بيان كفر وضلال من زعم أنه يجوز لأحد الخروج من شريعة محمد صلى الله عليه وسلم (هوسا)

  • earth Harshe
    (هوسا)
  • earth Wallafar:
    الشيخ عبد العزيز بن باز
PHPWord

 

 

 

بَيَانُ كُفْرِ وَضَلَالِ مَنْ زَعَمَ أَنَّهُ يَجُوزُ لِأَحَدٍ الخُرُوجُ
مِنْ شَرِيعَةِ مُحَمَّدٍ

 

Bayanin kafirci da ɓatan duk wanda ya raya cewa ya halatta ga wani ya kauce daga shari'ar (Annabi) Muhammadu
- tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi-

 

 

 

 

 

لِسَمَاحَةِ الشَّيْخِ العَلَّامَةِ

عَبْدِ العَزِيزِ بْنِ عَبْدِ اللهِ بْنِ بَازٍ

رَحِمَهُ اللهُ

 

Wallafar: Babban Malami

AbdulAzeez Bin Abdullahi Bin Baaz

Allah Yayi masa rahama

 


بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ

SAƘO NA GOMA SHA BIYU

Bayanin kafirci da ɓatan duk wanda ya raya cewa ya halatta ga wani ya kauce daga shari'ar (Annabi) Muhammadu - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi-.

Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, tsira da aminci su tabbata ga cikamakin Annabawa da Manzanni Annabinmu Muhammad, da alayansa da sahabbansa baki ɗaya.

Bayan haka: Haƙiƙa na karanta maƙalar da aka wallafa a jaridar al-Sharƙ al-Awsaɗ a lamba ta (5824) da kwanan wata 5/6/1415 H, wanda ya rubuta shine wanda ya kira kansa: Abdul Fattah al-Hayik, a ƙarƙashin taken: (Fahimtar da ba daidai ba).

Taƙaitaccen bayanin: Musuntawar da ya yi na abinda aka sani daga addinin Musulunci da wajibi, da nass da kuma ijma'i; wato gamewar aiken (annabi) Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi zuwa ga dukkan mutane, da iƙirarin cewa wanda bai bi (annabi) Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ba kuma bai yi masa biyayya ba kawai ya tsaya ya kasance Bayahude ko Banasara to yana kan addini na gaskiya, sannan ya yi suka ga Allah Ubangijin talikai - Tsarkakakke - a cikin hikimarsa na azabtar da kafirai da masu saɓo, ya sanya hakan cikin abinda ba shi da amfani.

Haƙiƙa ya tsayu wurin canza nassoshi na shari’a da sanya su ba'a bigiren su ba, ya kuma fassara su da son zuciyarsa, ya kuma kau da kai daga dalilai na shari’a da nassoshi da suke a bayyane waɗanda suke nuni akan gamewar manzancin (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, kuma suke nuni akan kafircin duk wanda ya ji shi kuma bai bi shi ba, kuma Allah ba Ya karɓar wani addini da ba Musulinci ba, da wanin haka na nassoshi fayyatattu waɗanda ya kau da kai daga gare su domin ya yaudari jahilai da maganarsa. Wannan abinda ya aikata kafirci ne kuma ridda ce daga Musulinci kuma ƙaryata Allah ne - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka -, kuma (ƙaryatawa ne) ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, kamar yadda duk wanda ya karanta maganar sa cikin malamai masu imani ya san hakan.

Abinda yake wajibi akan shugaba: Ya miƙa shi gaban kotu, domin ya tuba a kuma yi masa hukunci da abinda shari'ah mai tsarki ta hukunta.

Allah - Tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka - Ya bayyana gamewar saƙon annabi Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, da wajabcin binsa ga dukkan nauyaya biyu (mutum da aljann), kuma wannan ba zai ɓoyu ga wanda yake da ƙarancin ilimi cikin Musulmai ba.

Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce:

﴿قُلۡ يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ إِنِّي رَسُولُ ٱللَّهِ إِلَيۡكُمۡ جَمِيعًا ٱلَّذِي لَهُۥ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۖ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ يُحۡيِۦ وَيُمِيتُۖ فَـَٔامِنُواْ بِٱللَّهِ وَرَسُولِهِ ٱلنَّبِيِّ ٱلۡأُمِّيِّ ٱلَّذِي يُؤۡمِنُ بِٱللَّهِ وَكَلِمَٰتِهِۦ وَٱتَّبِعُوهُ لَعَلَّكُمۡ تَهۡتَدُونَ158﴾

{Ka ce: "Yã kũ mutãne! Lalle ne nĩ manzon Allah ne zuwa gare ku, gabã ɗaya. (Allah) Wanda Yake Shĩ ne da mulkin sammai da ƙasa; Bãbu wani abin bautawa da gaskiya fãce Shi, Yanã rãyarwa, kuma Yanã matarwa, sai ku yi ĩmãni da Allah da ManzonSa, Annabi, Ummiyyi, wanda yake yin ĩmãni da Allah da kalmominSa; ku bĩ shi, tsammãninku, kunã shiryuwa} [al-A'araf: 158]. Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿...وَأُوحِيَ إِلَيَّ هَٰذَا ٱلۡقُرۡءَانُ لِأُنذِرَكُم بِهِۦ وَمَنۢ بَلَغَ...﴾

{An saukar min da wannan Alƙur’anin dan na gargaɗe ku dashi da duk wanda zai isa zuwa gareshi} [al-An'am: 19]. Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿قُلۡ إِن كُنتُمۡ تُحِبُّونَ ٱللَّهَ فَٱتَّبِعُونِي يُحۡبِبۡكُمُ ٱللَّهُ وَيَغۡفِرۡ لَكُمۡ ذُنُوبَكُمۡۚ وَٱللَّهُ غَفُورٞ رَّحِيمٞ31﴾

{Ka ce: "Idan kun kasance kunã son Allah to, ku bĩ ni, Allah Ya sõ ku, kuma Ya gãfarta muku zunubanku} [Aal- Imran: 31]. Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿وَمَن يَبۡتَغِ غَيۡرَ ٱلۡإِسۡلَٰمِ دِينٗا فَلَن يُقۡبَلَ مِنۡهُ وَهُوَ فِي ٱلۡأٓخِرَةِ مِنَ ٱلۡخَٰسِرِينَ85﴾

{Kuma wanda ya nẽmi wanin Musulunci ya zama addini, to, bã zã a karɓa daga gare shi ba. Kuma shi a Lãhira yana daga cikin mãsu hasãra} [Aal- Imran: 85]. Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿وَمَآ أَرۡسَلۡنَٰكَ إِلَّا كَآفَّةٗ لِّلنَّاسِ بَشِيرٗا وَنَذِيرٗا...﴾

{Kuma ba Mu aika ka ba sai kana mai bãyar da bushãra, kuma mai gargaɗi} [Saba'i: 28]. Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿وَمَآ أَرۡسَلۡنَٰكَ إِلَّا رَحۡمَةٗ لِّلۡعَٰلَمِينَ107﴾

{Kuma Ba Mu aika ka ba sai kana mai rahama ga talikai} [al-Anbiyaa: 107]. Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿...وَقُل لِّلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡأُمِّيِّـۧنَ ءَأَسۡلَمۡتُمۡۚ فَإِنۡ أَسۡلَمُواْ فَقَدِ ٱهۡتَدَواْۖ وَّإِن تَوَلَّوۡاْ فَإِنَّمَا عَلَيۡكَ ٱلۡبَلَٰغُۗ وَٱللَّهُ بَصِيرُۢ بِٱلۡعِبَادِ﴾

{Kuma ka ce wa waɗanda aka bai wa littãfi da Ummiyyai: "Shin kun sallama?" To, idan sun sallama, haƙĩƙa, sun shiryu kuma idan sun jũya, to, kawai abinda ke kanka, shi ne iyarwa. Kuma Allah Mai gani ne ga bãyinSa}. [Aal Imran: 20]. Kuma - tsarki ya tabbatar maSa - Ya ce:

﴿تَبَارَكَ ٱلَّذِي نَزَّلَ ٱلۡفُرۡقَانَ عَلَىٰ عَبۡدِهِۦ لِيَكُونَ لِلۡعَٰلَمِينَ نَذِيرًا1﴾

{Albarka ta tabbata ga wanda Ya saukar da (Littãfi) mai rarrabẽwa a kan bãwanSa, dõmin ya kasance mai gargaɗi ga halitta} [al-Furƙan: 1].

Bukhari da Muslim sun ruwaito daga Jabir - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «An bani abubuwa biyar, waɗanda ba a baiwa wani daga cikin Annabawa a gabani na ba: An bani cin nasara ta hanyar tsoro (da ake jefawa abokan gaba) wata ɗaya gabanin haɗuwar mu, kuma aka sanya mini ƙasa ta zama wajen yin sallah na kuma abar yin tsarki, don haka duk wanda sallah ta riske shi cikin al'umma ta to sai ya yi ta, kuma an halarta min ganima, ba'a taɓa halartawa wani kafin ni ba, kuma an bani ceto, ya kasance ana aiko Annabi zuwa ga mutanensa kaɗai, ni kuwa an aiko ni zuwa ga mutane gaba ɗaya».

Wannan bayani ne fayyatacce da yake nuni akan gamewar manzancin (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - zuwa ga dukkan mutane, kuma manzancinsa ya share dukkanin shari’o’i da suka gabata, kuma duk wanda bai bi (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ba - kuma baiyi masa biyayyaba to kafiri ne mai laifi wanda ya cancanci uƙuba, (Allah) Maɗaukakin Sarki ya ce:

﴿...وَمَن يَكۡفُرۡ بِهِۦ مِنَ ٱلۡأَحۡزَابِ فَٱلنَّارُ مَوۡعِدُهُۥ...﴾

{Kuma wanda ya kafirta da shi daga jama'a to wuta ita ce makomarsa} [Hud: 17]. Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿...فَلۡيَحۡذَرِ ٱلَّذِينَ يُخَالِفُونَ عَنۡ أَمۡرِهِۦٓ أَن تُصِيبَهُمۡ فِتۡنَةٌ أَوۡ يُصِيبَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٌ﴾

{To waɗanda suke saɓa umarninsa su kiyayi kansu kada musiba ko fitina ta sauka a kansu ko kuma azaba mai raɗaɗi ta same su} [al-Nur: 63]. Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿وَمَن يَعۡصِ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ وَيَتَعَدَّ حُدُودَهُۥ يُدۡخِلۡهُ نَارًا خَٰلِدٗا فِيهَا وَلَهُۥ عَذَابٞ مُّهِينٞ14﴾

{Kuma wanda ya sãɓã wa Allah da ManzonSa, kuma ya ƙẽtare iyãkõkinSa, zai shigarda shi wuta, yana madawwami a cikinta, kuma yana da wata azãba mai walãƙantarwa} [al-Nisa'a: 14], Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿...وَمَن يَتَبَدَّلِ ٱلۡكُفۡرَ بِٱلۡإِيمَٰنِ فَقَدۡ ضَلَّ سَوَآءَ ٱلسَّبِيلِ﴾

{Kuma wanda ya musanya kãfirci da ĩmãni, to, lalle ne yã ɓace tsakar hanya} [al-Baƙara: 108], Kuma ayoyi da suka zo da wannan ma’anar suna da yawa.

Allah - tsarki ya tabbatar maSa - Ya haɗa biyayyar Manzo - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da biyayyarSa, kuma Ya bayyana cewa wanda ya yi imani da wanin Musulunci to shi mai hasara ne, ba za'a karɓa daga gareshi ba ko da sadaka ko fansa, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce:

﴿وَمَنْ يَبْتَغِ غَيْرَ الْإِسْلَامِ دِينًا فَلَنْ يُقْبَلَ مِنْهُ وَهُوَ فِي الْآخِرَةِ مِنَ الْخَاسِرِينَ85

{Kuma wanda ya nẽmi wanin Musulunci ya zama addini, to, bã zã a karɓa daga gare shi ba. Kuma shi a Lãhira yana daga cikin mãsu hasãra} [Aal- Imran: 85]. Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿مَنْ يُطِعِ الرَّسُولَ فَقَدْ أَطَاعَ اللَّهَ...

{Wanda ya yi ɗã'a ga Manzo, to, haƙĩƙa, yã yi ɗã'a ga Allah} [al-Nisa'a: 80]. Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿قُلْ أَطِيعُوا اللَّهَ وَأَطِيعُوا الرَّسُولَ فَإِنْ تَوَلَّوْا فَإِنَّمَا عَلَيْهِ مَا حُمِّلَ وَعَلَيْكُمْ مَا حُمِّلْتُمْ وَإِنْ تُطِيعُوهُ تَهْتَدُوا...

{Ka ce: "Ku yi ɗã'ã ga Allah kuma ku yi ɗã'ã ga Manzo. To, idan kun jũya, to, a kansa akwai abin da aka aza masa kawai, kuma a kanku akwai abin da aka aza muku kawai, Kuma idan kun yi masa ɗã'ã za ku shiryu} [al-Nur: 54]. Kuma Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:

﴿إِنَّ الَّذِينَ كَفَرُوا مِنْ أَهْلِ الْكِتَابِ وَالْمُشْرِكِينَ فِي نَارِ جَهَنَّمَ خَالِدِينَ فِيهَا أُولَئِكَ هُمْ شَرُّ الْبَرِيَّةِ 6

{Lalle ne waɗanda suka kafirta daga mutanen Littafi da mushirikai sana cikin wutar Jahannama suna madawwama a cikinta. Waɗannan su ne mafi ashararancin tãlikai} [al-Bayyinah: 6].

Muslim ya ruwaito a cikin Sahihinsa cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Na rantse da wanda raina yake a hannunSa, babu wani daga wannan al'umma Bayahude ko Nasara da zai ji wani abu game dani, sannan ya mutu bai yi imani da abinda aka aiko ni da shi ba, face sai ya kasance daga cikin 'yan wuta».

Kuma haƙiƙa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya bayyana da aikinsa da maganarsa ɓacin addinin wanda bai shiga addinin Musulunci ba, domin ya yaƙi Yahudawa da Nasara, kamar yadda ya yaƙi sauran kafirai, kuma ya karɓi jiziya daga wanda ya bayar daga cikinsu; har sai ba su hana isar da saƙo zuwa ga sauran su ba, muddin dai ba su hana wanda yake son shiga Musulinci ba daga cikinsu ba tare da tsoron mutanensa za su hana shi ko su tsare shi ko su kashe shi ba.

Bukhari da Muslim sun suwaito, daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Yayin da muke cikin masallaci sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya fito ya ce: Ku tafi zuwa ga Yahudawa". Sai muka fita tare da shi har muka zo gidan karatu, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya tashi, ya kira su sai ya ce: "Ya ku jama'ar Yahudawa, ku musulunta za ku tsira". Sai suka ce: Ka isar ya Abal Kasim. Sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wannan nake so, ku musulunta za ku tsira". Sai suka ce: Ka isar ya Abal Kasim. Sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wannan nake so". Sannan ya faɗa a karo na uku...» Hadisi.

Manufar ita ce: Cewa shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tafi zuwa ga masu addini cikin Yahudawa a cikin gidan karatunsu, sai ya kira su zuwa musulunci, kuma ya ce musu: «Ku musulunta za ku tsira». Ya kuma maimaita hakan a gare su.

Haka kuma: Ya aika da wasiƙa zuwa ga Hiraƙlu yana kiransa izuwa Musulinci, kuma yana ba shi labarin cewa idan ya ƙi, to zai ɗauki laifin duk waɗanda suka ƙi (shiga) musulunci saboda ƙin da ya yi. Haƙiƙa Bukhari da Muslim sun ruwaito a ingantattun littattafan su biyu, cewa Hiraƙlu ya ce, a kawo masa wasiƙar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, sai ya karanta, sai gashi a ciƙin wasiƙar: «Da sunan Allah Mai yawan rahama Mai yawan jin ƙai.

Daga Muhammad Manzon Allah zuwa ga Hiraƙlu sarkin Roma, aminci ya tabbata ga duk wanda yabi shiriya.

Bayan haka: Lalle ni ina kiranka da kira na Musulinci, ka musulunta za ka tsira, ka musulunta, Allah zai baka ladan ka sau biyu, idan kuma ka ƙi to laifukan Arisiyyun yana kanka. Kuma

﴿يَٰٓأَهۡلَ ٱلۡكِتَٰبِ تَعَالَوۡاْ إِلَىٰ كَلِمَةٖ سَوَآءِۭ بَيۡنَنَا وَبَيۡنَكُمۡ أَلَّا نَعۡبُدَ إِلَّا ٱللَّهَ وَلَا نُشۡرِكَ بِهِۦ شَيۡـٔٗا وَلَا يَتَّخِذَ بَعۡضُنَا بَعۡضًا أَرۡبَابٗا مِّن دُونِ ٱللَّهِۚ فَإِن تَوَلَّوۡاْ فَقُولُواْ ٱشۡهَدُواْ بِأَنَّا مُسۡلِمُونَ64﴾

Ka ce: 9Yã ku Mutãnen Littãfi! Ku taho zuwa ga kalma mai daidaitãwa a tsakã ninmu da ku; kada mu bauta wa kõwa fã ce Allah. Kuma kada mu haɗa kõme da Shi, kuma kada sãshenmu ya riƙi sãshe Ubangiji, baicin Allah." To, idan sun jũya bã ya sai ku ce: "ku yi shaida cẽwa, lalle ne mu masu sallamã wa ne) [Aal- Imran: 64]».

Sannan lokacin da suka ƙi, suka juya baya suka ƙi shiga Musulinci, sai (Annabi) -tsira da aminci Allah su tabbata gare shi- ya yaƙe su shi da sahabbansa - Allah Ya yarda da su - kuma (ma’aikin Allah) ya ɗora musu jiziya.

Domin tabbatar da ɓatan su da cewa suna kan addini na ƙarya bayan an shafe shi da addinin (Annabi) Muhammad -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi-; Allah Ya umarci musulmi da ya roƙi Allah a kowace rana da kowace sallah da kowace raka'a da Ya shiryar da shi hanya madaidaiciya ta gaskiya abar karɓa, wato shine: Musulunci, kuma Ya nisantar da shi daga hanyar waɗanda aka yi fushi da su, wato: Yahudawa da makamantansu waɗanda suka san suna kan kuskure kuma suka nace a kansa, Ya nisantar da shi daga hanyar ɓatattu waɗanda suke bautã ba tare da ilimi ba, kuma suna zaton suna kan hanyar shiriya, alhãli kuwa suna kan hanyar ɓatasũ ne: Kiristoci, da waɗanda suka yi kama da su daga sauran al'ummatai waɗanda suke bautã a kan ɓata da jahilci, Duka wannan: Domin Musulmi ya sani, sani na yaƙini cewa duk wani addini da ba Musulinci ba to ɓatacce ne, kuma duk wanda yake bautawa Allah ba ta (hanyar) Musulinci ba to ɓatacce ne, duk wanda bai ƙudirce hakan ba to baya cikin musulmai. Dalilai a kan wannan babi suna da yawa daga AlKur’ani da kuma Sunnah.

Ya zama wajibi a kan mai wannan maƙala - Abdul Fattah - ya gaggauta tuba, tuba tsaftacce, kuma ya rubuta maƙala inda zai bayyana tubansa, wanda ya tuba zuwa ga Allah tuba na gaskiya; Allah zai karɓi tubansa; saboda faɗin Allah - Maɗaukakin sarki -:

﴿...وَتُوبُوٓاْ إِلَى ٱللَّهِ جَمِيعًا أَيُّهَ ٱلۡمُؤۡمِنُونَ لَعَلَّكُمۡ تُفۡلِحُونَ﴾

{Kuma ku tuba zuwa ga Allah ya ku muminai baki ɗayanku ko kwa rabauta} [al-Nur: 31], Da faɗinSa - tsarki ya tabbatar maSa -:

﴿وَٱلَّذِينَ لَا يَدۡعُونَ مَعَ ٱللَّهِ إِلَٰهًا ءَاخَرَ وَلَا يَقۡتُلُونَ ٱلنَّفۡسَ ٱلَّتِي حَرَّمَ ٱللَّهُ إِلَّا بِٱلۡحَقِّ وَلَا يَزۡنُونَۚ وَمَن يَفۡعَلۡ ذَٰلِكَ يَلۡقَ أَثَامٗا68 يُضَٰعَفۡ لَهُ ٱلۡعَذَابُ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ وَيَخۡلُدۡ فِيهِۦ مُهَانًا69 إِلَّا مَن تَابَ وَءَامَنَ وَعَمِلَ عَمَلٗا صَٰلِحٗا فَأُوْلَٰٓئِكَ يُبَدِّلُ ٱللَّهُ سَيِّـَٔاتِهِمۡ حَسَنَٰتٖۗ وَكَانَ ٱللَّهُ غَفُورٗا رَّحِيمٗا70﴾

{Kuma waɗanda bã su kiran wani ubangiji tãre da Allah, kuma bã su kashe rai wanda Allah Ya haramta fãce da haƙƙi kuma bã su yin zina. Kuma wanda ya aikata wancan, zai gamu da laifuffuka,

A riɓanya masa azãba a Rãnar ƙiyãma. Kuma ya tabbata a cikinta yanã wulaƙantacce,

Sai wanda ya tũba, kuma ya yi ĩmãni, kuma ya aikata aiki na ƙwarai to, waɗancan Allah Yanã musanya miyãgun ayyukansu da mãsu kyau. Allah Ya kasance Mai gãfara Mai jin ƙai} [al-Furƙan: 68-70]. Kuma Saboda faɗin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: «Musulunci yana rusa abin da ya kasance gabaninsa, kuma tuba yana rusa abin da ya kasance gabaninsa». Kuma da faɗinsa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: «Mai tuba daga zunubi kamar wanda ba shi da zunubi ne».

Ayoyi da hadisai da suka zo da wannan ma’anar suna da yawa.

Ina roƙon Allah - subhanahu wa ta'ala - Ya nuna mana gaskiya gaskiya ce, Ya azurta mu bin ta, Ya kuma nuna mana ƙarya ƙarya ce Ya azurta mu nisantar ta, Ya kuma yi baiwa a gare mu da marubuci Abdul Fattah da dukkan musulmai da tuba na gaskiya, Ya kuma kare mu duka daga fitintinu masu ɓata da bin son zuciya da Shaiɗan, lalle Shi ne Majiɓincin wannan kuma Mai iko a kansa.

Allah Ya yi tsira da aminci ga Annabinmu Muhammad, da alayansa da sahabbansa, da wanda ya biyo bayansu da kyautatawa har zuwa ranar Alƙiyama.

***