أَحْكَامُ
الهَدْيِ وَالأَضَاحِي وَالتَّذْكِيَةِ
HUKUNCE-HUKUNEN HADAYA DA LAYYA DA YANKA
(هوسا)
HUKUNCE-HUKUNEN HADAYA DA LAYYA DA YANKA
GABATARWA
Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, tsira da aminci su tabbata ga wanda aka aiko shi rahama ga talikai, da alayensa da sahabbansa da wanda ya yi koyi da sunnarsa, ya kuma bi shiriyarsa har zuwa ranar sakamako, bayan haka:
Wannan taƙaitaccen saƙo ne, wanda ya ƙunshi mafi muhimmancin abinda musulmi yake buƙata a cikin hukunce-hukuncen hadaya da layya da kuma yanka, mun tattarashi dan masu ziyartar Harami biyu masu daraja maza da mata; domin su kasance cikin sani da fahimta game da al'amuran addininsu, muna roƙon Allah Mai karamci Mai baiwa Ya anfanar da shi, kuma Ya sanya shi mai kyau, kuma saboda Allah ne kaɗai, lallai Shi ne Mafi alherin wanda ake roƙo, kuma Mafi karamcin wanda ake fata.
Kwamitin Ilimi na Kungiyar hidimtawa Musulunci da yaruka daban daban.
HUKUNCE-HUKUNCEN HADAYA DA LAYYA
Hadaya: Duk abin da ake bayarwa ga Harami, kuma ake yankawa a cikinsa na dabbobin ni'ima da sauran su, an kira shi da haka; domin ana kai shi ga Allah ne - Maɗaukakin sarki -.
Al'udhiyya da dammar alif da kasrinta: Abin da ake yankawa saboda Allah ranar idi, da kuma ranakun Tashriƙ (yanyanan nama) don neman kusanci zuwa ga Allah.
Musulmai sun haɗu akan halaccinsu.
Mafi alherin hadaya: Raƙuma, sannan shanu, idan an fitar da su cikakku; saboda tsadar farashi, kuma amfanar talakawa da yawan nama ne, sannan tumakai.
Mafificin kowane jinsi shi ne mafi ƙiba, sannan mafi tsada; saboda faɗin Allah - Maɗaukakin sarki -:
﴿ذَٰلِكَۖ وَمَن يُعَظِّمۡ شَعَائِرَ ٱللَّهِ فَإِنَّهَا مِن تَقۡوَى ٱلۡقُلُوبِ32﴾ [الحج: 32[.
(Wancan ne. Kuma wanda ya girmama ibãdõdin Allah, to, lalle ne ita (girmamãwar) tanã daga ayyukan zukãta na ibãda) [al-Hajj: 32].
Ba ya isuwa sai ƙiba-ƙibar tunkiya, ita ce: Wacce ta cika wata shida, da mai fira daga wanda bashi ba kamar raƙuma da shanu da akuyoyi, mai fira daga raƙuma shine: Wanda ya cika shekara biyar, daga shanu kuma shine: Wanda ya cika shekara biyu, daga akuyoyi kuma shine: Wanda ya cika shekara ɗaya.
Kuma akuya tana isuwa a cikin hadaya ga mutum ɗaya, kuma a cikin layya tana isarwa mutum ɗaya da iyalan gidansa, kuma taguwa da saniya suna isuwa a cikin hadaya da layya ga mutum bakwai; saboda hadisin Jabir bin Abdullahi - Allah Ya yarda da su - ya ce: «Mun soke taguwa ɗaya ga mutum bakwai tare da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a shekarar Hudaibiyyah, haka kuma saniya ɗaya ga mutum bakwai». Kuma a cikin wani lafazin: «Mun fita tare da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - muna niyyar Hajji, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya umurce mu da muyi tarayya a raƙuma da shanu, kowanne bakwai daga cikinmu a cikin taguwa ɗaya». Kuma a cikin wani lafazin: «Munyi Hajji tare da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sai muka soke raƙumi ɗaya ga mutum bakwai, da saniya ɗaya ga mutum bakwai»1.
Da hadisin Abu Ayyuba al-Ansari - Allah Ya yarda da shi - lokacin da aka tambaye shi: Yaya akeyin layya a zamanin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sai ya ce: «Mutum ya kasance yana yin layya da akuya a madadinsa da kuma iyalan gidansa, sai su ci, su ciyar, har mutane suka fara yin alfahari da ita, sai ta zama kamar yadda kake gani»2.
Akuya ta fi ɗaya bisa bakwai na taguwa da kuma saniya.
Bamai isuwa a hadaya da layya sai kuɓutacce daga cuta da tawayar gaɓɓai da kuma rashin kiba; ba a yarda da dabba mai ido daya bayyananne ba, ko makaho, ko ramammiya wadda ba ta da ɓago a ciki, ko gurguwa wadda ba ta iya tafiya tare da lafiyayya, ko wadda aka rasa hakoranta daga asali, ko tsohuwa wadda hantsarta ta bushe daga madara saboda tsufa, kuma ba a yarda da mai cuta bayyananniya ba; saboda hadisin Barra'u Ibnu Azib - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya tsaya a cikinmu, ya ce: «Huɗu ba sa halatta a cikin dabbobin layya: Mai ido ɗaya wacce makantarta ta bayyana, da mara lafiya wacce rashin lafiyarta ya bayyana, da gurguwa wacce gurguncinta ya bayyana, da ramammiya wacce ba ta da ɓargo».3
Imam Tirmizi - Allah Ya yi masa rahama - ya ce: "Aiki ya tabbata akan wannan a wajen ma'abota ilimi"4.
Lokacin yankan hadayar Tamattu'i da dabbobin layya yana farawa ne bayan sallar idi har zuwa ƙarshen kwanakin Tashriƙ a bisa ingantaccen ra'ayi.
Ana son ya ci daga cikin hadayarsa idan ya kasance hadayar Tamattu'i ko ƙirani ne, da kuma daga layyarsa, yayi kyauta kuma yayi sadaka a raba kashi uku; saboda faɗin Allah - Maɗaukakin sarki -:
﴿... فَكُلُواْ مِنۡهَا وَأَطۡعِمُواْ ٱلۡبَآئِسَ ٱلۡفَقِيرَ﴾ ]الحج: 28[.
(Sai ku ci daga gare su, kuma ku ciyar da galabaitaccen matalauci) [al-Hajj: 28].
Amma hadayar gyara, itace: Wacce aka yi saboda aikata wani abu da aka haramta daga cikin abubuwan da aka haramta yayin harama ko saboda barin wani wajibi; to ba ya cin komai daga gareta.
Wanda ya yi nufin yin layya; idan goma ga watan Zul-Hijjah ya shiga; to kada ya yanki wani abu daga gashinsa ko farcensa har zuwa lokacin yanka dabbar layya; saboda faɗin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: «Idan goma ta shigo (ga watan Zul-Hijja), kuma ɗayanku yana son yin layya; to kada ya yanki wani abu daga gashinsa ko farcensa, har sai ya yi layya»5.
Idan ya aikata wani abu daga cikin wannan; to ya nemi gafarar Allah, babu fidiya a kan sa.
Siffar yanka hadaya da layya da sauran abin da ake yanka kamar haka:
1- Ba wanda zai yanka sai musulmi mai mayyazewa mai hankali, ko mazuwa littafi, kuma mai yankan yana nufin yin yanka, kada ya yanka ga wanin Allah, ba ya ambaton sunan wanin Allah, yana ambaton sunan Allah a lokacin yanka ko sokewa, kuma ya yanka da abin yanka mai kaifi banda haƙori da farce, ya zubar da jini a gurin da ya dace, kuma dole ne mai yankan ya kasance yana da izini a shari'a wajen yankansa6.
2- Ya zaɓi dabbar layya, dan haka yayi kwaɗayi a kan cikakkiyar dabbar layya; haƙiƙa: «Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi layya da raguna biyu masu farar fuska da baƙi-baƙi masu ƙaho, ya yanka su da hannunsa, ya ambaci sunan Allah, ya yi kabbara, kuma ya ɗora ƙafarsa akan fatun wuyayensu»7.
3- Kyautatawa ga abin yanka, a yi duk abin da zai hutar da ita a lokacin yanka, daga ciki: Yankan ya zama da abin yanka mai kaifi, kuma ya wuce shi a bigiren yankan da ƙarfi da sauri; domin abin da ake nema shi ne a gaggauta kashe rai a mafi kyawun fuskoki ba tare da azabtarwa ba; saboda hadisin Shaddad ɗan Aus - Allah Ya yarda da shi - ya ce: "Abubuwa biyu na haddace su daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Lallai cewa Allah Ya rubuta kyautayi akan kowane abu, to idan zakuyi kisa to ku kyautata kisan, idan zakuyi yanka to ku kyautata yankan, kuma ɗayaku ya wasa wuƙarsa, don ya hutar da abin yankansa»8.
Ba'a son ya wasa wuƙa alhali dabba tana kallonsa; saboda abin da ya zo daga Ibn Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yayi umarni da a wasa wuƙaƙe, kuma a ɓoyesu daga (ganin) dabbobi, sai ya ce: «Idan ɗayanku zai yanka; to yayi gaggawa»9.
4- Idan dabbar layya ta kasance daga cikin raƙuma ne; to ya yanka shi a tsaye, hannunsa na hagu a ɗaure; saboda hadisin Abdullahi Ibn Umar - Allah Ya yarda da su -: "Ya zowa wani mutumin da ya durƙusar da taguwarsa zai soketa sai ya ce: Ka tasheta a tsaye a ɗaure sunnar (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -"10.
5- Idan dabbar layya ta kasance ba daga cikin raƙuma ba ne; to ya yanka ta a kwance a gefen hagunta, kuma ya ɗora ƙafarsa akan fatar wuyanta; dan ya samu tabbata daga gareta; saboda hadisin Anas - Allah Ya yarda da shi - ya ce: «Manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya yi layya da raguna biyu, masu launin baƙi da fari, masu ƙahonni, ya yanka su da hannunsa, ya ambaci sunan Allah, ya yi kabbara, kuma ya ɗora ƙafarsa a kan fatar wuyansu»11.
6- Ambatan sunan Allah a lokacin yanka da kuma sokewa, kuma ita wajiba ce, saboda faɗin Allah - Maɗaukakin sarki -:
﴿فَكُلُواْ مِمَّا ذُكِرَ ٱسۡمُ ٱللَّهِ عَلَيۡهِ إِن كُنتُم بِـَٔايَٰتِهِۦ مُؤۡمِنِينَ118﴾ ]الأنعام:118[
(Sabõda haka ku ci daga abin da aka ambaci sũnan Allah kansa, idan kun kasance mãsu ĩmãni da ãyõyinSa) [al-An'am: 118].
da kuma faɗin Allah - Maɗaukakin sarki -:
﴿وَلَا تَأۡكُلُواْ مِمَّا لَمۡ يُذۡكَرِ ٱسۡمُ ٱللَّهِ عَلَيۡهِ وَإِنَّهُۥ لَفِسۡق وَإِنَّ ٱلشَّيَٰطِينَ لَيُوحُونَ إِلَىٰٓ أَوۡلِيَآئِهِمۡ لِيُجَٰدِلُوكُمۡۖ وَإِنۡ أَطَعۡتُمُوهُمۡ إِنَّكُمۡ لَمُشۡرِكُونَ121﴾ ]الأنعام: 121.[
(Kada ku ci daga abin da ba a ambaci sũnan Allah ba a kansa, Kuma lalle ne shĩ fãsiƙanci ne. Kuma lalle ne, shaiɗãnu, haƙĩƙa, suna yin ishãra zuwa ga masõyansu, dõmin su yi jãyayya da ku. Kuma idan kuka yi musu ɗã'a, lalle ne kũ, haƙĩƙa, mãsu shirki ne) [al-An'am: 121].
Kuma Saboda faɗin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: «Duk abinda ya zubar da jini kuma aka ambaci sunan Allah a kansa; to kuci shi, muddin ba haƙori ba ne ko farce»12.
An so yin kabbara: (Allahu Akbar) tare da ambaton Allah; saboda hadisin Jabir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na halarci babbar sallah tare da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a filin sallah, lokacin da ya gama huɗubarsa sai ya sauko daga mimbarinsa, sai aka kawo rago, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yanka shi da hannunsa, kuma ya ce: «Da sunan Allah, Allah ne mafi girma, wannan daga gare ni ne da kuma wanda bai yi layya ba daga cikin al'ummata»13.
7- Yanke maƙogwaro, da maɗaciya, maƙogwaro da jijiyoyi, da zubar da jini: Imam Ibn Baaz - Allah Yayi masa rahama - ya ce: (Lallai yankan shari'a na raƙuma da shanu da tumaki: yana da halaye uku:
Hali na farko: Mai yankan ya yanke: Maƙogwaro, da maɗaciya, da jijiyoyi, wannan shi ne mafi cikar yanka kuma mafi kyansa, idan an yanke waɗannan abubuwa huɗu; to yankan ya halatta a wurin dukkan malamai.
Hali na biyu: A yanke maƙogwaro da maɗaciya da ɗaya daga cikin jijiyoyi; wannan ya halatta kuma ingantacce ne mai daɗi, duk da bai kai na farko ba.
Hali na uku: A yanke maƙogwaro da maɗaciya kawai kawai ba tare da jijiyoyin wuya ba, wannan ma ingantacce ne, kuma wasu daga cikin malamai sun faɗi haka, hujjarsu ita ce faɗin Annabi - tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi -: «Duk abinda ya zubar da jini kuma aka ambaci sunan Allah a kansa to kucishi, banda haƙori da farce»14. Wannan shi ne abin zaɓi a wannan mas'alar15.
Allah ne abin roƙo Ya amfane mu da abin da muka sani, kuma Ya sanar da mu abin da zai amfane mu; lallai cewa Shi Mai yawan kyauta ne kuma Mai girma, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabinmu Muhammad da iyalansa da amincin Allah mai yawa.
Tirmizi da Ibn Maja ne suka rawaito shi.
Abu Daud ya rawaito shi, da Tirmizi da Nasa'i da Ibnu Majah.
Tirmizi ne ya rawaito shi.
Muslim ne ya rawaito shi.
Ahkamul udhiyya na mai yawan sani Muhammad bn Uthaymin, (shafi na 56 – 87).
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.
Muslim ne ya rawaito shi.
Ahmad da Ibn Maja ne suka rawaito shi.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.
Abu Dawud ne ya ruwaito shi, da Tirmizi, kuma Albani ya ingantashi.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.
Ka duba: Majmu'u fatawa Bn Baaz (26/18).
Muslim ne ya rawaito shi.