawanmu, to kuzo da wata sura irinsa (alkur'ani) kuma ku kira shedunku wanda ba Allah ba, in kun kasance masu gaskya ne (23)

To, idan ba ku aikata (kãwo sura) ba, to, bã zã ku aikataba, sabõda haka, ku ji tsoron wuta, wadda makãmashinta mutãne da duwãtsu ne, an yi tattalinta dõmin kãfurai (24)

Kuma ka bãyar da bishãra ga waɗanda suka yi ĩmãni. kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai, cwa lallene, suna da gidãjen Aljanna, ƙõramu na gudãna daga ƙarƙashinsu. Ko da yaushe aka azurta su da abinci daga wasu 'ya'yan itãce daga gare su, sai su ce: "Wannan shi ne aka azurta mu da shi daga gabãnin haka," Kuma a je musu da shi yana mai kama da juna, Kuma sunã da, a cikin su, mãtan aure mãsu tsarki, kuma su, cikin su madawwama ne} [Suratul Baƙarah, 21-25].

Me yasa Manzanni suke da yawa?

Tabbas Allah Ya aiko ManzanninSa zuwa ga al’ummatai, babu wata al’umma face sai da Allah Ya aika musu da Manzo, domin ya kira su zuwa ga bautawa Ubangijin su, kuma ya isar musu da umarninSa da kuma haninSa, kuma manufar kiran na su ya kasance ne gaba ɗaya itace: Bautawa Allah Shi kaɗai - Mai girma da ɗaukaka -. To a duk lokacin da wata al’umma ta fara bari ko ta rikitar da abinda Manzon ya zo da shi na kaɗaita Allah, sai Allah Ya sake aiko da wani Manzon domin ya gyara tafiyar, kuma ya kuma dawo da mutane kan tafarki na daidai, na kaɗaita Allah da kuma yi maSa biyayya.

Har sai da Allah Ya kammala aiko Manzanni da (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, wanda yazo da Addini cikakke da kuma shari’a tabbatacciya gamammiya ga dukkanin mutane har ranar alƙiyama, wacce ta cika kuma ta goge wacce ta gaba ce ta na shari’o’i, kuma Allah - Maɗaukakin sarki - Ya lamunci wanzar da wannan Addinin da kuma tabbatuwarsa har zuwa ranar alƙiyama.

Mutum ba zai kasance mumini ba har sai ya yi imani da dukkanin manzanni.

Allah Shine wanda Ya aiko manzanni, kuma Ya umarci dukkanin halittarSa da yi musu biyayya, wanda ya kafirce da saƙon ɗaya daga cikinsu to haƙiƙa ya kafircewa dukkannin su, babu wani zunubi mafi girma fiye da mutum ya juyarwa da Allah wahayinSa, babu makawa yin imani da dukkanin Manzanni domin shiga aljanna.

Abinda yake wajibi akan kowanne mutum a wannan lokacin shine yayi imani da Allah da kuma dukkanin Manzannin Allah, kuma yayi imani da ranar ƙarshe, hakan kuma bazai kasance ba sai idan yayi imani kuma yabi na ƙarshensu kuma cikamakinsu (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, wanda aka ƙarfafeshi da mu’ujiza madawwamiya ita ce Alƙur’ani mai girma, wanda Allah Ya lamunce kiyaye shi har sai ya gaje ƙasa da waɗanda ke kanta.

Allah Ya ambata a cikin Alƙur’ani cewa duk wanda yaƙi yin imani da kowanne Manzo daga cikin ManzaninSa to shi ya kafircewa Allah, kuma ya ƙaryata wahayinSa, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce:

﴿إِنَّ ٱلَّذِينَ يَكۡفُرُونَ بِٱللَّهِ وَرُسُلِهِۦ وَيُرِيدُونَ أَن يُفَرِّقُواْ بَيۡنَ ٱللَّهِ وَرُسُلِهِۦ وَيَقُولُونَ نُؤۡمِنُ بِبَعۡضٖ وَنَكۡفُرُ بِبَعۡضٖ وَيُرِيدُونَ أَن يَتَّخِذُواْ بَيۡنَ ذَٰلِكَ سَبِيلًا ١٥٠ أُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡكَٰفِرُونَ حَقّٗاۚ وَأَعۡتَدۡنَا لِلۡكَٰفِرِينَ عَذَابٗا مُّهِينٗا151﴾

{Lalle ne, waɗanda uke kãfirta da Allah da ManzonSa kuma sunã nufin su rarrabe a tsakãnin Allah da manzanninSa, kuma sunã cwa: "Munã ĩmãni da sãshe, kuma munã kãfirta da sãshe." Kuma sunã nufin su riƙi hanya a tsakãnin wannan (150)

Waɗannan sũ ne kãfirai sõsai, kuma Mun yi tattali, dõmin kãfirai, azãba mai walãkantarwa} [al-Nisa'i: 150-151].

Saboda haka mu musulmai muke imani da Allah da ranar lahira - kamar yadda Allah Yayi umarni -, kuma muna imani da dukkanin Manzanni da littattafan da suka gabata, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce:

﴿ءَامَنَ ٱلرَّسُولُ بِمَآ أُنزِلَ إِلَيۡهِ مِن رَّبِّهِۦ وَٱلۡمُؤۡمِنُونَۚ كُلٌّ ءَامَنَ بِٱللَّهِ وَمَلَٰٓئِكَتِهِۦ وَكُتُبِهِۦ وَرُسُلِهِۦ لَا نُفَرِّقُ بَيۡنَ أَحَدٖ مِّن رُّسُلِهِۦۚ وَقَالُواْ سَمِعۡنَا وَأَطَعۡنَاۖ غُفۡرَانَكَ رَبَّنَا وَإِلَيۡكَ ٱلۡمَصِيرُ285﴾

{Manzon Allah yã yi ĩmãni da abin da aka saukar zuwa gare shi daga Ubangijinsa, da mũminai. Kõwanensu yã yi ĩmãni da Allah, da mala'ikunSa, da littattafanSa, da manzanninSa. Bã mu rarrabwa a tsakãnin daya daga manzanninSa. Kuma (mũminai) suka ce: "Mun ji kuma mun yi dã'a; (Muna nman) gãfararKa, yã Ubangijinmu, kuma zuwa a gare Ka makõma take } [Surat al-Baƙara: 285].

Menene Alƙur'ani mai girma?

Alƙur’ani mai girma shine zancan Allah - Maɗaukakin sarki - kuma wahayinSa da Ya saukar da shi ga ƙarshan Manzanni (Annabi) Muhammad, shine ƙololuwar mu’ujizar da take nuni akan gaskiyar Annabtarsa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, Alƙur'ani mai girma shine gaskiya a cikin hukunce- hukuncensa, kuma gaskiya a cikin labaransa.

Tabbas Allah Ya ƙalubanci masu ƙaryatawa akan suzo ko da da sure ce guda ɗaya kwatankwacinsa sai suka kasa hakan; saboda girman abinda ya ƙunsa, da kuma gamewar abubuwan da ya tattaro na dukkan abinda yake da alaƙa da mutum a rayuwar duniya da lahiya, kuma ya ƙunshi dukkanin tabbatattun abubuwa na imani waɗanda ya wajaba ga mutum yayi imani da su.

Kamar yadda ya ƙunshi umarni da hani waɗanda suke wajaba mutum ya tafi akansu a tsakaninsa da Ubangijinsa, ko tsakanin sa da kansa ko kuma tsakanin sa da sauran halittu, dukkanin hakan a tsari na ƙololuwar balaga da kuma bayani.

Haƙiƙa (Alƙur’ani) ya ƙunshi da yawa daga dalilai na hankali da tabbatattun ilimi masu zurfi waɗanda suke nuni akan wannan Littafin cewa bazai taɓa yi wuwa a ce mutum ne ya ƙirkire shi ba, kai shi magana ce ta Ubangijin mutum - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka -.

Menene Musulinci?

Musulunci shi ne miƙa wuya ga Allah - Maɗaukakin sarki - da Tauhidi, da jawuwa gareShi da biyayya, da riƙo da shari’arSa da yarda da kuma karɓa, da kuma kafircewa dukkanin abinda ake bautawa ba Allah ba.

Haƙiƙa Allah Ya aiko da Manzanni da saƙo ɗaya shine: Kira zuwa ga bautar Allah Shi kaɗai ba Shi da abokin tarayya, da kuma kafircewa dukkanin abinda ake bautawa ba Allah ba.

Musulunci shi ne Addinin dukkanin Annabawa, kuma da’awarsu ɗaya ce, shari’o’insu sun sha banban, musulmai a yau su ne masu kaɗaita Allah su kaɗai, masu riƙo da ingantaccen Addini wanda dukkanin Annabawa suka zo da shi. Kuma saƙon Musulunci a wannan zamanin shine gaskiya, kuma shi ne saƙo na ƙarshe daga Mahaliccin mutum.

Ubangiji wanda Ya aiko (Annabi) Ibrahim da Musa da Isah - amincin Allah ya tabbata a gare su - Shine Ya aiko cikamakin Manzanni (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, haƙiƙa shari'ar Musulunci tazo tana mai shafe dukkanin shari’un da suka gabaceta.

Dukkanin addinai waɗanda mutane suke bauta da su a yau - in banda Musulunci- addinai ne da mutane suka ƙirƙira, ko kuma addinai ne waɗanda daga Allah suke sai mutane sukayi wasa da su, sai suka wayi gari a cakuɗe da ɗebe-ɗebe da tatsuniya da shaci faɗi waɗan aka gada, kuma sauran tunanin mutum.

Amma Addinin Musulmai to Addini ne guda ɗaya kuma a bayyane yake baya canzawa, kamar yadda bautarsu wacce suke bautawa Allah da ita ɗaya ce, dukkanin su suna salloli biyar, suna zakkar dukiyoyinsu, suna azumin wata Ramadan, kuma kayi la’akari da Littafin su shi ne Alƙur’ani mai girma shi littafi ne guda ɗaya adukkanin ƙasashe. Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce:

﴿...ٱلۡيَوۡمَ أَكۡمَلۡتُ لَكُمۡ دِينَكُمۡ وَأَتۡمَمۡتُ عَلَيۡكُمۡ نِعۡمَتِي وَرَضِيتُ لَكُمُ ٱلۡإِسۡلَٰمَ دِينٗاۚ فَمَنِ ٱضۡطُرَّ فِي مَخۡمَصَةٍ غَيۡرَ مُتَجَانِفٖ لِّإِثۡمٖ فَإِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٞ﴾

{A yau Na cika maku Addininku, kuma Na cika muku ni’imta a gareku, Na kuma yardar muku Musulunci shi ne Addini, to duk wanda ya shiga matsananciyar buƙata a yunwa ba tare da karkata ga lefi ba, to lalle Allah Mai gafara ne Mai jinƙai} [Suratul Ma’idah: 3].

Allah - Maɗaukakin sarki - a ckin Alƙur'ani mai girma Ya ce:

﴿قُلۡ ءَامَنَّا بِٱللَّهِ وَمَآ أُنزِلَ عَلَيۡنَا وَمَآ أُنزِلَ عَلَىٰٓ إِبۡرَٰهِيمَ وَإِسۡمَٰعِيلَ وَإِسۡحَٰقَ وَيَعۡقُوبَ وَٱلۡأَسۡبَاطِ وَمَآ أُوتِيَ مُوسَىٰ وَعِيسَىٰ وَٱلنَّبِيُّونَ مِن رَّبِّهِمۡ لَا نُفَرِّقُ بَيۡنَ أَحَدٖ مِّنۡهُمۡ وَنَحۡنُ لَهُۥ مُسۡلِمُونَ ٨٤ وَمَن يَبۡتَغِ غَيۡرَ ٱلۡإِسۡلَٰمِ دِينٗا فَلَن يُقۡبَلَ مِنۡهُ وَهُوَ فِي ٱلۡأٓخِرَةِ مِنَ ٱلۡخَٰسِرِينَ85﴾

{Ka ce: "Mun yi ĩmãni da Allah kuma da abin da aka saukar mana da abin da aka saukar wa Ibrãhĩma da Isma'ĩla da Is'hãƙa da Yãƙũba da jĩkõki, da abin da aka bai wa Mũsã da ĩsã da annabãwa daga Ubangijinsu, bã mu bambantãwa a tsakãnin kõwa daga gare su. Kuma mũ, zuwa gare Shi mãsu sallamãwa ne}(84)

{Kuma wanda ya nmi wanin Musulunci ya zama addini, to, bã zã a karɓa daga gare shi ba. Kuma shi a Lãhira yana daga cikin mãsu hasãra} [Aal Imran: 84-85].

Addinin Musulunci tsari ne da ya game dukkanin rayuwa, yayi daidai da ɗabi’a na halitta da hankali, kuma madaidaitun rayuka suna karɓarsa, Mahalicci Mai girma ne Ya shar’anta shi ga halittarSa, kuma shine Addinin alheri da rabauta ga mutane baki ɗaya a duniya da lahira, ba ya banbance ƙabila da ƙabila, ko nuna wariyar launin fata, mutane a cikinsa daidai suke, wani mutum a Musulunci baya fin wani sai da gwargwadon aikinsa na gari.

Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce:

﴿مَنۡ عَمِلَ صَٰلِحٗا مِّن ذَكَرٍ أَوۡ أُنثَىٰ وَهُوَ مُؤۡمِنٞ فَلَنُحۡيِيَنَّهُۥ حَيَوٰةٗ طَيِّبَةٗۖ وَلَنَجۡزِيَنَّهُمۡ أَجۡرَهُم بِأَحۡسَنِ مَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ97﴾

{Wanda ya aikata aiki na ƙwarai daga namiji kõ kuwa mace, alhãli yanã mũmini, to, haƙĩƙa Munã rãyar da shi, rãyuwa mai dãɗi. Kuma haƙĩƙa Munã sãkã musu lãdarsu da mafi kyãwun abin da suka kasance sunã aikatãwa} [al- Nahl: 97].

Musulunci hanya ce ta tsira

Musulunci Addini ne na dukkanin Annabawa, kuma shi ne Addinin mutane baki ɗaya, ba wai addini ne na Labawa kaɗai ba.

Musulunci shi ne hanyar samun farin ciki na haƙiƙa a duniya, kuma ni'ima madawwamiyya a lahira.

Musulunci shi ne Addini ɗaya da yake amsa buƙatun rai da jiki, da warware dukkanin matsalolin mutane, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce:

﴿قَالَ ٱهۡبِطَا مِنۡهَا جَمِيعَۢاۖ بَعۡضُكُمۡ لِبَعۡضٍ عَدُوّٞۖ فَإِمَّا يَأۡتِيَنَّكُم مِّنِّي هُدٗى فَمَنِ ٱتَّبَعَ هُدَايَ فَلَا يَضِلُّ وَلَا يَشۡقَىٰ 123 وَمَنۡ أَعۡرَضَ عَن ذِكۡرِي فَإِنَّ لَهُۥ مَعِيشَةٗ ضَنكٗا وَنَحۡشُرُهُۥ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ أَعۡمَىٰ124﴾

{Ya ce: "Ku sauka kũ biyu daga gare ta gabã ɗaya, sãshenku yanã maƙiyi ga sãshe. To, imma dai wata shitiya ta j muku daga gare Ni, to, wanda ya bi shiryarwãta, to, bã ya ɓacwa, kuma bã ya wahala}

Kuma wanda ya bijire daga ambatõNa (Alƙur'ãni) to, lalle ne rãyuwa mai ƙunci ta tabbata a gare shi, kuma Munã tãyar da shi a Rãnar ¡iyãma yanã makãho} [Ɗaha: 123-124].

Me musulmi yake fa’idantuwa da shi a duniya da lahira?

Musulinci yana da fa’idoji masu girma, daga cikinsu akwai:

- Rabauta da ɗaukaka a duniya wato mutum ya kasance bawa ga Allah, in ba haka bafa zai zama bawan son zuciya da shaiɗan da sha'awe-sha'awe.

- Rabauta a lahira shine Allah Ya gafarta masa, kuma Ya saukar maSa da yardarSa, kuma Ya shigar da shi aljanna, ya rabauta da yarda da ni’ima tabbatacciya, kuma mutum ya tsira daga azabar wuta.

- Mumini yana kasancewa ne a ranar alƙiyama tare da Annabawa da siddiƙai da shahidai da kuma salihai. Kai Amma wannan tawaga babu abinda ya kai ta daɗi, duk wanda bai yi imani ba to ya kasance ne tare da ɗagutai da ashararai da fanɗararru da maɓarnata.

- Waɗanda Allah Zai shigar da su aljnna za su rayu a cikin ni’ima ta har abada ba mutuwa ba rashin lafiya ko ciwon jiki ko tsufa ko baƙin ciki, kuma za’a biya musu buƙatunsu na duk abinda suke buƙatarsa. Wadanda za su shiga wuta za su kasance a cikin azaba ta har abada a dawwame ba ta yankewa.

Acikin Aljanna akwai abubuwan jin daɗin da idanu bai gansu ba, kunne bai ji su ba, kuma basu ɗarsuwa a zuciyar wani mutum ba. Daga dalilan hakan faɗinSa - Maɗaukakin sarki -:

﴿مَنۡ عَمِلَ صَٰلِحٗا مِّن ذَكَرٍ أَوۡ أُنثَىٰ وَهُوَ مُؤۡمِنٞ فَلَنُحۡيِيَنَّهُۥ حَيَوٰةٗ طَيِّبَةٗۖ وَلَنَجۡزِيَنَّهُمۡ أَجۡرَهُم بِأَحۡسَنِ مَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ97﴾

{Wanda ya aikata aiki na ƙwarai daga namiji kõ kuwa mace, alhãli yanã mũmini, to, haƙĩƙa Munã rãyar da shi, rãyuwa mai dãɗi. Kuma haƙĩƙa Munã sãkã musu lãdarsu da mafi kyãwun abin da suka kasance sunã aikatãwa} [al-Nahl: 97].

Maɗaukakin sarki Ya ce:

﴿فَلَا تَعۡلَمُ نَفۡسٞ مَّآ أُخۡفِيَ لَهُم مِّن قُرَّةِ أَعۡيُنٖ جَزَآءَۢ بِمَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ17﴾

{Kuma rai ba ta san abinda aka ɓoye musu na farin idanuwa ba, sakamako na abinda suka kasance suna aikatawa} [Suratus Sajdah, aya ta 17]

Me abinda wanda ba musulmi ba zai yi asara?

Mutum zai yi hasarar mafi girman ilimi da sani, shi ne sanin Allah, kuma zai yi hasarar imani da Allah, wanda ya ke bawa mutum aminci da nutsuwa a duniya, da ni'ima madawwamiyya a lahira.

Mutum zai yi hasarar tsinkaye a kan mafi girman littafin da Allah Ya saukar da shi zuwa ga mutane, da kuma imani da wannan Littafin mai girma.

Zai yi hasarar imani da Annabawa masu girma, kamar yadda zai yi hasarar zama tare da su a aljanna ranar alƙiyama, zai kasance abokin zaman shaiɗan da masu laifuffuka da ɗagwitai (waɗanda aka bautawa) a cikin wutar Jahannama tir da wannan gida kuma tir da wannan maƙotaka.

Allah - Madaukakin sarki - Ya ce:

﴿قُلۡ إِنَّ ٱلۡخَٰسِرِينَ ٱلَّذِينَ خَسِرُوٓاْ أَنفُسَهُمۡ وَأَهۡلِيهِمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِۗ أَلَا ذَٰلِكَ هُوَ ٱلۡخُسۡرَانُ ٱلۡمُبِينُ 15 لَهُم مِّن فَوۡقِهِمۡ ظُلَلٞ مِّنَ ٱلنَّارِ وَمِن تَحۡتِهِمۡ ظُلَلٞۚ ذَٰلِكَ يُخَوِّفُ ٱللَّهُ بِهِۦ عِبَادَهُۥۚ يَٰعِبَادِ فَٱتَّقُونِ16﴾

{Kace lallai hasararru sune waɗanda suka yi hasarar kawunann su da ahalin su ranar alƙiyama, ku saurara, wannan ita ce hasara bayyananna (15)

Sunã da waɗansu inuwõwi na wutã daga samansu, kuma daga ƙasansu akwai waɗansu inuwõwi. Wancan Shĩ ne Allah ke tsõratar da bãyinSa da shi. Yã bãyĩNa! To, ku bĩ Ni da taƙawa} [al-Zumar: 15-16].

Wanda yake nufin tsira a lahira, to ya wajaba a kansa ya kasance musulmi mai biyayya ga Allah, mai kuma bin Manzon Allah-tsira da amincin Allah su tabbata agare shi-

Daga tabbatattun abubuwan da Annabawa da Manzanni - amincin Allah ya tabbata a gare su - suka haɗu a kansu cewa babu wanda zai tsira a lahira sai musulmai waɗanda suka yi imani da Allah - Maɗaukakin sarki -, ba su haɗa kowa da Shi a bauta ba, kuma suka yi imani da dukkanin Annabawa da Manzanni, duk masu bin Manzanni waɗanda suka yi imani da su masu gasgata su, to za su shiga aljanna kuma za su tsira daga wuta.

Waɗanda suka yi imani a zamanin (Annabi) Musa suka yi imani da shi suka bi karantarwar sa to waɗannan musulmai ne, kuma muminai ne salihai, saidai bayan Allah Ya aiko da Annabi Isa ya wajaba ga mai mabiya Annabi Musa su yi imani da Annabi Isa su kuma bi shi.

Waɗanda suka yi imani da Annabi Isa to waɗannan musulmai ne salihai, wanda kuma ya yi watsi da imani da Annabi Isa ya ce, zan kasance akan Addinin Annabi Musa, to wannan bai yi imani ba, domin ya yi watsi da imani da Manzon da Allah Ya aiko shi.

Sannan bayan da Allah Ya aiko Manzon ƙarshe (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, ya wajaba akan kowa suyi imani da shi, Ubangiji Shi ne Ya aiko (Annabi) Musa da Isah kuma Shi ne wanda Ya aiko cikamakin Manzanni (Annabi) Muhammad, duk wanda ya kafircewa manzancin (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce zan kasance akan bin (Annabi) Musa ko Isa to wannan ba mumini ba ne.

Baya wadatarwa mutum ya ce shi yana girmama musulmai, kuma baya wadatarwa don samun tsiransa a ranar ƙarahe saboda ya bada sadaka kuma yana taimakawa talakawa, kai babu makawa sai ya kasance ya yi imani da Allah da littattafanSa da ManazaninSa da ranar ƙarshe; domin Allah Ya karɓi hakan daga gare shi!. Babu wani zunubi mafi girma da ya kai shirka da kafircewa Allah da ƙin yin imani da wahayin da Allah Ya saukar da shi ko ƙin yin imani da ƙarshan AnnabawanSa (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.

Yahudu da Nasara da sauransu waɗanda suka ji aiko (Annabi) Muhammad Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, suka ƙi yin imani da shi suka ƙi shiga Addinin Musulunci to za su kasance a wutar Jahannama masu dawwama a cikinta har abada, wannan shi ne hukuncin Allah ba hukuncin wani ba ne cikin mutane, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce:

﴿إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ مِنۡ أَهۡلِ ٱلۡكِتَٰبِ وَٱلۡمُشۡرِكِينَ فِي نَارِ جَهَنَّمَ خَٰلِدِينَ فِيهَآۚ أُوْلَٰٓئِكَ هُمۡ شَرُّ ٱلۡبَرِيَّةِ6﴾

{Lalle ne waɗanda suka kafirta daga mutanen Littafi da mushirikai sana cikin wutar Jahannama suna madawwama a cikinta. Waɗannan su ne mafi ashararancin tãlikai} [al-Bayyinah: 5].

Yayin da ƙarshen saƙo ya sauka daga Allah izuwa yan Adam, ya wajaba akan kowanne ɗaya da ya ji (bayanin) Musulunci ya kuma ji (bayanin) Annabin ƙarshe (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, ya yi imani da shi kuma ya bi shari'arsa, ya yi masa biyayya a umarninsa da haninsa, saboda haka wanda ya ji wannan saƙon na ƙarshe kuma ya ƙi binsa, to Allah ba zai karɓi wani abu daga gare shi ba, kuma zai azabtar da shi a lahira.

Daga cikin dalilan haka, faɗinSa - Maɗaukakin sarki -:

﴿‌وَمَن يَبۡتَغِ غَيۡرَ ٱلۡإِسۡلَٰمِ دِينٗا فَلَن يُقۡبَلَ مِنۡهُ وَهُوَ فِي ٱلۡأٓخِرَةِ مِنَ ٱلۡخَٰسِرِينَ85﴾

{Kuma wanda ya nmi wanin Musulunci ya zama addini, to, bã zã a karɓa daga gare shi ba. Kuma shi a Lãhira yana daga cikin mãsu hasãra} [Aal- Imran: 85].

Maɗaukakin sarki Ya ce:

﴿قُلۡ يَٰٓأَهۡلَ ٱلۡكِتَٰبِ تَعَالَوۡاْ إِلَىٰ كَلِمَةٖ سَوَآءِۭ بَيۡنَنَا وَبَيۡنَكُمۡ أَلَّا نَعۡبُدَ إِلَّا ٱللَّهَ وَلَا نُشۡرِكَ بِهِۦ شَيۡـٔٗا وَلَا يَتَّخِذَ بَعۡضُنَا بَعۡضًا أَرۡبَابٗا مِّن دُونِ ٱللَّهِۚ فَإِن تَوَلَّوۡاْ فَقُولُواْ ٱشۡهَدُواْ بِأَنَّا مُسۡلِمُونَ64﴾

{Ka ce: "Yã ku Mutãnen Littãfi! Ku tafo zuwa ga kalma mai daidaitãwa a tsakã ninmu da ku; kada mu bauta wa kõwa fã ce Allah. Kuma kada mu haɗa kõme da Shi, kuma kada sãshenmu ya riƙi sãshe Ubangiji, baicin Allah." To, idan sun jũya bã ya sai ku ce: "ku yi shaida cwa, lalle ne mu masu sallamã wa ne} [Aal- Imran: 64].

Meye ya lazimci musulmi?

Yana wajaba akan musulmi, yin imani da waɗannan rukunan guda shida:

Yin imani da Allah - Maɗaukakin sarki - kuma cewa Shi ne Mahalicci Mai azurtawa Mai juya lamura Mamallaki, babu wani abu da ya yi kama da Shi, ba Shi da mata ba Shi da ɗa, kuma Shi kaɗai ne wanda Ya cancanci a bauta maSa, kuma ba’a bauta wani tare da Shi, kuma Ya ƙudirce cewa bautawa dukkanin wanda ake bautawa koma bayanSa to bautarsa ɓatacciya ce.

Yin imani da mala'iku, cewa su bayin Allah ne - Maɗaukakin sarki -, Ya halicce su daga haske, kuma Ya sanya cewa daga cikin ayyukansu su suna sauko da wahayi ga AnnabawanSa.

Yin imani da dukkanin littattafan da Allah Ya saukar da su ga AnnabawanSa (kamar Attaura da Injila - kafin a jirkita su -) kuma ƙarshen littattafan shi ne Alƙur'ani mai girma.

Yin imani da dukkanin Manzanni, kamar (Annabi) Nuhu da (Annabi) Ibrahim da (Annabi) Musa da (Annabi) Isa, da na ƙarshensu shine (Annabi) Muhamad, kuma dukkaninsu daga 'yan Adam suke, (Allah) Ya ƙarfafe su da wahayi kuma Ya basu ayoyi da mu'ujizojin da suke nuni akan gaskiyarsu.

Imani da ranar ƙarshe, yayin da Allah zai tashi na farko da na ƙarshe, Allah kuma zaiyi hukunci tsakanin halittarSa, Ya shigar da muminai aljanna, kafirai kuma Ya shigar da su wuta.

Imani da kaddara cewa, Allah Ya san komai, abinda ya kasance ya wuce da kuma abinda zai kasance nan gaba, kuma hakika Allah ya rubuta haka, kuma ya so shi ya halicci komai.

Kuma ka bautawa Allah da abinda Ya shar’anta na sallah da zakkah da azumi da kuma hajji idan ka sami ikon tafiya gareshi. Sannan ya wajaba akan shi ya koyi Addininsa wanda zai zama tushen rabautarsa a duniya da kuma tsiransa a lahira.

***

Teburin bayani

 

Ubangiji Mahalicci Mai girma. 4

Wannan Ubangijin Mahalicci Mai azirtawa, Shi ne Allah - tsarki da ɗaukaka sun tabbatar masa -. 5

Siffofin Ubangiji Mahalicci. 6

Ubangiji abin bauta wanda ya siffantu da siffofin cika 7

To saboda me wannan Mahalicci Mai girma Ya haliccemu? Kuma me Yake so daga garemu? 10

Me yasa Manzanni suke da yawa? 14

Mutum ba zai kasance mumini ba har sai ya yi imani da dukkanin manzanni. 15

Menene Alƙur'ani mai girma? 17

Menene Musulinci? 18

Musulunci hanya ce ta tsira 21

Me Musulmi yake fa’idantuwa da shi a duniya da lahira? 22

Me abinda wanda ba musulmi ba zai yi asara? 23

Wanda yake nufin tsira a lahira, to ya wajaba a kansa ya kasance musulmi mai biyayya ga Allah, mai kuma bin Manzon Allah-tsira da amincin Allah su tabbata agare shi- 24

Meye ya lazimci musulmi? 28

***